Muassasar alhasanain (a.s)

Hakkin Salla

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

MARUBUCI: Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
HaKKIN SALLA
Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Kuma hakkin salla shi ne ka san cewa ita halartowa ce zuwa ga Allah madaukaki, idan ka san hakan, sai ka tsaya matsayin bawa mai kaskanci, kaskantacce, mai kwadayi, mai tsoro, mai kauna, mai jin tsoro, miskini, mai kaskan da kai, ga wanda yake tsayawa gabansa da nutsuwa da dumanina. Ka fuskanto da zuciyarka a kanta, ka tsayar da haddodinta da iyakokinta, -tare da sunkuyawa da kaskan da gefe, da tausasa kafadu, da kyautata ganawa da Allah ga kansa, da kwadaituwa zuwa gareshi a kan fansar wuyanka wacce kurakuranka suka kewaye ta daga wuta, kuma zunubanka suka halakar da ita-.
Salla kamar sauran ibadoji suna da matukar muhimmanci a kiyaye su domin umarni ne na Allah madaukaki, salla ita hanya ce ta saduwa da Ubangiji da ganawa da shi a wasu lokuta na musamman domin rusanawa da tunawa da ni'imominsa da gode masa, da kuma neman biyan bukatu wurinsa.
Wannan lamarin yana kama da ubangida da bayinsa ne da suke kai masa bayanin sakamakon abubuwan da suka wakana a wasu lokuta na musamman, sai dai wannan a matsayin misali ne. Lokutan salla wasu lokuta ne na musamman da ake sake dasano haske daga mahallicci, da tunawa da alkawuransa, da sake daukar wasu nauye-nauyen cewa za a ci gaba da rusuna masa, kuma shi kadai ne muke bautawa, kuma gareshi muke neman taimako.
Duk sa'adda mutum ya samu alakar kusanci da ubangijinsa sai alakarsa da shedan ta nisanta, sai ya ji tsoron Allah ya yi fushi da shi sakamakon wani mummunan aiki da zai yi, ko wani kyakkyawan aiki da ya bari, sai ya tabbata kan tafarkin shiriya abin yabo. Wannan lamarin ne ya sanya salla take hana alfahasha da mummuna, kuma alama ce ta karbuwarta, domin idan aiki da mummuna da nisantar kyakkyawa ya ci gaba alhalin akwai salla, to wannan yana nuna salla tana samun matsala ke nan, sai bawa ya yi kokarin gyaranta domin samun rabauta da arzuta, da kusanci wurin ubangijinsa.
Salla tattaunawa da Ubangiji ne kai tsaye, sai dai ta bambanta da sauran tattaunawa, domin tsayuwa ce da bawa zai yi a gaban ubangijin da ya halicce shi, wanda shi ne yake ba shi dukkan wani abu na rayuwa da samuwa, kuma yake tafiyar da dukkan lamurransa, yake kare shi daga dukkan sharri dare da rana, yake ba shi dukkan ni'imominsa a kodayaushe.
Sannan kuma ubangiji ne wanda ba a ganinsa, kuma ba a iya suranta shi a tunani, hotonsa ba ya iya zowa kwakwalwa, don haka shedan zai yi matukar kokari ya bata salla ta hanyar sanya wa bawa jin cewa ga kamannin ubangijinsa, sai ya bawa ya sawwala wani abu daban a tunaninsa sai ya bauta masa a matsayin ubangijinsa, har ya koma wurin ubangiji bai taba bauta masa ba, domin ya bauta wa surar da take cikin tunaninsa ne kawai.
Sannan an sanya wannan sallar sau biyar a sati domin dan Adam ya kasance bai gafala daga ubangijinsa ba, sai ya tuna shi har sau biyar a rana daya, kuma ubangiji ya ji muryar bawansa da bukatunsa ba don bai san shi ba, sai domin shi makusanci ne mai amsa addu'o'insa idan ya kira shi, sannan kuma salla ma'auni ce na su waye masu kiyaye umarnin ubangiji, su waye kuma ba sa kiyayewa.
Salla ibada ce mai fuskanto bawa zuwa ga daukakar rayuwar lahira da kawar da tunaninsa da dukkan rayuwar duniya da zoginta, da fuskantar da shi zuwa ga ambaton Allah, wannan lamarin yana ba wa ransa nutsuwa da samun yarda, da addu'a da kaskan da kai, da kuma rusana wa girman ubangiji da daukakarsa, da sanya wa bawa jin cewa shi ba komai ba ne sai bawan Allah, da daidaita shi a sahun samuwa daya da talaka da mai kudi, da jagora da mabiyi, duk babu wani bambanci.
Tun da salla tana hana alfahash da munkari, sannan kuma tana sanya nutsuwa ga bawa sai ta kasance mafi kololowar hanyar ganawa da ubangiji, kuma mafificiyar hanyar samar da nutsuwa ga bayin Allah. Kur'ani mai daraja da daukaka ya yi bayanin wannan lamari mai muhimmanci yayin da yake cewa: "... Idan sharri ya same shi sai ya kasance mai raki, idan alheri ya same shi sai ya kasance mai hani, sai dai masu salla...".
Sannan salla tana karfafa alakar zaman tare cikin al'umma ta yadda aka sanya musu bikin kowane sati ta hanyar yin sallar juma'a domin su taru su tattauna matsalolinsu da yadda zasu warware su, domin su dauki mataki daya bai daya kan dukkan abin da suke fuskanta na hadari da dukkan abin da yake damun su.
Sannan mai salla kada ya yi tsammanin cewa yin sallarsa yana nufin ya yi abin da ya so na sabon Allah ne, domin wannan yana nuna cewa ashe sallarsa ba ta karbu ba ke nan. Domin Hadisi Kudsi ya yi nuni da cewa: "… kawai ina karbar salla ga wanda ya kaskantar da kai ga girmana ne, bai yi takama da ita kan halitta ba, bai kwana mai dagewa kan sabona ba, ya yanke wuninsa kan ambatona, ya ji tausayin miskini da matafiyi da wacce mijinta ya rasu, ya ji kan ma'abota musiba, wannan haskensa kamar hasken rana ne, zan rene shi da izzata, mala'ikuna su kare shi, in kuma sanya masa haske a cikin duhu, da hakuri a gun wauta, misalinsa a cikin halittata kamar Firdausi ce a tsakanin aljanna" .
Bayanai masu yawa sun zo game da addu'o'in imaman shiriya cikin salla da yadda suke ganawa da ubangiji madaukaki, sai dai gudun yawaitawa ya sanya mu tsayawa hakan.
A cikin Wasika ta Ishirin da Bakwai a littafin Nahajul-balaga, cikin abin da ya rubuta zuwa ga Muhammad dan Abubakar yayin da ya sanya shi gwamnan Misira, yana cewa:
Ka yi salla a lokacin da aka sanya mata, kada ka gaggauta lokacinta don wani abu, kuma kada ka jinkirta ta daga lokacinta saboda shagaltuwa da wani abu, kuma ka sani cewa kowane abu na aikinka yana bin sallarka ne.
Sannan yin salla babu hankali tozarta ta ne, domin wanda yake holewa yana keta hurumin Allah alama ce ta cewa sallarsa tana da matsala, kamar yadda wanda bai san Allah ba, ya sawwala wani abu da ya saka shi a zuciyarsa yake bautarsa saboda jahiltar ubangijinsa shi ma ya yi asara ne kawai. A cikin Nahajul-balaga hikima ta 137: Imam Ali (a.s) yana cewa: "Sau da yawa mai azumin da ba shi da komai a azuminsa sai kishirwa, kuma da yawa mai tsayuwar sallar dare ba shi da komai sai wahala, madalla da baccin masu hankali da cin abincinsu!".
Sai dai wani lokaci wasu mutane suna kula da nafiloli sai su tozarta wajibai, wanna ma ba karbabbe ba ne a addini, a kan haka ne zamu ga a cikin Nahajul-balaga hikima ta 35: Imam Ali (a.s) yana cewa: Babu wani kusanci da Allah da nafiloli, idan ta cutar da farillai. A hikima ta 270 kuwa yana cewa: "Idan nafilfili suka cutar da farillai, to ka guje su".
Haka nan idan da wani lokacin mutum zai tsinci kansa a cikin kasalar ibada, ta yadda idan ya hada nafilfili da yin farilla to zasu cutu, shi ma sai mutum ya takaita da yin farillai kawa. A cikin Nahajul-balaga hikima ta 303: Imam Ali (a.s) yana cewa: "Zukata suna da gabatowa da juya baya, idan suka gabato sai ku yi ta nafilfili, amma idan kuwa suka juya baya, sai ku takaitar das u kan yin farilloli".
Sannan zan so yin nuni da wata al'ada maras kyau a kasashenmu da 'yan mata suke yi ta kin fara yin salla har sai sun yi aure, to su sani wannan yana da muni matuka, domin duk yarinyar da ta kai shekaru tara to wajabcin salla ya hau kanta, kamar yadda sauran ibadoji suka hau kanta. Ko da yake wasu mazhabobi sun sanya shekarun sama da tara, amma muhimmi shi ne irin wadannan 'yan mata su sani ba su da wani uzuri wurin Allah da zai hana su yin ibada. Kuma sakamakon barin salla yana jefa su cikin fushin Allah, sannan kuma duk sa'adda suka fadaka ya hau kansu ne dole su rama dukkan sallolin da suka bari bayan sun balaga.
Hafiz Muhammad Sa'id
www.hikima.org
hfazah@yahoo.com
Monday, January 03, 2011

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)