Matsayin Gidajen Annabawa A Cikin Kur’ani
Gidajen annabawa da manyan bayin Allah suna da wani matsayi na musamman, wannan kuwa a fili yake matsayin da suke da shi bai shafi wani abu na duniya ba ne, domin idan da haka ne, gidajensu ba su da wani bambanci da sauran gidajen mutane domin an gina su ne da yumbu da tubali kamar na kowa. Wadannan gidaje suna da wannan matsayi ne sakamakon mutane masu matsayi da suka zauna a cikinsu.
Kur’ani mai girma[57] yana siffanta hasken ubangiji da fitila mai haske ta yadda yake haske kamar tauraruwa. A ayar da take biye ma wannan aya kuwa ya nuna cewa wurin wannan haske yana gidajen wasu mutane masu girma wadanda suke ambaton Allah a ciki safiya da yamma.[58]
A cikin wannan aya jimlar da take cewa "Ana tasbihinsa safiya da yamma, tana nuna dalilin da ya sa aka daukaka wadannan gidajen wadanda aka ambata a cikin ayar da ta gabata. A ayar da take biye mata kuwa an siffanta masu yin ibada a cikin wadannan gidaje ne, inda yake cewa: "mutane ne wadanda kasuwanci ba ya shagaltar da su daga ambaton Allah da tsayar da salla, domin suna jin tsoron ranar da zukata da idanu suke jujjuyawa suna tsorata.[59]
Wannan aya tana bayani ne a kan girma da daukakar gidajen da ake zikirin Allah ake kuma tsarkake shi a cikinsu. A nan dole ne mu yi bayani a kan abubuwa guda biyu kamar haka:
1-Me ake nufi da gidaje a cikin wannan aya?
Masu tafsiri sun yi sabani a kan ma’anar wannan ayar ta yadda kowane ya dauki daya daga cikin ma’anonin kansa:
A-Ana nufin gidaje a cikin wannan aya da masallatai guda hudu
B-Ana nufin dukkan masallatai ne a cikin wannan aya
C-Ana nufin gidajen Manzo ne
D-Masallatai da gidajen Manzo
A cikinwadannan ma’anoni da aka ambata a kasa ma’ana ta uku ce kawai zata iya dai-dai kamar yadda zamu kawo dalilai da suke karfafa hakan.
1-Ta fuskar lugga kalmar Buyut jam’i ne na bait wato gidan kwana. Ibn manzur ya tafi a kan cewa bait yana nufin gidan mutum. Ragib kuwa yana cewa bait shi ne inda mutum yake fakewa da dare. Amma mawallafin "almunjid kuwa cewa ya yi, ma’anar bait tana nufin wurin zama wanda ya hada da hema da gidan da aka gina kasa da tubali.
Saboda haka fassara kalmar bait da masallaci wanda yake wurin ibada na kowa da kowa bai inganta ba, domin kuwa ba wurin da mutum yake fake wa ba ne da daddare. Saboda haka idan ma har ya inganta, amma abin zai zo ga kwakwalwar mutum shi ne gidan kwana, don haka idan har yana nufin masallaci ne ana bukatar abin zai nuna hakan. Ba tare da hakan ba, ba za a karbi wannan ma’ana ba.
Da wani kalamin ma Bait ya samu asali ne daga baituta wato mutum ya tsaya wani wuri har zuwa safe. Idan har ana mabata gidan mutum da bait saboda mutum yana kwana a cikin wannan gida ne har zuwa safe. Tare da kula da wannan ma’ana ta kalamar bait, fassara ta da ma’anar masallaci yana bukatar abin da yake nuna hakan, ba tare da wannan ba ba za a karbi wannan fassara ba.
2-Kur’ani duk lokacin da zai yi magana a kan wurin da al’umma suke bauta yana amfani ne da kalmar "masjid" ko "Masajid" ne. Sakamakon haka ne wannan kalma an yi amfani da ita sau 28 acikin Kur’ani mai girma. Amma duk lokacin da za a yi nagana a kan wurin da mutane suke kwana a kan yi amfani da kalmar "Maskan, Ma’awa" ne. Sannan an yi amfani da kalmar bait ta fuskar jam’i ko tilo. Saboda haka wannan kalma ta zo sau 66 a cikin Kur’ani da wannan manufa, sakamakon haka muna iya fahimata cewa a cikin Kur’ani kalmar "Masjid" da "bait" ba suna nufin ma’ana guda ba ne. saboda haka idan aka nemi fassara su da ma’ana guda zai zama da’awa ba tare da dalili ba.
Idan Kur’ani ya kira masallacin Ka’aba da "baitullahi"[60] ba don yana wurin bautar Allah ba ne, domin kuwa mun san cewa Ka’aba alkibla ce ta masu bautar Allah ba wurin da ake ibada ba. Saboda haka hada sunan Allah da wannan wurin kawai yana nuna girmamawa ne, kai ka ce wannan gida na Allah ta yadda za a girmama shi girmamawa ta musamman.
3-Akwai muhimmin bambanci tsakanin masallaci da gida, Bait ana nufin bangaye guda hudu da aka yi wa rufi, amma masjid kawai bangaye guda hudu ne, wato rufi ba sharadi ba ne kafin ya zama masallaci. Da yawan akan gina masallatai a wuraren da suke da zafi ba tare da rufi ba, wanda daya daga cikinsu shi ne masallacin ka’aba, alhalin kuwa gidan da mutum yake kwana yana bukatar rufi.
Wannan aya da zata zo a kasa tana bayar da sheda a kan bukatar gida daga rufi:
"Ba don hikimar Allah ta yi rigaye ba akan cewa komai zai kasance bai daya, da mun sanya gidajen wadanda suka kafirce wa Ubangiji mai rahama masu rufi da azurfa da tsanin da suke amfani zuwa sama".[61]
Wannan aya tana bayyana cewa "bait" sabanin "Masjid" yana da rufi, sannan ba don wata maslaha ba da Allah madaukaki ya bambanta gidajen kafirai da na muminai ta yadda zai sanya gidajen Kafirai rufinsu ya zama na azurfa, amma sai bai yi hakan ba.
4-Jalaluddin Suyudi ya ruwaito daga Anas bn Malik Yana cewa: Yayin wannan aya wadda take cewa "A cikin gidajen da Allah ya yi Umarni da a daukaka….". Sai ya karanta a cikin masallaci, sai wani daga cikin sahabban Manzo ya mike ya tambayi Manzo me ake nufi da wadannan gidaje?
Sai Manzo ya amsa masa da cewa: Ana nufin gidajen Annabawa, a wannan lokaci sai Abubakar ya mike ya ce: Ya nuna gidan Ali da Fatima (A.S) ya ce wadannan gidajen suna cikin wadanda Allah ya yi izini da daukaka su?. Sai Manzo (S.A.W). ya amsa masa da cewa: E, suna ma daga cikin mafi daukakarsu.[62]
Imam Bakir (A.S) yana cewa: Abin da ake nufi da gidaje a cikin wannan aya shi ne, gidajen Annabawa da gidan Ali (A.S)[63]
Bisa dogaro da wadannan dalilai muna iya fahimtar cewa abin da ake nufi da gidaje a cikin wannan aya ta cikin Suratun Nur shi ne gidajen annabawa da waliyyan Allah, sakamakon tasbihi da tsarkake Allah da ake yi a cikinsu yake da wani matsayi na musamman, kuma Allah ya yi izini da yin kokari wajen a daukaka su.
5-Sannan dalili wanda yake a fili a kan cewa abin da ake nufi da gidaje a cikin wannan aya su ne, ayoyi guda biyu da suka zo kamar haka: Allah madaukaki yana yi wa Annnabi Ibrahim da matarsa magana kamar haka:
A-"Rahmar Allah da albarkarsa ta tabbata a gare ku ya ku ma’abota gida[64];
B-Allah Kawai ya yi nufi ya tafiyar muku da kazanta yaku Ahlul Bait, ya kuma tsarkake ku tsarkakewa[65]; Kai ka ce wadannan gidaje su ne cibiyar hasken ubangiji.
Tare da kula da wadannan dalilai guda biyar da muka kawo muna iya cewa: Masati da daukakar wadannan gidaje sakamakon wadanda suke zaune a cikinsu ne, suna tasbihin ubangiji suna tsarkake shi. A hakikanin gaskiya wannan aya tana magana ne dangane da gidaje irin gidajen Annabi Ibrahim da Manzo (S.A.W). Wannan kuwa sakamakon tasbihi da tsarkake ubangiji da ake yi a cikinsu. Shi ne ya sanya Allah madaukaki ya daga martaba da darajarsu.
Mai yiwuwa a ce: Karkashin wannan aya ana cewa: "Yana tasbihinsa a cikinsu safiya da yamma": wato abin da ake nufi da "Buyut" Masallatai, domin kuwa musulmin farkon zuwan musulunci sun kasance suna halarta sallar jam’i baki dayansu. saboda haka tasbihi da tsarkake ubangiji ana yin sa ne a cikin masallaci.
Amma wannan fahimta ba daidai ba ce, domin kuwa ana aiwatar da sallar wajibi ne kawai a cikin masallatai, sannan mustahabbi ne a gabatar da sauran sallolin mustahabbi a cikin gidaje. Sannan ya kamata ma mutum ya kasa ibadarsa zuwa gida biyu, wato wani bangare na farilla ya aiwatar da su a cikin masallaci, sannan bangaren nafiloli ya gabatar da su a cikin gida.
Mai yiwuwa wasu suga wannan bai inganta ba, amma hakikanin al’amarin haka yake domin kuwa ruwayoyi da dama sun karfafa hakan. Muslim a cikin sahih dinsa, ya kawo babi mai zaman kansa wanda yake nuna mustahabbancin sallar nafila a cikin gida. A kan haka ya ruwaito ruwayoyi da dama, amma a nan kawai zamu kawo wasu a matsayin misali:
Manzo mai tsira da aminci yana cewa: "Fiyayyar sallar mutum a cikin gidansa, sai dai sallolin wajibi"[66].
Wannan ruwaya tana nuna mana cewa Manzo (S.A.W) da sauran sahabbansa suna yin sallolinsu na nafila a cikin gidajensu, sakamakon haka ne gidajen annabawa da na salihan bayi suka zama wurin zikirin Allah da tsarkake shi. Sannan kuma dalilin wannan ne Allah ya ba da izini a kan daukaka su.
A yanzu dole ne mu ga me ake nufi daga matsayin wadannan gidaje! me ake nufi da daukaka wadannan gidaje?
A baya mun yi bayanin cewa, kafa hujja da wannan aya yana bayyanar da abubuwa guda biyu ne. Abu na farko kuwa shi ne, bayyanar da ma’anar "buyut" wanda muka yi cikakken bayaninsa a baya, yanzu lokaci ya yi da zamu yi bayani a kan abu na biyu wanda shi ne daukaka wadannan gidaje da Allah yake horo da shi.
Hakika kalmar "Rafa’a" cikin Kur’ani tana zuwa ne da ma’anar daga gini kamar yadda ta zo a cikin wannan ayar: "Shin halittar su ita ce tafi wahala ko kuwa sama wadda ya gina ta?! Sannan ya daga rufinta ya kuma daidaita ta?![67]
Amma kalmar "rafa’a" a cikin wannan aya ba yana nufi yin gini ba, domin kuwa an dauka cewa akwai gida ne, Kur’ani yana magana a kan siffofin wannan gida ne. saboda haka abin da ake nufi da wannan kalma a cikin wannan aya shi ne daga matsayinsu da girmama su, mafi yawan masu tafisiri sun dauki wannan ma’ana duk da cewa wasu daga ciki sun tafi a kan ma’anar da muka ambata a baya. [68]
A bayyane zamu iya cewa: Wuraren da Allah yake ambatar "Buyut" yana nufin gidajen da bayin Allah suke kwana suna yin tasbihin ubangiji kuma suna tsarkake shi. Saboda haka daukaka wadannan gidaje ba ya nufin daga gininsu ko rufinsu ba ne, abin da ake nufi shi ne daga matsayi da martabarsu. Daya daga cikin wannan girmamawa da daga matsayinsu kuwa shi ne ya zamana an tsarkake su daga dukkan wata kazanta, sannan duk inda suka dan lalace a gyara su.
Dukkan wannan aiki za a yi shi ne saboda girmama wadanda suka kasance a cikin wadannan gidaje suna tasbihin ubangiji suna salloli kuma ba su kin fitar da zakka, domin girmama wadannan mutane ne Allah ya yi horo da a girmama wadannan gidaje, sannan a kare su daga rushewa.
Kowa ya san cewa an rufe Manzo (S.A.W) a cikin gidansa, wato a wurin da ya kasance yana ambaton Allah da yabonsa. Saboda haka tare da bin hukuncin wannan aya gidan Manzo ya cancanci girmamawa da daukaka matsayinsa, sannan a kiyaye shi daga kowane irin rushewa da lalacewa. Sannan kuma a kaurace wa sanya masa duk wani nau’i na kazanta, kai da yawa daga bangarorin Madina kaburburan manyan bayin Allah ne. Kamar yadda ya zo a cikin ingantattun ruwayoyi sayyida Fadima (A.S) ita an rufe ta ne a cikin gidanta[69]
Haka nan Imam Hadi da Imam Askari (A.S) an rufe su a gidajensu wadanda suka kasance suna ibada da zikirin ubangiji a cikinsu. saboda haka wadannan gidaje bisa la’akari da wannan aya sun cancanci a daukaka su, sannan dole ne a kauce wa rusa su domin ya saba wa wannan aya. A unguwar Bani Hashim a garin Madina shekaru kadan da suka gabata gidan Imam Hasan da Husain (A.S) da makarantar Imam Sadik (A.S) sun kasance a wadannan wurare, Marubucin wannan littafi shi kansa ya ziyarci wadannan wurare, amma abin bakin ciki tare da fakewa da fadada masallacin Manzo duk an rusa wadannan wurare masu dimbin tarihi da albarka. Duk da cewa ana iya yin wannan aiki na fadada masallacin Manzo (S.A.W) ba tare da rusa wadannan wurare ba.