FASALI NA HUDU
Tarbiyyantarwar Ahlul Baiti
Abubuwan Da Ahlul Baiti Suka Tarbiyyantar Da Mabiyansu A Kansu:
Ahlul Baiti (AS) sun sani tun tuni cewa hukumarsu ba za ta taba dawowa garesu a rayuwarsu ba kuma su da shi’arsu zasu ci gaba da zama a karkashin shugabannin da ba su ba, wadanda suke ganin wajabcin kawar da su da dukkan wata hanyar takurawa da tsanantawa. Don haka a bisa dabi’a suka riki “takiyya” a Addini da dabi’a garesu da su da mabiyansu matukar zata kare masu jininsu kuma ba zata munana wa wasu ba ko Addini, saboda su iya wanzuwa a cikin wannan rutsitsi mai ruruwar fitina mai ingizawa ga kiyayya da Ahlul Baiti (AS). Don haka ya zama tilas suka koma ga koya wa mabiyansu hukunce-hukuncen Shari’ar Musulunci da kuma fuskantar da su fuskantarwa ta Addini ta gari, da kuma sanya su kan hanya ta tafarkin zamantakewa da jama’a mai amfani domin su zama misalai na musulmi na gari mai adalci.
Tafarkin Ahlul Baiti (A.S) wannan dan littafi ba zai iya kawo dukkansu ba, akwai littattafan hadisai masu girma da suka dauki nauyin yada ilimin addini, sai dai ba laifi mu yi nuni da wasu da suke kama da babin akida cikin abin da ya shafi tarbiyyantarwarsu ga shi’arsu da tarbiyyar da zata kai su ga shiga cikin al’amuran zamantakewar al’umma mai amfani, suke kuma kusantar da su zuwa ga Allah madaukaki suke kuma tsarkake zukatansu daga dauda zunubai da laifuffuka, kuma suke mayar da su adalai masu gaskiya. Kuma magana ta gabata a game da takiyya da take daya daga tarbiyyar mai amfani ta zamantakewarsu, kuma zamu ambaci sashen abin da ya shafe mu na wadannan ladubban a nan.
34-Dukufa Kan Yin Addu’a
Annbin Allah (S.A.W) Ya ce: “Addu’a makamin Mumini ce, kuma jigon Addini ce kuma hasken sammai da kasa ce”. Shi ya sa ta zama daga siffofin shi’a da suka kebantu da su, hakika sun wallafa abin da ya kai gomomi na manya da kananan littattafai game da falalarta da ladubbanta, da kuma addu’o’in da aka rawaito daga Ahlul baiti (A.S). Kuma an rabuta abin da manzo da Ahlul Baiti (A.S) suke gurin cimma masa na kwadaitarwa a kan yin addu’a a cikin wadannan littattafai. Har ma ya zo daga garesu cewa: “Addu’a ita ce mafifciyar ibada”. Da kuma cewa: “Mafi soyuwar aiki a bayan kasa a gun Allah madaukaki ita ce addu’a”. Kuma ya zo cewa: “Addu’a tana mayar da kaddara da bala’i”. Da kuma cewa: “Addu’a waraka ce daga dukkan cuta”.
Kuma ya zo game da Amirul Muminin Ali Dan Abi Talib (AS) cewa shi ya kasance mutum ne ma’abocin addu’a -Mai yawan addu’a- hakan nan ya kamata shugaban masu Tauhidi kuma shugaban mabiya Ubangiji ya kasance. Kuma addu’o’insa sun zo kamar yadda hudubobinsa suke a matsayin alama daga almomin balagar magana da fasaharta kamar addu’ar Kumail Bn Ziyad wacce ta kunshi ilimin sanin Ubangiji da fuskantarwar Addini, da kuma abin da ya dace ya zamanto madaukakin tafarki ga musulmi na gari.
Hakika addu’o’in da suka zo daga Annabi (S.A.W) da Ahlul Baiti (AS) su ne mafificin tsarin rayuwa ga musulmi -idan ya yi tunani a kansu- sukan cusa masa karfin imani da karfin akida da ruhin sadaukar da kai a tafarkin gaskiya, da sanin kansa, da dadin ganawa da Allah da yankewa zuwa gareshi, kuma tana lakkana masa abin da ya wajaba a kan mutum ya san shi a addininsa da kuma abin da yake kusantar da shi zuwa ga Allah Madaukaki, ya kuma nesata shi daga barna da son zuciya da bidi’a batacciya. A takaice dai wadannan addu’o’in sun kunshi sanin Addini ta fuskar kyawawan dabi’u da tsarkake zukata, ta wata fuskar kuma sun kunshi akidar Musulunci, kai ita ce ma mafi girman madogarar ra’ayoyin falsafa, da binciken ilimi dangane da sanin Ubangiji da kyawawan dabi’u.
Idan da mutane sun iya kuma ba dukkansu ne masu iyawa ba, da sun shiriyu da shiriyar da wadannan addu’o’in suke kushe da ita a cikin abin da ta kunsa madaukaka, da ba zaka samu irin wannan fasadin da kasa take cike da shi ba, kuma da wadannan rayukan da sharri ya yi musu katutu sun yi shawagi a sammai domin jin gaskiaya, sai dai yaya dan Adam zai saurari maganar salihai da masu kira zuwa ga gaskiya alhalin fadinsa madaukaki ya nuna hakikaninsu da fadinsa: “Hakika rai mai umarni da mummuna ce”. Surar Yusuf: 53. “Kuma mafi yawancin mutane ko da kayi kwadayi ba masu shiryuwa ba ne”. Surar Yusuf: 103.
Na’am abin da ya kawo kafuwa da damfaruwar munanan ayyuka ga mutum shi ne rudin kansa da jahiltar munanan ayyukansa da yaudarar kansa cewa shi yana aikata aikinsa, sai ya zalunci ya ketare iyaka, ya yi karya, ya yi kage, ya bi sha’awarsa yadda ransa yake so, tare da haka yana yaudarar kansa da cewa shi bai yi komai ba sai abin da ya dace ya aikata, kuma ya runtse dagangan daga munin abin da ya aikata ya kuma karanta kuskurensa a idanunsa. Wadannan addu’o’in daga hadisai da suke samun karfafa daga tushen wahayi sun yi kokarin su sanya mutum ya koyi zargin kansa da kadaita zuwa ga Allah (S.W.T), domin su cusa masa furuci da kuskurensa da kuma cewa shi mai aikata zunubi ne wanda ya wajaba gareshi ya yanke zuwa ga ubangijinsa domin neman tuba da gafara. Kamar misalin fadin mai addu’a a cikin Addu’ar Kumail:
“Ya Ubangijina! Ya Majibincina! Ashe zaka gudanar da hukunci a kaina a kan abin da na bi son raina a cikinsa, kuma ban kiyaye kawatarwar abokin gabata ba a cikinsa, don haka ya rude ni da abin da ya so, kuma hukuncinka ya taimake shi a kan haka, har na ketare wasu daga cikin dokokinka saboda abin da ya gudana gare ni na daga hakan, kuma na saba wa wasu daga umarce-umarcen ka.”
Babu shakka cewa misalin irin wannan ikrarin a cikin kadaici ya fi sauki ga mutum a kan ikarari a cikin jama’a duk da kuwa yana daga cikin mafi tsananin halaye ga rai koda kuwa tsakaninsa ne da ransa. Idan da wannan hali zai samu ga mutum da ya samu sha’ani mai girma na kamala wajan rage takamar kansa mai sharri da tarbiyyantar da ita akan alheri. Duk wanda yake son tarbiyyar zuciyarsa to babu makawa ya koyar da ita kadaitaka da `yantaccen tunanin domin yi mata hisabi, kuma mafificiyar hanyar wannan kadaitakar ita ce dukufa a kan karanta wadannan addu’o’in da aka samo daga ruwayoyi wadanda ke ratsa zuciya kamar karanta addu’ar Abi Hamza Assumali (R.A.)
“Ya Ubangiji ka rufe ni da suturcewarka, ka yafe mini zargina da girman fuskarka”. Yi tunani a kan wannan kalma, “Ka rufe ni” a cikinta akwai abin da yake tayar wa zuciya kwadayin suturce abin da ta tattara a kai na mummunan aiki, domin mutum ya fadaka, a kan wannan al’amari ta yanda kuma zai san haka idan ya karanta wannan bayan waccan:
“Idan da yau wani baicin kai ya san da zunubina to da ban aikata ba kuma da na tsoraci gaggauta ukuba da na nisanci zunubin”. Wannan irin ikrari daga cikin zuciya da kuma fadaka zuwa ga kwadayin suturce abin da yake da shi na daga munana yana tayar da kwadayin neman gafara da yafewa daga Allah (S.W.T) don gudun kada ya tozarta shi a gurin mutane idan da Ubangiji ya so ya yi masa ukuba a nan duniya ko kuma a lahira a kan ayyukansa, sai mutum ya dandani dadin addu’ar asiri da zance da Allah a asirce, ya yanke ya koma ga Allah ya yi godiya gare shi, da ya yi masa afuwa baicin yana da kudura amma bai fallasa shi ba yayin da yake cewa:
“Godiya ta tabbata gareka a kan hakurinka bayan saninka da yafewarka bayan kudurarka”. Sa’annan kuma addu’ar ta sake nuna wa rai tafarkin neman uzuri daga abin da ta yi sakaci dangane da shi saboda wannan afuwa da hakuri daga gare shi (S.W.T) domin kada alakar da take tsakanin bawa da Ubangijinsa ta yanke, kuma domin koya wa bawa cewa sabonsa ba wai don kafirce wa Allah ba ne ko kuma wulakanta umarninsa yayin da yake cewa:
“Kuma hakurinka gare ni yana dauka ta yana ja na zuwa ga saba maka kuma Suturcewarka na kira na zuwa ga karancin jin kunya, kuma sanina game da yalwar rahamarka da girman afuwarka yana gaggautar da ni zuwa ga kifuwa a kan abubuwan da ka haramta”.
Wannan shi ne tsarin salon addu’ar a ganawa ta asirce ta tsakake zukata, da saba musu da da’a da barin aikata sabo. Wannan littafi ba zai wadatar ba ya kawo irin wadannan misalai fiye da haka ga su yawan gaske. Salon kafa tattauna da Ubangiji domin neman afuwa da gafara yana kayatar da ni kamar yadda ya zo a Addu’ar Kumail Bn Ziyad:
“Kuma kaicona! Ya shugabana majibincina! Ashe ka sallada wuta a kan fuskokin da suka kifu ga girmanka suna masu sujada, da kuma a kan harsunan da suka yi furuci da gasgatawa, sannan kuma yabo da godiyarka, da kuma a kan zukata da suke neman ilimi game da kai har suka zamanto masu tsoro, da kuma gabobi da suka yi kokari zuwa guraren ibadarka suna masu biyayya, suka kuma yi ishara ga afuwarka suna masu mika wuya? Ba haka zato yake game da kai ba, ba kuma mune muka fi sanin falalarka ba.”
Ka maimaita karanta wannan fakara sannan ka yi tunani game da taushin wannan irin kafa hujjar da kololuwar fasaharsa da azancin bayaninsa, a lokaci guda yana mai sanya wa zuciya furuci da takaitawarta ga ibada kuma tana cusa mata rashin debe tsammani daga rahamar Allah da baiwarsa, sa’annan kuma tana yi wa zuciya magana da zance na tausasawa, ta wani bangare a boye domin ya cusa mata sanin manyan wajibanta, domin tana kaddara cewa ita dama ta riga ta ba da wadannan wajibai baki daya, sannan kuma tana koya wa mutum cewa da wadannan ayyukan ne yake cancantar falalar Allah da gafararsa, wannan kuwa wani abu ne da kan zaburar da mutum ya koma ga zuciyarsa don ya aikata abin da ya wajaba a kansa ya aikata idan har bai aikata shi ba.
Karanta wani salon addu’ar da a ke neman uzuri a cikin ita wannan addu’ar da cewa: “Ya shugabana majibincina! Ka sani ina iya hakuri a kan azabarka amma ta yaya zan yi hakuri a kan rabuwa da kai! Kuma ko da na iya hakuri a kan zafin wutarka amma yaya zan yi hakuri a kan rashin dubi zuwa ga girmanka!”.
Wannan wani irin cusa wa zuciya jin dadin samun kusanci da Allah (S.W.T) da duba zuwa ga karamcinsa da kudurarsa ne don soyayya da bege gare shi da kuma nuna cewa wannan irin jin dadin ya kamata ne ya kai ga darajar da tasirin barinsa a wajan rai ya yi zafin wuta azaba. Idan muka kaddara cewa mutum na iya jure zafin wuta to da ba zai iya hakuri a kan waccan rabuwar ba, kamar kuma yadda daga wannan bangaren addu’ar za a fahinci cewa wannan soyayyar da jin dadin na kusanci da abin kauna abin bauta shi ne mafificin mai ceto ga mai zunubi a gurin Allah yadda zai yafe ya yi masa rangwame. Mamaki da kaskantar da kai ga Mai girma, Mai hakuri, Mai karbar tuba, Mai gafarta zunubi na taushin wannan salo ba zai buya ba.
Babu Iaifi mu rufe wannan bayani da kawo takaitacciyar addu’a da ta kunshi kyawawan dabi’u da kuma abin da ya kamata kowace gaba ta mutum ko kowanne ya sifantu da su na daga siffofi kyawawa ababan yabo:
“Ya Allah ka arzuta mu da muwafakar da’a da nesantar sabo, da gaskiyar niyya, da sanin abubuwa masu alfarma, kuma ka girmama mu da Shiriya da tsayuwa daidai da daidaita harsunanmu da daidaito da hikima, ka cika zukatanmu da ilimi da sani, ka tsarkake cikkunanmu daga haram da shubuha, ka kame hannayenmu daga zalunci da sata, ka runtsar da idanuwanmu daga fajirci da ha’inci, ka toshe kunnuwanmu daga jin maganar banza da giba, kuma ka yi falala ga malamanmu da zuhudu da nasiha, ga masu neman ilimi kuma da kokari da shauki, ga masu sauraro kuma da biyayya da wa’aztuwa, ga marasa lafiyar musulmi kuma da waraka da hutawa, ga matattunsu kuma da rangwame da rahama, ga tsofaffinmu kuma da natsuwa da kwanciyar hankali, ga matasanmu kuma da komowa da yawan tuba, ga matanmu kuma da jin kunya da kamewa, ga mawadatanmu kuma da kaskan da kai da yalwatawa, ga matalauta kuma da hakuri da wadatar zuci, ga mayaka kuma da cin nasara da galaba, ga ribatattun yaki kuma da kubuta da hutawa, ga shugabanni kuma da adalci da tausayawa, ga al’umma kuma da yin daidai da kyawun hali. Ka sanya albarka ga mahajjata da masu ziyara da guzuri da ciyarwa, kuma ka hukunta abin da ka wajabta masu na daga hajji da umara don falalarka da rahamarka, Ya mafi rahamar masu rahama”.
Kuma ni ina mai wasiyya ga ‘yan’uwana masu karatu da cewa kada damar karanta wannan addu’a ta kubuce musu, tare da sharadin yin tunani a kan ma’anoninta da abubuwan da take nufi tare da halarto da zuciya da fuskantowa zuwa ga Allah da tsoro da kaskan da kai, da kuma karanta ta tamkar yana magana da kansa ne, tare kuma da bin ladubban da aka ambata daga Ahlul Baiti (A.S) Domin karanta ta ba tare da fuskantar da zuciya ba to maganar baka ce kawai kuma ba ya kara wa mutum sani, ba ya sama masa kusanci, kuma ba ta yaye masa bakin ciki kuma ba a amsa masa addu’a da shi. “Hakika Allah mai girma da buwaya ba ya karbar addu’a daga zuciya rafkananniya, don haka idan ka yi addu’a ka fuskanto da zuciyarka sannan ka ji cewa lalle za a amsa
.
35- Addu’o’in Sahifatus Sajjadiyya
Bayan aukuwar al’amarin karbala mai ban takaici da kuma kame ragamar shugabancin al’ummar musulmi da Banu Umayya suka yi kuma suka dulmuya a cikin danniya suka yi dumu-dumu da jinin mutane sa’an nan suka yi watsi da koyar war Addini, sai Imam Zainul Abidin (AS) wato Sayyiddus Sajidin Ya zauna a gidansa yana bakin ciki da jin takaici, yana gida babu wani mai kusatarsa kuma ba zai iya yada wa mutane abin da ya wajaba a kansu ko ya kamata su sani ba.
Sai ya tilastu a kan ya dauki salon addu’a wanda muka ambata da cewa yana daga cikin hanyoyin tsarkake zukata a matsayin hanyar yada koyarwar Alkur’ani da ladubban Musulunci da kuma sanar da tafarkin Ahlul Baiti (AS) kuma hanyar cusa wa mutane ruhin Addini da zuhudu da abin da ya wajaba na daga gyaran zukata da kuma kyawawan dabi’u.
Wannan hanya ce da ya fare ta a fakaice don koyar wa mutane ba tare da ya jawo hankalin azzaluman Shugabanni da ke matsa masa ba, kuma ba zasu iya kafa masa wata hujja ba, don haka ne ya yawaita yin wadannan addu’o’i masu zurfi, a an tattara wadansunsu a littafin Sahifatus Sajjadiyya wanda ake yi wa lakabi da Zaburar Zuriyar Muhammad (S.A.W). Salonta da manufofinta sun zo da siga da salon Larabci mafi daukaka, da kuma mafi daukakar addini, da mafi ingancin asiran tauhidi da Annabci da kuma mafi ingancin hanyar koyar da kyawawan dabi’u ababan yabo da kuma ladubban Musulunci. Kuma ta kunshi maudu’ai daban daban ne na tarbiyya ta Addini da ta shafi koyarwar Addini da kyawawan dabi’u ta hanyar addu’a, ko kuma addu’a ce amma da salon koyar da Addini da kuma kyawawan dabi’u. Shi ne salon bayanin Larabci mafifici kuma mafi daukakar mashayar manufar sanin Ubangiji da kyawawan dabi’u bayan Alkur’ani da Littafin Nahjul Balagha.
Daga cikinsu akwai wanda yake sanar da kai yadda zaka daukaka Allah kuma ka tsarkake shi, da yabonsa da gode masa da komawa zuwa gareshi. Daga ciki akwai wadda ke sanar da kai yadda zaka yi zance da Allah da kebewa da shi da sirrinka da yankewa zuwa gareshi, daga cikinta akwai wadanda ke shimfida maka ma’anar Salati ga Annabi (S.A.W) da Manzannin Allah da zababbunsa daga cikin halittunSa da yadda ake yin sa, daga cikinsu akwai wadanda zasu fahimtar da kai abin da ya dace ka bi iyayenka da shi, da kuma abin da zai yi maka sharhin hakkokin Uba a kan dansa da na da a kan mahaifinsa, ko kuma hakkokin makwabta, ko na dangi ko hakkokin musulmi baki daya, ko hakkokin matalauta a kan mawadata da kuma akasin haka. Daga cikin addu’o’in akwai wanda zai fadakar da kai kan abin da ya wajaba na basussukan mutane akan ka, da kuma abin da ya kamata ka sani na al’amuran tattalin arziki da dukiya, a abin da ya kamata ka yi mu’amala da shi ga abokanka da sauran mutane baki daya, da wadanda kake neman yin mu’mala da su a maslaharka, da kuma abin da zai hada maka dukkan kyawawan dabi’u, kuma ya zama maka tafarki cikakke na ilimin kyawawan dabi’u.
Daga cikinsu akwai wadanda zasu koya maka yadda za ka yi hakuri a kan munanan abubuwa da suke aukuwa da kuma yadda za ka yi yayin da kake ciwo da kuma yayin da kake kalau. Daga cikinsu akwai wadanda ke maka sharhin ayyukan wajibi da suka hau kan sojojin Musulunci da wajiban mutane dangane da su, da dai sauran wadannan da kyawawan dabi’u abin yabo suke farlanta su, duk ta hanyar addu’a.
Abubuwan da suke kunshe cikin addu’ar imam su ne:
Na farko: Sanin Allah da girman kudurarSa da bayanin kadaita Shi da tsarkake shi da mafi zurfin kalmomi na ilimi, wannan kuwa yana maimaituwa ne a kowace addu’a da salo mabambanta, kamar yayin da kake karantawa a addu’a ta farko: “Godiya ta tabbata ga Allah na farko wanda babu wani na farko da ya kasance kafin shi, na karshen da babu wani na karshe da zai kasance bayansa, wanda idanuwan masu gani suka gaza ganin sa, wahamce-wahamcen masu sifantawa suka gajiya wajen siffanta Shi, Ya fari halittu da kudurarSa a farkon farawa ya kuma kago su kamar yadda ya so kagowa.”. Karanta ma’anar na farko da na karshe da kyau da kuma tsarkake Allah (S.W.T) daga kasancewar wani gani ko wahami ya gewaye da shi, da kuma tunani kan zurfin ma’anar halittawa da samarwa.
Sannan ka karanta wani salon wajen bayyana kudurar Allah da tadabburi a cikin addu’a ta 6: “Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya halitta dare da rana da karfinSa, ya rarrabe tsakaninsu da kudurarsa, ya sanya wa kowanne daga cikinsu iyaka ayyananniya, yana shigar da kowane daya daga cikinsu a cikin dan’uwansa, da kaddarawarsa ga bayi a cikin abin da yake ciyar da su kuma yake sanya su su girma. Sai ya halitta musu dare domin su huta daga wahalar kaiwa da komowa da dawainiya, kuma ya sanya shi sutura domin su lulluba da hutunsa sai ya zama musu wartsakewa da karfi domin su sami jin dadi da sha’awa da shi. Har zuwa karshen abubuwan da ya ambata na fa’idar halittar rana da dare da kuma abin da ya kamata mutum ya yi godiyarsa na daga wadannan ni’imomi.
A wani salon kuma na bayanin dukkan al’amura ga Allah (S.W.T) suke za ka karanta a addu’a ta 7 cewa: “Ya wanda da Shi ne ake warware kulle-kulle! Ya wanda da shi ne kaifin tsanani yake dakushewa! Ya wanda daga gare Shi ake neman mafita zuwa yalwar sauki! mawuyatan al’amura na rusunawa ga kudurarka! sabubba suna tasiri ne da ludufinka kaddarawarka kuma ta gudana ne a bisa ikonka, abubuwa suna zartuwa da iradarka ne, suna masu umartuwa da iradarka ba tare da fadarka ba, kuma masu tsawatuwa ne da nufinka ba tare da haninka ba.
Na Biyu: Bayani game da falalar Ubangiji ga bawansa, da kuma gazawar bawa wajen bayar da hakkin Ubangiji komai abin da ya yi na da’a da ibada kuwa, da kuma yankewa domin komawa zuwa ga Ubangiji kamar yadda kake karantawa a addu’a ta 37: “Ya Allah hakika babu wani da zai kai ga matukar godiya gare ka sai wata Kyautatawarka ta same shi waccea za ta sake lizimta masa wata godiyar, kuma ba ya kaiwa ga matukar da’arka koda kuwa ya dage sai ya gaza yin yadda ka cancanta ga falalarka, Mafificin mai godiya gare ka a bayinka ya gaza a kan godiyarka, kuma mafi bautarsu mai takaitawa ne ga bautarKa”.
Saboda girman ni’imomin Allah (S.W.T) kan bawansa da ba su da iyaka bawan ya yi kadan ya ba da hakkinsa komai kokarin da ya yi, yaya kenan idan kuma ya sabe shi yana mai tsaurin kai, yayin nan kuma ba zai taba iya kankare sabo koda guda daya ba, kuma wannan shi ne abin da fakara mai zuwa ta addu’a ta 16 take nunawa: “Ya Ubangijina idan da zan yi kuka har fatar idona ta fadi, kuma na yi kururuwa har muryata ta dushe, kuma na tsaya gare ka har kafafuwana su tsattsage kuma in yi ruku’u gareka har bayana ya sance, kuma na yi maka sujada har kwayar idandunana su faffado, kuma turbayar kasa ta cinye duk tsawon rayuwata, kuma na sha ruwan toka har zuwa karshen rayuwata, sa’an nan na yi ta ambaton ka duk tsawon wannan lokacin har sai harshena ya gaza, sannan kuma na zama ban taba daga ganina na dubi sama ba don jin kunyar ka, duk wannan ba zai wajabta shafe mini mummunan aiki daya daga munanan ayyukana ba.”
Na uku: Sanar da lada da ukuba da aljanna da wuta da kuma cewa ladan Ubangiji dukkaninsa kyauta ne kawai kuma bawa yana cancantar azaba ne da mafi karancin sabo da ya yi, kuma Ubangiji yana da hujja a kansa game da haka.
Kuma dukkan addu’o’in Sahifatus Sajjaddiya sun kawo maganar irin wannan azaba mai mai tasiri domin tsoratarwa da sanya tsoro a zuciya da sanya mata sa tsammani da ladan Ubangiji, dukkan wannan shaida ce a kan haka ta salo daban- daban da yake sa wa zuciya tsoron kan sabo. Kamar abin da zaka karanta a addu’a ta 46:- “Hujjarka tabbatacciya, Shugabancinka tsayayye ne ba ya gushewa, don haka tsananin azaba Madawwamiya ta tabbata ga wanda ya nisance ka, tabewar tozartuwa ta tabbata ga wanda ya karkace daga gare ka, tsiyacewar tsiyata ta tabbata ga wanda ya rudu ya bar ka, jujjuyawarsa a azabarka ta yawaita, kaikawonsa a cikin ukubarka ya tsawaita, bukatarsa ga burinsa na samun sauki ya nisanta, saukin samun mafitarsa abin yanke kauna ne, adalci ne daga hukuncinka ba ka zalunci a cikinsa, da kuma yin daidai a hukuncinka ba ya kaucewa, hakika ka bayyanar da hujjoji kuma ka jarraba uzurori…”
Kuma kamar yadda kake karanta addu’a ta 31: “Ya Allah! ka ji kan kadaitakata ta gabanka, da kidimewar zuciyata daga tsoronka, da firgicewar gabobina don haibarka, kuma ya Ubangijina! zunubina ya sanya ni a matsayin kaskanci a farfajiyarka, idan na yi shiru babu wani da zai yi magana madadina, idan kuma na nemi a cece ni to ni ban cancanci ceto ba.”.
Kamar kuma karantawarka a addu’a ta 39: “Domin kai idan har ka saka mini da gaskiya to za ka halakar da ni, idan kuma ba ka lullube ni da rahamarka ba to za ka halakar da ni, kuma ina rokon ka ka dauke daga zunubina wanda daukar nauyinsa ya gajiyar da ni, ka yi tsira ga Muhammad da Zuriyarsa, kuma ka ba wa raina kanta saboda zaluncinta…”.
Na Hudu: Jan mai addu’a zuwa ga dauke sawunsa daga aikata munanan ayyuka da kaskantantun siffofi domin wanke ruhinsa da tsarikake zuciyarsa, kamar yadda kake karantawa a addu’a ta 20: “Ya Allah ka cika mini niyyata da ludufinka, kuma ka inganta mini yakinina da abin da ke gare ka, ka gyara min abin da ya baci daga gare ni da kudurarka, Ya Allah! ka yi tsira ga Muhammad da Zuriyar Muhammad ka jiyar da ni dadi daga shiriya ingantacciya da ba zan taba neman musanya daga gareta ba, da kuma hanya ta gaskiya wacce ba zan taba karkacewa daga kanta ba, da kuma niyyar shiriya da ba zan taba kokwanto a cikinta ba.
Ya Allah kada ka bar wani hali da yake aibi ne da ake aibata ni da shi sai ka gyara shi, ko kuma wani laifi da za a zarge ni da shi sai ka kyautata shi, ko kuma wani halin karimci da yake tauyayye gare ni har sai ka cika Shi”.
Na biyar: Sanya wa mai karanta addu’ar dauke sawunsa daga mutane da rashin kaskantar da kansa gunsu, kuma kada ya kai kukan bukatarsa gun wani ba Allah ba, domin kwadayin abin da yake hannun mutune yana daga cikin mafi munin abin da mutum zai siffantu da shi kamar yadda zaka karanta a addu’a ta 20: “Kuma kada ka fitine ni da neman taimakon waninka idan na matsu da kuma kaskan da kai don tambayar wani ba kai ba idan na bukata, da kuma mika wuya gaba ga wanda ba kai ba idan na tsorata, saboda haka sai in cancanci tabarwarka da haninka da kawar da kanka”.
Da kuma misalin addu’a ta 28: “Ya Allah ni na tsarkake niyyata da yankewa zuwa gare, kuma na juyo zuwa gare ka baki daya, kuma na kawar da fuskata daga dukan wanda bai wadata da falalarka ba, na ga cewa bukatar mabukaci zuwa ga wani mabukacin wauta ce kuma bacewar hankalinsa ne.”
Da kuma misalin abin da kake karantawa a addu’a ta 13: “Duk wanda ya yi kokarin magance rashinsa ta gurinka kuma ya yi kokarin kawar da talauci da taimakonka, hakika ya nemi bukatarsa a gurin da ake tsammani, kuma ya zo wa bukatarsa ta gurin da ake tsammani, kuma ya zo wa bukatarsa ta fuskarta da ta dace. Wanda kuma ya juya da bukatarsa kuwa ga daya daga cikin halittunka, ko kuma ya sanya shi sababin samunta ba kai ba, to hakika ya jawo wa kansa hani kuma ya cancanci kubucewar kyautatawa daga gare ka”.
Na Shida: Koya wa mutane wajabcin kiyaye hakkokin wasu, da taimaka wa sashensu ga sashe, da fifita juna a tsakaninsu domin tabbatar da ma’anar yan’uwantakar Musulunci, kamar yadda kake karantawa a addu’a ta 38: “Ya Allah! ni ina mai neman uzuri daga gare ka a kan dukkan wani da aka zalunta a gabana amma ban taimake shi ba, da kuma wani kyakkyawan abu da aka kwararo mini shi amma ban yi godiyarsa ba, da kuma duk wani mummunan aiki da aka nemi uzurina ban bayar da uzuri ba, da kuma duk wani mabukaci da ya roke ni ban ba shi ba, da kuma hakkin mai hakki da ya hau kaina daga muminai amma ban cika masa ba, da kuma daga dukkan wani aibi na mumini da ya bayyana gare ni amma ban suturce shi ba…”.
Hakika irin wannan neman uzuri yana daga cikin mafi bayyanar abin da zai fadakar da zuciya zuwa ga abin da aikata shi ya kamata na wadannan kyawawan dabi’u madaukaka. A addu’a ta 39 akwai karin haske a kan hakan, sai ya sanar da kai yadda za ka yafe wa wanda ya munana maka, yana kuma gargadinka game da yin ramuwar gayya, yana kuma daukaka zuciyarka zuwa matsayin tsarkakku: “Ya Allah duk wani bawa da ya yi mini abin da na hana shi a kansa, ya kuma keta mini abin da na kange shi gareshi, sai mutum da nauyin zaluntata, ko zuciyata ta tuna shi yana rayayye, to ka gafarta masa abin da ya yi mini ka yafe masa abin da ya riga ya gabatar gareni, kada ka tsayar da shi don tambaya a kan abin da ya aikata a kaina, kuma kada ka tona asirinsa a kan abin da ya aikata a kaina, kuma ka sanya rangwamen da na yi masa na afuwa gare su da kama kyautar da na yi musu na daga sadaka gare su ya zama mafi tsarkin sadakar masu sadaka, kuma mafi daukakar addu’a ma’abota kusanci gare ka. Kuma ka musanya mini afuwata gare su da afuwarka, da addu’ata gare su rahamarka, har ya kowanne daga cikinmu ya rabauta da falalarka”.
Mamaki ya girmama ga wannan fakarar ta karshe! da kuma yawan girman tasirinta a cikin zukatan masu alheri! Domin dadakar da ita a kan kyakkyawar nufi ga dukkan mutane da nema wa kowa sa’ada hatta wanda ya zalunce shi. Irin wannan yana da yawa a cikin addu’o’in Sahifatus sajjadiyya, da yawa daga irin wadannan koyarwa ta ubangiji ga tsarkake rayukan ‘yan Adam da sun kasance masu shiryuwa.
36- Ziyartar Kaburbura
Ziyarar kaburbura -Annabi da na Imamai (AS)- da katange su da kuma yin gine-gine a kansu suna daga cikin al’amuran da Shi’a suka kebantu da su, kuma suna sadaukar da dukkan abu mai tsada da mai sauki a cikin imani da dadin rai. Wannan kuwa asalinsa yana komawa ne zuwa ga wasiyyar Imamai da kuma Zaburar da mabiyansu da kuma kwadaitar da su a kan irin ladan da yake da shi mai yawa a gurin Allah madaukaki, saboda kasancewarta daga mafifitan ayyuka biyayya da kusanci da Allah bayan ayyukan ibadu wajibai, da kuma cewa kaburburan suna daga cikin mafifitan guraren amsa addu’a da yankewa zuwa ga Allah (S.W.T).
Kuma sun sanya wannan daga cikin cika alkawura ga Imamai, domin ga kowane imami akwai alkawarinsa a kan wuyan mabiyansa, kuma yana daga mafificin cika alkawari, ziyartar, duk wanda ya ziyarce su yana mai kwadayin haka da gaskata abin da suka kwadaitar a kai to zasu kasance masu cetonsu a ranar lahira
. Akwai fa’idoji masu yawa na Addini da zamantakewa a cikin ziyartar kaburbura da suka sa Imamanmu himmantuwa da ita, domin bayan dada karfin soyayya da mika wuya da kauna tsakanin imamai da mabiyansu, hada da sabunta ambatonsu da tuna kyawawan dabi’unsu da jihadinsu a tafarkin gaskiya, tana kuma hada musulmi daban-daban wadanda suke warwatse a waje daya domin su san juna kuma ta dasa ruhin mikuwa zuwa ga Allah a cikin zukatansu da yankewa zuwa gare shi da bin umarninsa, tana kuma cusa musu hakikanin tauhidi a cikin ma’anonin addu’o’in ziyarorin da suke cike da fasaha wadanda aka samo daga Ahlul Baiti (AS) tare da koya musu tsarkin Musulunci da sakonsa da abin da ya wajaba a kan musulmi na daga dabi’u madaukaka da kaskan da kai ga mai tafiyar da al’amuran halitta (S.W.T) da gode wa ni’imominsa, don haka ta wannan bangaren tana amfani ne irin na addu’o’in da aka ruwaito wadanda bayaninsu ya gabata. Wasunsu ma suna dauki da sama da haka kuma mafi daukakarta kamar ziyarar “AminulLahi” wacce take ziyara ce da aka rawaito daga Imam Zainul Abidin (A.S) yayin da ya ziyarci kabarin kakansa imam Ali (A.S).
Kamar yadda wadannan ziyarorin da aka ruwaito suke fahimtar da matsayin imamai (AS) da irin sadaukarwarsu a tafarkin taimakon gaskiya da daukaka kalmar Addini da kadaitarsu ga ibadar Allah (S.W.T), ga shi kuma sun zo da salon na larabci mai fasaha madaukakiya, da ma’anoni masu sauki wadanda kowa da kowa yake fahimta, kuma suna kunshe da mafifitan ma’anonin tauhidi masu zurfi, da addu’a da yankewa zuwa gare shi madaukaki. Hakika tana daga cikin mafi ingancin laduban Addini bayan Kur’ani mai girma da Nahjul Balaga da kuma addu’o’in da aka ruwaito daga garesu (AS) domin a cikinta akwai takaitaccen bayanin sanin Imamai (AS) a dunkule, game da abin da ya shafi sha’anin Addini da gyaran zuciya.
Sannan a cikin ladubban ziyarar akwai koyarwa da shiryarwar da ke karfafa tabbatar da samuwar wadannan dabi’u na Addini madaukaka; da ya hada da daukaka tsarkin ruhin musulmi, da yaduwar tausasawa ga fakiri, da iya zamantakewa da al’umma, da son cudanya da jama’a, domin daga ladubanta akwai abin da ya kamata a aikata kafin a fara shiga cikin ginin makabartar domin ziyartarsa.
Daga nan kuma akwai abin da ya kamata a yi a tsakiyar ziyarar da kuma bayan ziyarar da mu a nan zamu bujuro da sashen wadannan ladubban domin fadakarwa kan manufarta a muka ambata:
1- Daga ladubbanta, mai ziyarar ya yi wanka yayin fara ziyararsa ya tsarkaka, fa’idar wannan kuwa cikin abin da muka fahimta a fili take, ita ce mutum ya tsarkake jikinsa daga dauda domin ya kubutar da shi daga rashin lafiya da cututtuka kuma domin kada mutane su gundara
da warinsa ya kuma ya tsarkake kansa daga kazanta. Hakika ya zo a cikin hadisai cewa; mai ziyara ya karanta wannan addu’a bayan ya kare wanka domin fadakar da shi game da wadancan manufofi madaukaka, sai ya ce: “Ya Allah ka sanya mini haske da tsarki tare, da kuma tsari mai isarwa ga dukkan cuta da ciwo da kuma dukkan aibi kuma ka tsarkake zuciyata da gabobina da kasusuwana da namana da jinina, da gashina da fatata, da bargona da kashina da kuma abin da kasa ta dauke shi daga gare ni, kuma ka sanya mini halarta ranar bukatata da fakirancina da talaucina.”
2- Ya sanya mafi kyawu kuma mafi tsaftar tufafin da yake da su, domin sanya kyawawa da tsaftatattun tufafi a taron jama’a abu ne da mutane suke so wa junansu yake kuma kusantar da su ga junansu tare da kara musu daukaka da jin daukaka a bukin da suke halartarsa.
Daga abubuwan da suka kamata mu jawo hankali gare Shi a wannan koyarwa Shi ne ba a wajabta wa mai ziyara sanya mafi kyawun tufafi baki daya ba, a’a sai dai ya sanya mafi kyawun abin da zai iya, domin ba kowa ne zai iya yin haka ba, kuma akwai takurawa ga talakawa al’amarin da tausayawa ba ta bukatar a yi haka, sai ya zamanto ya hada tsakanin wannan tarbiyya da abin da ya kamata na kawa da kuma kiyaye halin talaka da mai raunin hali.
3- Ya sanya turare matukar yana da shi, wannan fa’idarsa tamkar ta sanya sababbin tufafi ce.
4- Ya yi sadaka ga fakirai da abin da ya saukaka gare Shi, kuma fa’idar sadaka a irin wannan al’amari sananniya ce, domin a cikin hakan akwai taimaka wa gajiyayyu da kuma karfafa ruhin tausasawa gare su.
5- Ya tafi yana mai nutsuwa da kwanciyar hankali mai runtse ganin idonsa. Abin da ke cikin wannan irin natsuwar na girmama alfarmar wannan gurin da kuma wanda ake ziyarta da fuskanta zuwa ga Allah (S.W.T) da yankewa zuwa gare shi, ba boyayye ba ne, tare da abin da hakan ya kunsa na nesantar damun mutane da matsa musu a yayin wucewa, da kuma rashin munanawa sashensu ga sashe.
6- Ya yi kabbara da fadin: “Allahu Akbar” ya yi ta maimaitawa yadda ya so, kuma a wasu ziyarorin an kayyade kabbarorin zuwa dari. Akwai fa’idar jin rai ga girman Allah a cikin yin haka, da kuma cewa ziyara ba komai ba ce sai bauta ga Allah da girmama shi da tsarkake shi ta hanyar raya alamomin Allah da karfafa Addinin shi.
7- Bayan kammala ziyarar ga Annabi ko ga Imami sai ya yi salla raka’a biyu a mafi karanci domin bauta ga Allah domin godiya gareshi saboda dacen da ya yi masa ya kuma bayar da ladanta ga wanda ya kai wa ziyarar. A cikin addu’ar da aka ruwaito wacce mai ziyarar zai karanta bayan wannan salla akwai abin da zai fahimtar da mai ziyarar cewa wannan sallar tasa da aikinsa duk don Allah ne shi kadai da kuma cewa Shi ba ya bauta wa wanins, ziyarar ba wata abu ba ce sai wani nau’in neman kusanci zuwa gareShi madaukaki.
“Ya Uabangiji gareka na yi salla, gare ka na yi ruku’u, gareka na yi sujada, kai kadai ba ka da abokin tarayya, domin salla da ruku’u da sujada ba sa kasancewa sai gareka, domin kai hakika kai ne Allah babu abin bautawa sai kai. Ya Uabangiji ka yi tsira da aminci ga Muhammad da Zuriyar Muhammad (S.A.W) kuma ka karbi ziyarata, ka kuma ba ni abin da na roka, domin Muhammad da Zuriyarsa masu tsarki.”
A cikin irin wannan nau’in na ladabi akwai abin da yake bayyana wa wanda yake son fahimtar hakikanin manufofin Imamai (A.S) da mabiyansu masu koyi da su a ziyartar kaburbura, da kuma abin da yake toshe bakin masu nuna jahilta da suke raya cewa ziyarar kaburbura ibada ce gare su da neman kusanci gare su kuma shirka ce da Allah. Abin zato a nan shi ne cewa hadafin wadannan shi ne nesantar da jama’a daga abin da yake jawowa jama’ar imamiyya amfanin zamantakewa da na addini a bukukuwan ziyara, domin ya zama tsakuwar ido ga masu kiyayya da Ahlul Baiti (A.S), in ko ba haka ba ba ma tsammanin wadannan mutane suna jahiltar hakikanin manufar Ahlul Baiti (A.S), mustahili ne ga wadannan da suka tsarkake niyyarsu ga Allah suka kadaitu da ibada suka bayar da rayukansu wajan taimakon addini su kira mutane zuwa ga shirka da Allah.
8- Daga ladubban ziyara akwai cewa: Mai ziyara ya lizimci kyautata abotakar wanda yake tare da shi, da karanta magana sai dai da alheri, da yawaita ambaton Allah, da kaskan da kai, da yawaita salla, da salati da runtse idandunansa, kuma ya taimaka wa mabukata daga cikin yan’uwansa idan ya ga guzirinsu sun yanke, da taimaka musu, da tsantseni kan abin da aka hana, da kuma husuma, da yawaita rantsuwa da jayayya
.
Sannan hakikanin ziyara ba komai ba ne sai salati ga Annabi (S.A.W) da Alayensa da la’akarin cewa “Su rayayyu ne ana arzuta su gun Ubangijinsu”. Kuma suna jin magana suna amsawa, kuma ya isa ya ce: Assalamu alaika ya RasulalLah! Sai dai abin da ya fi ya karanta abin da aka rawaito na hadisai da suka zo game da ziyara daga Ahlul Baiti (A.S) saboda abin da yake cikinta na daga manufofi madaukaka da fa’idoji na addini, tare da balagarta da fasaharta, da kuma abin da yake cikinta na daga addu’o’i madaukaka da mutum yake fuskanta zuwa ga Allah makadaici a cikinta.
37- Shi’anci Gun Ahlul Baiti (AS)
Ahlul Baiti (AS) ba du da wata himma bayan sun debe tsammanin al’amarin al’umma ya dawo hannunsu sai gyara halin musulmi da tarbiyyantar da su tarbiyyar ta gari kamar yadda Allah (S.W.T) yake so daga gare su. Don haka suka kasance tare da duk wanda yake bin su kuma suka aminta da shi akan sirrinsu suna bayar da kokarinsu wajen koya masa hukunce-hukuncen Shari’a, da cusa masa ilimin addini, da sanar da shi abin da yake nasa da kuma wanda yake kansa. Ba sa daukar mutum cewa mabiyinsu kuma shi’arsu sai dan ya kasance mai bin umarnin Allah, mai nisantar son zuciyarsa mai riko da koyarwarsu da shiryarwarsu. Kuma ba sa ganin son su ya wadatar wajen tsira, kamar yadda wasu suke raya wa kansu daga cikin masu holewa da bin bin sha’awece-sha’awece da son ransu, wadanda ke neman uzurin kangare wa bin Allah, Imamai ba sa daukar sonsu da biyayya garesu mai tseratarwa ne sai dai idan ta hadu da kyawawan ayyuka, kuma mabiyansu sun siffantu da gaskiya da rikon amana da tsentseni da tsoron Allah.
“Ya Khaisama! ka isar daga garemu cewa ba za mu wadatar da su daga komai ba sai da aiki, kuma ba zasu samu soyayyarmu ba sai da tsentseni, kuma mafi tsananin hasarar mutane ranar alkiyama shi ne wanda ya siffanta adalci sannan kuma ya saba masa zuwa ga waninsa”
. Su suna son mabiyansu su zamanto masu kira zuwa ga gaskiya ne, masu shiryarwa zuwa ga alheri da shiriya kuma suna ganin cewa kira a aikace ya fi kira da harshe isarwa: “Ku kasance masu kiran mutane zuwa ga alheri ba da harsunanku ba, su ga kokari da gaskiya da tsentseni daga gare ku”
.
A yanzu za mu kawo maka wasu muhawarori da suka gudana tsakaninsu da wasu daga cikin mabiyansu domin ka san matukar tsanantawarsu da kwadayinsu a kan gyara dabi’un mutane:
1- Muhawarar Abu Ja’afar Bakir (AS) shi da Jabir Ju’ufi
: “Ya Jabir! Ashe ya isa ga wanda ya siffantu da cewa shi shi’a ne ya yi da’awar yana son mu? Wallahi! Ba kowa ne shi’armu ba sai wanda ya ji tsoron Allah ya bi shi”.
“Su ba a gane su sai da kas kan da kai da tsoron Allah, da rikon amana da yawan zikiri, da azumi, da salla, da bin iyaye, da taimakon makwabta na daga fakirai da mabarata da masu bashi da marayu da gaskiyar magana da karatun Kur’ani da kame harshe daga ambaton mutane sai dai da alheri, kuma su ne aminan jama’arsu a kan al’amura. Ku ji tsoron Allah ku yi aiki saboda abin da Allah ya tanada, kuma babu wata dangantaka tsakanin Allah da wani, kuma mafi soyuwar bayi a wajan Allah wanda suka fi jin tsoronsa suka fi biyayya gareshi. Ya Jabir! Wallahi ba mu kusanta zuwa ga Allah sai dai da da’a, kuma babu kubuta daga wuta a gare mu, kuma babu wani mai hujja a kan Allah, duk wanda ya kasance mai biyayya ga Allah to shi masoyi ne gare mu duk wanda ya kasance mai sabo ne ga Allah to shi makiyi ne gunmu, kuma ba a samun soyayyarmu sai da aiki da tsentseni.
2- Tattaunawar Abu Ja’afar (AS) da Sa’id Bn Hasan
:
Abu Ja’afar (AS) “ Shin dayanku zai zo ga dan’uwansa ya sanya hannunsa a jakarsa ya dauki abin da yake so bai cire shi ba?
Sa’id: Ban san da haka ba a cikinmu.
Abu Ja’afar (AS): To Babu komai kenan.
Sa’id: To halaka ke nan.
Abu Ja’afar (AS): Mutane ba a cika hankulansa ba tukuna.
3- Muhawar Imam Sadik (A.S) da Abu Sabah Al’kinani
.
Al’kinani: Muna shan wahalar mutane game da ku.
Abu Abdullah: Mene ne abin da kuke gamuwa da shi daga mutane?.
Al’Kinani: Magana ba ta gushewa tsakaninmu da mutun, sai ya ce: Wannan Dan Ja’afariyya ne mugu.
Abu Abdullahi: Mutane suna aibata ku da ni?.
Al’kinani: E.
Abu Abdullah: Wallahi karancin mai bin Ja’afar a cikinku ya yawaita! Kadai sahabbaina shi ne wanda tsantseninsa ya tsananta, ya yi aiki don mahaliccinsa ya kaunaci ladansa, wadannan su ne sahabbaina!
4- Abu Abdullah (AS) yana da wasu maganganu game da wannan al’amari da za mu kawo wasu kamar haka:
A- “Baya daga cikinmu sam, wanda ya kasance a wani gari da a cikinsa akwai mutane dubu dari ko fiye da haka, ya zama a cikin garin akwai wanda ya fi shi tsantseni”.
B- “Mu ba ma kirga mutum mumini har sai ya zamanto mai biyayya ga dukan umarninmu yana mai nufi, ku sani daga cikin bin umarninmu da nufinsa akwai tsentseni, don haka ku yi ado da shi Allah ya yi muku rahama”.
C- “Wanda mata masu tsari ba sa magana game da tsantsaninsa ba ya daga cikin shi’armu, haka nan wanda ya kasance a cikin wata alkarya mai mutane dubu goma a cikinsu akwai wata halitta ta Allah da ta fi shi tsentseni shi ba ya daga cikin masoyanmu”.
D- “Kadai shi’ar -Ja’afar- shi ne wanda ya kame cikinsa da farjinsa kokarinsa ya tsananta kuma ya yi aiki ga mahaliccinsa ya kaunaci ladansa ya ji tsoron azabarsa, to idan ka ga wadannan to wadannan su ne shi’ar Ja’afar.
38- Matsayin Zalunci
Ketare haddin wani da zaluntar mutane suna daga cikin mafi girman abubuwn da Imamai (AS) suke girmama muninsa, wannan kuma bi ne ga abin da Kur’ani ya zo da shi na daga tsoratarwa game da zalunci da munana shi, kamar fadinsa madaukaki: “Kada ka tsammaci Allah mai sha’afa ne game da abin da azzalumai suke aikatawa, sai dai kawai yana jinkirta su ne saboda ranar da idanduna zasu fiffito”. (Surar Ibrahim: 42)
Hakika abin da yake kai matukar bayyana munin zalunci da kyamar sa ya zo a maganganun Amirul Muminin Ali Dan Abi Talib (AS) kamar fadinsa shi mai gaskiya abin gaskatawa, daga a Nahjul balagha huduba ta 219: “Wallahi idan da za a ba ni Sammai bakwai da kuma abin da yake kasan falakinta a kan in saba wa Allah game da tururuwa da in kwace mata Sha’irin da ta jawo ba zan aikata ba”. Wannan shi ne matukar abin da mutum zai iya surantawa game da kame kai da tsoratarwa daga zalunci da kyamar yinsa. Shi ba zai zalunci tururuwa ba a kan kwayar sha’ir koda kuwa an ba shi sammai bakwai to yaya halin wanda yake zubar da jinin musulmi, yake handame dukiyoyin mutane, yake cin mutuncinsu? Yaya za a auna tsakaninsa da aikin Amirul Muminin? Kuma yaya matsayinsa da iliminsa (AS)? Wannan ita ce tarbiyyantarwar Ubangiji da addini yake bukatar ta daga kowane mutum.
Na’am, hakika zalunci yana daga mafi girman abubuwan da Allah ya haramta saboda haka ne zarginsa ya zama abu ne farko da ya zo a hadisan Ahlul Baiti (A.S) da addu’o’insu da kuma nesantar da mabiyansu daga gare shi.
Wannan ita ce siyasarsu (AS) kuma a kanta suke mu’amala hatta da wanda yake yi musu shisshigi yake rashin kunyar hawa matsayinsu. Kissar imam Hasan (AS) game da hakurinsa ga mutumin Sham wanda ya yi masa tsaurin ido ya zage shi, shi kuma ya tausaya masa ya kuma tausasa masa har sai da shi ya ji kunyar mummunan abin da ya aikata. Kuma ka riga ka karanta abin da ya gabata a addu’ar shugaban masu sujjada na daga ladubba madaukaka game da afuwa ga masu ketare iyaka da nema nema musu gafara. Wannan kuma shi ne matukar abin da daukakar ran mutum da kamalar mutumtakarsa, duk da kuwa ketare haddin azzalumi kwatankwacin yadda ya ketara ya halatta a shari’a, kamar yadda yin addu’a a kansa ya halatta, sai dai halatta wani abu ne, afuwa kuma wacce take daga kyawawan dabi’u wata aba ce daban, kai gun imamai shige gona da iri wajan yin addu’a a kan azzalumi ana kirga shi zalunci.
Imam Sadik (A.S) ya ce: “Bawa yana kasancewa abin zalunta, ba zai gushe ba yana ta yin addu’a har sai ya zamanto azzalumin”. Idan wannan shi ne halin wanda aka zalunta to yaya halin wanda ya fara zalunci da ketare iyakar tun karon farko! Yake kuma cin mutuncinsu, yana kwashe dukiyarsu, yana munafuncinsu gun azzalumai, ko yake yaudarar su, yana ya jefa su cikin halaka, ko ya cutar da su ko ya yi leken asiri a kansu? Irin wadannan a wajan Ahlul Baiti (AS) su ne mafi nesantar mutane a wajan Allah, mafi tasananinsu sabo da azaba, mafi muninsu ayyuka da dabi’u.
39- Taimakekeniya Da Azzalumai
Yana daga –abin da yake nuna- yake nuna girman zalunci da mummunan karshensa cewa Allah Allah (S.W.T) ya hana taimakekeniya da Azzalumai da kuma karkata zuwa gare su. “Kuma kada ku karkata zuwa ga azzalumai sai wuta ta shafe ku. Kuma ba ku da wasu masoya koma bayan Allah sannan ba za a taimake ku”. Wannan shi ne ladabin Kur’ani da Ahlul Baiti (AS). Hakika hadisai da dama sun zo daga garesu wadanda suka kai matuka wajan hana karkata zuwa ga azzalumai, da alaka da su, da yin aiki tare da su a cikin kowane irin aiki da taimaka musu ko da tsagin dibino ne.
Babu shakka mafi girman abin da aka jarrabci musulmi da musulunci da shi, shi ne sassauci ga azzalumai da kawar da kai game da miyagun ayyukansa, da mu’amala tare da su, ballantana taimaka musu a kan zaluncinsu. Ba abin da ya jawo wa al’ummar musulmi bala’o’i sai karkacewa daga tafarki madaidaci da gaskiya, har Addini ya yi rauni tare da shudewar zamani, karfinsu ya tafi, ya kai halin da yake a yau ya koma bako. Musulmi ko kuma wadanda suke kiran kansu musulmi suka zamanto ba su da wani mataimaki ban da Allah kuma su ba za a taimake su ba hatta a kan mafi raunin makiyansu da mafi kaskancin masu tsaurin ido a kansu kamar Yahudawa kaskantattu, balle kuma Kiristoci masu karfi.
Imamai (AS) sun wahala wajen nesantar da duk wanda ke da alaka da su daga taimakekeniya da azzalumai, suka kuma tsananta wa mabiyansu game da tafiya tare da ma’abota zalunci da cudanya da su, kuma hadisansu a game da wannan babin ba zasu kirgu ba; daga ciki akwai abin da Imam Zainul Abidin (AS) ya rubuta zuwa ga Muhammad Bn Muslim Azzuhuri bayan ya gargade shi game da taimakon azzalumai akan zaluncinsu da fadinsa: “Shin a kiran su gareka yayin da suka kiraka ba su sanya ka kan dutsin nika da suke juya nikan zaluncinsu da kai ba, kuma gada da suke ketarawa ta kanka zuwa bala’o’insu ba, da tsani na bi zuwa ga batansu, mai kira zuwa ga zaluncinsu, mai shiga tafarkinsu, suna sanya shakku da kai a zukatan malamai, kuma suna jan zukatan jahilai da kai zuwa gare su, waziransu na musamman da mafiya karfin mataimakansu ba su kai inda ka kai ba wajen gyara barnarsu, da kaikawon kebatattun mutane da saura jama’a zuwa garesu, abin da suka ba ka ya yi matukar karanta a maimakon abin da suka karba daga gareka da ya yi matukar girmama! Abin da suka gina maka ya yi matukar kankanta a maimakon abin da suka rusa maka da ya girmama! Ka duba kanka domin ba mai duban ta sai kai, ka yi mata hisabi irin na mutum abin tambaya”
.
Wannan kalma ta “Ka yi mata hisabi irin na mutum abin tambaya”. ta girmama! Yayin da son rai ya yi rinjaye a kan mutum sai ya wulakanta sirin samuwarsa da karamarsa, da wato ba zai sami wani ba zai samu wani mai daukar nauyin aikinsa ba, ya wulakanta abin da yake yi na ayyuka, ya raya cewa ba shi ne zai yi wa kansa hisabi a kan abin da yake yi ba na zunubi, wannan kuma yana daga sirrorin ran mutum mai umarni da mummuna, sai Imam (A.S) ya so ya fadakar da Zuhuri game da wannan sirrin na rai da yake boye a cikinta domin kada wahami ya yi galaba a kansa sai ya yi sakaci da nauyin da yake kansa. Mafi isa matuka daga wannan a suranta haramcin taimakekeniya da azzalumai shi ne maganar Safwan Jammal tare da Imam Musa Kazim (AS) wanda ya kasance daga cikin shi’ar Imam din, kuma daga masu rawaito hadisinsa amintattu (kamar yaddda ya zo a littafin Rijal na Alkashi game da Safwan) ya ce: “Na shiga wajansa.
Sai ya ce da ni: Ya Safwan duk wani abu daga gareka kyakkyawa ne mai kyau in banda abu daya.
Na ce: A sanya ni fansa gare ka! Wane abu ne?
Ya ce: Ba da hayar rakumanka ga wannan mutumin wato Harunar Rashid.
Na ce: Wallahi ni ban ba shi haya ba ina mai ashararanci, ko dagawa, ko don farauta, ko wasa ba, sai dai na ba shi haya ne don wannan tafarkin wato hanyar Makka kuma ba na aikin da kaina sai dai ina tura shi da bayina.
Ya ce: Ya Safwan kudin hayarka yana zama bashi a kansu?
Na ce: Na’am, a sanya ni fansa gare ka.
Ya ce: Shin kana so su wanzu har su biya ka kudin hayarka?
Na ce: Na’am.
Ya ce: To duk wanda ya so wanzuwarsu yana cikinsu, duk wanda ya kasance daga cikinsu shi mai shiga wuta ne.
Safwan ya ce: Sai na tafi na sayar da rakumana baki daya.
Idan son rayuwar azzalumai da wanzuwarsu ya kai wannan matsayi, to ina ga wanda suke hada kai da shi a kan zalunci ko kuma yake karfafa su a zalunci, ina ga wanda ya shiga cikin jama’arsu ko yake aiki irin nasu ko yake bin tawagarsu ko kuma yake bin umarninsu?
40- Aiki A Hukuma Azzaluma
Idan har taimakar azzalumai koda da rabin dibino ne, kai hatta ma son wanzuwarsu suna daga mafi tsananin abubuwa da lmamai (AS) suka yi gargadi game da su, to menene hukuncin tarayya da su a cikin hukunci da shiga cikin ayyukansu da rikon ofisoshinsu. Menene kuma hukuncin wadanda suke daga wadanda suka assasa daularsu, ko kuma ya zama cikin rukunan shugabacinsu masu dulmuya cikin karfafa hukumarsu, (domin karbar shugabancin azzalumi rusa gaskiya ne dukkaninta, da raya barna dukkaninta da bayyana zalunci da fasadi) kamar yadda ya zo a Hadisi a “Tuhaful Uku1” daga Imam Sadik (AS)
Sai dai kuma halaccin aiki a karkashin azzalumi ya zo daga gare su (AS) idan a ciki akwai kiyaye adalci, da tsayar da haddin Allah da kyautatawa ga muminai, da yin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna. “Allah yana da wadanda ya haskaka hujjoji da su, ya ba su iko a kasashe a kofofin azzalumai, da su ne yake kare waliyyanSa, ya kuma gyara al’amuran musulmi da su… wadannan su ne muminai na hakika. Su ne manarorin Allah a bayan kasa, su ne hasken Allah ne a cikin bayinsa…”. Kamar yadda ya zo a Hadisi daga Imam Musa Bin Ja’afar (AS). A wannan Babin akwai hadisai da dama da suke bayyana tafarkin da ya kamata masu rike ofis da ma’aikata su gudanar da ayyukansu a kai, kamar abin da ya zo a wasikar Imam Sadik (AS) zuwa ga Najjashi Shugaban Ahwaz
.
41- Hadin Kai A Musulunci
An san Ahlul Baiti (AS) da kwadayinsu a kan wanzuwar addinin musulunci, da kira zuwa ga daukakarsa da hada kan mabiyansa, da kiyaye ‘yan’uwantaka a tsakaninsu, da cire mugun kuduri daga zukatansu, da kullace kullace daga rayukansu, ba za a mance da matakin Amirul Muminin Aliyu dan Abi Talib (AS) game da halifofin da suka gabace shi ba, duk da fushin da ya yi da su da kuma yakininsa da kwacewarsu ga hakkinsa, amma sai ya tafi tare da su, ya zauna lafiya da su, kai an boye ra’ayinsa na cewa shi ne wanda aka wasiyya da halifancinsa, har ya zama bai bayyana nassin ba a bainar jama’a har sai da al’amarin ya koma hannunsa sannan ya kafa hujja da sauran wadanda suka rage daga cikin Sahabbai game da al’amarin nassin Al-Ghadir a ranar Rahba da ta shahara. Ya kasance ba ya boye shawara garesu game da abin da ya shafi musulmi ko Musulunci na amfani da maslaha, saudayawa yana fada game da wannan al’amari: “Sai na ji tsoron idan ban taimaki Musulunci da ma’abotansa ba zan ga gibi a cikinsa ko rushewa”.
Kamar yadda babu wani abu da ya taba zowa daga gare shi wanda zai yi tasiri a karfafa mulkinsu, ko raunana jagorancnsu ko rage kwarjininsu, sai ya kuntata wa kansa ya zauna a gida duk da abin da yake gani daga gare su. Dukkan wannan saboda kiyaye maslahar Musulunci ta gaba daya, da kiyaye kada a ga wani gibi a Musulunci ko rushewa, har aka san haka daga gare shi, kuma halifa Umar dan Haddabi ya kasance yana fada yana kuma maimaitawa: “Kada na kasance cikin wani al’amari mai wuyar sha’ani da Abul Hasan ba ya ciki.” Ko fadinsa: “Ba don Ali (A.S) ba da Umar ya halaka”.
Haka nan ba za a mance da matakin Imam Hasan dan Ali (AS) ba dangane da yin Sulhu da Mu’awiya ba, bayan ya ga cewa dagewa a kan yaki zai shafe ya kuma kawar da Alkawari mafi girma –Kur’ani- da adalci har da musulunci daga samuwa har zuwa karshen zamani, a kuma shafe shari’ar Ubangiji, a kuma gama da wadanda suka yi saura daga Zuriyar Manzo daga Ahlul Baiti, sai ya fifita kiyaye zahirin Musulunci da sunan Addini, duk da ya yi sulhu da Mu’awiya babban makiyin Addini da ma’abotansa, mai husuma mai mugun kuduri ga imam Hasan (A.S) da shi’arsa, tare da abin da ake tsammani na faruwar zalunci da kaskanci gareshi shi da mabiyansa, ga kuma takubban Banu Hashim da na shai’arsa a zazzare ba sa son komawa ba tare da yi aikinta ba na kariya da gwabzawa, sai dai maslahar musulunci madaukakiya ita ce ta fi dukkan wadannan al’amuran.
Amma Shahidi Imam Husain (AS) idan ya motsa to domin ya ga cewa idan aka ci gaba da halin da ake ciki Banu Umayya ba su sami wanda zai tona asirinsu ba to da sannu zasu shafe sunan Musulunci, su kawar da darajarsa, sai ya so ya tabbatar wa tarihi ketare iyakarsu, ya fallasa abin da suke kulla wa Shari’ar Manzon Allah (S.A.W). Ba don yunkurinsa mai albarka ba, da Musulunci ya zama wani labari ne da tarihi zai rika ambatonsa tamkar wani addinin barna. Kwadayin Shi’a a kan raya ambatonsa ta hanyoyi daban- daban ya zamanto saboda kammala sakon da yunkurinsa na dauki-ba-dadi da zalunci ne, kuma domin raya al’amarinsa cika umarni da biyayya ga Imamai (A.S)
.
A nan kwadayin Ahlul Baiti (A.S) na wanzuwar izzar musulunci zata bayyana garemu koda kuwa mai mulki ya kasance mafi tsananin makiyansu ne, a matakin Imam Zainul Abidin (A.S) da sarakunan Banu umayya alhalin sun maraita shi, an keta alfarmarsa a lokacinsu, kuma yana mai yawan bakin cikin a kan abin da suka yi wa babansa da da Ahlin gidansa a waki’ar karbala, amma duk da haka yana yi wa rundunar musulmi addu’a da nasara, musulunci kuma da izza, musulmi kuma da yalwa da aminci, kuma ya riga ya gabata cewa makaminsa kawai wajen yada ilimi Shi ne addu’a, ya koya wa Shi’a yadda zasu yi addu’a ga sojojin Musulunci da musulmi, kamar addu’arsa da aka sani da “Addu’ar masu dakon iyaka” wacce yake cewa a cikinta: Ya Allah! ka yi tsira ga Muhammad da Zuriyar Muharnmad, ka yawaitasu, ka kaifafa makamansu, ka kare matattararsu, ka kange iyakarsu, ka hada taronsu, ka shirya al’amarinsu, ka kadaita da wadatar da bukatunsu, ka karfafa su da cin nasara, ka taimake su da hakuri”. Zuwa inda yake cewa: “Ya Allah ka karfafa guraren Musulunci da haka, ka kiyaye gidajensu da shi, ka yawaita dukiyarsu da shi, ka shagaltar da su gabarin yakarsu don su dukufa ga ibadarka, da hana kai musu farmaki don su kadaita da kai, har ya zamanto ba a bauta wa kowa a bayan kasa sai kai, kuma ba a sanya wa goshi kasa saboda wani sai kai.” Haka nan ya ci gaba da addu’arsa mai fasaha, -kuma tana daga mafi tsayin addu’o’insa- wajen fuskantar da sojojin musulmi zuwa ga abin da ya kamace su na daga kyawawan dabi’u da kuma shirya kansu da tanadi a kan makiya, ta kunshi dukkan darussan yaki na jahadin Musulunci da bayanin manufarsa da fa’idarsa kamar kuma yadda take fadakar da musulmi da irin gargadi da takatsantsan dangane da makiyansu, da abin da ya wajaba su yi riko da shi a mu’amalarsu da kariyar kansu, da kuma abin da ya wajaba a kansu game da yankewa daga komai zuwa ga Allah baki daya da nesantar abubuwan da ya haramta, da yin abu saboda girman zatinsa.
Haka nan sauran imamai (A.S) a matakansu da suka dauka game da sarakunan lokutansu, duk da sun sami takurawa daga garesu iri-iri da kuma azabtar da su da dukkan nau’in na kekasar zuciya da tsanantawa, domin su ya yin da suka san cewa hukumar adalci ba za ta dawo hannunsu ba sai suka juya zuwa ga koya wa mutane al’amuran Addininsu suna fuskantar da mabiyansu fuskantarwa ta addini madaukaki. Dukkan wani yunkuri da ya faru a zamaninsu daga bangaren Alawiyawa da wasunsu bai kasance da ishararsu da son su ba, ya ma saba wa umarninsu da karfafawarsu ne a fili, duk da cewa sun fi kowa kwadayin kafa hukumar musulunci hatta sun fi Abbasawa su kansu.
Ya isa garemu mu karanta wasiyyar Imam Musa Alkazim (AS) ga shi’arsa: “Kada ku kaskantar da kawukanku da barin biyyyar shugabanku, idan ya kasance mai adalci to ku roki Allah wanzuwarsa, idan kuwa ya kasance azzalumi to ku roki Allah gyaransa, domin gyaruwarku na cikin gyaruwar shugabanku, kuma shugaba adali yana matsayin uba mai rahama ne, ku so masa abin da kuke so wa kanku kuma ku ki masa abin da kuke ki wa kanku”
.
Wannan ita ce matukar abin da ake siffantawa na kiyayewar al’umma ga amincin shugaba da su so masa abin da suke so wa kansu su ki masa abin da suke ki wa kansu.
Bayan duk wannan muna cewa: Alhakin shi’a da wasu marubuta na wannan zamani suke dauka girmama! Yayin da suke siffanta shi’a da cewa ita kungiya ce ta asiri mai barna ko kuma wata jama’a ce ta ‘yan juyin juya hali. Haka ne cewa wajibi ne a kan mabiyin koyarwar Ahlul Baiti (A.S) ya ki zalunci da azzalumai da fasikai, ya yi duba zuwa ga mataimakansu duba na kyama da rashin yarda da wulakanci, wannan dabi’a ba ta gushe ba suna gadonta jikoki da ‘ya’ya amma sam ba ya daga dabi’arsu su yi yaudara ko cin amana, kuma ba tafarkinsu ba ne yin juyin juya hali su yi tawaye a kan jagorancin da yake an kafa shi da sunan musulunci, ko a boye ko a sarari.
kuma ba sa halattawa kansu kisan gilla ko afka wa musulmi ko wace irin Mazhaba ko Darika yake bi, wannan kuwa domin rikoinsu ne da koyarwar Ahlul Baiti (A.S), kuma duk musulmin da ya yi kalmar shahada biyu a wajansu dukiyarsa da jininsa kubutattu ne, kuma cin mutuncinsa haramun ne; “Dukiyar mutum musulmi ba ta halatta sai da son ransa”. Musulmi dan’uwan musulmi ne, kuma yana da hakkoki a kansa kamar yadda bahasi mai zuwa zai yi bayani”.
42- Hakkin Musulmi A Kan Musulmi
Daga cikin mafi girma da kyawun abin da Musulunci ya yi kira zuwa gareshi shi ne ‘Yan’uwantaka tsakanin musulmi a kan duk sassabawarsu da martabobinsu da mukamansu. Kamar yadda mafi munin abin da musulmi suka yi a yau da kuma kafin yau shi ne sakacinsu wajan riko da wannan ‘yan’uwantaka ta musulunci. Domin mafi karancin koyarwar wannan ‘yanuwatakar ita ce “Ya so wa dan’uwansa musulmi abin da yake so wa kansa kuma ya ki masa abin da yake ki wa kansa kamar yadda zai zo a hadisin Imam Sadik (A.S).
Ka duba ka yi tunani a kan wannan dabi’a mai sauki a mahangar Ahlul Baiti (A.S) za ka samu cewa yana daga mafi wahalar abin da zaka iya samu wajan musulmi, da musulmi zasu yi wa kansu adalci su san addininsu sani na hakika su yi riko da wannan dabi’a ta so wa dayansu dan’uwansa abin da yake so wa kansa, da ba a ga zalunci daga wani ba ko ketare iyaka, ko sata, ko karya, ko yi da wani, ko annamimanci, ko zargi da mummuna, ko suka da karya, ko wulakanci ko girman kai.
Idan da musulmi sun tsaya sun fahimci mafi karancin ma’anar hakkin ‘yan’uwantaka a tsakaninsu kuma suka yi aiki da ita, da zalunci da ketare iyaka sun kau daga bayan kasa, kuma da ka ga ‘yan Adam sun zama ‘yan’uwa suna masu haduwa da juna cikin farin ciki kuma da mafi daukakar sa’adar zamantakewa ta cika garesu, kuma da mafarkin malaman falsafa na da na samar da mafificiyar hukuma ya tabbata, da sun kasance masu musayar soyayya a tsakaninsu da ba su bukaci wasu hukumomi da kotuna ba, ko ‘yan sanda ko kurkuku, ko dokokin laifuffuka, da dokokin haddi da kisasi, kuma da ba su rusuna wa ‘yan mulkin mallaka ba, kuma da dagutai ba su bautar da su ba, kuma da kasa ta canja ta zama aljannar ni’ima kuma gidan sa’ada.
Bugu da Karin cewa da dokokin soyayya sun jagoranci rayuwar ‘yan Adam kamar yadda Addini yake so na koyarwar ‘yan’uwantaka to da kalmar neman adalci ta bace daga harsunanmu da ma’anar cewa ba za mu zamanto muna bukatar adalci da dokokinsa ba ballantana har mu bukaci amfani da kalmarsa ba, saboda dokokin soyayya sun isar mana wajen yada alheri da aminci da sa’ada da murna, domin mutum ba zai bukaci amfani da adalci ko dokoki ba, sai idan ya rasa soyayya daga wanda ya wajaba ya yi masa adalci, amma a wajan wanda yake nuna masa kauna da soyayya kamar da da dan’uwa sai dai ya kyautata musu ya hakura da dama daga abubuwan da yake so, duk wannan sakamakon so da kauna ne daga yardar zuciya, ba don adalci ko masalahar kansa ba. Sirrin haka kuwa shi ne cewa mutum ba ya so sai kansa da kuma binda ya dace da kansa, kuma mustahili ne ya so wani abu ko wani mutum da yake wajen ransa sai dai idan yana da alaka da shi, kuma ya shiga ransa. Kamar kuma yadda yake mustahili ne ya sadaukar da zabin kansa gareshi a cikin abin da yake so yake kuma kauna saboda wani mutum da ba ya sonsa ba ya kuma kaunarsa, sai dai idan yana da wani imani mai karfi da ya fi karfin son ransa, kamar imani da kyawun adalci da kyautatawa, a yayin nan yana iya sadaukar da dayan abubuwan da yake so ya yi fansa da shi saboda son wani.
Farkon madaukakan darajoji da suka wajaba musulmi ya siffantu da su shi ne; ya kasance yana jin hakkin ‘yan’uwantaka ga sauran mutane, to idan kuwa ya kasa wannan to zai gaza aikata mafi yawa da haka saboda galabar son ransa, saboda haka yana wajaba a kansa ya cusa wa kansa akidar son adalci da kyautatawa biyayya ga shiryarwar musulunci, idan kuwa ya gaza hakan to bai cancanci ya zama musulmi ba sai dai a suna, kuma ya fita daga soyayyar Allah (S.W.T) kuma Allah ba ya da wani buri a kansa kamar yadda zai zo a hadisin imam (A.S) mai zuwa. Saudayawa sha’awar mutum takan yi galaba a kansa sai ya zamanto mafi wahalar abin da yake fama da shi, shi ne ransa ta yarda da akidar adalci, balle kuma ya samu imani cikakke da ya fi karfin sha’awarsa.
Saboda haka ne ma kiyaye hakkin ‘yan’uwantaka ya zama daga mafi wahalar koyarwar addini idan ba shi da imani na gaskiya game da ‘yan’uwantaka. Don haka ne imam Abu Abdullah (A.S) ya ji tsoron yi wa sahabinsa “Al’mu’ula Bn Khunais” bayanin dalla-dallan tambayarsa game da hakkin ‘yan’uwantaka sama da abin da ya kamata ya bayyana masa domin tsoron kada ya koyi abin da ba zai iya aiki da shi ba.
Sai Mu’ula ya ce
: Menene hakkin musulmi a kan musulmi?
Sai Abu Abdullahi ya ce: yana da hakkoki bakwai wajibai, babu wani hakki daga cikinsu sai ya wajaba a kansa, idan ya tozarta daya daga ciki to ya fita daga soyayyar Allah da biyayyarsa, kuma Allah ba shi da wani buri a gareshi.
Sai na ce masa: A sanya ni fansa gareka! Mecece?
Sai ya ce: Ya Mu’ula ni ina mai tausasawa gareka, ina tsoron ka tozarta ba za ka kiyaye ba, ko kuma ka sani ba za ka aikata ba.
Na ce: Babu karfi sai da Allah.
Yayin nan sai Imam (A.S) ya ambaci hakkoki bakwai bayan ya fada game da na farkonsu: “Mafi saukin hakki daga cikinsu shi ne ka so wa dan’uwanka kamar yadda kake so wa kanka, ka kuma ki masa abin da kake ki wa kanka”.
SubhanalLahi! Wannan shi ne hakki mai kankanta to yaya wannan hakkin mafi kankanta yake a gare mu yau mu musulmi? Kaicon fuskon da suke da’awar musulunci amma ba sa aiki da mafi kaskantar abin da ya wajaba na daga hakkoki. Abu mafi ban mamaki kuma shi ne a dangata wannan rashin ci gaban da ya samu musulmi ga Musulunci, alhalin laifi ba na kowa ba ne sai na wadanda suke kiran kansu musulmi amma ba sa yin aiki da mafi karancin abin da ya wajabta musu da su yi aiki da shi na koyarwar addininsu.
Domin tarihi kawai kuma don mu san kawukanmu da takaitawarta zamu ambaci wadannan hakkoki bakwai wadanda Imam (A.S) ya bayyana su:
l- Ka so wa dan’uwanka musulmi abin da kake so wa kanka, kuma ka ki masa abin da kake ki wa kanka.
2- Ka nisanci fushinsa ka bi yardarsa ka kuma bi umarninsa.
3- Ka taimake shi da kanka, da dukiyarka, da harshenka, da hannunka, da kafarka.
4- Ka zamanto idonsa, dan jagoransa, kuma madubinsa.
5- Kada ka koshi shi kuma yana cikin yunwace, kada ka kashe kishirwarka shi kuma yana jin kishirwa, kada ka zama a suturce shi yana tsirara.
6- In kana da mai hidima shi kuma dan’uwanka ba shi da mai hidima, to wajibi ne ka tura mai hidimarka, sai ya wanke masa kaya, ya dafa masa abinci, ya gyara masa shimfida.
7- Ka kubutar da rantsuwarsa, ka amsa kiransa, ka gaishe da maras lafiyarsa, kuma ka halarci jana’izarsa. Idan kuma ka san yana da wata bukata sai ka yi gaggawar biya masa ita, kada ka bari har sai ya tambaye ita, sai dai ka gaggauta masa. Sannan ya rufe maganarsa da cewa: “Idan ka aikata haka to ka hada soyayyarka da soyayyarsa kuma soyayyarsa da soyayyarka”.
Akwai hadisai da yawa da suka kunshi ma’anar da ta zo a wannan hadisi daga imamanmu (A.S) wasunsu daga littafin Wasa’il a babobi daban-daban.
Tayiwu wasu su yi tsammanin cewa abin nufi da ‘yanuwantaka a hadisin Ahlul Baiti (A.S) ya kebanci tsakanin musulmi ne wadanda suke daga mabiyansu a kebance, amma komawa ga ruwayoyinsu yana kawar da wannan zato, koda yake sun kasance ta wani bangare suna tsananta musantawa ga wanda ya sabawa tafarkinsu kuma ba ya riko da shiriyarsu. Ya wadatar ka karanta hadisin Mu’awiya Dan Wahab ya ce
:
Na ce masa
: Yaya ya kamata gare mu mu yi tsakaninmu da mutanenmu da kuma wadanda muke cudanya da su na daga mutane wadanda ba sa kan al’amarinmu”.
Sai Ya ce: “Ku duba Imamanku wadanda kuke koyi da su ku yi yadda suke yi, na rantse da Allah! su suna gaishe da maras lafiyarsu suna halartar jana’izarsu suna ba da shaida gare su da kuma da kansu kuma suna bayar da amana gare su.”
Amma ‘yan’uwantakar da Imamai suke son ta daga mabiyansu, tana saman wannan ‘yan’uwantaka ta musulunci, kuma kai ka riga ka ji wasu hadisai a fasalin bayanin sanin shi’a da ya gabata. Kuma ya isar ka karanta wannan muhawara tsakanin Abana Bn Taglib da Imam Sadik (A.S) daga hadisin
da Abbana ya rawaito da kansa yana mai cewa: Na kasance ina dawafi tare da Abi Abdullah (A.S) sai wani mutumi daga cikin mutanenmu ya bujuro mini wanda ya riga ya tambaye ni in raka shi wata biyan bukatarsa, sai ya yi mini ishara, sai Abu Abdullahi (A.S) ya gan mu.
Sai ya ce: Ya Abana kai wannan yake nema?
Na ce: Na’am.
Ya ce: Shin yana kan abin da kake kai?
Na ce: Na’am.
Ya ce: Maza ka tafi zuwa gare shi ka yanke dawafin.
Na ce: Koda ya kasance dawafin wajibi?
Ya ce: Na’am.
Abbana ya ce: Sai na tafi, bayan nan –wani lokaci- sai na shiga wajansa (A.S) na tambaye shi game da hakkin mumini. Sai ya ce: Bari kada ka kawo wannan! Ban gushe ba ina sake tambaya har sai da ya ce: Ya Abana ka raba masa rabin dukiyarka, sannan sai ya kale ni ya ga abin da ya shige ni, sai ya ce: Ya Abana ashe ba ka san Allah ya riga ya ambaci masu fifita wasu a kan kansu ba?
Na ce: Haka ne!
Ya ce: “Idan ka ba shi rabin dukiyarka ba ka fifita shi ba, kana fifita shi ne kawai idan ka ba shi daya rabin!
Na ce
: hakika a yanayinmu mai ban kunya bai dace ba mu kira kanmu muminai na hakika. Mu muna wani waje ne, koyarwar Imamanmu (A.S) tana wani wajen. Kuma abin da ya Shigi zuciyar Abbana zai Shigi zuciyar duk mai karanta wannan hadisin sai dai ya juya fuskarsa kawai yana mai mantar da kansa shi kamar wani ake wa magana ba shi ba, kuma ba ya yi wa kansa hisabi irin na mutumin da yake abin tambaya.