Tattaunawa Ta Biyar
MARUBUCI: Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
TATTAUNAWA TA BIYAR Amma da kake cewa kalmar "Wali" ba a fili take ba, kuma ka yi da'awar yardar Allah ga duk wanda ya yi halifanci kafin Ali (a.s), sai in ce maka: Yana da kyau ka yi wa kanka adalci: ina ganin ka kasa fahimtar abin da na kawo don haka ka koma sosai ka duba, ka kuma nemi taimakon malamanka a kai, kan batun "amm" da "khas" da na kawo. Sannan kuma wani abin mamaki shi ne dukkan hadisai da karinonin da na kawo sai ga shi kana maganar karina a kai. Ka koma wa bayanin baya zaka ga karinonin da na kawo na wasu ayoyi da hadisai da suka karfafi wannan maganar, hada da cewa farkon hudubar Manzo (s.a.w) da karshenta duk yana nuna wannan karinar karara. Wadannan karinonin kuwa a cikinsu akwai: “zikra liman kana lahu kalbun au alkas’sam’a wahuwa shaheed”.
Amma batun da kake cewa ba a ruwaito hadisin Gadir ba sai in ce maka: Sahabban da suka rawaito Gadir suna da yawa kwarai matuka, ka koma wa littafin Gadir na Allama Sheikh Amini ka sha mamaki, kuma akwai ruwayoyi sama da 360 da ya yi nuni da su, wadanda sun zo game da Gadir daga sama da sahabi 125.
Sannan kada ka dauka in ka kaddara masu ruwaya koda daya ce idan ta inganta ba ta zama hujja, domin ku kun doru a abubuwa da yawa kan ruwaya guda ne hatta a al’amarin akida. Wannan hadisin an kasa boye shi, don haka ya zo hannun mutane da ikon Allah (S.W.T), amma akwai wasu hadisai da siyasa ta kan sanya a ki yada su, ko kuma boye wasu kalmominsu ko canza su kamar karshen hadisin halifofin Annabi (s.a.w).
Amma da'awar cewa Annabi (s.a.w) ya yi mummunar addu'a ga wanda ya ki biyayya ga Ali (a.s) da cewa wannan ya saba wa usulubin da'awa ta gari da da'awarka ta cewa Annabi (s.a.w) ba ya yi wa al'umma addu'a mummuna da fakewa da cewa rashin taimakawar yana iya kasancewa cikin rashin sani. Sai na ce maka: Duk wannan babu kokwanto cikin shari’a idan ta inganta, amma a cikin maganganunka akwai alamar tsananin kushewa game da abin da ya zo yana yabon Ahlul Bait (a.s). ko kuma yana ba su wata falala, wannan ba ya cikin dabi’ar mumini. Kada tafarkinka ya kai ka cikin tabewa! Sannan abin da ka fada na cewa ya saba wa da’awar Annabi (s.a.w) da Kur’ani mai girma ta la’antar duk wani wanda ya saba wa tafarki bayan gaskiya ta zo masa: surar “Tabbata yada Abi lahabin” babban misali ne gareka. Hada da abin da yazo yana la’antar magabata kamar su Fir’auna da wadanda suka gabace shi da wadanda suka zo bayansa. Hada da la’antar munafikai da Kur’ani ya yi, da masu cutar da Annabi (s.a.w) aka kuma muzanta su muzantawa mai muni kamar kiransu marasa hankali da sauransu.
Amma da'awar ayar tablig a Arfa da ka yi hakika masdarori sun zo suna masu tabbatar da saukar wannan aya a Gadir, akwai dalilai masu yawa kan hakan, sannan kuma wasu sun kawo ta game da cewa a ranar hajjin wada’ ne. wasu kuma sun hada duka biyun ne, kuma wannan me sauki ne, ana iya hada su.
Sannan musun hadisi ko ingancinsa saboda ya yabi ahlul baita (a.s) wani abu ne da na fahimta yayin da kake maganar musun ruwayar Suyudi, ka sani wannan ya inganta daga littattafai masu yawa: tun kafin Suyudi, amma wani abin da nake fahimta daga wajenka duk wata magana da ta yabi Imam Ali (a.s) ko Ahlul Bait (a.s) ko ta karfafi wilayarsu, to kana kokwanton ingancinta ba tare da ilimi ba, ko kuma saboda inadi ne! Shiblanji ya karbo shi daga sa’alabi, sannan kuma halbi ya kawo shi mursali a matsayin wani hadisi da aka sallama wa ingancinsa, a siratul halbiyya, j 3, shafi 214.
Amma batun me Annabi (s.a.w) ya bari: wannan maganar ta abin da Annabi (s.a.w) ya bari wanda ya mutu a kai ya gabata, kuma ya riga ya tabbata cewa; shi ne tafarkin da Ahlul Bait (a.s) suke kai, su ne ma’auni da za a koma gareshi yayin sabani. Addini ya cika, kuma daga cikin cikarsa akwai biyayya ga Ahlul Bait (a.s) kamar yadda Manzo (s.a.w) ya yi wasiyya da bin su, wannan duk yana daga cikar addini. Allah (S.W.T) da manzonsa (s.a.w) sun barranta daga wautar da ake jingina musu, Manzo (s.a.w) ya san wannan addini shi ne karshe, kuma yana da hadafin shiryar da mutane gaba daya, ba zai yiwu ba ya tafi ya bar su kara zube, ba su san inda zasu dafa ba.
Kuma wannan rashin hikima abin takaici ba wanda ake jingina wa shi sai mafi hikimar bayin Ubangiji, kowane jagora zai tafi yana nuna wa al’umma makomar da ya kamata ta bi, amma sai Annabi (s.a.w) ne ake jingina wa rashin hadafi!
Amma batun da'awar da ka yi na cewa Allah (s.w.t) ya yi alkawarin kare sunnar ma'aiki sai na ce maka: Allah bai yi alkawarin kare Sunna ba, ya yi alkawarin kare Kur’ani ne! don haka ne ma Sunna take cike da mai inganci da waninsa: Wannan ne ma ya kawo ilimin hadisi da masu ruwayarsa da sauransu. Abin mamaki rashin ma’auni da kuma wata ka’ida ko madogara mai kyau da kake da ita, ya sanya ka kana magana kana warwara. Kana musun wata sunnar ta Annabi (s.a.w) da ya bari saboda ta yabi ko ta shugabantar da Ahlul Bait (a.s). a lokaci guda kuma kana cewa Allah ya yi alkawarin kare ta. Idan ka san Allah ya yi alkawarin kare ta to don me kake wahalar da mutane wajen musun ta da neman ba ka hujjoji kan ingancinta!?
Sannan ka ce ana kokarin jifan wasu da munafunci, wannan kuma wani abu ne da ka fahimta kuma ba na iya shiga kwakwalwarka in hana ka fahimtar abin da ka dama. Amma abu guda shi ne yana da kyau ka nisanci zargi domin ba shi da kyau.
Amma game da abin da aka yi wa alayen Annabi (s.a.w) ina mamakin jahiltar ka ga addini: Idan ka yi musun tarihin la’antar Imam Ali (a.s) to lallai ka nuna wa duniya rashin saninka da tarihin addininka sannan kuma ka jahilci musallamat na tarihi da al’umma ta hadu a kai. Amma Imam Hasan (a.s) bai bayar da iko hannun Banu Umayya ba, sai dai abu ne wanda ya zama masa tilas kamar yadda dukkan imamai (a.s) suka yi hakuri kan abin da ya fi karfinsu. A yanzu zaka iya cewa manzon rahama (s.a.w) ya bar mulki ga mutanen makka ne bisa sonsa, ba don saboda ba shi da karfin da zai iya kwata daga hannunsu ba?!
Sannan da kake cewa ya kamata a yi shiru kan abin da ya faru: Inda abin da ya faru ya kamata a yi shiru kansa da Kur’ani ya koyar da mu hakan: sabanin hakan Kur’ani ya karfafi mu binciki abin da ya faru baya domin kada mu fada irinsa, sannan kuma manzon rahama (s.a.w) da wasiyyansa (a.s) duk sun koya mana hakan; Wannan doka da Basari da Nu’uman suka sanya ta saba da Kur’ani da hadisai ingantattu kuma ba yadda za a yi ta fitar da mu matsalolinmu na duniya da lahira.
Ka sani binciken tarihin da ya gaba ta, ba don a gano laifin wani ba ne, sai dai domin ka san waye yake hujja kanka ka bi shi da wanda yake ba hujja ba, domin yanzu muna iya tambaya cewa; waye yake hujja ne bayan Annabi (s.a.w) a kanmu mu karbi addini daga gareshi waye kuma ba hujja ba?! Ku kun dauka domin a ce wane ya yi laifi ne, wane kuma bai yi ba shi ke nan. Idan kuwa haka ne da ba shi da amfani, da Kur’ani bai yi binciken halayen wadanda suka gabata ba?.
Amma game da Hakim da ya fitar da hadisin da ya san Buhari da Muslim sun yarda da shi, sai dai Buhari bai kawo shi ba, da kuma musun matsayin Hakim: Idan ka yi kokwanto kan Hakim to ka nuna jahiltarka da sunnanci. Amma da ka ce Manzo (s.a.w) ya bar duniya yana kan Kur’ani da hikima haka ne mana, amma wannan yana nuna abin da Manzo (s.a.w) ya yi ne, ba ya hana kuma cewa ya bar wa al’umma Littafin Allah da Ahlul Bait (a.s), ko kana da jur’ar da zaka ce da ya tafi sai ya tafi da kur’anin da hikimar bai bar wa al’ummarsa su ba ne! kuma mun sha nanatawa cewa Allah ya yi alkawarin kare kur’anin ne. amma Sunna abin da yake cikinta musamman ma maganganunsa ya gabata cewa; akwai wanda aka jingina masa, kuma tun yana raye aka fara yi masa karya, ka ga ke nan ina ga bayan idanuwansa (s.a.w).
Amma game da Halifofi sha biyu: Ya gabata mun ba ka madogara da ka yarda da ita kan halifofi goma sha biyu ne. kuma sanadin hadisin a gun Muslim shi ne dai ya zo a gunmu a littafin Kafi, sai dai ku kun ce dukkaninsu daga Kuraish ne, amma a gunmu dukkaninsu daga Banu hashim ne, Jabir ya yi furuci da cewa an yi kokarin canja karshensa har da neman boyewa, al’amarin da yake nuna Banu hashim ne daidai sai aka jirkita shi da kuraish domin ya game kowane irin bakuraishe. Haka nan Shiblanji mai Nurul Absar ya kawo tarihinsu gaba daya, bayan ya kawo na halifofin farko uku, ka koma wa littafinsa.
Amma fadinka: "Ba zan taba yadda da cewa babu alaka tsakanin son mutun da son ahalinsa ba": Shin ba ka fahimtar abin da kake cewa ne, dubi yadda ka yi magana sai kuma a karshenta ka warwareta. Kana cewa ne: akwai alaka tsakanin son mutum da son ahlinsa, sai kuma ka kawo yadda Annabi guda ya ki dansa kana mai warware jumlar baya.
Amma batun da kake neman shigar da wasu cikin Ahlul Baiti (a.s) wanda manzon Allah bai shigar da su ina ganin amsar da zan ba ka kamar haka: Don Allah ka rika kula da abin da kake cewa:
Na daya: Annabi (s.a.w) ne ya kore matansa daga Ahlul Bait (a.s) ba ni ba. Na biyu: Zaid bn Arkam ne yake da wannan ra’ayi cewa: su ne aali Ali (a.s) aali Abbas aali ja’afar da aali Akil, ba Annabi ba.
Aikin Annabi (s.a.w) doka ce mai karfi da ba mai ture ta sai munafiki ko kafiri, don haka idan Annabi (s.a.w) ya yi wani abu, to mu ba mu da wata doka da zamu kirkiro ta ture ta sai dai mu sallama.
Kuma a nan "lazim akali" ba hujja ba ne haka ma Urfi. Domin yana karo da nassi.
Waye Abdurrazak da kake cewa bai inganta Hadisuddar ba? Bin ibrahim khurasani ko bin hammam yamani, ko aljilani ko waye… ba mutum daya ba ne a ilimin ruwayoyi mai wannan suna sai ka kawo inda ya ture ta, kuma bisa wacce hujja ce. Sannan kuma ka sani wannan hadisi bai kebanta da Mustadrak ba! Amma hadisin manzila ya zo a wurare masu yawa kamar haka:
Na daya: Lokacin ‘yan’uwantaka da ya sanya wa kowa dan’uwa ban da Ali (a.s) sai ya gaya wa Imam Ali (a.s) wannan maganar. Kuma Suyudi a Durrul Mansur ya ruwaito shi a tafsirin ayar nan ta “Allah ne yake zabar manzanninsa daga mala’iku kuma daga mutane…” daga Bagawi da Bawardi da Ibn Kani’ da Tabrani da Ibn Asakir.
Da manakibu Ali gun Ahmad bn hanbal, da manakibul ashara, da kanzul ummal a manakibu Ali (a.s). wannan fa ka duba duk malaman Sunna ne.
Na biyu: A hadisuddar da ya gabata a cikin muhawarorinmu.
Na uku: A hudubar ranar Gadir ya ambace shi da kalmar wazirinsa.
Na hudu: A al’amarin toshe dukkan wata kofa banda ta Ali (a.s), Magazili ya ambace shi a manakib dinsa, a babin manakibu Ali (a.s).
Na biyar: A al’amarin ‘yar Hamza bn Abdulmudallib.
Na shida: A almarin kwana a cikin masallaci da ya hana kowa kwana a ciki sai shi.
Na bakwai a hadisin Ummu Salama da ya gaya mata game da Ali, Kamar yadda ya zo a littafin tarihi damishk.
Wannan kadan ke nan daga wuraren da manzon Allah (s.a.w) ya yi amfani da kalmar wazirinsa ga Imam Ali (a.s). Hada da abin da ka sani wanda ka kawo na yakin Tabuka, wanda shi ne na takwas a lissafinmu. Akwai hadisin a musnad Ahmad ya ce: wannan hadisi isnadinsa ingantacce ne. musnad, 1: 545.
Ka sani Manzo ya shelanta matsayin Imam Ali (a.s) a wurare da yawa da malaman Sunna suka ruwaito, duba ka ga me nisa’i ya kawo a khasa’is dinsa: 49-50. da yake cewa: manzon Allah (s.a.w) ya ce; kai ne halifana bayana kan kowane mumini da mumina, kai matsayinka gareni kamar na haruna ga musa, kai ne halifata a kan kowane mumini bayana.
Hada da abin da abu ya’ala a Masnad dinsa da kuma Mustadrak: 3: 1333. da tarihi damishk: 1: 209. da tarihi ibn kasir : m 4, j 7: 338. da isaba na ibn Hajar: 4; 270. da sauransu. duk sun kawo cewa: manzon rahama (s.a.w) ya ce: ba zai yiwu ba in tafi sai kana halifana.
Amma game da auren mutu'a da ka kawo ka sani ya inganta daga Imam Sadik (a.s) cewa: Mutu'a addinisa ce, kuma addinin kakanninsa ba. Sai dai ina nufin kana nufin ya ce: "Takiyya addinisa ce, kuma addinin kakannina", kuma haka ne wannan ya inganta daga Imam Sadik (a.s). Amma batun da ka kawo na cewa; Annabi (s.a.w) ya haramta Mutu'a a yakin Khaibar wannan labari ne da aka jingina shi ga Imam Ali (a.s) don a rusa tafarkinsa, kuma wannan bai inganta ba, domin ya ci karo da Kur’ani kuma ya ci karo da abin da ya zo mutawatiri daga Imam Sadik (a.s), daga kakansa Imam Ali (a.s), kuma tun da hadisin aahad ne, to bai isa ya rusa Kur'ani ko mutawatirin hadisi ba.
Sannan duba tarihin halifofi na Suyudi ka gani a babin awwaliyati Umar, cewa shi ne farkon wanda ya haramta auren mutu’a. Maliku ya kawo shi a muwatta’ Umar ya hana kuma ya kira shi da nikahussirri.
Ka kuma duba fadin Umar bn Khaddab cewa: Mutu’a biyu ta kasance a lokacin manzon Allah (s.a.w) amma ni na haramta su kuma ina ukuba a kai: Auren mutu’a da hajjin tamattu’i. Littattafai da dama sun kawo kamar Mugni na ibn kuddama bahambale.
Bayanin cewa Umar shi ne ya haramta auren mutu’a kan al’amarin ibn haris ya shahara sosai tsakanin malaman Sunna da Shi'a koda kuwa wasu masu kawo rudu a wannan zamani sun so hakan.
Allah waddan naka ya lalace; kai tir da masu musun hadisi ingantacce kamar fadin manzon Allah (s.a.w) game da kasancewar Imam Ali birnin ilminsa: Ban san sa’adda ka zama Harrani ba da zaka rika dukan falalar Imam Ali (a.s) ba tare da wani dalili ba, kai ba dan yankin HARRAN ba ne, balle ka taso da kin Ahlul Bait (a.s), ban sani ba ko gaba da wannan gida ya zo mana Nijeriya ne daga koyarwarsa, sai ya zama duk wani abu ingantacce daga Ahlul Bait (a.s) musamman game da Imam Ali (a.s) sai a rika gaba da shi.
Hadisin kasancewar Imam Ali (a.s) kofar birnin ilimin Annabi (s.a.w) yana daga musallamat gun dukkan musulmi har sai da Dan Harran ya zo yana inkarin duk wata falala ta Imam Ali (a.s), wannan kuwa ba mamaki domin shi dan HARRAN ne wanda yanki ne da suka sha gaba da wannan gida tun lokacin Mu'awiya dan Abu Sufyan.
Alharrani ya karyata wannan hadisi kuma ya danganta wadanda suka ruwaito shi da cewa zindikai, alhalin daga cikin masu ruwayar wannan hadisi akwai: Imam Ali (a.s) kansa, da Hasan da Husain ‘ya’yansa, da Abdullahi dan Abbas, da Jabir dan Abdullah, da Abdullahi dan Mas'ud, da Huzaifa alyamani, da Abdullahi bn Umar, da anas dan Malik, da amru dan asi, daga tabi’ai akwai Yahaya bn mu’in, da Ahmad dan Hambal, da Tirmizi, da Bazzar, da Dabari, da Hakim, da Baihaki, da ibn Asir, da da nawawi, da ala’ai, da ibn Hajar Askalani, da sakhawi, da Suyudi, da Makki, da sauransu, kuma abin mamaki ga Harrani da dukda ya dogara kan Yahaya bn mu’in da Tirmizi da Hakim a wajan karbar hadisansu, amma sai ga shi sun ruwaito hadisai da dama game da Imam Ali (a.s) amma ya ki karbar wannan daga garesu. Tirmizi ya karfafi wannan hadisi da cewa kyakkyawa ne, amma wajen ‘ya’yan HARRAN da wutar gaba da Alayen Annabi (a.s) ta huru a cikinsu a irin wadannan wurare makauniyar gaba ta rufe musu ido!.
Idan ka kasance kamarsa to ina ganin babu amfani ka ci gaba da muhawara, domin yana cewa ne: Rawafidhawa (yana nufin Shi'a) sun kasa tabbatar da imanin Ali (a.s) da adalcinsa. Ya ci gaba da cewa: idan sun kafa mana hujja da cewa akwai tawaturin zance kan musuluncinsa da hijirarsa da jihadinsa, to ai mu ma muna da tawaturin musuluncin Mu'awiya da Yazid da halifofin Banu Umayya da Banu Abbas da sallarsu da azuminsu da jihadinsu kan kafirai… duba: min hajussunna 2: 62.
A wani waje yana cewa: Sam babu tabbacin kafirai ko munafukai suna kin Ali (a.s) minhajussunna 7: 461. Ya ce: Ali bai muzanta wa wani ba daga cikinsu (kafirai ko munafukai) a jahiliyya ko a musulunci, domin wadanda ya kashe a yaki duka kanana ne ba manyan kafirai ba ne. ya ce: Umar ma ya fi shi gaba da su.
Amma da ya ga dai wanda yake kushewa ya kashe da yawa koda kuwa ya kira su kanana ne, kuma wanda ya yaba bai taba kashe koda daya ba, sai ya ce: Ali an ji ya kashe kafirai da takobinsa amma ba duka ya kashe ba, ya kashe wasu ne daga cikinsu, kuma sahabbai ma kamar Umar da Zubair da Hamza da Mikdad, da Abu Dalha, da Barra, kowa ya kashe kafirai.
Da ya ga babu wani tarihin da ya yi daidai da maganarsa sai ya ce: Umar ya kashe kafirai mana domin shi ma ya yi addu’a Allah ya kashe su, kuma yaki ba sai da takobi ba domin yaki da addu’a kamar yaki da takubi ne! Minhajussuna: 4: 480.
Ka duba ka ga yadda ake mummunan tawili ta krfin tsiya sai an nuna Imam Ali (a.s) bai yi wa musulunci wani abin kirki da ya cancanci yabo ba.
Idan kai ma kamar haka kake, to sai in hutar da alkalamina, idan ka gaya mini matsayinka sai in san da wa nake magana kan Ahlul Bait (a.s) shin da mai gaba da gidan ne, ko kuma mai neman sanin gidan mai neman gaskiya. Ka ga ke nan babu amfani ga wanda ya shata layi, yana ganin mabiyan Ali (a.s) ba zasu iya kawo hujja kwakkwara a kan ma musuluncinsa ba tukun balle a zo maganar jagora ne daga Allah (S.W.T) bayan Annabi (s.a.w)!.
Amma game da cewa; Imam Ali da 'ya'yansa (a.s) ba su nuna wa mutane kabarin Sayyida Fadima ba (a.s) da nuna cin mutunci ne hakan kansu, da nuna cewa; zagi ne garesu hakan da kuma ga Annabi (s.a.w), kai da mayar da magana kan bautar kabari: Ban sani ba shin za a yi wa maganar nan taka dariyar ne ko kuma kuka, Ina ganin idan ka kasa sai ka nemi taimakon malamanka, mene ne ya same ka haka kake cakuda maganganu iri-iri waje daya.
Na daya: Ka jahilci cewa mutum yana iya wasiyya yadda ya so idan zai mutu matukar ba ta saba wa addinin ba. Kuma Fadima dai ‘yar Manzo (s.a.w) da ita da mijinta da ‘ya’yanta, ba ka isa ka nuna masu yadda zasu yi addinin ba, kuma ita ta yi musu wasiyya da boye kabarinta, ko kai ma kana bakin cikin matakin da ta dauka ne!
Na biyu: Me ya kawo bautar kabari, wane musulmi ne ka gani ya riki kabari Ubangijinsa abin bauta?!
Na uku: Ban taba sanin ka yi nesa da sanin tarihin addini ba sosai sai da na ga wannan magana taka, ka sani kabarin Ibrahim (a.s) ba boye yake ba, kuma an je janazarsa kuma an yi masa salla, sannan kabarin yana nan Bakiyya kuma yanzu haka ina da taswirar duk inda kaburburan nan suke a Bakiyya duk da wahabiyawa sun rusa duka kaburburan bayin Allah da yake wajen karni guda da rabi da ya wuce. Haka ma kabarin Sayyida khadija (a.s) ba wanda ya boye shi, domin babu wata hikimar yin hakan sabanin kabarin Sayyida Zahara (a.s). Wannan kage ne ka yi wa Annabi (s.a.w) na cewa ya boye su, kuma wannan kagen idan daga gareka yake to ka yi hattara ka nemi gafara a kai, idan kuwa wani ya gaya maka ka ce da shi ya nuna maka inda ya samu wannan, idan bai yi ba ka sani shi mai karya ne ga fiyayyen halitta!.
Ina ganin ba ka san me kake cewa ba, ka nemi taimakon malamanka ka dakatar da magana, ka sani tanakudinka da warwarar maganarka sun yawaita, ka ce: kaburbura zuwa wajensu bauta ne, kuma ka ce an yarda mu je yanzu, ke nan Allah (S.W.T) da manzonsa (s.a.w) sun yi umarni da bautar kaburbura ke nan! Wal’iyazu billah!.
Amma maganar da kake yi na cewa Fikihu zai iya saba wa ma'aiki kuma ya yi daidai, kana mai nuni da cewa; shi kansa (s.a.w) ya sha ruwa kuma ya ce asha ruwa a lokacin. Sai na ce maka: Tir da fikihun da ya saba wa maganar Annabi, Allah ya tsare mu da shi, kuma wannan fikihun ba musulunci ba ne koda ka kira shi da hakan, kuma ka sani dukkan aikin Annabi (s.a.w) musulunci ne, babu wani abu da Annabi (s.a.w) yake yi da ya fita daga da’irar musulunci.
Sannan kuma shan ruwa idan kana nufin na azumi ne to akwai dalili da ya zo daga Kur’ani mai girma da sunnar Annabi (s.a.w) da zai sanya ka shan ruwa, idan kuma wani abu kake nufi daban to sai ka fada.
Sannan a ina ka samu hujjar maganarka ta cewa duk abin da yake wajen sahihain ba dole ba ne ya zama hujja. Ka sani Buhari da Muslim sun tara hadisai ne masu yawa kuma amma sun takaita da dan kadan daga abin da suka tattara, da wace hujja ne suka san sauran ba daidai ba ne?. ko kuma Allah da Manzo (s.a.w) ne suka yi bayani game da cewa Buhari da Muslim su kadai ne hujja!
Kamar yadda muka fada baya ne: Tara hadisai an fara shi ne; bayan kowa yana da nasa bangare, don haka kowa yana da nasa abin da yake karewa.
Ka rika sanin abin da kake cewa: Ka sani hujja tana cikin biyayya ga Littafin Allah da wasiyyan Annabi (s.a.w) wannan kuma su ne hujja a kan kowa, idan wani ya ki bin su wannan shi ya jiwo wa kansa, wannan kuwa ko musulmin tun lokacin Manzo (s.a.w) ko a yau ko a nan gaba, kamar yadda sauran kafiran duniya duk wannan hujja ne kansu.
Na ga ka kawo wasu ayoyin Kur’ani madaukaki kana maganarsu ba a mahallinsu ba, kuma ka kawo wani hadisi da Manzo (s.a.w) ya gargadi wani sahabi da ya zagi wani sahabin, kamar yadda ya zo cewa Khalid ya zagi Abdurrahman sai Manzo (s.a.w) ya yi masa gargadi: Ban sani ba me kake so ka ce game da su.
Sannan kuma me zaka ce game da la’antar Imam Ali (a.s) shekara tamanin da Mu'awiya ya assasa, kai kana ma iya zuwa farko yayin da Umar bn Khaddabi yake cewa da Abu huraira: Amima Ko Umaima ba ta yo kashinka ba domin ka zama jagoran mutane. Shin kana ganin sahabi ya zagi sahabi ne ko me kake gani, sannan kuma me ye fa’idar tayar da wannan bahasi?! Ina ganin ka rude matuka! Ba ka san me kake son cewa ba, sannan ba ka san me zaka gaya wa waninka ba.
Sannan kuma idan kana ganin hujja a wajenka ba ta da wani matsayi ko kima to sai ka yi addininka da yadda kake gani, domin kai ne abin tambaya kan ayyukanka ba ni ba, kuma a lahira ba ka da wata hujja a kaina kamar yadda kake neman nunawa. Wannan ya rage naka ne ka cigaba da bincike ko ka bari.
Kuma daga karshe ina son yi maka nasiha kan cewa ka daina zargi da cewa; za a zagi kowane irin mutum ne balle ka yi zargin zagin wasiyyan Annabi (a.s) ko annabin (s.a.w) ma kansa, idan ba ka da hujja sai ka yi shiru, domin zargi mummuna ba ya nuna komai sai hali maras kyau.
A natijar wannan bahasin mun cin ma abubuwa kamar haka: Na daya: Ahlul bait (a.s) su ne kadai makoma da Allah (S.W.T) da manzonsa (s.a.w) suka bari tare da Kur’ani mai daraja. Na biyu: Maganar manzon Allah (s.a.w) ita ce hujja, kuma ya yi wasiyya da Ahlul Bait (a.s). Na uku: Ahlul Baiti (a.s) su goma sha biyu ne, kuma Shi'a imamiyya suna biyayya garesu gaba daya a matsayinsu na halifofin Annabi (s.a.w) da Allah ya ayyana masa. Na hudu: Tun farkon zuwan Manzo (s.a.w) ya ambaci kalmar halifa da waziri ga Imam Ali (a.s). Na biyar: Har yanzu ka kasa nuna waye jagoranka da kake biyayya gareshi, ko kuma ma ba ka san shi ba!
Hafiz Muhammad Sa'id
www.hikima.org
hfazah@yahoo.com
Kammala gyarawa
01 /July/ 2009