Asalin Shianci
Asalin Shianci
SHEIKH WA'ILI
Fasali Na Daya
Yaushe Shi'anci Ya Fara
A bayanan da suka gabata mun tabbatar da cewa Shi'anci abu guda ne a da can da kuma yanzu, kuma samun ci gaban da yake faruwa a mas'alolinsa ba komai ba ne sai dai fikirorin da suka bubbugo daga asalinsa. Kuma da karin wasu babobin da suke samuwa sakamakon alakokin wadannan fikirori da kuma hada wasu mas'aloli da wasunsu da a kan samu a tarihin binciken ilimi na kowane addini ko mazhaba.
A yanzu zamu koma zuwa ga farkon Shi'anci da kuma asalinsa faruwarsa da nuna yadda yake haduwa da cewa shi ne hakikanin musulunci. Sannan kuma sai mu ga yadda yake tun farkon samuwarsa da kuma yadda aka samu share fagen kasancewarsa, kuma shin ya faru ne sakamakon ayyukan tausayi ko soyayya, ko kuma sakamakon ayyuka ne masu dogaro da hankali da masu rikon wannan mazhabi suka yi riko da shi bisa tirjiya da dagewa kan wahalhalu suna masu fadaka da hakan.
Idan muka koma wa wadannan al'amuran da aka saba a cikinsu muna masu bibiyar abin da masu bahasi suka fitar da abin da ya rigaya, da kuma dukkan abin da suka rinjayar a bahasinsu, to dole ne mu gabatar da wasu misalai na wasu ra'ayoyi a wannan fagage wadanda zasu kasance tanadaddu, sannan sai mu bar wa mai karatu fage domin ya fitar da hakikanin gaskiya da kansa, ya kawo wani ra'ayi nasa da zai yi kokarin da ya kasance ya dogara bisa ilimi. Yayin da masu tarihi da bincike suke iyakance lokacin faruwar Shi'anci suna iyakance shi ne da lokacin da ya fara tun lokacin Annabi (s.a.w) ne, karshensa kuma ya kare da lokacin da aka kashe Imam Husain (a.s), kuma zamukawo maka wasu daga ra'yoyinsu, sai mu bar maka nawa ra'ayi a karshen fasali.
a- Ra'ayin da suke ganin Shi'anci ya fara daga lokacin wafatin Annabi (s.a.w), kuma wadanda suka tafi a kan wannan ra'ayi sun hada da:
Na farko: Ibn Khaldon: Yana cewa: "Shi'anci ya bayyana yayin da Manzo Muhammad (s.a.w) ya yi wafati sai Ahlul-baiti (a.s) suka ga su ne suka fi cancanta da wannan al'amari kuma halifanci yana ga mazajensu ne banda wani daga kuraishawa, kuma yayin da wasu jama'a daga sahabbai suke mika jagoranci da biyayya ga Imam Ali (a.s) kuma suna ganin shi ne ya fi cancanta a kan waninsa yayin da suka ga an kauce masa zuwa ga waninsa sai suka ki yarda da hakan..." .
Na biyu: Dakta Ahmad Amin ya ce: Farkon irin da ka shuka Shi'anci da shi su ne wadanda suka ga cewa bayan wafatin Annabi (s.a.w) Ahlul-baiti (a.s) su ne suka fi cancanta da halifancinsa fiye da wasunsu .
Na uku: Dakta Hasan Ibrahim ya ce: Ba mamaki, a bisa hakika musulmi sun yi sabani bayan wafatin Annabi (s.a.w) game da wanda zai yi halifanci bayansa, sai dai al'amarin ya tuke da jagorancin Abubakar wanda ya kai al'umma ta kasu gida biyu na jama'ar al'umma masu yawa da kuma ta Shi'anci .
Na hudu: Ya'kubi ya ce: Ana ganin jama'ar da ta saba wa bai'ar Abubakar su ne digo na farkon na Shi'anci, wanda suka fi shahara a cikinsu, sun hada da: Salman Farisi, da Abuzar Gifari, da Mikdad dan As'wad, da Abbas dan Abdul Mudallib .
Bisa bayanin masu saba wa da bai'ar halifancin Abubakar ne, Dakta Ahmad Mahmud Subhi ya ce: Abubuwan da suka haifar da wannan sabani da suka sanya wasu barin bai'a ba zai yiwu a kafa dalili da su a kan cewa dukkaninsu Shi'a ba ne. Tayiwu abin da ya fada ya kasance gaskiya, amma masu tarihi sun karfafi cewa wadanda suka saba da bai'ar Abubakar cewa su Shi'a ne, kuma da sannu zamu yi nuni da hakan yayin bayanin game da hakan .
Na biyar: Mustashrik Julad Tasihar ya ce: Shi'anci ya fara ne bayan wafatin Annabi (s.a.w) kuma kai-tsaye bayan al'amarin Sakifa .
b- Ra'yin da ya tafi a kan cewa Shi'anci ya fara ne lokacin Usman kuma wadanda suka tafi a kan hakan: Sun hada da wasu malaman tarihi da marubuta daga cikinsu akwai Ibnu Hazam, da wasu jama'a da Yahaya Hashim Fargal ya fade su a cikin littafinsa dalla-dalla .
c- Ra'ayin da yake ganin an kafa Shi'anci ne lokacin halifancin Imam Ali (a.s) kuma daga wadanda suka tafi a kan wannan ra'ayi akwai Nubkhati a littafinsa na "Firakus Shi'a" da Ibn Nadim a littafin "Alfihrast", yayin da ya ayyana lokacin faruwar Shi'anci da yakin Basara da kuma abin da suka gaba ce ta, na al'amuran da suka yi tasiri kai-tsaye wajen habakar jama'ar Shi'a da kafuwarsu .
d- Ra'ayin da ya tafi a kan cewa Shi'anci ya bayyana ne lokacin da aka yi yakin Duff bisa sabanin yadda hakan ya faru, wasu sun tafi a kan cewa dukkan abubuwan da suka faru kafin wannan yakin ba su iya kai wa ga faruwar Shi'anci ba, amma ya faru ne lokacin da aka samu aukuwar yakin Duff, (wato Karbala). Yayin da wasu suka tafi a kan cewa Shi'anci kafin yakin Duff bai wuce al'amarin gina ruhi ba kamar sufanci da zuhudu da siffantuwa da kyawawan siffofi na halaye na gari, amma bayan yakin Duff sai ya samu motsi na siyasa da kafuwa cikin zukatan mutane, kuma ya samu fadada, kuma da yawa daga mustashrikun sun tafi a kan wannan ra'ayi ne, da kuma da yawa daga marubutan wannan zamani. Dakta Kamil Mustapha yana cewa: Wannan samun ma'ana ta Shi'anci kamar yadda yake a yau, ta samu ne bayan kashe Imam Husain (a.s) yayin da ya kasance wani tsari na mazhaba ta musamman.
Yayin da kuma Dakta Abdul'aziz Adduri ya tafi a kan cewa Shi'anci ya samu tsarin siyasa ne bayan kashe Imam Ali (a.s), kuma wannan ya hada har zuwa lokacin kashe Imam Husain (a.s), yayin da ya yi la'akari da wannan ci gaban lokutan da suka gabata ne .
Wannan shi ne ra'ayin Buruklman a cikin tarihin al'ummun musulmi yayin da yake cewa: A bisa gaskiya mutuwar shahada da Imam Husain (a.s) ya samu kuma ba ta da wani tasiri na siyasa kamar yadda yake rayawa- ta taka babbar rawa wajen samun ci gaban addini gun Shi'a rundunar Ali (a.s), wanda ya zama bayan haka ne mahadar jayayyar dukkan Larabawa -kuwa wannan ba haka yake ba- kuma yau kabarin Husain (a.s) a Karbala yana daga cikin mafi tsarkin wuri gun Shi'a, musamman Farisawa da ba su gushe ba suna ganin babban burinsu yana cikin tattaruwa gunsa .
Wannan ra'ayi na Buruklman hada da cewa yana da wata dasisa da ya kunsa haka nan ya saba wa mafi girman abin da masu fadin ra'ayoyi game da bayyanar Shi'anci sakamakon kashe Imam Husain (a.s) yayin da suka tafi a kan cewa an samukafuwar siyasar mazhabar Shi'anci bayan wannan waki'a ne, yayin da shi Buruklman yake ganin babu wata hakikanin gaskiya ta siyasa a cikin wannan waki'a, al'amarin da ya kasance musu ne ga abin da yake sananne karara.
Kuma wasu mutane sun goya wa Buruklman baya a wannan ra'ayi kamar Yahaya Fargal a cikin littafinsa , da cewa wannan ra'ayoyi hudu da suke bayanin faruwar Shi'anci ba zasu iya tsayawa ba kyam gaban dalilin da yake rusa su, kuma ba ina nufin in gaggauta raddinsu ba, da sannu zan ambaci ra'ayi na biyar wanda da shi ne zai iya tabbatar da cewa wadannan ra'ayoyi suna dogara ne da abubuwan da suka faru wadanda suke bayanin cewa Shi'anci ya kafu ne sakamakon tasirantuwa da wasu abubuwan da suka faru wadanda wadannan ra'ayoyi suka dogara da shi a tarihin da suka kawo na bayyanar Shi'anci sai suka yi tsammanin an same shi a wannan lokacin, alhalin an same shi ne a tun farko. A yanzu lokaci ya yi da zamukawo maka ra'ayoyin jama'ar Shi'a musamman masana daga cikinsu, daga cikinsu akwai:
e- Ra'ayin Shi'a da wasunsu na daga marubuta a wasu mazhabobin. Yayin da wasu suka tafi a kan cewa an samu Shi'anci ne lokacin Annabi (s.a.w) kuma Annabi (s.a.w) da kansa ne ya dasa irinsa ta hanyar hadisai da suka zo a harshen Annabi (s.a.w) kuma suka ba wa Ali (a.s) matsayi a wurare daban-daban da suka rauwaito, hada da cewa akwai amintattu daga malaman Sunna da suka ruwaito kamar Suyudi a ruwayarsa daga Ibn Asakir gun tafsirin ayoyin nan biyu ta shida da ta bakwai daga surar Bayyina da sanadinsa zuwa ga Jabir dan Abdullah da ya ce: Mun kasance gun Annabi (s.a.w) sai Ali (a.s) ya gaba to, sai Annabi (s.a.w) ya ce: "Na rantse da wanda raina take hannunsa wannan da shi'arsa su ne masu rabauta ranar kiyama: Sai aka saukar da fadin Allah madaukaki "Hakika wadanda suka yi imani suka kuma yi aiki na gari su ne fiyayyun talikai". Kuma Ibn Udayyi ya karbo daga Ibn Abbas cewa ya ce: Yayin da aka saukar da fadin Allah madaukaki "Hakika wadanda suka yi imani suka kuma yi aiki na gari su ne fiyayyun talikai". Sai Annabi (s.a.w) ya ce da Imam Ali (a.s) kai ne da Shi'arka. Kuma Ibn Mardawihi ya karbo daga Imam Ali (a.s) cewa, manzon Allah (s.a.w) ya ce: Shin ba ka ji fadin Allah (s.w.t) ba cewa "Hakika wadanda suka yi imani suka kuma yi aiki na gari su ne fiyayyun talikai". To kai ne da kai da shi'arka kuma alkawarin inda zan hadu da ku shi ne tafki, yayin da al'ummu zasu zo domin hisabi, to kai za a kira ku haskaka masu fararen alamomi , don haka ne ma Abu Hatim Arrazi ya tafi a kan cewa kalmar Shi'anci shi ne farkon suna da ya bayyana a cikin musulunci, kuma wannan lakabi ne da ake gaya wa hudu daga sahabbai da suka hada da Abuzar da Ammar da Mikdad da Salman Farisi, kuma bayan yakin Siffaini wannan lakabi ya shahara ga masu goyon bayan Imam Ali (a.s) .
Wadannan hadisai da suka gabata wadanda Ibn Asakir da Ibn Udayyi da Ibn Mardawihi suka ruwaito, kuma bayanin Ahmad Mahmud Subhi ya biyo bayansu a littafinsa na "Nazariyyatul Imama" yana cewa: Wadannan hadisai da suka zo a harshen Annabi (s.a.w) game da Imam Ali (a.s), ba sa nuna cewa akwai wata jama'a a lokacin Annabi (s.a.w) da tabayyana mai suna Shi'a kamar yadda dai Annabi (s.a.w) ya yi ishara da bayyanar khawarijawa da marikawa kamar yada yake ce wa Imam Ali (a.s): Zaka yaki Nakisin (A'isha su dalha da zubair) da Kasidin (Mu'awiya) da kuma Marikin (Khawarijawa). Kuma bai nuna akwai su ba a matsayin wata jama'a wacce take da akidu mabambanta ko wasu fikirori daban .
A nan ina son in juyo tunanin Dakta Ahmad Mahmud zuwa ga cewa Shi'a ba sa kafa dalili a kan Shi'anci da samuwar Shi'anci a lokacin Annabi (s.a.w) da abin da ya zo daga gareshi a hadisansa, mas'alar kamar yadda masu ilimin usul ne suke kiran ta da cewa: Tana matsayin doka ce ba wani abu wanda yake samamme a waje ba, wato ba dole ba ne a same su a wannan lokaci kamar yadda shi Dakta Ahmad Mahmud yake nunawa.
Wadannan siffofi ne da Annabi (s.a.w) ya ambata ga Shi'a kuma ko'ina ne aka same su kuma kowane zamani ne. Amma kafa dalili a kan cewa akwai Shi'a a lokacin Annabi (s.a.w) to ana iya fahimtarsa daga ruwayoyi da kuma karinoni masu yawa da a kan iya kawo su game da wannan al'amarin. Wadannan kuwa Dakta Abdul'aziz Adduri ya kawo wani bangare daga cikinsu, kuma ya kawo madogararta , tare da wasu bayanai da kuma wani kaidi da ya kawo kan cewa Shi'anci na ruhi da gina al'umma ne ake nufi a wannan lokaci akwai shi kamar yadda ya kawo a cikin wani bangare na dalilansu wanda a kan haka ne kuma Yahaya Hashim Fargal ya tafi a littafinsa .
Wasu daga wadannan ra'ayoyi suna komawa ne tun farko zuwa ga lokacin da Shi'anci ya bayyana a rayuwar Annabi (s.a.w) yayin da wasu jama'a suka fifita Ali (a.s) a kan waninsa na daga sahabbai kuma suka rike shi shugaba kuma jagora wadanda suka hada da Ammar dan Yasir, da Abuzar gifari, da Salman Farisi, da Mikdad dan Aswad, da Jabir dan Abdullah da Ubayyu dan Ka'abu, da Abu Ayyub Al'Ansari, da Banu Hashim , da sauransu.
Don haka ne ma yake kuskure ne wani ya kawo bayyanar Shi'anci da cewa ya zo bayan wannan lokaci na Annabi (s.a.w) tare da samuwarsu tun a lokacin Annabi mai tsira da aminni. Muhammad Abdullah yana fada a cikin littafinsa na "Tarihul Jam'iyyatus Sirriyya" gun bayaninsa da ta'alikinsa a kan abin da wasu litattafan tarihi suka ruwaito yayin da Annabi (s.a.w) ya tara danginsa yayin saukar fadinsa madaukaki: "Ka gargadi danginka makusata", Shu'ara': 214. Sai ya kira su zuwa ga biyayya gareshi ba su amsa masa ba, sai Ali (a.s) ne kawai ya amsa masa, sai ya yi riko da wuyan Ali (a.s) ya ce: Wannan dan'uwana ne, kuma wasiyyina, kuma halifana a cikinku sai ku ji daga gareshi kuma ku bi shi.
Muhammad Abdullah ya yi ta'aliki da cewa: Yana daga kuskure a ce: Shi'anci ya faru ne tun farko a lokacin da Khawarijawa suka ware daga rundunar Imam Ali (a.s), Shi'anci ya fara ne tare da bayyanar lokacin isar da sakon Annabi (s.a.w) yayin da aka umarce shi da ya yi gargadi ga danginsa makusanta a wannan aya.
Fasali Na Biyu
Dalilai A Kan Faruwar Shi'anci A Lokacin Annabi (s.a.w)
1- Litattafan tarihi da suka zo da siffofin wasu jama'a a lokacin Annabi (s.a.w) da ake kiran su da Shi'a kuma mun riga mun yi nuni da wannan, don haka ne Hasan dan Musa Annubkhati yake da wani bayani game da Shi'a yana cewa:
Shi'a su ne jama'ar da suka bi Imam Ali dan Abu Dalib (a.s) a lokcin Annabi (s.a.w) sannan sai ya kirga wasu mutane ya ce: Su ne farkon wadanda aka kira da Sunan Shi'a, domin Sunan Shi'anci ya kasance ya dade ga mabiya Ibrahim (a.s) .
2- Abin da jamhurin masu bahasi suka tafi a kansa na cewa Shi'anci ya bayyana ne ranar Sakifa, kuma wannan yana nuna dalilin samuwarsa a lokacin Annabi (s.a.w) ke nan, domin ba zai yiwu ba a hankalce a ce; ya habaka cikin sati gudakwai tsawon muddar ranar karshen rayuwar Annabi (s.a.w) zuwa gama al'amuran shirin zanajarsa bayan wafatinsa, wai sai aka samu wasu mutane da suke da wani tunani da fikira da akida ta musamman.
Wannan kuwa al'amari ne da ba zai yiwu ba, domin samuwar irin wannan jama'a tana bukatar lokaci ba kankani ba, kuma dukkan wanda yake da masaniya kan al'amarin Sakifa da matsayin da wadanda suka ki yin bai'a ga Abubakar da hujjojinsu a kan wannan lamarin zai samu yankewa da yakinin cewa wannan matsayi da suka dauka na kin bai'a ga Abubakar da biyayya ga Ali (a.s) ba ya faru ba ne a gajeren lokaci da gaggawa haka daga wafatin manzo (s.a.w) zuwa ga binne shi, saboda lamarin ya nuna akwai samuwar wannan fikira da akida mai asali tun farko kan wannan al'amarin tun farkon musulunci.
3- Wasu suna ganin cewa ba zai yiwu ba a hankalce a samu zuwan wasu hadisai daga harshen Annabi (s.a.w) da suke fifita shi sannan sai a samu wasu musulmi sun ki yarda da hakan suna masu yin kunnen shegu da wannan, alhalin suna masu imaninsu da biyayyarsu ga Manzo (s.a.w). Sai dai amma tarihin musulunci ya nuna mana faruwar hakan a wurare daban-daban da zamu ambata maka wasu daga ciki:
a- Mataki Na Farko:
Yayin da fadin Allah madaukaki ya sauka, "Ka yi gargadi ga jama'arka makusanta", aya ta 214 daga surar Shu'ara'. Masu tarihi suna cewa Annabi (s.a.w) ya kira Ali (a.s) ya umarce shi da ya yi abinci ya kuma kira alayen Abdul Mudallib kuma adadinsu a wannan rana mutane arba'in ne, bayan sun ci sun sha daga nonon da ya tanadar musu sai Annabi (s.a.w) ya mike tsaye ya ce: Ya ku 'ya'yan Abdul Mudallib ni wallahi ban san wani saurayi da ya zo wa Larabawa da fiye da abin da na zo muku da shi ba, hakika na zo muku da alherin duniya da lahira, kuma hakika Allah ya umarce ni da in kira ku zuwa gareshi, waye a cikinku da zai taimake ni a kan wannan al'amari a kan ya kasance dan'uwana kuma wasiyyina kuma halifana a cikinku,. Sai mutane suka tage gaba daya, babu wanda ya bayar da amsa. Ali (a.s) yana cewa: Sai na ce: -alhalin nafi kowa karancin shekaru a cikinsu kuma na fi su kananan idanu, na fi su girman ciki, na fi su shafaffen dudduge- Ni ne zan kasance wazirinka a kan hakan ya annabin Allah. Sai ya riki wuyan rigata, sannan sai ya ce: Wannan ne dan'uwana kuma wasiyyina kuma halifana a cikinkuku, ji ku bi daga gareshi, sai mutanen suka kwashe da dariya suna cewa da Abu Dalib: Ya umarce ka ka ji ga danka kuma ka yi biyayya .
b- Mataki Na biyu:
Abu Rafi'i alkibdi bawan Annabi (s.a.w) yana cewa: Na shiga wajen Annabi (s.a.w) ana cikin halin yi masa wahayi, sai na ga wata macijiya, sai na kwanta tsakaninta da Annabi (s.a.w) domin kada wata cutarwa daga gareta ta isa zuwa gareshi, har sai da wahayi ya kare daga gareshi, sai ya umarce ni da in kashe ta, sai na ji shi yana cewa: Godiya ta tabbata ga Allah da ya kammala wa Ali (a.s) burinsa, farin ciki ya tabbata ga Ali da fifitawar da Allah ya yi masa. Wannan kuwa bayan ya karanta fadin Allah madaukaki: "Kawai majibancin lamarinku su ne; Allah da manzonsa da wadanda suka yi imani wadannan da suke tsayar da salla suna bayar da zakka, alhalin suna masu ruku'u. Aya: 55, Ma'ida. Kuma malaman Ahlus-sunna da na Shi'a duk sun tafi a kan cewa wannan aya ta sauka ne ga Ali (a.s), daga cikinsu akwai Suyudi a Durrul Mansur gun tafsirin ayar da aka ambata, haka nan ma Arrazi a cikin Mafatihul Gaibi, da baidhawi a cikin tafsirinsa, da Zamakhshari a cikin Kusshaf, da Sa'alabi a cikin tafsirinsa, da Dabarasi a cikin Majma'al Bayan da wasunsu daga malaman tafsiri da masu hadisi.
Daga abin mamaki sai ga shi Alusi a cikin tafsirinsa na Ruhul Ma'ani ya tsaya a kan wata matsaya da take mai muni da rauni yana mai hana saukar wannan aya game da Ali (a.s), yana kuma fadawa cikin bangaranci da yakan kai mutun ga fadawa cikin kiyayya da gaba da gaskiya, da fadawa cikin magana mai karo da juna da warwara maras ma'ana. Mutum yakan yi mamakin wannnan mutumin, domin sau da yawa mukan gan shi da matsayin warware magana da suka ga Imam Ali (a.s), wani lokaci ya ba shi hakkinsa, wani lokacin kuma ya tsaya yana mai musun sa, kuma dukkan wanda ya karanta rubuce-rubucen Alusi ya san shi da hakan.
C- Mataki na uku:
Matakin da Annabi (s.a.w) ya dauka ranar Gadir Khum, yayin da ayar nan ta sauka: "Ya kai wannan Manzo ka isar da abin da aka saukar maka daga Ubangijinka, idan kuwa ba ka aikata ba, to ba ka isar da sakonsa ba, kuma Allah ne yake kare ka daga mutane" Ma'ida: 69. Yayin nan sai Annabi (s.a.w) ya tsayar da matafiya kuma aka yi masa mimbari daga kayan rakuma sai ya yi huduba a kansa da hudubar nan tasa mashahuriya sananniya sannan sai ya rike hannun Imam Ali (a.s) ya ce: Ba ni ne na fi cancantar jagorantar muminai ba fiye da kawukansu? Suka ce: Haka ne. Sai ya maimaita sau uku, sannan sai ya ce: "Duk wanda nake jagoransa to Ali wannan jagoransa ne, Ubangiji ka jibanci wanda ya jibance shi, ka ki wanda ya ki shi, ka taimaki wanda ya taimake shi, ka kuma tabar da wanda ya tabar da shi" sai halifa na biyu ya hadu da shi ya ce: Farin ciki ya tabbata gareka ya kai dan Abu Dalib, ka zama shugabana kuma shugaban dukkan wani mumini da mumina.
Kuma Razi ya kawo fuskoki goma daga cikin sababin saukar wannan aya; kuma daga cikin akwai cewa ta sauka kan Imam Ali (a.s) ne, sannan sai ya kara da bayanin bayan haka da cewa: Wannan shi ne fadin Ibn Abbas, da Barra'u dan Azib, da Muhammad dan Ali, -yana nufin Imam Muhammad Bakir (a.s) -. Kuma hadisin Gadir jama'a da yawa sun ruwaito shi daga mahardata hadisai na Ahlus-sunna, kuma Ibn Hajar ya ruwaito shi a cikin littafinsawa'ik dinsa daga sahabbai talatin, kuma ya kawo cewa dukkanin tafarkinsa ingantacce ne, kuma wasu kyawawa ne .
Ibn Hamza Alhanafi ya kawo shi daga Abiddufail Amir dan Wa'ila kamar haka ya ce: Usama dan Zaid ya ce da Ali: Kai ba jagorana ba ne, kawai jagorana shi ne manzon Allah (s.a.w), sai Annabi (s.a.w) ya ce: Kamar dai ni an kusa kira na sai in amsa, kuma hakika ni zan bar muku nauyaya biyu, daya ya fi daya girma, littafin Allah da kuma Ahlin gidana, ku duba yadda zaku maye mini a cikinsu, ku sani ba zasu rabu da ni ba, har sai sun riske ni a tafki, kuma Allah shi ne shugabana, kuma ni ne shugaban dukkan mumini da mumina, kuma duk wanda na kasance shugabansa, to Ali (a.s) shugabansa ne, ya Ubangiji ka agaza wa wanda ya bi shi, kuma ka ki wanda ya ki shi .
An wallafa litattafai masu yawa daga bangaren Sunna da Shi'a litattafai kusan guda ishirin da shida kan al'amarin Gadir, ba kuma ina son magana game da hadisin Gadir ba ne a nan game da jagorancin Imam Ali (a.s) da kuma shugabantar da shi a kan dukkan sahabbai, domin wannan al'amari ne da aka yi bincike masu yawa kansa ta fuskancin masu bincike, sai dai ni a nan ina son tambayar Dakta Ahmad Shalbi ne wanda yake cewa hadisin Gadir bai zo ba sai a litattafan Shi'a, ina mai tambayarsa shin akwai jin wani abu mai nauyi a kansa da ya dame shi ne da yake jin takaicin mas'alar Gadir da ayyana Imam Ali (a.s) a matsayin halifan annabi kuma jagoran musulmi, shi da ire-irensa na daga wadanda suke jifa da magana a kan iska, ka sani abin da yake kanka wanda ka sani na ilimi kana dauke da amana ne ga jama'a mai zuwa, kuma daga cikin kiyaye wannan amana shi ne ka gaya musu cewa irin litattafanka na Sunnanci sun zo da wannan magana daga madogararsu. Idan ka kasance kuma ba ka karatu ne, ko kuma kana karatu amma ba ka son ka sani to abin da ya fi maka shi ne kai shiru sai Allah ya ragwanta maka fiye da ka yi wannan al'amari bisa jahilci ko kuma bisa bangaranci.
Kuma haka nan wanda yake cewa: Maula a wannan hadisi tana nufin dan ammi shi ma kamar Dakta Shalbi yake, domin dogaro da cewa tana daga cikin ma'anoninta, kuma ni ba zan tsaya yi wa wannan raddi ba, sai dai ina cewa ne: Allah ka kiyaye mana hankulanmu daga shafewa. wannan ba komai ba ne sai daya daga misalan wuraren da Annabi ya yi nuni da falalar Imam Ali (a.s) kuma wadannan wurare suna da yawa ba tare da sun karfafa mutane a kan Ali (a.s) ba, kuma ba tare da sun tura su ga sanin cewa shi ne wasiyyin Annabi ba, wanda yake Kur'ani ya sanya shi daya daga cikin masu shugabanci na gaba daya bayan Allah da manzonsa. Sannan kuwa ba makawa ne musulmi su yi biyayya ga abin da ya zo musu na ma'anar Shi'anci da muke fada cewa Annabi (s.a.w) ne farkon wanda ya dasa shukarsa, kuma ya girmama ya yadu tun a lokacin rayuwarsa, ya yi 'ya'ya, har ma da wasu mutane da aka san su da shi'ar Ali, wadanda suke a gefensa, suna masu nuni da shiryarwa a kan hakan, kuma da sannu zamukawo sunayen na farko daga cikin sahabban da aka san su da Shi'anci da biyayya da mika jagoranci ga Ali (a.s).
Fasali Na Uku
'Yan Shi'a Na Farko
Su ne: Jundub dan Junadata, Abuzar algifari, da Ammar dan Yasir, da Salman alfarisi, da Mikdad dan Ammar dan Sa'alaba alkindi, da Huzaifa alyamani ma'abocin sirrin Annabi, da Khuzaima dan Sabit al'Ansari zusshahadatain, da Khabbab dan Arat alkhuza'i dayan wadanda suka sha azaba saboda Allah, da Sa'ad dan Malik, da Abu Sa'idul alkhuduri, da Abul Haisam dan Attihan al'Ansari, da Kais dan Sa'ad dan Ubbada al'Ansari, da Anas dan Alhardan Munbah dayan shahidai Karbala, da Abu Ayyubal Ansari, da khalid dan Zaid wanda Annabi ya nemi bakuncinsa yayin da ya shiga Madina, da Jabir dan Abdullahi al'Ansari dayan sahabban bai'ar akaba, da Hashir dan Abiwakkas almirkal wanda ya bude Jalula', da Muhammad dan Halifa Abubakar dalibin Imam Ali (a.s) kuma dan renonsa, da Malikul Ashtar Annakha'i, da Malik dan Nuwaira wanda Khalid dan Walid ya kashe shi, da albarra'u dan Azib al'Ansari, da Ubayyu dan Ka'abu sayyidul kurr'a'u, da Ubbada bn Samit al'Ansari, da Abdullahi dan Mas'ud ma'abocin ruwan alwalar Manzo (s.a.w) kuma daya daga shugabannin masu kira'a, da Abul'aswad Addu'uli wato; Zalim dan Umair wanda ya assasa tubalin ilimin nahawu da umarnin Imam Ali (a.s), da Khalid dan Sa'id dan Abi Amir dan Umayya dan Abdusshams na biyar din wanda ya musulunta, da Usaid dan Sa'alaba al'Ansari daga mutanen Badar, da Al'aswad dan Isa dan Wahab daga mutanen Badar, da Bashir dan Mas'ud al'Ansari daga mutanen Badar kuma daga wadanda aka kashe a waki'ar yakin Harra a Madina, da kuma Sabit dan Abu Fudhalatal Ansari daga mutanen Badar, da Haris dan Nu'uman dan Umayya al'Ansari daga mutanen Badar, da Rafi'u dan Khudaij al'Ansari daga shahidan Uhud bai balaga ba, amma Manzo (s.a.w) ya ba shi izini. Da Ka'abu dan Umair dan Ubadatal Ansari daga mutanen Badar, da Sammak dan Kharasha Abu Dujanatal Ansari daga mutanen Badar, da Suhail dan Amrul Ansari daga mutanen Badar, da Atik dan Attihan daga mutanen Badar, da Sabit dan Ubaida al'Ansari daga mutanen Badar, da Sabit dan Hudaim dan Udayyil Ansari daga mutanen Badar, da Suhail dan Hanif al'Ansari daga mutanen Badar, da Abu Mas'ud Ukuba dan Amru daga mutanen Badar, da Abu Rafi'i bawan Manzo (s.a.w) wanda ya halarci dukkan yakokin Annabi (s.a.w) tare da Imam Ali (a.s), kuma daga wadanda suka yi bai'a biyu ta Akaba da ta Ridwan kuma ya yi hijira biyu zuwa Habasha tare da Ja'afar da Madina tare da musulmi, da Abu Buraida dan Dinar al'Ansari daga mutanen Badar. Da Abu Umar al'Ansari daga mutanen Badar, da Abu Katada Alharis dan Ribi al'Ansari daga mutanen Badar, da Ukuba dan Umari dan Sa'alaba al'ansarri daga mutanen Badar, da Kurza dan Ka'abul Ansari, da Basher dan Abdulmunzir al'Ansari daya daga zababbun bai'ar Akaba, da Yazid dan Nuwaira dan Haris al'Ansari daga wadanda suka samu shaidar aljanna daga Annabi (s.a.w) da Sabit dan Abdullahil Ansari, da Jabala dan Sa'alaba al'Ansari, da Jabala dan Umair dan Aus al'Ansari, da Habib dan Badil dan Warka'ul Khuza'i, da Zaid dan Arkam al'Ansari da ya halarci yaki goma sha bakwai tare da Annabi (s.a.w), da kuma A'ayun dan Dhabi'a dan Najiya Attamimi, da Asbag dan Nabatat, da Yazid Al'aslami daga ma'abota Bai'ar Ridhwan, da Tamim bn Khuzam, da Sabit dan Dinar Abu Hamza Assumali ma'abocin addu'ar nan shahararriya, da Jundub dan Zuhair al'azdi, da Ja'ada dan Habira almahzumi, da Harisa dan Kudama attamimi, da Jubair dan Janab al'Ansari, da Habib dan Mazahir al'asadi, da Hakim dan Jabala al'abdi allaisi, da Khalid dan Abidujanata al'Ansari da Khalid dan Walid al'Ansari, da Zaid dan Suhan allaisi, da Alhajjaj dan Gariba al'ansari, da Zaid dan shurhabil al'Ansari, da Zaid dan Jibilatal tamimi, da Budail dan War'ka' al'khuza'I, da abu Usman al'Ansari, da Mas'ud dan Malik al'asadi, da Sa'alaba abu Umratal Ansari, da Abuttufail Amir dan Wa'ila Allaisi, da Abdullahi dan Hizam al'Ansari shahidin Uhud, da Sa'ad dan Mansur assakafi, da Sa'ad dan Haris dan Samadul Ansari, da Haris dan Umar Ansari, da Sulaiman dan Surad alkhuza'I, da Shurhabil dan Murratal Hamdani, da Shabib dan Rattul Namiri, da Sahal dan Umar ma'abocin Marbad, da Suhail dan Umar dan'uwan Sahal da aka ambata a baya, da Abdrrahaman alkhuza'i, da Abdullahi dan Kharash, da Abdullahi dan Suhail al'Ansari, da Ubaidullahi dan Al'azir, da Udayyi dan Hatim atta'I, da Urwa dan Malik Al'aslami, da Ukuba dan Amiris Salami, da Umar dan Hilal Ansari, da Urwa dan Malik Al'aslami, da Ukuba dan Amir Salami, da Umar dan Hilal Al'ansari, da Umar dan Ansa dan Aunil Ansari daga ma'abota Badar, da Hindu 'Yar Abi Hala Al'asadi, da Wahabu dan Abdullahi dan Muslimi dan Junada, da Hani dan Urwa Al'muhiji, da Habira dan Nu'uman Alja'afi, da Yazid dan Kais dan Abdulllahi, da Yazid dan Hurit Al'ansari, da Ya'ala dan Umair Alnahadi, da Anas An Mudrik Alkhas'ami, da Amrul Abdi Allaisi, da Umaira Allaisi, da Alim dan Salma Attamimi, da Umair dan Haris Assalami, da Alba'u dan Alhaisami dan Jarir da Babansa Alhaisam daga jagororinn yaki a yakin da aka yi da Farisa a Zi-kar, da Aunu dan Abdullahil Azdi, da Ala'u dan Umar Ansari, da Nahshal dan Dhamratal Hanzali, da Almuhajir dan Khalid Almakhzumi, da Makhnaf dan Sulaim Al'abdi Allaisi, da Muhammad da Umair Attamimi, da Hazim dan Haabi Hazim Annajli, da Ubaid dan Attihan Al'ansari, wanda shi ne farkon wanda ya yi bai'a ga Annabi (S.A.W) a daren Akaba, da Abu Fudhalatal Ansari, da Uwais Alkarni Al'ansari, da Ziyad dan Nadir Alharis, da Aiwad dan Alad Assulami, da Ma'azu dan Afara'ul Ansari, da Abdullahi dan Sulaim Al'abdi Allaisi, da Ala'u dan Urwatul Azdi, da Alkasim dan Uslaim Ala'bdi Allaisi, da Abdullahi dan Rukayya Al'abdi Allaisi, da Munkiz dan Nu'uman Al'abdi Allaisi, da Haris dan Hassan Azzuhali, ma'abocin tutar Bakir dan Wa'il, da Bujair dan Dalja, da Ayazid dan Hujjiyya Attamimi, da Amir dan Kais Adda'i, da Rafi'ul Gadafani Al'ash'ja'i, da Salim dan Abi Ja'ad, da Ubaidillahi dan Abil Ja'ad, da Ziyad dan Abil Ja'ad, da Abbana dan Sa'id dan Asi dan Umayya dan Abudsshams daga jagororin yakoki lokacin Annabi (s.a.w), Kuma Daya Daga Sahabban Imam Ali (a.s) na musamman, da Harmala dan Al'munzir Atta'i Abu Zubaida, dukkansu dari da talatin da Uku..
Wannan kadan ke nan ko kuma misali ke nan na wasu daga Shi'a da muka kawo ba tare da wani tacewa ko zaba ba, kawai na bi litattafan ilimin Rijal ne (na sanin tarihin majazen ruwayar hadisai) ne sai na kawo wadannan daga ciki, kuma wadannan litattafai masu zuwa sun kawo maganar shi'ancinsu .
Bayan mun lura da wannan jama'a ta farko daga Shi'a wasu al'amura masu muhimmanci suna bayyana garemu cewa a maganarmu wannan da zamu bujuro da ita ne gaban mai karatu wayayye mai bin gaskiya da ilimi. Domin kuwa da yawa a kan samu masu karatu da idanuwansu ba sa iya wuce abin da sadarori suka kunsa. Wani lokaci kuma yakan karanta amma ba ya son ya gaskata abin da yake karantawa tare da cikar sharuddan ingancin abin da yake karantawa, kuma tare da samun nutsuwar rai ga abin da yake karantawa, sai dai wanil lokaci abin da rai da kwakwallwa suka ginu a kansa tun yarinta, ta yada yakan kusa zama tamkar wani abu daga dabi'ar da dan'Adam ya tashi a kanta ne, sai ya kasance ya kasa barin abin da ya taso a kansa na akida.
Bayanin 'Yan Shi'a Na Farko
Wadannan kalamai da zan kawo zasu kunshi wani bayani ne game da nau'in Shi'a na farko kamar haka:
Na farko: Wadannan Shi'a da muka ambata duk da sun kasance suna ganin al'amarin halifanci na Imam Ali (a.s) ne domin shi ne wajibi a yi masa biyayya saboda nassin shari'a gareshi, tare da wannan imanin nasu da cewa duk wanda ya wuce ya sha gabansa to ya dauki abin da ba nasa ba ne, da kuma kin da yawancinsu suka yi na kin bai'a ga halifa na farko da kuma rikonsu ga gidan Imam Ali (a.s) duk da haka ba a samu wani daya daga cikinsu ya zagi wani daga sahabbai ba, ko kuma ya yi masa wani abu ta hanyar da take ba ta halatta ba, sun kasance ne dai kawai sun dage kan imaninsu da akidarsu. Ga dukkan alamu al'amarin zage-zage ya zo ne sakamakon wasu raddodi kan wasu ayyukan da suka gabata da zamu yi nuni kan haka nan gaba- duk da haka ba su riki yin zagi ba ga hukumomi ko wata magana ta banza, domin sun san cewa hakkoki ba sa iya dawo wa ta hanayr zagi, kuma zagi ba ya daga dabi'ar gwaraza, kuma nuna wani zalunci da aka yi ko kuma wani hakki da aka kwace to wannan ba zagi ba ne, sai dai akwai wasu hanyoyi masu sauki domin kai wa ga hadafi. Kuma Imam Ali (a.s) ya kwadaitar da mabiyansa kan wannan tafarki mai sauki kamar misalin abin da Nasar dan Muzahim ya ruwaito yana cewa: Imam Ali (a.s) ya wuce wasu sahabbansa da suke tare da shi a cikin rundunar yaki a Siffain sai ya ji suna zagin Mu'awiya da sahabansa, sai ya ce da dan Udayyi da kuma Umar dan Al'hamki da wasu mutane: Ina ki muku ku kasance masu la'anta masu zagi, kuna masu zagi kuma masu barranta, amma dai da zaku siffanta ayyukansu munana ku ce; suna yin kaza da kaza, kuma sun aikata kaza da kaza da ya fi kyau, kuma ya fi yanke uzuri, da maimakon la'anar da kuke yi musu da kuma baranta daga garesu zaku ce: "Ya ubangjiji ka kare jininmu da nasu ka gyara tsakaninmu da tsakaninsu, ka shiryar da su daga batansu har sai wanda ya jahilci gaskiya ya gane ta daga cikinsu, kuma wanda yake kan bata da kiyayya ya tsorata ya bari, da wannan ya fi soyuwa wajena kuma ya fi muku alheri. Sai suka ce: Ya Amirul muminin mun karbi wa'azinka kuma mun tarbiyyantu da ladabinka .
Wannan abu ya nuna mana cewa hanyar zagi hanya ce kaskantacciya ba ta da karimci, sannan kuma tafiyar da karfi ne a banza da za a iya amfani da shi da kuma juya shi domin wani aiki mai kyau, hada da cewa zagin yana kawo muzantawa ga abubuwan da mai zagin yake tsarkakewa, don haka ne ma malamai suka harmta zagin gumaka idan ya kai ga zagin Allah suna masu amfana daga wannan fadin na Allah madaukaki: "Kada ku zagi wadanda suke kiran wasu sabanin Allah sai su zagi Allah bisa gaba ba tare da ilimi ba". An'am: 108.
Don haka ne ma aka umarci Shi'a da tsarkake harsunansu daga zgin domin wannan ya fi nisantarwa ga mummuna kuma don haka ne ma muka ga da yawa daga masu talifofi masu ilimi suna karfafa siffantuwar Shi'a na farko da wannan siffa ta gari tare da cewa suna tabbatar da akidarsu ta fifita Imam Ali (a.s) a kan waninsa, daga cikinsu akwai:
a- Dakta Ahmad Amin:
Yana cewa: Irin wannan matsakaita din su ne wadanda suke ganin Abubakar da Umar da Usman da dukkan wadanda suka goya musu baya sun yi kuskure domin sun yarda da halifofi ne tare da cewa sun san fifikon Ali (a.s) da kuma cewa ya fi su .
b- Ibn Khaldon yana cewa:
Wasu jama'a daga sahabbai suna goyon bayan Ali kuma suna ganin shi ya cancanta fiye da waninsa, yayin da aka ba wa waninsa sai suka ki hakan, suka kuma ji takaici sai dai saboda sun riga sun kafu cikin addini da kuma kwadayinsu a kan hadin kai, ba su dada a kan haka ba sai ganawa da kuma kyama da jin takaici .
c- Ibn Hajar a littafin Isti'ab:
yana fada game da bayanin Ibn Dufail: Amir dan Wasila dan Kinana Allaisi Abud Dufail ya samu shekaru takwas daga rayuwar Annabi (s.a.w) kuma an haife shi a shekarar Uhud kuma ya mutu a shekara ta dari, yana cewa: Shi ne karshen wanda ya mutu daga wadanda suka ga Annabi (s.a.w) kuma ya ruwaito kusan hadisai hudu, ya kasance mai son Ali kuma daga sahabbansa a dukkan yakokinsa, kuma amintacce ne kuma yana ganin fifikon shaihaini (Abubakar da Umar) sai dai yana ganin Ali (a.s) ya fi su .
Bayan dukkan wadannan bayanai ina son in dan karkato da hankulanmu cewa yayin da nake karanta litattafan tarihi ban ga wani lokaci ba duk da yake yana da tsawo a duk fadin rayuwar halifofi da na samu wani ya yi zagi daga sahabban Imam Ali (a.s), kuma sai dai kawai akwai wanda ya yabi halifofi akwai kuma wanda ya yabi Imam Ali (a.s) hatta da masu tsananin riko da wilayar Ali ba mu samu wanda ya zagi wani ba daga wadanda suka gabatar da Imam Ali game da halifanci. Abul'aswad Addu'uli yana cewa:
Ina son Muhammad so mai tsanani
Da Abbas da Hamza da wasiyyi
Kaskantattu Banu Kushair suna cewa
Tsawon zamani kada ka manta da Ali
Ina son su saboda son Allah har sai
na zo, idan aka tashe ni a kan sona
'Ya'yan ammin Annabi makusantansa
Mafi soyuwar mutane dukkansu gurina
Idan son su ya kasance shiriya na dace
Ni ba mai kuskure ba ne idan halaka ne
Hada da cewa har ma zamani na biyu na lokacin Umayyawa mafi yawancin Shi'a suna kau da kai daga zagin Sahabbai, ko Tabi'ai: Ibn Khalikkan yana fada game da Yahaya bn Ya'amur: Ya kasance dan Shi'a ne daga masu yabon Ahlul-baiti (a.s) babu wani suka da yake yi ga waninsu .
Fasali Na Hudu
Shi'a Ba Su Ne Rawafidawa Ba
Daga dukkan abin da aka ambata zai bayyana cewa abin da masu rubuce-rubuce suka saba na jifan Shi'a da rawafidanci da kuma kiran su da wannan suna ya faru ne daga bayan saboda wasu dalilai da zamukawo wasu a nan:
Wannan zamani da aka fara kiran Shi'a da rawafidawa a lokacin Umayyawa ne, shi ya sa wasu litattafai suka zo suna siffanta rawafidawa da cewa wasu bangare ne su na Shi'a, ba wai Shi'a ba kamar yadda wasu suke son kawowa a wasu nassosi:
1- Muhamamd Murtada Zubaidi a Tajul Arus ya ce:
Rawafidawa dukkan wata runduna da suka bar jagoransu, kuma ana gaya wa wasu jama'a daga Shi'a Sunan rawafidawa. Asma'i ya ce: An kira su da wannan suna ne saboda sun yi bai'a ga Zaid dan Ali sannan sai suka ce ya barranta daga shaikhaini sai ya ki ya ce: Ba zai yi ba domin sun kasance wazirai ne na kakansa, sai suka bar shi suka ki shi sannan suka waste suka bar shi .
2- Isma'il dan Hammad Al'jawahiri ya fada a cikin Sihah:
Gun kalmar nan ta Rafadha, sai ya fadi abin Zubaidi ya fada kamar ya kwafa daga asali ne .
3- Al'kali Iyad:
Al'kali Iyad ya bambanta a littafinsa na "Tartibul Madarik fi a'alami mazhabi Malik" tsakanin Shi'a da rawafidhawa, yayin da ya kwatanta mazhabar Maliku da watanta ya ce: Ba mu ga wata mazhaba da tafi rashinsu kamar malikiyya ba, domin a cikin watanta akwai jahamiyya da rawafidhawa da khawarijawa da mur'ji'a da Shi'a, sai dai kawai mazhabar Maliku, domin ba mu ji wani ya cirato irin wadannan bidi'o'i ba a cikinta .
A fili yake cewa wannan jumla ta nuna cewa Rawafidhawa ba su ne Shi'a ba, domin samun bambanci a jerin da ya kawo. Irin wannan ne muke samu a cikin maganganun waninsa na daga ma'abota sani da ilimin addinai da mazhabobi suka cirato da wannan ma'anar ta lugga, kuma dukkan mutane da suka nisanci jagoransu ana kiran su da rawafidhawa. Kuma siffanta sahabban Zaid da wannan suna yana daga siffantasu ne da ma'anar kalmar don haka ne aka kira su da wannan suna bisa dogaro da bairn sa da suka yi yayin da suka nemi ya barranta da shaikhaini kamar yadda aka fada.
1- Wadannan da suka nemi barranta daga Zaid da sun kasance Shi'a ne to da babu makawa suna kwadayin taimaka wa Zaid ne, da kuma neman Shi'a ga shiga sahun dauki-ba-dadi da azzalumai ne domin matsayinsu yana da alaka da matsayi irin na Zaid, kuma idan ya samu rushewa to wannan yana nfin su ma sun rusu ke nan, musamman da yake cewa: Abokan gabarsu Umayyawa suna kashe duk wani wanda yake karkata ga alayen Abu Dalib hatta da a kan zato da tuhuma, to mene ne ya kai su ga kirkiro wannan bala'ai da zai kai karewar rundunar Zaid da kuma hasararsa a fagen yaki, da mutuwarsa shahidi a hannun Umayyawa. Don haka ba makawa wadannan mutane ba Shi'a ba, sai dai su wata jama'a ce da aka yi dasisarsu domin su kawo bala'i da fitina don gamawa da Zaidu da kawo masa rushewa a fagen daga.
2- Idan mun kaddara cewa akwai jama'a guda daya kebantacciya da take da ra'ayin kin shaihaini to mene ne ma'anar sanya wannan suna ga dukkan mai son Ahlul-baiti (a.s) har al'amarin ya kasance an sallama shi a matsayin suna ne da ya kebanta da su kawai, don haka ne sai ga Shafi'i yana fada a cikin baitinsa da ya shahara yana cewa:
Ya kai mahayin muhassabi a filin mina
Ka shelanta ga na zaune da na tsaye a taronta
A sahur idan mahajjata suka kwarara zuwa mina
Kwarara kamar tunkudar kogin Furat mai kwarara
Shin kun sani cewa Shi'anci ne mazhabata
Ni ina fadin haka kuma ban warware ba
Idan son alayen Muhammad shi ne rawafidanci
To al'ummu biyu su shaida ni barawafide ne
Baiti na karshe na wannan baitoti da Zubaid ya fada a littafin tajul'arsu a kalmar rawafidhawa da sauranta a bayanin tarihin Shafi'i ya zo a cikin litattafai masu yawa .
Kuma bayanin Imam Shafi'i da yake cewa: Idan dai son alayen Muhammad shi ne rawafidanci yana nuna cewa ana amfani da wannan kalma a kan dukkawan wani dan Shi'a har ma wannan kalma ta rawafidhanci ta shahara garesu kuma an yi amfani da shi don kinsu, kuma a cikin wannan akwai misali masu yawa, kuma daga cikin abin da yake nuna akwai wani kaidi da ake yi wajen amfani da wannan kalma shi ne yadda aka dora wa Shi'a wannan suna kuma har suka shahara da shi, shin an yi amfani ne t a hanya mai kyau ko maras kyau.
3- Tayiwu a ce babu makawa akwai wasu mutane masu zagin sahabbai amma me ya sa suka kasance hakan, yayin da Shi'a su ba su yarda da zagi ba haka ma imamansu ba su yarda da shi ba? Amsa ita ce ba makawa mu koma zuwa ga wasu dalilai da suke tasowa sakamakon wani abu na takurawa da ya haifar da wannan al'amari, kuma daya daga cikinsu shi ne:
Dalilan Zagi
a- Korewa da azabtarwa mai ban tsoro ga Shi'a da kuma abin da suka wahala sakamakon kisa ko kawarwa da batarwa bisa zato da tuhuma, mafi kyawun halin da suka samukansu a kansa shi ne bin su da kuma yakar su da aka yi bisa lamarin tatattalin arziki da hana su baitul mali, da kuma dora musu haraji mai tsanani, da kuma kawar da su a siyasance. Kuma mai karatu yana iya komawa zuwa ga tarihin Umayyawa a Kufa da wasunsu na daga garuruwan Shi'a domin ya san abin da halin ya kai su zuwa gareshi da abin da suka tuke zuwa gareshi a hannun Umayyawa na kekasar zuciya da kuma take hakkin 'yan'adamtaka da cin mutuncin da hatta da dabbobi suna barranta daga wannan al'amari da ya faru a lokuta biyu; na Umayyawa da Abbasawa .
Irin misalin wannan cusgunawa tana bukatar a samu wata hanyar lumfasawa daga wannan matsi mai tsanani kuma wannan lumfasawa domin samun sauki tana iya kasancewa ta hanya mai kyau, wani lokaci kuma tana iya kasancewa ta hanya maras kyau kamar zagi. Sai dai mu ba muna cewa yin zagin daidai ba ne a kowane hali kuwa kamar yadda ya gabata.
b- Kuma wanda ya assasa wannan al'amari su ne Umayyawa su da kansu domin sun zagi Ali (a.s) a kan mimbari suka kuma zagi Ahlul-baiti (a.s) tsawon shekaru tamanin, kuma wannan yanayi ya ci gaba duk da kuwa kokarin da wannan mutum mai kirki Umar dan Abdul'aziz ya yi na ganin ya kawar da wannan zagi amma bai ci nasara ba, kuma maganganun Banu Umayya musamman Mu'awiya sun riga sun karfafa cewa sun assasa wannan zagin ne domin yaro ya girma a kansa kuma babba ya tsufa a kansa, sai aka samu wannan zagi da ake tuhumar Shi'a da shi domin su yi ramuwar gayya. Kuma idan mutum ya zurfafa sosai zai ga cewa an samukarkatar hanyar warware wannan matsala wajen wasu malaman Sunna. Muna iya ganin misalin dan Taimiyya yana wallafa littafin nan na "Takobi zararre a kan kafirta duk wanda ya zagi Annabi (s.a.w) ko daya daga cikin sahabbai", yana kuma kawo dalilai a kan kafirta wannan zage-zage da ake yi sai dai duk da ya san Mu'awiya ne ya assasa wannan zagin da Umayyawa da zagin da suka yi wa Imam Ali da Ahalin gidansa da la'antar su, amma bai kafrita su ba. Aliyyu dan Abi Dalib (a.s) dan'uwan Annabi (s.a.w) ne kuma ya bayar da komai nasa wajen yin hidima ga musulunci da musulmi amma saboda me wanda yake zaginsa ba ya kafirta? A nan ne zaka ji wani jawabi mai ban mamaki ai ya tuba kuma Allah ya gafarta masa shi ke nan wai an warware wannan matsalar!!
Duba wani misalin: Yayin da Yazid dan Mu'awiya ya hau kan hukunci na shekaru uku kawai a shekarar farko ya kashe Imam Husain (a.s) da ahlin gidan Annabi (s.a.w) kuma ya ribace iyalinsu ya kuma yanka 'ya'yansu kuma ya yi musu abin da ko kisra da kaisar ba zasu yi musu ba.
A shekara ta biyu ya kashe musulmi dubu goma da makaranta Kur'ani dari bakwai daga sahabbai, sannan kuma ya halatta Madina kwana uku, ya ba wa rundunar Sham damar su keta mutuncin musulmai, ya yanka iyaye da yaransu, har sai ka ga sojan Sham ya dauki mai shan nono daga hannun uwarsa ya buga kansa a kan bango har sai kwakwalwarsa ta yi tarwatsi a kan bango, sannan kuma ya tilasta mutane yi wa Yazid bai'a a kan cewa su bayinsa ne, kuma ya tsorata Madina ya firgita mutane sannan kuma ya mayar da wannan gari na Annabi mai haske zuwa ga wata fadama da ta lalace da jini kaca-kaca.
A shekara ta uku kuwa ya sanya wa Ka'aba majaujawa kuma ya rusa ta kuma ya kona ta, sannan ya rusa rukunanta sannan ya yi yaki har cikin masallaci mai alfarma ya zubar da jini har sai da ya kwarara a Ka'aba, kuma mai litttafin "Tarihin Hamis" da "Diyarul Bakari" da "Dabari" da "Ibn Asir" da Mas'udi a "Murujuzzahab" da wasunsu na daga malaman tarihi sun kawo wannan dalla-dalla cikin bayain abubuwan da suka faru a shekarar sittin da daya har zuwa sittin da uku tahijira.
Amma duk da haka sai ka samu wasu da yawa daga malaman Sunna suna nuna kuskuren wanda ya fito domin yakar Yazid kuma suna ganin fitowa domin yakarsa fita ce daga addini, kai har wasu ma suna kai da nuna kuskuren Imam Husain (a.s) shugban samarin aljanna, kamar kai ka ce lokacin da Annabi (s.a.w) yake cewa: "Hasan da Husain (a.s) su ne shugabannin samarin 'yan aljanna" bai san zai yaki Yazidu ba ne, kuma lokacin da Annabi (s.a.w) yake cewa: "Hakika Husain (a.s) da sahabbansa zasu shiga aljanna ba tare da wani hisabi ba " kai ka ce bai san cewa zasu yaki Yazidu ba. Kai Allah ka shiryi mutanenmu! kai ka ce Ibn Arabi Almali ya fi Annabi (s.a.w) sanin makomar al'amura ne da yake nuna wa Husain (a.s) makomar al'amura kuma yana umartarsa da ya zartar da hakan!
Wai zuwa ga wane kaskanci da tabewa ne wannan duniya zata kai mutanen!
Sai mu ga Gazali a cikin abin da ya kawo irin wadannan abubuwan alhalin kuwa ga shi a gabansa akwai gomomin litattafai na tarihi da suke da karfafan hanyoyi amintattu kan al'amarin Yazid da ayyukansa. Sai ga shi amma a littafinsa na Ihya'ul ulum yana cewa game da la'antar Yazid:
Idan aka ce: Shin ya halatta a la'anci Yazid domin ya kashe Husain (a.s) ko kuma ya yi umarni da hakan? Sai mu ce: Wannan bai tabbata a bisa asali ba, don haka bai halatta ba a ce shi ne ya kashe shi ko kuma ya yi umarni da hakan matukar hakan bai tabbata ba, balle kuma a la'ance shi, domin bai halatta ba a danganta wa wani musulmi babban laifi ba tare da wani tabbaci ba, har dai yake cewa: Idan aka ce yaya fadin cewa "Allah ya la'anci makashin Husain (a.s), ko kuma wanda ya yi umarni da kashe shi" sai mu ce: Abin da yake daidai shi ne a ce: Wanda ya kashe Husain (a.s) idan ya mutu kafin ya tuba to Allah ya la'ance shi .
Don Allah mai karatu shin tunaninka zai iya jore wa jin wani yana fadin irin wadannan kalamai da suke zowa daga irin wannan mutumim!? Shin litattafan tarihi da suke hannun musulmi wadanda suka zo da wadannan al'amura da suka faru da umarnin Yazid kai tsaye dukkansu ba sa iya tabbatar da ayyukan Yazid ko kuma su hukunta shi su soke shi?! A wajensa yana ganin Yazid da ire-irensa makasa annabawa da 'ya'yan annabawa duk suna samun dacewar tuba?! Kuma duk wata hanya ba ta iya tabbatar da sukan Yazid gun Gazali, sai dai kawai abin da yake tabbata gunsa shi ne ya ga Yazidu ya hadu da Allah ya sanya hannunsa a kan hannunsa, kuma ya yi masa magana, kuma ya kwarara masa haskensa, da gafararsa .
Mai littafin Miftahussa'adati yana cewa: Abubakar Nassaj ya yi shisshigi kan al'amarin Gazali a kabarinsa ya fito yana mai jirkitaccen launi, sai suka tambaye shi me ya faru. Sai ya ce; Na ga wani hannun ne na dama ya fita ta bangaren alkibla, kuma na ji wani mai shela yana kira cewa dora hannun Muhammad Gazali a kan hannun shugaban manzanni . Sai ga irin wannan ya isa ya tabbatar da hujja a irin wannan, amma dukkan litattafan tarihi dukkansu ba sa iya tabbatar da wata hanya guda daya da zata soki Yazid!..
Kai al'amari ya kai ga jifan alayen Annabi da fita daga kan hanya, balle kuma share fagen zaginsu. Sai ga Ibn khaldon a mukaddimarsa yana cewa: Ahlul-baiti (a.s) sun fita daga hanya da kirkiro wata mazhaba da suka kago ta, suka kuma kadaita da ita a kan sukan wasu daga sahabbai, da kuma fadinsu na ismar imamai da kuma kawar da sabani daga zantuntukansu, kuma dukkan wannan asasi ne maras tushe.
Yana fadin haka alhalin ga hadisan Annabi (s.a.w) a game da Ahlul-baiti (a.s) a gabansa da Ibn hajar ya ruwaito a littafinsa na Sawa'ikul Muhrika cewa: "A cikin kowane zamani akwai masu adalci daga adalai daga Ahlin gidana da suke kore wa wannan addini karkatar batattu da hanyar mabarnata da kuma tawilin jahilai, ku saurara hakika jagororinku su ne masu zuwa ga Allah, sai ku duba wanda zaku zo tare da shi (a matsayin shugaba a ranar lahira".
Haka nan yana ganin abin da Hakim ya ruwaito a littafinsa na Mustadrak mai cewa: "Wanda ya so ya rayu irin rayuta kuma ya mutu irin mutuwata ya shiga aljanna da Ubangijina ya yi mini alkawarinta, ita ce aljannar dawwama to ya jibanci Ali da zuriyarsa bayana, hakika su ba zasu fitar da ku daga shiriya ba, kuma ba zasu shigar da ku kofar bata ba .
Amma duk da haka sai ya kira Ahlul-baiti (a.s) masu fandarewa masu bidi'a a nazarin ra'ayin Ibn khaldon, Allah ya sani, da zan zo da irin wadannan misalai da zan sanya hannu ne kawai a kan mikin da ya halakar da mu yana kunkuna ga zukata shekaru masu yawa. Kuma irin wadannan matakai na sukan juna ba komai suke zurfafawa ba sai sabani, don haka ne ma ambatonsu wani lokaci yake zama ba daidai ba.
Marubutan musulmi suna da nauyi a kansu na tsayawa kan wannan al'amuran da wadanda suka rubuta su suka mutu suka bar abin da yake bala'i a kan musulmi. Kuma wani abin mamaki a nan shi ne; shirun malamai da marubutan musulmi a kan irin wadannan maganganu na Ibn Khaldon da waninsa tare da samun dalilai masu karfi a kan cewa alayen Muhammad (s.a.w) su ne ci gaban wannan sako da ya zo da shi. Hada da cewa dukkan wannan ya zo a cikin sunnoni da aka ruwaito a tafarkin Ahlul-baiti (a.s) da ba a aiki da su alhalin ana aiki da bidi'o'in da istihsan ya zo su a tafarkin wasunsu, ka riki misali mas'alar kiran salla da aka cire wata fakara a cikinsa ta "Hayya ala khairil amal" tare da tabbatarta da cewa ya tabbata cewa ita wani yanki ne na kiran salla ta hanyoyi masu yawa.
Mai littafin Maba'di'ul Fikihu game da hakan yana cewa: Ga yadda ake kiran salla: Allahu akbar, allahu akbar, allahu akbar, allahu akbar, ash'hadu an la'ilaha illal-Lah, ash'hadu an la'ilaha illal-Lah, ash'hadu anna muhammadar rasulul-Lah, ash'hadu anna muhammadar rasulul-Lah, hayya alassalat, hayya alassalat, hayya alal falah, hayya alal falah, allahu akbar, la'aila illal-Lah. wannan shi ne kiran sallar da mutanen Basara da na Kufa suka hadu a kansa, kuma mutanen Sham da Misira suka bi su a kai, kuma shi ne mazhabar mutane Hijaz da Zaidiyya da Malikiyya, sai dai su a wajensu kalmar Allahu akbar sau biyu ce a kiran salla ba sau hudu ba, kuma a kan wannan ne mutanen Madina suke. Amma kalmar "Assalatu khairun minan naum" ba kiran salla ba ce na shari'a tun asali: A cikin littafin 'Taisirul wusul" ya zo daga Maliku cewa: Labari ya zo mini cewa mai kiran salla ya zo wajen Umar dan Khaddabi, yana yi masa kiran sallar asuba, sai ya samu yana bacci, sai ya ce: Assalatu khairum minan nau. Sai Umar ya umarce shi da ya sanya ta a cikin kiran sallar asuba! Don haka ne ma Abuhanifa ya ce: Wannan jumlar ana dada ta ne bayan kammala kiran salla, domin ita ba ta daga Sunna.
Amma kalmar "Hayya ala khairul amal" a mazhabar Ahlul-baiti (a.s) tana tsakanin "Hayya alal falah" da "Allahu akbar" ne. Dalilinsu kan hakan daga Sunna shi ne: Baihaki ya ruwaito a cikin Sunan dinsa cewa Aliyyu bn Husain -Zainul abidin- (a.s) ya kasance idan ya ce: "Hayya alal falah" to yana cewa kuma "Hayya ala khairul amal", yana cewa haka kiran sallar farko yake.
Kuma ya zo a cikin sharhin Tajrid kamar dai irin wannan ruwaya daga Bin Abi Shaiba sannan sai ya ce: Bai kamata ba a dauka a fadinsa wannan shi ne kiran sallar farko da cewa shi ne kiran sallar Manzon Allah (s.a.w), ya kuma dada kawo wata ruwaya daga Ibn Umar ya ce: Tayiwu ya dada wannan yanki na "Hayya ala khairul amal" a kiran sallarsa ne. kamar yadda Baihaki ma ya kawo wannan ruwaya daga Ibn Umar.
Ibn wazir ya karbo daga Al'muhib Dabar AsShafi'i a littafinsana "Ihkamul Ahkam" kamar haka: Ambaton hai'ala wato; "Hayya ala khairul amal" ya zo daga Sadaka dan Yassar daga Ibn Umama Sahal dan Hanif cewa idan zai yi kiran salla yana karawa da "Hayya ala khairul amal", Sa'id dan Mansur, ya karbo shi, kuma Ibn Hazam ya ruwaito daga littafin al'ijma daga Ibn Umar: Cewa ya kasance yana cewa "Hayya ala khairul amal".
Ala'uddin Mugaldaya Alhanafi ya fada a littafinsa na "Attalwih" sharhin jami'us sahih: Kamar haka: Amma "Hayya ala khairul amal" Ibn Hazam ya ambaci cewa ya inganta daga Abdullah dan Umar da Abi Umama Sahala dan Hanif cewa suna ambaton ta a kiran sallarsu "Hayya ala khairul amal", kuma aliyyun dan Husain yana yin hakan, kuma Sa'aduddin Taftazani ya ambata a hashiyar sharhin "Al'adhudi ala mukhtasaril usul" na Ibn Hajib cewa "Hayya ala khairul amal" ta kasance a lokacin Annabi (s.a.w) kuma Umar shi ne ya takura mutane su daina wannan, jin tsoron kada su yi rauni gabarin jihadi su dogara da yin salla kawai.
Ibn Hami ya fada a littafinsa: Kuma Ruyani ya kawo daga Shafi'i wata magana mash'huriya game da shi da ya fada game da "Hayya ala khairul amal", kuma da yawa daga malaman malikiyya da wasunsu na hanafiyya da Shafi'iyya sun ambaci cewa "Hayya ala khairul amal" tana daga lafuzzan kiran salla.
Zarkashi yana fada a littafin "Baharul Muhid": Daga cikin abin da aka yi sabani a cikinsa kamar sabanin da aka yi ne a cikin waninta, Ibn Umar ya kasance madogarar mutanen Madina yana ganin "Hayya ala khairul amal" daga cikin kiran salla yake .
Bayan dukkan abin da muka ambata da kuma abin da ya zo a cikin wannan fasali da aka karfafa da ruwayoyi ingantattu a tafarkin Ahlus-sunna don me ya sa ba a aiki da abin da ya zo daga alayen Muhammad da tafarkinsu na Sunna sahihiya tare da cewa su ne masaukar rahamar Allah kuma gidajensu ne masaukar wahayi, kirazansu kuwa jakar ilimin Annabi (s.a.w), shin wannan ba ya kawo wata dimuwa?
A yayin da muke ganin waninsu na hukunce-hukunce da ba sa iya haduwa da madogara kubutacciya ingantacciya amma duk da haka ana riko da ita, kuma ana ganin ta wata madogara, to duk irin wannan da me za a fassara shi. Muna neman tsarin Allah daga nisanta daga alayen Muhammad wadanda suke daidai da littafin Kur'ani a nassin da ya zo daga Annabi (s.a.w). Duba misali ka gani mana fadin wasu daga malaman Sunna suna cewa idan mutum ya bar salla da gangan to ba wajibi ba ne gareshi ya rama ta, amma idan ya bar ta da mantuwa to wajibi ne ya rama ta . Ina ganin wannan ya fita ne daga ra'ayin mai cewa ba a kallafa wa kafiri da aiki da rassan addini ba, domin mai barin ta da gangan tayiwu ya kasance ya bar ta saboda rashin imani da ita tun asali shi kafiri ne, ko yaya dai wannan rassan suna nesa da ruhin hukunce-hukunce ingantattu.
Babi Na Biyu
A Cikinsa Akwai Wasu Fasaloli
Fasali Na Farko: Farisancin Shi'anci
Wannan maudu'i yana daga cikin maudu'ai da aka fiye yawaita magana a kansu, kuma a bisa hakika ana neman kange Shi'anci ne kawai kamar yadda a baya na yi nuni da hakan. Masu gaba da Shi'a da dukkan wanda ya bi su na daga mustashrikai da dukkan wani mai neman ganin bayan Shi'a sun sanya wannan lamari ne da suka yarda da shi kuma suka reni dalibansu da su yi riko da shi, kuma suka yi duk wani kokari ta kowace hanya domin ganin sun karfafa wannan lamari da dasa shi a cikin tunanin mutane, kuma ba su bar wata hanya ba domin tabbatar da Farisancin Shi'anci sai da suka yi amfani da ita. Wani abin mamaki shi ne har yanzu wannan kage ba a daina yayinsa ba tare da bayyanar gaskiyar lamari da yaduwar ilimi da bayyanar gaskiya karara, don haka ne ma zan yi bincike kan wannan dalla-dalla saboda muhimmancinsa.
Shi'anci a ma'anar lugga yana nufin taimakekeniya da kuma kaunar juna, da jibantar lamarin juna, amma a isdilahi ana nufin imani da wasu akidu da suka hada akidun Shi'anci kamar riko da Ahlul-baitii (a.s), idan kuwa haka ne yaya za a yi Shi'anci ya kasance bafarise?
Domin mu tattaro dukkan bayanan da suka shafi wannan al'amari ba makawa mu yi sharhi da bayanin wasu bayanai kamar haka:
Na daya: Abin da Shi'anci ya kunsa gaba daya shi ne musulunci, kuma duk wani abu da ya fita daga musulunci da ya shafi akida da hukunci to Shi'anci ya barranta da shi saboda madogarar Shi'anci abubuwa hudu ne a jere:
a- Littafin Allah Mai Tsarki:
Shi ne abin da aka saukar da lafuza na musamman da usulubinsa kebantacce kuma aka kuma dauke shi a matsayin Kur'ani, kuma shi ne tattararrun wadannan takardu tsakanin bangwaye biyu wanda yake hannun musulmi kuma ya tsarkaka daga tawaya da jirkitawa wanda barna ba ta zo masa ta bayansa da kuma ta gabansa kuma kalmominsa mutawatirai ne kuma haruffansa sun zo bisa yakini tun lokacin Annabi mai daraja har zuwa yau wannan zamani, kuma an hada shi tun lokacin Annabi kamar yadda yake din nan, Jibril (a.s) yana karanta masa shi kowace shekara .
b- Sunna Madaukakiya:
Ita ce maganar ma'asumi ko aikinsa ko tabbatarwarsa wacce ta zo mana ta hanya ingantacciya daga amintattun adalai, wacce ba zamu iya fahimtar hukuncin shari'a ba sai da ita, kuma dalili ya zo daga Kur'ani a kan cewa hujja ce a fadinsa madaukaki: "Abin da Manzo ya zo muku da shi to ku rike shi, abin da kuma ya hane ku to ku hanu" Hashri: 7.
c- Haduwar Malamai:
Wannan shi ne haduwar dukkan malamai da take nuna cewa akwai yardar ma'asumi a cikinta, kuma masu haduwar suna da yawa ko kuma ba su da shi, kuma yana nuna dalili ne na Littafi ko Sunna ko hankali, ko kuma akwai wata hanyar da take nuna mana yardar ma'asumi, wacce take dalili ne daga Littafi ko Sunna ko Hankali ba.
d- Dalilin Hankali:
Wannan yana komawa zuwa ga hankali da dokokinsa yayin da aka rasa nassi ko kuma dalilai suka yi karo da juna kamar yadda aka yi sharhi a mahallinsa. A takaice: Shi ne riskar hankali a matsayinsa na hankali ga abin da yake kyakkyawa da mummuna a cikin sashen wasu ayyuka da suka lizimci riskar hankali garesu da hankula suka hadu a kansa, wannan kuwa sakamakon halittar hankali a kan hakan, kuma tunda mai shar'antawa shi ne shugaban masu hankula to lallai ya tabbata yanke cewa ya zartar da hukuncin shari'a game da hujjar hankali.
Duba zuwa ga sanin muhimmancin wannan madogarai dalla-dalla to zan wakilta wanda yake son bayaninta da fadi zuwa ga wasu litattafai masu zuwa :
Cewa wadannan madogarai kuma litattafai na shar'antawa su ne suka hada kashin bayan shari'a da ittafakin dukkan musulmi bisa sabani mai sauki game da bayananta dalla-dalla, kuma tun da madogarar shar'antawa gun Shi'a su ne wadannan to babu ma'anar Farisancin Shi'anci.
Idan masu bincike suna nufin Farisancin Shi'anci da cewa dukkan akidunsa ne. to wannan wani abu ne da nake korewa kuma nake nisantarwa, kuma ban ga wani wanda zai iya yin wannan da'awar ba, domin ba yadda za a yi wani ya yi tsammanin kawo hukuncin shari'a daga kabilanci, don haka ne ma masu kawo batun Farisancin Shi'anci sai dai su kawo wani abu daban ba wannan ba.
Akwai wasu masu tunanin cewa ma'anar farisncin Shi'anci shi ne; akwai wani irin ci gaban al'adu da wayewar Farisanci da ta shiga cikin Shi'anci kamar yadda yake bisa ma'anarsa ta isdilhi ta hannun wadanda suka karbi Shi'anci daga Farisawa kuma ba su fahimci Shi'anci ba, amma sai aka samu wasu bangare na akidunsu suka shiga Shi'anci, kuma ta wanzu cikinsa tun daga kakanni har zuwa jikokinsu. Wannan kuwa wani abu ne da wasu suka kawo shi, sai dai nan gaba kadan zamu yi nuni zuwa ga irin wasu ra'ayoyi kamar haka:
Rufewa
a- Idan wannan ne ake nufi da Farisancin Shi'anci to sai wannan ya shafi dukkan musulunci ne domin kuwa dukkan mafi yawan wadanda suka yi rubutu game da musulunci musamman a zamanin farko na musulmi wanda suka kunshi abin da a yau ake ganinsa akidarsa wanda ya faru sakamakon shigowar al'ummu zuwa ga musulunci wadanda suke dauke da tunani da akidu mabambanta jama'a-jama'a kuma ba su yarda wannan akidun nasu ba da al'adunsu mafi yawa wadanda suka hada da Rumawa da Farisawa da mutanen kasar Sin, da Ibrawa, kai har da ma wasu jama'a daga Yahudawa da wadanda dukkaninsu sun bayar da gudummuwa mai tasiri cikin ci gaban al'adun musulunci a fagage daban-daban. Kuma wannan ya faru ne ta hanyar tafsirin addini da kissoshin addini, domin su ma ma'abota Littafi ne, kuma a cikinsu akwai malamai masu dauke da hukuncin Attaura da kissoshin al'ummu da suka kiyaye na Ibrawa da labaru da kissoshi, kuma a wancan lokacin yankin Larabawa ya kasance yana kishirwar tunanin addini da abin da ya kunsa wanda al'adar Yahudawa ta taka babbar rawa a cikinsa domin cike wasu gurabu musamman a sunnanci wanda yake neman cire wannan riga domin ya yafa wa Shi'a ita, ta hannun tatsuniyar da aka kirkiro ta Abdullah dan Saba, sai dai bincike ya nuna abin da suka yafa wa Shi'anci su ne suke da shi.
Ra'ayoyin Yahudawa sun shigo musulunci ne ta hanya Ka'abul Ahbar da Wahabu dan Munabbah, da Abdullah dan Salam, da wasunsu, kuma suka samu wajen zama a litattafan tafsirai da hadisai da tarihi, kuma sun bar kufansu a cikin hukuncin shari'a. Kuma duk mai bincike yana iya bincikawa zai ga wannan da yawa a litattafai kamar "Tarihin Dabari", da tafsirinsa "Jami'ul Bayan", da littafin "Buhari" da sauran litattafai kamar yadda zamukawo nan gaba, kuma zaka samu wannan dalla-dalla kamar yaki da gabar mutum da macijiya da Dabari ya kawo a tafsirinsa da sanadinsa daga Wahab dan Munabbah, da kuma tafsirin nan na aya ta talatin da shida a surar Bakara a fadinsa madaukaki: "Muka ce ku sauka daga gareta sashenku makiya ne ga sashe…". Tabari yana cewa: Ina ganin wannan ne ya sanya yaki tsakaninmu da macizai, asalinsa kamar yadda malamanmu suka ambata a ruwayarmu daga garesu na shigar da Iblis aljanna ne da macijiya ta yi. Ya ci gaba da kawo wannan labari mai ban mamaki yana cewa a tafsirinsa game da bayanin ragon da aka yanka fansa da Ibrahim ya yi ga dansa Isma'il da umarnin Allah (s.a.w) da cewa ragon nan da Ibrahim ya yanka shi ne wanda dan Annabi Adam (a.s) ya gabatar ba a karba daga gareshi ba .
Yana kawo labaru masu mamaki a tarihinsa mai nuna cewa akwai yahudanci ciki, kamar yadda ya kawo yana mai cewa: Ishak (a.s) ya auri wata mata sai ta samu cikin yara biyu a cikin daya, lokacin da ta so ta haife su, sai yaran suka yi gaba, sai Yakub (a.s) ya so ya fita kafin Isu, sai Isu ya ce: Wallahi idan ka fita gabanina, to sai na fasa cikin mahaifiyarmu na fita kuma sai na kashe ta, to sai Yakub (a.s) ya yi baya Isu kuma ya fita kafinsa, sannan sai Yakub (a.s) ya fita. Don haka sai aka kira Isu da sunansa da yake nufin wanda ya saba, shi kuma Yakub (a.s) da sunansa da yake nufin wanda ya jinkirta, domin ya jinkirta bayan Isu. Sai yaran suka girma, kuma Isu ya fi soyuwa wajen babansu, shi kuma Yakub (a.s) ya fi soyuwa wajen babarsu, kuma Isu yana yin farauta ne. yayin da Ishak ya makance sai ya ce da Isu ka ciyar da ni naman farautarka ka kuma kusance ni domin in yi maka addu'a, Isu ya kasance yana da yawan gashi, Yakub (a.s) kuma ba shi da yawan gashi. Sai Isu ya fita yin farauta, sai mahaifiyar Yakub (a.s) ta ce da shi ka yanka rago ka gasa sannan ka sanya rigarsa ka kawo wa babanka domin ya yi maka addu'a, da ya zo sai babansu ya shafa shi sai ya ce: Waye? Sai ya ce: Isu. Sai ya ce: Jiki irin na Isu amma gashi irin na Yakub (a.s), sai babarsa ta ce: Shi ne danka Isu, sai ka yi masa addu'a… har zuwa karshen kissa .
Ban sani ba, yaya Ishak (a.s) ya kasance bai san muryar 'ya'yansa ba! Kuma yaya babarsa zata nemi albarka daga addu'ar Ishak tana mai yin karya, yaya kuma 'ya'yanta zasu yi karya, kuma wane Annabi ne wannan da gidansa yake irin wannan gidan, sannan kuma wane irin bayar da ma'anar sunaye ne aka yi wa wadannan 'ya'ya da aka cirato daga asalin wadannan kalmomin.
Amma a littafin Buhari kana iya ganin isra'iliyanci a wasu ruwayoyinsa, duba ka ga wasu misalai daga wadannan ruwayoyi domin ka gani a fili:
Buhari da sanadinsa daga Abuhuraira yana cewa: Babu wani Annabi sai shedan ya shfe shi lokacin da za a haife shi sai ya fado yana mai kuka banda Maryam da danta . Ban sani ba idan wannan falala ce, to don me aka hana annabinmu alhalin shi ne; shugaban annabawa, kuma idan ba matsayi ba ne to mene ne amfanin kawo shi, kuma mene ne laifin sauran annabawa da shedan zai shafe su.
Buhari ya kawo da sandinsa zuwa ga A'isha uwar muminai cewa an yi wa Annabi (s.a.w) sihiri har sai da ya kasance yana ganin kamar ya yi wani abu, amma bai yi shi ba .
Kuma Buhari ya ruwaito a kissar Musa (a.s) yayin da mala'ikan mutuwa ya zo domin ya karbi ransa sai ya mare shi a kan idanuwansa sai ya cire daya… har sai da Allah ya ce da mala'ikan mutuwa koma zuwa gareshi ka ce masa ya dora hannunsa a kan fatarsa, yana da yawan shekarun da tafinsa ya rufe na adadin yawan gashi .
A bisa hakika wannan al'amarin yana da mamaki, domin gashin da hannun tafinsa zai rufe zai iya kaiwa zuwa dubu biyar, kuma shekarun annabin Allah Musa sanannu ne, imma dai wanan ruwaya ta kasance karya, imma kuma mu karyata tarihi.
Buhari ya karbo daga ummul muminin A'isha cewa Annabi (s.a.w) ya zauna kwanaki kaza yana ganin kamar ya zo wa iyalansa amma bai zo musu ba, har dai ya ce: Ya ke A'isha Allah ya yi mini bayanin wani abu da nake tambayarsa da wasu mutane suka zo min daya ya zauna gun kaina dayan kuma gun kafafuna, sai wanda yake gun kafafuna ya ce da dayan, me ya samu mutumin ne? sai ya ce; an yi masa sihiri, sai ya ce: Waye ya yi masa? Sai ya ce; Lubaid dan A'asam… har dai sammun da aka yi masa ya tafi bayan tsawon lokaci .
Wato; wannan ruwaya tana nuna cewa Annabi ya rasa hankalinsa ba ya iya gane lokacin da ake yi masa wahayi har tsawon lokaci, idan kuwa ya halatta Annabi ya samu irin wannan rashin lafiyar to yaya kuwa za a aminta da wahayi, kuma ko yaya dai wannan nauyi yana kan mai ruwaya da Buhari, kuma littafin Buhari yana kunshe da irin wannan nau'i na akidun isra'iliyanci kamar dai na abin da ya ambata a babin neman izini, a babin yin farawa da sallama, ya ce:
Da sanadinsa daga Abuhuraira daga Annabi (s.a.w) Allah ya halicci Adam (a.s) a bisa kamarsa ne, tsayinsa zira'i sittin yayin da ya halicce shi sai ya ce masa tafi ka yi wa wadancan jama'ar na mala'iku da suke zaune ka ji yaya zasu gasihe da kai domin ita ce gaisuwarka da kai da zuriyarka, sai ya ce: Asslamu alaikum. Sai suka ce: Assalamu alaika wa rahmatul-Lah, sai suka kara wa rahmatul-Lah. Don haka dukkan wanda zai shiga aljanna yana kasancewa kamar girman Annabi Adam (a.s) ne, kuma halittu ba su gushe ba suna raguwa har yanzu .
Da sauran dai ruwayoyi irin wadannan wadanda suke da yanayi na nisanta daga musulunci saboda jingina wa Allah jiki, amma duk da haka ba mu samu mai jifan wadannan tunani da cewa fita ne daga musulunci ba ko kuma yahudanci ne, duk da cirato wannan da suka yi daga isra'iliyanci zuwa musulunci, amma da mutum zai yi Shi'anci nan da nan sai a ga shi'ancinsa yahudanci ne ko nasaranci, kuma duk wani mummuna da shara sai a watsa ta kansa tare da cewa duk wani laifi da wani ya yi yana kansa ne, kuma mun riga mun nuna cewa duk wani abu da ya kore musulunci to Shi'anci yana kin sa gaba daya.
Idan ma mun kaddara cewa akwai wasu fikirori da farisawan da suka zama Shi'a suka cirato suka taho da su tare da su, kamar fadin cewa akwai hakkin Allah kamar yadda Farisawa suke fada wa game da sarakunansu kuma Shi'a suka fadinsa ga imamansu duk da kuwa akwai bambanci tsakanin wadannan abubuwan biyu, to duk wannan ba zai zama aibi ba ga akida matukar ta samu asasi da asalinta ne da ta dogare da shi daga musulunci kuma wannan la'amari ne da yake sananne gun Shi'a da suke kiyaye su, ta yadda idan dai ka ga sun yi riko da wani abu to musulunci ne.
Kuma mu muna sane da cewa dukkan asasai da suke iyakance musuluncin musulmi to su ne dai abin da Annabi (s.a.w) da kansa ya iyakanta su da kansa kamar yadda ya zo a sahihul Buhari daga Anas cewa manzon Allah (s.a.w) ya ce: Duk wanda ya yi sallarmu, ya fuskanci alkiblarmu, kuma ya ci yankanmu, to wannan shi ne muslumi, kuma alkawarin Allah da manzonsa sun hau kansa, don haka kada ku keta wa Allah alkawarinsa.
Kamar yadda Buhari ya fitar da wannan daga Ali (a.s) cewa ya tambayi Annabi (s.a.w) ranar yakin Haibar cewa a kan me zan yaki mutane? Sai manzon Allah (s.a.w) ya ce: Ka yake su har sai sun shaida babu wani abin bauta sai Allah kuma hakika Muhammad manzon Allah ne, idan suka yi haka to sun kare jininksu daga gareka .
Imam Ja'afar Sadik dan Muhammad (a.s) yana cewa: Musulunci shi ne shaidawa babu wani abin bauta sai Allah da gaskatawa da manzon Allah kuma da wannan ne ake kare jini kuma a kansa ne ake yin auratayya da gado" . Don haka a bisa zahirin haka ake siffantuwa da musulunci kuma wannan suna yana tabbata ga wanda ya yi kalmar shahada kuma koda bai yi imani da Imamanci da cewa nassi ne daga Allah ba, da kuma cewa hkki ne na Allah, koda kuwa yana ganin imamanci yana tabbata da shura kuma hakki ne na mutane da suke sanya shi inda suka so!
Kai ko da bai yi imani da cewa Imamanci nassi ne ba, kuma ko da ya wuce hakan malaman musulunci ba sa kafirta shi, kuma da yawa daga malamai sun tafi a kan cewa ba a kafirta ko fasikantar da musulmi saboda wani abu da ya kudurce ko ya aikata, kuma dukkan wanda ya yi ijtihadi kan wani sai ya bi abin da yake ganin gaskiya ne, to za a ba shi lada guda biyu idan ya dace, idan kuwa ya yi kuskure zai samu lada daya, kuma wannan shi ne fadin Ibn Abi-laili da Abuhanifa da Shafi'i da Sufyanus sauri da Dawud dan Ali kuma shi ne fadin da yawan sahabbai .
An ruwaito daga Ahmad dan Zahr Sarakhsi, kuma yana daga sahabban Abul Hasan al'ash'ari, kuma a gidansa ne al'ash'ari ya rasu ya ce: Ash'ari ya umarce ni da in tara masa sahabansa sai na tara su sannan sai ya ce: Ku shaida mini cewa ni ba na kafirta wani daga ma'abota alkibla don wani sabo da ya yi domin ni na ga dukkansu suna nuni ne zuwa ga abin bauta daya, kuma musulunci yana hada su yana game su .
To duk bayan wannan al'amari mene ne abin da ya kawo alakanta Shi'anci da yahudanci ko kuma cewa a cikinsa akwai fikirorin Farisanci ko kuma alamomin Farisanci, sannan kuma idan akwai wasu fikirorin da idan mun kaddara cewa wanda suka muslunta sun kawo su kuma sun bi su, ai ba ta wuce wani ra'ayi ne da ya yi riko da shi da wani dalili ko kuma ya zamanto bidi'a kamar yadda muka kawo, kuma ka san ra'ayoyin malamai a kan hakan.
wannan irin wuce gona da iri ne kan musulunci da kuma daukar alhakinsu yana daga kaucewar tunani, kuma da sannu zaka san abin da Shi'a suka tafi a kansa daga Littafi da Sunna, kuma koda wasu sun dauka sun samu ne daga Farisawa sakamakon karancin saninsu ko kuma mummunan nufi da suke da shi, kuma Allah ne magani kan komai.
c- Wannan irin da'awar da ake yi ta Farisancin Shi'anci zamu tabatar maka da cewa al'amarin akasin haka ne, kai idan ma ta inganta to ba laifi idan dai bafarise ya kasance musulmi kuma mu muna ganin a addinin musulunci babu kabilanci, kuma takenmu shi ne: "Ya ku wadanda suka yi imani mu mun halitta ku daga namiji da mace, kuma muka sanya ku jama'u da kabilu domin ku san juna, hakika mafi girmanku a wajen Allah shi ne mafi tsoronku gareshi" Hujurat: 13.
Don haka ne ma wannan mataki ya yi daidai da na musulunci kuma idan muna magana ne ta kabilanci to da sai mu kebanta da luggarmukawai kuma babu wata lugga da zata kasance mun yarda dai ta, tare da cewa hankali yana kiran ne zuwa ga girmama mutane da kabilu, kuma maganar Imam Sadik (a.s) ta kayatar matuka a nan yayin da yake cewa: Ba ya daga bangaranci (bangaranci da kabilanci) ka so mutanenka, sai dai ta'asubanci shi ne ka sanya ashararan mutanenka sun fi zababbun wasu mutane da ba su ba.
Musulunci ba ya bambancewa tsakanin wani jinsi da wani, kuma ba ya la'akari da musulmi don yana da wani yare kawai, amma idan dai mai magana yana fakewa ne da yare karkashin wata manufa daban da yake da ita, to lallai wannan mutumin da yake ganin mutane kamar gafalallu shi ne hakikanin gafalalle, kuma nan gaba kadan zamu ga hadafin irin wadannan mutane da suke da wannan raye-rayen.
Akwai kuma wani abu daban cikin tasawwurin Farisancin Shi'anci kuma shi ne cewa dukkan ko galibin Shi'a Farisawa ne, kuma Farisancinsu ya yi galaba a kansu har sai da ya mamaye Shi'anci kuma wannan yakan kai ga karo da shari'ar musulunci saboda sabawarsa da wadannan akidoiji na musulunci kamar yadda suka raya, kuma wasunsu ma sun shelanta hakan a fili kamar yadda nan gaba zamukawo hakan cikin wasu ra'ayoyi a kan wannan, kuma da sannu zaka ga wannan ra'ayi cewa barna ne ba daidai ba ne, kuma dukkan wanda ya san tarihin musulmi da akidunsu ya san ba haka ba ne, kuma ya san hakan batacce ne saboda wasu dalilai kamar haka:
a- Akidun Shi'a sun cika litattafai masu yawa wadanda su ne madogara, kuma kowa yana iya dauka ya karanta, kuma suna hannun marubuta da masu bincike a dukkan laburorin duniya, kuma madogarar akidun Shi'a su ne; littafin Kur'ani da Sunna da ijma'I da hankali kamar yadda ya gabata, kuma mun yi nuni zuwa ga litattafai da suka yi bayanin hakan dalla-dalla hada da littafin 'awa'ilul makalat' na sheikh Mufid, da aka'id na Saduk da durar da gurar na sayyid murtadha, da a'ayusshi'a na sayyid muhsin al'Amin, da kuma litattafan hadisai da kuma litattafai hudu wadanda Shi'a suka dogara kansu a jumlace wadanda suka hada da "Man'la' yahdhuruhul fakih", na Saduk, da "Usulul Kafi" na Muhammad kulaini, da "Tahzib" da "Istibsar", na sheikh Dusi, tare da cewa ba duk abin da yake cikinsu ba ne ya inganta gunmu.
b- Sannan kuma farisawa wani yanki ne kankani na yawan Shi'awan da suke wannan duniya tamu, wadanda suka hada da Larabawa, da Indiyawa, da Turkawa, da Afganawa, da Kurdawa, da Mutanen kasar Sin, da mutanen Tibet, da sauransu, don haka ke nan Farisawa wani bangare ne kawai.
c- Sannan kuma inda aka kafa dashen irin Shi'anci duk yana yankin Larabawa ne na jazirar Larabawa, kuma a 'yan shi'ar farko babu wani daga wanda ba balarabe ba sai mutum daya wanda yake shi ne salmanul muhammadi kamar yadda Annabi (s.a.w) ya ambace shi wanda shi bafarise ne. kuma an ambace shi a cikin dabaka ta farko na Shi'a wadanda suke daga kabilu daban daban, kuma idan ka bi dabaka ta biyu da ta uku na Shi'a duk zaka samu mafi galibinsu duk Larabawa ne, kuma ba na son tsawaitawa a wannan wurin don akwai shi a litattafan tarihi kuma zamukawo maka abin da zai tabbatar maka da hakan a karshen wannan fasali.
Tare da dukkan abin da muka riga muka kawo na bayani to mene ne, kuma ta ina ne Shi'anci ya kasance Farisanci har ma ake daukar wannan kamar wani abu da aka riga aka tabbatar da shi. Don haka ne domin mukawo duk abin da ya shafi wannan maudu'i to ya zama dole ne mu shiga yin bayanai dalla-dalla da kawo ra'ayoyi masu yawa da kuma dalilan da aka kawo don kafa dalili da nuna ingancin wadancan ra'ayoyi.
Kuma ina tabbatar maka idan ka karanta abubuwan da suka zo raunin abin da suka kawo zai bayyana gareka, kuma zaka yi mamakin yadda irin wadannan marubuta duk da suna da ilimi da ba a rena shi amma suka gamsu da abin da suka kawo balle kuma har suna kawo shi domin su gamsar da wanin su saboda son rai da kuma bangaranci, Allah ya tsare mu daga wannan. Wannan kuwa yana daga gamsuwa da wata akidar danne gaskiya da rashin ba wa haske damar haskaka masa akidarsa da abin da ya riga ya dogara a kai har ya ga irin abin da yake haifarwa sakamakon mummunar makauniyar biyayya, sai ya ci karo da dalili mai inganci sai ya watsar da shi, ba ya duba ma'aunan shari'a ya yi riko da su.
Fasali Na Biyu
Maganganun Masu Ganin Farisancin Shi'anci
Magana kan danganta Shi'anci da Farisanci ta kasance ne a zamunan baya-bayan nan ne, kuma saboda wasu dalilai da yanayin siyasa wadanda mafi muhimmcinsu su ne:
Saboda kasancewar Farisawa suna da bakin jini gun Larabawa saboda wasu dalilai daban-daban, kuma saboda Shi'a sun kasance jama'a ce wacce take mai gaba da hukumar lokacin da ya gabata na farkon musulunci a lokacin Umayyawa da Abbasawa.
Kuma ta wata fuska wannan ya faru ne domin ganin an taskace Shi'anci da wanda ake ganin yana da bakin jini gun Larabawa, musamman ma domin ganin Larabawa ba su karbi wannan mazhabi ba, kuma wannan da'awa da ake yi ta taskace Shi'anci da Farisanci daya ce daga cikin kokarin da ake yi na ganin yin zagon kasa ga Shi'anci. Amma dalilan da su masu wannan kage kan Shi'anci suka kawo a matsayin dalilan da suka kai ga kyamar juna tsakanin Larabawa da Farisawa su ne kamar haka:
1- Farisawa ba su kasance suna banbancewa ba tsakanin musulunci da Larabci, kuma tun da musulunci ya kawar da daularsu kuma ya gama da su, to sai suka kasance bayan sun musulunta suna son dawo da martabarsu, kuma suka dauki hanyoyi biyu mai kyau da maras kyau, sai mulkin Umayyawa ya zo ya nemi taimakonsu wajen tafiyar da hukuma domin tsara al'amuran daularsu sakamakon ci gaban da suke da shi na zamani, wani lokaci kuma a kan nemi taimakonsu domin fuskantar abokan gaba yayin sabani, kuma wasu daga cikinsu sun kama manyan mukamai a wadannan lokauta biyu abin da ya sanya su suka samu damar kutsawa cikin daula, kuma wannan ya sanya gaba tsakanin larabawan kansu da kuma Farisawa a daya bangaren, domin Larabawa suna ganin su ne suka dauki sakon musulunci zuwa ga al'umma, kuma su ne wadanda musulunci ya doru ya kafu bisa kafadunsu da wahalarsu domin su shiryar da al'ummu, to don me za a shugabantar da wani a kansu? a gabatar da shi a kansu tauraruwarsa ta yi sama ta filfila a kan tasu? Su sami matsayi mai girma da ba su da shi?
Sai Farisawa suka ga cewa su ne suke da ci gaba mai dadewa kuma sun fi sanin al'amarin siyasar tafiyar da mulki fiye da Larabawa, da tafiyar da al'amarin hukunci da daula, to don me za a gabatar da wanda ba shi da wannan siffofi na cancanta a kansu?. Sai wannan ya kai ga jayayya da gaba tsakanin al'umma, kuma wannan ya bar kufai mai muni a zukata na gaba da juna da kiyayya da mugun kulli tsakanin wadannan al'ummu biyu kamar yadda ya kai ga yin zagon kasa ga juna.
2- Bude wannan fage da samun wannan kafa da sabani da tsagewar bango da Farisawa suka shigo ta cikinsa, ya kai ga shigar wasu mutane da ba Larabawa ba kamar turkawa da wasunsu cikin mukaman daula, kuma wannan ya haifar da mummunan sakamako mai muni kwarai da gaske, kuma sai Sunan Farisawa ya fi baci kan wannan al'amari domin da su ne aka fara wannan asakala, domin su ne farkon wanda ya bude wannan kofa abin da ya kai ga lalacewar halifanci daga baya.
3- 'Yan mulkin kama karya sun iza wutar wannan matuka da gaske wacce suka azuzuta ta, domin tabbatar da maslaharsu ta hanyar bude wannan kofa da fadada ta da kuma kawo kage da karairayi domin karfafa wanan sabanin tsakanin wadannan jama'u biyu da suka dade suna asakala da rashin jutuwa da juna, kuma suka yi amfani da mustashrikai (Turawa masana gabas musamman kasashen musulmi da addinin musulunci) a kan wannan, sai ga shi an samu jama'ar musulmi da suka rayu a kan teburin nan na koyarwar mustashrikai da suke da karancin tunani da hankali sun kama sun fi mai kora shafi, suna tabbatar da wannan da'awowin karyar su. Sai suka sanya irin wadannan musulmi kamar wata wuka ce da ake dukan duk bangarorin musulmi da su domin rusa akidunsa da kawo tashin hankali da fadada sabani tsakanin mabiyansa, har wannan ya bar kufai mai muni mai girma da yake neman ganin bayan duk kokarin da aka yi, a yau ana bukatar wani kokari mai girma domin kawar da wannan asakala.
Dalilan gaba sun kasance suna daga cikin dalilan da ake riko da su domin ganin an kawo kiyayyar Shi'a da kuma kyamarsu. Don haka ne ma ba za ka ga irin wannan tuhuma ga Shi'a a gun yan Sunna na farko ba sakamakon cewa babu irin wadannan dalilai a can baya a wancan zamani. Kuma wani abin mamaki shi ne; harsunan da suka fi kowa zagin Shi'a a wancan zamani -kafin su kansu Farisawa su zama Shi'a- zaka samu harsuna ne na Farisawa kamar yadda zamukawo maka nan gaba kadan.
Masu hadafin cimma maslaharsu sakamakon iza wutar wannan al'amari suna da yawa sai dai mun samu mustashrikai sun fi karfafawa kan iza wannan wutar, sannan kuma sai muka ga dalibansu masu daukar tunani daga garesu daga musulmi suna buga irin wannan gangar da su ma mustashrikai suke bugawa, wato; suna hura wannan wutar ta kyamar Shi'anci da kuma raba masa Farisanci domin cimma hadafinsu da manufarsu, kana iya duba ra'ayoyinsu kamar haka:
1- Mustashriki Duzi:
Mustashriki Duzi yana ganin cewa asalin Shi'anci mazhaba ce mai dauke da tunanin Farisanci, wannan kuwa ya kasance sakamakon cewa Larabawa suna rayuwa ne da 'yanci game da mulki, su kuma Farisawa suna da tunanin mulki da gado, ba su san ma'anar zabe ba, kuma tun da Annabi (s.a.w) ya tafi bai bar mai gado ba, to wanda ya fi kowa cancantar halifanci bayansa shi ne dan amminsa Ali (a.s) .
2- Mustashriki Pan Pulotin:
Wannan ma yana ganin irin ra'ayin da ya gabata ne, kamar yadda ya kawo a littafinsa na "Siyadatul Arabiyya" sai dai yana ganin cewa Shi'a sun riki wannan ra'ayi ne daga Yahudawa fiye da yadda suka karba daga Farisawa, da dokokinsu na asali .
3- Mustashriki Brawon:
Yana ganin cewa: Ba a riki tunanin cewa jagoranci na Allah ne ba da karfi (tsakanin musulmi) kamar yadda Farisawa suka rike shi, kuma sai ya yi nuni da cewa Shi'a sun samu wannan ne daga garesu .
4- Mustashriki Welhozan:
Wannan mustashriki yana ganin cewa Farisanci ya kunshi wani yanki mai yawa na Shi'anci a cikinsa ta yadda ya ambaci cewa sama da rabin mazauna birnin Kufa na daga wadanda ba Larabawa ba duk Shi'a ne, kuma mafi yawansu Farisawa ne .
5- Mustashriki Brukle Man:
Yana cewa: Shi'anci ya kasance abu ne da ya hada dukkan jama'ar da take gaba da Larabawa, kuma a yau kabarin Husain (a.s) ya kasance wuri mafi tsarki gun Shi'a musamman farisawan da ba su gushe ba suna ganin zuwa wannan wuri da tarewa a wurin shi ne babban burinsu da suke son cimma sa . A takaice dai idan mun koma wa bahasin mustashrikai a wannan al'amari zamu ga mutane masu yawa daga cikinsu sun tafi a kan wannan ra'ayi saboda wasu dalilai da ba boyayyu ba ne (ga mai hankali).
Kuma suka fitar da wata natija da suke so sakamakon damfara Shi'anci da Farisanci, kuma wannan sakamakon shi ne: Wato; tunda mafi yawan Farisawa Shi'a ne, kuma ana kiran su 'yantattun bayi, kuma tun da Larabawa sun kwace musu daularsu, kuma tun da daular Umayyawa tana da tunanin Larabawa ne, sai su wadannan 'yantattu suka yi kokairn ganin sun kayar da ita, kuma sun kafa daular Abbasawa wacce ta taimaki Farisawa, wacce tunanin Shi'anci ya shige ta kuma ya karfafa a cikinta sakamakon mulkin Abbasawa, kuma kana iya samun wadannan tunani gun mafi girman litattafan wannan zamani na musulunci musaman marubuta misirawa. Don haka muna iya fitar da natija kamar haka:
1- Sawwala kai harin nan na rundunar da ta zo daga Khurasan domin gamawa da daular Umayyawa da cewa na kabilanci ne, ba don al'umma ko mutuntaka ba ne, kuma wai jama'ar da ta taru mai kabilu masu yawa sun taru ne domin kawar da hankula daga hadafin nan da yake boye karkashin wannan harin.
2- Kuma cewa wuta uwar gami a wannan harin su ne Farisawa, domin su kawo hari na daukar fansa da yake son dawo da kima da martabar Farisawa ne wanda Larabawa suka kawar da shi, don haka ne da wannan sai a shafi babbar rawar nan da Larabawa suka taka wajen samun jagoranci.
3- Kasancewar tunanin Shi'anci yana cikin kwakwalen wadannan makiya da suka ci nasara a lokacin Abbasawa.
Sai dai dukkan wadannan al'amura ne da ba su faru ba, kuma ba za a yarda da su ba, kuma kokarin rufe abin da aka kasa tabbatarwa ne kawai.
Dorawa Kan Maganganun Farko
Ra'a yi Na Farko:
Wannan ra'ayi bai inganta ba saboda cewa wadanda suka jagoranci mutane sun jagorance su ne domin kubutar da su daga zaluncin Umayyawa, kuma duk wani mai bincike yana iya duba tarihin abin da ya wakana domin sanin gaskiyar abin da ya faru na halayen hukumomin Umayyawa wanda yake cike da zalunci tun farko har zuwa faduwarsa a lokacin Marwan dan Muhammad karshen sarakunan Banu Umayya, kuma ina ganin kuskure ne ma mukawo misali daya ko biyu a kan hakan domin dukkanin kwanakin hukuncinsu cike suke da zalunci, kuma ina neman mai karatu ya koma ya bi tarihin tun lokacin Mu'awiya na farko har zuwa karshen daular a litattafan da musulmi suka rubuta duka ba na Shi'a ba kawai. Tayiwu a ce Shi'a suna kin Umayyawa kuma suna jin haushinsu ne, amma sai ga litattafan da Dabari da Ibn Asir, da Ibn Kasir, da Ibn Khaldon, da duk abin da ka ga dama ka duba ka ga abin da suka rubuta inda al'amarin ya kai ga mawaka suna cewa:
Yakinku dai yakinku dai ya ku alayen Harbu
Ya alayen Harbu daga gareku yakinku dai
Daga gareku a cikinku zuwa gareku da ku
Akwai abin da, da mun fada da mun tozarta litattafai
Amma Ra'a yi Na Biyu:
Shi ma ya tabbata cewa karya ne saboda dukkan wadanda suka jagoranci yakin Larabawa ne, kuma Jahiz ya kawo hakan a cikin littafinsa mai Sunan "Manakibul Itra" kuma ya ambaci jagororin yakin kamar: Kahdaba dan Shabib Atta'i, da sulaiman dan Kasir al'khuza'i, da Malik dan Haisam al'khuza'I, da Khalid dan Ibrahim az'zuhaili, da Lahzi dan Darif Almuzni, da Musa dan Ka'abul Muzni, da Kasim dan Mujashi'i Al'muzani, kamar yadda tarihi ya kawo Sunan kabilun Larabawa daban-daban wadanda suke a nan Khurasan wacce ta kasance ta haifar da mafi girma runduran da mafi yawancinsu daga Khuza'a, da Tamim, da Dayyi, da Rabi'a, da Muzaina, da wasunsu na kabilun Larabawa.
Kuma idan kana son ka san sama da haka sai ka duba dukkan jagororin kabilun Larabawa da suka zo domin kawar da hukumar Umayyawa, ka koma zuwa ga littafin Ibnul Fudi marubucin tarihin Iraki na Muhammad Rida Shabibi, ya fadada tarihin daga manyan litattafai kuma ya yi sharhin hadafofin kawo wannan hari da kuma nau'in rundunonin da suka yi tarayya wajen kawo hari da dukkan wasu bayanai .
Bangare na biyu shi ne cewa rundunar da ba Larabawa ba ce ta so ne ta huce haushi da daukar fansa kan Larabawa don ba a ba ta mukamai ba a cikin hukumar Umayyawa wannan ma muna iya cewa ba ingantacce ba ne, domin da yawa daga wadanda suke ba Larabawa ba sun kama matsayoyi da mukamai masu girma a lokacin Umayyawa tun daga farko har karshe, kuma yanayin da suka samu a lokacin Abbasawa ba shi da wani bambancin azo-agani da wanda suke a kai lokacin Umayyawa, kuma Dakta Ahmad Amin ya yi nuni da hakan a cikin fadinsa: Jagorancin Farisawa ya dadu a lokacin Umayyawa musamman ma karshensa, kuma da ba su samu damar kafuwar Abbasawa ba to da sun samu wata damar daban mai wani yanayi da ya fi wancan .
Wasu jama'ar da ba Larabawa ba ne sun kama mukamai masu girma; daga cikinsu akwai Sarjun dan Mansur mai bayar da shawara ga Mu'awiya, da kuma shugaban fayel din wasiku, da shugaban haraji, da Muradis Maulan Ziyad wanda yake shugaban wasiku, da Zaza Nafrukh wanda yake jagoran harajin Iraki, da Muhammad dan Yazid maulan Ansar, wanda yake gwamnan Misira karkashin Umar dan Abdul'aziz, da Yazid dan Muslim maulan Sakif wanda yake gwamnan Misira, da kuma wasu alkalai da gwamnoni da manyan jagororin haraji, kuma sun shiga duk wani matsayi na daula da jama'arta da fadadawa .
Ta wani bangaren kuma yanayin Larabawa ba ya da wani tasiri sai daidai gwargwadon yadda zai iya tabbatar da maslahar Umayyawa ne, kuma idan suka ga ya saba da maslaharsu to sai su gwara kan Larabawa, su buga sashensu da wani sashen kamar yadda ya faru sau da yawa a lokacin jagorancin Umayyawa . Kuma Dakta Ahmad Amin ya kawo wannan yana mai sharhinsa dalla-dalla kuma yana bayyana yadda Larabawa suka rika dukan junansu; bangare-bangare sashe da sashe idan al'amarin ya kai ga hakan ne maslaha .
Amma Ra'a yi Na Uku:
Wannan ra'ayi yana ganin Shi'anci ya yadu ne ta hanyar Mawali (wadanda ba Larabawa ba ne) kuma suka samu martaba da kima saboda haka. To wannan ma karya ne kuma bai inganta ba, domin an kaskantar da Farisawa a lokacin Abbasawa ba sau daya ba, yana daga cikin al'amarin Abu Muslim da mabiyansa a lokacin Mansur da al'amarin Baramika lokacin Rashid, da al'amarin Ali Sahal lokacin Ma'amun da sauransu. Sai dai a dunkule cewa haka ne mawali sun yi tasiri a wasu fagagen daban, kuma an samu kutsawa da kuma tasirin Farisawa lokacin Saffah zuwa Ma'amun. Kuma wannan yana nufin babu wani tasiri da yake tabbata ga Farisawa wajen da'irar Abbasawa ta yadda zasu iya sanya su karkashinsu duk sadda suka so. Amma lokacin da Mutawakkil ya fara mulki har zuwa karshen mulkin Abbasawa to Abbasanci ya samu raunana har sai da ya rushe, wannan kuwa ya faru ne sakamakon raunin da wannan hukuma ta samu, kuma masu rubutu sun yi bayanai masu yawa kan dalilan rushewarta.
A bisa hakika abin da ake kawowa na tasirin Mawali a cikin daular abbasiyya ya kasance kambawa ne kawai domin al'ummu ba su samu wata dama mai karfi ba a wannan lokacin sai irin wacce suke da ita a lokacin Umayyawa, kuma idan Farisawa sun samu wani tasiri da samun shiga to bai kai ga yadda zai iya kange samun shigar Larabawa ba, sai dai kawai wani samun wuri da samun shiga ne da su larabawan da kansu suka ba su saboda wasu hadafofi da suke son su cim masu. A kan haka ne ma Falhozan yake cewa: Amma batun samun shigar Farisawa da kama wurinsu kamar yadda yake, ba wani abu ba ne da za a iya tabbatar da shi ba .
Amma bangare na biyu na wannan ra'ayi na cewa Shi'anci ya samu lumfasawa lokacin Abbasawa to wannan al'amari ne da ba shi da inganci domin akasin haka ne ma ya faru, saboda Abbasawa sun cakuda hannayensu da jinin Shi'a da jagororinsu, kuma Shi'anci ya samu an kai masa hari da fadawa jarabobi masu ban tsoro a lokota mabambanta in banda wasu lokuta kamar yadda ya faru a lokacin Buwaihiyyin. A takaice dai litattafan tarihi sun kawo mana wasu irin yanayoyi masu ban tsoro da firgici na azabtarwa da ak yi wa Shi'a da neman kawarwa a lokacin Abbasawa, kuma mai karatu yana iya komawa zuwa ga kowane irin littafin tarihi manya domin ya ga wannan a fili.
Bayan wannan gabatarwa ina iya koma wa zuwa ga yaran mustashrikai wadanda suka bi sahun malamansu suka bi su ido rufe a wadannan ra'ayoyin na Farisancin Shi'anci, da suka hada da:
1- Dakta Ahmad Amin:
Dakta Ahmad Amin ya tafi a kan cewa ra'ayin tunanin Farisawa ne ya mamaye Shi'anci, (duk da kuwa cewa Shi'anci ya riga Farisawa) domin mafi yawan Farisawa kamar yadda shi Ahmad Amin ya raya cewa tunanin Shi'anci ya mamaye su, kuma haka nan kana iya duba abin da ya fada na fentinsa na Farisanci, duba abin da ya fada:
Abin da nake gani kamar yadda tarihi yake nuna mana cewa Shi'anci ga Ali (a.s) ya fara tun kafin shigar Farisawa cikin musulunci ne, sai dai wannan da ma'anar Shi'anci mai sauki ce, amma Shi'anci da wannan ma'anar sabuwa ya samukafuwa ne sakamakon wasu tunani da suka shiga cikinsa daga wasu jama'ar ne, kuma tunda mafiyawan wanda ya shiga musulunci su ne Farisawa to suna da rawa babba da suka taka wajen yin tasriri kan al'amarin Shi'anci .
A wani wurin yana cewa: Kallon Shi'a ga Imam Ali da 'ya'yansa shi ne irin kallon su ga sarakunan sasaniyya, kuma imani da Ubangizai biyu na Farisawa shi ne asasi da rawafidawa suke dogaro da shi a musulunci, sai wannan ya motsa mu'utazilawa domin ture hujjojin rawafidawa .
A nan ina neman mai karatu ya yi la'ari ya lura sosai da wannan mummunan suka mai kaifi da warin sharri da hura wuta yake kunshe a cikinsa don gani da matakin Ahmad Amin da ire-irensa, kuma muna ganin Ahmad Amin ya saba da kawo wannan fikira da dogaro da ita kamar yadda yake a fili a cikin dukkan wallafe-wallafensa. Ba komai ba ne ya cika cikin Ahmad Amin sai gaba da kiyayya da mugun kaidi da mugun kulli kan Shi'a, hada da koyi da mustashrikai da yake yi kan abin da suke fada.
2- Sheikh Abu Zuhura ya tafi a kan irin wannan ra'ayi na Ahmad Amin yana mai karawa kan haka da cewa: Mafi yawan Shi'a na farko Farisawa ne. Duba abin da yake fada a wannan al'amarin yana mai kawo ra'ayoyin mustashrikai yana mai karawa a kan haka da cewa: A bisa gaskiya Shi'a sun tasirantu da tunanin Farisanci ne game da mulki da gado, kuma yana mai karawa da cewa mafi yawan Farisawa har yanzu suna daga cikin 'yan Shi'a ne, kuma shi'an farko sun kasance daga Farisawa ne !.
Allah ya ji kan Attayyib Mutanabbi yayin da yake fada a wani Baiti nasa da cewa: Zamanin da mutanensa mutane ne kanana, koda kuwa suna da jiki manya manya. To Abu Zuhrata ma wannan Baiti ya hau kansa yayin da yake cewa: Shi'an farko sun kasance daga mutanen Farisa ne.
Don Allah ina nema daga dukkan wani mai kartau ya fitar mini da mutane biyar daga Farisawa a Shi'ar farko, kuma ina karfafa musu tun da can ba zasu iya samun wannan adadi ba. Shin akwai wata kima da ta rage ga irin wadannan maganganu na Abu Zuhra, kuma magana nawa ce kuke tsammanin Abu Zuhra ya yi ta haka nan babu wani dalili.
3- Ahmad Adiyyatul-Lah:
Wannan mutumin yana daga cikin wadanda suka bi sawun mustashrikai a kan Farisancin Shi'anci, yana ganin cewa fikirar Shi'a ta tasirantu daga wani mutum na jabu da aka kirkira a tarihi aka ba shi sunan Abdullah dan Saba wanda aka ce shi ne ya kawo tunanin shi'anci iri-iri, kuma daga cikinsu akwai cewa shi'anci akida ce bafarisiya, yana mai cewa:
Ibn Sauda (kamar yadda suke kirkirar wannan sunan ga kagaggen mutumin nan wai shi Ibn Saba) ya cirata zuwa Madina, ya yada maganganu da suka saba wa musulunci da sun fito daga yahudancinsa ne, da kuma akidun Farisanci da suka yadu a kasar Yaman, kuma ya fito ne a matsayin mai da'awar taimako ga gaskiyar Imam Ali (a.s), yana mai kiran cewa kowane Annabi (a.s) yana da wasiyyi, kuma wasiyyin Muhammad (s.a.w) shi ne Ali (a.s) .
Wannan dai wani abu ne daga cikin misalai na maganganun mustashrikai, kuma kana iya samun wannan gun na wannan zamanin da zaka iya samun wannan a litattafai da suke gadar da tunani tun daga na farko har zuwa masu biye musu, sannan sai ka ga ya yi kokarin ganin ya kafa wannan tunani da dukkan abin da yake da shi na kwarewa.
Mu ba zamu fara raddi kan wannan ra'ayi ba tukun sai bayan mun yi bayanin wadannan ra'ayoyi dalla-dalla tukun wadanda suka kawo bayanin dalilin shigar Farisawa cikin Shi'a'nci, wannan zai kasance kamar shi ne kashin bayan bahasinmu. Kuma mafi girman ra'ayoyin da suka kawo na ganinsu na dalilin shigar Farisawa cikin Shi'anci sun kasu gida uku kamar haka ne:
Dalilan Shigar Farisawa Cikin Shi'anci
A Mahangar Wasu Marubutan Ahlus-sunna
1- Al'amari Na Farko:
Surukutar Imam Husain (a.s) ga Farisawa cewa ya auri 'yar sarki Yazdajir kuma shi daya ne daga sarakunan sasaniyawa kuma sunanta Shahezanan, sai tahaifa masa Aliyyu dan husani wanda gadon sarakuna ya taru a cikinsa, da kuma siffar Imamanci daga iyayensa maza, har ma Abul Aswad Addu'ali yana fada game da shi:
Hakika abin haifa tsakanin sarki Kisra da Hashim
Shi ne mafi girman wanda aka tara wa kamala
A game da haka ne Sumaira Allaisi take karawa kan ra'ayin nan na Arnold Toyinbe game da yaduwar musulunci tsakanin Farisawa da cewa: Auren Husain ga Shahbanu daya daga 'ya'yan Yazdajir shi ne abin da ya kawo yaduwar musulunci tsakanin Farisawa, kuma Farisawa sun ga 'yan'yan shahbanu da Husain su ne masu gado ga mulkinsu dadadde . Don haka auren Husain a ra'ayin wadannan yana daga abubuwan da suka kai wa ga yaduwar Shi'anci da biyayya ga Ahlul-baiti (a.s) gun Farisawa.
2- Al'amari Na Biyu:
Kusantar ra'ayoyi tsakanin Shi'a da Farisawa; daga wannan akwai batun hakkin Ubangiji, don haka kowa yana ganin hakkin Allah yana nan ga wanda ya zaba na daga jagorori, shi bafarise yana ganin wannan hakki ga sarakunan Farisawa, shi kuma dan Shi'a yana ganin wannan ga jagorrorinsa, wannan kuwa koda wasu suna ganin cewa Shi'a sun tasirantu da Farisawa ne, kuma tun da dai Shi'anci ya rigayi shigar Farisawa cikinsa, kuma tun da dai wadanda suka shiga cikinsa na daga Shi'a dukkaninsu Larabawa ne kamar yadda muka tabbatar da hakan a abin da ya rigaya, kuma tun da dai nazarin Shi'a game da Imami bai saba ba kamar yadda yake gun zurara daga abin da yake gun Ammar da Abuzar to don haka muna iya cewa nazarin nan na hakkin Allah da Shi'a suka yi ittafaki da Farisawa a kansa bai kasance sakamakon tasirantuwa da ra'ayoyin Farisawa ba ne, wanda yake kunshe da imanin Shi'a da cewa Imam Ali (a.s) wasiyyin Annabi (s.a.w) ne, kuma shi ne wanda aka yi nassi da bin sa, kuma da yawa daga mustashrikai sun saba da fadin irin wannan kusanci da su da dalibansu:
Muhammad Abu Zuhra yana cewa: Kuma wasu daga sashen malamai daga cikinsu akwai Duzi mustashriki ya tabbatar da cewa asalin mazhabar Shi'anci wani tunani ne daga Farisanci yayin da Larabawa suna da tunanin zabe ne, Farisawa kuma suna da tunanin mulki ne da gado, ba su san wani abu da ma'anar gado ba, har ya ce; Shi'a sun tasirantu da tunanin Farisanci game da mulki da gado .
Haka nan Ahmad Amin da wasu mustashrikai suka tafi a kan haka, kuma shi ma ya ambace su cikin wadanda suka tafi a kan wannan ra'ayi, kuma wannan ma'anar ta zo a littafinsa na Fajarul Islam yana mai karfafa ra'ayinsa da ra'ayoyin mustashrikai .
3- Al'amari Na Uku:
Wasu masu kin shi'ancin suna cewa: Shigar Farisawa Shi'anci ya kasance da nufin rusa muslunci ne da boyewa karkashin son Ahlul-baiti (a.s), sannan sai aka shigo da wadannan ra'ayoyin masu rusa musulunci kamar fadin batun Wasiyya, Raja'a, da Mahadi (a.s) da sauransu.
A kan haka ne Ahmad Amin yake cewa: A bisa gaskiya Shi'anci ya kasance mafaka ce da dukkan wanda yake son rusa musulunci yake fakewa da shi don gaba ko mugun kulli, haka nan dukkan wanda yake son shigar da koyarwar iyayensa na yahudanci da kiristanci da zardashtanci da indiyanci, da dukkan wanda yake son 'yancin kasarsa da fita daga masarautarsa sun labe karkashin son Ahlul-baitii ne.
Ina fatan mu duba irin wadannan maganganu masu muryoyi na kiyayya a kan Shi'anci kuma wannan magana ce da masu yawa tun kafinsa da bayansa suka kawo kamar mai littafin Manar . Kuma mun samu wannan tunani da yake ganin Shi'anci a matsayin wani tasiri na Farisanci a fili gun wasu mutanen masu gaba da kiyayya da tafarkin mazhabin Ahlul-baiti kamar Muhibbuddin Al'khadib, da Ahmad Shalbi, da Musdafa Ash'ka'a da sauransu.
Saoba kuma mu dan yi karin haske a kan inganci ko rashin ingancin wannan da'awar da take tabbatar da abin da aka fada Shi'anci dole mukawo wasu abubuwan da suka kawo a matsayin dalilai da ya sanya Farisawa shiga Shi'anci:
1- Raddi kan abubuwa uku
2- Iyakance hakikanin Shi'anci a bisa kabilanci
3- Iyakance hakikanin Shi'anci a tunani
4- Iyakance hakikanin sunnanci daga wannan al'amarin da dalilai da aka kawo daga littafin Sunna;
Amsa A Kan Dalilan Shigar Farisanci Shi'anci
1- Al'mari Na Farko:
Surukutar Imam Husain (a.s) ga Farisawa;
Yana daga cikin abubuwan da kowa ya yarda da su shi ne: Ka'idar nan ta cewa hukuncin abubuwan da suke iri daya kan abin da halatta da abin da bai halatta ba iri daya ne, don haka wannan ka'ida ta hau kan wadannan marubuta game da abin da suka kawo na shi'antar Farisawa saboda surukutar Imam Husain (a.s) ga Farisawa. Domin akwai wannan ga Abdullahi dan Umar dan Khaddabi, da kuma Muhammad dan Abubakar. Kuma Zamakhshari ya kawo wannan a cikin littafin Rabi'ul Abrar da waninsa na malaman tarihi cewa yayin da sahabbai suka zo da 'ya'ya uku na Yazdajir daga ribatattun Farisawa a lokacin halifa na biyu sai aka sayar da ribatattun kuma halifa ya umarci da a sayar da su. Sai Imam Ali (a.s) ya ce: Ba haka ake yi wa 'ya'yan sarakuna ba, su ba a yi musu kamar sauran mutanen. Sai Halifa ya ce masa yaya za a yi ke nan da su, sai ya ce: A yi musu kima, kuma duk yadda kudinsu ya kai sai wanda ya zabe su ya biya, sai aka yi musu kima, sai Ali (a.s) ya dauki daya ya ba wa Abdullah dan Umar, daya kuwa dansa Husain, daya kuma Muhammad dan Abubakar, sai aka haifa wa Abdullahi dan Umar dansa Salim, shi kuma Husain ya haifi Zainul-abidin, Muhammad kuma ya samu dansa Kasim, wadannan uwayensu mata 'ya'yan sarki Yazdajir ne .
A nan ne muke tambaya cewa: Idan dai surukuta ita ce dalili to don me ba zamu ga Farisawa sun karkata ga surukansu na Abdullahi dan Umar da Muhammad dan Abubakar ba!? Kuma kowanne daga cikinsu shi Muhammad da Abdullahi 'ya'yan halifofi ne, kamar yadda Husain yake dan halifa ne. Hada da cewa dukkansu kowanne Yazid dan Walid dan Abdulmalik, da babarsa Shafarand 'yar Fairuz dan Yazdajir, da Marwan dan Muhammad karshen halifofin Banu Umayya wanda babarsa ita baiwa ce daga Kurdawan Iran, don me ba ma ganin irin wannan dalili a kan al'amarinsu , kuma a bisa akasin haka don me ya sa Larabawa su ba sa karkata ga Ahlul-baiti (a.s) ai iyayensu Larabawa ne, yayin da muke ganin wasu jama'a daga Larabawa sun zamanto makiya ga Ahlul-baiti (a.s); wannan tambaya ce ga wadannan hankulan da suke rubutu amma ba sa tunani.
2- Al'amari Na Biyu:
Kusancin Ra'a yi Tsakanin Shi'a da Farisawa:
Kowanne daga cikin masu ra'ayin Hakkin Allah suna cewa akwai gado kuma babu batun zabi a jagoranci, wannan kuma ya tababatar da abubuwa biyu da suka sanya dalilin shiga Shi'anci: Wannan al'amari ina ganin duk wanda ba ya girmama hankalinsa shi ne zai kawo shi, domin yaushe ne dai kawai don kun yi tarayya da mutum a wani abu na akidu sai a samu haduwa a akida daya ya jefar da tasa ya yi riko da taka. (Kamar yadda su masu sukan suke kawo cewa Farisawa sun yi wurgi da ta su akida suka shiga shi'anci saboda kawai sun yi tarayya da shi a wani abu! Wannan wace irin wauta ce? Yaushe ne wani mai hankali yake yin hakan?)
Kuma duk wani mai bincike ya san cewa kowace al'umma tana da wani abu da ta hadu da wata al'ummar a kansa a wani ra'ayi ko wata mas'ala amma duk da haka wannan ba ya sanya a ce musu abu guda. Mu fara da Ahmad Amin kansa mu dora masa ra'ayinsa a kansa zamu ga dalilin da ya dora wa Shi'a shi ma yana hawa kansa; idan mun duba zamu ga yana tafiya a kan ra'ayin Jabar (tilasci) da Ikhtiyar (Zabi):
Mas'alar Tilasci da Zabi malaman Falsafa na Yunan sun yi magana kanta kafin musulmi su yi magana game da ita, kuma Saryaniyawa sun samu wannan daga garesu ne, kuma Zardashtiyyun su ma sun yi magana kanta kamar yadda Kiristoci suka yi, sannan sai Musulmi .
Don haka bisa dogaro da maganar Ahmad Amin muna iya cewa ke nan musulmi sun zamo Nasara saboda sun yi ittifaki da Nasara a kan wannan ra'ayi na Jabar, idan kuwa ba haka ba, mene ne dalilin Ahmad Amin na ganin Shi'a cewa Farisawa ne saboda kawai sun hadu da su kan maganar Hakkin Allah madaukaki?.
Amma abu na biyu na da'awar cewa dukkan kowanne daga Farisawa da kuma Shi'a suna ganin jagoranci a matsayin gado ne to wannan batacce ne game da Shi'a, domin Shi'a ba sa ganin jagoranci gado ne, suna ganin al'amari ne na nassi daga Allah (s.w.t) ta hannun Annabi (s.a.w) ko Imami (a.s), kuma litattafan Shi'a cike suke da wannan al'amari .
Kuma mas'alar nassin kan Imami (a.s) ba wata masl'ala ba ce da take ta jinkirta gunsu domin ita sananniya ce garesu tun farko gun dabaka ta farko ta Shi'a saboda bayyanar nassi gunsu kan mas'alar Imamanci. Kuma muna iya kawo misali kan haka na wata ganawa da ta faru tsakanin halifa na biyu da Abdullahi dan Abbas, kuma halifa na biyu ya kasance yana samun nutsuwa da Ibn Abbas kuma yana karkata zuwa gareshi sosai, sai wata rana ya ce da shi: Ya kai Abdullahi nauyi yana kanka idan ka boye mini wani abu, shin a cikin ran Ali (a.s) akwai wani abu na kaunar halifanci? Sai Ibn Abbas ya ce: Sai na ce; haka ne. Sai ya ce: Shin yana raya cewa manzon Allah ya yi masa nassi ne? Ibn Abbas ya ce; Sai na ce Na'am. Sai Umar ya ce: Hakika manzon Allah ya kasance yana kambama al'amarinsa kwarai da gaske da maganar da babu wata hujja da ta bari kuma babu wani uzuri da ba ta yanke ba, kuma ya kasance yana daukaka sha'aninsa wani lokacin, kuma lallai ya so ya shelanta sunansa a rashin lafiyarsa sai na hana shi saboda tausayawa da kuma kiyaye al'amarin musulunci. Sai Manzo (s.a.w) ya san na gane abin da yake cikin ransa sai ya kyale . Hanin nan da halifa Umar ya yi nuni da shi ne yayin da Annabi (s.a.w) ya nema daga sahabbansa su zo masa da takarda da tawwada a cikin lokacin rayuwarsa na karshe yana mai cewa: A ba ni tawwada da takarda in rubuta muku abin da ba zaku taba bata ba bayana har abada. Sai halifa Umar ya ce: Yana cikin sumbatu ne kuma ciwo ya yi galaba kansa .
A dunkule dai wannan muhawara da ire-irenta tana yi mana bayanin matsayin Shi'a kan al'amarin Imamanci, kuma ita nassi ce ba gado ba, don haka a ina ne mustashrikai da dalibansu suka samu wannan magana ta gado idan dai ba rashin sanin mene ne Shi'anci ba ko kuma son neman karkatar da gaskiya da son rai.
3- Al'amari na uku:
Shi ne shigar Farisawa musulunci domin son su rusa shi sannan kuma su tabbatar da hadafinsu da shigar da ra'ayin kakanninsu; wannan ra'ayi dai batacce ne, kuma muna iya cewa kamar haka:
Na farko: Litattafansu masu kariya ga musulunci da masallatansu da kuma cibiyoyinsu na addini da jihadinsu a tafarkin Allah duk wannan yana nuna mana karyar wannan da'awar da ake yi.
Na biyu: Ba makawa a tambayi wadannan masu wannan magana da cewa shin kuna nufin ganin bayan musulunci da rusa shi ya kebanci Farisawa ne kawai da suka zabi musulunci suka kuma zabi sunnanci ko kuma ya shafi dukkan Farisawa wadanda ya hada da Sunna da Shi'ansu. Kuma dole ne amsa ta kasance da E ne. Domin idan son ganin bayan addinin ya kasance saboda kasancewarsu Farisawa ne ba don komai ba, to idan haka ne don me muka ga ana sukan wadanda suke Shi'a ne kawai banda wadanda suka zama Sunna.
Tayiwu wani ya ce: Wannan ya kasance ne ga Farisawa Shi'a, don haka wannan yana shafar akidar Shi'a ne. To mun riga mun kawo cewa madogarar Shi'a ita ce Littafi da Sunna, don haka babu wata hanyar da za a rika sukan su da abin da yake kore littafin da sunnar, wannan kuwa ga mai binciken gaskiya ke nan -alhalin ya fi kowa nesa da ita- ba don irin wadannan mutane suna neman nesantar da al'umma daga alheri ba, da ba su kawo irin wannan tunani ba, da suka rarraba al'umma suka daidaita hadin kanta, kuma da sun ji kunyar irin wadannan maganganu nasu, kuma da sannu zamukawo maka cewa gwarazan mutane a tarihi da fikihu da akida su ne Farisawa kansu, kuma ba ma ganin wannan wani aibi ne matukar muna riko da masdari daya kuma matukar kur'aninmu dare da rana yana shelanta hadin kai da cewa asalinmu daya ne a fadinsa "Shin ba mu halicce ku ba daga ruwa abin wulakantawa" mursalat: 20.
Na uku: Mas'alolin da mutanen nan suka kawo kuma suke ganin su a matsayin al'amuran da suke rusa addini kuma suke jifan Farisawa Shi'a da su kamar wasiyya da Raja'a da kuma maganar mahadiyyanci duk wannan ma su ma Ahlus-sunna sun yi tarayya da su a ciki amma ba mu samu wani yana sukan su ba da ita ko kuma yana ganin shi abin zagi ne, kamar yadda wannan al'amura ne da suka zo a ruwayoyin Sunna ta hanya amintacciya da zamukawo wannan nan kusa in Allah ya so.
Wannan ke nan, hada da cewa wadannan ra'ayoyin ba laruri ba ne a musulunci gun Shi'a koda kuwa sun kasance laruri ne na mazhaba (kamar imani da Imam Mahadi (a.s) amma duk da haka me ya zo da wannan duk ka ce-nace din da ake kagowa, kuma me ya kawo duk wannan karfi da ake kararwa domin kawo baraka tsakanin ma'abota alkibla daya balle ma a yi maganar kyawunsa? Ko me ya kawo duk wannan hamasa da ake kagowa a kan abubuwan da ba su kebanta da Shi'a ba wadanda abubuwa ne da su ma Ahlus-sunna suna da su?.
Fasali Na Uku
Hakikanin Kabilancin Shi'anci da Ra'ayoyin Marubuta a Ciki
A farkon wannan bahasi mun kawo tambaya kan ma'anar Larabci da abin da yake zuwa a kwakwalwa a matakin farko na cewa balarabe shi ne wanda ake haifa da iyaye biyu Larabawa, kuma wanda ya gangaro daga jinin Larabci, sai dai wannan wani abu ne da ba zai yiwu ba domin ba zamu iya samu jini dari bisa dari ba wanda bai samu wata cakuda ba, kuma domin cewa jinin mutane dukkaninsu yana komwa zuwa ga madogara kuma asali daya ne duk ya cakuda, don haka sai mu nemi wata ma'ana daban, sannan kuma ba yadda zamu sawwala cewa jini yana tasirantuwa ne da akida da tunani da al'adu, me ke nan abin nufi da Larabci a wannan lamarin, sannan kuma duk da haka wannan ra'ayi yana iya tsayuwa a kan kaddara samuwar jini na Larabci tsantsa wanda yake tunani ne ba na ilimi ba, kuma ba zai yiwu a dogara da shi ba.
Idan ma mun sassauta mun yarda da ingancin wannan maganar, mun riga mun ambaci cewa 'yan Shi'ar da Shi'anci ya fara da su duk sun kasance daga kabilun Larabawa ne, kuma mun kawo dabaka ta fari daga cikinsu, don haka ba ma ganin mu dora wahala ga mai karatu kan wannan, don haka sai muka kawo masa dabaka ta biyu da ta uku, kuma mai karatu yana iya komawa zuwa ga manyan litattafan da suka yi bayani game da mazajen domin ya ga mafi yawansu daga Larabawa ne.
Sannan kuma idan mun kaddara cewa akwai wani jini tsarkakke da bai tasirantu da waninsa ba, to wannan maganar kawai ce, muna iya komawa maganarmu ta farko don mu ga mene ne ma'anar Larabci, zamu ga amsa ita ce; Larabci (a kabilance) ya hadu ne da tunani da al'adu da lugga (yare da harshe) da kuma kasa, don haka fahimtar ma'anar kabilar Larabci daga wadannan abubuwan ita ce fahimta mai inganci sahihiya, kuma ita ce take iya iyakance mana hakikaninsa, kuma mafi yawan rubuce-rubuce da suka iyakance hakikanin mutum sun karfafi wannan dalilai, wato; yare da tarihi da yanayi da kuma maslahar da aka yi tarayya a ciki sukan hadu su samar da abin da zai iya sanya a dangantu zuwa ga wata al'umma , don haka ne muna iya kawo magana game da Shi'anci ta fuskanci wadannan abubuwan sai mu fara da dalili na farko kamar haka:
Abubuwan da suke hada hakikanin jini (kabila)
1- Yanayin Kasa:
Yankin Larabawa shi ne wurin da aka reni Shi'anci tun farko, domin shi'ar Ali (a.s) na farko sahabbai ne kuma daga jazirar Larabawa kamar yadda muka kawo a baya, kuma idan an samu mutum daya ko mutane biyu kamar Salman Farisi da Abu Rafi'i Al'kibdi to muna iya ganin rayuwarsu a tsawon lokacin rayuwarsu a Hijaz ne, kuma daga Hizaj ne Shi'anci ya yadu zuwa sasannin kasa kamar Iraki da Siriya da Misira da Sham, da Afrika, da Indiya, da Khalij, da Turai, da Amurka, da Kasar Sin, da Rasha, da wasunsu na daga sasannin duniya tsawon shekaru masu yawa. Sannan kuma zamu ga maganar masu rubutu a kan wannan da kuma bayaninsu na cewa jazirar Larabawa ita ce wurin da aka haifi Shi'anci na farko.
2- Lugga (harshe)
Ana ganin harshe shi ne babban dalilin da yake sanya kirga mutum cikin wata kabila, domin yare wani yanki ne na al'ada, kai binciken karshe ya tafi a kan cewa shi yanki mai girma na tunani mai magana. Wannan kuwa saboda sun kasa tunani kashi biyu ne, akwai; tunani mai shiru da kuma mai magana .
Kuma tunda kasancewar Shi'a daga Hijaz suke to yarensu shi ne Larabci kamar yadda zamu ga shi'ar Ali (a.s) suke, kamar yadda ya bayyana daga bayanan da suka gaba ta na masu fasahar Larabawa kuma gwarazan iya bayani.
Kuma wannan fice da Shi'a suka yi wajen iya bayani sun same shi ne daga imaminsu Ali (a.s) shugaban masu bayani, har sai da suka yi fintinkau a cikin wannan kuma masu tarihi suka kirga su cikin kwararru na fasaha: Daga cikinsu akwai; Udayyi dan Hatimudda'i, da Hashimul Mirkal, da Khalid dan Sa'id Al'abshami Umawi, da Walid dan Jabiri dan Zalim Ad'da'i da wasunsu .
Kuma kasancewar yaren Larabci shi ne yaren Kur'ani mai girma to Shi'a sun kasance masu tsanantawa wajen ganin sun yi rubutu da Larabci a matsayinsa na luggar ibada kuma lugar kulla a aure, kuma ba su taba yin sakaci ba a cikin wannan, kuma babu wani yare da suka dauke shi a makwafin Larabci, a kan wannan kuma ana iya ganin wannan al'amarin ta hanyar ganin cewa a wajensu lugga ba kawai wani abu ba ne da yake ma'ana zalla kawai ba, domin da haka ne, to da wani yare ya tsaya a makwafinta, sai dai ita wani abu ne da yake da al'adunsa da dabi'unsa na asli daban wadanda suka bubbogo daga sako, don haka ne ma Kur'ani mai girma ya sauka da Larabcin.
Kuma muna iya ganin tarayyar malaman Shi'a sun tafi a kan rashin halaccin karatu a salla ko kiran salla ko kuma kabbarar harama sai da Larabci, yayin da zamu ga Abuhanifa kai tsaye ya tafi a kan cewa ya halatta a yi kiran salla ba da Larabci ba, haka nan ma Shafi'iyya da Malikiyya suna ganin ya halatta a yi kiran salla ba da Larabci ba idan mai kiran ya kasance ba'ajame, ko kuma zai yi kiran salla ga kansa ne, ko kuma zai yi wata jama'a irinsa ne .
Kuma muna iya ganin Shafi'iyya da Hanifawa da Malikiyya sun tafi a kan halaccin yin kabbarar harama ba da Larabci ba, idan ya kasance ba zai iya yin Larabci ba, kuma mai Fikihu ala Mazahibil Arba'a ya kawo wannan a babin sharuddan kabbarar harama a juzu'i na farko. Ban dai samu wasu madogara ba da kaina game da wannan wanda yake cewa suna da sharadi a kan yin kulla aure da Larabci yayin da Shi'a suka tafi a kan cewa ba zai yiwu ba sai da Larabci bisa zabi , kuma idan aka yi maganar kulla aure to Hanifawa da Malikawa da Hambalawa suna tafi a kan zai yiwu ba da Larabci ba tare da mutum yana da iko a kan hakan, kuma suna ganin ingancin wannan kullin .
3- Larabcin Halifa
Daga cikin abin da ya shafi al'amarin lugga don gane da muhimmancin Larabci a matsayin shari'a yana iya bayyana cewa Allah ya zabi wannan yare ne domin ya kasance mai dauke da tunanin musulunci, kuma Ubangiji madaukaki ya girmama wannan luga a littafinsa yayin da yake fada a aya ta biyu ta surar Yusuf: "Haka nan muka saukar da shi Kur'ani Larabci ko kwa hankalta" kuma yana fada a wata aya ta talatin da bakwai a surar Ra'adi "Haka nan muka saukar da hukunci larabaci" al'amarin da masu fassarar Kur'ani suka hadu a kan cewa Kur'ani hikima ce ta Larabci kuma muhawararsa tana tsare ne a bisa irin ta muhawarar Larabawa da usulubinsu, idan ka ga dama ka ce; ya dauki al'adar Larabawa da dukkan wata wayewa ta ci gabansu yayin da ya zabi lugarsu -yarensu- kuma amma bai kebanta da su ba domin sakon musulunci na duniya ne, sai dai Allah ya sanya yaren Larabci shi ne hanyar da yake ciratar da addini madaidaici zuwa ga mutane ta hanyarsa.
Don kiyaye wannan al'amari na sako sai da yawa daga jama'ar kungiyoyin musulmi suka tafi a kan cewa dole ne halifa ya kasance balarabe. Ba wai don wani dalili da ake iya fahimtar kabilanci daga wannan sakon na sama ba wanda ya tsarkaka daga hakan, sai dai jama'ar musulmi sun kasu gida biyu ne kan hakan: Kuma tayiwu mu ce Shi'a sun karfafi kasancewar halifa ya kasance balarabe saboda fadin nan na Annabi (s.a.w) "Jagorori (shugabanni) daga kuraishawa ne" . Yayin da muka ga da yawa daga musulmi wadanda ba Shi'a ba sun tafi a kan rashin la'akari da wannan sharadin. Kuma wannan yana iya farawa tun daga kan halifa na biyu yayin da ya ce:
Da dayan mutanen nan biyu ya riske ni da na sanya al'amarin jagoranci a hannunsa: Salim maulan Abu Huzaifa, da Abu Ubaida Aljarrah, da Salim ya kasance a raye da ban sanya ta shura ba .
Kuma a fili yake ke nan cewa ambaton Salim yana nuna mana cewa halifa bai shardanta Larabci ba, in ba haka ba, da ya yi nassi a kan Larabci kawai, kuma manyan mu'utazilawa sun tafi a kan hakan kamar Diraru dan Amru, da Sumama dan Asrash da Jahiz, da yawa daga wasunsu .
Kamar yadda Hawarijawa dukkaninsu suka tafi a kan rashin sharadin larabcin halifa da nassinsu karara kan hakan . Kuma a bisa wannan rashin sharadin nan Hanifawa suka tafi, kuma saboda haka ne ma suka inganta halifanci Daular Usmaniyya . Wannan sharadin na kasancewar halifa balarabe a bisa hakika ba yadda za a yi ya kasance sakamakon kabilanci domin wannan ba zai yiwu ba a sakon addinin musulunci wanda yake sakon karshe kuma addinin daidaito, sai dai da wannan sharadin musulunci yana iya kiyaye mana samuwar shugaba wanda ya san zurfin abin da shari'a ta kunsa da kuma wayewar da take da alaka da harshen Larabci, don haka musulunci yana iya sanya sharadin Larabci ga jagora ba tare da kuma ya tauye wasu ba ko kuma ya muzanta matsayinsu ko kuma ya soki ikhlasinsu ba.
4- Tarihi da Maslaha
Tarihin Shi'a da muka kawo wani bangare ne na tarihin jazirar Larabawa da dukkan abin da ya shafe ta wanda ya danganci tarihi. Haka nan ma maslahar da aka yi tarayya a ciki da kuma tsarin tunani da al'adu na al'ummar. Don haka ne ma sai musulunci ya yi kokarin ganin ya tseratar da musulmi daga dukkan wani abu da zai kawar musu da al'adunsa abin da yake wani abu ne da shi ne ya hada dukkan mazauna jazirar Larabawa. Kuma wannnan abu ne abu bayyananne da ba ya bukatar tsawaita bayani kansa, don haka ne ma zamu wadatu da abin da muka ambata, kuma dai da wannan bayanin da muka kawo ne zai bayyana a fili cewa Shi'anci a hakikaninsa balarabe ne tun farko, kuma a nan ne aka rene shi, don haka ne marubuta suka tafi a kan cewa Shi'anci balarabe ne gaba dayansa, wato; ina nufin marubuta na wannan lokacin domin kuwa wannan mas'ala ce da a zamanin farko ba ta cikin tunanin Shi'a na wancan lokacin na farko, batun raba wa Shi'anci asalin Farisanci ya faru ne daga karshe bayan Farisawa sun zama Shi'a tun daga karni na goma, amma tarihin lokacin da ya gabaci karni na goma babu wasu Farisawa da suke Shi'a ne sai 'yan kadan, kuma da sannu zamu yi magana game da hakan dalla-dalla. To lokacin da Farisawa suka zama Shi'a to a wannan lokacin ne sai ga shi ana bayyanar da aibobinsu da lokacin da suke sunnanci ba a fade su ba, kuma in Allah ya yarda zamu fitar da natijar haka a bahasosi na gaba.
Yanzu bari in kawo maka wasu misalai daga bayanin da wasu marubuta suka kawo game da wannan mas'ala da musun larabcin Shi'anci a lokacin da suke son zagin Shi'anci ta hanyar zagin Farisawa da kuma bayanin munanan halayensu sai ka saurara ka ji me suke cewa:
1- Dakta Ahmad Amin:
Ahmad Amin yana fada a cikin abin da muka kawo a baya kuma muka ambaci wani abu da ya shafi maganar da muke kai yana mai cewa: Abin da tarihi ya kawo masa shi ne; Shi'anci ya fara kafin shigar Farisawa cikin musulunci ne amma sai dai wannan da ma'anarsa mai sauki da take nufin Ali (a.s) ya fi waninsa cancanta ta fuska biyu; ta fuskacin kimarsa da kusancinsa da Annabi (s.a.w). Sai dai wannan Shi'anci ya samu wani yanayin salo daban ta hanyar shigar da wasu fikirori da akidu a cikinsa (a musulunci) na yahudanci da kiristanci da majusanci, kuma tun da dai wanda suka fi kowa shiga musulunci su ne Farisawa to suna da tasiri mafi girma a Shi'anci. Ra'ayinsa a nan a fili yake cewa shi'an farko ba Farisawa ba ne, duk da ya warware maganarsa a wani wurin .
2 Dakta Ali Husain Kharbudali ya ce:
Akwai wasu jama'a na Larabawa da suke biyayya ga Ali bayan halifanci ya koma hannun Abubakar, kuma Jolad Tasiher yana cewa: Wannan harka ta Shi'anci ta faro ne daga kasashen Larabawa tsantsa kuma sai da yawa daga kabilun Larabawa suka fantsama da wannan ra'ayoyin na jagorancin hukumar Allah, da shar'anta hakkin Ali (a.s) kan halifanci, sai mutanen Farisa a Iraki suka yi riko da koyarwarsu da dukkan kumaji, suka ga cewa Imamanci ba wani abu ne da ake ba wa al'umma hakkin ayyana jagoranta na musulmi da kanta ba ne, sai dai shi wani abu ne na jagorancin addini da jagorancin musulunci, don haka ya wajaba Allah ya ayyana Imami jagora kuma ya kasance ma'asumi, kuma Ali (a.s) shi ne wanda Annabi (s.a.w) ya ayyana shi .
3- Mustashriki Polhuzan ya ce:
Amma batun cewa ra'ayin Iraniyawa sun yi daidai da na Shi'a wani abu ne da babu kokwanto a cikinsa, amma kasancewar wadannan ra'ayoyin na Shi'a sun zo ne daga Iraniyawan to wannan wani abu ne wanda babu wani dalili da yake iya tabbatar da shi, kai ruwayoyin tarihi ma suna tabbatar da akasin hakan yayin da suke cewa sai da Shi'anci ya kafu tun farko a kasashen Larabawa sannan sai daga baya ya cirata zuwa ga Mawali .
4- Mustashriki Adam Mitz ya ce:
Manzhabar Shi'a ba kamar yadda wasu suka yi imani ba ne cewa wani abu ne na daukar fansa daga Iraniyawa domin saba wa musulunci, Jazirar Larabawa ta kasance Shi'a ce dukkaninta banda manyan birane kamar Makka da Tahama da San'a'. Kuma Shi'a sun yi galaba a wasu garuruwan kamar Amman da Hajar da Sa'ada da kuma wasu birane na Khuzistan wacce take karkashin Iraki ta yadda rabin mutanenta sun kasance Shi'a ne, amma Iran ta kasance Sunna ce banda Kum kawai, kuma mutanen Ispahan sun kasacne sun yi shisshigi wajen son Mu'awiya har ma wasu suka yi imani da cewa shi annabi ne mursali .
5- Mustashriki Jolad Tasiher ya ce:
Yana daga cikin kuskure a ce asalin Shi'anci da yaduwarsa ta kasance sakamakon tunanin Iraniyawa ne game da musulunci bayan sun rike shi kuma sun mika wuya ga jagorancinsa ta hanyar yaki ne. Wannan ra'ayi mummuna ya faru ne sakamkon abubuwan tarihi da aka yi musu mummunar fahimta, motsin nan na harkar alawiyyawa ya fara ne a kasar Larabawa tsantsa .
6- Mustashriki Noladkeh ya ce:
Kasashen Farisa sun kasance wani yanki ne mai girma da suke bin mazhabar sunnanci, kuma wannan ya ci gaba har zuwa shekara ta 1500 miladiyya yayin da aka shelanta mazhabin Shi'anci a matsayin mazhaba ta kasa da tsayuwar kafuwar daular safawiyya .
Bayan duk wannan maganganu da muka cirato daga marubuta wadanda suke tabbatar da larabcin Shi'anci a gaba dayansa, kuma a lokacin da wannan ba ya kore kasancewarsa ya samukarbuwa wajen wasu al'ummum, sauran al'ummu suna da kima da girma, kuma mu ba mu kasance muna da wani take a musulunci ba sai a fadin nan nasa madaukaki: "Ya ku mutane hakika mu mun halicce ku daga namiji da mace kuma muka sanya ku jama'u da kabilu don ku san juna, hakika mafi girmanku a wajen Allah shi ne mafi tsoronku (gareshi). Hujurat: 13.
Amma sai ga shi muna fuskantar wasu maganganu da suka shaharantar da mazhabin Shi'anci suna masu jingina shi da Farisanci, daga karshen magana muna iya gabatar da wani bayani game da mutanen da mazhabin Shi'anci ya tsayu kan alkalumansu da matsayinsu, bayan nan sai mu sanya kuma wasu bayanai da suke nuni ga kasancewarsa asalinsa Larabci ne da kuma bayanin asalin wasu mazhabobin daban.
Fasali Na Hudu
Su Waye Jagororin Shi'a?
Imaman Shi'a goma sha biyu tun daga kan Imam Ali (a.s) har zuwa ga Imami na sha biyu Muhammad dan Hasan (a.s) wadanda Shi'a suke ganinsu a matsayin ci gaban yaduwar sakon Annabi da isar da shi ga mutane dukkansu Larabawa ne kuma daga cikin gidan Hashim, kuma gidan Hashim kamar yadda aka sani yana daga mafi darajar gidajen Larabawa, don haka babu bukatar tsawaita bayani game da shi.
Sannan kuma wadanda suka dauki ilimi daga Ahlul-baiti (a.s) tun farko da kabilunsu da jama'arsu na Shi'a wadanda suka yada Shi'anci suka yi bishara da shi dukkaninsu su ma daga tsatson Larabawa ne, tun daga manyan malamai da aka samar da su daga koyarwar makarantar Imam Sadik (a.s) kamar su Abana dan taglib dan rabah alkindi, da kuma gidan aali a'ayun, da gidan aali hayyan taglibi, da aali adiyya, da banu daraj da sauransu . Sannan sai dabakar da take biye musu kamar sheikh Mufid Muhammad dan nu'uman, da sharif murtadha alamulhuda; Aliyyu bin abil Husain, da allama hilli jamaluddin Hasan dan yusfu dan mudahhar, da abdul'aziz dan naharir albarraj, da jamaluddin Ahmad dan musa dan dawus, da iyalin aali dawus, da muhammad dan Ahmad dan idris al'ajali, da najmuddin Ja'afar dan Hasan alhuzali wanda aka sani da muhakkik, da jamaluddin al'Mikdad dan Abdullahi assuyuri, da shahidul awwal Muhammad dan makki da shahidus sani zainuddin al'amili da wasunsu, dukkanin wadannan Larabawa ne.
Amma ma'abuta sihah na Shi'a wadanda su ne Muhammad dan ya'akub alkulaini mai littafin Kafi, da Muhammad dan Ali dan Husain da aka sani da Ibn babawaihil kummi mai littafin man'la yahadhuruhul fakih, da Muhammad dan Hasan dan Ali assheikh dusi mai littafin tahzib da istibsar, dukkanin wadannan babu wani tarihi da ya zo da cewa ba Larabawa ba ne kuma duk wanda ya iya samun wani dalili a kan ajamancinsu to ya amfanar da mu.
Daga karshe zan kawo mana ra'ayin da'iratul ma'arif mai cewa: Mafi dadewar manyan Shi'a duk sun kasance Larabawa ne tsantsa duk da sun kasance daga Yaman ne . Kamar yadda zan ambata wa dukkan wanda yake son fadadawa ya koma wasu litattafai na Shi'a da wasunsu don ya ga nasabar larabawan da suke Shi'a ne, wanda ya hada da mafi muhimmancin wadannan litattafai mai suna: Al'alam na zarkali, da ta'asisus Shi'a li'ulumil islam na sayyid Hasan haidar, da kuma a'ayanus Shi'a na muhsin al'Amin al'amili.
Sunnanci da Farisanci
Kafin mu shiga cikin maudinmu zamu fara da kawo bayanin Iran da yanayin mazaunanta na akida da iyakance inda mazaunanta Sunna da Shi'a suke, kuma ya zama dole mu yi wannan domin kawo haske game da hanyar bahasin.
Mun kawo a tarihi cewa an bude Iran ne tsawon lokacin halifanci har zuwa karshen hukumar Imam Ali (a.s) kuma wadannan garuruwan duk sadda aka bude su to akan bar wata runduna a wannan garin, kuma wasu daga cikinsu Shi'a ne daga wadannan suka dauki akidunsu suka yada su a nan, sai ga shi a lokacin mulkin ziyad dan babansa a Kufa ya takura matuka domin gama wa da Shi'a a Kufa har sai da sama da dubu hamsin suka yi hijira, aka tilasta musu hijira da kora su zuwa yankin Khurasan.
Ba makawa wadannan sun hayayyafa kamar yadda kuma suka yada akidunsu sai wasu jama'a suka bi su a kana hakan, kamar dai yaduwarsa a birnin Kum ta yadda tun lokacin Hajjaj ta riga ta zama birni, kuma muna iya ganin haka yayin da Abdurrahman dan ash'as ya kasance hakimin sajistan ta wajan Hajjaj sai ya yi wa Hajjaj tawaye ya fito domin yakarsa, yayin da harkarsa ta tarwatse ya kasance a cikin jama'arsa akwai malamai daga tabi'ai, daga cikinsu akwai; Abdullahi, da ahwas, da abdurraham, da ishak, da nu'aim, wadannan daga banu Sa'ad dan Malik al'ash'ari suke, sai wadannan mutane bakwai suka sauka a wasu alkaryu a yankin Kum, sannan sai suka mamaye ta suka sanya ta unguwanni bakwai na garin Kum, kuma sai wani dan Abdullahi dan Sa'ad da ya kasance Shi'a ne ya riske su wanda ya rayu ne a Kufa, sai ya kai wa mutanen Kum Shi'anci, don haka ne ma birnin Kum yake gari ne da bai taba samun mamayar tunanin Sunna ba dadai .
Wannan su ne masu dashen irin Shi'anci a Iran da ya yadu a hankali har ya kai kusan karni na goma, sannan sai ya juya bayan nan zuwa wasu yankuna masu yawan Shi'a a lokacin safawiyyawa. Amma da farkon budin kasar Farisa zuwa karni na goma duk Iran ta kansance Sunna ce wacce take an rarraba ta tsakanin mazhabobi in banda wasu yankuna 'yan kadan wadanda a kan samu Shi'a a cikinsu, kuma malaman Sunna sun karfafi wannan magana a zantuttukansu kamar haka:
Iran Basunniya ('Yar Sunna)
1- Shamsuddin Muhammad dan Ahmad yana cewa: Yankin Khurasan na mu'utazilawa ne da shafi'awa amma mafi yawa galibi mabiya Abuhanifa ne, sai dai kawai yankin shush su shafi'awa ne, kuma a ciki akwai wasu mutane mabiya mazhabar Abdullahi sarakhsi, kuma yankin rihab su ma mazhabarsu madaidaiciya ce sai dai cewa ma'abota hadisai ne hanabilawa. Kuma mafi yawa a badbil -tayiwu yana nufin ardabil- ne hanifawa ne, sannan kuma a rayyi akwai hanabilawa da yawa, mutanen Kum kuwa Shi'a ne, dinur kuwa mafi yawa mabiya Sufyanus sauri ne, kuma yankin khuzistan yana da mabiya daban-daban, kuma mafi yawan mutanen ahwaz da rame hurmuz da durak hanabilawa ne, sannan kuwa rabin ahwaz Shi'a ne, kuma akwai mabiya Abuhanifa da yawa a nan, sannan kuma ahwaz mabiya Maliku ne. yankin Farisa suna aiki bisa ra'ayin ma'abota hadisi ne, da kuma sahabban Abuhanifa, yankin kirman kuwa mafi yawa galibi shafi'awa ne, sannan kuma yankin sind mazhabarsu yawanci ma'abota hadisi ne, sannan kuma ma'abota mazhabar Shi'a suna sanya hai'ala a kiran salla -wato suna cewa: Hayya ala khairin amal- suna kuma yin ikama da maimaitawa, wato; suna maimaita Allahu akbar sau biyu, da kuma ash'hadu anla'ilaha illal-Lah sau biyu kuma haka nan- kuma ba a gushe ba ana samun sukan malamai a kan mazhabin Abuhanifa .
2- Ibn baduda a tafiyarsa a takaice ya ce:
Yayin da Khuda bandeh jikan Holako ya shelanta Shi'anci sai ya dora mutane a kansa a farkon karni na takwas kuma ya kasance a tare da shi akwai wani zindiki da ake ce masa jamaluddin bn mutahhar -yana nufin allama hilli- ya rubuta zuwa ga garuruwan azarbijan da kirman da Ispahan, da Khurasan da shiraz, da Iraki, da umarnin sanya Sunan Imam Ali (a.s) da wasu shi'arsa a hudubar jumma'a, da kuma cire ambaton Sunan sahabbai a nan, kuma farkon wanda ya fara kin yin aiki da hakan su ne bagadaza da shiraz da Ispahan, amma mutanen bagadaza sai suka futo da yawa suna cewa ba mu yarda da wannan ba! kuma an ki a yi! ba mu biyayya! ba mu saurarawa! kuma suka zo masallaci suka yi wa limamin gargadin kashe shi idan dai ya aiwatar da hakan, kuma haka nan mutanen Shiraz da Ispahan suka yi.
3- Alkali Iyad a mukaddimar "Tartibul Madarik" ya ce:
Yana mai bayar da labari game da yaduwar mazhabar Maliku: Amma khurasan da abin da yake bayan garuruwan Iraki a kasashen gabas sai Yahaya dan Yahaya attamimi ya fara shigar da wannan mazhaba da kuma abudllahi dan mubarak, da kutaiba dan Sa'id, (mazhabar malikiyya) ta kasance tana da jagorori tswon zamani, kuma ta yadu a kazwin da abin da yake bayanta na garuruwan duwatsu har dai ya kasance karshen inda haskenta ya bice a garin Naishabur ne a hannun Ishak dan kahdan, kuma mazhabar Abuhanifa da Shafi'i suka yi rinjaye a wannan yankunan .
4- Buruklaman yana fada a cikin "Tarihus shu'ub" ya ce:
Sarki Shah Isma'il safawi bayan ya ci nasara sai ya fuskantar da runduna yankin Tabriz sai malaman Shi'a suka ba shi labari cewa kashi biyu cikin uku na mazauna garin da sun kai kusan dubu dari uku Sunna ne . Tare da cewa wannan adadin mai yawa ya kasance a karni na goma ne kuma farkonsa.
5- Mustashriki Kib Yana cewa:
Akwai tunani na kuskure kuma har yanzu bai gushe ba yana yaduwa da yake cewa kasashen Farisa (Iran) su ne wuri na asali na Shi'anci, kuma wannan maganar ba ta da wani asali, abin da ya tabbata a tarihi shi ne cewa zardashtawa sun fi karkata zuwa ga karbar sunnanci gaba daya .
Kuma ba na son in tsawaita maka wannan al'amarin na nassosi da dalilai da suka kawo cewa Iran wuri ne na riko da sunnanci har zuwa karni na goma, kai har ma yanzu akwai yankuna da suke Sunna ne masu yin mazhabinsu da dukkan 'yanci kuma sun yadu gabas da yama da arewa da kudu, to yaya matsayin Iran yake game da sunnanci da Shi'anci, shin wadannan marubuta zasu iya amsa mana wannan tambayar, yaya maganar kiyayya da gaba zata kasance ta hankali ko ta tunani mai kyau.
Fasali Na Biyar
Lugga Da Mazhabobin Musulunci
Ya rigaya mun yi magana game da mazhabobin musulmi da yadda suke ganin sharadin Larabci da masu tabbatarwa da kuma masu korewa a cikin ibadoji da mu'amaloli, don haka babu amfanin dawo da wannan bahasin, amma dai ina son nuni ne a nan a kan cewa akwai wanda ya shardanta Larabci daga Sunna akwai kuma wanda ya kore wannan, yayin da mazhabar Shi'a take karfafa hakan, kuma wannan yana nuni zuwa ga larabcin Shi'anci da karkatarsa a fili ga Larabci.
Su waye shugabannin Sunna?
Ba ina son in dawo da mai karatu baya game da irin wannan bahasi ba ne, sai dai ina son ya sani cewa bai yi riko da abin da yake lazimi ba, Allah ya sani ba ina son in tauye wani mutum ba ne da yake dan wata kabila kamar yadda ba zamu iya kawo dukkan bayanai game da duk wani mai mazhaba ta Sunna ba, sai dai zamukawo wani dan bayani ne da zai yi nuni kan abin da muke son mu cimma sa. Tarihin duniya tun lokacin farko yana raba mutane biyu: Wani bangare sun kasance kamar ruhi ne ga jiki wasu kuma suna matsayin jiki ne, sannan wasu bangaren suna matsayin masu tukin jirgi, wasu kuma suna matsayin jirgi da ake tukawa, kuma zamu ga waye asalin wanda ya tuka wannan jiki na sunnacin Farisanci, kuma muna iya farawa da fikirorin da ake kira mazhabobi hudu:
Mazhabobi hudu:
Mafi yawan litattafai suna kawo cewa uku daga hudu na shugabannin mazhabobi hudu Farisawa ne, na hudunsu ne kawai balarabe, amma ukun na farkonsu:
Na farko: Abuhanifa nu'uman dan sabit dan zudi wanda yake maula ga banu taimil-Lah kuma an haife shi a Kufa .
Na biyu: Imam Shafi'i Muhammad dan Idris dan Abbas dan Usman dan Shafi'i maulan Abu Lahab, kuma ya nemi Umar ya sanya ce daga mawalin kuraishawa sai ya ki, sai bayan nan ya nema daga Usman dan Affana sai ya yarda da hakan don haka shi yana daga mawalin kuraishawa, kuma Razi ya kawo wannan a littafinsa na manakibus Shafi'i, da kuma Abu Zuhra a littafinsa na Imam Shafi'i .
Na uku: Imam Malik dan Anas dan Malik: Ibn Abdul Barr mai Istia'ab a littfinsa na Al'intika' ya tafi a kan cewa yana daga 'yantattun bayi daga mawalin Banu Taim kuma ba balarabe ne, haka nan ma Wakid Muhammad dan Isha, da Suyudi a littafin Tazyinul Mamalik .
Na hudu: Shi ne Imam Ahmad dan Hambal wanda yake shi ne balarabe kawai daga cikin wadannan shugabannin mazhabobin, kuma nasabarsa tana komawa zuwa ga Bukair dan Wa'il. Koda yake akwai wanda ya kawo cewa ukun da suka gaba ta ma Larabawa ne, sai dai wannan abu ne wanda ba zai boyu ba game da abin da ya zo a tarihinsu, sai dai kowane mai bahasi yana iya duba wa ya yi hukuncin abin da ya fahimta daga abin da ya zo na tarihinsu don ya kai zuwa ga wani ra'ayi na musamman .
Ma'abota Sihah (Ingantattun Litattafai)
Kamar yadda muna iya ganin bayanan da suka gabata a baya na ma'abota mazhabobi, to haka ma muna iya fada game da ma'abota ingantattun litattafai su ma sun zo kamar haka bisa nasabarsu:
a- Buhari Muhammad dan Isma'il dan ibrahim mai littafin nan da ya shahara: Ba'ajame ne (Bafarise).
b- Tirmizi dan Isa dan sura addarir dalibin Buhari haka nan shi ma (Bafarise).
c- Muhammad dan Yazid dan Majah, maulan rabi'a, shi ma ba'ajame ne (Bafarise).
d- Ahmad dan Ali dan shu'aibu nisa'i, wani gari nisa da yake Khurasan shi ma haka ba'ajame ne (Bafarise).
e- Sulaiman dan al'asha'as dan Ishak alsajistan (wani gari ne) kuma da harat, ana danganta shi da azd kuma ba su kawo asalinsa ba na nasaba ko kuma dangantaka, sai dai shi mutumin wannan gari ne (Bafarise).
f- Muslim dan Hajjaj dan muslim alkushairi balarabe ne shi, wanda aka kawo bayani game da cewa shi balarabe ne .
Bayani Na uku:
Wannan bayani ne na uku da muka kawo shi game da mazhabobi hudu a tsawon tarihi ba tare da la'akari da jerin zamaninsu ba mun kawo ne domin kawai mu yi nuni da abin da yake ga malamai Farisawa na mazhabobi hudu, kuma ba ina son in tsawaita ba ne domin yana iya bata mana lokuta masu yawa wadanda ya kamata a yi amfani da su a wani abun daban.
Mafi yawan masu ruwaya da malamai da masu tafsiri Farisawa ne, kana iya ganin misali kamar: Mujahid da Ada' dan Abu Ribah, da Ikrama, da Sa'id dan jubait, da Mujahid da Ikrama suna daga wadanda Buhari da Shafi'i suka dogara a kansu kuma suna riko da ruwayoyinsu a cikin jimla a dunkule .
Daga cikinsu akwai Lais dan Sa'ad dalibin Yazid dan Habib wanda ake ganin shi ne mai assasa cibiyar makarantar ilimin addini a Misira, kuma Shafi'i yana fada game da Lais da cewa ya fi Maliku ilimi sai dai sahabbansa ba su yada ilminsa ba ne, kuma shi bafarise ne daga mutanen Ispahan; daga cikin akwai Rabi'atur ra'ayi malamin Maliku shi ne Ibn Abdurrahman dan furukh daga mutanen Farisa, daga cikinsu kuma akwai dawus dan kaisan al'Farisi da Shirazi ya yi bayaninsa a dabakar malamai, daga cikinsu akwai Baihaki mai Sunan wanda aka fada game da shi cewa Shafi'i yana da wata falala a kan kowa sai Baihaki.
Daga ciki akwai Makhul dan Abdullah maulan Banu Lais, da Muhammad dan Sirin maulan Anas dan Maliku, da Hasanul Basari wanda aka ce ya fi kowa kamar mutane da Umar dan Khaddabi kamar yadda Shirazi ya kawo a Dabakat.
Daga cikinsu akwai Hakim mai Mustadrak, da Abdul'aziz dan Almajishun Al'ispahani maulan Banu Taim, da Asim dan Ali maulan banu Taima, daga malaman Buhari, da Abdul Hakki dan Saifuddin Addahalawi mai Littafin Mukaddima a Musdalahul Hadis, da kuma Abdulhakim Al'kandahari mai sharhin Bukhari a Hashiyarsa, da Abul Hamid Al'khasr da Shahi mai Ikhtisarul Mazhab fil Fikihil Shafi'i.
Da Abdurrahaman Rahim maulan Banu Umayya kuma masanin hadisai na Sham a bisa mazahbin Auza'i, da Abdurrahaman Al'adudi Al'ij mai littafin Almawakif, da Abdurrahaman Aljami mai Fususul Hikam, da Abdurrahman Alkarmani shugaban hanifawa a Khurasan, da kuma mai littafin Sharhin Tajrid, da Shaihi Zaidi mai littafin Majma'al Anhar Abdurrahman, da Ahmad dan Amir Almuruzi mai littafin Mukhtasar Almuzni. Da Sahal dan Muhammad Sajistani, mai littafin Kitabu I'irabil Kur'an, da Muhammad dan Idris Abu Hatim Razi wanda ake ganin yana matsayin Buhari ne, da Abu Ishak Shirazi mai littafin Tashbih.
Da Abdullahi dan Zakawa Abuzzinad malamin Madin masanin Farillai da Fikihu wanda yana daga cikin wadanda Maliku da Lais suka karbo ruwaya daga gareshi, da Ahmad dan Husain shihabuddin Al'ispahani mai littafin Gayatul Ikhtisar, da Ya'akub dan Ishak Naishaburi mai littafin Masnad Assahih Al'mukhrij ala Ktabu Muslim bn Hajjaj;
Da Ahmad danAbdullahi abu Na'im mai littafin Alhilya, da Ibn Khalikan mai Wafayatul A'ayan, da Ahmad dan Muhammad Ass'alabi mai Tafsiri .
Da na tsawaita maka a kan wannan magana to da mun kawo jama'a masu yawan gaske na malmai da masana tarihi da masu tafsiri daga Farisawa, kuma dukkan tunanin fikira na Sunna cike yake da Farisawa kuma an rina shi da Farisanci ne, kai hatta da Muhammad dan Abdulwahaba ya rayu ne kuma ya girma ne a hannun Farisawa kuma tarbiyyarsa da tasowarsa ta kasance tsakanin Kurdistan da Hamidan da Ispahan da Kum kamar yadda wasu jama' suka kawo . Don haka yana da kyau muka so cewa harsunan zagi masu kage da suke karya a kan wanda suka so na jama'ar musulmi musamman Shi'a harsunan Farisawa ne. Da sannu zan kawo maka misali na wanda ya fi kowa zakewa kan sukan mabiya Ahlul-baiti a zuciyarsa da harshensa da kuma alkalaminsa.
Misalai Biyu Daga Malaman Sunna Farisawa
1- Shahristani Muhammad dan Abdulkarim mai littafin Milal Wannihal daga mutanen Shaharistan:
Shaharistan gari ne tsakanin naishabur da Khurasan, amma wannan mutum ya rubuta Littafi game da kashe-kashen musulmi sai ya cakuda kan shirwa da na zabuwa, ya tara ya yi barkatai kuma ya yi kage ya kawo abubuwa ba tare da ilimi ba, har sai da aka kwatanta littafin da littafin "Bazadah mubu" sai wannan littafin ya bar kagen da wasu marubuta suka dauka haka nan babu wani bincike suka dora wa Shi'a shi, kuma Allah zai tambaye shi wannan. Kafin in kawo maka misalan maganganunsa yana da kyau in kawo maka wasu ra'ayoyin wasu malamai game da littafinsa.
a- Fakharur Razi:
yana fada a littafinsa na 'munazatun ma'a ahli naharawan' cewa: Mas'ala ta goma bayani game da littafin Milal WanNihal, shi Littafi ne da aka kawo bayanin mazhabobi a cikinsa da rayawar cewa mai littafin, sai dai ba a dogara da shi, domin ya kawo bayanin mazhabobin yana mai ciratowa daga littafin nan mai suna 'alfikar bainal firak ' daga wallafin abu mansur albagadadi, kuma shi mutum ne wanda yake da tsananin bangaranci a kan masusaba wa mahabinsa, kuma baya kawo mazhabinsa daidai, sannan shi wannan Shahristani ya cirato daga wannan littafin ne, don haka ne ma aka samu kurakurai masu yawa a cikinsa game da bayanin mazhabobin .
Wannan game da batun cewa yaya yake ke nan game da cirato magana, amma a addininsa da gaskiyarsa wasu suna fada game da shi cewa:
b- Yakut alhamawi a mu'ujam dinsa:
Yana fada game da Shaharistan cewa: Ba don cakudewarsa ba a akida da kuma karkatarsa zuwa ga shisshigi, da ya kasance shi ne jagora, sau da yawa mukan yi mamaki da wannan kima tasa da hankalinsa yaya ya karkata zuwa ga wannan shisshigi da ba shi da wani asali ya zabi abin da babu wani dalili a kansa na hankali ko nakali, muna nemn tsarin Allah daga tabewa da kuma bicewar hasken imani, kuma ba komai ya jefa shi wannan ba sai kaucewa shari'a da karkata zuwa ga duhun nan na falsafa. Kuma na halarci da yawa daga wa'azozinsa amma ban taba jin ya ce: Allah ya ce: Annabi ya ce: Ba, ko kuma ya bayar da wani jawabi na mas'alar shari'a, Allah ne kawai ya san halinsa .
Bayan ka ji maganganu game da Shahristani daga mutanensa bari in kawo maka wani abu da ya fada game da Shi'a domin ka san rashin amintuwa da shi da fadinsa game da Shi'a da yake cewa: Ba su kawo wani mutum ba a matsayin Imami bayan Hasan da Husain da Aliyyu dan Husain, kai sun yi sabani mai yawa kan haka fiye da kowace jama'a, har dai ya ce: Imam Sadik (a.s) ya barranta daga abin da mazhabar rawafidawa da wautarsu suka tafi a kai na gaiba, da Raja'a da Bada'i, da tanasuhi, da hulul, da tashbihi, sai dai Shi'a bayansa sun kasu gida-gida, kuma kowa ya tafi a kan mazhabarsa daban .
Duk wani wanda ya san tarihin Shi'a imamiyya ya san cewa babu wani sabani da suka samu game da imamai tun daga Imam Ali (a.s) har zuwa na goma sha biyu Muhammad dan Hasan (a.s) kuma imamiyya tun da suka kafu haka suke. Amma abin da ya fada game da Imam Sadik (a.s) cewa ya barranta daga wautar Shi'a wannan kage ne tsantsa ya yi, kuma babu wani wanda ya taba kawo wannan, kuma ma'abota gida su suka fi sanin abin da yake cikinsa. Da akwai wani abu makamacin wannan da wanin Shahristani ya kawo shi!
Amma kuma abin da ya fada na akidun Shi'a kamar tanasuhi da hululi da tashbihi, abin da yake cike da litattafan Shi'a yana karyata hakan, ga litattafan Shi'a nan ceke a hannun al'umma tun daga na da da na yanzu sai ya kawo mana inda suka kawo akidarsu ta tanasuhi, sai dai kuwa idan yana magana ne kan wata al'umma daban da ta shude ba Shi'a ba.
Sai dai Shi'a suna cewa Imam Mahadi (a.s) ya yi gaiba (boyu) daga sanin mutane, ta yadda suna ganinsa amma ba sa iya gane shi, kuma yana iya kawo wani ra'ayi nasa a wasu lokuta a wasu wurare kuma a amfana da wannan, kuma an samu wannan a ruwayoyi da suka zo daga malaman musulmi na Sunna da Shi'a kamar tirmizi da Ibn majah, da abu dawud da Ibn hajar da wasunsu, kuma fasalin da Ibn hajar ya kawo a sawa'ik ya ishe ka sai ka koma masa, kuma da sannu zamu yi maka sharhin wannan a wasu fasaloli masu zuwa na wannan littafin. Kamar yadda yake Shi'a sun yi imani da Bada'i (bayyanar da abu sabanin yadda yake a farko) suna masu amfana daga Littafi da Sunna:
A Littafi: Kamar fadinsa madaukaki: "Allah yana shafe abin da ya so, ya kuma tabbatar -da abin da ya so- kuma a gunsa akwai ummul kitab" Ra'ad: 39.
Amma a Sunna ya zo kamar a littafin Buhari cewa: Wasu mutane uku daga Banu Isra'il da kuturu da makaho da gurgu ya bayyana ga Allah ya jarrabe su, sai ya aika musu da mala'ika… .
Kuma Saduk ya ruwaito a littafinsa na "Ikmaluddin wa itmamun ni'ima" da sanadinsa daga Imam Sadik (a.s) cewa: Wanda ya raya cewa wani abu ya bayyana ga Allah da bai san shi ba jiya to ka barranta da shi . Don haka Bada'i a wajen Shi'a yana nufin bayyanar da abu da Allah yake yi, ba ana nufin Allah yana sani bayan jahilci ba, Allah ya daukaka daga haka. Wato; ilimin Allah ya rataya da wani abu da zai faru amma sai dai sharadin faruwarsa shi ne ilimin Allah ya ta'allaka da wani abun sabaninsa. Wannan shi ne ake nufi da Bada'i daga cikin hukuncin Allah madaukaki.
Duba zuwa ga muhimmancin Bada'i da kuma abin da aka kawo na jayayya tsakanin musulmi game da shi ni zan jingina wannan alma'ari ga mai karatu zuwa ga wani fasali muhimmi da Imam khu'I ya rubuta game da wannan a littafinsa na albayan na tafsirin Kur'ani .
Amma batun Raja'a wanda yake gun Shi'a to wani abu ne na fahimta daga littafin Allah, ga wasu ayoyi da suke kunshe da hakan, hada da wasu ruwayoyi da suka zo kan hakan suna masu karfafar wannan al'amarin na Raja'a, kuma mu sani ba ta daga cikin larurin musulunci gun Shi'a, kuma mai karatu yana iya komawa zuwa ga fadinsa madaukaki "Ranar da zamu tashi wasu mutane daga kowace al'umma".Nahal: 83.
Da fadinsa madaukaki: "sai muka tashe su ba mu bar koda daya ba" kahafi: 47.
Kuma ya zo a litattafan tafsirai gun dukkan malamansu da abin da yake tsakanin wadannan ayoyi biyu da yake nuna mana cewa akwai wani tashin kafin babban tashi, kuma wannan ya zo a ruwayoyn Ahlul-baiti (a.s) kuma sheikh Saduk a littafinsa na al'i'itikadat ya kawo fasali game da Raja'a kuma ya ambaci wannan ayoyi da hadisai a kan hakan, daga karshensa ya kawo cewa fadinsa madaukaki:
"Sai suka rantse matukar rantsuwa cewa Allah ba zai tashi wanda zai mutu ba, ba haka ba ne, alkawari ne a kansa, sai dai mafi yawan mutane ba su sani ba". Nahal: 38. Sannan sai bayan wannan aya kai tsaye ya ce:
Domin Allah ya bayyana musu abin da suke sabani, kuma wannan bayyanarwa tana kasancewa a duniya ne ba a lahira ba kuma wannan ayar tana magana ne kan Raja'a kamar yadda Saduk ya fahimta daga gareta, har dai Saduk ya ce; Sai dai ina mai cewa tayiwu wasu su fahimci tanasuhi daga maganar Shi'a sai su ce; akwai shi gun Shi'a alhalin batacce ne gunsu, kuma duk wanda ya tafi a kan tanasuhi kafiri ne, domin akwai karyata wuta da aljanna a cikin tanasuhi .
Don haka mas'alar Raja'a ba ta wuce fahimtar littafin Allah da kuma yiwuwar komowa wani lokaci ayyananne kuma duk wannan bai jawo ka ce-nace ba a littafin Ahlus-sunna, kuma da yawa zaka samu ra'ayoyi gun ahlussunnna wanda zamukawo wasunsu amma ba su jawo ka ce-nace ba, sai dai marubuta Shi'a suna yi musu bayani ne ta mahangar ilimi ba tare da wani suka ko takurawa ba, kuma suna girmama fahimtar kowane marubuci matukar yana daga nassi ne na Kur'ani ko Sunna, don haka sai in koma zuwa ga Shahristani yayin da yake cewa: Bayan Musa dan Ja'afar sai Shi'a suka ce; Imami bayan Musa shi ne Ali dan Musa arRidha kuma kabairnsa yana Dus ne, sannan sai Muhammad attaki bayansa yana makabartar kuraishawa ne, sannan sai Aliyyu dan Muhammad bayansa kuma kabarinsa yana Kum ne, sannan sai Hasan askari bayansa azzaki, sannan sai Muhammad dansa a bayansa almahadi wanda ake sauraro, wannan kuwa shi ne tafarkin Shi'a isna ashariyya , kuma dukkan masana sun sani cewa Shi'a ba sa fadin cewa Ali dan Muhammad annaki an binne shi a Kum ne, domin an binne shi a samra'u ne, kuma mutane suna ziyartarsa har yau, wanda aka binne a Kum ita ce 'yar'uwar Imam Ridha (a.s).
2- Ibn Hazam al'andulusi:
Wannan shi ne misali na biyu da zan gabatar da shi, shi yana daga mutanen da suka sanya kaifin harshensu da suka kan musulmi, kuma shi ne Aliyyu dan hammad dan Hazam al'andulusi alfarisi kuma ya ishe shi daukaka cewa kakansa khalaf yana daga na farkon wadanda suka shiga andulus. Da farko Ibn Hazam yana riko da mazhabar Shafi'iyya ne, sannan sai ya koma zahiriyya, kuma yana da litattafai masu yawa, daga ciki akwai alfasal filmilal wannihal, da almuhalla da sauransu, yana da yawan rainin wayo mai ban mamaki kan yin kage kan mutane, kuma yana da jur'ar suka da harshensa kan mutane, wadannan al'amura suna nuna karancin tsantseninsa da kuma rashin lizimtarsa ga gaskiya, kuma zan kawo maka wasu daga maganganunsa da ra'ayoyin mutane kansa da yadda suke ganinsa.
Abul Abbas dan arfi yana fada game da shi cewa harshen Ibn Hazam da takobin Hajjaj tagwaye ne. Abu Marwan Bn Hayyan mai kawo Tarihin Andulus ya ce: Yana daga cikin abin da ya sanya kin mutane gareshi tsananin son sa ga Banu Umayya tun na farkonsu har na karshensu, da kuma imaninsa da ingancin jagorancinsu har sai da aka dangata masa kin Ahlul-baiti (a.s).
Ibn Imad Hambali ya ce: Ibn Hazam ya kasance mai yawan sukan malamai da magabata, babu wani da ya tsira daga harshensa, sai duk zukata suka ki shi.
Mustapha burlisi albulaki yana fada game da shi cewa: Amma Ibn Hazam to yana daga malaman da ba su da wata kima, kuma kamar yadda malamai suka nakalto game da shi daga cikinsu akwai mai littafin attaj subki, da waninsa cewa ma'abotansa 'yan zahiriyya ne tsantsa da kusan hankulansu shafaffu ne, kai har sun kai ga cewa idan mutum ya yi fitsari a ruwa ya zama najasa, amma idan ya yi a kwano sannan sai ya zuba shi a ruwa to ruwan bai zama najasa ba, yaya kuwa za a cewa wannan mutumin yana da hankali balle a sanya shi cikin malamai. Kuma Ibn Hazam da ire-irensa suna da irin wadannan camfe-camfe da ba su da iyaka, kuma duk wanda ya yi la'akari da karyar da yake yi wa malamai musamman imamin Sunna abul hasan ash'ari ya san cewa yana da kyau abin da ya fi cancanta da shi da ire-irensa shi ne a jefa su kwandon shara da kuma yin banza da abin da ya zo daga garesu. Kuma ga abin da muka rubuta game da Ibn Hazam da yake a kasa, ya yi bayani sosai game da shi da tarihinsa .
To bayan shaidar wadannan malamai wadanda bisa hakika suna da wata haduwa a maslahar ra'ayoyi game da Ibn Hazam, to ni ba zan kawo wani bayani dogo ba game da abin da ya fada kan Shi'a sai fadin nan nasa da yake cewa Mutanen -Shi'a- a dunkule ma'abota addini ne batacce da hankula masu rauni kuma marasa kunya ne kuma muna neman tsarin Allah daga bata .
Idan dai wannan da irin Shahristani su ne suke rubuta wani abu game da akida da fikihu da kunguyoyin musulmi to shin zai iya yiwuwa kuwa al'umma mai zuwa ta aminta da tarihinta da kuma halayen marigayanta. Mafi muni daga hakan shi ne duk wadanda suke sukan Shahristani da Ibn Hazam suna yin hakan ne kawai idan dai sun suki mazhabinsu amma idan suka suki wani suka yi masa kage kamar Shi'a to wannan maganar gaskiya ce kuma ana karba, kuma maganarsu ba ta tayar da wata jijiyar wuya.
Misali na uku:
Da sannu zamukawo maka wasu misalai kan hakan, sai dai zamu gaggauta maka da guda daya da yake rayuwa a karni na ishirin, karnin wayewa karkashin sababbin jami'o'i wato shi ne Muhammad hito marubuci game da littafin mankhul na Gazali, wannan mutumin yayin da ya wuce wasu bayanai na Gazali game da wasu mazhabobin musulunci kamar Maliku da Ahmad dan hambal, da Abuhanifa sai ya kawo wasu ra'ayoyi nasu yana mai yi musu nakadi wani lokaci kuma yana mai sukan su. A misali Gazali ya kawo ra'ayin Abuhanifa a salla da yake cewa al'awala da nabiz (tsumin/giyar dabino) a farkon salla, da kuma hadasi -yin wani abu mai karya ta- karshenta, da kuma koton hankaka (koton kurciya) a tsakiyarta da kuma isuwa da mafi karancin kalma a salla kuma da Farisanci kamar "Mudahammatan" har dai zuwa karshen abin da ya kawo game da salla a ra'ayin Abuhanifa, sannan kuma ya kawo ra'ayin Maliku na halaccin kashe sulusin mutane idan akwai maslaha ga sauran sulusain da wasu ra'ayoyinsu da ya kawo.
A irin wannan al'amarin sai muka ga Muhammad Hasan hito yana fadawa cikin dimuwa bai san yadda zai yi ba, ko ya kore wannan, hakan kuma yana nufin karyata Gazali, ko kuma ya tabbatar da hakan wannan kuwa yana nufin suka ga shugabannin mazhabobin, sai gashi wani lokacin yana cewa: Wadannan maganganun sun faru ne sakamakon wata marhala ta rayuwa da Gazali ya shige ta, kuma ya bar wannan ra'ayi bayan nan, sannan kuwa sai ga wani lokaci yana cewa Gazali daya ne daga malaman da suke karfafa ahlul Hadis suke sukan ma'abota ra'ayi kuma wannan bangaranci ne da al'amari ne da Gazali ya bar shi daga baya a cikin litattafansa da suka zo bayan hakan kamar almustasfa.
Duk da kuwa zamu ga cewa wannan uzurin ba ya warware matsalar: Ko dai Gazali ya kasance makaryaci ko mai gaskiya, amma dai abin da yake damun mu a nan shi ne idan Gazali ya soki Shi'a a litattafansa to babu wani uzuri da za a bayar na cewa ya yi bangaranci ne da yake al'amari ne da ya bari daga baya ko wani abu makamancin hakan, kamar dai su Shi'a su ne suka cancanci zagi babu wata jayayya, kamar dai hadin kai tsakanin musulmi bai shafi wannan mas'alar ba idan dai Shi'a musulmi ne a wajen wadannan, idan kuwa ba haka ba, to wannan mas'ala zata kasance ba tada wani matsayi. Mun kawo irin wadannan kalamai ne domin mu yi matashiya ga ra'ayin hito game da Gazali ne kawai .
Daga karshe nake cewa: Dukkan abin da muka kawo game da shaida da misalai game da iyakance matsayin Sunna gun Farisawa da kuma bayanin matsayin larabcin Shi'anci ga wanda yake ganin wannan tawaya ce kuma waccan falala ce, amma dai musulmi da takensa shi ne taken Kur'ani da yake ganin dukkan musulmi a matsayin madaidaita ne a dukiyarsu da jininsu da mutuncinsu da nasabarsu. Idan dai akwai wasu abubuwan aibi ko na yabo da suka faru daga jini ko kabila shin bafarise dan Shi'a ne ko kuma bafarise dan Sunna ne babu wani bambanci kan hakan, kuma da haka ne muke iya bayar da cikakken adalcin daidaito a Shi'anci ko sunnanci, kuma duk wanda yake son fadadawa yana iya bin hanya ya yalwata bincike a kai game da wannan maudu'in.
Fasali Na Shida
Dalilan Jifan Shi'anci Da Farisanci
1- Domin mu amsa wannan tambaya muna iya cewa:
Babu wata hususiyya ga wannan tuhuma da Farisanci, kawai dai wani abu ne da aka kawo ta fuskacin jifa da dukkan wani abu da ake ki, kuma tunda alakar Larabawa da Farisawa ta yi tsami bayan Farisawa sun samu matsayi a daular musulunci kamar yadda muka yi nuni a baya, sai makiya Shi'a suka so jifansu da wani abu daban na Farisanci domin sun sanya karin aibi kan aibi.
Ta wani bangaren kuma yayin da Shi'a suka kasance tun farkon su suna fama da sabani da hukumomi ne domin suna ganin jagoranci da halifanci daga nassi ne ba da shura ba kuma cewa jagoranci na Imam Ali (a.s) da 'ya'yansa ne, kuma ya hakura ne tun farko domin maslahar musulmi da kuma sadaukar da kai da hakuri mai muhimmanci saboda cimma abin da ya fi muhimmanci wanda wannan ya kai ga kiyaye musulunci, kuma wannan imani nasu ya jawo musu bin diddiginsu musamman lokacin Mu'awiya da abin da ya biyo bayansa na zamanoni, haka nan kuma hukumomin sun dandana musu duk wani bala'i da gana musu duk wata azaba da kuma kawar da su daga fagen jagoranci da dukkan abin da suke mallaka na rusa wa ga Shi'a a matsayinsu na wadanda suka fita daga cikin biyayya, sannan kuma sai aka jingina wa Shi'a duk wani ra'ayin da yake nesa da musulunci aka kuma sawwala su a matsayin masu kira zuwa ga yamutsi da rikici kuma da yi musu dukkan kamu, kuma sai aka samu damar cewa faduwa ta zo daidai da zama musamman samuwar matsalar rashin jituwa tsakanin Farisawa da Larabawa don haka sai aka kawo wannan tuhuma domin a kara wa wutar fetur, da kara wa wuta zafi ba tare da kiyaye wani hali na gari na musulunci kan wannan kage da ake yi musu ba, kuma sai faduwa ta sake zuwa daidai da zama cewa kudi da abin rubutu da hukuma da dukiya duk suna hannun Shi'a, sai wannan ya kai ga haifar da irin wannan nau'i na kage, sannan kuma duk wani mai daukar makami ya zama ba shi da wani wanda zai yi gwaji a kansa sai Shi'a, kuma duk wanda bai shahara ba sai ya nuna wa duniya kansa ta hanyar shahara da zagin Shi'a, to sai Shi'a suka zama wani abu da kowa yake yin gwaji kansa domin ya kasance wani gwarzo kuma ya yi jur'ar yin hakan komai kuwa dakushewar takobinsa kuma komai makyarkyatar da hannayensa suke yi.
2- Dalili na biyu na jifan Shi'a da Farisanci
Wannan yana daga cikin abin da muka yi nuni da shi a baya cewa faisanci bai kasance abin zagi ba lokacin da Farisawa suke Sunna, wannan zagin ya kasacne ne lokacin da Farisawa suka koma Shi'a, kuma mun kawo dalili a kan cewa kana iya ganin dabakar farko da ta biyu suna daga wadanda suka hau Shi'a da suka da kage ba su yi irin wannan kagen Farisanci ba, kuma kana iya komawa abin da Ibn abdu rabbihi andulusi ya rubuta a akadul farid a fasali na biyar game da Shi'anci a gun da ya kawo suka kansu amma ba zaka samu wannan sukan ba . Haka nan da zaka koma wa abin da Shahristani ya rubuta a milal wannihal dinsa da abin da ya fada game da Shi'a zaka ga babu tuhumar Farisanci a ciki daga tuhumomin da ya kawo .
Haka nan shaihin masu zagi wanda yake da harshen da bai san wani tsantseni ba to duk da irin kagensa da ya yi da abin da ya cika shi na son rai kan abin da ya fada kan Shi'a bai kawo irin wannan tuhumar ba .
Kuma muna iya ganin Ibn Hazam ya kawo cewa akwai wasu Farisawa Shi'a cikin abin da ya kawo kamar yadda mukrizi ya kawo a karni na tara, sai ya so ya kawo cewa Shi'anci bafarise ne, don haka muna iya ganin mas'alar ta zo daga karshe ne , kuma akwai wadanda suka zo daga bayan wannan dabakar amma ba su kawo wannan irin suka ba a cikin soke-soke da tuhumar da suke yi wa Shi'a, wannan dai ya zo a bayan karni na tara da na goma ne. Wani abin mamaki shi ne cewa wasu daga gwarazan wannan sukan su ma Farisawa ne kansu sai suka nuna sun fi Larabawa son Larabci fiye da su larabawan kansu, Allah ya yi rahama ga wanda yake cewa:
Sannu dai da nasabar Amru yayin da kake nasabta shi
Domin hakika cewa shi balarabe ne daga Kawarir
Kuma babu wani mamakin cewa yana da wani mummunan hadafi kan hakan, don haka ne ma suka zamanto mustashrikai kamar yadda zai zo nan gaba:
3- Dalili na uku na jifan Shi'a'ci da Farisanci
Wannan kuwa yana cikin fadin Shi'a ne na cewa halifanci bisa nassi ne daga Allah madaukaki ba da shura ba, domin masu kawo dalilin shura suna kafa dalili da fadinsa ne: "Al'amarinsu shawara ne tsakaninsu" shura: 38. da kuma fadinsa: "Ka yi shawara da su cikin lamarin" aali imrana: 159. Tare da cewa wadannan ayoyi biyu ba su da wata alaka da wannan maudu'in domin fadin Allah madauaki "Al'amarinsu shawara ne tsakaninsu" yabo ne ga ansar (mutanen Madina) da suka kasance suna shawara kafin musulunci duk sadda suka so yin wani abu sai su yi shawara tsakaninsu kuma ba sa tilasta ra'ayinsu kan wani, amma fadinsa madaukaki: "Ka yi shawara da su" wannan yana son ya dadada zukatansu ne da jiyar da su cewa su ma'abota shawara ne domin ya karfafe su, sai Annabi ya kascne yana shawara da su a kan al'amarin yaki da wasu abubwan da suka shafi duniya, kuma mai karatu yana iya komawa zuwa ga tafsirai masu girma kamar tafsirin fakhrur Razi, da kasshaf na Zamakhshari, da Majma'al bayan na dabrasi, da wasunsu, kuma duk wadannan suna da bayani kan abin da na gaya maka, suka ce: Shawarar da Annabi yake yi da musulmi tana kan abin da babu nassi a kansa ne, wannan kuwa sun kawo shi yayin da suke fassara wadannan ayoyin biyu ne da muka ambata.
Don haka ayoyin biyu ba su sauka kan al'amarin zabar jagora ba ta hanyar shura, kuma wasu sun so ne kawai su amfana da wadannan ayoyi n kamar haka:
Suna cewa: Tun da halifanci wani abu ne da Annabi (s.a.w) ya yi shiru bai dora wani a kai ba, kuma tun da Kur'ani yana yabon shura a kan al'amura masu muhimmanci to sai mu koma zuwa ga tsarin shura , amma Shi'a sai suka ki wannan suka tafi a kan cewa:
Na farko: Annabi (s.a.w) ya kasance idan ya yi tafiya ba ya barin Madina ba tare da wani jagora ba koda kuwa tafiyar kwana daya ce, to yaya zai tafi ya bar al'amuran mutane ba tare da wani mai kula ba.
Na biyu: Ya tabbata cewa shari'ar musulunci ta farlanta wa kowane musulmi yin wasiyya hatta a kan wani abu da ya shafi gado mai sauki, a kan haka ne Kur'ani mai girma yake cewa: A surar bakara: Aya ta 180: "An wajabta muku idan mutuwa ta zo wa waninku idan ya bar alheri (dukiya ko wani abu) to wasiyya ga iyaye da makusanta da ma'arufi kuma tabbas ne wannan a kan masu takawa" to yaya kuwa zai bar wannan al'amari mai muhimmanci ba tare da ya yi wasiyya da shi ba alhalin samun zaman lafiyar al'umma ya doru kan haka ne, kuma idan babu wannan to al'amarin zai koma zuwa ga jayayya!.
Na uku: Akwai dalilai masu yawa a Littafi da Sunna kan cewa jagoranci Allah ne yake bayar da shi, kuma akwai fadinsa madaukaki: "Muka sanya su jagorori ne da suke shiryarwa da umarninmu" surar anbiya: 73.
Da fadinsa madaukaki: "Kuma muna son mu yi baiwa ga wadannan da aka raunatar a ba'yan kasa… kuma muka sanya su jagorori" kasas: 5.
Da fadinsa madaukaki: "Kuma muka sanya su jagorori ne da suke shiryarwa da umarninmu yayin da suka yi juriya" sajada: 24.
Wannan wasu daga sashen wasu ayoyi ne da ake kafa dalili da su kan cewa Imamanci daga Allah yake. Hada nan akwai wasu nassosin daga Annabi (s.a.w) a kan jagora bayansa, daga cikin wannan akwai abin da ya wakana a Gadir yayin da fadinsa madaukaki "Ya kai wannan ma'aiki ka isar da sakon da aka saukar zuwa gareka daga Ubangijinka" ya sauka. Ma'ida: 70, Sai Annabi (s.a.w) ya tara mutane ya yi huduba sananniya din nan wacce a karshenta ya ce: Shin ba ni ne nake mafi cancantar ku fiye da kawukanku ba, sai suka ce: Haka ne. sai ya ce; Allah ka shaida kuma kai ma jibril ka shaida ya kuma maimaita sau uku. Sannan sai ya kama hannun Ali dan Abu Dalib ya daga shi har sai da aka ga hasken hammatarsu, sannan sai ya ce: Duk wanda nake jagoransa to wannan Ali jagoransa ne, yaUbangiji ka shaida ka kuma ki wanda ya ki shi, ka taimaki wanda ya taimake shi, ka tabar da wanda ya ki taimaka masa, ka la'anci wanda ya kafa masa kiyayya da gaba" har zuwa karshe.
Kuma sahabi dari da ishirin da tabi'ai tamanin ne suka ruwaito wannan sako, kuma wannan adadi na wadannan masu ruwaya daga shugabannin hadisai ya wuce masu ruyawa dari uku da sittin, kuma marubutan Shi'a da Sunna ishirin da shida ne suka wallafa littafi kansa, kuma sun kawo duk bahasi kan al'amarin sosai .
Kuma duk da wannan nassi mai yawa kan wannan al'amarin da ya bayyana karara amma sai ga shi ba ka rasa wanda zai yi wa wannan nassin tawili na rainin wayo, sai ga wani yana cewa wannan hadisin bai zo ba sai a litattafan Shi'a kamar yadda Ahmad shalbi yake fada a littafinsa, sai ga shi kana jin wanda zai ce ai Shi'a ne suka sanya wannan ruwayoyi cikin litattafan Sunna da makamancin wannan maganganun na wauta wadanda suka yi kama da tatsuniyoyin masu gazawa. A takaice dai wannan wani maudu'i ne na Imamanci (jagoranci) an rubuta gomomin litattafai kansa kuma ba shi ne mahallin maganarmu ba, sai dai na kawo shi ne don ya gindaya, kuma ya bayyana cewa Shi'a sun dogara da nassi ne kan maganar jagoranci ba shura ba, domin kuwa shura a nan ba ta da wani dalili daga Kur'ani da Sunna a nazarinsu, ita dai kawai wani kokari ne na su musulmin da suka yi tsammanin babu nassi a nan. Sannan kuma su Shi'a suna tambayar ina shura din take kuma mene ne rukunanta da sharuddanta, yaya take, kuma cewa shin an yi ta a lokacin halifofi ne, kuma don me ya sa halifofi ba su ma yi amfani da ita ba, kai ba sa ma ambatonta, hada da cewa mutum biyu ne suka yi wa halifa na farko bai'a a Sakifa, wato halifa na biyu da abu Ubaida. A wata ruwayar mutane hudu ne kamar yadda halbi ya kawo a sirarsa, da Buhari a babin falalar Abubakar, don haka ne ma sai ga wasu daga Ahlus-sunna suna cewa: Ai jagoranci zai iya yiwuwa da mutane biyu kawai daga jagororin nadi. Kuma wannan a fili yake cewa wannan ra'ayin yana neman gyara abin da ya faru a Sakifa ne kawai da kuma kawar da tanakudin da yake cike da al'amarin nazarin nan na ra'ayin shura, domin babu wani mai hankali da zai sawwala cewa a zabi halifa daga mutane biyu kawai kuma sai wannan ya kasance ya wakilci duk sauran musulmi, idan kana son sanin adadin wadanda suka yi bai'a da kuma adadin wadanda suka yi nadin sai ka koma wa wadannan litattafai .
Kuma maganar gaskiya ta kalmar nan ta halifa na biyu Umar dan Khaddabi ta sawwala mana yadda matsayin bai'ar take yayin da yake cewa: Halifancin Abubakar fitina ce da Allah ya kare musulmi sharrinta, kuma wannan bayanin na halifa da ya yi yana karfafa mana cewa bai'ar ba ta kasance bisa wani tsari da ya rigaya ba .
Masu tarihi sun kawo cewa mutane biyu ne suka yi bai'a, sannan sai wannan bai'ar ta cika daga baya kuma ba ta ketare wasu daga gidajen Madina ba. To yanzu shin za a samu yin shura da ta iyakantu da mutane biyu kawai ko ma gari guda gaba dayansa tare da cewa al'amarinsu shawara ne tsakaninsu ya hada dukkan musulmi ne gaba daya, idan kuma ba ta shafi dukkan musulmi ba to ashe ke nan ita shura ba wata dalili ba ce kamar yadda yake a fili, kai mafi muni daga wannan ma ka ga wani malami daga malaman Sunna yana cewa: Ma'anar shura yana iya tabbata koda da mutum daya ne ma, mai fadin wannan magana kuwa shi ne Ibn Arabi bamalike yayin da ya kawo shi a tafsirinsa ga ma'anar shura.
Sannan kuma akwai wata tambaya kamar haka: Shin halifa na biyu ya karbi hukunci da jagoranci karkashin shura ne ko kuma ta hanyar ayyanawa da halifa na farko ya yi masa kamar yadda ya faru , sannan kuma Shi'a suna da tambaya ta uku cewa shin halifa na uku da ya karbi jagoranci ta hanyar shura ne ko kuma ta hanyar mutane biyar da halifa na biyu ya ayyana su kuma babu wanda ya zabe shi sai mutane uku . Don haka ne ma babu wani masani marubuci da ya dogara da ra'ayin hsura a shari'ar musulunci a nazari ko a aikace.
Amma yanzu mu dawo kan al'amari na uku sai mu ce; tun da dai nazarin ra'ayin shura ba shi da wani karfi yayin da kuma nazarin ra'ayin nassi daga Allah yake da hujjoji masu karfi da ya tsayu a kansu, amma sai wasu suka so su nisantar da wannan dalili daga musulunci sai suka kawo cewa wannan abu ne da Farisawa, suka ce sarakunansu da ma sun tafi a kan hakki ne na Allah, kuma tunda Imam Husain (a.s) ya yi surukuta da Farisawa to sai ya auri 'yar Yazdajir, sai wannan hakki na Allah ya ciratu zuwa gareshi, kuma mun riga mun yi bayanin wannan a farkon littafin.
Don haka hadafin kawo wannan ba komai ba ne sai domin a rushe dalilin nan na cewa akwai nassi da wasiyya, domin a kawar da shi daga musulunci a nuna wani abu ne na gado na Farisawa da suka shiga Shi'anci da shi tare da su. Kuma idan ka ce da wadannan mutane ai wasiyya ta tabbata da nassi kafin Farisawa su shiga musulunci sai su ce; ai wannan ruwayoyi ne da Farisawa suka raba su a litattafan Sunna, sannan kuma idan ka kawo musu hanyoyi daban-daban na wannan ruwayar sai suce maka ai wannan wasiyyar da kuka tafi a kanta to ita a kan al'amura ne masu sauki kananna kuma ba ta da alaka da maganar halifanci.
A gani na wadannan su ne manyan dalilan da suka sanya jifan Shi'anci da Farisanci, wato cewa ya zama wani abu ne da zai rusa kansa daga cikinsa sakamakon samun wani dalili na daban wanda yake bayyana hakikaninsa. Sai kuma mustashrikai suka zo daga baya suka hau wannan turbar da duka, a tare da su akwai dalibansu mabiyansu suna masu rawa da wakarsu (duk inda suka karkata sai su ma su karkata) sai hadafinsu wanda ba ya buya ya kasance jifan tsuntsu biyu da dutse daya, (wanda yake shi ne tarwatsa hadin kan musulmi) sannan kuma su kawo musu rudun tunani, don haka ne ma zaka samu litattafan mustashrikai suna karfafa wannan al'amari kuma suna kawo abubuwa da yawa karkashinsa, kamar dai wannan al'amarin ya kebanta da Shi'a ne kawai, amma su Farisawa Sunna to su an kare su daga kawo dasisar tunanin Farisanci cikin sunnanci koda kuwa sun kai tamanin cikin dari ne.
Ba ina kore sauran dalilai ba ne na jifan Shi'anci da Farisanci, wani lokaci zai iya yiwuwa a samu kuskuren fahimta ko mummunar fahimta da za a dauki tasirin wasu ra'ayoyi biyu kuma yana iya kasancewa haka ne, amma dai kasancewar ra'ayin Shi'anci a wata mahanga ya yi daidai da na Farisawa a wata mahangar ba ya iya sanya cewa Shi'anci daga Farisanci yake, musamman da yake fikirar addini a akida da hukunci ta dogara da Littafi ne da kuma Sunna, yayin da fikirar Farisawa na da can wani abu ne na al'ada da ba shi da wata alaka da shari'ar musulunci ko wasu shari'o'in balle a ce wadannan ra'ayoyin masu kima na addini sun samu ne daga tunaninsu na al'ada.
?
Yaya Farisawa suka zama Shi'a?
Idan muna son binciken tarihin yanayin Farisawa zamu samu cewa wadanda suka zama Shi'a daga cikinsu sun kasu kamar haka:
1- Kashi na farko:
Wannan kashin su ne wadanda suka zama Shi'a ta hanyar zabin kansu ta hannun sahabban da suka yi yakokin bude kasashe, kuma suka dauki wannan akida ta Shi'anci, kuma an samu karin karfin giwa da taimakawa wajen karbar Shi'anci cewa karbar Shi'anci a wannan lokaci ba ya sabbaba musu matsaloli, domin shi wani abu ne wanda aka riga aka saba da shi musamman saboda a wannan lokaci Shi'anci ya nisanci duk wani abu da zai kawo sabani da bacin rai, kuma da cewa fikirarsa ta kasance game da akida ne kawai da nisantar al'amuran siyasa, kuma mafi shaharar sanannen yankunan da ya yadu su ne Khurasan, sannan sai Kum.
2- Kashi na biyu:
Su ne wadanda suka zama Shi'a suna masu tausayawa ga Shi'a saboda wahalhalu da takura da suka samu a wannan zamanin kuma ya kasance su ma suna cikin takura tare da Shi'a, irin wadannan su ne mawali wadanda suke masu yawa ne kuma suke rayuwa a garuruwan musulmi ne ko kuma wadanda suka samu takurawa a cikin Iran. Sai wasu jama'a masu yawa da muhajirai (mutanen Makka) suka rika zuwa suna taruwa tare da su saboda shi'ancinsu, wadanda ziyad dan babansa ya kora sama da dubu hamsin zuwa Khurasan domin Kufa ta huta kuma ta kubuta daga Shi'a wani lokaci ma daga rashin zama lafiya, kuma sai wannan al'amarin ya sanya akidarsu ta yadu a inda ake kora su, kuma an samu cewa tarkura musu ya dauki lokaci mai tsawo, abin da ya taimaka wannan akida ta kafu daram, domin sau da yawa tarkura da muzgunawa sukan taimaka wa akida ta kafu daram.
3- Kashi na uku:
Su ne wadanda suka zama Shi'a ta hanyar al'adunsu masu zurfi, domin Shi'a suna son su zurfafa al'adunsu ta hanyar shiga bahasi na ilimi da binciken ra'ayoyin mazhabobi da addinai mabambanta domin su zurfafa kuma su karfafa iliminsu, kuma su bayar da kariya ga mazhabarsu da addini gaba daya musamman ma ganin yadda suke samun suka ta fuskoki mabambanta na marasa tausayi, kuma musamman karfi da hukuma ba hannunsu suke ba, sai wannan ya sanya da yawa daga akidunsu suka yadu a kasashen Farisa saboda abin da suke da shi na wayewa da hujjoji masu iya kariya ga akidun Shi'a wacce ba takobi ce ko zubar da jini ko kuma raba dukiya ko kwadayi ya yada ta ba, sai dai domin samun nutsuwa da hujjoji kawai.
4- Kashi Na hudu:
Su ne wadanda suka shiga Shi'anci tare da wasu jama'a da hukuma ce ta ingiza su, kuma suka shelanta wajebcin karkata zuwa ga mazhabar Shi'anci, wadannan 'yan kadan ne da ba su da wani yawan azo-agani, kuma wasunsu irin wadannan sun shelanta shi'ancinsu a zahiri ne kawai domin ba yadda za a yi a tilasta wa mutum yin akida. Wannan kuwa ya kasance ne yayin da sarki Khuda bande ya shelana hakan, sannan kuma daga bayansa safawiyyawa suka zo a farkon karni na goma suka shelanta mazhabar Shi'a a matsayin mazhabar daular kamar dai yadda ya faru a "Diyaru bakr" da "Rabi'a" wadanda suka kasance Shi'a lokacin hamdaniyyin, sannan sai sarakunan da suka yi juyin mulki suka mayar da ita sunnanci, kuma kamar dai yadda ya faru a Misira bayan hukumar fadimiyya sai aka mayar da ita sunnanci a lokacin ayyubawa, kuma dai kamar dai yadda ya faru ga garuwa masu yawa.
Ba ina rayawa cewa sam babu wanda ya shiga Shi'anci da mummunar manufa ba, domin da yawa daga Yahudawa akwai wadanda suka shiga musulunci domin su bata shi, kuma suna bayyanar da cewa su mutane ne nagari ne, alhalin a cikin rayukansu akwai kiyayya mai tsanani gareshi, kuma wannan ba laifin addinin musulunci ba ne, kamar dai yadda aka samu wasu jama'a sun shiga musulunci ko mazhabar Shi'anci amma suna da wani hadafi mai guba wadanda ba zasu iya yin wani tasiri ba, kuma ba zasu iya zama hadari ba, saboda shi ainihin musulunci abin karewa ne duk da kuwa akwai irin wadannan, kuma ba zai yiwu mu hukunta addini da wannan ba ko wata mazhaba saboda kawai wasu daga cikin masu dasisa da aka san su da munanan akidu sun shiga cikinsa, musamman ma idan asasin mazhabin ya kasance bayyananne a fili yake da ba yadda za a yi masu dasisa da munafunci su yi tasiri a kansa. Nacewa da hukunta wata mazhaba da dora mata nauyin laifin aikin wasu masu dasisa na wauta ko bata bai dace da ma'aunin hankali ba.
Babi Na Uku
Hakikanin Akidun Shi'anci
Akwai Fasulla A Cikinsa
Fasali Na Farko
Share Fage
Kafin mu shiga cikin wannan maudu'in babu makawa ne mu yi nuni da wata magana mai muhimmanci da ya kasance dole ne a fara da ita wacce da yawa masu rubutu game da Shi'anci suka samu rudewa a cikinta sakamakon wasu dalilai, kuma wannan ya kai su ga nisantar hakikanin gaskiya da samun rikicewa da kuma wasu maganganu na karya masu kama da gaskiya.
Abin takaici irin wadannan maganganu na rudu sun samu gindin zama a cikin tarihi kamar dai gaskiya ne su, kuma an karbe su a matsayin abin da kowa ya yarda da shi da wadanda suka zo daga baya suke karba daga magabata ba tare da komawa bayan ba da tabbatarwa da dogaro da ma'aunan ilimi, kuma lallai alhaki ya girmama a wuyan wadanda suka haifar da wadannan abubuwan suka wuce suka bar wadannan ra'ayoyin masu cike da guba ana samun jarraba musulmi da su, kuma Allah muke neman ya yi mana maganinsu, don haka ga wasu 'yan muhimman bayanai da zamu fara da su:
1- Bayani na Farko:
Shi'an da nake rubutun nan game da su kuma nake kare su, su ne; Shi'a imamiyya isna ashariyya, wadanda su ne suka hada jama'ar Shi'a a yau, wadannan da litattafansu suka cika duk laburorin nahiyoyin duniya, idan ka dama kana iya cewa su ne wadanda tunaninsu yake rayuwa a yanzu, kuma suke rayayyu, kuma ake rubuta ra'ayoyinsu a litattafan fikihu da akida da tarihi, ni ba ina magana kan Shi'a a lugga ba ne wadanda suka tafi a kan fifikon Imam Ali (a.s) a kan waninsa sai suka san Shi'anci da wannan ma'anar kuma suka ninsanta daga abin da Shi'anci ya kunsa na akidu da fikihu. Domin akan samu wanda ake kiran sa Shi'a ne amma ba shi da wani abu na Shi'anci sai dai kawai ya yi imani da cewa Ali (a.s) ya fi waninsa, ko kuma shi rayayye ne bai mutu ba. Irin wadannan mutane babu su a yau, sai dai amma wasu suna kakaba su cikin 'yan Shi'a har zuwa yau din nan.
Irin wannan magana ya kamata a yi mata dariya kuma a yi mata kuka, abin dariya a nan da ake kiran irin wadannan mutane da sunan mazhaba, abin kuka a nan shi ne yadda al'amarin musulmi ya kai ga suna amfani da irin wadannan tunane-tunane domin kawai su soki 'yan'uwansu, bari in kawo maka misali game da wannan maudu'i sai ka kula sosai:
Razi ya kawo a littafinsa na "I'itikadatu firakil islam" cewa kamiliyya wasu jama'a ne daga 'yan Shi'a, sannan sai ya ce:
Suna rayawa cewa sahabbai dukkaninsu sun kafirta yayin da suka mika jagoranci ga Abubakar, kuma Ali ma ya kafirta saboda bai yaki Abubakar ba. Sannan wadannan mutanen da Razi bai kawo matsayinsu ba ko adadinsu a mahangarsa su wata jama'a ce, kuma dukkan akidunsu a wajensu su ne wadannan kalmomi hudu kawai, sannan kuma wani abin mamaki shi ne duk da wai suna kafirta Ali (a.s) amma wai su ma Shi'a ne a ra'ayin Razi. Wai shin ka taba jin labarin Akwas mai fadin gemu, to irin wadannan ne; wannan tanakudi (magana mai karo da juna) ya yi yawa a ce su Shi'a ne masu bin Ali (a.s) amma kuma suna kafirta Ali (a.s). Shin ka ga yadda mai gaba yake mantuwa hatta a abubuwan da suke a fili kururu, wane mutum ne wannan! Wai Razi ke nan ma'abocin hankali mai girma amma duk da haka ya kai matukar gaya wajen wannan shirme.
Ya Ubangiji muna neman tsarinka daga zamewar kafafu! Ka koma wa littafin Razi ka ga abin da ya rubuta game da wannan jama'a ta Shi'a da makamanciyarta sannan sai ka duba irin wannan tanakudin da suke ciki .
2- Bayani na Biyu:
Wasu daga cikin abubuwan da masu rubutu game da mazhabobi suke kira mazhaba a bisa gaskiya ba mazhaba ba ce, tayiwu bai wuce mutum daya ba mai wani ra'ayi da ya fita daban ko kuma nadiri ko kuma wasu jama'a da ba su kai goma ba, ko kuma su kasance babu su sun kau daga doron kasa kuma ba su da wani abu da suka bari na kufai da za a tuna su da shi sai abin da yake kwakwalwar wasu ko kuma wasu 'yan takardu na litattafai da suke dadaddu da aka kauracewa, to yaya kuwa za a danganta wadannan da mazhaba ta akida!.
Idan dai har za a samu tunanin wani mutum daya daga wata mazhaba sai a kira shi mazhaba to da kowace mazhaba ta kasu gidaje dubunnai ke nan, kuma sai ya kai mu ga kirga kowane mutum a mazhaba a matsayin mazhaba ke nan har sai dai an samu ke nan babu wani mutum mai ra'ayi na daban.
Amma ra'ayoyin da suke nadirai matukar kuwa masu wannan mazhaba ba su yarda da su ba, kuma wani abu ne da bai yadu cikinsu ba, to ba yadda za a yi a sanya shi cikin ra'ayoyinsu. Kuma wasu masu ra'ayoyin sun kare tuntuni babu irinsu amma sai ga shi har yau ana jingina ra'ayoyinsu ga wasu jama'ar da suke raye a yau alhalin su wadannan mutane sun barranta daga wadancan irin ra'ayoyin.
Bayani na Uku:
Ya zama wajibi ga dukkanin marubuci, idan har yana so ra'ayin sa ya zama yana da ma'auni ya rika zamowa yana kaffa- kaffa da abin da zai fadi, saboda abin da ka iya biyo bayan hakan na daga, tasiri da hadari da kuma rawar da maganar take takawa a cikin al'umma, babu makawa a yayin da yake yin rubutun, ya zama dogara akan masadarori ita kanta jama'ar (kungiyar da yake magana a kanta) bisa cewa lalle ne masdarin ko littafin ya zamo abin la'akari a wajen al'ummar da yake yin rubutun a kanta, kuma wandanda aka sallama a kan cewa suna bayyana matsayar al'ummar kuma suna ayyana yadda ra'ayin su yake da abin da mazhabar su ta tafi a kai, kamar sahihan hadisai a wajen Ahlus-sunna, da sahihan hadisai a wajen Shi'a, na daga abin da suka sallama a kan sa daga ruwayoyi kuma suka tabbatar da ingancin su,ba dukkanin abin da ya zo a cikin litattafan su ba, domin a cikin ingantattun litattafan na su akwai abin da ba a la'akari da shi . Tare da dukkanin hakan lalle a yi la'akari da fagen binciken da kuma abin da yake tabbatacce, balle kuma ka ga wani mai bincike ya yi rubutu a kan wasu jama'u sannan kuma matattarar bincikensa a kan su ya zamo daga cikin litattafan makiyan su ne, kuma ina ma dai makiyan da ake jingina da su wajen dauka labaran, wadanda aka sani ne da gaskiya da amana, a maiamako haka sai ka ga suna dogara da da wadanda an san su da karya da kire, sai ka ga sun dauki ra'ayin su dauka irin ta abin da aka sallama a kan ingancinsa kuma su kakkare maganarsa da duk wani abu da zai sa a rike ta kyam. Irin wannan kiren ne ke jawo kaga dukkanin irin wadannan litattafan su zama ba ababban la'akari ba. Duk lokacin da karya da kire suka zama tushen dabi'un matane, to lalle Allah Madaukaki ya hana mu gasgata fasikai.
Bayani na Hudu:
Marubucin ya kasance wanda yake yin riko da masdarin da ya kebanta da abin da yake yin rubutu a kai, ba zai yiwu a cirato wani ra'ayi na fikihu na wasu jama'u daga cikin littafin kyawawan halaye ko na kissoshi ba. Kuma ba a cirar akidar wasu mutane daga litattafan wasu kamar yadda muka ga wasu mutane suna yi, alhalin kowane bangare daga cikin bangarorin sani yana da litattafan da suka kebanta da shi. Don haka ya kamata mu koma zuwa gare su idan har muna so mu kiyaye sosai a cikin abin da muke rubutawa, in ba haka ba, ba zai zama rubutu na ilimi ba.
Lalle abin la'akari shi ne; litattafan da suke bayyana akida ko fikihu a wajenmu, kuma da yawan marubuta suna yin riko da su a matsayin matsama/matattarar bincike a kan abin da yake rubutawa na akida da hukunce-hukuncen addini, ba ina so in ce gaba daya ba a dogaro da dukkanin litattafan adabi wajenmu, kawai abin nufi shi ne litattafan ma'abota akida su suka fi damfaruwa da abin da suke magana a kansa, kuma sun fi dacewa, kuma da haka ne za a samar da masdari amintacce.
Bayani Na Biyar:
Gyararrakin da a ke yi wa litattafan bangarori da wasu suke yi na kokarin saita mazhabobin, gyararraki ne wadanda ba su dace da tsarin ilimi ba, domin kuwa abin da tsarin ya tabbatar shi ne; akida da fikihun kowace mazhaba su zamo masdarin su daya ne, daga cikin masdarorin nan na shari'a wadanda aka yarda da su, kuma wadanda shari'ar ta tabbatr da su, kamar littafi "Kur'ani" da Sunna da ijma'i da makamancin su, idan bisa misali Shi'a suka tafi a kan ra'ayin ayyanawa a cikin halifanci kuma suka zo da dalili daga littafi ko Sunna, ya kamata a yi duba zuwa dalilin su idan har dalilin ya zamo wanda ya cika sharadan inganci a kan halifanci shi ke nan, in ba haka ba sai a tattauna a kan dalilin tattaunawa ta ilimi. ba a ce: Lalle farisawa suna ganin cewa sarakunan su suna da hakkin yin mulki daga Allah ba, gama cewa Shi'a sun tafi a kan cewa da nassi ake yin halifancin ba da shura ba, to lalle sun dauki wannan ne daga farisawa.
Lalle irin wannan maganar ba zata taba zuwa daga nunannen hankali ba, yaushe ne haduwa da mutane kawai, ya zama dakkowa daga gare su. Lalle musulunci ya tafi a kan `'yan kasanci a wasu yanayoyi ayyanannu, idan gamammiyar maslaha ta tsayu a kan hakan, kuma kwaminisanci ma ya tafi a kan `'yan kasanci, shin wannan yana nufin cewa musulunci ya zama kwaminisanci ko kuma kwaminisanci ya zama musulunci, domin sun hadu da musulunci a fage guda ayyananne. Ina fatan mai karatun littafin nan zai koma zuwa litttafan bangarorin, idan har ya samu wani yanayi wanda ba wannan ba, to ya fadi abin da yake so, mafi yawan hujjojin Ibn Hazam da Shahristani da Ibn Abdi Rabbihi da wanda duk ya bi sawunsu, suna daga cikin irn wadannan misalsalin, kuma sashin su ma har fatawa suke fitawa ba tare da dalili ko abin da ya yi kama da dalili ba, ba komai ba ne sai zunzurutun kyautata zato da ya yi baki a kafu a cikin zuciyar sa kuma yaso ya dawwama shi ba tare da jin wani nauyi ba.
Bari ma in baka misali guda daya, shi ne cewa Lahwaz banasare (bayammace) yana cewa: Asalin Shi'a daga wani bayahude ne, kuma ya jingina wannan maganar tasa ne zuwa, Sha'abi, kuma lalle ma'abota litattafan mazhabobi sun cirato wannan maganar kamar irin su Ibn Hazam da Shahristani da Ibn Abdi Rabbihi Ba'andaluse. Kuma maganar da ake danganawa ga Sha'abi ita ce:
Maganar Sha'abi
Sha'abi ya ce: Ina tsoratar da kai daga soye-soyen zukata masu batarwa: Mafi sharrinsu Rafidhawa su ne yahudawan wannan al'ummar, suna kin musulunci kamar yadda Yahudawa suke kin nasaranci, kuma ba su shiga musulunci bisa son zuciya ko kwadayi daga Allah ba, son Rawafidhawa daidai yake da son Yahudawa, Yahudawa sun ce mulki ba zai taba kasancewa ba face a cikin alayen Dawud, kuma Rawafidhawa sun ce mulki ba zai taba kasancewa ba face a cikin alayen Ali, kuma Yahudawa sun ce babu wani jihadi a tafarkin Allah har sai Mahadi ya bayyana, kuma Rawafidhawa sun ce babu jihadi a tafarkin Allah har sai Mahadi ya bayyana, kuma Yahudawa suna jinkirta sallar magriba har sai taurari sun fito haka ma Rawafidhawa. Karshen maganar ke nan a takaice .
Abubuwa Biyu Da Suka Biyo Baya
Dakta Arafan Abdulhamid ya bijiro da wannan kissar a littafinsa "Dirasatun fil Firak" sannan ya biyo bayan ta yana mai warware ta, sannan ya jero abubuwa masu zuwa.
NA DAYA: Lalle Akdul Farid da Tarihu Dabari litattafan adab ne da tarihi ba litattafan Akida ba ne.
NA BIYU: Dabari ya jingina Saifu dan Umar a wannan ruwayar kuma shi makaryaci ne wanda ake tuhuma da kire, kuma lalle litattafan auna matsayin masu ruwaya "Jurhu wat Ta'adil" sun bayyana karyarsa kuma ba sa karbar mganarsa a kan komai,
NA UKU: Shi kansa Sa'abi ana tuhumar sa da shi'anci don haka bai inganta a gare shi ya fadi wannan maganar, kawai sun zabe shi ne suka kirkiri wannan kissar da yawunsa, alhali Ibn Sa'ad da Shahristani sun ambace shi a dan Shi'a, kuma bari ma in kara maka da abubuwan da Dakta Arafan ya yi tsokaci da shi.
A- Tambaya: Shin Yahudawa suna da wata sallar da aka shardanta mata lokacin faduwar rana? wannan ta wani bangaren ke nan, ta wani bangaren kuma ga litattafan Shi'a na fikihu nan baki daya, kuma nayi fito-na-fito da duk wanda ya samo ra'ayi guda daya da ya tafi a kan cewa, lokacin sallar magriba yayin faduwar taurari ne, tabba sabin da suka hadu a kai shi ne, bayan faduwar rana ne kai tsaye, kuma wasunsu kan yi taka tsantsan sai suka shardanta gushewar jan rana na yamma, don haka mai karatu na iya komawa kowane tittafi daga littafansu na fikihu.
B- Amma jihadi: Babin jihadi a cikin dukkanin litattafan Shi'a, ya isa mai yin raddi a kan wannan kiren, hukuncin jihadi a wajen su shi ne cewa abin tsayarwa ne a kowane lokaci bisa sharuda, kamar yadda yake a wajen sauran bangarorin musulmai.
C- Amma kasancewar shugabanci a wajen su dole ta zamo a cikin alayen Ali, wannan ba daga gare su ba ne lalle sun dogara ga da Kur'ani da Sunna ne a kan hakan, kuma sashin wannan ya gabata, sannan da sannu wani bangaren daga gare shi zai zo nan gaba, don haka ya kamata a yi duba zuwa dalilan su, a kuma yi mata hukunci, da cewa shin, gamsassu ne ko kuwa, sannan kuma ya kamata a fuskantar da wannan nakadin ga Manzo (s.a.w) domin shi ne ya ce: Imamai (shuwagabanni) daga cikin kuraishawa suke, kamar yadda mafi yawan musulmai suka tafi a kan hakan, misalin irin wannan maganganun zasu nuna maka yadda kwakwalen wadannan marubutan suke, wadanda suke yin rubuta game da Shi'a kuma masdarin su shi ne, yasasshen zancen wanda ake jinginawa zuwa wani mutum tun kafin shekara dubu daya, alhali a hannun su akwai masdarorin Shi'a sun ki su koma zuwa gare su, yaya zaka kira wannan?
Bayan dan wannan tsokacin, bari mu koma zuwa hakikanin yadda akida take a wajen Shi'a domin ba ta saba da wani abu daga yadda akidun sauran bangarorin suke ba, sai dai idan muka togace lamarin Imamanci da abin da yake kunshe da ita, na daga siffofiin Imami. Amma sauran mahalli sabanin da ke tsakanin Shi'a da sauran musulmai, abin da ke tsakanin mazhabobi hudu su kan kan su na sabani ya ninninka wanda ke tsakanin Shi'a da Sunna, balle Malaman mazhaba daya da malaman fakihan ta sabanin da ke tsakanin su ya fi wanda yake tsakanin Shi'a da Sunna, ba tare da wani kari ba, kuma ta yiwu abin da zai karfafa wannann da'awar zai zo mana a tsakankanin bahasi na gaba in-sha'Allah.
?
Akidojinsu da Hannunsu ya Rubuta
A nan zan ambaci wasu yanjimloli takaitattu dangane da abin da malaman Shi'a suka fadi su akan kan su game da ra'ayoyin su na addini da kuma akidojin su, domin su zama `yar manuniya ga wanda yake son fadadawa da bincikar gaskiya, yana mai nisantar son rai da son zuciya.
1- Ibn Babawaihil Kummi:
Littafinsa "Akidojin Shi'a" yan daga cikin litattafan da suke na gaba-gaba a wannan fagen, ya tattro dukkanin akidun Shi'a, ba tare da wani kokwanto ba, don haka ne ma littafinsa ya zama yana daga cikin masdrorin da ake komawa zuwa gare su, kari a kan cewa shi wannan bawan Allah yana daga cikin tsauninnikan wannan mazhaba kuma daga cikin shuwagabannin wannan jama'ar. Kuma wannan dan tsokaci ne dangane da abin da ya rubuta a kan akidar imamiyya a kan lamarin Ubangijintaka, ya ce:
Akidarmu a kan tauhidi: Allah Madaukaki shi kadai yake, wani abu bai yi kama da shi ba, mara farko ne bai gushe ba kuma ba zai taba gushewa ba, mai ji ne, mai gane ne, mai hikima ne, rayayye ne, wanda ya tsaya da kansa, mabuwayi, tsarkakkake masaniya, mai iko. Ba a siffanta shi da jauhari ko jiki ko sura ko wani abu, kuma ya fita daga haddodi guda biyu haddin (ibdali) rashin samuwa, da kuma haddin kamanceceniya.
Akidarmu a kan Kur'ani shi ne: Shi zancen Allah ne kuma wahayinsa ne kuma abin saukarwarsa ne kuma littafinsa ne kuma lalle barna ba ta zo masa ta gabansa da ta bayansa, kuma shi ne wanda yake tsakanin bangwaye guda biyu, kuma shi ne wanda ya ke hannun mutane, babu wani abu sama da haka ,kuma wanda ya jingina mana cewa munafadinsama da haka to shi makaryaci ne-, wannan shi ne abin da Ibn Babawaihil kummi ya rubuta, wanda ya rayu ne a tsakiyar karni na hudu kuma ya yi wafati a shekara ta 381AH.
2- Shehul Mufid Muhammad bin Nu'uman, a "Awa'ilul Makalat":
Yan cewa: Allah mai girma da buwaya, shi kadai ne a cikin Allantaka da rashin farko wani abu ba ya kama da shi kuma bai halatta wani abu ya yi kama da shi ba, kuma shi kadai ne ake yi wa bauta, ba shi da na biyu a cikin ta takowane bangare, da kuma sababi, kuma a kan wannan ne ma'abota tauhidi suka hadu in banda wadanda suka fita taron daga cikin ma'abota kamantawa, (tashbih) kuma lalle Allah Madaukaki rayayye ne a kan kansa ba tare da rayuwa ba, kama shi masani ne da kan sa, ba kamar yadda masa kamanta shi suka tafi a kai ba, kuma mai iko ne a kan kan sa, kuma ni mai tabbatar da cewa lalle Kur'ani zancen Allah ne kuma wahayin sa ne, kuma shi fararre ne kamar yadda Allah Madaukaki ya fadi, kuma ban yarda da cewa gabadayan sa fararre ba, kuma Allah yasan duk abin da zai kasance kafinn kasancewar sa, kuma babu wani abu da zai faru face sai ya san shi kafin faruwar sa, kuma babu wani abu sananne, kasantacce, wanda zai kasance face sai ya zoma masani absa hakikanin sa. Kuma wani abu baya boyuwa a gare shi a sama ko a kasa, wannan ne abin da dalilai na hankali da rubutacce littafi suka tabbatar.
Sannan Shehul Mufid ya yi magana kuma ya yi nuni zuwa fadin wanda yake da'awar cewa lalle an shafe wani abu daga cikin Kur'ani, farkon wannan maganar ita ce cewa lalle abin da aka shafe shi ne sharhohi da fassarori, kuma babu wani abu shafaffe daga cikin Kur'ani, kuma ya fadi cewa yana daga cikin wadanda suka tafi a kan wannan ra'ayin, sannan sai ya ce:
Wasu jama'u daga Imamiyya sun ce; Ba a shafe aya ko kalma ko sura, sai dai an shafe abin da yake tabbatacce a cikin littafin Ali na daga ta'awilinsa, da kuma fassarar ma'anoninsa, wanda aka saukar da shi a kan su, kuma wannan tabbataccen abu ne, koda kuwa bai zama daga cikin littafin Allah madaukaki ba domin a kan kira ta'awilin Kur'ani da Kur'ani, kuma Allah Madaukaki ya ce: "Kada ka gaggautawa (yin bayanin) Kur'anitun kafin a yi bayanin wahayinsa a gare ka" .
Kuma a wajena wannan fadin ya fi kama da fadin wanda ya yi da'awar tawayar wasu kalmomi daga cikin Kur'ani.
3- Assayyid Muhsin Al'aminu Al'amili
Akidar Shi'a lalle wanda ya yi shakka a kan samuwar mafarin komai ko muka kadaitakar sa ko annabtar Annabi (s.a.w) ko ya sanya masa abokin tarayya a cikin annabci, wannan ya fita daga addinin musulunci, kuma duk wanda ya yi guluwwi a cikin wani daga cikin Ahlul-baiti ko ma wanin su ko ya fitar da shi daga matsayin mai bauta ga Allah, kuma ya tabbatar masa da annabci ko yin tarayya a cikin sa, ko kuma wani abu da ga siffar ubangiji, to wannan ya fita daga igiyar musulunci, kuma Shi'a sun barranta daga dukkani gullat da mufawwidha da makamancin su, karshen maganar ke nan a takaice.
4- Muhammad Ridha Al'muzaffar
Kuna kudurce cewa lalle Allah daya ne, mara farko ne bai gushe ba kuma ba zai taba gushewa ba, shi ne farko shi ne karshe, masani ne mai adalci mai iko rayayye mawadaci mai ji mai gani, ba a siffanta shi da abin da ake siffanta ababan halitta, kuma muna kudurce cewa ya wajaba a kadaita shi ta kowace jiha, da cewa shi daya ne a cikin hakan kuma siffofinsa su ne ainihin zatinsa, haka ma ya wajaba a kadaita shi a cikin ibada, kuma muna kudurce cewa lalle annabta aiki ne na Allah kuma wakilci ne daga ubangiji, da Allah yakan sanya shi ga wanda ya zaba daga cikin bayin sa na gargaru sai ya aiko su zuwa saurn mutane domin ya shiryar da su, kuma muna kudurce cewa lalle imamanci, tushe ne daga cikin tushen addini wanda imani baya cika sai da akidantuwa da ita, kuma wajibi ne a yi duba (tunani) a cikin ta kamar yadda ya wajaba a yi duba a cikin tauhida da annabta, kuma ita kamar annabta ce, ludufi ne na Allah, kuma muna kudurce cewa lalle Kur'ani wahayi ne na Allah, abin saukarwa daga Allah Madaukaki a harshen annabinsa, kuma canjawa da gayyarawa da jirkitawa ba sa zo masa, kuma duk wanda ya yi da'awar wanin haka a bisa wannan, to lalle shi makaryaci ne, ko mai kawo rudani kuma dukkanin su ba a kan shiriya suke ba, lalle shi zancen Allah Madaukaki ne wanda barna bata zomasa ta gabansa ko ta bayan sa.
Wadannan `yan misassalin guda hudu na gabato da su ne saboda su zama matashiya ga wanda yake so ya fadada a wajen sanin akidoji Shi'a kuma domin ya koma zuwa littatfan su, kuma ya ishe ka sheda a kan wannan kasantuwar litattafan wadanda suke tun farko-farkon tarihin Shi'a sun zo da bayanin dalla-dalla, kuma mutum biyu daga cikin wadanda aka ambata wato Suduk da Mufid sun rayu a karni na hudu, amma na sauran biyun sun rayu a karni na goma sha hudu, yana daga cikin abin ban dariya mu tsaya muna tabbatar da cewa mu musulmai ne, sai dai sau da yawa larura ta kan tilasta mutum yin abubuwan dariya, me zamu yi alhali ba mu gushe ba a matsayin wadanda ake saitawa domin a jefa, kuma mafi saukin abin da ake jifan mu da shi ne abin da zai fitar da mu daga musulunci ya kai ga kafirtar mu, kuma dalilin da ya sa na dan bijiro da wadannan misalsali a farkon magana shi ne, domin su zama tunatar wa ga mai karatu mai gairma a yayain da yake biye da ni a wajen kokarina na in ga na nusar da shi zuwa abin da ake jingina wa Shi'a na ban mamaki, makaratun da nake nufi a nan na musamman shi ne makarantu basunne, domin surar da ke cikin kwakwalwar sa game da Shi'a abu ne mai wuya in cire masa ita da sauki, sai dai buri na a nan da temakon Allah da kuma kyakykyawar manufa ta ta tsarkake wannan mazhabar daga rudu shi ne in bude wata kofa ta aza harsashin da zai kai ga kadaitakar musulmai.
Cibiyar Haidar don Yada Musulunci
www.hikima.org
hfazah@yahoo.com
Hafiz Muhammad Sa'id
Monday, December 10, 2012