Sakon Ali a.s ga Malik Ashtar
Wannan shi ne Sakon Imam Ali (a.s) zuwa ga Malik Ashtar kamar yadda ya zo a Nahjul-balaga: Wasika / 53. Yana daga mafi tsayin sako da aka rubuta kuma wanda ya fi kowanne tattaro kyawawan sakonni.
Da sunan Allah mai Rahama mai Jin kai
Wannan shi ne abin da bawan Allah sarkin muminai Ali (a.s) ya umarci Malik dan al'Haris al'Ashtar da shi a sakonsa zuwa gareshi yayin da ya sanya shi shugaban Masar: Hada harajinta, da yakar makiyanta, da gyara mutanenta, da raya kasarta.
Ya umarce shi da jin tsoron Allah da zabar biyayyarsa, da biyayya ga umarninsa a littafinsa: daga farillansa da sunnoninsa wacce babu wanda zai rabauta sai da biyayyarta, kuma babu wanda zai tabe sai da musanta ta da tozarta ta. Kuma (ya umarce shi da) taimakon Allah matsarkaki da zuciyarsa da hannunsa da harshensa, domin shi Ubangiji (sunansa ya girmama) ya lamunce wa wanda ya taimake shi da taimakonsa, da daukaka wanda ya daukaka shi.
Kuma ya umarce shi da ya kame kansa gun sha'awowi, ya rike kansa gun burace-burace, domin rai mai umarni ce da mummuna sai dai wanda Allah ya yi wa rahama.
Sannan ka sani ya kai Malik ni na aika ka zuwa gari ne da ya kasance adalci da zalunci sun gudana a karkashin wasu dauloli kafin zuwanka, kuma mutane zasu duba lamarinka kamar yadda kai ma kake duba lamarin masu mulki kafin kai, kuma zasu fadi abin da kake fada kan wadancan a kanka.
Kuma kawai ana gane salihai ne da abin da Allah yake gudanarwa garesu ta harsunan bayinsa, don haka tanadin aiki na gari ya kasance shi ne mafi soyuwar tanadi gunka.
Ka mallaki son ranka, ka hana kanka abin da bai halatta gareka ba, ka sani hana rai shi ne yi mata adalci cikin abin da ta so da wanda ta ki.
Ka sanya wa zuciyarka tausayin al'umma da kauna da tausayawa garesu, kada ka zama wani zaki mai cutarwa garesu da ake farautar cinsu, domin ka sani su (jama'a) iri biyu ne, ko dai dan'uwanka a addini, ko kuma tsaranka a halitta, suna samun yin kuskure, kuma cututtuka suna samun su, kuma ana ganin ayyukansu na gangan da na kuskure, sai ka ba su afuwarka da yafewarka kamar yadda (kai ma) kake so Allah ya ba ka afuwarsa da yafewarsa, ka sani kai kana samansu, mai jagorancin lamari duka (shugaban kasa) yana samanka, kuma Allah yana saman wanda yake jagoranka. Kuma tabbas ya wadatar da kai lamarinsu, ya kuma jarrabe ka da su (don ya ga yaya zaka yi adalci ga kanka da kawukansu).
Kada ka sanya kanka mai gaba da yakar Allah, domin babu wani taimako gareka daga azabarsa, kuma ba ka da wata wadatuwa daga afuwarsa da rahamarsa, kada kuma ka yi wata nadama kan wata afuwa, kada ka yi takama da azabtarwa (ga wasu mutane), kuma kada ka yi gaggawar zartar da wani abu (na ukuba) da ka samu mafita (hanyar yafewa) gareshi, kuma kada ka ce ni ma abin umarta ne sai in bi, wannan yana sanya barna a cikin zuciya, kuma shisshigi ne a addini, kuma kusantuwa ne zuwa ga wani (mutum ba Allah ba)!.
Idan wani abu na takama da jin kai (jin isa) ya sosu a zuciyarka saboda mulkin da kake kansa, to sai ka duba girman mulkin Allah a kanka, da ikonsa kanka da abin da kai ba zaka iya masa ba ga kanka, to wannan zai kwantar da daga kanka, kuma ya kange maka wanda yake iza (zuga) ka, kuma ya dawo maka da abin da ya ragu na hankalinka.
Ka yi hattara da daidaita kanka da Allah a cikin girmansa, da kamantuwa da shi a cikin jabarutinsa, hakika Allah yana kaskantar da dukkan jabberi, yana wulakanta dukkan mai takama. Ka yi wa Allah adalci, kuma ka yi wa mutane adalci ga kanka da kuma kebantattun makusantanka, da dukkan wanda kake kauna daga jama'arka, domin idan ba ka yi haka ba, to ka yi zalunci, wanda kuwa ya yi zalunci ga bayin Allah, to Allah zai kasance abokin husumarsa don kariya ga bayinsa, wanda kuwa Allah ya yi husuma da shi to zai kaskantar da madogararsa, kuma shi ya kasance ke nan mai yaki da Allah har sai ya bari ya tuba.
Kuma babu wani abu da ya fi gaggawar canza ni'imar Allah da gaggauta azabarsa fiye da tsayar da zalunci, domin Allah yana jin addu'ar wadanda aka danne, kuma shi mai yin tarko ne (a madakata) ga azzalumai.
Abin da ya fi soyuwa gunka ya kasance shi ne abin da yake mafi tsakaituwa cikin gaskiya (ba shisshigi babu kuma takaitawa), kuma ya kasance shi ne ya fi zama adalci, mafi soyuwa gun al'ummar kasa. (Ka sani) cewa fushin al'umma yana taushe (ya danne) yardar manyan gari, (ta yadda ko manyan gari sun yarda da kai, to ya zama a banza matukar al'umma tana fushi da kai), amma kuma fushin manyan gari to ana shafe shi da yardar al'umma (wato ko manyan gari suna fushi da kai, amma al'umma tana yarda da kai, to wannan shi ne abu mai amfanarka).
Kuma ka sani babu wani mutum a cikin al'umma da ya fi zama (mai dora) nauyi a kan jagora yayin yalwa, kuma ya fi karancin taimaka masa yayin bala'i, ya fi kowa kin adalci, ya fi kowa nacewa da roko, ya fi kowa karancin godiya yayin da aka ba shi kyauta, ya fi kowa karancin bayar da uzuri yayin da aka hana shi, ya fi kowa gajen hakuri yayin da bala'o'in zamani suka fado, fiye da manyan kasa (manyan gari).
(Ka sani) babu wata madogarar addini da hadin kan musulmi, wanda shi ne zaka yi tanadinsa don kariya daga makiya fiye da mutanen gari cikin al'umma, don haka sauraronka ya kasance garesu, karkatarka ta kasance tare da su.
Mafi nesa da kai daga al'ummarka kuma mafi muninsu a gunka, su kasance su ne wadanda suka fi kowa son tono aibin mutane, ka sani mutane suna da aibobi, shugaba shi ne ya fi cancanta ya rufe su (aibobin).
Kuma kada ka nemi tono abin da ya buya daga gareka, kai aikinka shi ne ka gyara abin da ya bayyana kawai gareka, kuma Allah shi ne mai hukunci kan abin da ya boye maka. Ka rufa asirin (mutane) iyakacin yadda zaka iya, sai Allah ya rufa naka asirin da kake so ka boye shi ga al'ummarka.
Ka kore wa mutane dukkan wani kulli na gaba, ka yanke masu duk wani dalilin juya wa juna fuska, ka kau da kai daga dukkan abin da bai bayyana gareka ba, kuma kada ka gaggauta gaskata duk wani mai kawo maganar wasu, domin duk mai kawo maganar wasu maha'inci ne ko da kuwa ya shiga rigar masu nasiha.
Ka da ka shigar da marowaci cikin shawararka da zai hana ka yin alheri yana mai nuna maka (zaka) talauta, ko wani matosaraci da zai kawo maka rauni daga lamurranka, ko mai kwadayi da zai kawata maka zari (handuma da babakere) da danniya, ka sani rowa da tsoro da kwadayi dabi'u ne mabambanta, munana zato ga Allah shi ne asasinsu.
Lallai mafi munin waziranka su ne wadanda suka kasance wazirai ga ashararan jagorori da wadanda suka yi tarayya da su cikin sabon Allah kafinka! Kada ka bari su zama abokan sirrinka, ka sani su mataimakan masu sabo ne, 'yan'uwan azzalumai. Kuma zaka iya samun wasu mutanen da suka fi su wadanda suke da ra'ayoyi da matsayi kuma ba su da irin laifuffukansu da zunubansu daga wadanda ba su taimaki azzalumi a kan zaluncinsa ba, ko wani mai sabo a kan yin sabonsa ba.
Wadannan su ne suka fi karancin dora maka nauyin (bakin jini), kuma suka fi kyautata maka taimako, suka fi tausayawa gareka, suka fi karancin samun sabo da wani ba kai ba. To sai dauke su a matsayin na kusa da kai domin kebewarka da shiga taronka, sannan kada ya zama wanda ya fi kowa a gunka, shi ne wanda ya fi gaya maka gaskiya mai daci, ya fi karancin ba ka taimako kan abin da kake yi wanda Allah yake kin sa ga masoyansa, komai kuwa son da kake wa wannan (sabon).
Kuma ka damfaru da masu tsantseni (gudun haram), da gaskiya, sannan sai ka yi musu kashedi kan cewa kada su sake su zuga ka da kambama ka (da yabon da zasu kai ka inda ba ka kai ba), kuma kada su kuranta ka da wata barna da ba ka yi ta ba, domin yawaita kambamawa tana haifar da kwalisa, kuma tana nisantarwa daga izzar (daukaka).
Kuma kada mai kyautatawa da mai munanawa su kasance daya a gunka, domin wannan zai sanya tauyewa ga ma'abota kyautatawa a kyautatawarsu, da kuma ingiza masu munanawa a kan munanawarsu, sai dai ka dora wa kowannensu abin da ya dora wa kansa (mai kyautatawa ya ga sakamako mai kyau, mai munanawa ya ga munanawa).
Ka sani cewa babu wani abu da ya fi ye wa wani shugaba ga al'ummarsa fiye da kyautata zato (garesu), da saukakewarsa garesu nauyin da yake kansu na rayuwa, da barin tilastawarsa garesu kan abin da ba daga garesu yake ba, to ya kasance kana da wani lamari kan haka da zai kasance kana da kyakkyawan zato ga al'ummarka da shi, domin kyautata zato yana yanke maka surkukiya mai nisa, kuma wanda ya fi cancanta ka kyautata masa zato shi ne wanda jarabawarka ta kyautata gunsa (wanda ka jarraba shi ka ga yana da amana), kuma wanda ya fi cancanta da munana zato shi ne wanda jarabawarka ta munana gunsa (wanda ka jarraba shi ka ga yana da ha'inci).
Kuma kada ka rushe wata al'ada mai kyau da farkon al'umma suka yi aiki da ita, al'umma ta saba da ita, jama'a su samu gyaruwa saboda ita.
Kuma kada ka farar da wata al'ada da zata cutar da wani abu da ya gabata na al'adun farko, sai ya kasance ladan yana ga wanda ya farar da ita, zunubi yana kanka saboda ka rusa ta.
Ka yawaita tuntubar ilimin malamai, da zaman (tattaunawar) masu hikima domin tabbatar da abin da zai gyara lamarin kasarka, da tsayar da abin da ya tsayar da (gyaran) al'umma kafin zuwanka.
Ka sani jama'a hawa-hawa ne, ba yadda za a yi wasu su samu gyaruwa sai da wasunsu, kuma ba yadda za a yi wasu su wadatu daga wasunsu.
Daga cikinsu akwai rundunar Allah (jami'an tsaro), daga cikinsu akwai dabakar kasa (na mutane) da dabakar sama (na mutane), daga ciki akwai alkalan adalci (kotu), daga ciki kawai ma'aikatan adalci da tausayi da jin kai (masu kula da walwalar jama'a), daga ciki akwai ma'abota jiziya da haraji daga mutanen amana (wadanda ba musulmi ba) da musulmin mutane. Daga ciki akwai 'yan kasuwa da masu sana'o'i, daga cikin akwai dabakar kasa daga masu bukatu da miskinanci, kuma kowanne Allah ya fadi rabosa, ya sanya masa wani rabo nasa a littafinsa da sunnar annabinsa, wannan wani alkawari (sani da amana) ne da aka kiyaye shi a gun mu.
Runduna ('yan sanda) da izinin Allah su ne kariyar al'umma, adon jagorori, daukakar addini, hanyoyin samun aminci, kuma ba yadda za a yi al'umma ta daidaitu sai da su.
Sannan su kuma rundunoni (sojoji) ba yadda za a yi su samu tsayuwa sai da abin da Allah ya fitar musu na daga harajin (dukiyar kasa), da zasu karfafu da shi a kan yakar makiyansu, su dogara kansa cikin abin da zai gyara su, kuma ya dauke musu bukatunsu.
Sannan su kuma wadannan nau'i biyu ('yan sanda da sojoji) ba yadda za a yi su daidaitu sai da wani nau'i na uku na alkalai da ma'aikata da sakatarori, da (su alkalai) zasu yi hukunci da shi na al'amuran da suka shafi kulla (kasuwancinsu da yarjejeniyoyi), da abin da (su ma'aikata) zasu tara na amfani, da dogaro da za a yi da su (sakatarori) kan abubawan da suke kebantattu da na gaba dayan jama'a.
Su kuwa duka wadannan ba yadda za a yi lamarinsu ya daidaitu sai da masu sana'o'i na abin da suke taruwa kansa na kayan ciniki, da abin da suke kasuwanci a kasuwanninsu, kuma su dauke wa (sauran al'umma kamar ma'aikata da runduna) nauyin yin kasuwanci da kansu, da kasuwancin waninsu (wadanda ba 'yan kasuwa ba) ba zai kai nasu ba.
Sai kuwa dabaka ta kasa daga masu bukata da masakai wadanda suka cancanci yalwata musu da taimaka musu, kuma Allah yana da kason (da ya ba wa) kowa, kuma kowa yana da wani hakki kan shugaba daidai gwargwadon abin da zai daidaita lamarinsa.
Kuma shugaba ba zai iya fita daga hakikanin abin da Allah ya dora masa ba na wannan sai da himmantuwa da neman taimako da Allah, da dora wa kansa cewa lallai ne zai lizimci yin gaskiya, da dagewa a kanta cikin abin da yake mai sauki da mai nauyi.
Ka sanya jagora ga rundunarka (soja da dan sanda) wanda a ganinka ya fi kowannensu yin biyayya ga Allah da manzonsa da imamai (wasiyyan manzon Allah), wanda ya fi su tsarkin aljihu (ba ya tara haram), ya fi su hakuri (da juriya), wanda ba ya saurin fushi, yana yarda da uzuri, yana tausaya wa masu rauni, yana kuma nisantar masu karfi. Wanda neman fada (da shi) ba ya sanya shi hamasa, rauni kuwa ba ya sanya shi ya zauna (ya yi langwai).
Sannan ka rabu da ma'abota darajoji da 'yan gidaje na gari, da masu kyakkyawan rigo, sannan sai masu sadaukantaka da jarumtaka da baiwa da yafiya, wannan wani tattaro (siffofi) ne na karimci, kuma wata jama'a ce ta nagarta.
Sannan ka bibiyi lamurransu kamar irin yadda iyaye suke bibiyar lamarin 'ya'yansu, kada ka ga girman abin da ka karfafe su da shi a ranka , kuma kada ka raina wani tausayi da ka yi musu shi ko da kuwa ya karanta, domin wannan zai sanya su bayar da rangwame (yafiya) gareka, da kyautata maka zato.
Kada dogaro da yin manyan ayyuka ya sanya ka barin kananan lamurransu, domin dan karamin ludufinka yana da wani amfani da suke samu da shi, kuma shi babban lamari ba sa wadatuwa da shi (domibn ba ya wadatarwa ga barin karami). Kuma zababbun manyan rundunarka gunka su kasance su ne wadanda suka fi taimakon (su mutane), wanda kuma yake ba su daga arzikinsa (albashinsu) da abin da zai yalwace su kuma ya yalwaci wadanda suke bari (a gida) na iyalansu, domin hadafinsu ya zama hadafi daya a yakar makiya, ka sani tausaya musu yana sanya tausayinka a zukatansu.
Kuma mafi zaman sanyin idanuwan jagorori shi ne tsayar da adalci a gari (da kasa), da nuna kaunar al'umma, kuma soyayyarsu ba ta bayyana sai da amincin zukatansu, kuma nuna kaunarsu ba ta inganta sai da kiyayewarsu ga jagororinsu, da karanta nauyin da yake wuyansu (saukaka musu rayuwa), da barin neman jinkirta yankewar muddarsu (don gaggauta haduwa da su), to ka yalawata gurinsu, ka rika yabon su akai-akai, ka rika ambaton abin da wani babban abu (na gudummuwa) da wani daga cikinsu ya yi, ka sani yawan ambaton kyakkyawan ayyukansu yana zaburar da mai jarumtaka, yana kwadaitar da mai nuku-nuku (domin shi ma ya tashi ya yi kokari) in Allah ya so.
Sannan ka kyautata wa kowane mutum daga cikinsu abin da ya yi (na gudummuwa), kada ka dora kokarin wani mutum ga waninsa, kuma kada ka takaita shi kasa da gudummuwar da ya bayar, kuma kada girman wani mutum ya sanya ka girmama wani dan karamin abu da ya yi na gudummuwa, kuma kada kaskancin mutum ya sanya ka karanta wani abu (muhimmi) mai girma da ya yi.
Ka mayar da abin da ya gajiyar da kai na lamurra zuwa ga Allah da manzonsa, da abin da yake rikitar maka na lamurra. Hakika Allah madaukaki ya ce wa wasu mutane da ya so shiryar da su cewa: "Ya ku wadanda kuka yi imani, ku bi Allah ku bi Manzo da ma'abota jagoranci a cikinku, idan kuwa kuka yi jayayya cikin wani abu, to ku mayar da shi ga Allah da Manzo…", mayarwa zuwa ga Allah shi ne riko da abin da ya bayyanar a cikin littafinsa, mayarwa zuwa ga Manzo kuwa shi ne riko da sunnarsa hadaddiya (da aka hadu kanta) ba rababbiya (wacce aka yi sabani kanta) ba.
Sannan ka zabi mafificin al'ummarka a wurinka domin yin hukunci tsakanin mutane, wanda al'amura ba sa samun kunci da shi, jayayya ba ta sanya shi kaucewa, ba ya ci gaba da yin kuskure, ba ya kasa koma wa gaskiya idan ya gano ta, ransa ba ta hangen kwadayi, ba ya isuwa da mafi karancin fahimta har sai ya fahimta sosai. Kuma ya kasance wanda ya fi kowa tsayawa gun shubuha, ya fi kowa riko da hujjoji, mafi karancinsu kosawa (da gajiyawa) don yawan masu zuwa kara, mafi hakurinsu a kan gano (ainihin gaskiyar) lamurra, mafi karfin yankewarsu ga hukunci yayin da hukuncin (lamarin) ya bayyana. Kuma ya kasance wanda yabo (da kambama shi) ba ya wawaitar da shi (ya yi sabanin gaskiya), kuma rudi ba ya jawo hankalinsa, wadannan (mutanen irinsu) 'yan kadan ne. Sannan sai ka yawaita bibiyar alkalancinsa (hukuncinsa), ka yalwata masa a kyauta (dukiya) da abin da zai kawar da lalurorinsa, kuma (saboda) bukatunsa ga mutane ya karanta da wannan (alherin da kake yi masa), kuma ka ba shi matsayi gunka matsayin da wani daga mukarrabanka ba ya kwadayin irinsa domin ya samu amintuwa gunka daga kisan da wasu mutane zasu yi masa. To sai ka duba wannan duban lura matuka, ka sani wannan addinin ya zamo ribatacce a hannun ashararai ne da ake aiki da son zuciya cikinsa, kuma ake neman duniya da shi.
Sannan ka yi duba cikin lamurran ma'aikatanka, sai ka ba su aiki kana mai jarraba su, kada ka ba su aiki don kauna da yin gaban kai, ka sani su wadannan halaye ne da suka tattaro dukkan zalunci da ha'inci.
Ka nemi masu tajriba (sanin makamar aiki) daga cikinsu, da masu kunya daga gidaje na gari, da kuma masu dadewa a musulunci da rigo, domin su sun fi kyawawan halaye, sun fi ingancin mutunci, da karancin kwadayi saboda kima, mafi isuwa a ra'ayi a cikin abin da zai kai ya dawo. Sannan sai ka yalwata musu da arziki domin a wannan ne suke da karfi a kan gyara kawukansu, da wadatuwa daga neman abin da yake hakkin na kasa da su, kuma ya zama hujja a kansu idan suka saba wa lamarinka, ko suka ci amanarka.
Sannan ka bibiyi ayyukansu, sai ka aika musu masu bincike na asiri daga mutane masu gaskiya da cika alkawari, domin bibiyarka ga lamarinsu a cikin sirri, kwadaitarwa ce garesu a kan yin aiki da amana da tausaya wa al'umma. Kuma ka kula da masu taimakonka (a aiki), domin idan wani daga cikinsu ya sanya hannunsa cikin ha'incin da labarin masu sanya ido na asiri suka kawo maka kansa, to wannan ya isa sheda gunka, sai ka shimfida masa hannun ukuba a jikinsa, ka rike shi da abin da ya yi na (mummunan) aikinsa, sannan kuma sai ka sanya shi a gun kaskanci, ka yi masa alamar (da zata nuna yana da) ha'inci, ka rataya masa aibin tuhuma.
Ka bibiyi lamarin haraji da (kula da) abin da zai gyara (yanayin rayuwar) masu kulawa da shi, domin a cikin gyaransa da gyaransu akwai gyaran wasunsu, kuma babu gyara ga waninsu sai da su domin dukkan mutane suna dogaro kan haraji ne da masu kulawa da shi. Kuma dubanka kan gyaran kasa ya fi yawa fiye da dubanka kan samo haraji, domin wannan (harajin da kudaden shiga) ana iya samunsa ta hanyar raya kasa. Duk wanda ya nemi (a bayar da) haraji ba tare da (ya) raya kasa ba, to zai rusa kasa ne ya halaka bayi, kuma lamarinsa ba zai daidaitu ba sai kadan. Idan suka kawo kukan wani bala'in (kamar fari da bushewar kasa) ko wata cuta (kamar kwalara), ko yankewar ruwan sha, ko danshin kasa, ko ambaliyar ruwa da ya mamaye wata kasa, ko rashin ruwa da ya lalata ta, to sai ka saukaka musu da (taimakon da) zaka gyara lamarinsu da shi.
Kada ka ga ji nauyin abin da ka saukaka musu rayuwa da shi, domin shi ajiya ce da zasu sake dawo maka da shi domin raya kasa, da kawata jagorancinka, tare da jawo (maka) kyakkyawan yabonsu, da farin cikinka na yada adalci a tsakaninsu kana mai dogaro da mafificin karfinsu da abin da ka yi musu tanadi na yalwata musu da amintuwa da su da abin da ka saba musu da shi na adalcinka garesu a cikin tausasawarka garesu. Ta yiwu wani lamari ya faru daga baya wanda idan ka dora (alhakin yin) shi a kansu sai su dauki nauyinsa suna masu yarda da shi da kansu. Ka sani raya kasa yana dauke duk wani abu da ka dora masa ne, kuma rushewar kasa yana zuwa ne ta hanyar talaucin mutanenta, kuma talauci yana samun mutane ne daga kwadayin tarin dukiyar (jama'a) da jagororinsu suke yi, da munana zatonsu ga (rayuwar) nan gaba (ta yadda suke jin tsoron idan sun sauka daga mulki zasu talauta), da kuma karancin daukarsu ga darasin rayuwa (domin da yawa sun sauka daga mulki amma abin da suka sata din bai amfane su ba).
Sannan sai ka duba masu aikin ofishinka ka dora alhakin kula da lamarinsa hannun wanda ya fi su (tsoron Allah), ka zabi mutumin da ka san yana da salihancin halaye wanda don ka girmama shi ba zai yi maka takama ba (wata rana), sai ka dora masa alhakin kula da wasikunka (fayalolinka) da kake shigar da dubarunka (salon shugabancinka) kuma kake tattara dukkan sirrinka a cikinsu, domin kada wata rana ya yi jur'ar a kanka ya saba maka a gaban mutane.
Kuma ya kasance sha'afa ba ta sanya shi takaitawa kan ya kawo maka duk wasikun ma'aikatanka zuwa gareka, da kuma bayar da jawabinta daidai da yadda ka bayar daga wurinka, mai kula da abin da ya karba daga wurinka da wanda yake bayarwa daga gareka, kuma ba ya raunata wani abu da ka kulla (yana iya zartar maka da shi), kuma ba ya gazawa wurin warware abin da yake na cutuwarka, kuma ba ya jahiltar (matukar) gwargwado iyakacin kansa a lamurra, domin wanda ya jahilci gwargwadon iyakarsa, to kuwa zai kasance ya fi jahiltar gwargwadon iyakar waninsa.
Sannan kada zabarka garesu ta kasance bisa kyautata zatonka da nutsuwarka da kyakkyawan zatonka, domin mutane suna neman a san su ta hanyar kyautata zaton jagorori da nuna yin kyakkyawan aiki (a zahiri) da kyautata hidimarsu, (ta haka kuwa) babu wani rangwame da amana da za a samu, sai dai ka jarraba su ne da (aikin) abin da suka yi wa (shugabanni) na gari kafin kai, to sai ka dogara da wanda ya fi kyautatawar cikinsu da ya kasance (alherinsa) ya fi yin tasiri a cikin al'umma, wanda shi ne ya fi saninsu ga amana, domin wannan shi ne abin da zai nuna biyayyarka ga Allah da kuma (kyautata kulawarka ga) wanda kake kula da aikinsa (jagorancinsa).
Kuma ka sanya wa kowane lamari daga lamurranka wani jagora wanda babban lamari ba ya rinjayarsa (sai ya aiwatar da shi), kuma yawan lamurra (ayyukan ofis) ba ya rarraba masa hankali, kuma duk wani wanda yake daga ma'aikatanka da yake da wani aibi kuma sai ka kawar da kanka daga gareshi (ba ka dauki mataki kansa ba) to kai ne za a dora wa alhaki.
Sannan ka yi wasiyyar alheri ga 'yan kasuwa da masu sana'o'i: Mazauninsu da mai tafiye-tafiyensu da dukiyarsa, da mai aiki da karfin jikinsa, ka sani su ne mabubbugar kayan amfani kuma musabbabin (saukaka wa mutane) samun kayan more rayuwa, masu kawo su daga nesa da manisantan kasashe, ta kasa ne ko ta ruwa, a kwari ne ko tudu, inda mutane su ba zasu iya zuwa ba, kuma ba su da juriyar yin hakan ma.
Su aminci ne da ba a jin wani abin tsoro da su, su aminci ne da ba a jin tsoron gurbacewarsa, don haka ka bibiyi lamarinsu a inda kake da kuma duk sasannin kasarka.
Amma fa duk da haka ka sani cewa da yawansu suna da munana mu'amala, da kauro mai muni, da boye kayan amfani, da kuma sarrafa (yin coge) cikin kayan sayarwa, wannan kuwa cutarwa ce ga al'umma, kuma aibi ne ga jagorori.
To ka hana boye kaya, hakika manzon Allah (s.a.w) ya hana shi, kuma kasuwanci ya zama mai sauki, da ma'auni mai daidaito (babu tauyewa), da farashin da ba ya cutar da bangarori biyu; mai sayarwa da mai sayowa. Kuma duk wanda ya boye kaya bayan ka hana shi, to sai ka yi masa ukuba, sai dai ukubar da babu wuce iyaka.
Sannan ka ji tsoron Allah game da dabakar kasa wadanda ba su da wata dubara, da miskinai, da mabukata, da ma'abota musibu da nakasassu, domin a cikin wannan dabakar akwai wanda yake bara da wanda ba ya yin bara. Kuma ka kiyayi Allah a abin da ya ba ka kiyayewa na hakkinsa a game da su, ka sanya musu wani rabo daga Baitul-mali, da wani kason daga kayan da ake samu daga ganimar (dukiyar kasa ta) musulunci a kowane gari, ka sani na nesa daga cikinsu shi ma yana da (hakkin da) na kusa yake da shi.
Kuma duk kowa ka kiyaye hakkinsa, kada yabon wasu daga cikinsu ya daukar maka hankali, ka sani ba a yi maka uzurin tozarta karamin abu don ka kyautata da yawa muhimmai, kada ka bar himmantuwa da su (talakawan), kada ka daga musu kai, ka bibiyi lamarin wanda ba ya iya isa zuwa gareka daga cikinsu daga wadanda idanuwa suke rena su, mutane suke wulakanta su, to ka samar wa wadannan wasu amintattunka daga masu tsoron Allah da kaskan da kai, sai su rika kawo maka lamarinsu, sannan ka yi musu abin da Allah zai ba ka uzuri ranar da zaka hadu da shi, domin wadannan (dabakar) a cikin al'umma su ne suka fi bukatuwa da a yi musu adalci fiye da waninsu, kuma (game da) kowa ka nemi uzuri wurin Allah a kan bayar da hakkinsa zuwa gareshi.
Ka nemi (yin alheri ga) ma'abota maraici da masu yawan shekaru wadanda ba su da wata dabara, kuma ba sa iya yin roko, wannan kuwa abu ne mai nauyi kan shugabanni, kuma gaskiya dukanta tana da nauyi, amma Allah yana saukaka shi ga mutanen da suka nemi rangwame, sai suka yi juriyar kansu, suka amintu da gaskata alkawarin Allah garesu.
Ka sanya wa masu bukatau wani lokaci da zaka ba su (ka hadu da su) da kanka, ka zauna da su zaman shekara sai ka kaskantar da kai a cikinsa ga Allah da ya halicce ka, kuma ka zaunar da rundunarka da mataimakanka daga masu tsaronka da 'yan sandanka don mai yin magana daga cikinsu ya yi maka magana ba tare da wani tsoro ba, hakika ni a wurare da yawa na ji manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Al'umma ba zata tsarkaka ba matukar ba a karbar wa mai rauni hakkinsa daga mai karfi, ba tare da wani tsoro ba". Sannan (su wadannan raunanan al'ummarka da ka zauna da su) sai ka jure wa kaushin maganarsu, da kasa maganarsu (a gabanka), ka kawar musu da kuncin ransu, da girman kai, to (idan ka yi haka), Allah zai shimfida maka lullubin rahamarsa, ya wajabta maka samun ladan biyayyarsa.
Kuma ka bayar da abin da ka bayar kana mai saukakawa, (idan kuwa babu to sai) ka hana a cikin (fadin) kyakkyawar magana, da kawo hanzari.
Akwai wasu abubuwan da babu makawa kai zaka yi su da kanka: Daga ciki amsa wa ma'aikatanka abin da sakatarorinka ba zasu iya ba. Biyan bukatun mutane yayin da aka kawo su, na daga abin da mataimakanka suke jin haushin yin sa (sau da yawa wasu mataimakan ba sa son biyan bukatun mutane da wuri don girman kai ko don wani amfani nasu).
Kuma ka zartarwa kowace rana aikinta, ka sani kowace rana tana da ayyukanta, ka sanya mafi kyawun lokuta tsakaninka da Allah (s.w.t), ka girmama wannan bangarorin, duk da yake dukkaninsu (lokutan Allah da na mutanen) na Allah ne idan niyya ta kyautatu a cikinsu, al'umma ta samu salama daga garesu.
Ya kasance daga cikin kebantaccen abin da kake bayar da shi ga Allah kawai na addininka shi ne tsayar da wajiban da suke nasa ne kawai.
To ka ba wa Allah wani abu na jikinka da darenka da ranarka, ka cika (kyautata) abin da kake kusanta da shi zuwa ga Allah daga wadannan (ibadojin) cikawa ba tare da ragewa ko tauyewa ba, ko me kuwa zai yi wa jikinka.
Kuma idan ka tsayu don yin salla da mutane kada ka zama mai korewa (mai sanya wa mutane kyamar jam'i saboda dadewa da jan doguwar raka'a) ko mai tozartawa (mai tauye wasu rukunoni na salla), ka sani a cikin mutane akwai wanda yake da matsala (kamar rauni don tsufa ko yarinta ko rashin lafiya) da mai bukata (da yake son ya gama salla da wuri).
Hakika na tambayi manzon Allah (s.a.w) yayin da ya tura ni zuwa kasar Yaman cewa yaya zan yi salla da su, sai ya ce: Yi salla da su kamar sallar mafi raunin cikinsu, ka kasance mai tausayi ga muminai.
Kuma bayan haka kada ka tsawaita kangiyar kanka daga mutane, ka sani kangiyar jangorori daga al'umma wani abu ne na (mai kawo) kunci, da karancin ilimi a lamurran (kasa). Kuma kange su yana yanke musu sanin abin da aka kange musu shi, sai abu mai girma ya zama karami gunsu, karamin abu kuma ya girmama gunsu, kyakkyawa ya munana (gunsu), mummuna ya kyautata (gunsu), gaskiya kuma ta cakude da karya. Ka sani shugaba mutum ne da bai san abin da mutane suke boye masa shi ba na lamurra, kuma babu wata alama a kan gaskiya da ake gane nau'o'in gaskiya da karya da ita. Kai dai daya daga cikin mutane biyu ne:
Ko dai mutum ne wanda ranka take da baiwar kyauta bisa gaskiya, to a kan me zaka kange mutane daga samun wajibin hakkin da kake bayarwa ko wani kyakkyawan karimci da zaka yi shi. Ko kuma dai kai (mutum) ne da aka jarraba da yin rowa, to ai nan da nan ne mutane zasu daina tambayarka idan suka yanke kauna daga samun kyautarka, tare da cewa mafi yawan bukatun mutane wurinka babu wani abu mai nauyi a kanka cikinsu, (su bukatun sun hada da) wata kara ce kan wani zalunci, ko neman yin wani adalci a wata mu'amala.
Sannan ka sani shugaba yana da wasu kebantattun mutane abokan shawara na musamman da suke da son handuma da babakere (a kan komai), da karancin adalci a mu'amala, to ka yanke tushen (wannan hali) nasu da yanke dukkan sabuban wadannan munanan halaye (nasu).
Kada ka kebance wa wani daga na gefenka da makusantanka da wani babban daji, kada ya yi kwadayin samun wani babban yanki daga gareka da abin da zai zama cutarwa ga wanda yake makotaka da ita na daga mutane na wurin shan ruwa, ko wani aikin tarayya da zasu rika dora nauyinsa kan wasunsu, sai ya zamanto nasu shi ne jin dadin wannan (lamarin) ban da kai, kai kuma aibinsa yana kanka a duniya da lahira.
Ka lizimci gaskiya (bayar da lada ko ladabtarwa) ga wanda ya lizimce ta makusanci ne ko manesanci, kuma ka kasance mai juriya mai neman lada a kan (zartar da) hakan, wannnan kuwa ya kasance ne daga 'yan'uwanka da kebantattun mutanenka ne ta yadda ya faru. Ka ladabtar da shi da abin da yake yi maka nauyi gunsa, domin sakamakon wannan yana da kyau. Idan kuwa al'umma ta yi maka zargin zalunci to ka yi musu bayani a fili da uzurinka, ka kawar da zatonsu a kanka da bayyanawarka, domin a cikin wannan abin (da zaka yi) akwai tarbiyyantar da kanka, da tausasawa ga al'ummarka, da bayar da uzuri da zaka iya isa zuwa ga bukatarka na daidaita su kan gaskiya.
Kada ka sake ka ki wani sulhu da wani makiyi ya kira ka zuwa gareshi don akwai yardar Allah cikinsa, ka sani a cikin sulhu akwai hutu ga rundunarka, da hutawa daga bakin cikinka, da aminci ga kasa.
Sai dai ka yi hattara matukar hattara daga makiyinka bayan yin sulhu, domin tayiwu makiyi ya kusa da ya shammace ka ne, to ka yi riko da shiri, ka tuhumi kyautata zato a cikin (irin) wannan.
Idan ka kulla wani alkawari da kai da makiyinka, ko ka sanya masa wani alkawari daga gareka, to ka kiyeye alkawarinka da cikawa, ka yi tsantsenin alkawarinka da kiyaye amana, ka sanya kanka garkuwa ga abin da aka ba ka (na alkawari), ka sani babu wani abu na wajibcin hukuncin Allah da mutane suka fi tsananin haduwa a kansa duk da (kuwa) rarrabuwar (kawukansu sakamakon) son ransu da (kuma) daidaitar (bambancin) ra'ayoyinsu, fiye da girmama cika alkawuran (yarjejeniyoyi).
Kuma hakika wannan ya lizimci mushrikai a tsakaninsu banda musulmi yayin da suka samu bala'in sakamakon yaudara (a lokacin annabi). Don haka kada ka yi yaudarar alkawarinka, kada ka karya yarjejeniyarka, kada ka shammaci makiyinka, ka sani ba mai yi wa Allah karan tsaye (shisshigi) sai jahili tababbe. Kuma lallai Allah ya sanya alkawarinsa da yarjejeniyarsa aminci ne da ya bayar da shi ga bayinsa da rahamarsa, kuma hurumi ne da suke nutsuwa da shi zuwa ga kariyarsa, suke kwarara zuwa ga kariyarsa. Don haka babu barna, babu algush, babu yaudara a cikinsa.
Kada ka kulla wani abu da kake halatta yin jirwayen magana a cikinsa, kada ka dogara kan jirkita magana bayan karfafawa da kullawa, kada kuncin lamarin da (daukar alkawarin yarjejeniyar) ya lizimta maka (na daga) alkawarin Allah a cikinsa ya nemi ka bata shi ba tare da wani hakki ba, ka sani hakurinka kan kuncin wani lamari da kake sauraron mafitarsa da samun kyakkyawar mafitarsa shi ya fiye maka yin yaudara da kake jin tsoron mummunan sakamakonta, kuma (idan ka yi yaudara ka karya yarjejeniyar) wani mummunan (zunubi) ya kewaye ka daga Allah wanda ba zaka iya samun mafita a cikinsa a duniyarka ko a lahirarka ba.
Kuma na hana ka zubar da jini ba tare da halal dinta ba, domin babu wani abu da ya fi kawo azaba, wanda yake mafi girma ga mummunan sakamako, kuma mafi kusa da gushewar ni'ima da yanke rayuwa, fiye da zubar da jini ba tare da hakki ba.
Kuma Allah madaukaki zai fara hukunci tsakanin bayi ne cikin abin da suka zubar na jini ranar kiyama. Don haka kada ka karfafi mulkinka da zubar da jinin haram, domin wannan yana raunana shi ya rusa shi, kai yana kawar da shi ne ya ciratar da shi. Kuma ba ka da wani uzuri wurin Allah ko a wurina a kisan ganganci, domin akwai sakamakon kisasi a cikinsa.
Idan kuwa aka jarrabe ka da (kawo maka wani mutum wanda ya yi kisa bisa) kuskure, (sai ka zartar da) hukuncinka (a kansa amma sai ka samu bisa kuskure hukuncin da ka zartar) ya samu wuce iyaka da bulalarka ko takobinka ko hannunka da wata ukuba (bisa kuskure, kamar a wurin kisasin wata gaba sai aka wuce iyaka), to ka sani a cikin (kowane kuskuren zartar da hukunci ko da kuwa) naushi (ne) da abin da ya yi sama da hakan (kamar ya kai ga kashe shi, to) akwai (yiwuwar) kisa, don haka kada tumben (takamar) mulkinka ya sanya ka daga kai har ka hana ma'abota jini hakkinsu (na kisasi ko diyya).
Ka yi hattara da jin kanka da amintuwa da abin da yake burge ka daga kanka, da son yabo (gareka), domin wannan ita ce mafi samun damar shedan, domin ya shafe maka abin da kake (da shi) na kyautatawar masu kyautatawa.
Na hana ka yi wa al'ummarka gorin kyautatawarka, ko neman su kambama abin da ka yi na aikinka, ko ka yi musu alkawari sai ka bi alkawarinka da sabawarka, ka sani yin gori yana bata kyautatawa ne, neman kambamawa yana tafiyar da hasken gaskiya, saba alkawari yana jawo kiyayya gun Allah da gun mutane. Allah madaukaki yana cewa: "Zargi (zunubi) ya girmama gun Allah ku fadi abin da ba kwa aikatawa".
Kuma na hana ka yin gaggawa a lamurra kafin lokacinsu, ko kuma ka saryar da su (ka fasa yin su bayan an zartar da) yayin da za a yi su, ko kuma yin taurin kai a cikinsu idan aka yi su, ko raunana su idan suka bayyana, ka sanya komai a mahallinsa, ka ajiye kowane aiki a wurinsa.
Kuma na hana ka kebance (kanka) da abin da yake mutane suna da daidaito a cikinsa, da yin banza da abin da ake nufi da shi (na hadafinsa) na daga abin da ya bayyana ga idanuwan (mutane), ka sani shi (abin da ka wawashe na al'umma) abin karba ne (don a mayar da shi) ga waninka (na al'umma masu hakki a lahira) daga gareka (domin saka wa al'umma), kuma da sannu ba dadewa (a lahira) abubuwan da suka boyu (a nan duniya) zasu bayyana (a lahira), a yi wa wanda ka zalunta (na daga al'umma) adalci kanka.
Ka mallaki shisshigin kanka, da zafin ranka, da tsananin hannunka, da kaifin harshenka, ka kiyaye dukkan wannan da kame yin munanan maganganu, da jinkirta hukunci har sai ka sauka daga fushinka (tukun) ka samu (hucewa daga haushinka da samun) zabi (sannan sai ka zartar da hukunci).
Kuma ba zaka iya hukunta wannan a kanka ba har sai ka yawaita bakin cikinka da tuna makoma zuwa ga ubangijinka, kuma wajibi ne ka tuna abin da ya gabata na wadanda suka gabace ka daga hukumomin adalci, ko wata al'ada mai kyau, ko wani aiki (da aka samo) daga annabinmu, ko wata farilla a littafin Allah, sai ka yi koyi da abin da ka gani daga abin da muka yi aiki da shi a cikinsa, ka yi matukar kokarin kanka na ganin ka yi biyayya ga wannan rubutu nawa da na aiko maka da shi wanda na amintu da shi na daga hujjojin kaina gareka don kada ka samu wata matsala yayin gaggautawar kanka zuwa ga son ranta.
Kuma ni ina rokon Allah da yalwar rahamarsa da girman kudurarsa kan bayar da dukkan abin nema, da ya ba ni dacewa da ni da kai bisa abin da yake akwai yardarsa cikinsa na tsayuwa kan uzuri bayyananne zuwa gareshi da halittarsa, tare da kyautata yabo cikin ibada, da kyakkyawan tasiri cikin gari (kasa), da cikar ni'ima, da ninka karimci, kuma ya cika mana ni da kai da rabauta da shahada, kuma mu masu kwadayi ne zuwa gareshi. Kuma aminci ya tabbata ga manzon Allah (s.a.w) da alayensa tsarkaka (a.s)
Cibiyar Al'adun Musulunci
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Thursday, July 28, 2011