Bukatun Jiki
Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Gyaran Rai Na Daya A nan zamu so mu yi nuni da kusurwowin samuwar mutum guda biyu masu muhimmanci da ya hada da rayinsa da jikinsa da siffofin duka biyu da yadda ya kamata a tarbiyyantar da su. Wannan kuwa shi ne mafi muhimmanci a rayuwar dan Adam da idan ya gyaru to dukkan bangarorin sun samu gyaruwa, amma idan ya baci to dukkan bangarorin sun baci. Jikin mutum yana da abubuwan da yake bukata na rayuwa domin ci gaba da samuwa, wadannan abubuwan idan babu su to karshensa ya zo ke nan. Yana bukatar abubuwa biyu na ciki da na waje, da kuma wani abu na uku da ya shafi rayuwarsa a matsayinsa na dan Adam.
Na ciki sun hada da ci, da sha, da magani domin waraka daga cututtuka, sai kuma abin da jiki yake furzarwa wadanda suke fita daga gareshi domin samun sauki kamar kashi, da bawali, da amai, da mani, ko wadi da mazi, da gumi ko zufa, da hawaye, da majina, da daudar kunne, da yawun baki.
Na waje kuwa sun hada da wanke dauda, da sanya tufafi kamar riga da wando, da takalmi da hula, da sanya abu mai kanshi kamar turare, da kayan ado kamar sarka da dan kunne, da awarwaro, da mai domin shafawa, da mai domin gyaran gashi, da jan farce. Kamar yadda yake bukatar wurin zama da inda zai samu rayuwa mai kyau da shakatawa, sannan ya samu wani abu da zai rage masa wahalar cirata daga wuri zuwa wani wurin kamar mota ko babur.
Amma a bangare na uku yana bukatar wasu abubuwa da suka shafi zaman tare na al'umma, da hukumar da yake karkashinta, idan mun duba irin wadannan abubuwan zamu ga suna cikin bayanai kamar haka:
Mutum yana bukatar wasu abubuwan saukaka rayuwa da yalwarta kamar wutar lantarki da ruwan famfo, da titi mai kyau, da amincin gari ta yadda babu wani wanda zai zo domin satar kayansa, ko dukansa ko kisansa, kuma yana bukatar kare duk wani abu da ya shafi jininsa, ko mutuncinsa, ko dukiyarsa. Amma sama da hakan akwai 'yancin fadin ra'ayi da kare hakkinsa domin kada wani ya takura masa a wannan fage mai muhimmanci. Fadin ra'ayi yana kama da amai ko atisshawa ne da idan ba su fito ba to suna kumewa a cikin jiki, haka nan ra'ayi yakan zama ya kume a cikin tunani sai ya kasance wani bakin ciki da yake taruwa a cikin zuciya.
Akwai wani abu da yake bukatarsa wanda ya fi kowanne muhimmanci wanda shi ne akidarsa, kowane mutum yana bukatar inda zai rayu da imani da akidarsa, yana kare akidarsa da hujjojinsa na shari'a ko na hankali.
Idan mun duba sai mu ga kowane bangare sai da shari'a ta ba shi matsayi na musamman domin kamalar mutum. Don haka ne a nan zamu yi nuni da wasu daga ciki a dunkule, mai son duba bayanai masu fadi sai ya koma wa littattafan shari'a.
Idan mun duba bukatun jiki na ciki sai mu ga shari'a ta muhimmantar da su ta yadda ta hana ci ko shan wani abu da yake cutarwa ko lahantawa, da yawa ayoyin da suka yi bayani kan haka a cikin littafi mai tsarki na Kur'ani, wasu ayoyin sun yi nuni da cewa: "… kuma ba a sanya muku kunci a cikin addini ba..." , wasu kuwa sun yi nuni da cewa: "... kuma yana haramta musu mai muni -cutarwa- ..." . A nan muna iya cewa hatta da abu mai sanya maye da aka haramta a shari'a yana komawa ga cutuwar mutum a hankalinsa ko jikinsa ne.
Sai shari'a ta haramta dukkan mai sanya maye da mai cutarwa domin ta kare tarbiyyar mutum ta jiki da ta rayinsa, da gujewa sanya masa kunci a cikin rayuwarsa, da kaucewa ransa ko jikinsa daga fadawa cikin wahala da halaka.
Dogaro da wannan maslahar ne shari'a ta sanya wajabcin yin magani ga wanda ba shi da lafiya domin ba ta halatta masa cutar da kansa ko wata gaba ta jikinsa ba, don haka ne ta hana sayar da wani bangare na jikinsa wanda zai kai shi ga cutar da ransa ko jikin, sai dai idan babu cutuwa a ciki kamar sayar da wani bangare na jininsa.
Sannan hikimar Allah ta sanya masa wasu dokokin da zai samu sauki a cikin jikinsa kamar furzar da majina ko miyau, ko amai, ko kuma fitar da dauda da dattin da ya taru a cikin jikinsa ta hanyar bawali da bayan gida, ko kuma fitar da maikon da yana iya daskarewa ta hanyar gumi da zufa. Da ba a sanya masa hanyoyin da zai samu sauki ba da ya halaka, da rayuwarsa ta kare, amma sai ya kasance an ba shi hanyoyin sararawa.
Sannan aka sanya masa hanyar sanyaya ransa da zuciyarsa ta hanyar yin kuka abin da yake ni'ima ce babba ga bayi da Allah ya yi musu. Kuma iyakacin bala'in da ya fada wa mutum da nauyinsa a kan zuciya ne ransa take bukatar fesar da shi ta hanyar yin kuka domin samun lumfasawa.
Ruwaya ta zo cewa: "Masu kuka mutum biyar ne..." . Kuka wani abu ne da ake son yin sa domin wasu abubuwa da suka hada da tsoron Allah ga wanda ya tuna zunubansa, ko yayin wata musiba kamar mutuwa. Wasu mutane sun so hana kuka yayin mutuwa, sai dai wannan ya taso daga rashin fahimtar maganar manzon Allah ne da wani sahabi ya yi, sai Ai'sha matar Annabi (s.a.w) ta gyara masa cewa ba haka ake nufi ba, sai dai abin da aka hana a kukan mutuwa shi ne fadin abin da ya saba wa shari'a.
Wata hanyar samun lafiya da Allah ya sanya wa bayinsa ita ce hanyar fitar wasu abubuwa da shari'a ta sanya wanka saboda fitarsu, wadannan abubuwan sun hada da mani, da jinin haila da na haihuwa, da na istihala idan yana da yawa sosai. Akwai kuma wasu ruwa masu fita daga mutum da ba a sanya komai a kansa ba don sun fita, wadannan su ne mazi da wadi, kuma shari'a a bisa mahangar Ahlul-baiti (a.s) ta yi musu hukunci da tsarki.
Wasu kuwa an sanya yin tsarki ne saboda fitarsu wadannan abubuwan sun hada da bawali da gayadi, wadannan idan sun fita sai mutum ya yi tsarkinsu. Akwai kuma wasu halaye su ma da ake son wanda ya yi su ya yi alwala, wadannan abubuwan sun hada da yin bacci ko suma.
Amma abubuwan da suke daga wajen jiki sun hada da tsarkin daudar jiki, shari'a ta sanya tsarkake jiki daga dauda domin kada ya yi wari ya cutar da kanda da mutane. Wata ruwaya tana cewa da mu: "An gina addini a kan tsafta ne" , wata kuwa tana cewa: "Tsafta tana daga imani ce" . Kazamin mutum ba ya samun kima da daraja a cikin mutane, mutane suna wulakanta wanda suka gani cikin kazanta komai kimarsa.
Akwai kuma kayan sawa da suka hada da riga da wando, da takalmi, da hula, da turare, da gashin mata, da sauran kayan ado kamar sarka da awarwaro da dan kunne, ko jan farce da sauransu. Shari'a dukkaninsu ba ta hana su ba, sai dai a tufafin mace ta wajabta mata rufe dukkan jikinta in banda fuska da tafuka.
Wadannan tufafin kowace al'umma tana da nata yanayin shiga, kuma dukkan shigar al'umma ba ta da wata matsala a shari'a matukar dai ba ta saba wa waccen doka da aka sanya wa mace ba. Al'adun Hausa mace tana iya sanya atamfa da dan kwali da zane, da mayafi, sai ta rufe duk jikinta da wannan, tana iya sanya wando ko ta hada zane da wando.
Muna iya ganin a wasu al'ummun namiji ne yake daura zane mace kuma wando, wannan yana nuna mana kowace al'umma tana da nata yanayin shiga, kuma babu wata shiga da musulunci ya hana sai dai kawai ga mace idan zai kai ga bayyanar da jikinta da ya hana.
Wasu jama'un namiji yakan iya sanya gajeren wando da 'yar riga, mace kuwa ta sanya siket da riga. Musulunci bai hana su wannan shiga ba, sai dai mace idan zata yi siket ya ja har kasa ta yadda zai rufe dukkan kaurinta har kafarta babu wani haramci a kan hakan, kanta kuwa da jikinta ta sanya riga zuwa karshen hannunta, ta sanya kuma abin da zai rufe kanta.
Muhimmi a cikin tufafi shi ne kiyaye wancan ma'anuni da musulunci ya sanya, idan aka kiyaye wannan babu wani tufafin wata al'umma da ya fi na wata. Babu bambanci, babban tufafi da karami duka daya suke, babu bambanci tsakanin babbar riga da kot da wando a wurin shari'a wannan duk yana komawa ga tunanin al'adun mutane ne.
Muna iya ganin yadda hula take da muhimmanci a wata al'umma, a wasu al'ummu girman mutum yana kan hularsa ne, da zai je taro babu hula to da kimarsa ta fadi ke nan. Amma a wasu al'ummu hula ba ta da wata kima ta a zo a gani, wasu suna ganin cewa sanya hula da dare yana haifar da matsala a ganin mutum, wasu sun tabbatar da matsalar yawan rufe gashi kodayaushe.
Amma wasu al'ummu idan ba su sanya hula ba suna ganin kamar ba su kammala ba, kana iya ganin mutum yana rufe kansa da zafin rana, kansa yana ta yi masa kaikayi amma ba zai cire hular ba, mafi muni shi ne likita yana iya hana shi sanya hula amma don kada al'umma ta gan shi karamin mutum sai ya sanya, haka nan al'adu suke cutar da al'ummu daban-daban.
Musulunci yana son tufafi ne na takawa, don haka kowace irin shiga al'umma take da shi ba shi da muhimmanci a wurinsa, abu muhimmi a nazarinsa shi ne takawar mutum, mutumin da yake sanya gajeren wando da karamar riga yana mai jin tsoron Allah da kiyaye dokokinsa shi ne abin so wurin Allah, amma mutumin da ya sanya rawani da alkyabba, ga babbar riga da mota mai tsada ba shi da wata kima wurin Allah sai idan shi ma yana da takawa.
Wannan ne ya sanya ma'aunin Allah da yake kallon bayinsa da shi ya saba da ma'aunin da mutane suke kallo da shi. Ma'aunin Allah ya doru bisa ganin dukkan halittarsa a daidai a cikin al'adunsu matukar ba su saba wa dokokinsa, amma tsukakken tunanin mutane yana girmama dan Adam ta cikin al'adu da abin duniya ne.
Idan muka waiwayi kayan adon mata haka nan babu wani ado da musulunci ya hana mace kowane iri ne, sai dai bai halatta ta bayyanar da adonta ga wasu mazaje ba sai dai ga mata ko mutane da suke muharramai kamar 'yan'uwanta, babu wani dan kunne ko sarka, ko man shafawa, ko karin gashi, ko rina gashi, ko jagira, ko jan farce, da sauran kayan ado da addini ya hana mace.
Sai dai namiji yana da dabaibayi da shari'a ta yi masa na cewa bai halatta ya sanya zenare ko azurfa ba, ko alhariri bisa sabani, don haka mace tana iya sanya zinare amma namiji bai halatta ya sanya shi ba. Zai iya yiwu wata al'ummar ya kasance namiji yana yin kitso ko ya sanya dan kunne da sarka ko awarwaro don adon namiji, shi ma a nan musulunci ya hana namiji sanya sarkar zinare, wannan haramcin na zinare ga namiji ba shi da bambanci a cikin al'ummu.
Game da wurin zaman rayuwa kamar gida, ko kuma wani abin hawa kamar mota, babu wani wanda Allah ya yi wa haramcinsa kamar namiji ko mace, a irin wannan abubuwan shari'a ba ta hana komai ba sai idan na haram ne. Idan gida ya kasance na kwace, ko filin kwace, to sai shari'a ta haramta zama da yin salla a cikinsa, kamar yadda ta haramta hawa motar sata ko ta kwace.
Wasu masu daskararren tunani game da musulunci sai suka hana mace tuka mota bisa jahilci, irin wannan jahilci ana yin sa a wasu kasase abin takaici da sunan musulunci. Kamar yadda zamu ga wasu kasashen ko kungiyoyi, ko ma wasu masu bayar da fatawa bisa tsukakken tunaninsu sun takaita kaya da irin na al'adarsu suna masu daukar cewa shi kadai ne na musulunci.
Amma a bangare na uku mutum yana bukatar wasu abubuwan saukaka rayuwa da yalwarta da ya hau kan hukumar da yake rayuwa karkashinta ta samar masa da su, irin wadannan abubuwan sun hada da wutar lantarki da ruwan famfo, da titi mai kyau, da amincin gari ta yadda babu wani wanda zai zo domin satar kayansa, ko dukansa ko kisansa.
Aminci wani abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar dan Adam, idan babu shi to al'umma ba ta samun sukunin ci gaba. Don haka yana bukatar mai kare masa jininsa, da mutuncinsa, ko dukiyarsa. Kamar yadda yake matukar bukatar wanda zai kare masa 'yancin fadin ra'ayinsa, da kare hakkinsa domin kada wani ya takura masa a wannan fage mai muhimmanci.
Sannan akwai wani abu da yake bukatarsa wanda ya fi kowanne muhimmanci wato 'yancin akida, kowane mutum yana bukatar inda zai rayu da imani da akidarsa, yana kare akidarsa da hujjojinsa na shari'a ko na hankali. Kuma wannan akida wani abu ne da ya kafu a ransa, ya yi rassa a gabobinsa, don haka ne ba a tilasta mutum ya bar akidarsa, idan ana son gamsar da shi cewa akidarsa batacciya ce, to ya zama ta hanyar hankali ko hujjar shari'a.
Cibiyar Al'adun Musulunci
www.hikima.org
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Tuesday, May 25, 2010