Wasiyyar Luqman (a.s)
Wasiyyar Lukman (a.s) ga Dansa
HAFIZ MUHAMMAD SA'ID hfazah@yahoo.com
Nasihohin Lukman Hakim (a.s) ga Dansa
Zamu so kawo karashen wannan magana game da tarbiyyar yara da nasihohin Lukman (a.s) ga dansa wadanda suka tattaro dukkan hikimomi masu yawa da amfani a dukkan janibobin rayuwar mutum ta duniya da lahira.
Ubangiji madaukaki yana cewa: "Hakika mun ba wa Lukman hikima ka godewa Allah wanda ya gode yana godewa ne ga kansa kuma wanda ya butulce hakika Allah mawadaci ne abin yabo. Yayin da Lukman ya ce da dansa yana mai yi masa wa'azi Ya dana! Kada ka yi shirka da Allah (an ce dansa ya kasance mushriki, bai gushe ba yana yi masa wa'azi har sai da ya musulunta) hakika shirka zalunci ne mai girma ".
Wannan munin nata kuwa saboda ita shirka daidaita mafificin samammu ne da mafi kaskancinsu ce, da kuma daidaita mai ni'imtarwa mawadaci tsantsa da kuma mai ni'imtuwa (wanda ake ni'imtarwa) matalauci tsantsa. Don haka ne sai Lukman (a.s) ya fara gabatar da wa'azi game da hanin shirka domin tauhidi shi ne asalin wa'azi, kuma shirka zalunci ne wanda Allah ba ya yafe shi idan an mutu ba a tuba ba sabanin sauran zunubai. "Ya dana, ka sani cewa" wato; Dabi'a mummuna ko kyakkyawa "idan tana kwatankwacin kwayar Khardal" wato nauyin aikin, shi Khardal wani tsiro ne na ciyayi da yake fitowa a gonaki da kuma gefen hanya, kwayarsa karama ce sosai kuma launinsa baki ne kuma ana buga misali da shi a kankanta ana cewa ba ni da koda kwayar khardal, kuma ana amfani da ita a magani da kuma kansasa abinci, "To zata kasance a sahara ne ko samammai ko kasa" wato wannan dabi'ar koda tana mafi boyuwar waje kuma mafi taskatuwar wuri kamar cikin duwatsu wacce tafi kowane dutse tsauri ko mafi nisan waje to "Allah zai zo da ita" ya yi hisabinta, "hakika Allah mai tausayi ne" a iliminsa da abin da ya boyu "kuma masani" da dukkan komai.
"Ya dana, ka tsayar da salla" wato domin kamalar kanka "ka yi umarni da kyakkyawa ka yi hani da barin mummuna" wannan kuma domin kamalar waninka "ka yi hakuri domin abin da ya same ka" na bala'ai da wahala da cutarwa a kan hanyar umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna "hakika wannan" hakurin "yana daga manyan al'amura" wanda ya kamata a dage a kansu. "kada ka karkatar da kanka ga mutane" ai ka karkatar da kanka kana barin mutane don wulakaci, an ce; Yana nufin kada ka karkato zuwa garesu don kwadayin abin hannunsu . Daga Imam Ja'afar Sadik (a.s) ayar tana nufin: Mutane su kasance daya ne a wajenka a sani .
"Kada ka yi tafiya a bayan kasa kana mai jiji da kai, hakika Allah ba ya son mai takama mai alfahari". Daga Annabi (s.a.w) yace: Wanda ya yi tafiya a kan kasa yana mai takama kasa zata la'ance shi da abin da yake karkashinta da abin da yake kanta . "Ka tsakaita a tafiyarka" wato tsakanin takama da kuma kaskantar da kai, wato ba labo-labo ba, ba kuma gudu-gudu ba. Shi ya sa ya zo a cikin hadisi cewa saurin tafiya yana tafiyar da kwarjinin mumini . "Kuma ka kaskantar da sautinka, hakika mafi munin sauti shi ne muryar jaki". Wato kada sautinka ya yi kasa kuma kada ya yi sama domin mafi munin sauti sautin jaki, wannan kuma misali na shesshekarsa da daga sauti sama wannan kuma misali ne mai kyau da ake nufin irin jinsin abu ba wai daidaikunsa ba.
Daga Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: Ita (mafi munin murya) atisshawa da murya mai muni, da mutumin da yake daga sautinsa da magana dagawa mai muni sai dai idan ya kasance mai kira ne ko yana karanta Kur'ani .
Ko kuma a gaban makiya saboda fadinsa madaukaki: "Masu tsanani ne a kan kafirai". kamar yadda ya kamata ko ma mustahabbi ne ladani ya kasance mai murya madaukakiya domin a samu isar da sakon sanarwa, a kan wannan kuwa hadisan Ahlul Baiti (a.s) sun zo game da hakan .
Ya kamata dalibi ya kasance mai sassauta muryarsa kasa-kasa daga muryar malaminsa da babansa da ladabi kuma ba kyau daga murya a kan muryarsu.
Lukman ya kasance ya ce da dansa: Ya dana! Yaya mutane ba sa tsroron abin da aka yi musu alkawari, kuma alhalin kullum suna rage rayuwarsu, yaya wanda yake da ajali ba ya tanadi saboda abin da ake yi masa alkawari, Ya dana!; Ka riki duniya guzuri kada ka shiga cikinta shiga da zai cutar da lahirarka, kuma kada ka ki ta sai ka kasance naunyi a kan mutane. Ka yi azumi da zai yanke sha'awarka, kada ka yi azumin da zai hana ka yin salla, ka sani salla ta fi azumi a wajen Allah.
Ya dana! Kada ka nemi ilimi domin ka yi wa malamai yanga da shi, ko jayyayya da wawaye, kada ka bar ilimi domin kin sa da son jahilci. Ya dana! Ka zabi mazauni, idan ka ga mutane suna ambaton Allah ka zauna tare da su, domin idan ka kasance malami ne sai ya amfane ka kuma su dada maka ilimi, idan kuwa ka kasance jahili sai su sanar da kai, ta yiwu Allah ya mamaye su da rahama sai ta mamaye ka tare da su.
Ya dana! Idan kana kokwanton mutuwa sai ka dauke wa kanka yin bacci, amma ba zaka iya ba. Idan kuwa kana kokwanton tashin kiyama to ka dauke wa kanka farkawa, wannan kuwa shi ma ba zaka iya shi ba, ka sani idan ka yi tunani zaka san cewa ranka ba a hannunka take ba, bacci kamar mutuwa ne kuma farkawa bayan bacci kamar tashi ne da ba mutuwa.
Ya dana! Dukkan dabba tana son irinta, amma dan Adam ba ya son irinsa, kada ka yada alherinka sai wajen mai sonsa, kamar yadda babu abota tsakanin rago da kyarkeci, haka nan babu abota tsakanin na gari da fajiri, wanda kuwa ya kusanci alfahasha to sashenta zai rataya a jikinsa, haka nan wanda ya yi abota da fajiri to zai damfaru da shi, wanda yake son jayayya za a zage shi, wanda ya shiga wuri mummuna za a tuhumce shi, wanda yake da aboki batacce ba zai kubuta ba, wanda bai mallaki harshensa ba zai yi nadama.
Ya dana! Yi abota da dari kada ka yi gaba da daya.
Ya dana! Ni tun da na fado duniya sai na juya mata baya na fuskanci lahira, domin gidan da zaka tafi ya fi kusa fiye da gidan da kake nisa da shi.
Ya dana! Tsentseni daga haramun ya kasance shi ne zaka yi wa makiyinka galaba da shi, fifikon addininka da kuma kare mutumcinka da girmama kanka kada ka daudantar da ita da sabon mai rahama da munanan dabi'u da ayyuka da boye sirrinka da badininka, idan ka yi haka to ka aminta da suturtawar Allah domin kada wani makiyi ya sami wata damar yada sirrinka ko kuma ya samu wani abin suka gareka, kuma kada ka aminta da makircinsa sai ya samu dama a kanka a wani halin, idan ya samu dama a kanka sai ya hau kanka, kuma ba zai rufa maka wani asiri ba. Ka karanta abu mai yawa idan wajen neman amfani ne, kuma ka gimama dan karamin abu idan a wajen cutuwa ne.
Ya dana! Kada ka zauna da mutane ba abisa tafarkinsu ba, kada kuma ka dora musu abin da ya fi su karfi, sai abokin azamanka ya rika kin ka kuma wanda ka dora masa sama da karfinsa sai ya nisance ka.
Sai ka koma kai kadai ba ka da abokin zama da zai taimake ka, idan kuma ka rage kai kadai sai ka zama kaskantacce, kuma ka kasa bayar da uzuri ga wanda ba ka son ya karbi uzurinka, kuma ba ya ganin hakkinka, kuma sai a lokacin ka zamanto ka nemi taimako a al'amuranka ga wanda yeke neman wani abu na lada ne wajenka, wanda shi biyan bukatarka a wajensa kamar biyan bukatarsa ne. Domin bayan cin nasararka ga bukatunka to (gareshi shi ma) sai ya zama riba a duniya mai karewa kuma ajiya a lahria mai wanzuwa sai ya yi kokarin biyanta gareka.
'Yan'uwanka da kake neman taimakonsu a kan al'amuranka su kasance ma'abota mutumci da kamewa da arziki, da hankali da kamewa wadanda idan ka amfane su sai su gode maka, idan ba ka nan sai su ambace ka da alheri.
Lukman ya ce da dansa: Idan ka ladabtu kana karami to zaka amfana kana babba, wanda ya damu da ladabi zai himmantu, wanda kuwa ya himmantu da shi zai yi kokarin saninsa, wanda ya yi kokarin neman iliminsa to zai yi kokarinsa, wanda kuwa ya yi kokarin nemansa zai riski amfaninsa sai ya rike shi al'adarsa. Kuma kada ka yi kasalar nemansa ka shagaltu wajen neman waninsa.
Idan neman ilimi ya kubuce maka, to ba zaka taba samun tozarta ba da take mafi muni daga barinsa.
Ya dana! Ka zauna da dangi da abokai ma'abota ilimi idan sun cika maka alkawari, ka yi hattara da su juya maka baya, domin gabarsu ta fi gabar na nesa muni, saboda mutane zasu yarda da su kanka saboda sun san me kake ciki.
Ka zama mai hankali mai kame baki, kada ka zama jahili mai yawan magana, ka sani cewa kowane abu yana da alama, alamar hankali kuwa ita ce tsawaita tunani da lizimtar shiru.
Ya dana! Idan ka yi tafiya tare da mutane ka yawaita neman shawararsu cikin al'amuranka, da yawaita murmushi a fuskarsu, ka kasance mai kyauta garesu, idan suka kira ka sai ka amsa musu, idan suka nemi taimakonka ka taimaka musu. Ka yi galaba a kansu da abu uku: Tsawaita shiru, da yawaita salla, da yawan kyauta ko bayar da aron dabbarka da dukiyarka da guzurinka.
Idan suka nemi shaidarka kan gaskiya ka yi musu sheda, ka yi kokari a ra'ayinka garesu idan suka nemi shawararka, sannan kada ka yi niyya har sai ka tabbatar ka duba, kada ka amsa musu wata shawara har sai ka tashi ka zauna ka yi bacci ka ci abinci ka yi salla kana amfani da kwakwalawarka da tunaninka da hikimarka game da shawararsu, domin wanda bai bayar da nasiha ba ga wanda ya ba shi shawara sai Allah ya cire masa ra'ayinsa ya kuma fitar masa da aminci.
Idan ka ga wani daga sahabbanka yana tafiya to ka tafi tare da su, idan ka gan su suna aiki to ka yi aiki tare da su, idan suka bayar da sadaka suka kuma bayar da rance kai ma ka bayar, ka ji maganar wanda ya fi ka shekaru, kuma idan suka umarce ka da wai al'amari suka tambaye ka sai ka bi su, ka ce: Na'am, kada ka ce: A'a, domin fadin hakan aibi ne.
Idan kuka samu dimuwa a hanya sai ku sauka, idan kuka yi kokwanto sai ku tsaya, ku nemi shawara, idan kuka ga wani mutum daya kada ku tambaye shi, kuma kada ku nemi ya nuna muku hanya, domin mutum daya a jeji abin kokwanto ne, ta yiwu ya nuna muku hanyar barayi da 'yan fashi, ko kuma ya kasance shi ne shaidanin da ya dimautar da ku, ku kiyayi mutane biyu, sai dai idan kun ga abin da ni ban gani ba, ku sani mai hankali yana ganin abu da idonsa sai ya gane gaskiyarsa, kuma mai gani yana iya ganin abin da wanda ba ya nan ba ya gani.
Ya dana! Idan lokacin salla ya zo to kada ku jinkirta ta don wani abu, ku yi salla ku huta daga gareta, domin ita bashi ce, ka yi salla a jam'i koda kuwa a kan mashi zaka yi ta, kada ka yi bacci a kan dabbarka, domin wannan yana saurin halaka ta, kuma wannan ba aikin masu hikima ba ne, sai dai idan kana wani yanayi da kake son mike jikinka don mika.
Idan ka yi kusa da gida sai ka sauka daga kan dabbarka to zata taimaka maka, kuma ka fara ciyar da ita kafin kai ka ci, idan kana son sauka to ka sami wajen da ya fi kowanne kyau wanda ya fi taushi da ciyayi, kuma idan ka sauka sai ka yi salla raka'a biyu kafin ka zauna, idan kana son biyan bukatunka sai ka nisaci hanyar mutane, idan zaka tafi ka yi salla raka'a biyu sannan sai ka yi bankwana da kasa idan zaka tafi, ka yi sallama ga ma'abotanta da kuma mutanneta, domin ka sani kowane waje yana da mala'iku, idan zaka iya to ka yi sadaka da aibinci kafin ka ci.
Ka karanta littafin Allah matukar kana haye, kuma ka yi tasbihi matukar kana aiki, ka yi addu'a matukar kai kadai ne, na hana ka tafiya a farkon dare, kuma ka rika sauka don hutawa, ka tafi da dare daga rabinsa zuwa karshensa, na hana ka daga murya a tafiyarka.
Ya dana! Ka tafi da takobinka da huffinka da rawaninka da abayarka da kuma abin shan ruwanka, da allurarrka da zarenka da jakarka, ka yi guzuri tare da magani da zaka yi amfani da shi kai da wadanda suke tare da kai, kuma ka kasance mai tausayawa ga abokanka sai dai idan sabon Allah ne.
Ya dana! Ka sani za a tambaye ka gobe kiyama idan ka tsaya a gaban Allah (s.w.t) game da abubuwa hudu: Game da samartakarka yadda ka yi ta, da rayuwarka yadda ta kare, da dukiyarka yaya ka same ta, kuma yaya ka kashe ta, don haka ka shirya wa bayar da wadannan amsoshi, kuma kada ka yi bakin cikin wani abu na duniya da ya wuce ka, domin kadan din duniya ba ya dawwama, yawanta kuma ba ya kariya daga bala'i, ka yi hattara, ka yi kokari cikin lamarinka ka yaye fuskarka, kuma ka fuskanci alherin Ubangijinka, ka yi tuba, ka yi amfani da damarka kafin tafiyarka, a biya maka bukatarka, kuma a shiga tsakaninka da abin da kake ki.
Ya dana! Ka sani ni na yi hidima ga annabawa dari hudu kuma na karbi magana hudu daga zantuntukansu ita ce; Idan kana salla ka kare zuciyarka, idan kana kan tebur din abinci ka kiyaye makogaronka, idan kana gidan wani ka kare idanuwanka, idan ka kasance tsakanin halitta ka kiyaye harshenka.
Ya dana! Ka sanya kurakuranka gabanka har sai ka mutu, amma kyawawanka kada ka kula da su domin mai kiyayewa ba ya mantawa.
Ya dana! Kowane abu yana da alamomi da ake gane shi da ita, kuma addini yana da alamomi uku ne; Ilimi da imani da aiki da shi, kuma imani yana da alamomi uku: Imani da Allah da littafinsa da manzanninsa. Kuma malami yana da alamomi uku ne: Ilimin sanin Allah da abin da yake so da kuma abin da yake ki. Mai aiki yana da alamomi uku ne: Salla da azumi da zakka. Haka nan mai kallafawa yana da alamomi uku: Yana jayayya da wanda yake samansa, yana fadin abin da bai sani ba, yana bin abin da ba ya iya samu. Mai zalunci yana da alamomi uku ne: Yana zaluntar na samansa da sabo, na kasansa kuma da galaba, yana kuma taimakon azzalumai. Munafuki yana da alamomi uku ne: Harshensa yana saba wa zuciyarsa, zuciyarsa kuma tana saba wa aikinsa, zahirinsa kuwa ya saba wa badininsa, kuma mai sabo yana da alamomi uku ne, yana ha'inci, yana karya, kuma yana saba wa abin da yake fada. Mai riya yana da alamomi uku ne: Yana kasala idan shi kadai ne, yana nishadi idan ya kasance a gun mutane, yana kuma yin abu don yabo. Mai hassada yana da alamomi uku ne: Yana giba idan ba ya nan, yana dadin baki idan ya zo, kuma yana yin dariyar (farin cikin) musifa da ta samu wani. Mai barna yana da alamomi uku ne: Yana sayen abin da ba nasa ba, yana daura abin da ba shi da shi, yana cin abin da ba shi da shi. Mai kasala yana da alamomi uku ne: Yana jinkiri har sai ya wuce gona da iri, yana kuma wuce gona da iri har sai ya tozarta, yana tozartawa har sai ya yi sabo. Mai gafala yana da alamomi uku: Rafkanwa, wasanni, mantuwa.
Ya dana! Na hana ka raki da mummunar dabi'a da karancin hakuri, ka sani mai wannan halaye ba shi da aboki, ka kyautata halinka tare da kowa.
Ya dana! Idan ka rasa abin da zaka sadar da zumuncinka kuma ka yi kyauta da shi ga 'yan'uwanka to kada ka rasa kyawawan halaye da kuma sakin fuska, ka sani wanda ya kyautata halayensa to zababbun (mutanen kirki) zasu so shi, kuma munana zasu yi nesa da shi, idan ka wadatu da abin da Allah ya ba ka, rayuwarka ta yi daidai, idan kana son hada izzar duniya to ka yanke kwadayinka daga abin da yake hannayen mutane, annabawa sun kai wannan matsayin nasu ne da yanke wa daga abin da yake hannayen mutane.
Ya dana! Duniya kadan ce kuma rayuwarka gajeriya ce.
Ya dana! Ka guji hassada kada ta kasance aikinka, ka nisanci mummunar dabi'a kada ta kasance halinka, ka sani ba wanda zai cutu da su sai kai, idan kuwa ka cutar da kanka ka isar wa makiyinka al'amarinka, domin gabarka ga kanka ta fi cutarwa a kan gabar waninka gareka.
Ya dana! Shugaban hikimar kyawawan halaye shi ne addinin Allah, misalin addini kamar shuka ce tabbatacciya, imani da Allah shi ne ruwanta, salla kuwa saiwowinta, zakka kuwa jijiyoyinta, 'yan'uwantaka a addinin Allah kuwa rassanta, kyawwan halaye ganyayyakinta, fita daga sabon Allah 'ya'yan itaciyarta, itaciya ba ta kammala sai da 'ya'ya masu dadi, haka nan addini ba ya kammala sai da fita daga haram.
Ya dana! Idan aka cika tumbi sai tunani ya yi bacci kuma hikima ta kurumta, gabobi su kasa ibada.
Ya dana! Idan barawo ya yi sata sai Allah ya hana shi arzikinsa kuma ya kasance yana da sabonsa a kansa, da ya yi hakuri da ya samu wannan kuma arzikinsa ya zo masa ta hanyarsa (ta halal).
Ya dana! Ka yi biyayya saboda Allah kada ka cakuda ta da wani abu na sabo, sannan sai ka yi wa biyayyar ado da bin ma'abota gaskiya, ka sani binsu yana tare da bin Allah.
Lukman ya ce: Ya dauki duwatsu da karafa da dukkan mai nauyi, amma ban ga wani abu da daukarsa ta fi nauyi ba fiye da mummunan makoci, kuma na dandani dacin rayuwa duka amma ban dandani wani abu wanda ya fi daci fiye da talauci ba.
Ya dana! Kada ka dauki jahili dan sako, idan ba ka samu mai hankali mai hikima dan sako ba, to ka zama dan sakon kanka.
Ya dana! wanda yakininsa ya takaita, kuma kokarinsa na neman arziki ya yi rauni ya dauki darasi, ya sani Allah ya halicce shi a cikin halaye uku ne, ya kuma ba shi arzikinsa ba tare da yana da wata dubara ko kokarin kansa, a kan cewa Allah zai arzuta shi a hali na hudu. Amma na farko ya kasance a mahaifar babarsa da yake arzuta shi a nan ba tare da wani sanyi da yake cutar da shi ko wani zafi da yake cutar da shi ba, sannan sai ya fitar da shi hakan ya gudanar da nonon babarsa gareshi ıyana sha daga gareshi ba tare da wani dubara ko karfi ba, sannan sai aka yaye shi daga wannan kuma aka sanya masa arzikinsa ta hanyar iyayensa da tausayinsa a zukatansu, har ya girma ya yi hankali kuma ya nemi arzikinsa rayuwa ta yi masa kunci, sai ya yi ta mummunan zato ga Ubangijinsa ya yi musun hakkokin dukiyarsa ya kuntata wa kansa da iyalansa saboda tsoron talauci.
Ya dana! Ka wa'aztu da mutane kafin mutane su wa'aztu da kai.
Ya dana! Ka wa'aztu da karamin bala'i kafin babba ya sauka kanka.
Ya dana! Kada ka ci bashi domin sai ka yi ha'inci saboda bashi.
Ya dana! Ka sanya duniya kurkukunka sai lahira ta kasance aljannarka.
Ya dana! Ka yi abota da miskinai ka kuma kebantu da talakawa da miskinai daga cikin musulmi.
Ya dana! Ka kasance kamar uba mai tausayi ga maraya, kuma kamar miji mai tausayi ga bazawara (da mijinta ya mutu).
Ya dana! Ka sani ba duk wanda ya ce: A gafarta mini ne aka gafarata wa ba, sai ga wanda ya yi biyyaya ga Ubangijinsa.
Ya dana! Da gidaje sun kasance a kan gaggawa da babu wani mutum da zai yi makwabtaka da wani mummunan makoci har abada.
Ya dana! wane ne ya bauta wa Allah sai ya tozarta shi, wane ne kuma ya neme shi bai same shi ba.
Ya dana! wanne ne ya ambaci Allah bai ambace shi ba, wane ne kuma ya dogara ga Allah sai ya jingina masa al'amarinsa zuwa waninsa, wane ne ya kaskanta zuwa gareshi bai tausaya masa ba.
Ya dana! Ka yi shawara da babba, kada ka ji kunyar shawartar karami.
Ya dana! Kada ka yi abota da fasikai, su kamar karnuka ne idan suka samu abin da zasu ci gunka zasu ci, idan ba haka ba sai su zarge ka su tozarta ka, ka sani soyayya a tsakaninsu ta awa daya ce kawai.
Ya dana! Gaba da mumini tafi abota da fasiki.
Ya dana! Mumini kana zaluntarsa shi kuma ba ya zaluntarka, kana nemansa sai ya yarda da kai, fasiki kuwa ba ya kiyaye wa Allah balle ya kiyaye maka.
Ya dana! Ka fara wa mutane da sallama da gaisuwa kafin magna.
Ya dana! Kada ka yi husuma a game da ilimin Allah ka sani ilmin Allah ba a riskarsa kuma ba ya karewa.
Ya dana! Kada ka yada sirrinka ga matarka ko ka sanya majalisinka kofar gidanka.
Ya dana! Mata kala hudu ne: Biyu na gari biyu kuma la'anannu ne, amma salihai na gari su ne;
Ta daya: Da mai daukaka a cikin mutanenta, mai kankantar da kanta, wacce idan aka ba ta sai ta gode, idan aka samu jarabawa sai ta yi hakuri, kadan a hannunta mai yawa ne, ta gari a cikin gidanta.
Ta biyu kuma ita ce; Mai soyayya mai haihuwa, da take jawo wa mijinta alheri, ita kamar uwa ce mai tausayi da take tausayin babba take kuma jin kan karami tana kuma son iyayen mijinta koda kuwa su ba nata ba ne, mai kyawawan dabi'u mai yardar da miji, mai gyara kanta da 'ya'yanta da dukiyarta da 'ya'yanta, ita kamar jan zinare ce, farin ciki ya tabbata ga wanda aka arzuta shi ita, idan mijinta yana nan sai ta taimaka masa, idan kuwa ba ya nan sai ta kare mutuncinsa.
Amma ta farkon la'anannu biyun: Ita ce mai girman kai ga mutane amma ita kanta kaskantacciya ce, wacce idan aka ba ta sai ta ki godewa, idan aka hana ta sai ta yi zargi ta yi fushi, mijinta kullum cikin bala'i kuma makwabtanta kullum cikin bala'inta, ita kamar zaki ne da idan ka yi makwabtaka da shi zai cinye ka idan ka gudu kuma ya kashe ka.
Amma la'ananniya ta biyu; Ita ce wacce tana wajen mijinta amma tana son makwabtanta ne, mai saurin fushi mai sauri hawaye, idan mijinta yana nan ba ta amfanarsa, idan kuma ba ya nan sai ta ci amanarsa, ita kamar kasa ce busasshiya mai tsandauri, idan aka ba ta ruwa sai ya kwarare ya nutse kasa, idan aka bar ta hakan nan kuma sai ta yi kishirwa, idan aka ba ta da ba ta amfana da shi.
Ya dana! Kada ka zagi mutane sai ya zama kai ne ka zagi iyayenka.
Ya dana! Ka karbi wasiyyar uba mai tausayi.
Lukman ya ce da dansa: Ka kaskantar da kanka ga gaskiya ka kasance mafi hankalin mutane, ka sani mai hankali gun gaskiya 'yan kadan ne.
Ya dana! Hakika duniya kogi ne mai zurfi, da jama'a masu yawa suka nutse a cikinsa, takawarka ta kasance jirginka, lodinta kuwa imani, tampol dinta kuwa dogaro ga Allah, mai jan hta kuwa hankali, jagoranta kuwa ilimi, masu zama cikinta kuwa hakuri.
Ya dana! Kada ka sanya zuciyarka ga yardar mutane da yabonsu ko zarginsu, wannan ba ya samuwa koda kuwa mutum ya yi iyakacin kokarinsa. Sai dansa ya ce da shi me ke nan: Ina son in ga misali ga hakan ko na aiki ko na magana. Sai ya ce da shi: Zan fita da ni da kai.
Sai suka fita a tare da su akwai wata dabba, sai Lukman ya hau ya bar dansa yana tafiya a bayansa sai suka wuce wasu mutane, sai suka ce: Wannan tsoho yana da kekashewar zuciya, mai karancin tausayi ne, ya hau dabba kuma shi ya fi yaron karfi, amma ya bar yaronsa yana tafiya a kasa a bayansa tir da wannan dubara. Sai ya ce da dansa: Ka ji maganarsu da musawarsu ga hawana da kuma tafiyarka? Sai ya ce: Na'am. Sai ya ce: Kai hau kai da yaronka ni kuma in tafi kasa, sai dansa ya hau shi kuma ya taka a kasa, sai suka wuce wasu mutane, sai suka ce: Tir da wannan uban kuma tir da wannan yaron, amma babansa bai yi tarbiyyarsa ba har sai ya hau ya bar uban yana tafiya a bayansa alhalin uban shi ya fi shi cancantar girmamawa da hawan, amma dan ya saba wa babansa da wannan halin nasa, duk dai ba su da hali mai kyau.
Sai Lukman ya ce da dansa: Ka ji me suka ce? Sai ya ce: Na'am. sai ya ce: Mu hau mu biyu kan dabbar, sai suka hau, sai suka wuce mutanen sai suka ce: Kai wadannan mutane biyu ba su da tausayi kuma babu wani alheri da zasu samu wajen Allah suna hawan dabba su biyu sai sun yanke bayanta tukuna suna dora mata abin da ba zata iya ba, da ma dayansu ya hau dayan kuma ya tafi a kasa da ya fi kyau.
Sai ya ce: Ka ji? Ya ce: Na'am. sai ya ce da dan: Mu sauka mu bar ta haka nan, sai suka kora dabbar suna tafiya kasa sai kuma suka wuce wasu mutane, sai suka ce: Mamakin wadannan mutane biyu sun bar dabba ba komai ba mahayi suna tafiya kasa, mutanen suka zarge su, a kan hakan kamar yadda suka zarge su a baya.
Sai ya ce da dansa: Shin kana ganin akwai wata dubara da mutum zai iya samun yardarsu? Don haka kada ka waiga su, ka shagaltu da neman yardar Allah madaukaki a nan ne ya kamata mai shagaltuwa ya shagaltu da arzutar duniya da fuskantarta, da kuma ranar hisabi da tambaya.
Ya dana! Ka zauna da malamai ka kuma gwamatse su da gwiwarka, ka sani Allah yana raya zukata da hasken hikima kamar yadda yake raya kasa da mamakon ruwa.
Ya dana! Kada ka wulakanta wani saboda tsufan tufafinsa, ka sani Ubangijinka da Ubangijinsa daya ne.
Ya dana! Idan ka raya cewa magana daga azrufa take to shiru daga zinare yake.
Ya dana! Mutane sun tara yaransu kafinka amma babu wani abu da ya rage na daga abin da suka tara, ka sani kai bawa ne mai haya da aka umarta da aiki kuma aka yi maka alkawarin ladan, to ka cika aikinka ka nemi ladanka kada ka kasance a duniya kamar akuya ce da ta fada gona mai kore shar ta ci ta yi kiba, sai halakarta ta kasance ta hanyar kibarta, amma ka sanya duniya kamar digo ne a bakin korama da ka wuce ka bar ta ba ka kuma koma mata ba har abada, ka rusa ta kada ka raya ta, ka sani ba a umarce ka da raya ta ba.
Ya dana! (Ka zabi) aboki sannan sai hanya.
Ya dana! Kada zakara ya fi ka hankali, yana tashi da sahur yana neman gafara, kai kuma kana bacci.
Ya dana! Ka sanya wa ranakunka da dararenka da awowinka wani lokaci domin neman ilimi, ka sani ba zaka taba samun kwatankwacin abin da ka tozatar ba.
Ya dana! Koshi yana hana ka lura kuma harshen yana hana ka hikima, ya nauyaya ka ga barin ibada.
Ka halarci mazaunai kada ka halarci walimomi ka sani mazauni yana tuna maka lahira amma walima tana tuna maka duniya.
Ya dana! Ka nemin sanin hikima sai ka daukaka da ita, ka sani hikima tana nuna maka addini kuma bawa yana daukaka da ita a kan da, kuma miskini yana daukaka da ita a kan mawadaci, kuma yaro yana daukaka kan babba da ita, kuma tana kai miskini matsayin sarakuna, kuma tana dada wa mai daraja daukaka, shugaba kuma ta kara masa matsayi.
Yaya dan Adam zai yi tsammanin al'amarin addininsa da duniyarsa zai tsayu ba tare da hikima ba? Misalign hikima ba tare da biyayya ba kamar jiki ne ba tare da ruhi ba, kuma kamar misalin wuri ne ba tare da ruwa ba. Kuma babu gyara ga jiki idan babu ruhi, kuma babu rayuwa ga wuri idan babu ruwa, kuma babu hikima ba tare da biyayya ba.
Ya dana!; Dukan uba ga dansa kamar taki ne a cikin shuka, wanda kuma ya yi karya sai mutuncinsa ya zube, wanda kuma dabi'arsa ta yi muni sai bakin cikinsa ya yi yawa, ka sani kawar da duwatsu daga wurinsu ya fi sauki fiye da fahimtar da wanda ba ya fahimta.
Kada wani ya ci abincinka sai masu tsoron Allah, kuma ka shawarci malamai a al'amarinka.
Ya dana! Idan kana son abota da wani mutum sai ka sanya shi fushi da farko, idan ya yi maka adalci sai ka rike shi aboki, amma idan ba haka ba to ka guje shi.
Kalmarka (maganarka) ta kasance mai dadi kuma fuskarka ta kasnce sakakkiya sai ka kasance mafi soyuwa wajen mutane fiye da mai ba su kyauta.
Ya dana!; Wanda ya riski ilmi to menene ya rasa?
Ya dana! Ka ji tsron Allah tsoron da, da za a zo da kai ranar alkiyama da biyayyar halittu biyu (mutum da aljan) kana jin tsoron kada ya azabtar da kai, kuma ka kaunci Allah kaunar da, da ka zo da zunubin halittu biyu da kana kaunar ya gafarta maka. Sai dansa ya ce da shi: Ya babana! Yaya zan iya hakan alhalin zuciya daya nake da ita?! Sai ya ce: Ya dana! Ka sani da za a fitar da zuciyar mumini a tsaga ta da an same ta da haske biyu, hasken tsoro da hasken kauna, kuma da an auna da ba abin da ya rinjayi dayan koda kuwa daidai kwayar zarra. Wanda ya yi imani da Allah ya gaskata fadin Allah zai aikta abin da ya umarce shi ne, amma wanda bai aikata abin da Allah ya umarce shi ba bai gaskata fadin Allah ba; Domin wadannan halaye ne da wasu ke gaskata wasu, wanda ya yi imani da Allah imani na gaskiya zai yi aiki don Allah, kuma wanda ya yi aiki don Allah yana mai tsarkakewa to ya yi imani da Allah da gaskiya, wanda kuma ya bi Allah ya ji tsoronsa, wanda yaji tsronsa hakika ya so shi, wanda ya so shi zai bi umarninsa, wanda kuwa ya bi umarninsa ya cancanci aljannarsa da yardarsa, wanda kuma bai bi yardar Allah ba to ya ha'inci Allah, wanda kuma ya ha'inci Allah ya cancanci fushinsa da azabarsa, muna neman tsarin Allah daga fushinsa da azabarsa da tabewarsa da kuma kamunsa.
Ya dana! Ba a iya aiki sai da yakini kuma mutum ba ya aiki sai daidai gwargwadin yakininsa, kuma mai aiki ba ya takaita wa sai daidai gwargwadon yakininsa, kai ka ce dai yakini ya fi ilimi domin shi ne yake kaiwa ga aiki, kuma duk abinda ya fi kaiwa ga aiki to ya fi kaiwa zuwa ga bauta, kuma duk abin da ya fi sanyawa a yi bauta ga Allah to ya fi kaiwa ga biyan hakkin Ubangijintaka kuma shi ne ya fi kaiwa zuwa ga kamalar cikakken rabo.
Ya dana! An hana kauro, ka sani shi tsoro ne da firgici da dare kuma kaskanci da rana.
Ya dana! Ka yawaita fadin: Ubangiji ka gafarta mini, ka sani Ubangiji yana da wata awa da baya mayar da rokon mai addu'a.
Ya dana! Idan shaidan ya zo maka ta fuskacin kokwanto to ka rinjaye shi da yakini da nasiha, kuma idan ya zo maka da kasala da yanke kauna to ka rinjaye shi da tuna kabari da kiyama, idan ya zo maka da kwadayi da tsoro, to ka sanar da shi cewa wannan duniya mai karewa ce abar bari ce.
Ya dana! Ka riki tsroron Allah fatauci riba zata zo maka ba tare da kayan haja ba.
Ya dana! Kada ka jinkirta tuba, ka sani mutuwa tana zuwa bagatatan.
Ya dana! Kada wani mutum da ya zare damatsansa yana zubar da jinin muminai ya bakanta maka rai, ka sani a gurin Allah (da saninsa) akwai wanda zai kashe shi kuma ba haka nan kawai zai mutu ba.
Ya dana! Ka sani hikima ce ta zaunar da miskinai mazaunin sarakuna.
Ya dana! Kada ka zauna da ashararai, ka sani babu wani alheri da zai same ka da zama da su, kuma ta yiwu daga karshe wata ukuba ta sauka kansu sai ta same ka.
Ya dana! Idan ka je wajen mutane to ka jefa musu mashin nan na musulunci (wato sallama) sannan sai ka zauna a gefensu, idan suka kutsa cikin ambaton Allah sai ka zauna tare da su, amma idan suka shiga wanin wannan sai ka juya ka bar su.
Ya dana! Idan mutum ya zo maka yana mai kawo kara ga shi kuma idanuwansa biyu sun fita, to kada ka yi hukucni sai abokin husumarsa ya zo, ta yiwu shi ma ya zo maka shi an cire masa idanuwa hudu ne.
Ya dana! Ka tsayar da salla, ka sani babu kamarta a cikin addinin Allah, ita kamar amudi ne, idan amudai suka tsayu daidai sai wannan ya amfani turaku da inuwa, idan kuwa bai tsayu ba babu wata turaku ko inuwa da zata amfanar.
Ya dana! Ka abotakanci malamai ka kuma zauna tare da su, ka ziyarce su a gidajensu tayiwu ka yi kama da su sai ka zama daga cikinsu.
Ya dana! Ka sani cewa ni na dandani hakuri da kuma nau'o'in dacin rayuwa ban ga abin da ya fi talauci daci ba, idan ka yi talauci wata rana to ka sanya talaucinka tsakaninka da Allah kada ka gaya wa mutane sai ka wulakanta a wajensu, sannan ka tambaya cikin mutane ka ji shin akwai wanda ya yi addu'a Allah bai karba masa ba, ko kuma ya roke shi bai ba shi ba?
Ya dana! Ka aminta da Allah sannan sai ka tambayi mutane, shin akwai wanda ya aminta da Allah bai amsa masa (amintuwa) ba?
Ya dana! Ka dogara ga Allah sannan sai ka tambaya cikin mutane shin akwai wanda ya dogara ga Allah bai isar masa ba?
Ya dana! wanda ya nemi yardar Allah to zai yi fushi da kansa da yawa, wanda kuma bai yi fushi da kansa ba to ba zai yardar wa Ubangijinsa ba, wanda kuma ba ya hadiye bakin cikinsa to zai zagi makiyinsa.
Ya dana!; Wane ne ya nemi yardar Allah bai samu ba, wane ne ya dogara zuwa ga Allah bai kare shi ba.
Ya dana! Ina kwadaitar da kai ga dabi'u shida, babu wata dabi'a daga ciki sai ta kusantar da kai zuwa ga yardar Allah madaukaki, kuma ta nisantar da kai daga fushinsa; Ta farko ita ce ka bauta wa Allah kada ka yi shirka da shi da wani abu. Na biyu: Yarda da hukuncin Allah cikin abin da kake so da kuma wanda kake ki. Na uku: Ka so don Allah ka kuma ki don Allah. Na hudu: Ka so wa mutane abin da kake so wa kanka, kuma ka ki musu abin da kake ki wa kanka. Na biyar: Ka hadiye bakin cikinka ka yi hakuri, ka yafe wa wanda ya cutar da kai. Na shida barin son rai da sabawa bata .
Ya zo daga Imam Ja'afar Sadik (a.s) cewa: Lukman mai hikima ya kasance yana yi wa dansa wa'azi, bai gushe ba har sai da dansa ya rabe ya tsage, wannan kuwa yana nuna matukar tasirantuwa ne.
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012