Muassasar alhasanain (a.s)

Tarbiyyar Yara3

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5


Tarbiyyar Yara A Musulunci3
      
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com

Godiya ta tabbata ga Allah (s.w.t) Kuma Aminci ya k'ara tabbata ga bayinsa wad'anda ya zab'a
Ka bar shi tare da mu a gobe, ya ji dad'i, kuma ya yi wasa. Kuma lalle mu masu tsaro ne gareshi .
Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Yaro a shekara bakwai na farko shugaba ne kuma sarki, a shekara bakwai kuma bawa ne ribataccen yak'i, a shekara bakwai kuma d'an'uwa ne kuma waziri" .
Gabatarwar Mawallafi
Ina godiya ga Allah da ya ba ni damar rubuta wannan littafi "Tarbiyyar Yara a Musulunci" domin bayanin yadda ya kamata a tarbiyyantar da yaro, an rubuta wannan littafi ne saboda bukatar da take cikin al'ummarmu ta ganin an kiyaye hakkin yara da tarbiyyantar da su tarbiyya ta gari domin shi ne sirrin ci gaban kowace al'umma da habakarta a fagage daban-daban, kuma hanya mafi dacewa wajan ilmantarwa. Domin idan yara suka gyaru suka ta so da Azama, da Kishi, da Ilimi, da Tunani mai kyau, wannan yana nufin al'umma zata ci gaba, kuma zata kai ga cimma burinta da gaggawa ba tare da wani tsoro ko fargaba ba.
Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Yaro a shekara bakwai na farko shugaba ne kuma sarki, a shekara bakwai kuma bawa ne ribataccen yaki, a shekara bakwai kuma dan'uwa ne kuma waziri" . Wannan Hadisi yana nuna mana shekara ishirin da daya da zaka yi tare da yaro, da irin mu'amalar da zaka yi da shi a kowacce daga shekaru bakwai. Kuma zamu yi kokarin ganin mun gina wannan littafin bisa wannan asasin mai marhaloli uku masu muhimmanci a shekarun yaro.
Wannan tsarin da na bi wurin rubuta wannan littafin shi ne na farko da ban samu wani ya yi irinsa ba. Domin tsari ne na bayanin rayuwar yaro bisa dogaro da wannan hadisi madaukaki, da marhalolin rayuwarsa mai gida uku, da suka kasa shekaru ishirin da daya har kashi uku.
Magana kan yara wani abu ne da babu abin da ya kai shi muhimmanci a tarihin rayuwar dan Adam Saboda su ne manya a gobe, kuma idan ba a tarbiyyatar da su yadda ya kamata ba to wannan yana nufin rushewar al'adun al'umma na gari, da shafe kufan abin da ta gada kaka da kakanni. Shi ya sa ma a tarihin juyin juya halin al'ummu zamu ga yana faruwa ta hannun Yara da Samari ne, idan mun duba tarihin Annabawa (a.s) da Manzon Rahama (s.a.w) da ma juyin da ya faru a bayansu, zamu ga ya faru ne ta hannun samari.
Don haka ne mushirikan Makka suka koka da cewa Manzo ya bata tunanin samarinsu saboda samari ne su suke karbar canji, don haka muka ga mabiyansa samari ne. Amma tsohon jini da ya kafu a bisa wata Akida da ta kafu a tunaninsa da ra'ayinsa, yana da wahala ya canja da sauri ko ya samu sauyi, don haka ne ma Musulunci ya bayar da muhimmaci a kan shekarun samartaka. Masana tarbiyya suna ganin cewa yana da wahala ga mutum ya canja da wuri bayan ya yi shekaru arba'in kan wani ra'ayi. Misali idan mutum ya kai shekara arba'in ba ya sallar dare to yana da wahala ya iya jurewa ya dage a kai, Shi ya sa idan saurayi ya dore a kan hanya ta gari to yana da wahala ya canja.
Amma ba mu kore cewa mutum yana iya samun canji kan abin da ya rayu ba, misali mutum yana iya rayuwa kan wani abu na gari wanda yake nuni da cewa; shi na gari ne a zahirinsa, amma idan ya zama yana da dauda a zuciya kamar hassada, ko mugun kulli kan bayin Allah, to duk wannan yana iya tasiri wajan lalacewarsa koda yana ayyuka ta bangaren ibada, a nan ba mamaki ba ne karshensa ya ki kyau. Bil'am dan Ba'ur malami ne, amma saboda ya yi wa Annabi Musa (a.s) hassada sai ya lalace, haka ma Iblis yana daga mala'iku masu ilimi na koli, amma sai ya yi hassada, shi ke nan sai ya kaskanta, darajarsa ta yi kasa.
Don haka ne ya zo a wata ruwaya cewa: "Kada ku duba yawan sallarsu, da azuminsu, da yawan hajji, da kyawawa, da kuma sautinsu da dare, ku duba gaskiyar magana da rikon amana" . Wato; kada a duba yawan salla, da ruku'u, ko sujadar mutum, ta yiwu wata al'ada ce da ya saba da ita, idan ya bari sai ya ji babu dadi, amma a duba ayyukansa da mu'amalarsa, irin wadannan mutane suna sallar jam'i ko ta dare, da azumin nafila, amma ba sa tasiri a ayyukansu sakamakon lalacewar zukatansu.
Don haka idan yaro ya saba da wani abu haka zai taso da shi a matsayin saurayi, idan da ya saba da karatu sai ya zama saurayi to ba zai iya bari ba kuma haka zai manyanta ya tsufa matukar wani yanayi na tilas da lalura bai fado ba. Amma yaron da ya taso yana bin bata gari, yaya zai taso? Don haka ne tarbiyyar yara, da samari, da ilmantar da su domin a samu al'umma ta gari take bukatar hukuma, da iyaye, da 'yanuwa, da makwabta, da malamai, su sanya hannu.
Mu sani cewa babban mutum da muke iya gani ko tsoho to fa ya wuce marhalar yarinta kafin ya kai ga wannan marhalar, don haka tsohon kirki shi ne yaron kirki a da, da wannan tarbiyyar yaron ne ya zama tsohon kirki ya iya tasowa har ya zama mai amfani ga al'ummarsa a ko da yaushe. Da wannan lamarin ne zamu fahimci cewa akwai bukatar gyaruwar marhala ta farko domin samun gyaruwar marhala ta gaba mai biye mata.
Sannan ka da mu mance cewa akwai abubuwa masu yawa da suke tasiri a tarbiyyar yara da suka shafi nau'in halitta, tsawo, ko yanayin wuri kamar zafi, sanyi. Haka nan al'adun wuri suna tasiri wurin tarbiyyar yara kamar siyasa, arziki da talauci, karatu, nau'in tsarin rayuwar al'umma, iyali da dangi, a gida. Hatta da abinci wani lokaci yana tasiri a rayuwar mutum kamar masu cin cin macizai, jakuna, abinsha gurbatacce, ko yanayin abin da uwa take ci yayin da take da ciki, ko abin da take kallo ko take tunaninsa. Kuma nau'in tasowa tana da nata tasiri kamar marasa gida, rayuwar titi, maraici, makaranta, malamai, tunani, abokai, da sauransu. Don haka ne akan iya samun yara sun fito ciki daya amma sai a samu kowanne yana da hali sabanin yadda dan'uwansa yake.
Akan samu bambanci tsakanin 'ya'ya a halaye da tunani koda kuwa sun samu kalar tarbiyya da komai iri daya.
Mayar da yaro mutum cikakke shi ne babban jihadin da mutum zai iya yi don kawo cikakken ci gaba a al'ummarsa. Ana cewa: Mutum shi ne mai rayuwa mai hankali. Don haka domin wannan bayani game da mutum ya samu dole ne iyaye su zage damtse don wannan muhimmin aiki.
Tun da ya kasance hadafinmu shi ne gina gida na gari da al'umma saliha wacce zata zama ta daukaka Addinin musulunci da kyawawan dabi'u a cikin al'umma, shi ya sa a wannan karon muka ga ya dace mu bayar da himma wurin bincike game da yadda ya kamata a reni manyan gobe, da fatan Allah ya sa wannan aiki ya zama karbabbe a wurinsa ya kuma karfafi Addinin musulunci da shi. Ina rokon Allah ya bayar da ladan rubuta wannan littafi ga Dan'uwana Ahmad Muhammad kuma ya haskaka kabarinsa da shi.
Hafiz Muhammad Sa'id / hfazah@yahoo.com / www.hikima.org / www.haidarcip.org / Facebook: Haidar Center
Haidar Center for Islamic Propagation
Shahribar1382 H.Sh -
Satumba 2003 M
Rajab 1424 H.K
    

 

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)