Muassasar alhasanain (a.s)

Hakkokin Allah2

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

Sakon Hakkoki: Imam Ali Sajjad (a.s) Tarjama da Sharhi: Hafiz Muhammad Sa'id
Ci gaba daga fayel na farko: Malamai sun yi nuni da hanyoyi masu yawa domin tabbatar da samuwar Allah madaukaki wanda zamu iya yin ishara da wasu daga ciki da suka hada da samuwar halitta da kuwa samuwar tsarin da take a kansa, wadanda suke nuni da samuwar mai halitta su da zamu yi nuni da wasu daga ciki.
Imam Sadik (a.s) ya yi nuni da wannan lamarin mai muhimmanci yayin da Disani (shi wani mutum ne da bai yi imani da samuwar Ubangiji ba) ya tambaye shi a wata ruwaya mai tsayi da zamu kawo ta kamar haka:
Daga Ali bn Ibrahim, daga muhamad dan Ishak al'khafifi, ko daga babansa, daga Muhammad dan Ishak ya ce: Abdullahi Disani ya tambayi Hisham dan Hakam sai ya ce masa: Shin kana da Ubangiji? Sai ya ce: haka ne. Ya ce: Shin shi mai iko ne? Ya ce: E, mai iko ne. Sai ya ce: Shin zai iya shiga da duniya dukanta cikin kwai ba tare da ya kirmama kwai ba, ko ya kankanta duniya? Sai Hisham ya ce: Jira ni. Sai ya ce: Zan jira ka shekara.
Sannan sai Hisham ya fita daga wurinsa zuwa ga Abu Abdullahi Imam Ja'afar Sadik (a.s), sai ya nemi izinin shigowa, sai ya yi masa izini. Sai ya ce masa: Ya dan manzon Allah (s.a.w) Abdullahi Disani ya zo mini da wata mas'ala ta babu wani madogara gareta sai dai Allah da kuma kai, sai imam Sadik (a.s) ya ce masa: Me ya tambaye ka. Sai ya ce: Kaza da kaza, sai Abu Abdullahi (a.s) ya ce: Ya Hisham! Mariskanka nawa ne? sai ya ce: Biyar. Sai ya ce: Wanne ne ya fi karanta? Sai ya ce: Mai gani. Sai ya ce masa: Yaya girman mai ganin? Sai ya ce: Kamar girman wake ko kasa da hakan. Sai ya ce masa: Ya kai Hisham! Duba gabanka da samanka kuma ka gaya mini me kake gani? Sai ya ce: Ina ganin sama da kasa, da gidaje, da binaye, da filaye da duwatsu, da koramu. Sai Abu Abdullahi (a.s) ya ce: To wannan da ya sanya kamar gwargwadon kwayar wake ko kasa da ita ta ga haka, yana da ikon ya sanya duniya dukkaninta a cikin kwai ba tare da ya kankanta duniya ba, ko ya girmama kwai. Sai Hisham ya fadi yana sumbuntar hannayensa, da kansa, da kafafunsa. Ya ce: ya ishe ni ya dan manzon Allah (s.a.w), sannan ya koma gidansa.
Wace gari Disani ya zo masa, sai ya ce masa na zo maka mai musulunta ne, ba na zo maka mai neman jawabi ba. Sai Disani ya fita daga wajensa har sai da ya zo kofar gidan imam Sadik (a.s) sannan ya nemi izini, shi kuwa imam (a.s) ya yi masa izini. Yayin da ya zauna a gabansa sai ya ce: Ya kai Ja'afar dan Muhammad (a.s) nuna mini Abin bautata -Ubangijina-? Sai Abu Abdullahi (a.s) ya ce masa: Yaya sunanka? Sai ya fita bai gaya masa sunansa ba. sai abokansa suka ce masa, me ya sanya ka ba ka gaya masa sunanka ba? Sai ya ce: Da na ce masa Abdullah, to da ya ce: Wane ne wannan da kake bawansa. Sai suka ce masa: Koma ka ce ya gaya maka Ubangijinka amma kada ya tambaye ka sunanka? Sai ya koma ya ce: Ya Ja'afar dan Muhammad (a.s) nuna mini ubangijina amma kada ka tambaye ni sunan? Sai Imam Sadik (a.s) ya ce masa: Zauna. Sai ga wani yaronsa karami a hannunsa akwai kwai yana wasa da shi, sai Abu Abdullahi (a.s) ya ce masa: Ba ni kwan nan ya kai yaro, sai ya mika masa. Sai Abu Abdullahi ya ce masa: "Wannan wata katanga ce rufaffiya tana da fata mai kauri, kuma a karshita akwai wata fata siririya, kuma akwai wani ruwan zinare da na azurfa karkashin siririyar fatar, sannan wannan ruwan zinariyar ba ya cakuda da ruwan azurfar, kuma na azurfa ba ya cakuda da na zinare, suna yadda suke, babu wani mai gyara da ya fito daga ciki balle ya bayar da labarin daidaitar su, kuma wani mai barna bai shiga cikin su ba, balle ya bayar da labarin lalacewarsu, ba a sani ba shin an halitta ne don namiji ko mace, yana tsagewa ga misalin Dawisu, shin kana ganin akwai mai shirya hakan?
Ya ce: Sai ya sunkuyar da kai tsawon lokaci, sannan sai ya ce: Na shaida babu ubangiji sai Allah shi kadai ba shi da abokin tarayya gareshi, kuma na shaida cewa Muhammad bawansa ne kuma manzonsa, kuma kai ne imami hujja daga Allah a kan halittarsa, kuma ni na tuba daga abin da nake a kansa .
A wata ruwayar akwai karin cewa: Sai Disani ya ce: Mu ba ma imani sai da abin da muka riska da idonmu, ko ji, ko shaka, ko dandano, ko tabawa. Sai imam Sadik (a.s) ya ce masa: Ka ambaci mariskai, su kuwa ba sa amfanar komai sai da hankali .
Sannan akwai dalilin da yake nuni da cewa dole ne a samu wani wanda dukkan halitta ta tuke zuwa gareshi, wanda babu wani wanda yake samansa, wanda daga gareshi ne dukkan samammu suka gangaro, wannan kuwa shi ne Allah mahalicci.
Don haka babu ma'ana wani ya tambayi cewa waye ya yi ubangiji, domin shi ne karshen wanda samuwa take tukewa zuwa gareshi. A irin wannan ne masu hikima suka kawo wani labari na wani dalibi mai hikima da ya ba wa wani masanin kwayoyin halitta amsa game da samuwar Allah madaukaki kamar haka:
Wannan masanin kwayar halittar ya tambayi dalibin ilimin addini game da cewa: Waye ya yi Ubangiji? -sai wannan dalibin ya ga babu ma'ana wani ya tambayi waye wanda samuwar komai daga gareshi take, don haka- Sai ya amsa masa da cewa wani Ubangiji ne da yake sama da shi. Sai ya ce masa: Waye ya yi wannan Ubangijin? Sai ya ce masa: Wani Ubangijin ne da yake sama da shi kuma. Sai ya sake tambayarsa ta uku, sai ya ba shi wannan amsar. Sai ya ce masa: Dole ne ke nan a samu wani Ubangiji da babu wani samansa, wanda yake sama komai. Sai ya ce masa wannan shi ne Allah ke nan.
Ta haka ne ya iya isar masa da muradinsa, domin kowace rayi tana furuci a cikin zuciyarta da cewa akwai wani wanda shi ne ya yi ta, kuma ya yi komai, kuma shi babu wani rashi da ya gabace shi, domin shi samamme ne tun fil azal .
Don haka da za a sawwala wani ubangiji a tunani bayan Allah madaukaki, da samuwarsa ta kasance daga Allah take, sai ya kasance ke nan bawa ne daga cikin bayin Allah (s.w.t), sai ya kasance ke nan ba ubangijin ba ne, wannan shi ne abin da wannan dalibi ya lurasshe da wancan masanin ilimin halitta.
Sannan akwai wasu hanyoyi uku da malamai suka tafi a kan cewa su ne hanyoyin da ake sanin Allah madaukaki kamar haka:
1- Hanyar Dalilin Fidirar Halitta: Wannan hanyar tana tare da dukkan wani abin halitta, domin nau'in halitta ce da Allah (s.w.t) ya dora kowane mai rayi a kanta. Wannan hanyar tana nuna wa dukkan wani mai hankali cewa idan ya duba kansa zai san ba shi ya samar da kansa ba, kuma ba wani mai kama da shi ne ya samar da shi ba. Don haka ne ba ya ganin babansa ko shugabansa a matsayin wanda ya samar da shi, kamar yadda ba ya ganin wani abin halitta kamarsa ne ya samar da shi. Da wannan ne zai kai ga natijar cewa akwai wani wanda ya samar da shi wanda yake babu wani wanda ya yi shi.
Da irin wannan ne ake yawaita misali kan cewa idan mutum ya ga kashin rakumi sai ya samu yakini cewa da akwai rakumi, idan ya ga sawun tafiya, sai ya tabbatar da cewa akwai wanda ya yi tafiya, kuma idan ya ga wani aiki sai ya samu yakini cewa akwai wanda ya yi wannan aikin.
Daga cikin muhimmancin wannan dalilin shi ne cewar kowane mai hankali zai iya amfana daga gareshi, don haka a nan babu bambanci tsakanin jahili da malami, ko tsakanin babba da karami, ko tsakanin adilin mutum da fasikin mutum.
2- Hanyar dalilin hankali: Wannan hanyar ita ce ta dalilin hankali wacce take iya kai mu ga sakamakon cewa akwai Allah madaukaki ta hanyar kafa hujja da kwakkwaran dalili na hankali da aka fi sani da Burhan. Masu ilimin akida suna amfani da ita domin kafa dalilin samuwar Allah, sai dai sukan bi ta sanin siffofinsa domin su kafa hujjar samuwarsa bayan sun dogara da dalilan addini da suka zo daga wahayi. Su kuwa masu ilimin Falsafa suna kafa hujja da wannan hanya kan samuwar Allah amma ta hanyar lizimtar samuwarsa. Don haka ne wannan hanya ta kebanta da ma'abota nazari da ilimi, masu karfin ikon tunani da kafa hujja ta hankali.
3- Sai dai akwai wata hanyar ta masana Allah (s.w.t) da aka fi sani da Arifai, su ne wadanda suke sanin Allah (s.w.t) ta hanyar tsarkake zukata daga dukkan wata dauda, da kuma yi mata ado da dukkan tsarki. Sai a fitar da dukkan wani sabo daga cikin tunani da aiki, sannan sai a siffantu da dukkan aikin kwarai a cikin tunani da aiki, idan zukata suka tsarkaka sai hasken Allah ya haskaka su da saninsa, sai su kasance kamar gilasai ne da haske yake haskakawa, bayan da can sun kasance kamar bango ne da koda kuwa rana ta haskaka shi amma yana kare shigar hasken cikinta.
Haka nan dalilai suke a bisa matakai hawa-hawa, da akwai dalilin da yake ana bin sanin fararre domin sanin sababinsa, amma mafi daukakar ilimi shi ne a bi hanyar sanin sababi sannan sai a san fararrensa. Don haka ne ma aka tambayi imam Ali (a.s) game da sanin manzon rahama (s.a.w) aka ce masa: Shin kasan Allah ta hanyar Muhammad ne ko kuwa ka san Muhammad ta hanyar sanin Allah ne? Sai ya ce: Na san dai Muhammad ta hanyar sanin Allah ne. (Sharhin Risalatul Hukuk: s; 35).
Domin sanin Allah hakikanin sani muna bukatar taimakon Allah da ludufinsa, sannan kuma ta namu bangaren sai mu yi motsi domin neman saninsa, allah mai tausayi ya yi mana nasa ludufin da hankali da ya ba mu, da kuma shari'a da ya saukar, don haka sai ya rage ga bayinsa su tashi domin kusantar ludufin.
Ludufin Allah (s.w.t) ya hukunta samar da ni'imarsa ga dan Adam domin ya kusantar da shi zuwa ga saninsa da bautarsa, sai ya aiko masa annabawa (a.s) suna masu bin juna, kuma bai bar wata al'umma ba sai da ya aiko mata da sako, sannan sai ya bi annabawan da wasiyyai a kowane zamani, domin dai kada dan Adam ya rasa shiriyar sanin Allah, kuma kada kofar sanin bautarsa ta toshe masa.
Domin dan Adam ya samu kamala yana da tambayoyi masu yawa da suke yawo a tunaninsa wadanda Allah ya ba shi amsarsu kamar haka:
Daga ina muke kuma meye asalinmu? A yanzu inda muke me ye abin yi? Daga nan kuma ina zamu, kuma yaya yake?. Sai kur'ani madaukaki a amsa masa wannan tambayoyi, Allah (s.w.t) bai taba barin duniya babu hujjarsa ba, koda a zahiri kamar lokacin imam Ali (a.s) da sauran wasiyyan manzon Allah (s.a.w), ko kuma boyaye kamar imam Mahadi (a.s).
Annabawa (a.s) sun zo ne domin motsa hankali ya yi tunani da imani da samuwar Allah, da kadaita shi a ibada, da zatinsa, da siffofinsa, da ayyukansa, da yarda da annabawan da ya aiko da riko da sakonnin da suka zo da su. Annabawa ba su ce a bi su ba tare da dalili ba, wannan lamari ne ya sanya Allah yake ba su mu'ujiza da take dalili ce a kan cewa sakon da suke dauke da shi daga gareshi ne, wannan kuwa zai samar da nutsuwa a zukata har mutane su karbi sakon.
Amma hukuncin rassan addini an sanya su bisa biyayya da maslaha ne wacce ba kasafai aka santa ba sai dai a bi umarnin Allah a ciki, don haka ne Allah yake sanya wa kowane Annabi (a.s) wasiyyi da zai yi wa mutane bayanin abin da sakon ya kunsa bayan wafatinsa, kamar yadda annabin rahama (s.a.w) ya yi wasiyya ga wannan al'umma da imam Ali (a.s) da goma sha daya daga zuriyarsa a bayansa.
Matsalolin da wasiyyan Annabi suka fuskanta na kawar da su daga fagen jagorancin al'umma da kisa sun sanya Allah (s.w.t) ya boye na karshensu imam Mahadi (a.s) domin kada a kashe shi, domin ya zo a karshen duniya ya cika ta da adalci bayan an cika ta da zalunci. Shi kuwa imam Mahadi (a.s) kafin ya boyu ya yi wasiyya da riko da malamai na gari. Saboda haka duk wanda ya kai matakin Ijtihadi da daukaka a ilimi sanin hukuncin shari'a a kan sauran mutane, da takawa, da adalci, da kamala, da tsentseni, ya kasance dan halal ne, to ya zama dole ne a bi shi a umarninsa.
Sanin Imamin lokacinmu yana daga cikin hakkokin Allah a kanmu, domin duk wanda ya mutu bai san Imamin zamaninsa ba ya yi mutuwar Jahiliyya , haka nan ya zo a Kur'ani mai girma cewa a Ranar Lahira kowace al'umma za a kira ta tare da imaminta . Wadannan imamai Allah bai bar mu mun zabe su da kanmu ba sai da ya shelanta su ta hannun manzonsa (s.a.w) wanda ya sanar da mu cewa su goma sha biyu ne: Na farkonsu Ali (a.s) na karshensu Mahadi (a.s) wanda yake shi ne imamin wannan zamanin.
Sanin Imami ya hada da bin sa, da koyi da abin da ya bari na wasiyyarsa, da bin koyarwarsa da malaman da suke shiryarwa zuwa ga abin da ya bari, da kin makiyansa . Kuma hatta da salla da azumi da duk wata ibada idan babu mika wuya ga Imami Allah ba ya karba. Manzon tsira (s.a.w) ya ce: "Wanda ya mutu bai san Imaminsa ba ya yi mutuwar Jahiliyya" . Domin zai tashi a Ranar Lahira kamar wanda ya yi zamani kafin a aiko Annabi ba shi da komai da Allah (s.w.t) ya karba daga gare shi.
Littafin Allah ludufi ne nasa ga bayinsa domin su samu wani kundin tsarin rayuwar duniya da lahira, sannan an sanya lada mai yawa da karanta shi da aiki da shi. Kuma yana dauke da dukkan abin da muke bukata a maslahar rayuwar duniya da lahira.
Karanta littafin Allah da saninsa suna daga cikin hakkokinsa a kanmu, amma sanin littafin ba yana nufin mu san sunansa ba kawai domin hakan ko kadan ba shi da wata ma'ana, amma abin nufi shi ne ya zama mun siffantu da Kur'anin a aikace. Idan ba haka ba a ranar lahira akwai kara da zai shigar a kotun Allah wacce ba a zalunci a nan kuma ba a iya boye gaskiya.
Kuma a bi shi kamar yadda Manzo da wasiyyansa goma sha biyu daga Alayensa suka fassara domin su ne ya ce: "Idan an yi riko da su ba za a taba bata ba har abada". Kuma: "Da Su da Littafin Allah ba sa rabuwa har sai sun riske shi a tafki" .
Haka nan al'amarin yake a matsayin al'umma, dole ne Littafin Allah ya yi iko da rayuwarmu a matsayin al'umma, in ba haka ba, ba mu sauke nauyin da yake kanmu ba. Kuma idan ba mu siffantu da shi ba, to yana da hakkin karar cewa musulmi sun bijire masa.
Sannan masu tafsirin Kur'ani su sani cewa kowace kalma a cikinsa tana da ma'ana, kuma manzon Allah (s.a.w) ya yi bayanin ta, don haka yana da hadari su fassara Kur'ani da ma'anar kalmomin lugga kawai. Ya hau kan dukkan mafassarin Kur'ani ya duba abin da manzon rahama (s.a.w) ya ayyana game da manufar kowace aya ba kawai ma'anarta ta lugga ba.
Manzon Allah (s.a.w) ya bayyana wadanda ake nufi da Ahlul-baiti da cewa su ne Ali, Zahara, Hasan, Husain , ya bayyana wadanda ake nufi da al'umma a fadin Allah madaukaki kun kasance mafificiyar al'umma da aka fitar wa mutane da ma'anar wasiyyoyinsa . Kuma kowace aya sai da manzon Allah (s.a.w) ya nuna wadanda ake nufi da ita domin kada al'ummarsa ta halaka da fassara shi da ra'ayinta. Don haka ne ya zo cewa; Masu fassara kur'ani da ra'ayinsu, su tanadi mazauninsu a wuta.
Addinin Musulunci ludufi ne na Allah ga bayinsa da ya aiko da shi domin tsara rayuwar dan Adam, kuma wannan addini yana da hakkin kare shi a kan kowane musulmi da bakinsa da basirar da Allah ya ba shi, da wajabcin saninsa da taimakawa wajan yada shi a aikace , da kokarin hada kan mabiyansa, da raddi cikin hikima ga masu gaba da shi, da girmama fahimtar ma'abotansa don ba ka sani ba ta yiwu shi mai waccan fahimtar da ta saba da taka shi ne yake a kan daidai.
Kada mutumin da bai fahimta ba ko bai sani ba ya tsoma baki da jayayya a kan mas'alolin Addini wannan na malamai ne. Shari'a ta hana jayayya da jahilci, don haka kada malami ya sa mutane cikin rikicin Addini, haka ma maras Ilimi kada ya sanya kansa cikin rikicin Addini, bayyana ra'ayi kan mas'aloli abu ne na malamai, kamar dai lamarin likitanci ne da babu mai shiga sai likita.
Sannan Imam (a.s) ya yi nuni da cewar idan muka san hakkin Allah madaukaki, muka yi biyayya gareshi babu shirka, to ya yi mana alkawarin gyara mana lamurran duniya da lahira, sannan ya kiyaye mana abin da muke so a cikinsu. Wane alheri da ni'ima ne ya fi wannan a cikin samuwar dan Adam gaba daya.
Cibiyar Al'adun Musulunci
www.hikima.org
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Tuesday, May 18, 2010

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)