Ikon Hajji
Mukaddimar Safarar Hajji
1. Kamar yadda hajji kansa yake wajibi, haka ma mukaddimar safara zuwa hajji take wajibi a kan mutum, wato idan mutum ya samu iko to ya zama wajibi a kansa ya tafi sayan tiket, da yin paspot, da biyan kudin kujera, da sanya sunansa a shiyarsa, wadannan duka wajibi ne yin su.
Sharuddan Ikon zuwa Hajji
Sai dai tambaya a nan ce ta waye mai kion zuwa hajji wanda ahajji ya zama wajibi a kansa? Ta yiwu sau da yawa wani zai ya yi tunanin cewa shi ba mai iko ba ne alhalin shi mai iko ne, ko kuwa ya yi zato cewa shi mai iko ne alhalin ba mai iko ne don haka idan ya je makka dole ne ya yi aikin hajji da niyyar mustahabbi ba niyyar wajabci ba tun da hajji bai zama wajibi a kansa ba ta hanyar samun iko.
Mene ne sharudan iko? Iko kala hudu ne: ikon dukiya, ikon jiki, ikon zamani, ikon hanya, kuma zamu yi bayaninsu daya bayan daya kamar haka:
2. Ikon duniya shi ne wanda mutane suka fi sani, kuma wani lokacin idan aka ce wane yana da ik, to yawancin abin da yake zuwa tunanin mutane shi ne wane ya samu ikon dukiyar yin hajji, sai dai akwai sauran wasu irin sharudan ma. Ta yiwu wani yana da iko ta fuskancin dukiya, amma ba shi da iko na jiki; idan mutum wani lokaci ya samu dukiya misali ta hanyar gado, ko kuma rayuwarsa daga karshe ta yi kyua, amma ba zai iya zuwa aikin hajji ba, wannan ba shi da iko tun da ta fuskacin jiki ba zai iya ba, kuma hajji bai zama wajibi a kansa ba.
Ko kuma mutumin da a lokacin da ya samu dukiya, ba zai iya sayan kujerar makka ba, ko kuma ba a dauka da shi ba a hukumar alhazai, kuma ba zai iya zuwa ta wata hanyar ba, to wannan bai zama mai iko ba har sai an dauka da shi.
Amma ikon dukiya yana iya kasance ta hanyoyi daban-daban kamar haka: Na farko dai wadannan abubuwan sun hada da samun guzuri isasshe, da bin hawa, kamar a yau shi ne tiket, wato kudin ya zama zai iya sayan tiket da kuma guzuri isasshe har ya je ya dawo, da kudin kujera baki daya. Haka nan da wani zai saya masa kudin kujera kawai amma shi zai tanadi guzuri to duk wannan ya isar masa zama mai ikon zuwa hajji.
Na biyu shi en ya kasance akwai dukiyar da zai bar wa iyalinsa su rayu har ya je ya dawo ba tare da ya fada cikin cin bashi ba, misali a tsawon wata daya da kwana ishirin ko makamancin haka da zai yi a aikin hajji kada ya kasacne yana bukatar bashin kula da rayuwarsu ko makamancin hakan.
Na uku shi ne ya kasance yana da abubuwan da suek na tilas a rayuwa kamar gidan zama da yake bukata daidai gwargwadon bukatuwarsa bisa yanayin rayuwar mutum kamarsa, haka nan ma idan yana bukatar abin hawa da lallai yake bukatarsa a rayuwarsa to shi ma ya kasance yana da shi.
3. Da wannan ne zamu ga cewa idan misali mutum ba shi da gidan zama yana haya ne, kuma hayar ta zama masa da wahala, sai dai yana da kudin da zai iya zuwa hajji, to wannan ba mai iko ba ne domin tanadin gidan da zai zauna shi ne farko tukun. Haka nan idan mutum ba shi da abin hawa, kuma bisa hakika lallai yana da bukatar sa, kuma idan ya yi hajji ba zai iya saya ba, to wannan ma ba mai iko ba ne.
Haka nan idan yana da wasu abubuwa da yake son ya saya wadanda suek na tilas a rayuwarsa kamar misali doki, kayan gida, da sauran su, kuma lallai yana bukatar su, to ya zama dole ya tanade su.
Amma idan yana zaman haya a wani gida, kuma ba shi da wata matsala ta fuskacin yin haya, ko yana zama a gidan gwamnati ko kamfani, ko gidan babansa da yake zama kuma babu wata matsala, kuma yanayinsa ne hakan ba komai, sannan yana da kudin da zai iya yin hajji, kuma ba shi da wasu sharudan a kansa, to wannan mutumin yana samu iko.
Mutane da kansu sai su duba wadannan bayanai su kwatanta da halin rayuwarsu su gani idan suan da matsala ko ba su da ita?
Na hudu shi ne cewar bayan sun dawo daga aikin hajji ya kasance kuma suna da abin da zasu ci gaba da juya rauwarsu ta fuskancin hakki, ko kudi, ko albashi, ko sana'a, ko aiki. Amma idan ya kasance idan suka tafi hajji suka dawo zasu fuskanci matsala ta wadannan fuskokin, kamar idan ya dawo zai tarar da an kwace masa aikinsa, ko an kore shi daga aiki, ta yadda ba zai iya gudanar da raywarsa ba, to a nan bai zama mai ikon yin hajji ba.
4. Saboda haka jerin samun iko na dukiya sun hada da: Na daya shi ne guzurin tafiya da kudin da za a kashe a hajji. Na biyu kudin rayuwr iyali a muddar safarar yin hajji. Ta yuwu wani mutum ba shi da kudin da zai bari amma yana da wani abu da zai sayar, to wannan mutumin ma shi ma mai iko ne. Na uku shi ne kayarn rayuwa na tilas kamar abinci a bisa yadda ya dace da rayuwarsa. Na hudu shi ne bayan ya dawo ya kasance yana da abin da zai ci gaba da juya rayuwarsa da shi. To wannan mutumin da yake da wadannan abubuwan ya zama mai iko ta fuskacin dukiya.
Don haka idan wani mutum yana da ikon dukiya gwargwadon yadda aka fada a nan, kuma yana da ikon jiki (karfin jiki) da zai iya yin aikin hajji da shi, ta yadda zai iya zuwa makka, kuma hanya a bude take gare shi, sannan akwai isasshen lokacin da zai iya safara har ya kai ga yin aikin hajji ba tare da lokaci ya kue masa ba.
Yanzu da wani mutum zai samu dukiyar yin hajji, amma lokacin da zai yi aikin hajji ya kure masa ta yadda ba zai iya sayan kujera ba, ga kuma mutane suna tafiya, wannan shi ya kasance ba zai iya zuwa ba ke nan, ba shi da damar yin aikin hajji.
Da gaske ko da kuwa yana da dukiyar da zata ishe shi, sai dai bai samu damar lokaci ba, to wannan ba mai iko ba ne, idan ya kasance har zuwa shekara mai zuwa yana nan kan wannan sharadin to ya zama wajibi ya tafi a shekara mai zuwa.
A takaice mun kawo mas'alolin da suka shafi iko, don haka mutanen da suka samu iko ya zama wajibi su yi aikin hajji.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Thursday, December 15, 2011