Muassasar alhasanain (a.s)

Rundunar Jahilci

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Gyaran Rai Na Uku Hankali da Jahilci wasu rundunoyi biyu masu harin juna da gaba mai tsanani tsakaninsu, domin duk sa'adda aka samu wani abu to babu mai yarda wani ya dauka shi kadai, kuma babu mai yarda a raba, kowanne yana son ya mallaka shi kadai ne. Don haka ne idan mutum ya samu kansa a karkashin harin wadannan abubuwa biyu babu makawa ne ya zabi daya domin ba sa haduwa wuri daya, kuma filin yaki da dauki-ba-daninsu shi ne jikin mutum, kowannen daga cikin yana son ba shi umarni ne sabanin dayan.
Da dayan zai ce dauki haram dayan zai hana, haka nan kallon haram, ko taba haram, ko jin haram, ko cin haram, ko karbar haram, duk suna karkashin umarnin rundunar jahilci ne da hanin rundunar hankali, kamar yadda jin halal, da aikata halal, da karbar halal, da ganin halal suke karkashin hanin rundunar jahilci da umarnin rundunar hankali.
Amma kafin mu ga yadda za a warware wannan rigimar ta yadda za a samu rundunar hankali su yi galaba kan rundunar jahilci cikin sauki ba tare da daga jijiyar wuya ba, zamu so kawo wasu daga cikin misalan wadannan rundunoni biyu domin mu san su tukun.
Zamu yi kokarin kawo misalai game da wannan mummunar runduna mai karya garkuwar tsaron rayukan mutane, mai jan su zuwa ga azabar Allah da fushinsa. Ita wannan rundunar tana da bangarori biyu, na farko ya shafi hukuncin shari'a, na biyu kuwa ya shafi kyawawan halaye.
Sannan zamu fara kawo Rundunar Jahilci sannan Rundunar Hankali ne domin sai an yi wanka an wanke dauda an shafa mai, sannan sai a yi ado da kaya masu kyau a sanya musu turare. Haka nan ne yake game da wadannan lamurran biyu, sai an cire munanan halaye an cizge su daga zuciya da ayyukan jiki, sannan ne idan aka yi kyawawa sai su zauna daram cikin ado. Amma mutumin da yake warin dauda, ya yi bududu da kura, fuskarsa ta dusashe, ga gumi ya jike jikinsa warin dauda yana tashi, sai kuma ya sanya tufafi masu kyau a kan wannan daudar, to haka ne misalin wanda yake yin kyawawan ayyuka amma kuma bai bar munana ba, don haka muka fara kawo su kafin mu kawo kyawawan ayyuka.
Allah madaukaki yana cewa: "Ka ce ku zo in karanta muku abin da Ubangijinku ya haramta muku" . Kamar yadda ya lizimci musulmi ya nemi sanin wajibai haka nan ya lizimta masa neman sanin haram da kuma nisantar su, kuma mu a nan zamu kawo galibin abubuwan da aka haramta a fikihu ne musamman wadanda ana iya cin karo da su kamar haka:
Taimakawa ga yin sabo, Taimakon azzalumi, Nutsuwa da fushin Allah, Musun mu'ujiza, Musun ranar sakamako da tayar da jikin mutane ko wani daga asasin addini ko na mazhaba, Musun larurin addini, Kawar da kai daga ambaton Allah, Izgili ga muminai, Yin Barna, Dagewa kan kananan sabo, Sanya zoben zinare ga namiji, Jawo mani kamar da hannunsa ko da na wani amma idan ta hannun matarsa ne to ba komai, Cutar da muminai, Kauce wa hukuncin shari'a, Amfani da kwanon zinare da azurfa koda don ado ne, Wulakanta musulmi, Yada sirrin wanda bai yarda a yada ba, Yada sirrin juna tsakanin miji da mata, Rashin biyayyar mace ga mijinta cikin abin da yake wajibi ne ta bi shi, Rashin biyyar 'ya'ya ga iyayensu, Wasa da kayan caca tare da sanya kudi, Bayyana sabo, Yada alfahasha, Ci a Ramadan ko ranar azumin wajibi ba tare da wani uzuri na shari'a ba, Boye kaya, Rashin nisantar bawali da najasosi, Rashin yarda da Allah a cikin kaddararsa, Umarni da mummuna, Cutar da makwabta, Karbar lada a kan wajibi ayyananne, Karkata zuwa ga azzalumai, Jefa kai cikin halaka, Jingina yaro ga wanda ba babansa ba, Fitar mace ba tare da izinin mijinta ba, Sumbuntar namiji ko mace ga bare, Sumbuntar mutum waninsa don sha'awa sai dai miji da matarsa kawai ko baiwarsa, Bidi'a cikin addini, Mutum ya auri 'yarsa ko duk matar da take haramun gareshi, Mummunan zato da gini kansa, Yin Kage, Bayan gida tare da ba wa alkibla baya ko gaba, Girman kai ga barin bautar Allah, Adon namiji da zinare, Duban taurari, Girman kai, Barin salla wajiba, Barin kowane irin wajibi, Jinkirta hajji daga shekarar da ya samu iko, Karyata wani abu na Kur'ani ko hukuncin shari'a, Yin Barna, Jinkirta salla har lokacinta ya fita, Kai hukunci gun azzalumi ba larura, Halartar wajen shaye-shaye, Mace ta yi ado ga namiji bare, Hore mala'ika ko rohani ko aljani da sauransu, Sanya bacci na maganadisu, Boye aibin kaya da algus, Jinkirta rama Ramadan har wani Ramadan din, Barin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna, Barin ladabtar da yara da zai kai ga fasadi, Haramta halal, Halatta haram, Leken aibobin mutane, Tsoratar da mumini, Barin takiyya wajen da yake dole, Kamantuwa da kafirai, Ji wa wani ciwo ko dukansa ko zaginsa ko yanke masa wata gaba, Rashin amsa sallama, Hukunci ba da abin da Allah ya saukar ba, Tsare hakkin Allah, Tsare hakkokin mutane, Tsare wani babu wani hakki, Sanya tufafin alhariri ga namiji babu wani uzuri na shari'a, Hassada da kuma aiki da ita, Tozarta hakkin mutane, Kiyaye littattafan bata da jaridu ko mujallu na bata da sayar da su da sayansu da koyar da su da koyonsu da yada su, Cin dukiyar maraya, Shan abu mai sanya maye, Cin mushe, Cin naman alade, Cin naman dabbar da aka haramta, Cin naman dabbar da ba a ambaci sunan Allah ba wajen yanka ta ko ta rasa wani sharadi na yanka, Cin tabo ko sauran abubuwan da aka haramta, Yin Ha'inci, Kayan kide-kide da muzik, kamar sayar da su da sayen su da kuma ajiye su da amfani da su, Yin Yaudara, Neman auren mace mai miji ko kuma mai idda, Cin maniyyin tumaki, Cin sauran abubuwan da aka haramta a jikin dabba, Sayar da karen kwararo ko alade da sayansu, Yakar shugaba adali, Cin najasa ko abu mai najasa da shan su, Karya ga Allah da manzonsa da Imamai (a.s), Buga ganga ko garaya da molo da ihu tare da maganganun banza da suka saba wa shari'a, Yin Sata, Yada barna, Kashe gaskiya.
Sannan akwai wasu abubuwan da aka haramta su a matsayin halaye munana da suka zo a ilimin fikihu da zamu kawo wasu daga ciki kamar haka:
Daudanci da hada zina tsakanin mutum biyu, Yin Karya, Shiga kungiyoyin bata, Shiga addinan bata, Kiyayya da mumini, Son makiya addini, Zagi musamman ga Allah da Annabi da Imami da addini da Kur'ani da mazhaba da sauran abubuwa masu tsarki, Taba littafin Kur'ani babu tsarki, Mai baki biyu; ya yabi mutum idan ba ya nan kuma ya zage shi, Karbar rashawa da cin hanci domin boye gaskiya da bayyanar da karya, Karbar rashawa da bayar da ita cikin al'amuran hukunci sai da larura, Karbar riba da bayar da ita da rubuta sheda a kanta da zama tsakatsaki a kai, Zama kasar da mutum ba zai iya kare addininsa ba ko gusar da alamomin musulunci, Zuwa kasar da zata cutar da addinin mutum, Yin Fashi, Aske gemun wani ba da yardarsa ba, Yin Rawa musamman mace gaban mazaje ajnabiyyai, Shiga cikin cacar ful, Tafiya makarantun da zai kai ga fasadi, Tafiya bandaki da wurin wanka na iyo da makarantu da wuraren da ake cakudar da ba ta dace ba tsakanin maza da mata, Raddi ga Allah da manzonsa da imamai da marja'ai da suke kan tafarkinsu cikin hukuncin shari'a, Yarda da sabo, Jifan wani da zina, Yin Annamimanci, Sauraron annamimanci, Zuwa sinimar da ake nuna fasadi da barna, Kokarin rusa masallatai, Taimako ga azzalumai koda dan aike ne, Amfani da kayan kida da caca da kuros da sauransu, Waka da fadin karya a ciki, Toshe titi da hanyar musulmi, Aibata mumini da wulakanta shi da zarginsa, Karanta girman zunubi da zai kai ga jinkirta tuba, Fitar mata ba tsari da kuma cire lullubi, Shirka da Allah mai girma, Yada alfasha, Saba wa karya, Warware alkawri, Yin Shedar zur, Sharadi da sanya kudi na tsere sai dai abin da aka fada a littafin fikihu a babin tsere da harbi, Yin Rufa ido, Yin Munafunci, Ba wa azzalumi da 'yan bidi'a uzuri da kaunarsu, Tozarta wanda ake ciyarwa, Wasa da tattabaru da tsuntsaye da sauransu na daga abubuwan da sukan kai ga haram kamar sanya kudi, Zalunci da ta'addanci, Yin Zihari, Saba wa iyaye, Aikin tsafi da kuma abin da zai raba miji da mata ko kuma abin da yake sanya son wani ba tare da sonsa ba, Cin dukiyoyin mutane da barna, Jiji da kai a ibada, Yin Algus, Wakar bata da sauraronta, Canja wasiyya, Fushi da yakan kai ga haramun, Giba wato rada da sauraronta, Fasadi a bayan kasa, Yin Fitina, Fasikanci da fajirci, Sayar da littafi madaukaki, Sayar da makami ga kafirin yaki, Kiyafa wato danganta mutane da iyayensu ta hanyar kallon kafafunsu ko jikinsu da canke, Caca da kayan shadaranji idan an sanya kudi, Yanke salla wajiba, Rantsuwa bisa karya, Tone kabari, Yanke zumunci, Jingina 'ya'ya ga Allah, Yin Bokanci, Bayar da fatawa ba da ilimi ba, Fada da tafarkin Allah, Kisa ba da hakki ba, Auren mace da aka haramta da nasaba ko shayarwa ko surukuta, Aurar namiji da aka haramta aurarsa, Kin zuwa jihadi domin kare kai da addini yayin da aka kawo masa hari, Gudu daga filin daga, Yin Kafirci, Kasuwanci da abin da aka haramta sayarwa, Tauye mudu da awo, Boye sheda, Boye gaskiya, Wake da siffanta mace mai kamewa ko yaro a ciki, Zambon mumini a waka, Bude al'aura ga wanda ya haramta ya gani, Yin Luwadi, Wasannin banza na holewa, Taba jikin ajnabi ko ajnabiyya (mace ko namiji bare), Taba mace ko namiji da sha'awa ba ta hanyar halal ba, Amfani da kayan maye kamar sha, da saye, da sayarwa, da dasa su ko shuka su, da aikinsu, da cin kudinsu, da kai wa wani, da kuma hayar kanti ko abin hawa ko wani abu daban don sayarwa, da kuma sauran amfani kamar yin magani da su idan ba da larura ba, Saba wa bakance, Aikata abubuwan da aka haramta wa mai harama da aikin hajji, Zuwa wajen bokaye da 'yan bori da 'yan camfi da masu halarto da rauhanai da aljanu da sauransu, Mata su shafi juna da sha'awa, Maza su shafi juna da sha'awa, Hana zakka ko humusi ko sauran hakkoki na wajibi, Jinkirta hakkoki, Yin Hannu da ajnabiyya babu kyalle a tsakanin hannayensu, Jayayya da Allah da manzonsa da Imami bisa shisshigi, Saba wa Allah da manzonsa da imamai (a.s), Keta umarnin Annabi (s.a.w), Shisshigi da wuce gona da iri musamman ga Allah, Leken gidajen makwabta, Zama a kan teburin da ake shan giya, Hana aikata kyakkyawa, Shiga ayyukan azzalumai, Keta alfarmar Ka'aba da wurare masu tsarki, Yanke kauna daga rahamar Allah, Ruku'u da sujada ga wanin Allah, Rantsuwa da barranta daga Allah da manzonsa ko Imami ko addinin musulunci, Kai wa zuwa ga mulki ba ta hanyar shari'a ba, Azabtar da mutane don su fadi wani abu da ake bincike.
Muna iya ganin wasu abubuwan da muka fada kafirci ne yin su wasu kuma shirka ne, wasu kuma manyan zunubai ne, wasu kuma akwai kaffara a kansu wasu kuwa akwai haddi ga yinsu kamar yadda aka yi bayani dalla-dalla a littattafai.
Sannan akwai munanan halayen dadabi'u da suke munana kuma ya kamata ga dukkan musulmi ya kaurace musu kuma suna da yawa malaman ilimin kyawawan halaye sun ambace su a littattafansu kuma a nan zamu kawo wasu daga ciki, duk da wasu ma an haramta su a shari'ance, wadanda suka hada da:
Daukar fansa, Yin Alfahari, Cutarwa koda ba da haramun ba kamar ya gina gidansa ta yadda zai kare wa makwabcinsa rana ko iska, Wulakanci ko da bai kai haddin haramci ba, Wulakanta mutane, Tsoratar da mutane koda bai kai haddin haramci ba, Yada abin da ake son boyewa, Karya a cikin raha, Yin Izgili, Wuce iyaka kamar ya zauna tarabbu'i a waje mai tsukuku, Wulakanci cikin alheri, Kage cikin raha; kamar ya ce wane yana da ci, Magana da abin da babu ruwan mutum, Dogaro kan mutane, Aikin lagawu (wasannin banza), Boye abubuwan da aka boye da ba su shafi mutum ba, Raki gun musifa, Jur'ar yin munana, Bakin ciki a kan abin da ya kubuce na duniya, Rashin kula da al'amuran lahira, Son yabo da kurantawa, Son shugabanci da girma, Son dukiya, Son duniya, Hassada matukar ba ta kai haddin haramci ba, Yin Kwadayi, Dora nauyi kan wani, Hikidi da mugun kuduri da mugun kulli, Tsoron mutane, Kutsawa cikin munanan halaye, Neman zabar rayuwar da ya so ta duniya kamar kayyaduwa da nau'in tufafi da sauaransu, Saba alkawari, Riya koda a wanin ibada ne, Munana zato ga Allah, Munana zato ga mutane, Yin Mummunar dabi'a, Halartar Mummunan waje, Kokarin aikta mummuna da ba haramun ba ne, Rashin yarda da rabo, Zama da kaskantattun mutane, Kukan sha'anin rayuwa, Yin Rowa, Shige gona da iri a rayuwar duniya, Shagube koda ba na haramun ba, Kaskanta mutane, Kaskantar da kai, Kaskantacciyar himma, Dukan kai, Kwadayi, Yawan bacci, Dogon buri, Rashin kishi, Kishi a inda bai dace ba, Yin Gaggawa, Shisshigi daidai gwargwadon da bai kai haram ba, Kyautata zato ga kansa, Kabilanci da bangaranci, Rashin girmama babba, Rashin tausaya wa karami, Rashin dogara da Allah, Fushi babu wani dalili na shari'a, Yawan wadatar da ta kasance dalilin dagawa da girman kai, Yin Dimuwa, Yin Gafala, Fankama da abin mutane, Mummunar magana koda ba haramun ba ce, Tayar da fitina, Kekasar zuciya, Raba kan mutane da rashin jituwa, Yin Girman kai, Boye gaskiya koda kuwa boyeta bai kai wajibi ba koda kuwa ta hanyar shiru ne, Ganin alherin kansa da yawa, Karanta alherin wani, Yawaita sharrin wani, Karanta sharrin kansa, Butulcewa ni'ima, Rashin godiya, Yawan raha, Rashin daidaituwa tsakanin zahiri da badini koda kuwa a kan al'amuran duniya ne, Rashin kunya, Nisantar muminai, Zaman banza, Yawan dariya, Waswasi a al'amuran duniya, Yawan shagaltuwa da rayuwa, Kazanta da rashin lizimtar tsafta, Rashin adalci, Shisshigi a al'amuran duniya, Sakaci a ciki, Zama da masu sabo, Yunkune da bata fuska, Rashin kulawa da mustahabbai, Lizimtar makaruhai, Rashin kulawa da abin da ya ce da abin da aka ce game da shi, Rashin bayar da muhimmanci ga hukuncin shari'a.

Rundunar Hankali
Akwai misalai masu yawa game da wannan rundunar wasunsu sukan kasance ta babin fikihu ne, wasu kuwa ta babin kyawawan halaye kamar yadda yake a janibin rundunar Jahilci, a babin na farko na fikihu muna da misalai masu yawa. Ubangiji madaukaki yana cewa: "Allah yana umarni da adalci da kyautatawa da kuma baiwa ga ma'abocin kusanci" . Sai ya lizimta mana sanin wajibai da aiki da su da zamu kawo wasu daga ciki a nan:
Ba wa mace sadakinta ko ladanta, Ba wa mai shayarwa ladanta, Ba wa mai girbi hakkinsa, Ba wa ma'abocin kusanci hakkinsa, Bayar da zakka, Bayar da dukiyar maraya, Tsoro da takatsantsan ga abin da Allah ya hana, Rikon ado gun masallaci, Rikon abin da Manzo da Ahlul Baiti (a.s) suka zo da shi, Bayar da amana, Bayar da sheda, Bayar da hakkin Allah da na mutane, Neman izinin shiga gidan mutane, Umarni da kyakkyawa, Aikata kyakkyawa, Imani da Allah da ranar lahira, Kaskantar da kai ga Allah, Barranta daga makiyan Allah da waliyyansa, Kin makiya Allah, Neman tsani zuwa ga Allah, Neman yardar Allah, Kin ma'abota bidi'a, Kwana gun matarsa, Biyayya ga Annabi da alayensa, Bin limami a salla, Kawar da fasadi, Tuba, Tabbata kan gaskiya, Tabbata a kare kai, Nisantar mummnan zato, Nisantar bauta ga wanin Allah, Nisantar karya da shedar zur da muzik, Karkata zuwa ga sulhu, Amsa wa Allah da manzonsa, Son Allah da waliyyansa, Hijabin mace ga namiji bare, Yin aikin Hajji, Zantawa da ni'imar Allah, Haramta abin da Allah da manzonsa suka haramta, Kyautata zato ga Allah,
Renon 'ya'ya, Kiyaye farji, Kiyaye salla da ibadu da alkawura da amana, Hukunci da abin da Allah ya saukar, Neman yafewar wanda aka zalunta, Gaisuwa, Tsoron Allah da rusuna masa, Kaskan da kai ga muminai, Humusi, Tsoron Allah, Addu'a, Kira zuwa ga Allah, Kariya ga addini da rayuka, Kare mummuna, Ambaton Allah a kowane hali, Tarbiyyar yara, Amsa sallama, Shiryar da mutane zuwa ga gaskiya, Yarda da hukuncin Allah, Ziyarar Annabi da imamai, Mika wuya da tsarkake wa ga Allah, Rige zuwa ga gafarar Allah, Sauraron Kur'ani mai hikima, Tafiya a bayan kasa domin daukar darasi, Godiya ga Allah da iyaye, Yin Hakuri, Soyayyar iyaye da makusanta, Gaskiyar magana, Gyara tsakanin mutane, Azumin wata Ramadan, Rama abin da ya jawo lalacewarsa da batansa, Ciyar da mai jin yunwa, Neman arziki, Neman ilimi, Biyayya ga Allah da manzonsa da majibinta lamurra, Bayyana gaskiya, Bayyana ki ga masu sabo, Bautar Allah, Daukar darasi daga darussan rayuwar wasu, Yin Adalci, Zama da mata da kyakkyawa, Sanin ilimin wajibi na asasin addini da rassansa da kyawawan halaye da ladubba, Taimakekeniya, Runtse gani daga haram, Neman gafara, Yin Kishi, Matsawa wasu a mazauni, Ilimin addini, Tunawa da ni'imar Allah, Hukunci da gaskiya, Tsayar da addini da aiki da shi, Fadin kyakkyawa, Daidaita al'amura, Neman halal, Kasancewa tare da masu gaskiya, Nisantar wanda Allah ya la'anta, Hana kafirai shiga masallatai, Nadama kan zunubai, Nasiha ga mumini da taimaka masa, Ciyarwa a tafarkin Allah, Yin Aure, Hana mummuna, Hanuwa daga abin da Allah da manzonsa suka hana, Komawa zuwa ga Allah, Niyyar gaskiya da kyakkyawa, Yin Tahajjudi, Hijira saboda Allah, Rushe bata, Son ma'abota kusanci, Tsentseni a haram, Awo da ma'aunin adalci, Cika alkawari, Kare rai da iyali daga wutar lahira, Dogaro da Allah, Yakini da Allah da ranar lahira.
A bangaren kuwa kyawawan halaye da aka yi umarni da siffantuwa da su muna iya ganin akwai dabi'u mafifita abin yabo da musulunci ya yi maraba da su kuma ya yi umarni a siffantu da su, da ya kamata mutum musulmi ya siffantu da su kuma suna da yawa, amma zamu kawo abin da ya samu daga cikinsu kamar haka;
Nutsuwa da alkawarin Allah, Yin sannu-sannu a al'amura, Kaskantar da kai gun Allah, Adalci da fadin gaskiya game da mutane, Wadatuwa daga mutane, Fifita wasu a kan mutum kansa, Ciyarwa a tafarkin Allah, Taimakon mutane, Saba wa kai aikata alheri, Umarni da kyakkawa, Hani ga mummuna, Gyara tsakanin mutane, Ikhlasi a ayyuka, Nutsuwa da Allah, Biyayya ga iyaye, Kaskan da kai, Ziyartar juna, Jituwa da juna, Tuba daga aikata haram, Mika wuya ga umarnin Allah a komai, Dogaro ga Allah, Tabbata kan al'amura kyawawa, Yin Hakuri, Aikata Kyawawan halaye, Kiyaye hakkin makota, Son Allah da wanda Allah ya yi umarni a so, Soyayya saboda Allah, Kiyayya saboda Allah, Jin Tsoron Allah, Kaunar Allah, Jin Tsoron aikata zunubai, Rashin dogaro da ayyuka, Cudanya da mu'amala da mutane, Magana da kawukanmu, Cudanya da iyalinmu da 'ya'yanmu, Yarda da rabon Allah, Yin Zuhudu, Yin Baiwa da kyauta, Sitirta sirrin mutane, Gyara aibobin kai, Dadada magana, Godiya ga mai ni'ima wanda ya yi maka alheri, Gyara ga mutane ta hanyar hikima da wa'azi, Sakin fuska, Yawaita sadaka da taimakon raunanan mutane, Sadar da zumunci, Yada sallama, Bin halaye da raunana da marasa lafiya suke ciki, Yin Tsafta, Suturta aibobin mutane, Daidaituwar zahiri da badini a komai, Yin Gaskiya da nisantar karya koda a raha, Yin Hakuri, Karbar bakuncin muminai, Amsa kiran bakuntar muminai, Aika wa da kyauta wuraren da suke na alheri da kuma karbarsa, Rangwame ga mutane, Kame kai, Adalci a komai, Girmama ma'abota addini, Nisantar kaskantattun dabi'u, Yin Kishi, Son talakawa, Mujahada da rai, Bayar da rance, Biyan bukatun muminai, Kame cutar da su, Kiyaye sirri da rashin yada shi, Ambaton mutane da alheri, Gaggauta alheri, Yi wa kai hisabi, Nasihar muminai yana mai neman shawara ne ko kuwa, Yin Niyyar alheri, Tsarkake kai da kawar mata munanan halaye, Yin Takawa, Yin Tsentseni, Nisantar shubuha, Juriya kan barin sabo, Juriya kan bin Allah, Ambaton mutuwa, Wadatar zuci, Jin Kunya, Sakin fuska.
Cibiyar Al'adun Musulunci
www.hikima.org
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Tuesday, May 25, 2010
 

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)