Bayan Kwanakin Mina
Darasi Na Sha Biyu: Mas'alolin Da Suka Shafi Ayyukan Makka
Ayyukan Makka
Ayyukan Makka kamar yadda muka kawo su ne: 1.Dawafin hajji, 2.Sallar dawafin hajji, 3.Sa'ayi tsakanin Safa da Marwa, 4.Dawafin mata, 5.Sallar dawafin mata. Wadannan ayyukan idan mutum yana da dama yana iya zuwa Makka a ranar idi bayan ya yi jifa da yanka da aski ya tafi Makka ya yi su. Mustahabbi ne ga wanda zai iya ya tafi ya yi su ya dawo Mina, idan bai samu dama ba, sai ya yi su ranar sha daya bayan jifa, in bai yiwu ba sai ya yi ranar sha biyu bayan jifa. Idan bai iya yin su ba, har sai da ya gama kwanakin Mina ya dawo Makka to yana da damar yin su har zuwa karshen watan zulhijja ne. Da yawan alhazawa saboda gajiyawa sukan bari sai sun dawo Makka baki daya, sannan sai su yi ayyukan Makka da suka rage.
Wasu Muhimman Bayanai Kan Ayyukan Makka
1. Kafin kawo bayanai dalla - dalla zamu fara kawo wadannan bayanai a takaice kamar haka:
Na farko: Dole na a jeranta wurin yin wadannan ayyukan kamar haka: 1.Dawafin hajji, 2.Sallar dawafin hajji, 3.Sa'ayi tsakanin Safa da Marwa, 4.Dawafin mata, 5.Sallar dawafin mata.
2. Na biyu: Wadannan ayyukan ka da a cakuda fahimtar su da na umara domin a umara ana yanke suma ko farci (akaifa) bayan Sa'ayi, amma a nan bayan Sa'ayi babu rage suma ko akaifa domin mun riga mun yi su bayan jifa a ranar idi, don haka bayan Sa'ayi sai mu yi abin da ya rage na dawafin mata, da sallar dawafin mata kawai.
3. Na uku: A aikin hajji wadannan ayyukan ana yin su ba a tufafin harami ba, don haka ana yin su a tufafin gida ne, domin ana cire tufafin harami tun ranar idi bayan an yi jifa da yanka ne kamar yadda ya gabata. Don haka bayan an dawo Makka da wannan tufafin gida ne za a ci gaba da aikin hajji na dawafi da sallar dawafi har a kammala. Sai dai wajibi ne tufafin su kasance suna da sharudan tufafin salla ne da ya hada da tsarki, halacci, kada ya kasance daga fatar mushe, ko daga fatar dabbar da cin namanta haram ne, da sauran sharudda.
4. Wadannan ayyukan na Hajji Tamattu'i da suka rage wadanda za a yi su bayan an dawo Makka, a yanayin aiki ba su da wani bambanci, sai dai a niyya da kuma tufafi kawai, domin na hajji da tufafin gida ne ake yin su ba da na harami ba. Amma dukkan sharuddan da aka kawo baki daya iri daya ne, haka ma yanayin yin aikin tun daga inda za a fara, da karewa da yadda ake yin sa, da sauran sharudan duka babu wani bambanci.
5. Haka ma sa'ayi tsakanin Safa da Marwa, da kuma dawafin mata da sallar dawafin mata, su ma dai duk haka ne, babu wani bambanci da yadda ake yin na umara sai dai a niyya kawai. Don haka duk wani dawafi ko sallar dawafi yadda ake yin su iri daya ne, sai dai kawai bambancinsu a niyya ne, haka ma na mustahabbi duka iri daya ne sai a niyya kawai ake samun bambanci.
6. Tun a yayin da muka zo maka muka yi: 1.Dawafin hajji, 2.Sallar dawafin hajji, 3.Sa'ayi tsakanin Safa da Marwa, 4.Dawafin mata, 5.Sallar dawafin mata. Mun kammal komai ke nan, sai dai akwai wasu bayanai sababbi da zamu yi na musamman game da dawafin mata da sallarsa.
Halartuwar Jin Kanshi
7. Bayan mun dawo Makka mun yi 1.Dawafin hajji, 2.Sallar dawafin hajji, 3.Sa'ayi tsakanin Safa da Marwa. To duk wani abu mai kamshi a nan ne zai halatta gare mu shakarsa.
A kula cewa a Mina duk da bayan aski mun cire kayan harami mun sanya na gida, kuma abubuwan da aka haramta sakamakon aikin hajji sun halatta gare mu, amma abu mai kamshi da mata su ne abubuwan da suke ragewa ba su halatta gare mu ba, don haka a lokacin kada mu yi amfani da duk wani abu mai kamshi da ya hada da sabulu ne, ko man shafawa, ko wani abin goge baki mai kamshi, ko abinci mai kamshi, ko tufafi mai kamshi, ko wani shamfu, kuma ko da mun je wurin jifa muna sayan turare da muka gani a hanya, to bai halatta mu sansana kamshin ba, don haka sai a kiyaye duk wannan.
Haka nan ma mace da miji haram ne kwanciya da junansu shi ma.
8. A lokacin da muka yi dawafin mata da sallar dawafin mata, to a lokacin ne miji da mata suke halatta ga junansu.
Bayan nan babu wani abu da zai rage da ya haramta ga mahajjaci sakamakon yin harami.
Marhalolin Fita Daga Ihramin Hajji
Don haka fita daga abubuwan da aka haramta marhala uku ce: da farko lokacin da muka yi aski ko saisaye ko rage suma a ranar idi komai da aka haramta ya halatta gare mu ban da abu mai kamshi da da miji ko mata ga junansu. Sai kuma bayan dawafin hajji da sallar dawafin hajji da Sa'ayi, sai abu mai kamshi ya halatta gare mu. Sai kuma bayan dawafin mata da sallar dawafin mata, sai miji da mata su halatta ga junansu. Wadanann su ne matakai uku.
Dawafin Mata da Sallar Dawafin Mata
9. Dawafin mata da sallar dawafin mata su ne abu na karshe a ayyukan Hajji Tamattu'i idan ba mu zo a kwananki Mina mun yi su ba har muka dawo Makka baki daya. Amma da mun zo ranar goma ko sha daya muka yi su baki daya muka koma Mina, to abu na karshe a hajji zai kasance shi ne jifan ranar goma sha biyu ke nan.
10. Sai kuma wasu bayanai game da dawafin mata da zamu kawo a nan:
Dawafin mata duk da ana ce masa dawafin mata, amma bai kebanta da mata ba, maza ma dole ne su yi. Kuma bai kebanta da masu aure ba, hatta da marasa aure dole ne su yi, kai hatta da yaro da bai balaga ba idan ya yi aikin hajji shi ma dole ne ya yi dawafin mata da sallar dawafin mata, domin wadannan mutane idan ba su yi ba, to ba dama su yi aure, wato aure ya haramta gare su ke nan, har sai sun yi shi, ko sun wakilta wani wanda zai yi musu.
11. Duk wani hajji ko umara idan aka gama su suna da dawafin mata da sallar dawafin mata ban da Umarar Tamattu'i, don haka ne idan wani ya yi hajjin ifradi, ko kirani, ko Umara Mufrada ita kadai to dole ne daga karshe ya yi dawafin mata. Ita Umarar Tamattu'i ba ta da dawafin mata da sallarsa ne saboda a hade take da hajjin tamatt'I, sai dai idan mutum ya yi wa Umarar Tamattu'i dawafin mata da sallarsa ita ma babu matsala, sai dai ba wajibi ba ne.
12. Wannan dawafin da sallarsa ba shi da bambanci da sauran dawafofi da sallarsu sai a niyya kawai, wasu suna damuwa da shi domin kawai sai an yi shi ne maji da mace suke iya halatta ga junansu, don haka sai su yi a nutse ba tare da sun shiga cikin damuwa ba.
13. Da wannan bayanin ne komai ya bayyana game da dawafin mata da sallar dawafin mata baki daya da muka kawo muku a nan.
Wasu Tambayoyi Game da Ayyukan Makka
14. Wasu suna tambaya cewa shin za a iya yin ayyukan Makka kafin Arfa? Amsa a nan shi ne babu yadda za a iya yin ayyukan Makka har sai an yi yanka ranar idi, don haka ayyukan Makka ba sa yiwuwa kafin Arfa har sai an yi yankan ranar idi tukun. Daga bayan yankan ranar idi har zuwa karshen watan zulhijja ana iya yin sauran ayyukan Makka kamar yadda ya gabata.
Sai dai akwai wasu mutane da aka toge daga ciki, su suna iya yin wadannan ayyukan na Makka kafin zuwa Arfa da zamu yi bayanin su a nan yanzu.
15. Nau'in mutane uku da zasu iya yin ayyukan Makka kafin su tafi Arfa sun hada da; Mutane na farko su ne wasu jama'a daga mata. Na biyu: wasu mata da maza ne da ba zasu iya yin ayyukan Makka ba daga baya. Na uku: marasa lafiyar da ba zasu iya yin wadannan ayyukan daga baya ba.
Amma na farko: Su ne matan da suke da uzuri wadanda suka san cewa bayan sun dawo daga Mina to zasu fuskanci wani uzuri na shari'a kamar jinin haila wanda zai hana su yin wadannan ayyukan, domin ba zasu iya zuwa masallaci su yi dawafi da sallar dawafi ba sakamakon haila. Haka nan matan da suke jin tsoron faruwar hakan a kansu, su ma suna iya yin wadannan ayyukan kafin zuwa Arfa.
Amma na biyu: Su ne mutanen da ba su da karfi kamar tsofaffi maza da mata, ko suna da wata matsala makamancin hakan. Wadannan mutanen idan sun san cunkoso zai hana su yin ayyukan Makka bayan dawowa daga Mina to suna iya yin ayyukan Makka kafin su tafi Arfa. Ko kuma idan suna jin tsoron ba zasu iya yin ayyukan Makka bayan Mina ba, shi ma suna iya ayyukan Makka kafin Arfa.
Mutane na uku: Su ne marasa lafiya da ba zasu iya yin wadannan ayyukan bayan Mina ba, su ma sai su yi ayyukan Makka kafin tafiya Arfa.
16. Sai dai wadannan mutanen dole ne su lura da wasu abubuwa biyu kamar haka:
Muhimmin bayan na farko: Shi ne su sani cewa dole ne sai sun yi haramar hajji sun sanya harami tukun sannan zasu yi wadannan ayyukan, ta yadda bayan sun kammala wadannan ayyukan zasu ci gaba da zama cikin haraminsu har su tafi Arfa. Don haka idan sun yi ayyukan Makka sai su kama hanya zuwa Arfa. Ko da yake idan ba ranar takwas ba ce, to suna iya zaman su kamar ko da kwana daya ne misali, in ya so ranar tafiya Arfa sai su kama hanyar Arfa. Don yin ayyukan Arfa, sannan sai yin ayyukan Muzdalfa sannan sai na Mina, shi ke nan sun kammala ayyukan hajji.
Muhimmin bayani na biyu shi ne: duk da mun ce: bayan dawafin hajji da sallar dawafin hajji da sa'ayi, abu mai kamshi yana halatta, kuma bayan dawafin mata da sallarsa miji da mata suna halatta ga juna. Sai dai mu sani wadannan mutane da suke yin wadannan ayyukan na Makka kafin tafiya Arfa wadannan abubuwan ba sa halatta gare su. Su zasu ci gaba da zama cikin harami kuma duk abin da ya haramta ga mahajjaci ya haramta gare su, amma da zarar sun yi jifar Akaba a ranar Arfa sun yi yanka, kuma sun yi aski ko rage suma, to duk wani abu da ya haramta ga mahajjaci saboda hajji ya halatta gare su baki daya lokaci guda.
Halarcin Haramtattun Ayyukan Lokacin Harami
17. A fahimta cewa muna cewa duk wani abu da yake haram ga mahajjaci yana halatta gare shi bayan ya yi wadanna ayyukan nasa bisa yadda muka yi bayani a baya, sai dai a sani cewa abu biyu suna nan haram ne ga mahajjata, wato farauta da kuma cire shukar haramin Makka, wannan abubuwa guda biyu saboda ba suna zama haram ba ne don umara ko hajji, su ayyuka ne da suke haram ga kowa a kowane lokaci ga duk wanda yake a haramin Makka.
Dawafin Mustahabbi
18. Mahajjacin da ya zo masallacin ka'aba ya yi haramar hajji don ya tafi Arfa ya fara ayyukan hajji, bisa ihtiyadi wajibi ba a son ya yi dawafin mustahabbi, wannan rashin halaccin yin dawafin mustahabbi tsakanin yin harama da hajji a masallacin ka'aba da kuma ayyukan Arfa yana nan ko da kuwa mahajjaci yana da damar yin hakan.
Na biyu: A lokacin da muka dawo daga Mina don yin ayyukan Makka da suka rage to shi ma bisa ihtiyadi wajibi bai halatta mu yi dawafin mustahabbi ba, ko da kuwa muna jin zamu iya.
Haka nan idan muka yi harama da umara daga mikati bayan mun sanya harami, bayan mun zo Makka domin yin ayyukan umara, to nan ma bai halatta mu yi dawafin mustahabbi ba kafin yin dawafin umara.
Don haka a takaice a wurare uku bai halatta mu yi dawafin mustahabbi ba ke nan kamar haka: Na farko: Tsakanin haramar umara bayan mun baro mikati mun iso Makka da kuma yin dawafin umara. Na biyu: Tsakanin harama da hajji da zuwa Arfa. Na uku: Tsakanin ayyukan Mina da yin dawafin hajji.
Ayyukan Hajjin Tamattu'i a Dunkule
19. A takaice mun yi bayanin ayyukan da mahajjaci ya kamata ya yi tun kafin tafiya hajji, da bayanin abubuwan da suka shafi tafiya Madina kamar salla, ziyara da sauransu, sai kuma muka shiga bayanin mas'alolin mikati duka ko masallacin shajara ko sauran mikatoti da abubuwan da ya kamata a yi, sannan muka yi bayanin fara ayyukan umara tun daga mikati har zuwa Makka, muka yi bayanin ayyukan umara da ya shafi harami daga mikati, dawafi gewayen ka'aba, sallar dawafi a bayan makamu Ibrahim, sa'ayi tsakanin Safa da Marwa, sai kuma rage suma. Sai kuma mu zauna a Makka har kwanakin hajji su gabato, sai mu yi harami da niyya mu fara tun daga ranar takawas ga wata ko kuma daren tara da muka riga muka yi bayani a baya, sai kuma mutafi a Arfa, ranar tara daga azahar zuwa magariba muna Arfa, sai kuma mu tafi Mash'arul haram, sai mu kasance a nan muzdalifa da niyyar tsayuwa daga bullowar alfijir zuwa bullowar rana da niyyar ibada, da rana ta bullo sai mu kama hanya zuwa Mina, sai mu jefi Akaba, mu yi yanka, mu yi aski ko rage suma.
20. Sai kuma zama rabin daren sha daya ga wata da na sha biyu ga wata a Mina, da kuma jifar bangwaye uku duka a ranar sha daya da sha biyu ga wata, bayan azahabar din goma sha biyu ga wata sai mu kama hanya zuwa Makka don yin sauran ayyukan Makka da suka hada da: dawafin hajji, sallar dawafin hajji, sa'ayi tsakanin Safa da Marwa, dawafin mata, sallar dawafin mata.
Wannan shi ne dukkan bayanan da muka gabatar muku wadanda suka shafi ayyukan Hajji Tamattu'i a takaice. Muna rokon Allah madaukaki ya arzuta mu baki daya da dacewarsa ga samun damar yin ayyukan hajji, da ziyarar wurare masu tsarki, da yin ayyukan bisa daidai.
Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Thursday, April 12, 2012