• Farawa
  • Na Baya
  • 19 /
  • Na Gaba
  • Karewa
  •  
  • Gurzawa HTML
  • Gurzawa Word
  • Gurzawa PDF
  • Budawa: 3977 / Gurzawa: 4081
Girma Girma Girma
Tawassuli

Tawassuli

Mawallafi:
Hausa

KAMUN KAFA(Tawassuli)

Wallafar: Ayatullahi Ja'afar Subhani

Fassarar: Hafiz Muhammad Sa’id

KAMUN KAFA DA ANNABAWA DA WALIYYAN ALLAH

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Imam Mahadi (A.S) yana cewa : “Kuma Kowane mutum daga cikinku ya yi aiki da abin da zai kusanta da shi zuwa ga soyayyarmu, kuma ya nisanci abin da zai kusantar da shi ga kinmu da fushinmu” Biharul Anwar: 53, shafi 126.

Kamun kafa

Tsarin duniya yana bisa ka'idoji da dalili a kan komai, saboda haka duk wani abu wanda zai faru a duniya yakan faruwa tare da dalili wanda ya kebanci shi abin da ya farun, sannan shi ma wannan abin da ya faru zai tasiri ga wani abu na daban, tasirin da wani abu yake sanya a cikin wani daban duk yana faruwa ne da izinin Allah madaukaki. Allah shi ne wanda ya halicci duniya sannan ya sanya alaka tsakanin abubuwan da suke duniya ta yadda wasu sukan yi tasiri a cikin wasu. Babu shakka rana tana bayar da wani sinadari wanda sauran halittu suke amfani da shi don su rayu, haka nan wata yana bayar da haske, sannan wuta tana bayar da zafi. Dukkan wadannan abubuwa suna yin tasiri ga waninsu, sannan akwai alaka ta musamman tsakanin rana da wata da wuta da kuma abin da suke bayarwa. Sannan dukkan wannan tasirin da ake gani babu wanda yake sanya shi sai Allah wanda shi ne ya halicce su, sannan kuma shi ne ya sanya wannan alakar da take akwai abin da yake faruwa tsakanin abubuwa daban-daban, kuma dukkansu suna samuwa daga gare shi maudakaki. Sakamakon haka ne wani lokaci yakan dauke tasirin da abu yake da shi, kamar yadda ya dauke zafin wuta ga annabi Ibrahim (A.S) ya kuma daidaita ta tamkar wani lambu mai sanyi, wannan kuwa duk don ya nuna cewa daga gare shi ne dukkan wannan tasirin na hakika yake da kuma niyyarsa ne.

Daga wannan bayanin muna iya daukar sakamako cewa: duk wani abu wanda yake faruwa a cikin duniya muke ganinta, a lokacin da muke ganin cewa ta samu ne daga wani abu daga cikin abubuwan da suke a cikin duniya, a daida- wannan lokacin kuma suna zuwa ne daga Allah kuma aikinsa ne. Sannan wannan abin bai saba wa hankali ba ta yadda za a ce ba zai yiwuwa ba. Domin kuwa Allah shi ne wanda yake da cikakken iko yake kuma yin wani abu ba tare da taimakon wani ba, amma dukkan wani yayin da zai aikata wani abu sai da taimakon Allah. wato duk abin da suke aikatawa tare da izinin Allah suke aikata shi, don haka muna iya cewa su ne suka aikata kuma muna iya cewa Allah ne domin kuwa a hakikanin gaskiya shi ne ya aikata, domin kuwa da bai bayar da izini ba, ba za ayi hakan ba.

Sannan kowa ya san daya daga cikin matakan tauhidi ko kadaita Allah shi ne kataita Allah a cikin halitta, wato babu wani mai halittawa sai Allah madaukaki, amma duk da haka kadaita Allah a cikin halittawa ba yana nufin kore duk wani tasiri daga wani abu ba, wato ma'anarsa shi ne halitta ba tare da dogara da wani ba, shi kadai ne yake iya yin haka, sannan duk wani tasiri na sauran wasu halittu yana samuwa ne da izinin Allah.

A cikin wasu ayoyin an yi nuni da dukkan wadannan nau'o'i guda biyu na yin tasiri. Misali aiki guda a daidai lokaci guda ana a jingina shi zuwa ga Mutum, sannan kuma ana jingina shi zuwa ga Allah, duk da cewa aiki guda yana gangarowa ne kawai daga abu guda. Amma tunda wadannan masu aikin daya yana karkashin daya ne babu matsala, wato daya shi ne na asali dayan kuwa yana bin na asalin, saboda haka babu abin da zai hana hakan.

Allah yana cewa wa Manzo (S.A.W): "Ba kai ne ka yi jifa ba a lokacin da ka yi jifa". A nan Kur'ani yana jingina aiki guda daya zuwa ga masu aiki guda biyu kamar haka:

1- Lokacin da ka yi jifa.

2- Allah ne ya yi jifar.

Dukkan wannan jinginawa guda ta yi daidai kuma ta dace da wurin, domin kuwa aikin Manzo ya faru ne da taimako da izinin Allah, saboda haka jingina wannan aiki guda daya ga dukkansu ya yi daidai. Sannan kamar aiki guda a jingina shi ga Allah sannan a jingina zuwa ga wani daban ya zo da yawa a cikin Kur'ani. Amma a nan kawai zamu bayar da misali guda biyu kawai:

1-Kur'ani a lokaci guda yana jingina rubuta ayyukan bayi zuwa ga mala'iku, sannan a wani wurin daban yana jingina wannan aiki zuwa ga Allah madaukaki.

2- A wani wuri ana jingina daukar rayukan mutane zuwa ga mala'ikun mutuwa, amma a wani wuri ana jingina wannan aiki zuwa ga Allah. Wadannan ayoyin suna bayyanar da yadda tsarin halitta yake karkashin ka'idar tasiri da mai tasiri, ta yadda abubwan da suke fauwa suke tasiri tsakanin juna. Amma dukkan wannan tsari suna jingina ne zuwa ga Allah madaukaki, sannan a karkashin nufinsa da izininsa suke ci gaba da rayuwarsu. Saboda haka duk wani abu wanda yake yin tasiri a cikin tsarin duniya, yana karkashin rundunar Ubangiji ne sannan kuma aikata abin da Allah ya umurce su ne. Sannan Allah kawai ne ya san yawan wannan runduna ta Allah.

Tare da la'akari da wannan bayani, wanda yake matsayin nuni daga wahayi, (cewa babu mai halitta da gaskiya sai Allah) sakamakon binciken dan Adam na ilimi (ta yadda suka tabbatar da yadda tasirin da yake akwai tsakanin halittu a cikin duniya) ba ya nuni da sabani a kan abin da muka ambata kokadan. Wadanda suke ganin wahayi ya saba wa ilimi ko kuma addini ya sabawa ilimi, ba su yi kyakkyawar fassara ba ne a kan hakan. Ko kuma sun yi wa ilimin zamani mummunar fahimta. Da wata ma'anar kuwa, duk wadannan abubuwa guda biyu na kasa sun dace kuma sun yi daidai su ne kamar haka:

1-Imani da kadaita Allah a cikin halittawa cewa babu wani wanda yake yin wani abu ba tare da dogara da wani ba sai Allah.

2-Tasirin wasu abubuwan a cikin wasu ayyuka dukkansu suna faruwa ne da izinin Allah da nufinsa. Idan muka ga wadannan asali guda biyu wani lokaci suna karo da juna, wannan ya samu asali ne ta yadda wasu suke fassara kadaita Allah a cikin halitta da wata ma'ana wacce ba ta inganta ba. Ta yadda suke daukar babu wani mai yin wani abu sai Allah kawai, wato duk wani mai yin wani abu, ba shi yake yin abin ba, kawai Allah ne yake yin komai, dan Adam ba shi da hannu wajen yin ayyukansa (nazarin Asha'ira). Ko kuma kamar yadda wasu suke ganin bayan wadannan abubuwan da muke gani a cikin duniya suna da tasiri ga wasu abubuwa, babu wani da sunan Allah wanda yake da tasiri a cikin duniya, wato duk abin da mutum ya yi daga gareshi ne babu hannun Allah a cikin. (Nazarin wadanda ba su yarda da wani abu ba a bayan wannan duniyar da muke gani).

Saboda haka dukkan wannan fahimta guda biyu kuskure ce kuma ba ta inganta ba, wanda dukkan biyun yana nuni ne ga takaitawa da kuma wuce wuri. Rashin ingancin fahimta ta biyu kuwa ya faru ne sakamakon yadda suke ganin duniya kawai ta takaita ne ga wannan duniya da muke gani kuma muke iya jinta, wato ba su yi imani da duniyar gaibu ba, wanda ba ya bukatar wani Karin bayani. Domin kuwa a nan muna magana ne da wadanda suka yi imani da Allah kuma suna ganin rashin ingancin akidar daukar wannan duniyar ita ce kawai kuma babu wani abu a bayanta. Amma rashin ingancin fahimta ta farko kuwa yana komawa ne ga wasu daga cikin malaman akida wadanda suka tafi a kan wannan fahimta, alhali kuwa Allah madaukaki a fili yana nuna yadda halittu suke da tasiri a cikin rayuwa, wajen faruwar wasu abubuwa. Sannan kuma kowa zai iya shaida hakan domin kuwa wani abu ne wanda muke gani da idanummu.

Saboda haka ta yaya zamu ki yarda da tasirin da halittu suke da shi a cikin rayuwa, shi kuwa wahayi yana bayyana gaskiyar wannan al'amari. A matsayin misali yana bayyanar da ruwa a matsayin wanda yake da tasiri wajen rayuwar tsirrai, kamar yadda yake cewa: "Shi ne wanda ya sanya muku kasa a shimfide, sannan ya gina muku sama, Kuma yana saukar da ruwa daga sama, sannan yana fitar da 'ya'yan itatuwa daga ruwa wadanda arziki ne a gare ku. "

Saboda haka nufin Allah ya yi rigaye a kan cewa duk da cewa dole ne mutum ya yi imani da cewa komai yana zuwa ne daga Allah, amma duk da haka mutum dole ne ya tanaji wasu abubuwa wadanda zasu kai shi zuwa ga cimma abin da yake nema.

Wannan asali da ka'ida kuwa, tana gudana har da abubuwan da suka shafi shiryarwa da makamantansu, sakamakon haka ne Allah madaukai ya bai wa mutum wata halitta a cikin zatinsa wacce zata taimaka masa wajen yin imani da Allah, haka hankali, annabawa da malamai da masana da makamantan wannan, Allah madaukaki ya sanya su a matsayin wadanda zasu yi mana jagora domin mu samu shiriyar Ubangiji. Kamar yadda ya kasance a wasu wurare a cikin Kur'ani mai girma Allah yana bayyana cewa shiriya wani abu ne daga gare shi, kamar inda yake cewa: "Yana batar da wanda ya so yana kuma shiryar da wanda ya so" .

Sannan wani wurin yana cewa: "Lallai kana shiryarwa zuwa ga hanya madaidaiciya".

Sannan babu karo da juna don an jingina shiryarwa zuwa ga dukkansu su biyun, wato asalin shiryarwa yana ga Allah, sannan Manzo wanda yake kamar sila ne na aiwatar da wannan aiki, babu laifi a jingina wannan aiki zuwa gare shi.

Takaitaccen tunanin wasu wadanda suke aibata kasantuwar tasirin wasu halittu ya samu asali ne sakamakon rashin fahimta mai kyau a kan koyarwar Kur'ani mai girma kamar yadda suke ganinsa ya saba da azirtawar Ubangiji da kuma tawakkali da shi, don haka ne ba su iya fassara koyarwar Kur'ani ba da kyau kamar yadda ya kamata.

Kasantuwar tasirin wasu daga cikin abubuwan halitta, sama ba ya karo da tawakkalli ko kadaita Allah a cikin tafiyar da al'amura, haka nan a cikin kadaita Allah a cikin ayyukansa. Domin kuwa a wajen mutum mai tauhidi wanda kuma yake da ilimi, dukkan wasu abubuwan da suke tasiri a cikin rayuwa suna yin wannan tasiri ne a karkashin inuwar Ubangiji da izininsa. Sannan yana ganin duk wani tasiri da yake a cikin duniya yana bayyana nufin Ubangiji wanda ba shi da iyaka wajen aikinsa kuma wanda ya halicci duniya baki daya.

Sannan dangane da bukatun ruhi da na zahiri a wajen hakan, babu wani bambanci. Sakamakon haka ne Allah yake umurtar masu imani da su tashi domin su yi kamun kafa a wajensa inda yake cewa: "Yaku wadanda kuka yi imani, ku ji tsoron Allah, sannan ko nemi tsani zuwa gare shi, Kuma ku yi jihadi a tafarkin Allah ko kun rabauta".

A nan dole mu yi bincike a kan ma'anar wannan tsani da aka ambata a aya ta sama me ake nufi da shi?

Marubuta kamusun lugga sun bayani a kan yadda ake amfani da lafazin wasila cikin harshen larabci kamar haka:

1-Makami da matsayi: a wani hadisi Manzo (S.A.W) yana cewa: "Ku nema mini matsayi a wajen Allah"

2- Kusanci zuwa wajen Allah.

3- Samar da abubuwan da zasu kusantar da mutum ta yadda zai samu kusanci zuwa ga Allah.

Tabbas ma'ana ta farko ba ita ake nufi ba a nan, domin kuwa matsayin da Manzo yake da shi a wajen Allah babu wanda yake da shi, kuma babu wanda zai samu kamarsa. Saboda haka dole ne mu fassara wannan aya da daya daga cikin ma'anoni biyu na karshe, kuma ga dukkan alamu wannan aya tana daukar ma'ana ta uku ne, domin kuwa abin da yake tabbatar da hakan bayan an yi umarni da neman tsani, yana yin umarni da jihadi wanda yana sanya kusanci zuwa ga Allah. Sannan wannan ya zo a cikin hadubar Imam Ali (A.S) wanda ya dauki ma'anar tsani da cewa shi ne riko da abin da zai kusantar da mutum zuwa ga Ubangiji, inda yake cewa: Mafificin abin da masu neman kusanci zuwa ga Allah zasu nemi kusanci zuwa gare shi, shi ne yin imani da shi, da manzonsa da yin jihadi a tafarkin Allah, sannan da tsayar da salla domin kuwa hanya ce kuma shari'a ce, sannan fitar da zakka.

A cikin wannan huduba ta Imam yana kawo wajibai na shari'a wanda yake nuna cewa su ne suke kusantar da mutum zuwa ga Allah. Ayar da aka ambata a sama, tare da hukuncin hankali tana yi mana nuni ne tana cewa: Dan Adam, wajen samun daukaka ta ruhi kamar kusanci zuwa ga Allah, kamar yadda ya kasance yana neman abin da zai biya bukatunsa na duniya, suma haka dole ne ya nemi abin da zai kusantar da shi zuwa ga wadannan abubuwan da yake bukata na ruhi, sannan ba tare da wannan ba mutum ba zai iya cimma abin da yake bukata ba.

Abin da yake akwai a nan shi ne abubuwan da suke kusantar da mutum zuwa ga Allah dole shari'a ce zata bayyana su. Domin kuwa hankalin dan Adam ba zai iya gano wadannan abubuwan ba, ta yadda zai gano abubuwan da zasu kusantar da shi zuwa ga Allah da abubuwan da zasu kai shi zuwa ga gafara da makamantansu, sannan bai kamata ba a nan wani ya yi tunanin cewa da wannan ayar ne kawai za a iya kafa hujja a kan ingancin kamun kafa da annabawa da waliyyai. Wannan aya kamar wata ka'ida ce ta baki daya wacce kuma hankali yake hukunci a kan ingancinta, amma dangane da abubuwan da zasu kusantar da mutum ko su sanya ya samu gafara ko ya samu biyan bukatunsa na ruhi, hankali ba zai iya gane wannan ba, saboda haka dole ne Allah ko manzonsa da ma'asumai (A.S) su bayyanar da hakan. Kamar yadda imam a huduba ta sama yake bayyanar da cewa imani da Allah da manzonsa da jihadi a tafarkin Allah, da tsayar da salla da bayar da zakka suna daga cikin muhimman abubuwan da suke kusantar da mutum zuwa ga Allah.

Yanzu kuma lokaci ya yi inda zamu bayyanar da kashe-kashen neman tsani ko kamun kafa da wata ma'anar, sannan mu yi bayanin hukuncin kowane ta yadda ya dace da Kur'ani da Sunna ko kuma sabanin hakan.

Kamun kafa yana da kashe-kashe kamar yadda zamu ambata a kasa kamar haka:

1-Kamun kafa Da Sunaye Da Siffofin Allah

Daya daga cikin rabe-raben kamun kafa ko neman tsani zuwa ga Allah shi ne neman kusanci zuwa ga Allah ta hanyar kiran sunaye da siffofinsa. Wannan nau'i kuwa na kamun kafa ko tawassuli ya zo da yawa a cikin ruwayoyin Ahlul baiti (A.S), amma a nan kawai zamu wadatu da hadisai guda biyu da suke nuni a kan haka:

Tirmizi a cikin Sunan dinsa ya ruwaito daga Buraida shi kuma daga Manzo (S.A.W) cewa yaji wani mutum yana cewa: Ya Allah ina rokon da kasantuwar na sheda cewa babu abin bauta da gaskiya sai kai, sannan kai kadai ne kuma mai biyan bukata, sannan ba a haife ka ba kuma ba ka haifa ba, sannan babu wani wanda ya yi daidai da kai.

Sai Manzo ya ce masa lallai ka roki Allah da babban suna wanda idan aka kira sa da shi zai amsa, idan kuwa aka roke shi da shi zai bai wa mutum abin da ya nema.

2-Ya zo a cikin wata addu'a Imam Bakir da Imam Sadik (A.S) suna cewa: "Ya Allah ina rokon ka da babban sunanka wanda ya fi kowane girma, mafigirma da daukaka wanda idan aka roke ka da shi domin kofofin da suke a kulle a sama ana so su bude zasu bude, sannan idan aka kira ka da shi domin fadada kofofin da suke kasa zasu fadada, kuma idan aka roke ka da shi domin samun sauki, za a samu saukin. "

2-Kamun kafa Da Kur'ani

Daya daga cikin hanyoyin da ake kamun kafa da su domin neman kusanci ga Ubangiji shi ne mutum ya karanta Kur'ani, ta wannan hanyar sai Allah ya biya masa bukatarsa. A hakikanin gaskiya wannan nau'in kamun kafa, kamun kafa ne da ayyukan Ubangiji, domin kuwa Kur'ani maganar Allah ce wacce ta sauka a kan zuciyar Manzo (S.A.W)

Ahmad Bn Hambal ya ruwaito daga Imran Bn Husaini yana cewa: Na ji daga manzon Allah (S.A.W) yana cewa: "Ku karanta Kur'ani ku roki Allah da shi, kafin wasu gungun mutane su zo wadanda zasu roki mutane da shi.

Idan muka lura da kyau a cikin wannan hadisi yana nuna mana wani abu, wannan kuwa shi ne, kamun kafa da duk wanda yake da girma da matsayi a wajen Allah wani abu ne wanda ya halatta, saboda mustahabbi ne a daren lailatul kadari mutum ya buda Kur'ani ya karanta ya roki Allah da shi tare da wannan addu'a kamar haka: "Ya Allah ina rokonka da wannan Kur'ani da abin da ka saukar a cikinsa, a cikinsa akwai babban sunanka da sunayenka kyawawa…

3-Kamun kafa Da Kyawawan Ayyuka

Kamar yadda muka ambata a farkon wannan Bahasi cewa idab mutum yana so ya cimma wani abu na rayuwar duniya ta hanyar hankalinsa ne zai gano ta wace hanya ce ya kamata ya bi domin ya cimma wannan abin da yake nema. Wato mutum ya san abin da ya dace ya aikata domin ya biya bukatunsa na rayuwa, misali kamar idan mutum yana jin yunwa ko kishirwa ya san cewa abinci ko ruwa zai sha don ya yi maganin wannan kishirwa da yunwar. Amma dangane da abin da ya shafi ruhi ko lahira, ba zai yiwu ba mutum ya iya gano hanyar da zai bi don ya cimma abin da yake so ya cimmawa, saboda haka a nan yana da bukatuwa zuwa Allah ko wakilinsa wanda zai gwada masa hanyar da ya kamata ya bi, sannan ba tare da jagorancinsa ba babu yadda zai yi ya isa zuwa ga hadafinsa, domin kuwa bin wata hanya wacce ba shari'a ba ce ta bayyana hakan zai zama bidi'a a cikin addini. Saboda haka musulmi dole ne a nan dangane da abin da ya shafi addini ya yi riko da abin da yazo a cikin Kur'ani da Sunna.

Kamun kafa da kyawawa kyawawa wanda shi ne nau'i na uku a cikin wannan Bahasi, a cikin Kur'ani an yi nuni da shi duk da cewa ba a bayyane ba ne kamar yadda ya zo a bayyana ne a cikin hadisai, bayaninsa kuwa atakaice shi ne, idan mutum ya aikata wani aiki domin Allah, yayin da mutum ya shiga wata matsala, yana iya ambatar wannan aikin da ya yi mai kyau domin Allah madaukaki ya yaye masa matsalar da ya shiga. Kai duk lokacin da mutum ya aikata wani aiki mai kyau yana iya rokon Allah da ya biya masa bukata da wannan aiki da ya aikata. Ga wasu abubuwa da suka zo a tarihi wadanda suke ba da sheda a kan hakan.

1-Annabi Ibrahim yayin da yake gina dakin ka'aba, ya roki Allah da ya sanya shi da dansa Isma'il su kasance masu biyayya ga Allah. Ga abin da Kur'ani yake cewa a kan haka: "A lokacin da Ibarahim shi da Isma'il suke daga ginin Ka'aba, sai suka ce ya Allah ka karba mana kai ne mai ji masani. Ya Allah ka sanya mu masu mika wuya gare ka, sannan daga zuriyar mu ka sanya su masu mika wuya a gareka, ya Allah ka koyar da mu ayyukan hajji, ka kuma karbi tubarmu, lallai kaine mai karbar tuba mai jin kai. " Mun ga yadda annabi Ibarahim da dansa Isma'il suka yi kyakkyawan aiki na ginin dakin ka'aba, a wannan lokaci sai suka roki Allah wasu abubuwa kamar haka:

A-Karbar wannan aiki daga dukkan su biyun.

B-Allah ya sanya su masu biyayya a gare shi.

C-Koyar da su aikin hajji.

D-Karbar tubarsu da sanya su a cikin rahama.

2-A cikin wata ayar ga abin da ya zo: "Muminai wadanda suke cewa: Ya Allah lallai mun yi imani ka yi mana gafara a kan zunubbammu, sannan ka tseratar da mu daga azabar wuta".

A cikin wannan aya sun roki Allah da cewa ya gafarta musu zunubbansu sakamakon ayyukan kyawawa inda suke cewa "lallai mun yi imani da kai".

Kamar yadda muka yi bayani a baya, ayoyin Kur'ani sun yi nuni da halascin kamun kafa da ayyuka na gari duk da cewa ba a bayyane ba ne. Amma a cikin ruwayoyi an yi bayanin hakan a fili. Sannan masu ruwaito hadisi daga bangarori guda biyu, sun ruwaito cewa wasu muminai guda uku sun kasance a cikin daji, sai ruwan sama ya taso, sai suka shiga cikin wani kogo domin su buya. Amma cikin rashin sa'a sakamakon wannan ruwa da iska sai wani bangaren dutse ya gangaro daga sama ya rufe kofar wannan kogo, a wannan lokaci sai daya daga cikinsu ya ce: Fadin gaskiya ce kawai abin da zai fitar da mu daga cikin wannan dutse, don haka ku zo duk wanda ya yi wani kyakkyawan aiki ya fada, sai mu roki Allah sakamakon albarkacin wannan aiki ya tseratar da mu. Dukkansu ukun suka fadi wani aiki wanda suka yi saboda Allah, kamun kafar da suka yi da wadannan ayyuka na su, cikin ikon Allah sai wannan dutse ya bude suka fita daga wannan hali da suka shiga.

Malamin Hadisi Baraki (ya rasu shekra ta 274) bayan ya ambaci wannan labari sai ya ce: Daya daga cikinsu cewa ya yi, ya kasance na baiwa wata mace kudi domin mu aikata wani aiki wanda bai dace ba, sannan kuma ita ma ta shirya a kan hakan, amma sai na tuna cewa akwai azabar lahira ga masu yin hakan, sai na kaurace wa wannan aiki, a wannan lokaci sai kofar ta dan bude kadan.

Sai daya kuma daga cikinsu shi ma ya ce:

Na ksance na tara wasu mutane domin su yi mini aikin kwadago, sannan zan ba kowane daya daga cikinsu rabin darhami matsayin ladar aikinsu. Bayan sun gama wannan aiki sai wani daga cikinsu ya nemi in ba shi darhami guda, wato a matsayin shi ya yi aikin mutum biyu ne, amma sai ban amince da abin da ya fada ba, sai bai amshi komai ba ya fita, (sai na kasance na yi amfani da kudin na wadanda suke a hannuna) na yi noma sannan kuma na samu amfani mai yawa. lokacin da ya ji wannan labari sai ya zo a wajena, sai ba shi darhami dubu goma, ya Allah na yi wannan aiki ne domin neman yardarka. a wannan lokaci sai kofar kogo ta dan kara budewa.

Sai na ukkunsu ya ce: Wata rana na kawo wa babana da mamana kwanon madara sai na tarar da su duk suna barci. Sai na yi tunani a cikin raina cewa idan na ajiye musu wannan madara a kasa na tafi gida mai yiwuwa kafin su tashi kuda ko sauro ya fada musu a cikin wannan madara, sannan kuma ba ni so in tayar da su daga barci. saboda haka sai na yi tsaye da wannan madara har suka ta shi daga barci sannan suka sha wannan madara. A wannan lokaci sai kofar kogo ta bude dukkanta suka fita daga wannan hali da suka shiga.

Wannan kissa kuwa masu hadisi daga bangare guda biyu Sunna da Shi'a sun kawo ta duk da cewa akwai sabani a wasu abubuwa.

4-Kamun kafa Da Adu'ar Manzo (S.A.W)

Manzo (S.A.W) mutum ne wanda yake ya fi kowa girma da daukaka a cikin dukkan halittar da Allah ya yi, Ayoyin Kur'ani sun yi nuni da haka a wurare da dama, saboda haka ba zai yiwu ba mu kawo dukkansu a wannan wuri.

Dangane da darajar Manzo ya wadatar da mu a kan cewa yana matsayin mai kare al'umma daga azabar Allah, Allah yana bayyanarwa a cikin Kur'ani cewa, matukar Manzo yana a cikin al'umma to Allah ba zai kama wannan al'ummar ba da azaba ba, kamar yadda yake cewa: Allah bai kasance zai azabtar da su ba matukar kanacikinsu, sannan Allah ba zai azabtar da sub a matukar suna neman gafara".

Sannan ya wadatar da mu a kan girman Manzo inda Allah madaukaki ya sanya sunan Manzo a gefen sunansa, sannan ya sanya biyayya ga Manzo tare da biyayya ga Allah, a kan haka Allah yana cewe: "Duk wanda ya bi Allah ya bi Manzo, lallai ya samu babban rabo".

Wadannan ayoyi da masu kama da su suna bayyanar da dajara da karama ta Manzo (S.A.W) matsayi da darajar da babu wani a cikin halitta wanda yake da shi, sakamakon wannan matsayin da daukaka da Manzo yake da shi a wajen Allah duk abin da yaroka za a biya masa bukatarsa. Don haka ne aka bai wa masu laifuka da zunubbai umurnin cewa, su nemi Manzo daya nema musu gafara a wajen Allah, inda Allah madaukaki yake cewa: "Da wadanda suka zalunci kawunansu zasu zo maka suna masu neman gafara a wajen Allah, kuma Manzo ya nema musu gafara, da sun samu Allah yana mai gafara kuma mai karbar tuba".

Sannan zamu iya fahimta daga wasu ayoyi cewa, sakamakon matsayi da daukaka manzanni sun kasance ana iya kamun kafa da su a wajen Allah kamar yadda zamu gani dangane da 'ya'yan annabi Yakub (A.S) lokacin da kuskuransu ya bayyana a fili, sai suka cewa mahaifinsu: "Ya babanmu ka nema mana gafara lallai mun kasance masu kuskure. Sai ya ce musu zan nema muku gafara a wajen ubangijina, kuma lallai shi mai gafara ne mai rahama".

Dangane da halascin wannan nau'i na kamun kafa babu wani shakku a cikinsa, domin kuwa babu sabani a kan haka. Abin da yake da muhimmanci a nan shi ne, sanin dalilin da ya sa nya ake karbar addu'ar annabawa.

Babu shakka tushen abin da ya sanya ake karbar addu'ar annabi ya samo asali ne daga tsarkin ruhinsa, sannan da kusancinsa ga Allah madaukaki. Don haka sakamakon wannan girma da daukaka ne na ruhi ya sanya Allah yake karbar addu'arsu.

Babu shakka addu'ar da ta taso daga ruhi mai tsarki wanda yake cike da soyayyar Ubangiji, ba tare da wani bata lokaci ba zata samu karbuwa a wajen Allah madaukaki.

Idan har akwai wata magana a kan halascin wannan kamun kafa kuwa, zai kasance ne dangane da kamun kafa da annabawa yayin da suka rasu wato lokacin da ba su raye a duniya. Tare da kula da abin da muka fada a wajen ziyarar kabari, mun yi bayani kan cewa babu wani bambanci tsakanin lokacin da annabawa suke a raye da lokacin da ba su raye a duniya, domin kuwa Manzo a cikin wadannan hali guda biyu yana iya nema wa mutum gafara a wajen Allah. Zamu yi cikakken bayani a kan wannan a cikin nau'in kamun kafa na shida insha Allah.

5-Kamun kafa Da Addu'ar Dan'uwa Mumini

Kur'ani yana bayyanar da cewa mala'iku suna yi wa masu imani addu'a, kamar haka:

"Wadanda suke daukar al'arshi da na gefensa, suna tasbihi da godiyar ubangijinsu, kuma suna masu imani da shi, sannan suna neman gafara ga wadanda suka yi imani" .

Wannan ba yana nuna cewa ba mala'iku ne kawai suke yi wa masu imani addu'a. Domin kuwa Kur'ani a fifli yana bayar da labarin yadda muminai suke wa junansu addu'ga abin da Kur'ani yake cewa: "Wadanda suka zo a bayansu, suna cewa, ya ubangijinmu! Ka yi mana gafara da 'yan'uwammu wadanda suka riga mu da imani, ya Allah kada ka sanya jin zafin a cikin zukatanmu dangane da wadanda suka yi imani, ya Allah kai ne mai rangwame mai rahama".

A cikin ayoyin da muka ambata a sama zamu iya fahimtar cewa, addu'ar mala'iku masu daukar al'arshi da kuma addu'ar muminai a kan 'yan'uwansu ta cancanci karbuwa. Saboda haka wannan aya tana nuna mana cewa mutum yana iya neman addu'a daga mala'ku da kuma sauran 'yan'uwansa masu imani.

Dangane da karbar adduar mumini kuwa, ya wadatar da mu inda Manzo (S.A.W) yake neman muminai su yi masa addu'a, inda yake cewa: Ku nema mini tsani a wajen Allah domin kuwa matsayi ne a cikin aljanna, babu kuwa wanda zai samu wannan matsayin sai wasu da suka cancanta daga cikin bayinsa, ina fata in zama nine, don haka duk wanda ya nemi kamun kafa da ni, cetona ya halasta gare shi". Kasantuwar wannan kamun kafar ya karbu a wajen dukkan musulmi ba tare da wani sabani ba, muna iya wadatuwa da wannan.

6-Kamun kafa Da Addu'ar Manzo Bayan Rasuwarsa

Bahsin da ya gabata ya tabbatar mana yadda kofofin rahama suka kasance a bude ga masu laifuka, ta yadda zasu iya kamun kafa da Manzo kamar yadda aya take nuni da hakan (da wadanda suka zalunci kawunansu sun…) wato suka nemi Manzo da ya neman musu gafara a wajen Allah. Sakamakon haka ne Kur'ani yake zargin munafukai domin kasantuwarsu sun rasa wannan falalar mai dimbin yawa. Ga abin da yake cewa: "Duk lokacin da aka ce musu, ku tafi zuwa Manzo domin ya nema muku gafara sai su kawar da kansu".

A nan akwai abin tambaya: shin sakamakon tafiyar Manzo zuwa ga rahamar Ubangiji wannan kofar gafarar da jin kai shi kenan ta kulle, ta yadda babu wani musulmi da zai je wajen Manzo ya roke shi da ya nema masa gafara a wajen Allah, ko kuwa wannan kofar albarka tananan bude kamar lokacin da yana raye? Wato musulmi har yanzu idan suka je haraminsa suna iya neman addu'arsa, ta yadda wannan ayar da muka ambata; "Da wadanda suka zalunci kansu sun zo wajenka suka neme ka da nema musu gafarar..". tana amfani a dukkan lokuta guda biyu, wato zamanin raywarsa da kuma bayan wafatinsa?

A wajen bayar da wannan masa dole ne a ce: Musulmi daga sahabbai da tabi'ai har zuwa yanzu sun kasance a aikace suna daukar wannan kofa a bude take, sannan musulmai a lokacin da suka ziyarci raudhar Manzo bayan yi wa manzon tsira sallama sukan karanta wannan ayar da muka ambata, tare da neman gafara daga Allah kuma suna rokon Manzo da ya nema musu gafara a wajen Allah madaukaki, saboda haka duk lokacin da mutum ya je ziyarar Manzo zai ga wannan al'amari daga al'ummar musulmi.

Bayan abin da tarihi yake nunawa ta hanyar ayyukan al'ummar musulmi danagane da neman addu'ar Manzo, addu'ar ziyarar Manzo ma wacce sunna da Shi'a suka ruwaito wannan addu'a tana tabbatar da wannan magana ta neman addu'ar Manzo. Domin jan hankalin masu karatu kuma suka kara natsuwa da abin da muke magana a kai, zamu kawo wassu daga cikin maganganunsu, ta yadda zai bayyanar mana yadda manyan malamai tun tsawon zamani suke neman kamun kafa da Manzo wajen yi musu addu'a:

1-Zakariya Muhyiddin Nawawi (631-676) Yana rubuta cewa: Mai ziyara yakan fuskanci Manzo ya yi kamun kafa da Manzo a kan abin da yake bukata kuma ta hanyarsa ya nemi ceto daga Allah, yana daga abu mafi kyau kasantuwar Mawardi, Alkali Abu Tayyib da wasu daga cikin manyan malamai suka ruwaito daga Utba tare da yabo suna cewa:

Utba yana cewa: Na kasance a wajen Manzo (S.A.W) wani mutum daga daji ya zo wajen Manzo ya ce "Assalamu alaika ya rasulullah, na ji Allah yana cewa: "Da wadanda suka zalunci kansu sun zo wajenka suka nemi gafara, kuma Manzo ya nema musu gafara, da sun samu Allah yana mai karbar tuba kuma mai jin kai"Lallai na zo wajenka ina mai neman gafara daga zunubaina sannan mai neman ceto a wajen Allah tare da kamun kafa da kai".

Kada mu yi tunanin cewa Nawawi ne kawai da malamansa suka tafi a kan ingancin kamun kafa da neman ceto daga Manzo. Malaman fikhu da na hadisi da dama sun kawo wannan a cikin littafansu na ziyara.

2-Kuddama Hambali (ya rasu shekara ta 620) a cikin ladubban ziyarar kabarin Manzo inda yake kawo maganar cewa"Mustahabbi ne ziyarar Manzo" Yaruwaito daga Abu Huraira yana cewa Manzo (S.A.W) ya ce: Duk wanda ya yi mini sallama, zan amsa masa sallamarsa. Sannan sai ya ruwaito daga Utba abin da muka ambata a baya kadan cikin hadisin Nawawi. Ya ce manufarsa wajen kawo wannan hadisi shi ne, don ya nuna cewa ana gabatar da ziyarar Manzo kamar haka:

3-Samhudi a cikin littafin "Mustau'ab" wanda Muhammad Bn Abdullah Samiri Hambali ya rubuta, yana ruwaito yadda ake ziyarar Manzo kamar haka:

Assalamu Alaika ya Rasulallah, assalamu alaika ya Nabiyyallah! Ya Allah kai ne ka fada a cikin littafinka ga annabinka cewa: "Da wadanda suka zalunci kawunansu…Ya Allah ga ni na zo wajen manzonka (S.A.W) ina mai neman gafara, ya Allah ina rokonka a kan ka wajabta mini rahamarka, kamar yadda ka wajabta ga wanda ya zo wajensa yayin da yake a raye, ya Allah ina ina kamun kafa da annabinka zuwa gare ka".

4- Gazali (ya rasu 505) Dangane da falalar ziyarar Madina da yadda ake ziyarar Manzo ya ruwaito a bayyane yana cewa: Bayan mutum ya gama sallama ga Manzo, sai ya dubi kabarin Manzo yana tsaye, sannan ya yi godiya ga Allah da yabonsa, sai ya aika gaisuwa mai yawa zuwa ga Manzo, sannan ya karanta wannna ayar da take cewa: Da wadanda suka zalunci kawunansu sun zo, sannan ya ce ya Allah mun ji kiran ka kuma mun amsa umurninka, sannan mun yi kamun kafa da manzonka muna neman cetonka daga zunubbammu, lallai zunubbai masu nauyi sun yi mana yawa…"

5- Sheikh Hasan Bn Ammar sharanbalani a cikin littafinsa "Murakil falah" yana ruwaito ziyarar Manzo kamar haka:

"Amincin Allah ya tabbata gareka ya kai shugabana ya manzon Allah, Amincin Allah ya tabbata a gareka ya annabin Allah! Lallai kurakurai sun karya mana kashin baya, sannan nauyin zunubban ya yi mana yawa a kan kafadummu. Kai ne mai ceto kuma wanda ake karbar cetonsa. Allah madaukaki ya yi maka alkawarin ceto da matsayi mai girma kuma abin yabo a wurinsa, sannan yana cewa: "Duk lokacin da suka zalunci kawunansu sannan suka zo wajenka suna masu neman gafarar Allah sannan Manzo ya nema musu gafara a wajen Allah, zamu samu Allah mai karbar tuba kuma mai jin kai.

Mun kasance mun zalunci kawunammu ga mu mun zo wajenka sannan muna neman gafara dangane da zunubbammu, ka nema mana gafara a wajen Allah".

6- Sayyid Ibn Dawus (ya rasu 664) ya ruwaito yadda ake ziyarar Manzo daga Imam Sadik (A.S) ga abin da yake cewa: Ya Ubangiji kai ne ka ce wa manzonka duk lokacin da suka zalunci kawunansu kuma suka zo wajenka suna neman gafarar Allah, sannan Manzo yanema musu gafara, zasu samu Allah yana mai karbar tuba kuma mai jin kai"

Ya Ubangiji ban kasance ina rayuwa a zamanin Manzo ba, amma yanzu na zo ziyararsa, kuma ina mai tuba daga munanan ayyukana, kuma ina neman gafara daga zunubbaina kuma ina mai ikrari a kan aikata su".

Mun kawo wasu daga cikin misalai dangane da yadda ake ziyarar Manzo, sannan mun ga yadda suka hadu a kan karanta wannan aya ga mai ziyara. A hakikanin gaskiya wannan aya wani nauyi ne aka aza wa mai ziyara aka kuma aza wa Manzo:

Amma nauyin da aka aza wa mai ziyara shi ne, mutum ya je wajen Manzo ya nemi gafarar zubbansa, sannan nauyin da ya hau kan Manzo shi ne ya neman wa mai ziyara gafara a wajen Allah.

Dukkan wadannan ladubban ziyara suna nuna mana yadda mai ziyara yake neman ceto daga Manzo a yayin da ba shi duniya, babu bambanci da lokacin da yake raye ta yadda mutum zai yi kamun kafa da shi.

Ibn Taimiyya Da Mabiyansa

Ibn Taimiyya da mabiyansa suna cewa: Neman addu'a daga Manzo ya kebanta ne da zamanin rayuwarsa ne a duniya kawai, don haka wannan ba ya halatta bayan wafatin Manzo! Haka ne zai yiwu mutum ya ziyarci Manzo, sannan ya yi addu'a a gefen kabarinsa sannan ya nemi abin da yake so a wajen Allah.

Dangane da amsar wannan magana kuwa zamu yi fadakarwa a kan cewa, dole ne a fahimci matsayi da darajar Manzo a wajen Allah, wato matsayin da zai sanya al'ummar musulmi masu zunubi su zo wajensa domin ya nema musu gafarar Ubangiji ta yadda addu'arsa karbabba ce.

Shin wannan matsayi da daraja ta Manzo ya samu asali ne daga jikinsa ko kuwa wani abu wanda ya shafi rayuwar duniya, ta yadda sakamakon wafatinsa zai kawo karshe, ko kuwa wannan matsayin sakamakon tsarki da daukakar ruhinsa ne?

Ra'ayi na farko kuwa ya saba wa hankali da shari'a, domin kuwa kamar yadda muka yi bayani a cikin bahsin rayuwar barzahu mun ga yadda ya kasance cewa; hakikanin mutum ruhinsa ne ba jikinsa ba. Sannan mun ga cewa ruhin mutum bayan rasuwarsa zai ci gaba da rayuwa a rayuwar barzahu, wato mutuwa ba yana nufin karshen rayuwa ba ne, ci gaba ne da rayuwa a wata duniyar ta daban. Don haka matsayi da daukakar Manzo ta samo asali ne daga girma da daukaka na ruhinsa, don haka bayan wafatinsa wannan matsayi yananan kamar yadda yake lokacin da yake a raye.

Sannan a bahsimmu da ya gabata mun tabbatar da kasantuwar alakarmu da wadanda suka riga mu gidan gaskiya, ta yadda suna jin duk abin da muke fada.

Tare da kula da abin da muka ambata, ayar da muka ambata a baya ba ta kebanta da lokacin rayuwar Manzo ba, kuma riko da hakan wani abu ne marar dalili. Sannan zamu tambayi wadanda suke inkarin kamun kafa da Manzo da cewa: me ya sanya bai halatta a yi kamun kafa da Manzo bayan wafatinsa ba? Shin don ya kasance ne duk wani girma da daukaka da kusanci ya samu ne a gare shi sakamakon yanayin jikinsa ne, ta yadda sakamakon rasuwarsa wannan matsayin da kusancinsa a wurin Allah zai kawo karshe?! Shin mutuwa shi ne karshen rayuwar mutum ta yadda Manzo bayan wafatinsa ba shi da sauran rayuwa?!

Shin sakamakon wafatin Manzo shi kenan ba mu da sauran wata alaka da shi?!

Amsar dukkan wannan tambayoyi kuwa ita ce; a 'a, don haka dole ne mu amince da cewa kamun kafa da Manzo a dukkan lokuta guda biyu (rayuwa da rasuwarsa) babu bambanci.

Daga karshe zamu yi tunatarwa da cewa, Sheikh Khalil Ahmad saharnafuri ya tattara fatawowin malaman AhlusSunna 75 dangane da halascin kamun kafa da Manzo.

A cikin wannan littafi da muka ambata a sama, an yi Karin bayani da cewa: A nazarimmu da manyan malamammu shi ne, ziyarar kabarin Manzo yana daya daga cikin manyan hanyoyi wajen neman kusanci zuwa ga Allah madaukaki, sannan yana daya daga cikin muhimman ayyuka masu lada kuma wata hanya ce domin samun matsayi da daraja madaukakiya. Wannan kuwa wani umarni ne wanda yake kusa na wajibi da farillai na shari'a, madamar isa zuwa ga hakan ba zai janyo tsanani ko asarar rayuwarka ba. Kamun kafa kuwa da annabawa da waliyyai da manyan bayin Allah, shahidai da siddikai, a cikin addu'a a lokacin rayuwarsu ne ko kuwa bayan rayuwarsu ya halatta.

Tambayoyi Da Amsoshi

Dalilai a kan halascin kamun kafa da Manzo bayan wafatinsa wani abu ne wanda ya bayyanar mana. Amma dangane da hakan akwai wasu tambayoyi wadanda dole ne mu bayar da amsarsu.

Tambaya ta farko: Shin neman addu'a daga mamaci shirka ne?

Wasu suna tunanin cewa neman addu'a daga wanda yake raye, wato yana iya yin addu'ar wani abu ne wanda ya halasta, amma yin haka ga mamaci shirka ne. Amma shin wannan tunani daidai ne?

Abin da ake nufi da shirka kuwa a cikin wannan tambaya da tagabata shi ne shirka a cikin ibada, (hadallah da wani a cikin bauta) wato neman addu'a daga mamaci yana nufin yi masa bauta kenan.

Wannan tunani na sama sam ba ya inganta, saboda:

Na farko: Idan neman addu'a ga mamaci yana nufin yi masa bauta, to wannan ya nuna cewa neman addua'a daga mutumin da yake a raye shi ma yi masa bauta ne domin kuwa babu bambanci, domin kuwa neman addu'a ne tare da kaskantar da kai, don haka wadanda suke ganin neman addu'a daga wanda yake raye ba ya nufin bauta masa ba ne, don haka dole ne su amince da cewa yin hakan bayan rasuwa ma ba yana nufin bauta ba ne, ballantana ya zama shirka ko sabanin tauhidi.

Na biyu: A cikin fasali na hudu na wannan littafi mun bayani a kan ma'anar ibada bisa dalilai na hankali, ta yadda muka nuna cewa ba duk neman wani abu ko addu'a ko makamancinsa ba ne ibada. Abin da ake nufi da ibada shi ne wani nau'i ne na girmamata musamman wacce take tare da wata akida ta musamman, wato mutum ya dauki wanda yake kaskantar da kansa a gare shi a matsayin Allah, wa'iyazu billah, ko kuma mutum ya dauka cewa wani abin halitta ne yake tafiyar da wasu daga cikin ayyukan Allah kamar yadda masu bautar gumaka suke dauka.

Amma girmamawa da kaskantar da kai wanda ya koru daga wannan akida marar tushe, ta yadda mutum yana ganin wanda yake girmamawa a matsayin wani bawan Allah ne, kuma wanda yake da kusanci zuwa ga Allah, sakamakon haka ne yake kamun kafa da shi yana neman addu'arsa, sam ba a kiran wannan bauta, ballantana ya zama shirka da Allah.

Tambaya ta biyu: Shin neman addu'a daga mamaci ba shi da wani amfani?

Daya daga cikin abin da masu inkarin wannan al'amari suke kawowa shi ne, mutumin da ya mutu sam ba shi da ikon da zai iya biya wa mutum bukatarsa. Saboda haka neman wani abu daga wanda ya mutu sam wani abu ne marar amfani.

Amsa: Tushen wannan tamabaya yana komawa ga yadda mutum yake ganin duniya, wato kamar cewa wannan duniyar da muke gani ita kawai ce duniya bayan wannan babu wani abu, wdan da suke kuma ganin cewa mutum da zarar ya mutu shi kenan babu sauran wata rayuwa, don haka wadanda suka gabata sama ba su da wata rayuwa, don haka neman wani abu daga gare su wani abu ne marar amfani.

Amma tare da kula da ka'idojin da muka ambata a sama, amsar wannan tambaya a fili yake, haka ne mutum da ya mutu ba shi da rayuwa irinta duniya, amma yana da wata rayuwar ta lahira, sannan tare da izinin Ubangiji yana iya amsa na bukatocinmu.

Tambaya ta uku: Shin tsakanimmu da wadanda suka rasu akwai wani shamaki wanda zai hana su jin maganarmu?

Wadanda suke da wannan tunani suna ganin tsakaninmu da wadanda suka rasu akwai wani abu wanda ya kare tsakanimmu, wanda Kur'ani yake ambata da barzahu. "A bayansu a kwai barzahu, har zuwa ranar tashin kiyama". Don haka kirammu ba zai isa zuwa gare su ba.

Amsa: Barzakh a harshen larabci ba tana nufin shamaki ko hijabi ba, wato ana nufin shamaki wanda yake hana su dawowa zuwa rayuwar wannan duniya, ba wai abin da zai hana su alaka da wadanda suke a raye ba. tare da kula da ayar da take da alaka da barzahu muna iya fahimtar wannan al'amari kamar yadda Kur'ani yake cewa:

"Zuwa lokacin da mutuwa zata zo wa daya daga cikinsu, zai ce: Ubangiji ka mai da ni zuwa duniya, domin kuwa zanyi aiki mai kyau a cikin abin ya ragu gare ni, sam ba haka ba ne kawai magana ce wacce mai yin ta yake fada".

Tare da kula da abin da mamaci yake fada shi ne Kur'ani yake ba shi amsa da cewa: "A bayansu akwai abin da ya kare su ta yadda ba zasu koma ba har zuwa ranar kiyama". Saboda haka wannan shamaki na hana dawowa a duniya ne, ba wanda zai hana wadanda suka rasu ba su yi alaka da wadanda suke a raye.

Tambaya ta hudu: Shin Manzo yana jin maganarmu?

Kur'ani yana kamanta yadda mushirikai suke da matattu, manufarsa kuwa da wannan shi ne, kamar yadda matacce ba ya jin magana, masu shirka suma haka suke, a kan haka ne yake cewa: "Lallai kai ba ka iya jiyar da matattu" "sannan ba ka iya jiyar da wadanda suke cikin kabari" Dangane da kamanta mushirikai da matattu dangane da rashin jin magana, muna iya cewa wani abu ne wanda babu shakku a cikinsa cewa an kamanta mushirikai da matattu.

Amsa: Babu shakka a cikin kowace kamantawa ko misaltawa a kwai wata fuska da abu guda biyu a kan kamanta su, misali lokacin da za a ce Ali kamar zaki yake, tabbas a nan an dauki fuskar jarunta ne aka siffanta Ali da zaki domin kuwa duka guda biyun suna da wannan siffa. Saboda haka a nan zamu ga menene fuskar da ta sanya a kamanta matacce da mushiriki?

Tabbas babu yadda za a ce ta fuskar cewa sam ba su ji ko kadan, domin kuwa idan muka dauki hakan cewa mamaci ba ya ji, to shi ma mushiriki zai rasa wannan halitta ta ji ke nan, ga shi kuwa mushiriki yana jin maganar Manzo da ma ta sauran al'umma.

Saboda haka wannan kama da ta sanya aka kamanta su da wani abu daban, wannan kuwa shi ne rashin sauraren magana mai amfani. Wato kamar yada kiran wanda ya mutu zuwa ga aiki mai kyau ba shi da amfani, domin kuwa lokacin aikin ya riga ya gabata, haka nan kiran mushrikai zuwa ga aiki mai kyau ba shi da wani amfani, domin kuwa sam ba su da niyyar amsa wannan kira, tare da lura da ayoyin da suke magana a kan rayuwar barzahu zamu iya fahimtar wannan hakika.

Saboda haka magana guda a nan ita ce, kiran mushrikai zuwa ga imani kamar kiran wadanda suka mutu ne zuwa ga aiki mai kyau. Don haka kiran wadannan gungu guda biyu (Mushrikai da matattu) sam ba zai samu wata riba ba. Mushiriki yana ji amma ba shi niyyar karbar gaskiya, mamaci shi ma yana ji amma lokacin aiki ya riga ya wuce yanzu lokacin sakayya ne ga abin da mutum ya aikata ne.

Abin burgewa a nan shi ne almajirin Ibn Taimiyya wato Ibn Jauziyya, shi ma a cikin littafinsa (Arruh) ya fassara wannan aya da ake tambaya a kanta kamar yadda muka fassara. Yarda da wannan tafsiri da Ibn jauziyya ya yi, yana nuna kaucewa daga ra'ayin malaminsa Ibn Taimiyya a kan wannan magana.

7-Kamun kafa Da Mutane Tsarkaka Da Mutane Masu Daraja

Bahsin da ya gabata an yi magana ne dangane da kamun kafa da addu'ar mutane masu tsarki da daraja, wato wanda yake da wata bukata yana neman su yi masa addu'a domin Allah ya biya masa bukatarsa, wato addu'arsu zata sanya ya samu kusanci.

Amma abin da muke magana a kansa a cikin wannan Bahasi shi ne yin kamun kafa da su kansu don samun kusanci zuwa ga Allah madaukaki. Wato mai neman biyan bukata ba tare da ya nemi addu'arsu ba domin ya samu biyan bukatarsa, sai ya yi kamun kafa da su domin kasantuwarsu suna da matsayi a wajen Allah, sakamakon haka sai ya nemi abin da yake bukata a wurin Allah madaukaki, ta hanyar wannan matsayi da daukaka da suke da su a wajen Allah, sai Allah ya biya masa bukatarsa. Wannan nau'in kamun kafa kuwa ana yin sa ta hanyoyi daban-daban kamar haka:

Ya Allah don matsayin da suke da shi a wurinka!

Ya Allah don kusancin da Masoyanka waliyyanka suke da shi a wurinka!

Ya Allah albarkacin manzonka da iyalansa tsarkaka!

A cikin dukkan wadannan jumloli shi kan shi mutum wanda yake da matsayi a wurin Allah da siffofinsa masu kyawu su ne zasu sanya a biya wa mutum bukatarsa, bayan shaharar wannan nau'i na kamun kafa, akwai ruwaya ingantacciya da ta zo a kan haka wacce ake kira da "dharir"harda kuwa wadanda suke da sabani a kan wannan al'amari sun tafi a kan ingancin wannan ruwaya. Domin kuwa mun kawo yadda aka kafa hujja da wannan hadisi zamu kawo wannan hadisi a nan kamar haka:

Usman Bn Hanif yana cewa: Wani mutum makaho ya zo wajen Manzo (S.A.W) ya ce ya manzon Allah ka yi mini addua'a Allah ya ba ni waraka. Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Idan kana so zan yi maka addu'a idan kuma zaka yi hakuri shi ne abin da ya fi.

Sai wannan makaho ya ce ka kira Allah ka yi mini addu'a! A wannan lokaci sai Manzo ya ce: ka je ka yi alwala mai kyau, sannan ka yi salla raka biyu ga wata addu'a nan ka karanta.

Ya Allah ina rokonka ina fuskantarka da manzonka Muhammad wanda yake annabin rahama ne ina kamunka kafa da shi a wurinka! Ya manzon Allah ina Kamun kafa da kai a wajen Allah domin ya biya mini bukatata. Sai Manzo ya ce: Ya Ubangiji ka biya masa bukatarsa domin ni.

Ibn Hanif yana cewa: Mun kasance a wajen Manzo ba tare da tsawon lokaci ba sai wannan mutum ya shigo a wajenmu kamar bai taba samun matsalar ido ba. Kafa hujja da wannan hadisi kuwa ya samo asali ne ta hanyar kasantuwar ingancin dangane da kuma ma'anarsa wacce take a fili.

Amma ta bangaren dangane da wannan hadisi kuwa Tirmizi yana cewa: wannan hadisi ne mai kyau kuma ingantacce. Ibn maja shi ma wanda ya ruwaito wannan hadisi yana cewa: wannan hadisi ne ingantacce. Sannan cikin sa'a shi ma Ibn Taimiyya ya tafi a kan ingancin wannan hadisi. Rufa'i wanda yake daya daga cikin marubutan wahabiyawa kuma na wannan zamani yana cewa: Babu shakka a kan kasantuwar ingancin wannan hadisi kuma mashahuri ne.

Saboda haka dangane da sanad ko danganen wannan hadisi babu sauran wani kace-nace. Saboda haka a nan abin da ya yi saura shi ne muyi bincike dangane da ma'anarsa a kan halascin wannan nau'i na kamun kafa.

Domin kuwa bayyana wannan ma'ana zamu tunatar da wasu abubuwa guda biyu kamar haka:

1-Menene makaho ya nema a wajen Manzo?

2-Domin ya samu biyan bukata wane irin Tawassuli ko kamun kafa da Manzo ya koyar da shi? !

Cakuda wadannan abubuwa guda biyu zai sanya a kasa gane gaskiyar al'amarin, babu shakka wannan makaho ya roki addu'a daga Manzo, wato ya yi kamun kafa da addu'ar Manzo, a nan babu sabani a kan hakan.

Magana kuwa tana nan a cikin abin da Manzo ya koyar da wannan makaho, a cikin wannan addu'a da Manzo ya koyar da shi ya nuna masa ne ta yadda zai yi kamun kafa da shi kansa manzon, wato ya sanya Manzo tsakiya a tsakaninsa da Ubangiji, ta yadda sakamakon haka Allah ya biya masa bukatunsa. Sheda kuwa a kan hakan shi ne jumlolin da suka zo a cikin hadisin wadanda suke nuni da hakan. su ne kuwa kamar haka:

1- "Ya Allah ina rokonka ina fuskantarka da annabinka" wato ina rokonka da annabinka kuma ina fuskantarka da annabinka. Wace jumla ce ta fi wannan bayyana a kan cewa mai addu'a yana hada Allah ne da manzonsa wajen neman biyan bukatarsa.

A nan yana nuna ya yi kamun kafa ne da shi kansa manzon sakamakon girmansa a wajen Allah yake neman biyan bukatunsa.

2-jumlar "Muhammad annabin rahama"

Wannan jumla tana nunawa a fili cewa Manzo wanda yake rahamar Ubangiji ce a bayyane, shi ya sanya yake kamun kafa da wannan rahama da Ubangiji zuwa ga Allah.

Abin mamaki a nan shi ne irin wannan al'amari ya sake faruwa a zamanin Usman. Sannan matsalar mutumin da yake neman biyan bukata a wannan lokaci ta warware ne ta hanyar wannan addu'a, amma akwai bambanci kadan cewa wanda ya koyar da wannan addu'a a lokaci na farko shi ne Manzo da kansa, amma alokacin na biyu Usman Bn Hanif ne, a nan zamu kawo cikakken abin da ya faru daga mu'ujamul kabir na Dabarani kamar haka:

Wani mutum a zamanin hukumar Usman ya je wajen Usman domin wata bukata tasa amma bai samu biyan bukata ba, wata rana wannan mutum sai ya hadu da Usman Bn Hanif kuma ya gaya masa abin da yake damunsa, sai ya ce masa: ka je ka yi alwala ka yi salla raka biyu, sannan ka ce:

"Ya Allah ina rokonka kuma ina fuskantarka da manzommu Muhammad annabin rahama, ya Muhammad ina kamun kafa da kai zuwa wajen ubangijinka don a biya mini bukatata".

Sai ya aikata wannan aiki, sannan ya tafi wajen Khalifa sai kuwa ya biya masa bukatarsa, sai ya sake haduwa da Usman Bn Hanif, ya tambaye shi danganen wannan addu'a, sai ya ce masa wata rana mun kasance a wajen Manzo (S.A.W) sai wani mutum mai ciwon ido ya zo wajen Manzo ya nemi ya yi masa addu'a, sai Manzo ya koyar da shi abin da na koyar da kai.

3-Jumlar "Ya Muhammad ina fuskantar Ubangiji da kai".

Wannan lafazi na "da kai"yan nuna kamun kafa ne da shi kansa Manzo din, saboda haka duk da cewa ya roki Manzo addu'a, amma ba shi ne matsayin shedarmu ba a nan. Amma a cikin abin da Manzo ya koyar da shi akwai shi kansa Manzo wanda yake rahamar Allah ne a cikin halitta, kuma shi ne silar biyan bukatar wannan makaho. Sannan jumlar "Ka ba shi lafiya don girmana" ita ma tana nuni ne ga sakamakon girman za a wajen Allah, zai samu biyan bukatarsa.

Wata kila a fahimci cewa wannan jumla ta sama tana nufin cewa; Ya Allah! Ka karbi addu'arsa da na yi masa, amma zahirin wannan hadisi ba ya nuna cewa Manzo ya yi wa wannan makaho addu'a, domin kuwa ya koyar da shi ne addu'ar kamar yadda muka yi bayani a sama. Ballantana Manzo ya bukaci Allah ya amsa addua'r da ya yi masa don girmansa a wajen Allh. Idan kuwa da Manzo ya yi wa wannan makaho addu'a bayan addu'ar da ya kowar da shi, to tabbas da wannan babban sahabi ya ruwaito wannan addu'a ta Manzo.

Bayan wannan ma idan mun dauka cewa bayan addu'ar da Manzo ya koyar da wannan makaho shi ma ya yi wa makahon addu'a, a nan ba zai cutar da kafa hujjar da muka yi ba da wannan hadisi, domin kuwa ba muna magana ne ba a kan addu'ar da Manzo ya yi masa. Domin kuwa muna kafa hujja ne a kan addu'ar da Manzo ya koyar da makaho ta yadda ya koyar da shi yadda zai yi kamun kafa da shi kansa Manzo sakamakon matsayi da daukaka da yake da shi a wajen Allah.

Idan da zaka bai wa wani masanin harshe wannan hadisi wanda ba shi da wata masaniya a kan haka, babu abin da zai fahimta bayan kamun kafa da Manzo (S.A.W) a wajen Allah madaukaki.

Ibn Taimiyya da mabiyansa lokacin da suka fuskanci wannan hadisi sun yi kokari su kawo matsala dangane da ma'anar wannan hadisi dangane da jumlolin da suke nuni a kan kamun kafa da Manzo a fili, sai su ce yana nufin addu'a ne, suna cewa:

Jumlar da take cewa: "Ina fuskantarka da manzonka" sai su ce wai ina fuskantarka da addu'ar manzonka.

A wannan akwai wani abin da ba a fada ba wannan kuwa shi ne sun yi hukunci ne sakamakon akidar da suke da ita tun da farko na haramcin kamun kafa da waliyyan Allah, amma wannan tawili nasu sam bai dace ba da jumlolin da muka ambata dangane da hakan.

Idan kuwa gaskiya ne makaho ya yi kamun kafa ne da addu'ar Manzo, to me ya sa Manzo ya ce masa ka ce: "Muhammad annabin rahama" sannan ya ce masa ka ce: "Ya Muhammad lallai ina fuskantarka"

Bayan wannan idan muka dauka ma'anar wannan yana nufin addu'a ne, to wannan zai bata tsarin jumlar.

Alusi Bagdadi (ya rasu 1270) wanda ya kasance daya daga cikin wadanda suka yada wahabiyanci a nan yana mika wuya zuwa ga gaskiya, inda ya tafi a kan cewa kamun kafa da waliyyan Allah Manzo ne ko waninsa ba shi da wani laifi, da sharadin cewa mu dauka wannan mutumin yana da matsayi ne a wajen Allah .

Tarihin Kamun kafa Da Bayin Allah Tsarkaka

Tarihi a bayyane yana nuna cewa tun kafin zuwan musulunci mutane masu kadaita Allah sun kasance suna Kamun kafa da wadanda suke ganin suna da matsayi a wurin Allah, sannan kuma sakamakon tsarkin fidirarsu su suna ganin wannan aiki wani aiki ne wanda yake mai kyau. A nan zamu yi nuni da wasu daga cikinsu:

1-Abdul Mutallib da kamun kafa da Muhammad (S.A.W) a lokacin da yake shan nono, tsananin fari ya mamaye Makka da kewayenta, sai Abdul mutallib ya dauki jikansa mai shan nono ya daga sama, sannan ya roki Allah ruwan sama, har ana cewa mashahuriyar wakar Abu Dalib ya yi ta ne dangane da haka wacce take cewa: Fuska mai haske wacce gizagizai suka yi ruwa dominta, wacce sakamakon haka ne marayu da mata gwagware suka samu mafaka.

2-Abu Dalib da kamun kafa da Manzo a lokacin da yake saurayi

Kamar abin da ya faru lokacin Abdul mutallib a lokacin shugabancin Abu Dalib ma ya sake faruwa, sakamakon haka ne sai kuraishawa suka zo wajensa suka kawo masa kuka a kan fari da rashin ruwa da ake ciki, Sai Abu Dalib ya yanke shawara a inda ya roki Allah da ya saukar musu da ruwa tare da kamun kafa da dan dan'uwansa Muhammad wanda yake karamin yaro ne a wannan lokaci. Sai ya kama hannun Manzo ya jingina bayansa ga dakin ka'aba, wani lokaci yana nuni da wannan yaro wani lokaci kuwa yana nuni da sama, wato Ubangiji albarkacin wannan yaro ka saukar mana da rahamarka. Ba tare da tsawaita lokaci ba, sai hadari ya mamaye garin Makka da kewayanta, sai koramu da tabkuna suka cika makil da ruwa .

3-Sallar rokon ruwa tare dakananan yara da tsofaffi

A cikin ladubban sallar rokon ruwa ana cewa ya fi dacewa masu sallar rokon ruwa su fita tare dakananan yara da tsofi, har wasu ma suna cewa a tafi tare da dabbobi ma wajen wannan sallar rokon ruwa. Manufar kuwa zuwa dakananan yara marasa laifi da tsofaffi raunana da dabbobi wadanda ba su magana shi ne, domin suna cewa idan su ba su cancanci rahamar Ubangiji ba sakamakon zunubbansu .

Ya Ubangiji wadannan kananan yara mararsa laifi, da tsofaffi raunana, da dabbobi wadanda ba su iya magana, sun cancanci rahamarka.

Ya Ubangiji albarkacinsu ka aiko mana da rahamarka!

Ya uabngiji! Mai lambu saboda itaciya guda daya yake ban ruwa, amma sakamakon haka sai ciyawu ma su samu!

Wannan yana nuna mana cewa tun kafin zuwan musulunci mutane a dabi'ance sun kasance suna kamun kafa da abubuwan da suka cancanci rahamar Allah, don neman biyan bukatunsu, kuma da musulunci ya zo ya tabbatar musu da hakan.

4-Khalifa na biyu yana kamun kafa da Ammin Manzo (S.A.W)

Bukhari a cikin sahih dinsa yana ruwaito cewa Umar Bn khattab a lokacin fari da tsananin rashin ruwan sama ya kasance yana kamun kafa da Abbas dan Abdul Mutallib domin su samu ruwan sama, ga abin da yake cewa: Ya Allah muna muna rokonka albarkacin annabimmu ka shayar da mu ruwa, ya Allah muna kamun kafa zuwa gareka da ammin annabimmu ka shayar da mu sai su sha!

Dangane da danganen wannan hadisi kuwa babu sauran wata magana domin kuwa sahih bukhari karbabbe ne a wajen 'yan Sunna, saboda haka magana kawai ta rage wajen ma'anarsa.

Duk lokacin da aka bai wa wani balarabe wannan hadisi wanda a cikin zuciyarsa bai hadu da wani sabani ba zai ce: Khalifa na biyu ya kasance yana kamun kafa ne da ammin Manzo domin Allah madaukaki ta albarkacinsa ya aiko da ruwan sama ya shayar da su saura su samu.

Wannan addu'a kuwa tana nufin cewa ya Allah idan harm u ba mu cancanci ka yi ruwa saboda mu ba, to albarkacin ammin Manzo domin alakar da suke da ita a tsakaninsu ka aiko mana da ruwan sama.

Saboda haka idan a nan ana nufin kamun kafa da wani mutum ne, to kamun kafa da Manzo ya fi komai dacewa, domin kuwa Abbas ya samu darajarsa ne daga Manzo (S.A.W) saboda haka me ya sa a nan ya bar Manzo ya yi kamun kafa da Abbas, wannan shi ne abin tambaya a nan?

Amsar wannan kuwa shi ne a wajen rokon ruwa ana kamun kafa ne da wadanda masu rokon ruwa suke daya da shi wajen bukatr ruwan, kamar kananan yara da tsofaffi, ta yadda zasu motsa rahamar Ubangiji, su ce ya Allah idan mu ba mu cancanci wannan ba to wadannan kananan yara da tsofi sun cancanta ka aiko saboda su.

Saboda haka wannan ya cancanta ga ammin Manzo wanda ya kasance yana raye a wannan lokaci, ba wai Manzo ba domin kuwa shi a wannan lokaci ya bar duniya kuma halin da suke ciki ya bambanta.

Wadanda suke sabani a kan halascin kamun kafa ko tawassuli da manyan bayin Allah suna fito-na-fito ne da wannan hadisi, saboda haka ko ta halin kaka suna kokari ne suga sun karkatar da ma'anarsa, suna cewa abin da khalifa yake nufi a nan yana kamun kafa ne da addu'ar Abbas, ba wai yana kamun kafa ba ne da shi kansa Abbas ko wani matsayi na shi. Wannan tawili kuwa ta fuskoki daban-daban ba zai inganta ba:

Na farko: Sallar rokon ruwa da addu'ar, umar ne ya gabatar da su ba Abbas ba, saboda haka a nan babu magana a kan addu'ar Abbas.

Abin da kuwa yake tabbatar mana da cewa wannan addu'a umar ne ya yi ta ba Abbas ba, lafazin da ya zo a cikin addu'ar kamar haka: Ya Allah mun kasance muna kamun kafa da Manzo ka shayar da mu, yanzu muna kamun kafa da ammin Manzo ka shayar da mu, a wannan lokaci sai ruwa ya sauka aka shayar da su.

Saboda haka wannan yana nuna cewa wanda ya gabatar da wannan shiri tun daga farko har karshe khalifa ne, ba wai Abbas ammin Manzo ba, ballantana Umar ya yi kamun kafa da addu'arsa.

Na biyu: Dalili na biyu shi ne a cikin babin da wannan addu'a ta zo yana magana ne a kan neman mutane daga shigaba don ya roka musu ruwan sama yayin da aka samu fari da rashin ruwan sama.

Wannan yana nuna cewa mutane su ne suka nemi khalifa da ya roka musu ruwan sama, shi kuma ya amsa musu rokn da suka yi masa.

Saboda haka a cikin wannan al'amari matsayin Abbas shi ne lokacin da umar yake addu'a ya yi nuni da shi inda yake cewa: "Ya Allah muna kamun kafa da ammin Manzo ka shayar da mu"

Na uku: Ibn Asir ya yi bayani yadda aka gabatar da wannan salla da addu'ar rokon ruwa, yana cewa Umar ya kasance yana nuni da Abbas yana cewa: "Wallahi wannan shi ne tsani zuwa ga Allah kuma mai tsayi a wurinsa" Ya kasance yana rokon Allah ruwa a cikin wannan hali. Don haka kamun kafa ya kasance da shi kansa Abbas ne ba da addu'arsa ba.

Ibn Hajar Askalani (ya rasu 852) a wajen sharhin wannan hadisi yana rubuta cewa: dangane da abin da ya faru da Abbas yana nuna mana yadda ya halatta mutum ya yi kamun kafa da mutanen kwarai da iyalan gidan Manzo don samu ruwan sama .

A karshen wannan Bahasi zamu yi tunatarwa da cewa, Tawassuli ko kamun kafa da addu'a wacce take kowa ya aminta da wannan, wani nau'i ne na kamun kafa da wanda yake addu'a sakamakon matsayi da girma da yake da shi a wajen Allah. Domin kuwa idan da mai yin addu'ar ba shi da wani matsayin na musamman a kan abin da ya shafi tsarkin ruhi, sam addu'arsa ba zata iya zama mai tasiri ba.

Kamun kafar Masu Tsarki Da Matsayi A Cikin Ruwaya

Ya zo a cikin ruwayoyi da dama na AhlusSunna dangane da kamun kafa da manyan bayin Allah tsarkaka, amma abin mamaki a nan shi ne masu sabani da wannan abu duk da cewa suna ganin wadannan ruwayoyi har yanzu suna ci gaba da wannan fito na fito nasu, a nan masu wannan akida suna koyi ne da Ibn Taimiyya ba suna koyi da gaskiya ba ne, idan da ba suna yanke hukunci ba ne tun kafin su ga dalilai tabbas da ba zasu dage ba a kan wannan akida tasu ba.

A nan zamu kawo wasu daga cikinsu:

1-Atiyya Aufi ya ruwaito daga Abu Sa'idul Kudri yana cewamanzo ya ce: duk wanda ya fito daga gidansa da nufin zai je masallaci ya yi salla idan ya karanta wannan addu'ar rahamar Ubangiji zata lullube shi, sannan mala'iku da yawa zasu yi masa addu'a su nema masa gafara a wajen Allah. Wannan addu'a kuwa ita ce: "Allahumma inni as'aluka bi hakkis Sa'ilina alaika, wa as'aluka bihakki mashai haza, Fa inni lam akhruj ashran wala batran wala rayyan wala sum'a, innama kharajtu itka'a saktik wabtiga'a mardhatika, an tu'izani minan nar, wa an tagfira zunubi, innahu la yagfiruz zunuba illa ant"

Wato, ya Ubangiji! Ina rokonka don matsayin masu rokonka, ina rokonka da matsayin wannan tafiya tawa, kuma ban fito ba don jin dadi ko saboda riya in nuna wa wasu mutane, ya Allah na fito ne domin tserewa fushinka da azabarka da neman yardarka, ya Allah ka tseratar da ni daga wuta, kuma ka gafarta mini zunubbaina don babu mai gafarta zunubbai sai kai.

Wannan hadisi dangane da ma'anar a kan abin da muke magana a kan shi na kamun kafa da masu matsayi da tsarki a fili yake. Sannan sanad ko danganen wannan hadisi ingantacce ne domin kuwa dukkan maruwaitan wannan hadisi an amince da su, sai kawai mutum guda wanda dole mu yi bayani a kansa, wannan kuwa shi ne Atiyya Aufi.

Masana ruwaya sun yi hukuncin da ya dace a kansa:

Abu Hatim yana rubuta cewa: Ana iya rubuta hadisinsa.

Ibn Mu'in yana cewa: Mutumin kirki ne.

Ibn Hajar yana cewa: Mai gaskiya ne.

Ibn Adi yana cewa: Ya kasance yana ruwaito hadisi daga mutanen kirki.

Ibn Sa'ad yana cewa: Hajaj ya rubuta wa wani daga cikin hakimansa mai suna Muhammad Bn Kasim takarda cewa: Ka kama Atiyya, sannan ka bijiro masa da zagin Ali ya kara da cewa shi mutum ne amintacce sannan hadisansa ingantattu ne.

Idan har ma wasu sun kasance suna sukarsa laifinsa bai wuce shi'anci ba, shi'an da ma'anarsa shi ne son Ali da 'ya'yansa (A.S)

Sannan yanayin wannan hadisi yana tabbatar mana cewa maganar ma'asumi ce, sannan makamantan wannan hadisi suna da yawa a musulunci.

Kamun kafa Da Manzo Da Annabawan Da Suka Gabata

Dabarani a cikin mu'ujam dinsa, ya ruwaito hadisi tare da dangane daga Anass Bn Malik yana cewa: lokacin da Fadima bnt Asad ta rasu, Manzo ya halarci gadon mutuwarta, sai ya ce: Ya Allah ka yi wa mamata ta biyu rahama, kin kasance kina jin yunwa kina kosar da ni, kin kasance kina rasa sutura kina suturta ni, kinkasance kina kin cin abin ci mai dadi ni kuwa ki ba ni mai dadi, ba ki da wata manufa a cikin wannan aiki sai neman yardar Allah.

Sai Manzo (S.A.W) ya ba da umarni da a yi mata wanka sau uku, sannan ya ciro rigarsa ya ce a yi mata likkafani da ita, sannan ku yi mata lahadu (wani nau'in kabari ne) da umurnin manzon Allah, sannan shi da kansa ya shiga cikin kabarin, ya debo kasar lahadun da hannayansa, bayan ya gama wannan aiki, sai ya kwanta a cikin kabarin ya ce: Ya Allah wanda yake kashewa kuma shi a raye yake ba ya mutuwa, ka gafarta wa uwata Fadima bnt Asad, ya Allah ka fahimtar da ita hujjarka, Ya Allah ka yalwata kabrinta albakarcin girman manzonka da manzanninka da suka gabata, kamar yadda kake mafi jin kan masu Jin kai .

Wannan hadisi yana bayyanar da matsayin mahaifiyar Imam Ali (A.S) kamar yadda wannan hadisi yake nuna cewa ana iya kamun kafa da masu tsarki. Kawai abin da zai jawo hankalin masu sabani a cikin wannan al'amari shi ne, wani maruwaici guda daya mai suna ruh Bn Salah, duk da cewa Ibn Habban da Hakim Nishaburi wadanda suka kasance babu kamarsu a cikin ilimin hadisi a zamaninsu sun yi bayani a kan cewa wannan mutum amintacce ne.

A nan zamu takaita dangane da kawo hadisai AhlusSunna, duk da cewa akwai ruwayoyi da dama da suka fi haka a kan wannan magana, amma dangane da ruwayoyin da suka zo daga Ahlul baiti (A.S) danagane da wannan nau'i na kamun kafa suna da yawan gaske, ta yadda suna da yawan gaske a cikin addu'o'in Amirul mumininna da Husain da addu'o'in Imam Zainul abidin (A.S)

Imam Husain (A.S) a cikin addua'r arfa ga abin da yake cewa:

Ya Allah muna fuskantarka a cikin wannan dare wanda ka daukaka shi ka kuma girmama shi, Allah muna kamun kafa da Manzonka Muhammad wanda shi ne fiyayyen halittarka sannan amintaccenka wajen kai wahayi.

A nan zamu yi nuni dangane da wasu kalu bale a takaice:

Kalu balanta Da Amsoshinsu

Kalu bale na farko: shi ne, wannan nau;in tawassuli ko kamun kafa bai kasance ba a lokacin sahabbai da tabia'i?

Amsa: Ta fuskar ka'idoji na ilimi, aikin ma'asumi yana nuni a kan halascin abu, amma barinsa a kan aikata wani abu ba ya nuni a kan haramcin abu. Idan muka dauka cewa sahabbai ba su yin sabo ko kuskure, wato muka yi musu hukuncin ma'asumai, a nan rashin aikatawarsu ba ya zamar mana dalili a kan haramcin abu ba. Bayan haka, ma'auni a wajen sanin haramci ko halascin abu shi ne maganar Manzo ko magadansa ma'asumai (A.S) don haka muna iya ganin wannan nau'i na Tawassuli a fili a cikin ruwayoyin Manzo da addu'o'in Ahlul baiti (A.S)

Kalu balanta ta biyu:

Halittu ba su da hakki a kan Allah: Wannan nau'i na tawassuli kamar wani dora nauyi ne ga Allah ta yadda dole ne Allah ya bayar da wannan hakki da ya hau kansa, alhali kuwa babu wani nauyi na wani abin halitta wanda yake a kan Allah madaukaki.

Amsa: Hakkin abin halitta a kan Allah muna iya kallon sa ta fuska biyu:

A-Sakamakon wasu ayyukana bawa yakan iya samun wani hakki a kan Allah kamar yadda mai bin bashi yake da hakki a kan wanda yake bi bashi. Irin wannan hakki ba zamu iya tunaninsa ba a kan Allah madaukaki daga bangaren bawa, domin kuwa bawan Allah bai mallaki komai ba, ta yadda ta hanyar wannan zai samu wani hakki a kan Allah.

B-Hakin da shi da kansa Allah ta hanyar wani lutfi wanda ya yi ga shi bawa, ta wannan hanyar sai bawan ya samu hakki a wajen Allah. Wato hakikanin kuwa shi ne wata falala ce wacce Allah ya yi wa bawa sakamakon haka sai ya sanya bawan yana da wani hakki a kan Allah madaukaki, ta yadda ya sanya kansa matsayin wanda ake ba shi, shi kuma bawa matsayin mai bin bashi, bayan kasantuwar cewa wannan yana iya yiwuwa a cikin Kur'ani akwai dalilai masu tabbatar mana da hakan.

Wani lokaci Allah yana daukar kansa matsayin wanda ya dauki bashi daga bayinsa, shi kuwa bawa masatyin mai ba ba bashi, a kan hakane yake cewa: "Wa zai bai wa Allah rance mai kyau".

Bayan wannan akwai ayoyi da yawa wadanda suke bayani a kan cewa sakamakon wata baiwa da Allah yake wa bayinsa, zasu kasance suna samun wani hakki na musamman ga Allah wanda yake ba shi da farko ba shi da karshe. A wasu wurare ga abin da yake cewa:

1-"Ya kasance hakki a kanmu mu taimaki muminai" .

2-"Alkawari ne a kan Allah kuma hakki ne a cikin Attaura da Injila" .

3-"Kuma hakki ne a kanmu mu taimaki muminai" .

4-Karbar tuba ya wajaba a kan Allah ga wadanda suke ayyuka mummuna sakamakon jahilci, sannan sai suka tuba ba tare da jinkiri ba" .

Sannan a cikin hadisai da dama zamu iya ganin irin wadannan hakkoki. Don haka a nan kawai zamukawo daya daga cikin a matsayin misali kamar haka: Manzo (S.A.W) yana cewa ya wajaba ga Allah ya taimaki wanda ya yi aure domin tsoron kada ya fada a cikin haram.

Kalu bale na uku:

Wannan nau'in na kamun kafa ko Tawassuli kiran wanin Allah ne. Ayoyi da yawa a cikin Kur'ani mai girma sun yi bayani a kan cewa musulmi bai halatta ba ya kira ko ya roki wanin Allah, kamar yadda Allah madaukaki yake cewa: "Kada ku kira wani tare da Allah" "Lallai wadanda kuka kira suma bayi ne kamar ku" .

Daga wadannan ayoyi guda biyu muna fahimtar cewa a wajen addu'a babu wanda ya kamata a kira sai Allah madaukaki shi kadai ba wanin Allah ba, don haka kamun kafa da wani ko matsayin wani kiran wanin Allah ne.

Amsa: Abin da yake mafi rashin tushen a cikin kalu balantar da ake yi dangane da kamun kafa ko Tawassuli shi ne wannan wanda aka ambata a sama, wanda kuma da wannan ne masu kin amincewa da tawassuli suke riko da shi, ta yaddacikin rashin adalci suke dora ayoyin da suka zo a kan mushrikai masu bautar gumaka a kan musulmai da manyan bayin Allah. Duk da cewa wadannan ayoyi sun sauka ne a kan mushrikai wadanda suke daukar gumakansu matsayin alloli komasu tafiyar da duniya. Ba kamar yadda musulmi ba ya dauka cewa Manzo (S.A.W) bawan Allah ne kuma mai kira zuwa ga kadaita Allah madaukaki, sakamon ana yin amfani da irin wadannan ayoyi a wajen irin haka, don haka zamu yi dan bayani a kan wadannan ayoyi kamar haka:

1-Ayoyin da suke cewa: Kada ku kira wanin Allah, wadannan ayoyi suna nufin kiran Allah da ma'anar bauta ne, ba wai da nufin kira ba kawai ga wani mutum mai matsayi koda kuwa da niyyar cewa shi kawai wani mutum ne mai tsarki, domin kuwa a matsayin sheda a ayar da ta gabata yana cewa: "Kada ku kira wani tare da Allah". Idan cikin wannan aya ana nufin kira ko roko ne kawai ba yana nufin bauta ba ne, to zai zamana ma'anar wannan aya ta sabawa umurnin Kur'ani, domin kuwa Kur'ani yana ba da umarni ga musulmi cewa su tafi wajen Manzo su neme shi da ya roka musu Allah gafara, sannan shi ma ya gafarta musu.

A nan mutum yana kiran Ubangiji yayin da yake neman gafarar Allah da kansa, sannan yana kiranmanzo yayin da yake so ya gafarta masa. Saboda haka ma'nar cewa kada ku kira wani tare da Allah shi ne, kada ku hada wani tare da Allah wajen bauta.

Kamar haka ne a cikin aya ta biyu ma babu bambanci, domin kuwa abin da ake nufi da "kuke kira" a cikin aya ta biyu ana nufin bauta ne, domin kuwa jimalar da ta zo a bayanta wacce kuma take haramta yin hakan tana cewa: "Domin kuwa su bayi ne kamarku". Wato kada ku bautawa wadannan gumakan na karya domin kuwa ba su da wani bambanci da ku, suma kamarku suke bayi ne na Allah.

Saboda haka hanin da aka yi na kada a kira wani tare da Allah ko kuma a kira shi ba tare da Allah ba, ana nufin kira ne wanda yake da ma'anar bauta, wanda ya samo asali ne daga imanin mutum da cewa shi wannan abin a matsayin Allah ne, ba wai kawai kira ba tare da wannan imanin ba, domin kuwa rayuwar dan Adam baki daya ta doru a kan haka ne. Kur'ani mai girma yana cewa: "Zamu kirawo 'ya'yammu kuma ku kirawo 'ya'yanku" .

Sannan a cikin wata aya ana cewa bai kamata ku kira Manzo ba kamar yadda kuke kiran sauran mutane a tsakaninku, ga abin da ayar take cewa: "Kada ku sanya kiran Manzo kamar a tsakaninku kamar yadda kuke kiran junanku" .

Saboda haka kiran da ake magana a cikin wannan aya ba ana nufin kawai kira ba haka nan, ana nufin kira da sunan bauta ga Allah ko ga wani wanda mutum ya dauka cewa shi ne yake tafiyar da wasu ayyukan Ubangiji.

Don haka wadannan ayoyi guda biyu da wasu misalinsu, wace alaka suke da ita dangane da rokon da muke wa Manzo a matsayinsa na bawan Allah mai matsayi, ko kuma kawai mu kira shi ba tare da nufin ibada ba.

A cikin Littattafan masu inkarin kamun kafa da wani bawan Allah, sun tattaro duk ayoyin da suke magana danagane da mushrikai da suke kiran gumakansu na karya, sannan suka dora wadannan ayoyi a kan musulmai masu kamun kafa da ruhin manyan bayin Allah. Duk da cewa tare da la'akari da wasu abubuwa guda biyu sun fita daga bahsimmu kamar haka:

1-Wadannan ayoyi suna magana ne a kan mushrikai ba masu kadaita Allah ba.

2-Kasantuwar mashrikai sun yi imani da cewa wadannan gumakansu su suke tafiyar da wasu ayyukan Ubangiji (rububiyya) shi ya sanya kira ko rokon da suke wa gumakan ya zama ibada, amma musulmai sakamakon tsarkin imaninsu da kadaita Ubangiji suna girmama bayin Allah kuma suna kamun kafa ne da su sakamakon Allah ne ya ba da iko a hakan.

A takaice: haramta kira da aka yi a cikin wadannan ayoyi guda biyu, ya kasance ne sakamakon suna yin hakan ne a matsayin bauta, ba wai ko wane kira ko roko ba wanda yake baya tattare da wannan siffa. Domin kuwa mu gane wannan shiri na masu inkarin Tawassuli da bayin Allah, zamu ka wo wasu daga cikin ayoyin da suke kawowa a wajen bayanai da rubuce-rubucensu, ta yadda zai bayyana yadda suka yi amfani da wadannan ayoyi suka canza wannan al'amari, ta yadda suka dora ayoyin da suka sauka a kan mushrikai a kan musulmai, ga wadannan ayoyi kamar haka:

"Wadannan wadanda suke kira ba su amsa musu da komai" .

"Wadannan wadanda kuke ba zasu iya taimakonku da komai ba, sannan ba zasu iya taimakon kawunansu ba" .

"Wadannan wadanda kuke kira suma bayi ne kamar ku" .

"Wadanda kuke kira sabanin Allah ba su mallaki koda bawon dabino ba"

"Ka ce yanzu mun kira wanin Allah wanda ba ya amfanar da mu kuma ba ya cutar da m u" .

"Kada ka kira wanin Allah wanda ba ya amfanar da kai haka nan ba ya cutar da kai"

Masu inkarin Tawassuli da bayin Allah a wuraren wa'azuzuwansu da rubuce-rubucensu suna kafa hujja ne da wadannan ayoyin suna dora su a kan musulmi masu kamun kafa da bayin Allah ba tare da wani dalili ba, alhali kuwa wadannan ayoyi ba su da wata alaka da tawassuli da ake yi a cikin musulunci. Masu karatu suna iya komawa zuwa ga tafsirai domin su ga dalilan saukar da wadannan ayoyi a bayyane.

Wadannan ayoyi suna magana ne da masu bautar gumaka wadanda suke da imanin cewa amfani da cutarwa, daukaka da kaskantarwa duk suna hannun wadannan allolin nasu na karya, haka nan samu nasara a wajen yaki duk yana hannunsu, ta haka ne abin da suke yi ya zama bauta, domin su samu wadannan abubuwan da suke gani suna zuwa ne daga gare su. Amma musulmi masu kamun kafa da bayin Allah akidarsu kilo mita dubu ta nisanta da wannan akida batacciya, cin nasara da kariya dukkansu suna zuwa ne daga Allah. Don haka girmamawar da suke wa ma'asumai (A.S) sam ba shi da alaka da cewa sun dauka ne su alloli ne ballantana ya zama bauta, suna haka ne domin suna ganinsu bayin Allah ne masu girma da daukaka a wajen Allah.

Mafi yawa cikin addu'o'immu muna cewa ne; "Ya Allah don matsayin Manzonka Muhammad da alayansa" wannan mastayi kuwa ya yake? Wannan matsayi kuwa shi ne matsayin da Allah ya ba su, sannan Kur'ani mai girma yana ambatar wasu daga cikin annabawa da wannan matsayin kamar yadda yake cewa dangane da annabi Musa (A.S) "Ya kasance yana da matsayi a wajen Allah" Haka nan yana cewa dangane da annabi Isa (A.S) "Yana da matsayi a duniya da lahira" Wannan shi ne matsayin da Allah da kansa ya ambata a cikin kur'ani dangane da bayinsa, wanda sakamakon haka ne suke da kusanci da matsayi a wurin Allah madaukaki.

Kalu bale na hudu:

Kamun kafa yana nufin neman taimako daga wanin Allah, Mutumin da yake tawassuli a lokacin da ya shiga cikin halin kaka- na-kayi, wannan yana nufin yana neman taimako daga wanin Allah, duk da yake cewa babu wani wanda za a iya neman taimako daga gare shi sai Allah, kamar yadda Kur'ani yake cewa: "Kawai gare ka muke neman taimako".

Amsa: wannan kuwa yana zama matsala ne ga mutumin da yake bai san wani abu ba daga Kur'ani, domin kuwa a baya mun yi bayani a kan cewa ana iya jingina aiki guda daya zuwa ga Allah a lokaci guda a jingina shi zuwa waninsa, haka nan mun kawo wurare da dama daga cikin Kur'ani da suke bayani a kan hakan, kamar misalin daukar rai ko rubuta ayyukan bayi, sannan muka yi bayani cewa wannan ba shi da wata matsala, domin kuwa jinginawa zuwa ga Allah a matsayin komai yana zuwa daga gare shi ne kuma sai da izinisa, jingina shi kuwa ga wani bawan Allah da ma'anar ya yi wannan aiki ne karkashin ikon Ubangiji.

Allah madaukai ba tare da ya nemi taimako ba daga wani wuri yake aiwatar da ayykansa, amma waninsa yana yin hakan ne tare da izinin Ubangiji, don haka aikinsa ma aikin Allah ne da wannan ma'ana.

Don haka babu matsala a lokaci guda cewa babu wanda za a nemi taimako daga gare shi sai Allah kuma a nemi taimako daga waninsa, domin kuwa neman taimako daga wani bawan Allah ba yana nufin cewa neman taimako daga gare shi maimaikon Allah. Domin kuwa yana yin komai ne da izinin Ubangiji, bisa haka ne Kur'ani yake cewa a wajen Allah kawai ake neman taimako, kuma a wani wuri yake cewa mu nemi taimako daga wanin Allah, kamar yadda yake cewa: "Ku nemi taimako daga hakuri da salla, domin kuwa suna da girma a wajen masu tsoron Allah".

Zulkarnaini lokacin da yake so ya gina bango domin ya kare mutane daga harin yajuju ga abin da yake cewa mutanensa: "Abin da Allah ya hore mini ya fi abin da zaku yi mini, don haka ku taimaka mini da masu karfi"

Duniya musamman duniyar mutane ta kafu ne kan taimakekeniya, sun kuma kasance suna neman taimako da sunayen annabawa da manyan bayin Allah daga junansu, sannan sam ba su ganin wannan ya saba wa asalin kadaita Allah madaukaki, domin kuwa taimakon wanin Allah yana karkashin iko ne na Allah madaukaki, wanda ya bai wa mutum wannan damar.

Abin mamaki a nan shi ne wadanda suke inkarin neman taimako daga wanin Allah suna ganin ana iya neman taimako daga wanin Allah a lokacin da yake raye, amma bayan ya mutu ya haramta kuma yin hakan ma shirka ne, alhalin idan abu shirka ne kasantuwar bangare guda yana da rai da bashi da rai ba ya canza wannan abu, saboda haka neman taimako daga wani idan har ya kasance muna ganin cewa yana iya yin hakan ne tare taimakon Allah sam ba shirka ba ne, wannan kuwa ya kasance yana da rai ne ko kuwa bayan mutuwarsa ne. Daga karshe zamu yi tunatarwa a kan wasu abubuwa guda uku kamar haka:

1-Ruwayoyin Halascin Tawassuli Ko Kamun kafa, Mutawatir Ne

Ruwayoyi da suke magana a kan Tawassuli wadanda muka kawo kadan daga Littattafan AhlusSunna kodai mutawatir ne ko kuma gab suke da su zama mutawatir, saboda haka ba zai yiwu ba ta hanyar raunana danganen wadannan ruwayoyi mu yi inkarin wannan al'amari, domin kuwa wadannan ruwayoyi suna nuni da cewa wannan al'amari ya kasance kamar ruwan dare a tsakanin al'ummar musulmi a tsawon tarihi, idan har mun kauce wa ambatar wasu da hakacikin wadannan ruwayoyi da suke magana a kan Tawassuli wadanda wasu daga cikinsu ta fuskar sanad ko dangane suna da rauni, wannan ba zai cutar da abin da muke managa a kansa ba, kamar yadda muka san cewa al'amarin haka yake dangane da hadisi mutawatir.

2-Littattafai Dangane Da Tawassuli

Al'amarin Tawassuli ko kamun kafa da bayin Allah, wani abu ne wanda yake an sallama a kansa a cikin musulunci, sakamkon haka ne manyan malaman hadisi da na fikihu sun rubuta littafai da dama a kan wannan mas'ala tun kafin Ibn Taimiyya da kuma bayansa, wadanda a nan kawai zamu kawo wasu daga cikinsu:

1-Alwafa fi fadha'ilul Mustafa Ibn jauzi (Ya rasu shekara ta 597) a cikin wannan littafi akwai babi na musamman wanda yake magana a kan kamun kafa da Manzo da neman ceto da shi da kabarinsa mai albarka.

2-Misbahuz zulam fi mutagisina bi khairi anam, wanda ya rubuta shi Muhammad Bn Nu'uman Maliki (ya rasu shekara ta 973) Samhudi a cikin littafinsa wafa'ul wafa ya ruwaito da dama daga wannan littafi dangane da Tawassuli.

3-Al-bayan wal ikhtisar, wanda Ibn Daud Maliki shazali ya rubuta, a cikin wannan littafi ya kawo yadda manyan malamai da bayin Allah suke kamun kafa da Manzo (S.A.W)

4-Shifa'us sikam, wanda Takiyyuddin Subki ya rubuta ya yi kariya da kyau a kan kamun kafa da Manzo a cikin wannan littafi nasa.

5-Wafa'ul wafa li'akhabari daril Mustafa, wanda Sayyid Nuruddin samhudi ya rubuta, (ya rasu shekara ta 911) ya yi Bahasi a kan Tawassuli a cikin juz'i na hudu na wannan littafi.

6-Al-mawahibud daniyya wanda Abu Abbas kustalani (ya rasu a shekara 933) ya yi bahsin Tawassuli a cikin wannan littafi nasa.

7-Sharhul mawahibud diniyya, wanda Misri zarkani ya rubuta, (ya rasu a shekara ta 1122) ya yimaganar Tawassuli a cikin mujalladi na takwas.

8-Sulhul Ikhwan: Wanda Khalidi Bagdadi ya rubuta, (ya rasu a shekara ta 1299) a cikin wannan littafi ya rubuta risala ta musamman raddi a kan Alusi bayan rasuwarsa a shekara ta 1306 a ka buga littafin.

9-Kanzul matalib: wanda Adwi Ahmzawi ya rubuta, (ya rasu shekara ta1303).

10-Furkanul kur'an wanda Izami shafi'i ya rbuta.

Amma ta bangaren Shi'a an rubuta littafai masu yawa a kan haka, a nan kawai zamu kawo wasu daga cikinsu kamar haka:

1-Sabilur rashad liman aradas sadad, wanda sheikh Ja'afar Kashiful Gida ya rubuta, (ya rasu 1227) an buga wannan littafi saudayawa.

2-Kashful irtiyab, wanda Sayyid Jabalil Amuli ya rubuta, (1282-1373).

3-Al-gadir, Allama Amini ya yi Bahasi mai tsawo a kan wannan magana.

3-Sabani Tsakanin Mabiya Ibn Taimiyya Da Sauran Musulmi

An rubuta wasu litattafai daga bangaren masu inkarin tawassuli da bayin Allah daga bayan-bayan nan, inda suke nuna cewa wani sabani ne tsakanin Shi'a da Sunna, alhalin kuwa wannan sabani bai shafi tsakanin Sunna da Shi'a ba, wani sabani ne wanda yake tsakanin mabiya Ibn Taimiyya da sauran al'ummar musulmi, kuma a baya kadan mun kawo wasu Littattafan manyan malaman AhlusSunna wadanda aka rubuta a kan raddi ga Ibn Taimiyya da mabiyinsa Muhammad Bn Abdul wahab, don haka muna iya gane cewa sabani ya fari ne tsakanin wadannan mutum biyu da mabiyansu da sauran dukkan al'ummar musulmi wadanda suka tafi a kan ingancin kamun kafa da waliyyan Allah, wato sauran musulmi ba su da sabani a kan haka, don haka ba sabani ne ba tsakanin Shi'a da Sunna kamar yadda wasu suke riyawa, kamar yadda muka gani da kuma abin da zamu gani a nan gaba wanda yake tabbatar da hakan.

Abin Da Littafin Ya Kunsa

KAMUN KAFA(Tawassuli)1

Wallafar: Ayatullahi Ja'afar Subhani 1

Fassarar: Hafiz Muhammad Sa’id 1

KAMUN KAFA DA ANNABAWA DA WALIYYAN ALLAH 1

Kamun kafa 2

1-Kamun kafa Da Sunaye Da Siffofin Allah 7

2-Kamun kafa Da Kur'ani 8

3-Kamun kafa Da Kyawawan Ayyuka 9

4-Kamun kafa Da Adu'ar Manzo (S.A.W) 11

5-Kamun kafa Da Addu'ar Dan'uwa Mumini 13

6-Kamun kafa Da Addu'ar Manzo Bayan Rasuwarsa 14

Ibn Taimiyya Da Mabiyansa 17

Tambayoyi Da Amsoshi 19

Tambaya ta farko: Shin neman addu'a daga mamaci shirka ne? 19

Tambaya ta biyu: Shin neman addu'a daga mamaci ba shi da wani amfani? 19

Tambaya ta uku: Shin tsakanimmu da wadanda suka rasu akwai wani shamaki wanda zai hana su jin maganarmu? 20

Tambaya ta hudu: Shin Manzo yana jin maganarmu? 20

7-Kamun kafa Da Mutane Tsarkaka Da Mutane Masu Daraja 22

Tarihin Kamun kafa Da Bayin Allah Tsarkaka 25

Kamun kafar Masu Tsarki Da Matsayi A Cikin Ruwaya 28

Kamun kafa Da Manzo Da Annabawan Da Suka Gabata 29

Kalu balanta Da Amsoshinsu 30

Kalu balanta ta biyu: 30

Kalu bale na uku: 31

Kalu bale na hudu: 33

1-Ruwayoyin Halascin Tawassuli Ko Kamun kafa, Mutawatir Ne 35

2-Littattafai Dangane Da Tawassuli 36

Abin Da Littafin Ya Kunsa 38