Hakkin Ilimi
MARUBUCI: Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Kuma hakkin mai tarbiyyantar da kai da ilimi -mai ilmantar da kai-, shi ne ka girmama shi, ka kuma karrama majalisinsa, da kyautata sauraronsa, da fuskantowa zuwa gareshi, kuma kada ka daga sautinka, kuma kada ka amsa wa wani mutum wani abu da yake amsa masa sai dai ya kasance shi ne wanda yake amsawa, kada ka yi wa wani magana a majalisinsa, kada ka yi gibarsa, kuma ka yi kariya gareshi idan aka ambace shi da mummuna, kuma ka suturta aibinsa ka bayyanar da darajojinsa, kada ka zauna da mikiyinsa, kuma kada ka yi gaba da masoyinsa. Idan ka yi haka, to mala'ikun Allah zasu yi maka sheda cewa ka nufe shi kuma ka san iliminsa saboda Allah ne ba don mutane ba".
Wannan ita ce shiryarwar Imam Aliyyu Sajjad (a.s) ga dalibi dangane da malaminsa, amma malami shi ma akwai hakkin dalibi a kansa, sai dai na malami ya fi girma, don haka shi ma malami yana hawa kansa ya tausaya wa dalibai, ya san cewa dansa ne don haka yana neman tsiransa ne, sannan kada ya yi wa dalibinsa gori ko ya yi masa mummunar ma'amala ko ya kausasa masa hali.
Malami mai hikima shi ne wanda yake yi wa dalibansa nasiha, ya nisantar da su daga miyagun halaye, kada ya muzanta musu wani ilimi da ba a wajansa suke koyon sa ba, kamar idan shi malamin nahawu ne to kada ya rika kushe musu Ilimin mandik, ya rika yi musu magana daidai fahimtarsu, kada ya yi musu rowar Ilimi.
Ilimi ko ilmi an fassara shi da ma'anoni daban-daban bisa yadda kowane ilimi yake kallon sa, misali ilimin falsafa yana ganin ilimi shi ne halartowar wani abu gun wani abu, idan abu maras mariskai na zahiri (wato maras jiki na zahiri) ya samu halarta gun wani kamarsa, kamar yadda rayin mutum take samun ilimi da wani abu ta hanyar daukar fotokofinsa da yake halarto mata sai ta san shi. Amma ilimin sanin tunanin dan Adam da yadda za a gyara shi wanda aka fi sani da ilimin mantik da ya tashi sai ya ce; ilimi shi ne halartar surar wani abu a cikin tunani.
Sannan wasu ruwayoyi sun yi nuni da cewa ilimi shi ne biyayya ga Allah, sabo kuwa shi ne jahiltar Allah, don haka zamu ga ashe ke nan ba wani abu ba ne jahilci sai sabo, ba wani abu ba ne ilimi sai biyayya ga Allah.
Sannan akwai wasu bayanai game da ilimi da wasu malaman yamma suka tafi a kansa da ma'anar cewa duk wani abu da ba ya iya yiwuwa a yi bincikensa ta hanyar tajribar mariskai to wannan abin ba ilimi ba ne, don haka duk wani ilmi da muke gani kamar ilimin addini, ba ilimi ba ne, domin babu wata laboratare da za a iya bincike a gano akwai Allah ko babu don haka addini ke nan ba ilimi ba ne. Kuma idan muka dauki ilmin falsafa shi ma ba ilimi ba ne domin babu wata laboratare da zamu iya binciken wani abu samuwa.
Don haka ne sai wannan bayanin yake nuna ilimi a matsayin wani abu ne da ya shafi duk wani abu da yake da alaka da zahirin samammu, amma duk wani ilimi da yake binciken wasu abubuwa da ba a riskar su da zahiri da mariskai kamar Allah, rayuka, da makamantansu to wannan ba ilimi ba ne.
Wannan isdilahi ne da ya faro daga turai tun lokacin da suka yi juyin tunani da ya samar da sabon tunani a turai, sai suka dauki addini da duk abin da ya shafe shi a matsayin wani abu da ba ilimi ba.
Idan mun duba duka wannan bayanai game da ilimi zamu ga kowane ilimi yana duba mene ne ma'anar ilimi daidai gwargwadon nau'in binciken da ya dogara kansa, ko kuma bisa akidar mai bincike.
Don haka ne zamu ga falsafa tana ganin halartar samamme gun samamme (wanda yake halarta ce ta maras jiki gun maras jiki) domin yana bahasi kan samuwa ne. Amma ilimin mantik tun da yana binciken gyara tunanin dan Adam ne sai ya ga ilimi a matsayin halartar surar wani abu a cikin tunani. Sannan idan muka duba yadda masu binciken ilimin dabi'a suka yi bayanin ilimi zamu ga sun yi bayaninsa yadda ya yi daidai da imaninsu ne, ta yadda ba su yadda da wani abu ilimi ba sai idan ya kasance za a iya binciken sa ta hanyar laburatare.
Ilimi yana da kima matuka kuma darajarsa a kan komai ba ta boyuwa, ubangiji ya yabi masu ilimi kuma ya yi nuni da cewa su kadai ne suke tsoronsa, sai dai wannan ilimi da zai kashe a bisa hakika shi ne ilimi a wurin Allah, ba abin da yake shi ne ilimi a wurin sauran mutane ba.
Kuskuren da mutane suke yi sai su ga wani wanda suke ce masa malami yana munanan ayyuka, ba ya tsoron Allah, sai su ce wannan malami ba ya tsoron Allah, alhalin wannan ba malami ba ne a wurin Allah, shi dai kawai wani mutum ne da ya san wasu abubuwa na shari'ar addini, sannan sai ya dauki kayan malamai ya sanya, sannan mutane suka yi imani da shi a matsayin malami, amma a wurin Allah ba malami ba ne.
Imam Ali yana siffanta ilimi a cikin Nahajul balaga daga cikin maganarsa da ya yi wa Kumail dan Ziyad an'Nakha'i. Kumail ya ce: Imam Ali (a.s) ya riki hannuna, sai ya fito da ni zuwa makabarta, yayin da ya kai sahara sai ya yi lumfashi mai tsawo sannan sai ya ce:
"Ya kai Kumail dan Ziyad, Hakika wannan zukata jaka ce, wacce ta fi su ita ce mafi kiyayewa, to ka kiyaye abin da nake gaya maka: mutane uku ne: Masani na Allah, da mai neman sani mai tsira, da kuma yuyar gayya masu bin duk wani mai kira, suna masu karkata tare da kowace iska, ba su haskaka da hasken ilimi ba, kuma ba su karkata zuwa ga wata madafa mai aminci ba".
Ya Kumail dan Ziyad, sanin ilimi addini ne da ake yi, da shi ne mutum yake samun biyayya a rayuwarsa, da kyawun taraswa bayan mutuwarsa, ilimi mai hukunci ne, dukiya kuwa abin hukuntawa.
Ya kai Kumail dan Ziyad, masu taskace dukiya sun mutum alhalin suna raye, malamai kuwa masu wanzuwa ne matukar zamani ya wanzu: Idanuwansu suna rasa -bacci- misalansu suna cikin zukata.
Lallai hakika a nan akwai tarin ilimi mai yawa -ya nuna kirjinsa- da ma na samu masu daukarsa! Sai da na samu masu saurin fahimta amma ba abin amincewa ba gareshi, wadanda suke amfani da addini a matsayin tsanin samun duniya, suna masu danne bayin Allah da ni'imarsa, da kuma danni masoyansa da hujjojinsa, ko kuma -ban samu wani wanda zan ba wa wannan ilimi ba sai- mai karkata zuwa ga rikon gaskiya amma ba shi da basira a tare da shi, shakku yana shiga zuciyarsa da zaran wata shubuha ta zo masa.
Ku sani babu wannan babu wancan! Ko kuma -ban samu wani wanda zan ba wa wannan ilimi ba sai- mai zari da jin dadi, mai saukin ja ga sha'awa, ko kuma -ban samu wani wanda zan ba wa wannan ilimi ba sai- mai ruduwa da tarin -dukiya- da boyewa, wadanda babu ruwansu da wani addini, abin da suka fi kusanci da shi su ne dabbobin kiwo! da haka ne sai ilimi yake mutuwa da mutuwar masu rike da shi.
Ya ubangiji haka ne! Babu wani lokaci da duniya zata zamanto babu mai tsayuwa da hujjar Allah, Imma dai zahiri mashahuri, ko mai jin tsoro mai boyuwa, domin kada hujjar Allah da ayoyinsa su baci.
Ya girman wancan -ina shi- ina wadancan? Wadancan wallahi! Su ne suka fi kowa karancin adadi, da girman daraja, da su ne Allah yake kiyaye dalilansa da ayoyinsa, har sai sun mika ta ga tsararrakinsu, su kuma kafa ta a cikin zukatan makamantansu, ilimi ya zo musu a cikin hakikanin basira, suka kuma kusanci ruhin yakini, suka tausasa abin da masu shekewa suka tsaurara shi, suka samu nutsuwa da abin da jahilai suka samu dimauta da shi, kuma suka sahibanci duniya da jikinsu, rayukansu suna rataye da mahalli mafi daukaka, wadannan su ne halifofin Allah a cikin duniyarsa, masu kira zuwa ga addininsa, kauna dai kauna zuwa ga ganinsu!. -sannan sai imam Ali (a.s) ya ce masa juya (tafi) idan ka so-. Nahajul-balaga; Hikima: 139.
Idan mun duba zamu ga wannan magana ta imam Ali (a.s) tana da ma'anoni masu darja da kima, da farko fadin Kumail dan Ziyad an'Nakha'i cewa; "Imam Ali (a.s) ya riki hannuna, sai ya fito da ni zuwa makabarta, yayin da ya kai sahara sai ya yi lumfashi mai tsawo sannan sai ya ce". Zamu ga Imam Ali (a.s) ya yi nuni da daya daga cikin hanyoyin tarbiyya ga dalibi, yayin da ya kama hannun dalibinsa domin ya nuna masa wani abu mai kima da daraja.
Sannan kuma daukar sa da ya yi zuwa sahara da wurin da yake mai sukuni da shiru kamar makabarta shi ma wata hanya ce mai amfani wurin tarbiyyar dalibi domin gaya masa wani abu muhimmi domin wannan yakan sanya shi tuna abin da aka gaya masa, da zauna masa a zuciya.
Bayan samun wannan yanayi mai kyau domin isar da sako muhimmi sai Imam Ali (a.s) ya fara da cewa: "Ya kai Kumail dan Ziyad, Hakika wannan zukata jaka ce, wacce ta fi su ita ce mafi kiyayewa, to ka kiyaye abin da nake gaya maka". Wannan ma wata hanya ce mai girma a matsayin gabatarwa domin shirya dalibi ya karbi magana mai muhimmanci, sai ya fara da nuna masa nau'in zukata, domin ya kiyaye me za a gaya masa.
Sannan sai Imam Ali (a.s) ya fara da cewa: " mutane uku ne: Masani na Allah, da mai neman sani mai tsira, da kuma yuyar gayya masu bin duk wani mai kira, suna masu karkata tare da kowace iska, ba su haskaka da hasken ilimi ba, kuma ba su karkata zuwa ga wata madafa mai aminci ba".
A nan ne fifikon ilimi da muhimmancinsa yake bayyana a fili, domin mutane guda uku, ko dai ya kasance mai ilimi masani da ubangijinsa, ko ya kasance mai neman sani, ko kuma ya kasance halakakke, wanda ba shi da wani haske, kuma duk inda ya ji wani kira sai ya bi ba tare da sanin gaskiya ko karyar wannan kiran ba, irin wadannan su ne wadanda ba su da wata madafa mai kyau.
Sannan sai Imam Ali (a.s) ya ce: Ya Kumail dan Ziyad, sanin ilimi addini ne da ake yi, da shi ne mutum yake samun biyayya a rayuwarsa, da kyawun taraswa bayan mutuwarsa, ilimi mai hukunci ne, dukiya kuwa abin hukuntawa.
A nan ma wata kimar ilimi ta sake bayyana a fili ta yadda zamu ga na farko shi kansa ilimi addini ne, kuma duk wanda ka saurara ka karba daga gareshi to ka karbi addini daga gareshi ne, yana iya kasncewa na gari ko waninsa. Sannan kuma idan babu ilimi babu biyayya, don haka wanda bai san Allah ba, kuma ya yi da'awar yana biyayya gareshi ya yaudari kansa, sau da yawa irin mutanen da suka jahilci Allah idan sun tashi domin bauta masa sai su sawwala wani gunki a kwakwalwarsu kamar yadda wani yake gaya mini sai ya ga kamar wani zaki ne babba a gabansa yake bauta wa, ko wani sarki a kan karagar mulki. Irin wadannan mutane da suka jahilci Allah bas u da bambanci da Abujahal, sai bambancin cewa shi yana da gunki na fili da yake bautawa, su kuwa suna da gunki na kwakwalwarsu da suke bautawa.
Don haka ne zamu ga Imam Ali (a.s) bayan ya nuna cewa da ilimi ne ake samun biyayya sai kuma ya nuna cewa babu wani sakamako da ake samu sai da ilimi da fadinsa "da kyawun taraswa bayan mutuwarsa" wato bayan mutuwar bawa.
Sannan kuma sai ya yi nuni da wani abu muhimmi na cewar ilimi shi ne gaba da komai har dukiya, ita dukiya it ace ya kamata a sarrfa ta yadda aka so, amma ilimi shi ne hasken da yake nuni da yadda za a sarrfa ta, don haka mutane suna iko kan dukiya, shi kuma ilimi shi ne yake da iko a kan mutane sai Imam (a.s) ya yi nuni da hakan a fadinsa: "ilimi mai hukunci ne, dukiya kuwa abin hukuntawa".
Sannan Imam Ali (a.s) ya ce: "Ya kai Kumail dan Ziyad, masu taskace dukiya sun mutu alhalin suna raye, malamai kuwa masu wanzuwa ne matukar zamani ya wanzu: Idanuwansu suna rasa -bacci- misalansu suna cikin zukata".
A nan zamu ga ya sake nuna cewa dukiya da ilimi duk abubuwa ne da ake taskacewa, sai dai mai taskace dukiya ya bambanta da mai taskace ilimi, domin shi mai taskace dukiya ya halaka, kuma shi matacce ne tun kafin ya mutu, amma mai taskace ilimi yana rayuwa ne har abada, koda kuwa ya mutu a zahiri to bai mutu ba.
Amma su waye masu ilimi sai mai daraja ya yi nuni da cewa suna rasa bacci da dare, wadannan abubuwan da sukan hana su bacci suna da yawa, sun hada da duba cikin ilimi, da munajati da Allah, da tausayin al'umma.
Sannan ana iya fassara shi da samuwarsu ta narke cikin zatin Allah (s.w.t) ta yadda ba sa ganin kawukansu sai dai ubangijinsu, don haka ne suke muhimmantar da lamurran Allah da bayinsa a kan nasu, kamar yadda zamu ga suna kwana suna yi al'ummar Allah da bayinsa addu'a kamar yadda sayyida Zahara da muke juyayin ranar wafatinta da shahadarta a yau ta shahara da wannan, ta kasance tana kashe dare gaba daya tana ibada tana yi wa al'umma da makota addu'a, danta Imam Hasan (a.s) yana ibada tare da ita dukkan dare alhalin yana kasa da shekaru tara, yana tambayarta ya baba! Na ga ina ibada gaba dayan dare kina yi wa muminai addu'a amma ban ji ko sau daya kin yi wa kanki ba? Sai ta ce: "Ya kai dana, na waje tukun sannan gida"!. Ko kuma ana iya fassara shi da "makoci tukun sannan gida"!. (Ilalus Shara'i: 1; 181).
Sannan Imam (a.s) ya yi nuni da cewa misalansu a zukata suke, domin ya nuna cewa masu wannan siffofi suna da ilimin sanin Allah ba kawai a kwakwalensu da tunaninsu ba, wadannan masana Allah ne wadanda suke da ilimi cikakke da shi da zukatansu. Su ba da ilimi na tunani kawai suka san ubangijinsu ba, su sun san Allah madaukaki da zukatansu, ta yadda babu wani abu da suke fuskanta da zukatasu sai shi. Imam Ali (a.s) yana cewa: "Ban taba ganin wani abu sai na ga Allah a cikinsa ko a farkonsa ko tare da shi", yana cewa: "Ban taba bautawa ubangijin da ban gan shi ba". Al'aka'idul islamiyya: Markazul Mustapah: j 2, s; 311).
Wannan yana nuna mana ilimin badini wanda aka fi sani da cewa ilimi ne na kashafi da yake da shi, wannan ilimin ba a kwakwalwa yake ba, ilimi ne da yake a zuciya. Don haka ne Imam (a.s) ya nuna cewa sai da ya ga ubangijinsa da wannan ilimi na zuciya, sannan sai ya bauta masa.
A nan ne zamu ga bambanci tsakanin ilimi na mariskai, da kuma na kwakwalwa, da na zuciya da martabobin da suke tsakaninsu masu nisa. Kamar dai bambancin mutumin da ya ji labarin wuta da siffofinta, da wanda kuma ya ga wuta da yadda take kona abubuwa, da wanda ya shiga wuta ya dandani zafinta ne.
Sannan sai Imam Ali (a.s) ya fadi cewa; "Lallai hakika a nan akwai tarin ilimi mai yawa -ya nuna kirjinsa- da ma na samu masu daukarsa! Sai da na samu masu saurin fahimta amma ba abin amincewa ba gareshi, wadanda suke amfani da addini a matsayin tsanin samun duniya, suna masu danne bayin Allah da ni'imarsa, da kuma danne masoyansa da hujjojinsa, ko kuma -ban samu wani wanda zan ba wa wannan ilimi ba sai- mai karkata zuwa ga rikon gaskiya amma ba shi da basira a tare da shi, shakku yana shiga zuciyarsa da zaran wata shubuha ta zo masa".
A nan zamu ga Imam Ali (a.s) yana nuna kirjinsa da cewa akwai ilimi mai tarin yawa, amma al'ummar ba zata iya daukarsa ba, sannan ya kawo dalilan haka:
Na farko su ne mutanen da zasu iya fahimta amma idan suka sani zasu yi amfani da shi wurin tara duniya da danne bayin Allah da fatawowin son rai domin su samu wani abin duniya gun sarakuna da masu mulki, wadannan su ne masu sayar da ayoyin Allah da kankanin kudi na rayuwar duniya.
Sai na biyu; su ne mutanen da suke da ikhlasi amma ba su da wayewa da basira saboda karancin hankalinsu, suna iya samun ilimin amma ba ya canja yadda suke ganin rayuwar duniya da lahira, sannan ba sa iya wayewa. Don haka ne ko yaya shubuha da abubuwa masu rikitarwa suka zo sai su dabarbarce.
A nan ne abin da muka rubuta a wata makala kan cewa al'umma tana da zababbu da kuam bita-zuwai, sannan muka nuna cewa ilimi ba ya sanya mutum cikin zababbu sai idan ya haskaka tunaninsa da zuciyarsa. Matukar ba haka ba, to ko ya shekara 50 yana karatu zai kasance yana tunani kamar yadda wanda ya rayu a titi yake tunani, wannan lamarin yana daga cikin abin da aka jarrabe mu da shi a cikin makarantun ilimin addini, sai ka ga dalibi ya yi karatu shekaru 16 amma ba shi da tunani kuma wannan ilimin bai canja mahangarsa kan rayuwa da addini, da sanin Allah ba.
Don haka ne sai mu samu wasu ba su halarci makaranta ba, amma suna da wayewa da ita tantance mai kyau, wasu kuwa sun halarta amma ba su da wannan hasken. Wannan babu bambanci a makarantun addini ne ko kuwa a Jami'o'i, sau da yawa kakan samu farfesa amma ba ya buda tunaninsa. Kakan samu farfesa a ilimin lissafi (mathematic) mantik (Logic) amma duk wannan hankalin da yake da shi a ilmance idan ya zo al'ummarsa sai ka same shi cikin masu bautar shanu!.
Sannan sai Imam Ali (a.s) ya yin nuni da cewa: "Ku sani babu wannan babu wancan! Ko kuma -ban samu wani wanda zan ba wa wannan ilimi ba sai- mai zari da jin dadi, mai saukin ja ga sha'awa, ko kuma -ban samu wani wanda zan ba wa wannan ilimi ba sai- mai ruduwa da tarin -dukiya- da boyewa, wadanda babu ruwansu da wani addini, abin da suka fi kusanci da shi su ne dabbobin kiwo! da haka ne sai ilimi yake mutuwa da mutuwar masu rike da shi".
Imam Ali (a.s) ya sake ci gaba da lissafa mutanen da ya samu wadanda ba zai yiwu a ba su ilimi ba, sai ya ci gaba da lissafa na uku da cewa; shi ne mutum mai zari da jin dadi, mai saukin ja ga sha'awa, wanda ba shi da iyaka a sha'awarsa, ba shi da kaidi ga jarin duniya da neman kece raini da jin dadi da holewa, mai katon ciki da neman mata domin kawar da sha'awarsa.
Sai kuma na hudunsu wanda yake mai ruduwa da tarin -dukiya- da boyewa, burinsa ya ga bankunansa sun cika, ta yadda zai samu matakin yanke talauci, kuma duk abin da zai yi na son rai domin ya samu duniya zai yi. Irin wadannan mutanen sau da yawa sukan samu sirrin ayoyin Allah sai su mayar da su abin sihiri.
Don haka sai Imam Ali (a.s) ya siffanta wadannan mutanen da cewa su babu ruwansu da wani addini, don haka sun fi kusa dabbobi a siffofinsu fiye da mutane.
Sai Imam (a.s) ya yi nuni da cewar da haka ne ilimi yake mutuwa, domin idan malami bai samu wanda zai ba wa wannan amana ba, bai halatta ya sanya ta wuri lalatacce ba kamar gun irin wadannan mtuane guda hudu, don haka sai malami ya mutu, sai ilimin da yake tare da shi ya mutu.
Don haka ne sai Imam (a.s) ya koka zuwa ga ugangijinsa da cewa: Ya ubangiji haka ne! Babu wani lokaci da duniya zata zamanto babu mai tsayuwa da hujjar Allah, Imma dai zahiri mashahuri, ko mai jin tsoro mai boyuwa, domin kada hujjar Allah da ayoyinsa su baci".
Tun da Imam Ali (a.s) a karshen rayuwarsa bai samu wanda zai ba wa ilimi ba sakamakon cewa munafukai sun kashe dukkan sahabbansa masu ikhlasi da imani sahihi, ta yiwu wani ya tambaya cewa shin ilimi ya kare da rasuwarsa ke nan? To domin gudun kada wani ya yi wannan tunani sai Imam Ali (a.s) ya yi nuni da cewa bayansa a kowane zamani akwai wasiyyin annabi (a.s) da zai ci gaba da rike sakon Allah (s.w.t), imma dai wannan wasiyyin da muka fi sani da imami a zahiri yake, kamar shi Imam Ali (a.s) da Hasan da Husain da kuma sauran imamai tara bayan Husain (a.s), imma dai boyayye kamar Imam Mahadi (a.s) imami na goma sha biyu kuma karshen wasiyyan annabi (s.a.w) wanda ya buya da umarnin Allah da ilhamar ubangiji (s.w.t) saboda tsoron kisa tun sama da shekaru dubu daya ke nan yana mai jiran umarnin Allah da bayyana.
Sannan sai Imam Ali (a.s) ya yin nuni da karancin adadinsu yana girmama karancin adadin yana mai cewa: "Ya girman wancan lamarin! -ina shi- ina wadancan? Wadancan wallahi! Su ne suka fi kowa karancin adadi", Imam Ali (a.s) yana mai rantsuwa da Allah domin nuni zuwa ga cewa adadin yana da matukar karanci. Idan mun duba dukkan littattafan musulmi sunna da shi'a duka sun yi ittifaki da cewa manzon Allah (s.a.w) ya fadi cewa su goma sha biyu ne kawai.
Sannan sai Imam Ali (a.s) ya ci gaba da nuni ga siffofinsa yana mai cewa: "da girman daraja, da su ne Allah yake kiyaye dalilansa da ayoyinsa, har sai sun mika ta ga tsararrakinsu, su kuma kafa ta a cikin zukatan makamantansu".
Wato bayan adadi mai karanci, sai kuma girman daraja, domin sun fi sauran annabawa daraja kamar yadda manzon Allah (s.a.w) ya yi nuni da su a fadinsa cewa: "Malaman al'ummata sun fi annabawan Banu Isra'il daraja". (Awa'ilul Makalat: Sheikh Mufid; s 178).
Sannan ya yi nuni da cewa da su ne Allah yake kare dukkan halitta, kamar yadda manzon Allah ya yi nuni da cewa matukar suna nan to lamarin al'umma yana nan kamar yadda yake a ruwayar Muslim da waninsa. Wasu ruwayoyin kuma sun yi nuni da cewa idan suka kare to babu duniya dole ta tashi, ko dole ne ta rushe gaba daya.
Sannan a fadinsa "har sai sun mika ta ga tsararrakinsu, su kuma kafa ta a cikin zukatan makamantansu". Yana nuna cewa duk sa'adda wani daga cikinsu ya zo yana kasancewa kamar magabacinsa ne, babu wani abu da yake jahilta a cikin duk wani ilimi, a tare da shi akwai dukkan abin da duniya take bukata babu ko tawaya daya. Imami tsaran imami ne kuma makamancinsa ne, don haka babu wani wanda zai zo sai wanda zai biye masa ya kasance kamarsa a komai babu wani bambanci.
Idan kuma muka duba su zamu ga suna da ilimi da ba su taba karatu gun wani ba, sai Imam (a.s) ya yi nuni da yadda suke samun ilimi cewa dukkan wasiyyin annabi (s.a.w) yana samun iliminsa imma daga koyarwar imamin da ya gabace shi, ko kuma ilhama daga Allah madaukaki, don haka sai yake cewa: "ilimi ya zo musu a cikin hakikanin basira, suka kuma kusanci ruhin yakini". Wannan hanyar samun ilimi babu wani wanda Allah ya hore wa ita hakikanin horewa da ma'anarta ta hakika sai su. Don haka ne ya zama dole ga sauran mutane su nuna mana dalilinsu, da inda suka samo, amma su manzon Allah (s.a.w) ya riga ya yi wasiyya da su, don haka su suna da lasisi daga Allah kai tsaye, kuma jefa musu ilimi a zukatansu daga Allah yana tare da hasken littafinsa da ba ya saba masa faufau.
Sannan Imam (a.s) ya yi nuni da rashin kuskure a iliminsu sabanin ilimin sauran mutane sai ya fadi siffofinsa yana mai cewa: "suka tausasa abin da masu shekewa suka tsaurara shi, suka samu nutsuwa da abin da jahilai suka samu dimauta da shi, kuma suka sahibanci duniya da jikinsu rayukansu suna rataye da mahalli mafi daukaka, wadannan su ne halifofin Allah a cikin duniyarsa, masu kira zuwa ga addininsa, kauna dai kauna zuwa ga ganinsu!.
A nan zamu ga Imam (a.s) yana nuni da nau'i biyu na ilimi; ilimin da yake babu kuskure a cikinsa wanda yake daga Allah da manzonsa zuwa ga wasiyyansa, da kuma ilimin masu neman duniya da shi, da wadanda suka kaucewa gaskiya suna sane ko bisa jahilci.
Idan ilimi ya kauce wa gaskiya, sai ya tsananta wurin da aka tausasa, ko ya yi akasin hakan ya tausasa wurin da aka tsananta, sai ya takaita ko ya wuce gona da iri. Ya kuma sake nuni da dimautar jahilai da ake kira malamai da abin da su wasiyyan Annabi (a.s) suka nutsu da shi, da kuma akasin hakan, wanda ya yi bincike mai zurfi zai ga yadda irin wadancan mutane suke haramta halal saboda suna samun dimautuwa saboda ita, suka kuma halatta haramun saboda suna samun nutsuwa da ita.
Sannan sai ya yi nuni da cewa iliminsu yana da alaka da Allah madaukaki da tsoronsa, kuma ilimi ne na hakkul yakin, kamar yadda a baya kafin wadannan sadarori ya yi nuni da ilmul yakin, da na ainul yakin. Don haka sai Ali (a.s) ya ce: "kuma suka sahibanci duniya da jikinsu rayukansu suna rataye da mahalli mafi daukaka, wadannan su ne halifofin Allah a cikin duniyarsa, masu kira zuwa ga addininsa, kauna dai kauna zuwa ga ganin su".
Su suna rayuwa da ruhinsu a lahira, amma jikinsu yana wannan duniya ne, alakarsu da duniya kamar 'ya'yan itace ne da suka nuna ta yadda ko yaya iska ta kada su sai su fado su bar jikin uwa. Haka nan alakar jikinsu da rayukansu ta ke, amma lahira kuwa rayuka suna manne like da ita, ta yadda komai girgiza ba zasu rabu da ita ba.
Wannan su ne siffofin halifofin Allah a wannan duniyar, kuma su ne suka cancanci a bi su. Domin rashin damfaruwarsu da duniya yana nuna babu wata maslaha da suke nema a cikinta ga kawukansu balle su yi zalunci. Sannan iliminsu da zahiri da kuma badinin samammu yana ba su damar sanin yadda zasu shimfida adalci a tsakaninsu. Sannan saninsu da Allah madaukaki yana ba su yakini da babu shakku a cikinsa, don haka wadannan su ne suka fi cancantar kasancewa masu wakiltar Allah a kan bayinsa.
Daga karshe bayan wadannan kalamai masu daraja sai imam (a.s) ya juya yana gaya wa Kumail cewa yana iya tafiya kamar yadda muka kawo a sama cewa: "-sannan sai imam Ali (a.s) ya ce masa juya (tafi) idan ka so-".
Sannan Imam Ali (a.s) yana tabbatar mana da wannan siffofi nasu masu daraja yayin da yake cewa: "Ban taba kokwanton gaskiya ba tun da na gan ta". Nahajul-balaga; Hikima: 174. Wannan siffa ce ta wanda al'umma ya kamata su bi, domin duk wanda yake da yakini kan lamarinsa shi ne ya fi cancanta da biyayya ba wanda yake kan kokwanto ba.
Wadannan hikimomi masu daraja ba don Imam (a.s) ya furta su an nakalto su daga gareshi ba, da duniya ta rena masa, wannan yana nuna mana girmansa (a.s), sannan yana nuna mana gaskiyar maganarsa yayin da yake cewa: "Mutum boyayye ne karkashin harshensa". Hikima: 140, domin da maganarsa da zancensa ake sanin kimarsa.
Sannan a nan muna iya fahimtar cewa kowane mutum yana da matsayinsa domin irin wadannan kalamai masu kima da daraja suna nuna mana wani sirri a wata marhalar rayuwar Imam Ali (a.s), wanda ba kowane zai iya gaya wa wannan ba, idan mutum ya san kimarsa da darajarsa, da iyakacin matsayinsa ya rabauta. Imam Ali (a.s) yana cewa: "Mutumin da bai san kimarsa ba, ya halaka". Hikima: 141.
Sannan idan akwai wata magana mai daraja da kima to bai kamata ba a yi shiru ba a isar da ita ba, domin akwai wadanda suka dace da ita, don haka ya hau kan malami ya bayyanar da ilimi yayin bukatar hakan, kamar yadda yake wajibi kan jahili ya yi shiru. Imam Ali (a.s) ya ce: "Babu alheri cikin yin shiru ga hukunci, kamar yadda babu alheri cikin yin magana da jahilci". Hikima: 172.
Ilimin Gaibi
Sannan akwai wani bahasi da ake yi game da ilimin gaibi wanda yake cikin bahasosin da aka tayar da jijiyar wuya a kansu. Sai dai yana da kyau mu san me ake nufi da gaibi domin amsar ma'anar sanin gaibi ta fito a fili. A cikin littattafai ya zo cewa; Gaibi shi ne duk wani abu da ya boya ga mutum. Kitabul Ain: Khalil Farahidi; 4/454, Lisanul Arab: 1/654, Majma'ul Bahrain: 2/134.
Don haka muna ganin gaibi shi ne abin da ya boyu daga gabobinmu da muke riskar abubuwa da su, wadanda muke kiran su da "Mariskai", wadannan mariskar sun hada da ji, da gani, da lasa, da shafa, da shaka. Sai dai a cikin Kur'ani mai girma an yi amfani da kalmar Gaibi ga dukkan abin da yake ba mahalarci ba ne. kamar yadda ya zo a cikin Surar An'am: 73.
Da kuma fadinsa: "Masanin gaibi da sarari, kuma shi ne mai hikima mai masaniya". Kamar yadda ya zo a surar Tauba: 94, da 105.
Domin lamarin mas'alar gaibi ya bayyana garemu sosai ya zama wajibi mu yi duba zuwa ga kashe-kashen gaibi; idan mun duba zamu ga gaibi ya kasu gida biyu: Sakakken gaibi, da Gaibin dangantaka. Sakakken gaibi; Shi ne gaibin da yake sake ba kaidi, wanda yake babu wani wanda ya san shi sai mahaliccin duka, kuma babu wata hanya da za a iya saninsa, irin wannan gaibin ya hada da sanin zatin Allah madaukaki, da sanin hakikanin siffofinsa da sauransu. Amma Gaibin danganta; Shi gaibi ne wanda saninsa ya danganta da matsayin ilimin mai saninsa da kusancinsa da mabubbugar gaibi duka wato; Allah mahalicci. Yana buda wa bayinsa saninsa daidai gwargwadon yardarsa da su, da karfin dauke sakonsa da suke da shi, da kuma zamani ko wurin da zai ba su wannan sanin na gaibi, kuma ya yi nuni da hakan a cikin surar Jinni: 26-28.
Da wannan ne wani abin yake zama gaibi dangane da wani mutum, amma ba gaibi ba ne dangane da wani, sai aka ambace shi Gaibin dangantaka. Sai wani abu ya kasance gaibi ga mariskai amma bai gaibi ba ne ga hankali; mariskai ba sa iya riskar dokoki gama-gari, sai dai suna riskar daidaikun halittun da ake iya riskar su a fili ta hanyoyi mabambanta kamar ji, da gani, da shaka, da tabawa. Haka nan ma abin da yake cikin gida ba gaibi ba ne ga wanda yake cikinsu, amma gaibi ne ga wanda yake wajen gidan. Sai wani abu ya kasance gaibi gun mutane amma ba gaibi ba ne gun wasu dabbobi, ko aljanu, ko mala'iku; musamman zamu ga akwai wasu dabbobi da suke iya gani ko jin wasu sauti da dan Adam ba ya iyawa. Haka nan wani abin yake gaibi a wurin dukkan halittun Allah, amma babu wani abu da yake gaibi a wurin Allah madaukaki, domin shi ne ainihin ilimi.
Shin Akwai Wanda Ya San Gaibi Ban Da Allah?
Idan muka duba ayoyin Kur'ani mai girma zamu ga suna nuna mana sanin gaibi da ma abin da yake sarari duk na Allah ne; ayoyi kamar: Naml: 65, da An'am: 59. Sai dai idan mun lura zamu ga sanin gaibi da ma'anar da ya zo a wannan ayoyin bai kore samuwar saninsa ga wasu bayi da Allah ya zaba ba, don haka ne zamu iya fahimtar ma'anar babu wanda ya san gaibi sai Allah tana nufin asalin saninsa, da cewa; babu wanda ya san gaibi da kansa sai ubangiji madaukaki. Amma wanin ubangiji idan ya san gaibi to da sanarwar ubangiji ne ba da kansa ba, don haka saninsa da gaibi yana bin sanarwar da Allah ya yi masa ne, da ba shi kyautar wannan ilimi da Ubangiji madaukaki ya yi, don haka ne zamu ga ayar nan ta surar Jinn: 26-28, da sauran ayoyi kamar: Aali Imran: 179, 44, da Yusuf: 102, duk suna nuni da haka.
A cikin Kur'ani mai girma ya zo da bayanin annabawa (a.s) da Allah madaukaki ya sanar da su gaibi, idan mun koma wa ayoyi kamar haka: Yusuf: 41, da Aali Imran: 49, zamu ga yadda annabawa suka san gaibi kuma suka gaya wa mutane shi. Kamar yadda zamu samu labarun fadin abubuwan da zasu wakana da imam Ali (a.s) da sauran imamai (a.s) suka yi, kamar yadda ya zo a cikin Nahajul Balaga: 186, An'am: 75, da Kafi: 1/257. Sai dai sun sanar da mutane cewa wannan duk daga koyarwar manzon Allah (s.a.w) ce da ya sanar da su, wato ba sun sani ba ne su a kashin kansu, sai dai sanarwa ce daga Allah da manzonsa.
Cibiyar Al'adun Musulunci
www.hikima.org
hfazah@yahoo.com
Hafiz Muhammad Sa'id
Saturday, March 05, 2011