Muassasar alhasanain (a.s)

Imam Ridha

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

Imam Ali Ridha (a.s)

Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com

Imam Ali Ridha (a.s) Imami Na Takwas: Imam Ali Ridha Dan Musa Al-Kazim (a.s)
Sunansa da Nasabarsa: Ali dan Musa dan Ja'afar dan Muhammad. Mahaifiyarsa: Kuyanga ce mai suna Najma. Alkunyarsa: Abul Hasan, Abu Ali. LaKabinsa: Arrida, Assabir, Arradiyyu, Alwafi, Alfadil. Tarihin haihuwarsa: 11 Zul-ka'ada 148H. Inda aka haife shi: Madina.
Matansa: kuyanga ce mai suna: Sakina, an ce sunanta Al-hizran, da Ummu Habib 'yar Al-mamun. 'Ya'yansa: 1-Muhammd Al-jawad 2-Al-kani'u 3-Ja'afar 4-Ibrahim 5-Al-Hasan ko Al-Husaini 6-A'isha.
Tambarin zobensa: Masha'Allah la Kuwwata illa bil-Lahi. Tsawon rayuwarsa: shekara 55. Tsawon Imamancinsa: Shekara 20. Sarakunan zamaninsa: Abu Ja'afar Al-mansur da Muhammad Al-Mahadi da Musa Al-Hadi da Harunar-Rashid da Al-amin da Al-ma'amun dukkaninsu sarakunan Abbasiyawa ne.
Tarihin shahadarsa: Karshen Safar 203H. Inda ya yi shahada: Garin Duss a Khurasan. Sababin shahadarsa: Shan guba a lokacin halifa Al-ma'amun. Inda aka binne shi: A Al'karyar San'abad a Duss Khurasan. A yau wurin yana cikin birnin Mash'had.
Shi ne Imam Ali Ridha dan Musa (A.S) kuma babarsa ita ce Najma, an haife shi a ranar alhamis a goma sha daya ga zulKi'ida, shekara ta dari da arba'in da takwas a Madina, kuma ya yi shahada da guba a ranar juma'a Karshen watan safar shekara ta dari biyu da uku, kuma dansa Imam Jawad (A.S) shi ne ya shirya janazarsa, kuma ya binne shi a Khurasan inda kabarinsa yake yanzu.
Ya kasance mafi ilimi da fifiko da baiwa da kyawawan halaye da KasKan da kai da ibada.
Ma'amun ya kira shi daga Madina zuwa Khurasan kuma ya sanya shi halifan musulmi, sai dai Imam mai zuhudun duniya (A.S) bai karba ba, saboda ya san makirci da yaudara da take cikin hakan, kamar yadda kakansa Imam Ali (A.S) bai karba ba a yayin da dan Auf ya bijiro masa da sharadin tafarkin halifofi biyu, domin Imam ya san cewa halifanci a wannan zamani ta tsayu a kan abubuwa biyu ne kuma dukkansu Karya ne ga Allah kuma Allah bai yarda da wannan ba.
Na farko: ya karbi sharadi sannan sai ya Ki aiki da shi kamar yadda Usman ya yi, wannan kuwa Karya ce ta magana kenan kuma abin Ki wajen Allah (S.W.T).
Na biyu: ya Karbi sharadin sai ya yi aiki da shi, wannan kuwa yana nufin tafarkin halifofi biyu, wanda shi kuma bai yarda da su ba kuma Karya ce wannan ta aiki kenan kuma abin Ki wajen Allah. Don haka ne ma Imam Ali (A.S) bai ga wata hanya ba da zai samu yardar Allah sai dai ya Ki karbar hakan .
Da Imam Ali Rida (A.S) ya Ki karbar halifanci sai Ma'amun ya samu rushewa mai tsanani kuma abin da ya kira Imam saboda shi, kenan bai samu nasara a kansa ba, sai ya bijiro masa da ya karbi mai jiran gado, kuma ya tilasta shi a kan hakan, sai dai Imam (A.S) ya shardanta masa cewa ba zai shiga sha'anin daula ba, kuma ya karbi mai jiran gado a kan wannan sharadi ne.
Ya gaji ilimi daga kakanninsa masu daraja da girma (A.S) kuma wannan ya bayyana ga addinai da mazhabobi da fikirori a majalisin tattaunawa da Ma'amun ya shirya masa tare da manyan mazhabobi da addinai.
Haka nan ya kasance mai yawan ibada, kuma yana raya dararensa da ita, yana sauke Kur'ani a kwana uku, kuma saudayawa yakan yi salla da dare da wuni har raka'o'i dubu, kuma yana yin sujada mai tsayi har sai ya dauki wasu sa'o'i, kuma ya kasance mai yawan azumi. Ya kasance mai yawan kyawawan halaye, mai yawan baiwa da sadaka a boye musamman a darare masu duhu.
Daga kyawawan halayensa da ladubbansa ya kasance bai taba yi wa wani magana ta jafa'i ba kuma bai taba kaurara wa wani magana ba. Bai taba yin dogaro tsakanin abokin zamansa ba, kuma bai taba yin KyaKyata dariya ba, bai taba yin tofi a gaban wani ba kuma idan aka zo masa da abinci sai ya kira dukkan ahlinsa da masu yi masa hidima ya ci tare da su.

 

 

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)