Sanin Mikatoti
SANIN MIKATOTI
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Darasi Na Uku: Sanin Mikatoti Da Jerin Ayyukan Hajji
Masallacin Shajara Da Ayyukan Umarar Tamattu'i
1. Lokacin da kwanakin zaman mu a madina mai haske suka zo karshe, sai mu shirya zuwa ga masallacin shajara, mu fara yin ayyukan umarar tamattu'I. wadanda suka fara ayyukansu da madina wadanda sun fara da madina ne kafin yin ayyukan hajji, to idan suka nufi makka, a wajen garin madina a masallacin shajara ne zasu tsya su yi ihrami, su fara ayyukan umara, a wannan lokacin ne ayyukan harami zasu fara.
2. Wadanda kuma sai daga baya ne zasu tafi madina kamar misalin masu aikin hajjin wasu kasashe kamar iran sai su fara tafiya juhufa, wato kafin tafiya makka sai su fara zuwa juhufa, ko wani mikati sai su yi harami a can, sannan sai su tafi makka. Ban da mikatin shajara, da juhufa, muna da wasu mikatin. Ke nan muan da mikatoti har zuwa biyar.
Mikati yana nufin wurin da ake yin harami, wanda suka hada da masallacin shajara, juhufa, wadi akik, wanda ake cewa da shi "zatu irkin", da karnul manazil, sai kuma yalamlam.
Wadanda daga madina suke tafiya sai su tsya mikatin masallacin shajara su yi harami, wadanda kuma daga jidda suek zuwa makaka, sai su tafi mikatin juhufa su yi harami, wadanda kuma daga garin Da'ifa suek zuwa sai su tafi karnin manazil su yi harami.
Jerin Ayyukan Umara Da Hajji
Ko da yaya ne dole ne mai harama ya yi daga mikati sannan sai ya tafi makka domin yin ayyukan hajji.
3. Ayyukan da dole ne mu yi su dole ne su kasance bangare biyu: Na farko shi ne umarar tamattu'I, Na biyu kuma shi ne aikin hajjin tamattu'i. ni da farko zan kawo jerin ayyukan umara da hajji tukun, sannan in Allah ya so sai kuma mu yi maganar su taya bayan daya, kuma mu kawo hukunce-hukunce kowanne daga cikinsu. Da farko zamu fara da harami da hukunce-hukuncensa sai mu ce: Wato kamar mikatin masallacin shajara ga wanda ya tafi daga madina zamu kawo yin harami da kuma mas'alolin da suka shafin harami sannan sai dafafi, sai kuma sauran ayyuka.
4. Ayyukan umarar tamattu'i guda biyar ne da zamu kawo su a jere kamar haka: harama daga mikati; dawafin ka'aba a masallaci mai alfarma a gewayen ka'aba; sallar dawafi raka'a biyu a bayan mukamu Ibrahim a masallaci mai alfarma; sa'ayi tsakanin safa da marwa a wurin sa'ayin wanda yake tsakanin safa da marwa; sai kuma yanke gashi daga karshe.
5. Amma ayyukan hajjin tamattu'I a jere sun hada da: harami daga garin makka; tsayawa a arfa; tsayawa a masha'arul haram; jifa jamrar akaba a ranar idi; yin yanka; aski ko rage suma (wadannan ayyukan uku a ranar idi ake yin su); sai kwana a mina, wato zama a daren mina a daren sha daya da na sha biyu na watan zulhajji, jifan sauran jamrori a ranar sha daya da sha biyu na watan zulhajji, sannan kuam sai ayyukan makka.
Ayyukan Makka
Amma ayyukan makka bayan an gama na mina zamu kawo su a jere su ma kamar haka: dawafin hajji; sallar dawafin hajji; sa'ayi tsaknin safa da marwa; dawafin mata da salalr dawafin mata. Wannan su ne jerin ayyukan hajjin tamattu'i.
6. Ayyukan umarar tamattu' da na ayyukan hajjin tamattu' suna farawa da ihrami ne, wato yin ihrami shi ne farkon ayyukan umara da hajji. Don haka ne lokcain da muke tafiya mikati zamu fara ayyukan umara da ihrami ne.
Akwai tambayoyi uku da ake yi sau da yawa game da ihrami da zamu kawo su a nan, sanna saimu bayar da jawabin kowanne daga cikinsu:
Tambaya ta farko: Wane lokaci ne zamu yi haramar yin umarar tamattu'i?
Tambaya ta biyu: Ina ne zamu yi wannan haramar mu sanya ihrami?
Tambaya ta uku: Yaya ne zamu kasance masu ihrami? Wato wannan wajibin na aikin farko yaya zamu yi shi ne?
7. Lokacin yin ihramin umarar tamattu'I a tsawon shekara yana kasancewa ne a watannin hajji; wato shawwal, zulki'ida, da zulhajji, kuma karshen hajji yana kasacnewa ne zuwa lokacin da zamu iya yin ayyukan umarar har mu samu tsayuwar arfa. Tsayuwar arfa kuwa tana kasacnewa ne a azhara din ranar tara ga zulhajji; wato kafin wannan aikin na tsayuwa a arfa dole ne mutum ya yi ihramin haramar aikin umarar tamattu'I ya zo da dukkan ayyukanta.
Saboda haka idan mutum ya je makak a watannin ramadhan ko sha'aban ko rajab ba zai iya yin ayyukan umarar tamattu'I ba. Idan ya je dakin Allah domin yin ziyara ne sai dai ya yi umarar mufrada. Amma umarar tamattu'I wacce take wani bangare ce ta ayyukan hajji ba zai yiwu ya yi ta ba, sai dai a watannin hajji kamar shawwal, zulki'ida, ko zulhajji. Don haka idan wani mutum ya je makka a watan shawwal to zai iya yin uamarar tamattu'I har zuwa takwas ko tara ga watan zulhajji da yake a makka, sannan sai ya sake yin ihramin hajjin tamattu'I ya nufi arfa, haka nan idan ya je makak a watan zulki'ida ko farkon watan zulhajji zai iya yin umarar tamattu'I, wannan duk lokutan haramar umarar tamattu'I ne.
Wurin Harami
8. Amma tambaya ta biyu cewa ina ne zamu yi ihrami watowurin da zamu yi ihramin umarar tamattu'i? da farko mun yi nuni da mikati da nan ne ake yin ihramin umarar tamattu'I wanda muka ce shi ne wurin yin haramar umarar tamattu'I, kuma mun kawo mikatoti guda biyar sanannu da suka hada da: masallacin shajara, masallacin juhufa, wadi akid (zatu irk) duk da cewa zatu irki wani bangare ne na wadi akidi, sai dai yanzu duk ana cewa da wurin zatu irk, haka nan kuma sai karnin manazil, sannan sai yalamlam.
Mutanen da suka zo ta wata fuska daga wadannan mikatoti, duk ta inda suka zo, to wannan wurin shi ne wurin mikatinsu, idan kuma sun zo ne ta wurin da babu mikati, to sai su yi kirdadon wurin da yake saitin mikati ne wato wurin da damansa ko hagunsa zai iya zmaa mikati da zasu kai zuwa gare shi, to a nan ne zasu yi haramin umarar tamattu'I, sannan sai su kama hanyar makka don yin sauran ayyukan umarar tamattu'i.
9. Mutanen da suka fara zuwa madina idan zasu tafi makka sai su yi ihrami daga masallacin shajara. Amma idan zasu fara daga makka ne to sai su fara da yin ihrami daga daya daga cikin mikatotin da muka kawo kamar juhufa.
10. Amma batun cewa yaya muke yin ihrami; wato yaya zamu fara yin ayyuukan umarr tamattu'i? in Allah ya so lokacin da muke fara sanya tufafin ihrami a masallacin shajara misali to a nan ne zamu yin bayanin wannan lamarin. Don haka bari mu leka masallacin shajara mu ga me yake wakana.
11. Yanzu idan muka kama hanya zuwa masallcin shajara a nan ne zamu fara yin ayyukan umarar tamattu'I. Yawanci wasu mutanen suna sanya tufafin haram ne tun a madina saboda tunanin ko ba zasu iya samun damar wurin wankan mustahabbi a masalacin shajara ba, sanya tufafin harami kafin zuwa mikati ba shi da wata matsala. Don haka mutane suna iya sanya tufafinsu tun daga madina, sai sun zo mikati sai su yi niyya kawai, sai su ce labbaik. Da fadin labbaika ne mutum zaizama ya yi hara da umarar tamattu'I, sai kuma ya kama hanyar maka.
12. Bayan mun je masallacin shajara mun isa mikati da yake hanyar madina; wato bayan kwanaki da muke yi a madina, yanzu kuma don mu yi ayyukan umarar tamattu'I sai mu kama hanyar makak, farkon abin da muke yi shi ne ihrami a mikati.
13. Idan muka isa farkon zamu ga wurin alwala, bayan nan a farfajiyar tsakiya akwai masallaci da yake tsakiya, sai mu shiga masallaci wanda yake a gefen wuraren nan masu fulawowi mai grima da zamu iya gani a wurin, manara da wruin fulawosi ba bangaren masallaci ba ne su, don haka dole ne a shiga cikin masallacin. An raba bangaren maza da mata. Mata ma zasu ciga cikin masallaci ne, su yi harami, kuma duk inda suka tsaya a cikin masallacin har da bangarorin da aka kara a yau duk ya yi babu komai suna iya yin harami, ba dole ba ne su shiga cikin masallaci suan yawo suna fadin labbaik.
14. matan da suke da uzuri na shari'a ba zasu iya shiga cikin masallaci su tsaya ba, to sai su shiga ta wata kofar su wuce ta daya kofar masallacin, a yayin da suke cikin wucewa ta cikin masallacin sai su yi niyyar haramar yin umarar tamattu'i yayin da suke tafiya, kuma su yi labbaik. Haka nan suna iya yin harama tun a madina da nuzuri, shi ma babu matsala a ciki; wato sai su yi nuzurin zasu yi haramar yin umarar tun daga madina, sai su yi harama tun daga nan haramar yin umarar tamattu'I.
Kuma akwai sigar kalmomi na musamman don yin nuzuri dole ne a karanta ta, da harshen hausa zata kasance kamar haka: Yin haramar umarar tamattu'i tun daga madina saboda Allah ya hau kaina. Sai dai a sani cewa wannan ita ce sigar yin nuzuri ba yin haram da umarar tamattu'I ba, don haka yin haramar tamattu'I daban take, kuma ana yin ta ne yayin nufin yin ihrahmi wato haramar yin uamarar tamattu'I, kuma ita wannan niyyar ta yin umarar tamattu'I babu matsala a fade ta da lafazi bayan yin niyya a zuci. Sannan mai hajjaci ya fadi labbaika ya zama mai ihrami.
Mutanen da suke zuwa makka ta hanyar masallacin shajara ko kuma masu zuwa makka ta sauran mikatotyi suna yin harama ta can su sani ba dole ba ne su shiga cikin masallatan da suke wadannan mikatotin, saboda a masallacin shajara ne kawai ya zama wajibi masu yin haram su shiga cikin masallaci, amma sauran mikatotin idan ma a yankin ne mutum ya yi harama ya sanya kayan ihrami kamar a yankin juhufa ko karnul manazil, to haramarsa ta yi.
15. Tun da an yi masallatai a wuraren, to zuwa cikin masallatan da yin harama a ciki babu wata matsala ya yi.
Yayin da muka yi haram muka sanya harami, sai mu shirya don zuwa makka da yin sauran ayyukan umarar tamattu'I da suka hada da: dawafi, sallar dawafi, sa'ayi tsakanin safa da marwa, yanke suma. Da zarar mun yi harama mun yi niyya mun fadi labbaika, to duk abubuwan da aka haramtawa mai harama da umara ko hajji sun haramta gare mu, don haka su mu kula sosai kada mu yi su.
Maimaita fadin labbaika shi ma mustahabbi ne; wato mustahabbi en mu maimaita fadin labbaika ko da kuma fadin wasu jumololi ne nata kamar "labbaikal lahumma labbaik". A wasu wurare mustahabbancin haka yana karruwa; kamar yayin da mutum zai hau wani hawa, ko kuma zai yi wata gangara, ko ya hau abin hawa, ko zai sauka, ko lokaicn da yake hawa, amma lokacin da ya isa makak wato garien da yake da dakin Allah, to sai a daina fadin labbaika a yanke ta.
Ku masu ziyarar dakin Allah sakamakon abubuwan da muka kawo ne da suak gabata zaku ga ke nan wasu sun sanya tufafin ihrami sun zama masu hara da yin umarar tamattu'I a nan masallaci, sun fito daga masallaci, sun kama hanyar makka. Wasu kuma sun zo tun daga madina suna sanye da tufafinsu na haramar yin umarar tamattu'I suna shiga masallaci don su yi harama, da niyyar fara ayyukan umarar tamattu'I, da fadin labbaik.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Sunday, January 15, 2012