Rayuwar Musulmi da Kirista
Da SunanSa Mad'aukaki Amincin Allah ya tabbata ga Annabi da Alayensa
RAYUWAR MUSULMI DA KIRISTA Rikicin Jos (Jos Crises)
Rikin Jos (Jos Crises) wasu tattararrun fadace-fadace da fitinu da suke kunshe da kyamar juna da kai hari kan juna tsakanin mutanen wannan yankin da suka hada da kabilu mabambanta da masu addinai daban-daban musamman musulunci da kiristanci wanda yakan kai ga rasa dukiya da rayuka. Kuma wadannan rikice-rikice sun fara kafin goman karshe na wadannan shekarun.
Mutum halitta ce mai kima da daraja wurin Allah, kuma Allah ya halicce shi ne domin ya samu kamalar da ta fi ta kowace halitta tun daga aljanu da mala'iku zuwa Ruhu mai girma har ya wuce hakan. Sai dai yana iya yin kasa har ya kai ga mafi munin halitta, sai ya zama kamar kura mai farautar dan'uwansa mutum, ya zama guba mai daci gare shi, ya kasance sharri maimakon ya zama alheri. Lallai ne mun halicci mutum a cikin mafi daidaituwar halitta, sannan sai muka mayar da shi mafi kaskanci kaskantattu: kur'ani; surar Tin; 4-5.
Dalilai masu yawa ne sukan kai ga mutum zama hakan; wani lokaci matsalar tunani ce take samun sa sakamakon jahilci ko gadon wani mummunan tunani na al'ada, ko munanan halaye kamar hassada da kyashi, ko ingizawa daga waninsa, ko kyamar abu maras dalili, ko bangaranci ko kuma huce haushihsa.
Imam Hasan mujtaba jikan manzon rahama Muhammad dan Abdullah (a.s) yana cewa: Mutum makiyin abin da ya jahilta ne. (Gurarul Hikam: 423)
Musulunci addini ne na rahama da sulhu da zaman lafiya, bai yi umarni da wani ya taba wani ba sai idan ya kasance ta fuskacin kariyar kai ne , sannan ya shelanta cewa babu wani tilasci a addini (Bakara: 256).
Don haka ne zamu ga dukkan yakokin da manzon rahama (s.a.w) ya yi a rayuwarsa don kare kai ne, bai taba kai hari kan wasu babu dalili mai karfi ba. Don haka an samu yakoki masu yawa a Madina kuma dukkanninsu sun zama domin kare kai ne daga makiya mushrikai da yahudawa da kiristoci da suke kai hari kan musulmi, kuma Annabi a kowane lokaci yana zabar bangaren sulhu da zaman lafiya ne da rangwame, don haka ne ma adadin wadanda ake kashewa daga bangarorin biyu ba su da yawa a dukkan yakokinsa tamanin da wani abu, wato; wadanda aka kashe na musulmi da kafirai duka ba su kai sama da dubu daya da dari hudu ba.
Musulunci ya sanya rahama da ayyukan tausayi da jin kai su ne kashin bayan asasinsa, kusan talauci ya kawu daga dukkan daula da take kusan fadin kwata na duniya gaba daya, kuma ya kasance labari a lokacin halifancin Imam Ali dan Abi dalib.
Hurrul amuli ya ambaci cewa: Imam Ali (s) yana tafiya a cikin lungunan garin Kufa wata rana, sai ya ga wani mutum yana rokon mutane (yana bara), sai ya yi mamaki sosai, sai ya juya da shi da wadanda suke tare da shi suna tambayarsa mene ne haka?
Sai ya ce: Ni tsoho ne kuma kirista na tsufa ba na iya aiki kuma ba ni da wata dukiya da zan rayu da ita, sai na shiga bara.
Sai Imam Ali (s) ya yi fushi ya ce: Kun sanya shi aiki yana saurayi sai da ya tsufa zaku bar shi?! Sai ya yi umarni a sanya wa wannan kirista wani abu na albashi daga Baitul-mali da zai rika rayuwa da shi .
Haka nan ne musulunci ya yi mu'amala kyakkyawa ga kowane mutum ba tare da la'akari da addininsa ko launinsa ko kabilarsa ba!. Don haka a yaushe ne aka samu sabanin hakan a rayuwar musulunci! Tabbas idan wani abu sabanin haka ya wakana to sai dai idan an kauce wa koyarwar musuluncin ce.
Sannan kiristanci ma ya zo da salon kira da kyautata halaye da tausayi da jin kai kamar dai yadda musulunci ya zo da shi, sai dai musulunci ya zo da kari kan hakan da abubuwa masu yawa domin shi tsari ne da yake da mahanga a kowane fage na ilimi da aiki.
Al'ummarmu ta dade tana zaman lafiya a tare tsakanin musulmi da kiristoci, amma sai ga shi a wadannan shekarun na karshe abin ya yi kamari, ta yadda aka samu kashe-kashe baji-bagani tsakanin masu wadannan addinai. Ya isa kawai wancan ya ga wannan sai ya hau shi da kisa da duka! da kona dukiyarsa! da rusa gidansa!. Wannan abin takaici yana wakana lokaci bayan lokaci, amma sai ya yi ta maimaituwa ta fuska iri daya, kuma a wuri daya, a kasa daya, amma babu wani mataki na hankali ko doka da masu hukunci a wannan kasa suke dauka. Imma dai saboda mai hukuncin yana ganin zai hukunta masu addini daya da shi, ko kuma zai hukunta masu yare daya da shi, ko kuma shi ma yana goyon bayan irin wannan abin a boye.
Sai ra'ayoyi suka bambanta kan sababin wannan mummunan lamarin; da mai ganin jahilci ne, da mai ganin siyasa ce, da mai ganin talauci ne da ya yi wa al'umma yawa, da mai ganin coci ce take tunzura kirista auka wa musulmi, da mai ganin akida ce karkatacciya da take kunshe cikin tarihi mai ramuwar gayya na abin da aka yi wa wadanda ba musulmi ba, da mai ganin tuhumar musulmi ce da kirista suka yi kan bom da aka sanya, da mai ganin akwai hannun kasashen waje kan wannan lamari, da mai ganin sakacin gwamnati ne ya jawo hakan saboda rashin yi wa tubkar hanci, da mai ganin cewa kyamar juna da kyashi, da hassada ce ta jawo wannan lamarin. Muna iya nuni da wasu ra'ayoyi a takaice da ake muhawarori kansu kamar haka:
1- Bakin Talauci
Talauci mummunan abu ne a cikin al'umma, don haka ne musulunci ya yi kokarin ganin matakin farko shi ne kawar da shi, sai ya sanya dokokin humusi, da zakka, da sadaka (cibiyoyin ayyukan alheri a yau da jin kan raunanan mutane), da kyauta, da lamunin rayuwa, da biyan bashin talaka, da aurar da shi, da ba shi jari don sana'a, kuma ya kara da halatta wa mutane raya wuri da cewa; idan suka raya wuri to na wanda ya raya shi ne.
Tabbas talauci yana taka rawa mai girma cikin rigingimu, sai dai ba shi ne kawai dalilin da ya sanya wannan rikici na Jos ba, don sau da yawa an zauna a talauci tun da can, amma ba a samu wannan ba. Kuma akwai al'ummu masu yawa da suka rayu tare da juna da talauci amma ba su yi wannan rigimar ba, maimakon haka sun taimaka wa juna ne kan ci gabansu, kamar yadda zamu iya gani ba kawai Jos ce ake fama da talauci ba, tayiwu yankuna masu yawa na Nijeriya su fi Jos talauci, amma ba a samu wannan ba.
Sai dai ba muna kore cewa talauci yana taimakawa kan irin wadannan rikice-rikice ba, amma yaushe ne masu hankalin wannan al'umma da shugabanninta suka zauna domin ganin sun samar da hanyoyin kwarai domin kawar da talaucin da yake cikin wannan al'umma, yaushe ne suka yi wani abin azo-agani kan hakan!.
Don haka idan talauci ne matsalar to alhakin dukkan wannan rikicin yana kan hukumar da lamarin Jos ya shafa ne da ba ta yi wani abu ba domin rage kaifinsa da samar da mafita kan wannan lamari mai dacin gaske!.
2- Duhun Jahilci
Jahilci wata siffa ce mummuna ga dan Adam, kuma duk inda aka same shi, to akwai karancin tunani da hankali tare da shi, kuma akwai kaskanci da yake kunshe cikinsa. Sai dai masu ganin wannan ra'ayin ba su tantance mana wane irin jahilci suke nufi ba, shin jahilci ne da addinan juna, ko kuma jahiltar juna ne, ko jahiltar al'adun juna ne, ko kuma jahilci ne na rashin karatu kawai, ta yadda inda mutane suna karatu kamar sakandare, ko jami'a da ba su fada cikin wannan rikicin ba.
Idan kuwa haka ne, yana da kyau mu san jahilcin da yake sabbaba rikici da rigima da kashe juna tsakanin al'ummarmu domin sanin asasin wannan bal'ain don kawar da shi. Matukar ba mu san wane jahilci ba ne to wannan yana nufin ko da yaushe rayuka da dukiyoyin mutane suna cikin hadari. Idan kuwa dukkan wadannan nau'o'in jahilci ne suke haddasa wannan rikici, to wannan yana nufin aiki babba ya hau kan gwamnati da al'umma da malaman addini su tashi haikan don yakar wannan jahilcin.
Sai dai tambaya a nan ita ce; shin a cikin masu kai wannan harin kan junansu babu wadanda suke da ilimi mai zurfi a addini ko ilimin zamani kuwa?! Wannan tambaya ce wacce kowane mai hankali yake kawo ta, kuma a fili yake ganin amsarta cewa masu yawan tayar da wannan rikici da shiga cikinsa tsundum har da harbin mutane da bindigogi wani lokaci cikin kayan ma'aikata ma suke kawo wannan harin.
Nau'in hare-haren da ake kaiwa, da masu kai harin yana nuna mana cewa ba jahilai ba ne masu kawo wannan harin! Idan ana nufin rashin yin karatun boko shi ne jahilcin kamar yadda yawancin masu wannan ra'ayi suke nufi. Wannan yana iya nuna mana ke nan masu kai harin dai mutane ne masu wata manufa daban da suke son su cimma.
3- Makircin Siyasa
Akwai magana mai karfi da take yawo a cikin wannan al'ummar cewa masu wannan rikici da masu tayar da shi suna samun karfafa daga 'yan siyasa ne, kuma su 'yan siyasar suna da hadafi na musamman kan wannan lamarin wanda yake shi ne tabbata kan mulki, don haka sai su rika tayar da wannan rikici domin kashe mutanen da suke ganin abokan hamayya ne da zasu iya cin nasara kan su.
Wannan ra'ayi ne mai karfi matukar gaske, domin 'yan kabilar gwamna da mutanensa ko masu addini daya da shi suna iya yin kwanaki suna kisa amma babu jami'an tsaro a kan titina. Wani abin takaici da za a karar da dukkan musulmin da suke wannan nahiya to gwamnatin Jaha ba zata iya tura ko da dan sanda daya ba domin ba su kariya har sai dai gwamnatin tarayya ta sanya hannu, don haka ne wannan ra'ayin yake da karfi matukar gaske.
Inda wannan ra'ayi yake dada karfi bayan abin da muka kawo shi ne abin da wadanda suke wannan wuri suke gani da idanuwansu, da abin da jaridu suke bugawa, da kiraye-kirayen da ake yi wa gwamnatin tarayya na ta shiga cikin lamarin domin bayar da kariya duk suna nuna hakan.
Idan da za a ce duk wani gwamnan da aka samu a jaharsa an yi irin wannan rikicin ko da kuwa mutum daya ne aka kashe, to shi ba kawai ya rasa mulkinsa ba ne, wannan yana iya kai shi ko ga rasa nasa ran, ko kuma zaman gidan yari har mutuwa, da ba zaka taba samun wannan ya faru a ko'ina ba cikin fadin kasarmu.
Idan akwai wasu dokoki masu tsauri kan mai mulki, to da zarar gwamna ya ji wuta ta huru daidai da minti daya ba zai yi sakaci ba wurin kare rayukan wadanda aka zalunta. Kuma da ka gan shi ya gaggauta tsayar da adalci kan wadanda suka yi wannan lamarin domin babu hannunsa, kuma da zai yi wa masu yin wannan harin hukuncin da wani ba zai sake sha'awar kawo irin wannan rudun ba!
4- Ingizawar Coci
Akwai masu ganin Coci ce take tunzura kirista da ingiza su don auka wa musulmi da kisa, sai wannan lamarin ya kasance ya yi kamari kuma ba yadda za a yi ya dakata tun da ya samo daga akida ne, don haka dole ne a dakatar da abin daga Coci domin a samu zaman lafiya.
Sai dai wannan lamari ne wanda ban samu wani dalili kansa ba, domin idan Coci tana yin haka, sai dai idan Cocin Jos ce take yin haka, ko kuma wasu daga malaman Cocin Jos, domin akwai Coci a ko'ina a Nijeriya amma ba a samu wannan lamarin ba. Kuma tun da akwai Coci amma ba a samu tana yin haka ba, sai dai idan masu wannan tunani su ce daga baya ne ta fara yin wannan da'awar kawar da musulmi da sunan "Baki" daga garin Jos! To wannan ma yana bukatar dalili daga masu wannan ra'ayin.
Duk da mun san mahangar Coci kan dan Adam cewa shi sharri ne, kuma wannan sharrin yana tare da shi har ya mutu sakamakon zunubin asalin da babar dan Adam ta sanya babansu ya yi, kuma wannan sharri da ya faro daga sakamakon zunubin asali ba ya kawuwa sai da fansar jinin Isa (a.s), sai dai duk da haka ba mu samu cikin akidun Kiristanci ba cewa ya halatta zubar da jinin mutane haka kawai. Mahangar musulunci tana ganin asalin mutum alheri ne, sai dai yana gurbata ne idan ya cakuda da wasu tunani munana na al'adu ko karkatattun addinai , ko munanan ayyukan lalacewar halaye, don haka ne ma takensa na farko ya kasance shi ne mutun rahama ne ga junansa, kuma ta mahangar da Allah yake so ya kalli dan uwansa ne zai kalla.
Idan kuwa aka samu wani Kirista yana halatta zubar da jinin wasu addinai balle ma a ce lamarin ya taso daga wani malamin Coci, to abin ya munana matuka, kuma wannan kiristan karya yake yi ba kirista ba ne shi sai dai a suna kawai.
Idan da masu wannan da'awar zasu tabbatar da wannan lamarin da haujja to da zamu dora alhakin abin hannun cocin da take yin haka ne kawai ba dukkan Coci ba, ba kuma dukkan kirista ba!
5- Karkatacciyar Akida
Akwai masu ganin cewa karkatacciyar akida ce da take kunshe cikin tarihi mai neman ramuwar gayya na abin da aka yi wa wadanda ba musulmi ba take jawo wadannan rikice-rikice.
Masu wannan mahanga suna ganin cewa a tarihin rayuwar daulolin musulmi da aka yi a wadannan yankunan, an samu zalunci da aka yi wa wadanda ba musulmi ba, don haka ne bayan sun samu ilimi da wayewa sai suke rama abin da aka yi musu! Don haka sai ko da yaushe suke shiri su auka wa musulmi don daukar fansa, su yi kisan kare dangi da ya hada da maza da mata da yara babu wani tausayi!
Sai dai wannan ra'ayin idan mun kaddara cewa haka ne, to yana bukatar tabbatar da zaluncin da aka yi wa wadannan al'ummu da sunan musulunci wannan ke nan. Idan kuma mun kaddara an yi zalunci da sunan musulunci to ya hau kan malamai da sauran masanan musulunci su wayar da kansu kan wasu abubuwa kamar haka:
Wannan zaluncin da ake da'awar an yi musu idan haka ne to bai shafe su kawai ba, domin ya hada har da musulmin kansu da aka zalunta a wadannan daulolin, ta yadda ana iya kwace wa musulmi gonarsa, da arzikinsa, ana iya korarsa daga kasarsa.
Wannan zaluncin yana koma wa ga sarkin da ya yi wannan zaluncin ne, wanda shi ne wuka da nama a kan komai don haka ba musulunci ba ne, aiki ne na wasu mutanen daidaiku da suka yi mulki suka wuce.
Idan wani ya yi zalunci to wannan yana koma wa kansa ne, ba ya shafar wani mutum a duniya ko da kuwa dansa ne, balle kuma zaluncin wani ya shafi wasu al'ummu da suka zo baya wadanda yawancinsu ma ba su san me ya faru a tarihi ba! Babban misali kan haka, babu wani kirista a yau da yake kashe musulmi da zai so don ya yi wannan a yau, a shekaru masu zuwa shi ma sai a hau jikokinsa da 'ya'yansa da kisa, balle shi abin da yake yi yau ba yana kashe jika ko da na wanda yake ganin ya yi wa kakanninsa haka ba ne, sai dai yana kashe wanda shi ma a wadancan lokutan an zalunci kakansa da babansa ne shi ma.
Idan wani ya yi zalunci to ana auna kimar abin da ya yi da sakamakon abin ne, don haka idan wani ya bautar da wani, ko ya kwace masa gona, sai ya biya hakkin bautar da shi da ya yi ne, ko kuma ya mayar masa da gonarsa, amma ba ya kashe shi ba. Balle kuma wanda ake kashewa ya zama bai san ma an yi wani abu kwace gonaki ko bautar ba.
Hada da cewa: Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Allah ya tsine wa wanda ya kashe wanda ba shi ya kashe shi ba, ko kuma ya doki wanda ba shi ya doke shi ba" .
Mu musulmi idan ya tabbata akwai wani musulmi da ya yi zalunci kan wasu jama'a ko wata al'umma a tarihin wannan yanki to mu ne farkon masu suka da la'anarsa kan abin da ya yi, domin idan ya yi da sunan kansa ne, to ya yi ta'addanci, amma idan ya yi da sunan addininsa ne, to laifinsa ya yi girman da ba zamu taba yafe masa ba! Kuma muna yin tir da abin da ya yi da sunan addini!.
6- Sanya Bom
Akwai ra'ayin da yake ganin tuhumar musulmi da kirista suka yi kan Bom ce ta jawo rikicin da ya wakana a wannan ranakun da ya shafi rikicin karshe a Jos, sai dai wannan ya shafi rikicin karshe ne kawai da ya wakana a yankin.
karancin tunani da sanya hankali cikin lamurran da suke faruwa a wannan duniya yana da yawa idan mutum ya duba yadda abubuwa suke gudana. Da zato ne aka kai hari kan Afganistan babu yakini kan wanda ya kai hari kan cibiyar kasuwanci ta duniya domin minti 20 bayan faruwar abin shugaban Amurka ya fadi hasashen wadanda ake zato!, sannan da zato ne aka yaki Iraki babu yakini kan samuwar makamin Nukiliya, haka nan da zato ne ake kai wa juna hari a cikin al'ummarmu.
Akwai bukatar a tantance wanda ya sanya Bom domin hukunta shi, amma ba kawai don wani abu ya faru ba, sai kuma a kai hari kan wata al'umma bataji-batagani ba.
A wannan duniya an fi ye yawo da hankulan mutane da wasa da su, kuma makiyan al'ummu sun samu sabon salon hada rikici tsakaninsu sai su koma gefe suna dariya. Don haka duk sa'adda suka so tayar da fitina sai su aiwatar da wani abu domin su sanya daya ya tuhumi daya, sai gaba, sai rikici, sai yaki. Wannan wani salo ne da makiya dan Adam suke yin sa aduniya.
Don haka ne duk sa'adda wannan lamarin ya faru to yana bukatar sanya hankali, kuma babu wanda ya kamata ya zama hakan sai masu jagorancin al'umma, sai dai mutane Jos ba su yi sa'ar jagorori ba, domin tunanin masu tafiyar da mulkin yankin bai dace da yanayin 'yan adamtaka ba. Sai duniya ta kasance tana da hasashe mai ban mamaki, sai zato ya zama yakini, sai kokwanto ya zama gaskiya. Idan da an sanya hankali zamu iya lura da wasu abubuwa kamar haka:
Ba yadda za a yi musulmi ko kirista da yake yankin Jos ya sanya wannan bom domin bom din ya kashe duka musulmi da kiristan Jos ne.
Musulmai suna girmama bukin da ya shafi annabi Isa (a.s) don haka ba yadda za a yi ranar da ake murnar haihuwarsa su sanya bom don lalata bukin.
Talaka musulmi da kirisata da suke wannan yankin ba yadda za a yi su sanya wannan bom din domin babu mamaki ba su taba ganin bom ba, kai yawancinsu ba su ma taba rike bindiga ba, ba su san yadda ake harba ta ba!.
Ko bindiga ce aka samu a hannun wasu mutane, to laifin hukuma ne balle kuma bom, don haka tun da alhakin tsaro nata ne, laifin yana koma wa kanta, don haka ne dole ta bayar da tsaro ga dukkan al'ummarta babu bambancin addini ko kabila!.
Idan wani abu irin wannan ya faru dole ne a bari gwamnati mai hankali ta yi bincike ta yi iya kokarinta don gano musabbabin abin, zai iya yiwuwa bisa hatsari ne ya fashe, kamar a ce yana hannun soja ne da ya zo wucewa da shi don kai shi wani wuri bisa umarnin gwamnati, ko kuma wasu 'yan ta'adda ne suka dasa shi, kuma su waye? Kuma mene ne hadafinsu? da sauran bincike!.
Mu musulmi idan ya tabbata akwai wani musulmi da yake da hannu kan sanya Bom a Jos to mu ne farkon masu goyon bayan a tsayar masa da dukkan hukuncin da ya dace, domin idan ya yi da sunan kansa ne, to ya yi ta'addanci, amma idan ya yi da sunan addininsa ne, to laifinsa ya yi girman da ba zamu taba yafe masa ba, kuma muna neman a zartar masa da hukunci mai tsanani kan cin mutuncin addininmu da ya yi!.
Sanya Bom a kasashen gabas ta tsakiya ya sanya neman bata musulunci da sunan cewa addinin ta'addanci ne, wannan kuwa shi ne babban rashin adalci da ake yi wa musulunci, domin kafin masu sanya Bom su kashe wanda ba musulmi ba daya, sun kashe musulmi dubu. Don haka wadanda suke sanya wannan Bom ko da kuwa sun kira kansu musulmi to ba musulmai ba ne, sai dai su makiya musulunci da musulmai ne!.
7- kasashen Waje
Wannan ma ya shafi lamarin rikicin da ya faru kwanan ne wanda sakamako fashewar bom ya jawo shi. Masu wannan ra'ayin suna danganta abin da wasu kasashen waje da suka saba haifar da rikici tsakanin al'ummu don cimma burinsu, suna bayar da misalin irin wannan da yake faruwa a kasashen gabas ta tsakiya.
Irin wannan Fashewar Bom yana faruwa a wasu kasahe, kuma yana kai wa ga rikici kamar yadda zamu kawo a misali, irinsa ya faru a Labnon da ya kashe tsohon shugaban kasar Rafik Hariri. Sau da yawa irin wannan idan ta faru ana zargin juna ne tsakanin jama'u masu rigima da gaba, wani lokaci kuma a zargi kasashen waje.
Muna iya ganin lokacin da ya faru sai nan take aka zargi Syria da cewa ita ce, har ma aka sanya shedun karya domin su bayar da shedar zur, sai dai duk da an gano shedun karya aka sanya amma sai aka takura kasar Syria da fita daga Labanon.
Daga nan ne sai Syria ta dora alhakin sanya bom din kan mutanen da suke gaba da ita a cikin Labanon masu taimako daga kasahen larabawa da turai, da Isra'ila a matsayin kasar da take gaba da ita da cewa su suka sanya Bom din don su yi kamfen din korarta da shi daga Labanon.
Da yake dan Adam bai san gaibi ba, kuma yana jahiltar abubuwa masu yawa, kuma yana da sauki a wannan yanayin farfaganda a yi wasa da tunaninsa, sai kuma aka koma ana Zargin Lahud tsohon shugaban kasar Labanon bai ji ba, bai gani ba.
Da wannan bai samu ba, sai kuma aka koma yin sabon Fayel din zargi wanda yake neman ya dora alhakin abin a kan kungiyar Hizbullah ta Labanon, kuma aka so yin amfani da wannan domin rusa ta saboda hadafin babban makiyinta kasar Isra'ila ya tabbata na ganin bayanta.
Wannan lamarin ne ya sanya ita kuwa Hizbullahi ta kawo cikakkun shedu da nuna cewa tana da wasu karihar shedun idan ana neman karin hujjoji kan cewa Isra'ila ta sanya bom din ta kashe shi domin ta samu hargitsa kasar sai ta shigo kamar yadda ya faru a shekarun baya don dai ta shigo wannan karon ta rusa Hizbullah.
Wani abin da yake bayar da mamaki shi ne, shi Firaministan da aka kashe yana da kyakkyawar alaka da kungiyar ta Hizbullah, wannan lamarin ne yake sake ba wa masana siyasa hujja da nuna cewa lallai ba ta da hannu a kashe shi, domin masoyinta ne.
Da wannan ne Hizbullah da wasu kungiyoyi na kasar suka kai ga natijar cewa Isra'il ce ta sanya Bom don ta kashe shi, sai kuma ta hargitsa kasar ta cikin gida. Kuma suna dada karfafa wannan da cewa; bayan wannan lamarin ba wanda aka jefa sai masu gaba da Isra'il, wanda suka hada da Syria da Hizbullah domin fitar da Syria daga kasar, ita kuwa Hizbullah a kawar da makamanta, wannan ne kawai kuma matakan da zasu kawar da barazanar da take damun Isra'il da ta hana ta shiga Labanon don mamaya kamar yadda ta so.
8- Sakacin Gwamnati
Akwai masu ganin sakacin gwamnati ne ya jawo hakan saboda rashin yi wa tubkar hanci, domin duk sa'adda wani rikici ya faru, to yana bukatar a binciki sababinsa, a kuma yi maganin maimaituwarsa, to amma a wadannan yankunan ba haka ba ne. Maimakon duk sadda ya faru a yi bincike don maganin maimaituwa, da kuma yi wa masu laifi ukubar sakamakon abin da suka yi, sai maganar ta sha ruwa kawai.
Wannan lamarin yana daga cikin abubuwan da kowa ya yarda yana daga cikin abin da yake sake haifar da rikici, kuma matukar ba za a yi wa tubkar hanci ba, zai ci gaba har abada.
Abin takaici a nan shi ne; da gwamnan zai yi rashin lafiya da yanzu ka ga ya yi tafiya har kasashen waje domin kawai ya ga likitan da zai duba ya gano musabbin ciwon da yake damunsa don yi masa maganinsa, amma irin wannan mutumin ne babu ruwansa da al'ummar da aka kashe a jaharsa, bai damu da gano ciwon da yake damun al'ummarsa ba! Domin yana da tabbacin abin ba zai shafe shi ba, ba kuma zai shafi matarsa da 'ya'yansa ba!.
Kuma idan ya tabbata cewa akwai hannunsa ma, to wannan lamarin shi ne ya fi kowanne muni!.
9- kyashi da Hassada
Akwai masu jingina irin wadannan rigingimu da ganin cewa kyamar juna da kyashi, da hassada ce take jawo shi! Idan haka ne kuwa to akwai abin bakin ciki a kasa kamar Nijeriya da kowane dan kasa yana da ikon ya zauna inda yake so don samun ci gabansa da na al'ummar kasarsa, amma a samu wasu suna yi wa wasu hassadar ci gaban da suke samu.
Ci gaban mutum daya na kasa baki daya ne, domin misali wanda ya yi odar motoci ya sayar to babu wanda zai amfana sai 'yan kasa, haka nan sauran abubuwan more rayuwa da amfanin al'umma. Amma sai ciwon hassada da kyashi ya shiga al'umma daya, ana yi wa juna hassada da keta da mugunta, wannan lamarin ne ya sanya da rikici ya tashi babu wani abu da wasu suke kai hari kansa sai kayan kasuwancin al'ummar nan.
Idan dai wannan lamarin ya kasance yana daga cikin dalilai to shi ma yana bukatar aiki tukuru domin wayar da kan wannan al'ummar, kuma nauyi ne da ya hau kan malamai da sauran masana da gwamnati kai tsaye. Sai dai yana da nauyi sosai kan malaman addinai don su wayar da kawukan mabiyan addinai kan munin lalacewa halaye, da mummunan sakamakonsa wurin Allah!.
10- Rashin Mu'amala
Wasu kuwa suna ganin rashin mu'amala kyakkyawa daga musulmi da kyama da suke nuna wa kiristoci ne ya jawo hakan, don haka sai wadannan kiristocin suke ganin kamar ana yi musu wani ganin raini da wulakanci, ta yadda hatta da sunan da ake gaya musu kamar kalmar arne tana yi musu ciwo, don haka sai wannan ya yi musu zafi, sai suka fara tunanin yadda zasu kawo karshen wannan lamarin, sai su ma suka fara gaya wa musulmi wannan sunan na arna ko kafirai, sannan wannan bai isa ba, sai suka fara tanadin ganin bayan dukkan musulmi da kashe su, da lalata dukiyarsu.
Idan wannan lamarin ya tabbata to an samu sakaci da takaitawa daga bangarori biyu ke nan; bangaren musulmi da na kiristoci, sai dai hanyar da kirista suka dauka don rama laifin wancan sunan da ake gaya musu ta saba wa hankali da tunani mai kyau. Domin kamar yadda muka kawo ne cewa kowane laifi a bisa doka ta hankali yana da nasa mataki gwargwadon girmansa ne, babu zalunci babu karbar zalunci.
Matakin da ya dace a nan bai kamata ya kai ga kisa ko halaka dukiyar al'umma ba, mataki ne da ya kamata kotu da malamai su warware shi, sai a yi dokar da ta dace da shi!. Ta yadda babu wani musulmi da zai sake gaya wa wani kirista sunan arne, sai ya gaya masa sunansa da hatta da musulunci abin da ya san shi da shi ke nan.
Kai hatta da kalmar kafiri bai kamata a gaya wa kirista ba matukar tana da ma'anar wanda ba shi da addini ne. Kalmar kafiri kalma ce mai fadi da tana da ma'anoni daban-daban, don haka a yankunanmu tana da ma'ana da su masu addinai da ya saba wa musulunci ba sa fahimtarta, don haka sai a kira su da sunan da shi ne sunansu na yanka da musulunci ya kira su da shi, kuma suka kira kansu da shi.
Ayar Kur'ani a surar Hajji: 17, ta nuna mushrikai daban, kirista daban, domin sunansa ke nan hatta a musulunci. Kalmar kafiri tana da fadi, wani lokaci hatta da rashin godiya da butulci an kira shi da kafirci, wasu mazhabobi kamar wahabiyawa suna kiran wasu musulmin kafirai saboda suna yin wani aiki da ya saba wa musulunci a mahangarsu, don haka kalmar kafirci sifa ce ba suna ba ce, sifa ce da tana iya hawa kan wanda yake kiran kansa musulunci idan ya kauce wa hanya ta gari, kamar musulmin da suka yi imani a fili amma bai kai zuci ba (munafukai) an kira su da kafirai a littafin Allah, haka ma wanda ya yi imani da wani bangare, bai yarda da wani ba, an kira shi da kafiri.
Don haka matukar matsalar suna ce to ya hau kan masana su tashi domin ganin sun wayar da kan musulmi kan mene ne musulunci. Sai dai hanzari ba gudu ba, duk sa'adda na yi tunani irin wannan na kan samu cewa, sama da kashi 97% na masu kiran kansu malaman musulunci a kasashenmu ba su ma gama sani ma'anonin da musulunci yake amfani da su shi kansa balle kuma su wayar da kan sauran musulmi.
Wallahi da musulmi sun san musulunci kamar yadda yake, sun san iliminsa kamar yadda yake, sun bi kofar birnin ilimi annabin rahama (s.a.w) imam Ali dan Abudalib (a.s) da ba a samu wani mutum daya da yake kyamar musulunci ba, da dukkan duniya sun rungumi wannan rahama da ta bayyana ta hannun annabin Allah na karshe Muhammad al-mustafa (s.a.w).
11- Aikta Zunubi
Akwai wasu masu ganin cewa aiwatar da zunubi ne da ya yi yawa yake jawo wannan lamarin, domin musulmi ba su kame kansu ba, suna haifar da 'ya'yan banza da matan wuraren ta hanyar da ta saba da addini, sai kuma su watsar su bar musu renensu!.
Sai irin wadannan 'ya'ya suka yi yawa, fasadi ya yadu, aka shagaltu da sabon Allah (s.w.t), don haka sai azabarsa ta sauka ta hanyar sallada kiristoci a kan musulmi domin su gana musu azaba!.
Wannan ra'ayi idan ya kasance haka ne, to yana bukatar sanin gaskiyar hakan tukun kafin hukunci a kai, sai dai abin da ba mai musunsa shi ne sabo yana kawo azabar Allah matuka, amma shin wane irin sabo ne? Kuma shin wannan yankin ne kawai yake da irin wannan sabon ko kuwa? Da sauran tambayoyi da sai an samu amsarsu domin yanke hukunci da karfafar wannan ra'ayin.
12- Gabar kabilanci
Akwai masu ganin cewa; fadan na kabilanci sai, kuma wannan kalmar sai sai zaka ji tana yawo a kafafen watsa labarai, babu wani abu sai kalmar addini sai kabilanci wani lokaci a kara sai siyasa.
Idan wannan ra'ayi sai zama tabbatacce to yana bukatar sai san wadanne kabilu sai suke rigima a tsakaninsu tukun domin sanin mene sai asalin rigimar, shin kyamar kabila sai kawai babu wani dalili sai kawai wata kabila sai hau wata sai kisa, ko kuwa tsokana sai tsakanin kabilu yake kawo hakan, ko kuwa babu wani dalili sai dai kawai gaba maras hankali.
13- Rashin Adalci
Rashin adalcin gwamnatin jahar Fulato kan 'yan wannan jahar yana daga cikin abin da ya fi yawo a bakunan mutane, kuma wannan ne yake jawo rikici a wata mahangar. Domin wadanda suka yi laifi suka kashe mutane ba a taba su, wadanda kuwa aka zalunce su idan suka rama sai a gaggauta kama su, misalai da yawa ne suka faru kamar na kama Fulani da aka yi a bayan rikicin January 2010, bayan an kashe musulmi an kona su, an kashe Fulani an kama shanunsu babu ko mutum daya da gwamnatin Jaha ta kama, amma suna zuwa su dauki fansar shanunsu da aka kashe cikin lokaci kankani sai ga shi duk an kama su a hannun 'yan sanda!.
Don haka wannan wuta ce wacce zata yi ta ruruwa a ko da yaushe, babu wani lokaci har abada da zata tsaya matukar bakin zalunci ya yi katutu a wannan nahiya tamu kuma babu wani adalci da wanda aka zalunta yake gani. Wannan lamarin yana nufin wata rana ya tsallaka jahohin Jos, da Bauchi ya watsu duk kasar Nijeriya, a nan ne wanda yake jin dadin wannan lamarin zai gane cewa kasarsa zata yi masa wahalar zama saboda zaluncin da ya yi wa al'ummarsa.
14- Zafin Addini
Wannan ra'ayin yana ganin rikicin na addini ne kawai ba wani abu ba, kuma wasu addinan ne suke kyamar wasu, don haka suke ganin kawar da su da neman ganin bayansu. Don haka ne ba za a samu kwanciyar hankali ba matukar kiristan wannan wurin yana ganin musulunci matsala ce gare shi kuma zai ci gaba da kai masa hari duk sadda ya samu dama!.
Suna ganin wannan lamarin ne ya sanya kiristan wurin yake kiran musulmi bako, don haka duk musulmai baki ne, kuma dole ne su bar wannan yankunan baki daya. Sai dai wannan dalilin ya fi kama da na kabilanci, ko 'yan garanci, ko bangaranci, amma ana iya jingina shi da addini saboda shi mai kin abu yana iya ba shi duk sunan da ya ga dama don bata shi.
Idan kuwa ya tabbata cewa kin wani addini mai girma kamar musulunci ne ya jawo wannan to yana bukatar sanin masu wannan tunanin, shin duk kiristan wannan wurin ne, ko kuwa wasu daga cikinsu ne, ko wata Coci ce mai wannan tunanin. Duk wadannan abubuwan suna iya sanya bincike mai ma'ana da zai iya gano asalin matsalar, idan kuwa ba haka ba, to wannan yana nufin ci gaban wannan matsalar ko da yaushe, kuma a ko'ina!.
Idan duk wadannan abubuwan suka tabbata to duk kowa ya yi tarayya cikin rikicin da fitina, don haka sai a zauna domin ganin an warware matsalar daga tushe.
15- Ramuwar Gayya
Akwai masu da'awar ramuwar gayya a ko da yaushe aka samu rikici, sai dai kana iya rasa ramuwar gayya a kan waye? Kuma me ya yi ake yin ramuwar gayya a kansa? Da sauran tambayoyi da ba su da amsa!. Idan wani ya yi wani abu wanda ba a san shi ba, ba ma'ana a yi ramuwar gayya kan wani, balle kuma shi kansa abin da aka yi din ba a san shi ba!. Kuma ko da an san wani abu da wani ya yi kan wasu mutane, to ramuwa tana hawa kan shi mai laifin ne ba kan wata al'umma ba! Masu hankali da hangen nesa ne suke iya sanin maboyar makirce-makirce irin wadannan.
Da za a samu kwamitin gaskiya don neman warware matsalolin nan masu cin rai da suke addabar al'umma, mu a shirye muke mu taimaka don samun mafita mai dorewa! Sai dai kash!
Da wannan ne zamu iya sanin kima da girman shahararren malamin nan na Iraki mai daraja Sayyid Sistani yayin da yake cewa da makiyan al'ummar Iraki masu sanya bama-bamai a masallatai da hubbarorin ziyarar 'yan Shi'a yana mai cewa: Da zasu kashe rabin Shi'ar Iraki da ba zai bayar da izinin ramuwa ba. Sayyid Sistani ya san sarai cewa; masu yin wannan aiki karyar sunnanci suke yi domin sunan musulunci ma bai cancance su ba.
Wannan shi ne lamarin gaskiya da marubucin Jaridar nan ta "Akhbarul Arab" ta turanci mai suna malam "Jamal al-Khashakji" ya yi furuci da shi yana mai girgizawa da girmamawa ga Sayyid Sistani wannan hikima da tunani mai zurfi nasa, sai dai amma abin bai yi wa malaman wahabiyawa a Saudiyya dadi ba. Malamin yana cewa: Ya kamata malaman Azhar, da mai fatawar Saudiyya, da Sheikh kardawi su tafi Najaf domin su sumbanci hannun Sayyid Sistani. Yana cewa; Ku sani da Shi'a sun ga dama su ma zasu iya kashe wadannan masu sanya musu Bam, sai dai Sayyid Sistani ya tsayar da wannan fitina, da fatawar da ya ba wa 'yan Shi'a ta rashin halaccin kashe wani mutum musulmi ko mece ce mazhabarsa.
Na gama wannan rubutu da safiyar ranar da Sadik dan Sheikh Muhammad Nur Das (a.j.k) ya rasu a nan Kano sakamkon wutar lantarki da ta ja shi zuciyata tana zafin bakin cikin munanan halayen da aka sanya kasashenmu ciki, sai da safiyar na yi tafiya zuwa Birnin Tehran don warware wani rashin fahimta, sai dai ina can wurin zaman sai wannan labari mai tsananin daci da bakanta rai ya same ni. Don haka duk wanda ya karanta wannan rubutu nawa ya yi salati ya bayar da ladan ga wannan yaro.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Sunday, February 06, 2011