Muhammadu Manzon Allah
- An yada a
-
- Mawallafi:
- NURA IBRAHIM KHALIL, ZARIYA. G.S.M 0803 371 8219/0818 444 2461
An ambaci wannan suna (Muhammad) mai albarka sau hudu a cikin Alkur’ani mai girma. Sannan an ambace shi da wasu sunaye da siffofi irin su Daha, da Yasin, da Nuun, da al-Muzammil, da al-Mudathir, da al-Bashir, da an-Nazeer da wasun wadannan.
Danganensa
Shi ne Abul-Kasimi, Muhammadu dan Abdullahi, dan Abdul-Mudallibi, dan Shaibatul-Hamd, dan Hashim, dan Abudu Manaf, dan Kusayyu, dan Kilab, dan Murrata, dan Ka’ab, dan Lu’ayyu, dan Galib, dan Fihir, dan Malik, dan Nadhar, dan Khazimata, dan Madrakatu, dan Ilyas, dan Madhar, dan Nazar, dan Ma’ad, dan Adnan. Wannan shi ne gwargwadon inda aka dace a kan nasabarsa ta wajen mahaifi, abin da ya wuce wannan haddi kuwa ana da sabani a kai; illa dai tabbas ne cewa nasabar Adnan na karewa ne da Annabi Isma’il dan Annabi Ibrahim (AS). Har ma riwaya ta zo (ta hanyoyinmu) cewa shi (SAWA) ya ce: “Idan danganena ya kare da Adnan ku kame.”[1]
Mahaifyarsa kuwa ita ce: Aminatu ‘yar Saidi Bani Zuhrah (wanda shi ne) Wahbu dan Abdu-manaf, dan Zaharata, dan Kilab, wanda aka ambata cikin cikin jerin kakanninsa wadanda kuma suka kare da Annabi Ibrahim (AS). Kenan mahaifiyarsa ta hada dangi da mahaifinsa ta wajen kakansu Kilab dan Marrata.
Haihuwarsa (SAWA)
Akwai sabani tsakanin Musulmi game da ranar haihuwar Annabi (SAWA), wasu sun tafi a kan cewa ranar 17 ga watan Rabi’ul-Awwal ne (wannan shi ne abin da ya shahara ta riwayoyin Ahlulbaiti (AS)). Yayin da wasu duka tafi a kan cewa ranar 12 ne ga wannan wata na Rabi’ul-Awwal (wannan shi ne abin da ya shahara ta riwayoyin Ahlussunna).[2] Ko ta halin kaka dai, an haife shi (SAWA) bayan alfijirin wata rana daga cikin watan na Rabi’ul-Awwal, kuma an hafe shi maraya, a sasan da ake kira da Shi’ibu Abi Dalib dake wani gida da aka fi sani da Gidan Muhammad dan Yusuf dake garin Makka (Wahabiyawa sun rushe wannan gida a halin yanzu).
Abin da ya shahara a tarihi shi ne cewa bayan haihuwarsa da dan lokaci kadan sai aka bayar da shi shayarwa! Kai wasu riwayoyi ma sun nuna cewa mahaifiyarsa ba ta shayar da shi ba sai na kwanaki biyu ko uku kawai!! Daga nan sai Suwaiba, kuyangar Abu Lahabi, ta shayar da shi[3]; daga nan kuma sai wata mata mai daraja da ake kira da Halimatus-Sa’adiyya ta zo birnin Makka tare da wasu abokan tafiyarta don neman jariran da za su shayar don samun abin kalaci da haka. Da cewa Halimah da farko ba ta karbe shi ba da ta ji cewa maraya ne, amma da ba ta sami waninsa ba sai ta dawo ta amshe shi, da wannan ta ga alhairai da albarkatu masu yawa.
Wannan shi ne takaitaccen abin da ya shahara game da shayar da shi (SAWA), abin da babu littafin tarhin Annabi da ke rasa shi, sawa’un na Ahlussunna ne ko na Shi’a. Sai dai wasu malaman mu sun yi raddi a kan wasu sassa na wannan bangare, kamar yadda Aribeli ya yi bayani[4]; kai! wasu daga masu bin diddigi ma sun yi inkarin kissar shayarwar daga tushenta, kamar yadda malami mai bin diddigi, Sayyid Ja’afar Murtala al-Amili ya yi cikakken bayani[5]
Bayan ya cika shekaru shida da haihuwa ne mahaifiyarsa Amina ta dauke shi zuwa Madina don su ziyarci kabarin mahaifinsa. Suna dawowa sai ciwon ajali ya kamata a hanya, sai ta rasu a wani wuri da ake kira da suna al-Abwa’. Annabi ya yi matukar bakin ciki da rabuwa da mahaifiyarsa, ya kuma yi kuka mai tsananin gaske.
Bayan rasuwar mahaifiyarsa sai kakansa Abdul Mudallabi ya dauki nauyin rike shi. Abdul Mudallabi ya kasance kamilin dattijo, wanda ya siffantu da dukkan siffofin madalla, wannan ya sa shi ya cancanci shugabanci, don haka ya kasance shugaban Kuraishawa. Ya kasance yana bin addinin kakansa Annabi Ibrahim (AS) tare da daukacin iyalansa.
Bayan Annabi (SAWA) ya cika shekaru takwas da haihuwa sai Allah Ya yiwa kakansa Abdul Mudallabi rasuwa. Daga nan sai baffansa Abu Dalib ya dauki dawainiyar rikonsa bisa horon mahaifinsa Abdul Mudallabi. Yayin da ya kai munzilin koyon sana’a sai ya shiga koya masa kasuwanci.
Bayan ya cika shekaru ashirin da biyar da haihuwa, sai Allah Ya hada shi da wata kamilar mace, wadda Allah Ya hada mata kyawayan dabi’u da dukiya, ana kiranta da suna Khadijah bint Khuwailid. Irin yadda labarin gaskiya da rikon amanar Annabi (SAWA) ya yadu a ko’ina ne ya kai har kunnenta. Sai ta bukaci da su hada gwiwar yin kasuwanci tare. Annabi kuwa ya yarda, bayan dan lokaci kadan sai wannan hulda ta yi albarka, a karshe ta haifar da yin aurensu, a lokacin yana da shekaru ashirin da biyar, ita kuma tana da shekaru ashirin da bakwai*
Hakika wannan aure ya kasance abin koyi ta fuskokin da yawa, inda a cikinsa matar da mijin suka kasance sassa biyu masu karfafa juna da taimakekeniya; kauna da tausayin juna suka kasance tubalin da rayuwarsa ta ginu a kai. Wannan ya sa Annabi (SAWA) bai yi tunanin auren wata mace a tare da ita ba, duk da tayin da aka yi ta yi gare shi kuwa. Wane aure zai yi tunanin yi kuwa alhali yana da mace irin Khadijah? Wadda ta riga ta toshe kowace kafa da kywawan halayenta da imaninta.
Bayan kimanin shekaru ashirin da hudu da yin aurensa da Khadijah, sai Allah Ya yi mata rasuwa bayan ta sadukar da dukkan dukiyarta a kan hanyar Allah.
Abin da ya shahara shi ne cewa Khadija ta rasu ta bar ’ya’ya Shida, amma nazari na tabbatar da sabanin haka, inda tabbacin ’ya’ya biyar ya inganta, sauran kuwa suna nan a fagen kila-wa-kala.*
Halayen Annabi Kafin Aiko Shi
An shaidi Annabi (SAWA) da adalci, da gaskiya, da rikon amana, da kwazo, da rashin kasala, da tsari a rayuwa, da iya gudanar da abubuwa, da saukin kai da sauran wadannan; ta yadda ba shi da abokin kwatantawa a wadannan dabi’u. Wannan ya sa duk mutanen Makka na sauraronsa, suna komawa gare shi cikin sabaninsu, kuma suna amincewa da duk abin da ya hukunta ba tare da jayayya ba. Kamar yadda suka kasance suna bayar da ajiyar kadarori da dukiyoyinsu a hannunsa.
Ya Zama Annabi
Bayan ya cika shekaru arba’in da haihuwa sai Allah Ya yi masa wahayin farko. Wannan ne ya sanar da abin da aka dade ana ganin alamu daga gare shi, wato cewa Allah Ya zabe shi a matsayin AnnabinSa na karshe zuwa ga duniya baki daya. Saukan wahayin farko gare shi ya kasance ne a ranar 27 ga watan Rajab mai alfarma. ’Yan Shi’a na matukar girmama wannan rana, inda suka sanya ta cikin jerin manyan ranakun da suke rayawa da murna don nuna godiya ga Allah Madaukaki.
A lokacin saukar wahayin farko Imam Ali na wajen. Yana ganin Annabi a lokacin da ya ke karbar wahayi; kuma shi ne farkon wanda ya fara ba da gaskiya da sakon Musulunci a maza, Khadijah kuma a mata; wannan wata daraja ce da Allah Ya kebance su da ita, ba wata kumbiya-kumbiyar tarihi da neman kutso da wasu wannan sahun da zai iya canza ta!
Duniya gaba dayanta ta kasance cikin wani yanayi na duhun jahilci da wata irin rayuwa ta dabbanci, da rashin kan-gado, rayuwar da ba ta kunshi komai ba sai jahilci, da fadace-fadace, da sakarci; mai karfi na danne mai rauni; tatsar jinin juna, da sabawa ingantaccen tafarkin rayuwa suka zama rowan-dare. Wannan ne ma ya sa akewa wannan zamani lakabi da zamanin Jahiliyya.* Tsibirin Larabawa ba a cewa komai a wannan lokacin! domin duhun jahilci ya kai su da har suna bautawa gumakan da suka sassaka da hannuwansu. Su na cin mushe, su sha giya su yi ta hauka. Da kan gaji matar ubansa idan ya mutu, koda kuwa uwarsa ce. Kamar sauran kabilun duniya, ba sa ba mace wata kima; kai! na su jahilcin ma har ya kai su ga suna bisne ’ya’ya mata da ransu bisa wani dalili da ya fi ta’asar ban haushi.
A wannan hali ne duniya da tsibirin Larabawa suka kasance har Allah ya aiko da Annabi (SAWA) a matsayin haske da rahama ga duniya baki daya. Sai dai babban abin takaicin da suka aikata shi ne irin adawa da suka nuna ga sakon Musulunci da matsanancin cutar da Manzo (SAWA) da suka yi. Bai tambaye su wani lada kan abin yake kiran su akai ba. Bai dora musu wani nauyi ba, illa kawai su bar wadancan miyagun dabi’u dake harde rayuwarsu da hana su ci-gaba. Hakika Kuraishawa sun cutar da Manzo (SAWA) matuka; in banda baffansa Abu Dalib da ya kasance yana ba shi kariya.
Zuwa Isra’i
Bayan shekaru takwas da aiko shi ne Allah Ya yi Isr’ai da shi, wato tafiyar nan ta dare daya daga Makka zuwa Kudus, daga can kuma zuwa Sama, inda ya shaida ayoyin Allah masu yawan gaske. Wannan Isra’i ya kasance da ruhi da jikin Annabi, kuma yana farke ba cikin barci ba, kuma yana sane ba rafkane ba. Daga Kudus din ne ma aka ba shi wannan sallar da mu ke yi a halin yanzu. Nassosin tarihi sun ce daga lokacin ne aka fara kiran wannan wajen da Masallacin Kudus.*
Shekarar Bakin-Ciki
Bayan shekaru goma da aiko shi kofar matsaloli ta kara budewa ga Annabi da sauran Musulmi ’yan tsiraru a lokacin; yayin da Khadijah bint Khuwailid ta rasu kenan. Kwanaki uku kacal da wannan sai Abu Dalib ma ya rasu. Habawa! Ai Mushrikai sai suka daura sabon damara da yaki da Musulumci da Manzo (SAWA).
Manzo ya yi matukar bakin ciki da rasuwar wadannan gwarazan Musulunci biyu, wanda wannan ya sa ya sawa wannan shekara suna Shekarar Bakin-ciki. Na farko dai duk sun kasance sassan rayuwarsa, kuma sassa masu tasiri cikin aikinsa na isar da Sakon Allah. Rasuwarsu na nufin cewa Musulunci ya shiga wani sabon mayuyacin yanayi kenan[6].
Abu Dalib ya rasu yana mai imani da Annabi (SAWA), har ma ya sha wasu wahalhalu saboda musuluntarsa; sabanini abin da wasu marubta tarihi ke kokarin nunawa na cewa bai musulunta ba.
Hijira Zuwa Habasha
Ganin shiga tsananin da sabuwar al’ummar Musulmi ta yi daga bangare mushrikan Makka bayan rasuwar Abu Dalib, ya sa Annabi ya hori wasu Musulmi da yin hijra zuwa Habasha garin sarki Najjashi, wanda ba a zaluntar wani a gabansa.* Wannan hijra ta kasance karkashin ja-gorancin Ja’afar dan Abu Dalib.
Duk da kokarin da Mushrikan Makka suka yi na kokarin shiga tsakanin sarki Najjashi da Musulmi, amma abin ya ci tura; domin bayan sarkin ya yi musu tambayoyi, kuma Ja’afar ya ba shi amsa a kan abin da ya hada su da mutanensu, da irin abin da sakonsu ya kunsa, sai ya amince ya ba su mafaka, kuma ya kori wakilan da kafiran Kuraishawa suka turo da kyautar da suka kawowa sarki don kwadaitar da shi a kan kin karbar Musulmi. Sai suka koma suna wulakantattu masu hasara. Najjashi dai ya sanar da Musuluncinsa daga baya, shi da mutanen kasarsa gaba daya.
Hijra Zuwa Madina
Bayan cika sheru goma sha uku da aiko shi sai ya yi hijra zuwa Yathrib bisa horon Allah; saboda wani shiri da mutanen Makka suka shirya na kashe shi. Allah Ya tserar da shi ta hanyar sadaukar da kai da Imam Ali (AS) ya yi, ya kwana a kan gadonsa don dauke hankalin wadanda ke labe suna jiran duhu ya shiga don aiwatar da mummunan nufinsu. Sai Manzo (SAWA) ya fita ba tare da sun gan shi ba, ya kama hanyar Madina shi da Abokinsa Abubakar da wani yaronsa dake yi musu hidima a hanya. Bayan dawainiya da wahalhalu masu yawa sai Allah Ya sa suka isa wani wuri da ake kira Kubah dake ’yan mila-milai kadan daga Yathrib, a nan Manzo ya yi zango ya jira har sai da Imam Ali (AS) ya iso tare da Fatima mahaifiyarsa, da Fatima ’yar Manzon Allah, da wasu Musulmi marasa karfi. Daga nan suka dunguma suka shiga Madina baki daya. Al’ummar Yathrib, wadanda suka cimma yarjejeniya da Annabi tun tuni kan cewa ya yi hijra zuwa gare su, sun yi matukar maraba da zuwan Annabi (SAWA).
Hijira zuwa Yathrib, wadda saboda hijrar Annabi aka canza mata suna zuwa Madinatun-Nabi, ta bude wani shafi mai mahimmanci a tarihinmu na Musulunci; domin a nan ne Manzo (SAWA) ya kafa gwamnatin Musulunci ta farko da zata nunuwa duniya irin karfin da Musulunci ke da shi wajen iya tafiyar da rayuwar mutane. Ikon da Musulunci ke da shi ta fuskokin siyasa, da tattalin arziki, da tsarin zamantakewa, da diplomasiyya da aikin soji sun bayyana a shekaru goma da Manzon Allah (SAWA) ya yi a rayuwar Madina; wadanda ke kunshe da yakoki, da yarjeniyoyi, da shari’anta hukunce hukuncen dukiya, da haddodi, da kisasi, da tsarin tsaron kasa da sauran su.
Wani abu mai mahimmanci da ba zai kufce mana ba a nan shi ne cewa: Wannan bangare na tarihin Musulunci na kunshe da abubuwa masu ban sha’awa da kowane Musulmi ke alfahari da su. Musulmi sun nuna bajinta matuka da sadaukar da kai. Musulmin Makka (Muhajirun) sun baro dukiyoyinsu, da danginsu, da kasarsu da sana’o’insu; ba don komai ba sai don su tsira da addininsu. Su kuma mutanen Madina (Ansar) sun nuna dattaku da halin ya kamata, yayin da suka karbi baki masu yawa ba tare da nuna kyashi ba, suka raba dukiyoyinsu da gidajensu tare, wasu suka saki matansu masu kyawawan halaye don bakinsu su aura su sami kwanciyar hankail da natsuwa a sabon yanayin da suka sami kansu a ciki. Kai! babu wata al’umma a tarihi da ta taba gabatar da irin wannan bajinta; kuma babu wani shugaba da iya sana’anta al’umma mai irin wannan hali in ba Muhammadu dan Abdullahi ba. Allah Ya saka masa da alheri, Ya kuma kara masa tsira da aminci. AlKur’ani, a cikin wasu ayoyinsa, ya yabi wannan bajinta yadda ya kamata, don wannan ya zama jinjinawa daga gare shi da kwadaitarwa ga masu zuwa da dabi’antuwa da irin wannan dabi’a.
Malaman Shi’a na yabon wannan bajinta ta Muhajirun da Ansar, suna tinkaho da ita a duk lokacin da suke bayani a wannan fagen, suna kwadaitar da mutane da yin koyi da haka. Kai! A aikace ma yau babu masu dabi’antuwa da wannan dabi’a kamar su; ga su nan saboda takura musu da ake yi a kasashensu suna hijra zuwa inda duk za su sami sassauci, kuma ’yan’uwansu na wadancan garuruwa na kwatanta abin da Ansar din farko suka yi. Wannan wata karyatawa ce ga abin da wasu suka takarkare suna yadawa, na cewa ’yan Shi’a ba su da aiki sai zagin Sahabbai, magana a kan haka na zuwa a mahallinsa in Allah Ya yarda.
Mu’ujizozin Annabi
Mu’ujiza wata tagazawa ce daga Allah Madaukaki ga bayinSa, don su sami saukin fahimtar gaskiyar Annabi su bi shi. Ba kwalliya ba ce ga Annabi kamar yadda wasu ke dauka, rashin ta a kowane lokaci kuma ba gazawa ba ne, kamar yadda wasu limaman Kirista ke nunawa.
Mu’ujiza ita ce duk abin da zai bayyana a hannun wani Annabi a lokacin da ya yi ikrarin Annabta. Dole ta fi karfin tunani mutane da iyawarsu, tana da ban mamaki kuma ba mai iya zuwa da irin ta. Tana bayyana ne kawai a wasu lokuta da ake bukatar bayyanar ta wajen tabbatar da wani abu ga wasu ko kore wata barna da aka jarabci wasu da ita. Mu’ujizar kowane Annabi na dacewa da abin da ya shahara a zamaninsa ne a galibi.
To Annabinmu Muhammadu ma ba abar shi a baya ba a wannan, yana da Mu’ujizozin da suka ma ketare na Annabawan da suka gabace shi. Wasu daga Mu’ujizozinsa sun hada da:
1. AlKur’ani: Mu’ujizancin AlKur’ani ya wuce Mu’ujizar kowane Annabi. Da wata maganar muna iya cewa, babu Annabin da ya zo da Mu’ujizar da ta kama hanyar AlKur’ani. Mu’ujizar AlKur’ani ta hadu ne a jerin ayoyinsa, zabin kalmomi da haruffansa da irin tarin ma’anoninsa. Shi ba waka ko wake ba, amma in ana karanta shi yana ratsa jiki fiye da yadda duk wata waka ke ratsa jikin mai son ta. Shi ba rubuntun zube ba ne, amma baya ginsarwa kamar sauran littaffai. Tun saukarsa ya kalubalanci masu ja da shi da su zo da koda sura daya karama [kamar surar Tawhid ko Takwir] amma suka kasa. Dalilin kashin su kuwa shi ne yadda suka koma suka zabi yakarsa da takobi maimakon harshe, alhali a da can –kafin zuwansa- sun kasance masu takama da hikima da iya tsara magana. Har yau kuma Musulmi na nan a kan wannan kalubale, suna cewa: ‘Idan akwai wanda ya iya kawo mana irin AlKur’ani muna shirye mu bar addninmu.’ Amma muna sane da cewa babu wanda zai iya haka, in kuma mutum zai kwatanta ga fili nan ga mai doki.
2. Saukin Haihuwa: Mahaifiyar Manzo (SAWA) bata sha wahala wajen daukar cikinsa da haihuwarsa ba. Ta kuma haife shi ita kadai, kuma cikin saukin da ba a saba ganin irinsa ba.
3. Lokacin haihuwarsa an shaida wani haske da ya rika fitowa daga dakin.
4. Ana haihuwarsa katangun fadar Kisra (sarkin babban daular Roma mai karfi) ta wargaje; alhali a da sun kasance masu karfin da ba a suranta abin da zai iya rushe su cikin sauki.
5. Tun yana karaminsa girgije ke masa inuwa a wasu lokutan tsananin rana, yana kuma binsa duk inda ya tafi.
6. Ya kasance yana gani ta baya kamar yadda ya ke gani ta gaba.
7. Ya kasance yana ji idan yana barci kamar yadda ya ke ji idan yana farke.
8. Ya kasance yana magana da dabbobi da harshen su.
9. Akwai hatimi (stamp) na cikan Annabci a kafadarsa, wanda aka rubuta kalmar Shahada a kai.
10. A kan ji tasbihin tsakuwa daga tafin hannusa.[7]
11. Ruwa na bubbbugowa daga tsakanin ’yan yatsun hannunsa.
12. Ya bayar da labaran abubuwa kafin su faru, kuma sun zo ba tare da sabani da yadda ya fada ba.
Wannan kadan kenan daga Mu’ujizozinsa (SAWA) wadanda wasu malamai sun kididdigo har 4,440.[8]
Sai dai ya zama dole a nan mu yi ishara da wata ‘yar fadakarwa mai mahimmancin gaske dandagane da mu’ujizar Annabawa (AS). Ya kamata a lura da cewa Annabawa ba su dogara da mu’ujiza a koda yaushe. Ba sa aiki da ita sai a lokutan da bukatar haka ta taso. Bikatuwar haka kan tashi ne kuwa yayin da da’awarsu ke fuskantar barazanar kawo rudu ga gama-garin mutane daga masu kawo rudani. Da wani zance muna iya cewa: irin nau’in mutanen da Annabawa (AS) kan fuskanta yayin kiransu nau’i biyu ne; akwai wadanda hujjoji da dalilai kan wadace su a ko wane irin yanayi, irin wadannan na iya zama su yi nazari da amfani da hankulansu a duk lokacin da aka so wasa da hankulansu ko jefa su cikin rudani. Sai kuma wadanda suke sabanin wadancan, su saboda tsaurin tunaninsu, suna iya fadawa cikin rudu cikin sauki, don haka suna bukatar tantancewa ko “gani-da-ido” na kowane abu. To Annabawa na gabatarwa kowane bangare da abin da zai taimaka masa wajen fahimta da gane sakon Allah Madaukaki, wannan kuwa cikan tausayin Allah ne.
Wani abu karkashin wannan kuma shi ne al’amarin masu neman kawo cikas wajen isar da sakon Annabawa ta hanyar yin amfani da sihiri ko wata harkalla da dabaru, a irin nan ma Annabawa na amfani da mu’ujiza don tonawa irin wadancan asiri, da kunyata su da nuna karyarsu kowa ya gani.
Matan Annabi (SAWA)
Annabi ya auri matan da adadinsu ya kai tara ko goma sha uku (a wasu riwayoyin). Mafificiyarsu ita ce Khadijah al-Kubra, uwar dukkan ’ya’yansa in banda Ibrahim, wanda Mariya ta Haifa. Babu wanda Allah Ya halattawa auren wannan adadin na mata sai shi. An halatta masa ne kuwa saboda wadansu maslahohi da amfaninsu ke komawa ga Musulunci; sabanin yadda masu sukar Musulunci ke kokarin nunawa na zargin son mata da sauran surkullensu.
Hakika malamai daga dukkan bangarorin Musulmi na Shi’a da Ahlussunna sun yi kyawawan bayanai game da wannan mas’ala, sun kuma yi rubuce-rubuce da harsuna dabam daban a kan wannan. Allah Ya saka musu da alheri.
’Yan Shi’a na mutunta matan Annabi (SAWA) saboda darajar zama da shi. Suna kara girmamawa ga wadanda suka dake, kuma suka ci-gaba a kan abin da Annabi ya dora su a kai na taribiyya da kamun kai, a lokacin rayuwrsa da bayan rasuwarsa. Sai dai ba sa ganin zama matar Annabi na nufin kariya daga laifi ko aminta daga kaucewa hanya da bata.
’Ya’yan Annabi (SAWA)
Bin diddigin tarihi na tabbatar da cewa Annabi na da ’ya’ya biyar kamar haka:
1. Kasim: A kan kira shi da Tahir. Shi ne babban dansa kuma ya rasu arayuwar Makkah. Da shi akewa Annabi lakabi da Abul-Kasim. Khadijah ce ta haife shi.
2. Abdullahi: Shi ma ya rasu a rayuwar Makka, Khadijah ce ta haife shi.
3. Ibrahim: An haife shi a Madina, bayan hijra, ya rasu yana karami, mahaifiyarsa ita ce Mariya al-Kibdiyyah.
4. Zainab: An haife ta a rayuwar Makka, kuma ta rasu tana karama a rayuwar Makka din dai. Khadiha ce ta haife ta.
5. Fatima: An haife ta a rayuwar Makka. Ita Allah ya zaba don yada tsatson Annabi. Khadijah ce ta haife ta.
Amma an riwaito cewa ’ya’ya bakwai ke gare shi da karin: Rukayya da Ummu Kulthum. Sai dai wannan ba tabbatacce ba ne ta fuskar nazarin tarihi da kyau.[9]
Rasuwar Annabi (SAWA)
Lokacin da ciwon ajali ya kama shi, ya yi wa Imam Ali (A) wasici da cewa idan ya cika ya yi masa wanka shi kadai. Ya tabbatar masa da cewa Mala’iku za su taimaka masa. Ya kuma yi wasici da cewa idan ya cika a rufe shi a dakin da ya cika (wato dakinsa), kuma a yi masa likkafani da suturu uku. Daga nan sai aka ga ya kai bakinsa kunnen Imam (AS) ya yi masa wata doguwar magana da babu wanda ya ji, alamu dai sun nuna cewa tana da matukar muhimmanci, domin an ga fuskar Imam ta canza kuma zufa na karyo masa.
Yayin da lokacin sallah ya yi, Bilal ya kira sallah, sai Annabi ya bukaci Imam Ali (AS) da baffansa Abbas dan Abdul-Mudallibi da su rike kafadunsa su kai shi masallaci. Bayan ya ja-goranci jama’a sallah sai ya yi musu hudubar karshe, wadda a cikin ta ya jaddada musu wasu daga wasiyyoyin da ya yi musu tun tuni; ya kuma kara karfafa wasiyyarsa a kan riko da nauyayen nan biyu da ba a bata matukar an yi riko da su; wato Littafin Allah da Ahlulbaiti (AS). Yayin da Musulmi suka ga halin da ya ke ciki duk sai suka rude da kuka, suna kururuwa sun fadar Inna Lillah Wa Inna Ilaihi Raji’un.
Bayan ya gama hudubarsa, sai Imam Ali (AS) da Abbas (RA) suka kama shi suka shiga da shi gida ya ci gaba da jinya, har lokacin da Allah Madaukaki Ya karbi ransa a bayan sallar la’asariyar ranar litinin, 17 ga watan Safar, shekaru goma cur bayan hijirarsa. Amincin Allah Ya tabbata gare shi a duk fadin rayuwarsa da bayan mutuwarsa.
Bayan rasuwar Manzo (SAWA), sai Imam Ali (AS) ya yi masa wanka, kamar yadda ya yi wasici, sannan a daren talata da laraba aka yi ta masa sallah. Imam Ali da zuriyyarsa da wasu Sahabbai (irin su Salman, da Abu Zar da Ammar) ne suka fara yi masa salla, daga baya sai sauran Musulmi suka rika shiga jama’a bayan jama’a suna yi masa sallah har suka kare.
Sai dai kuma wani abin takaici shi ne, mafi yawan Musulmin wannan lokacin ba su sami daman halartar bisne shi ba saboda shagaltuwa da suka yi da rikicin Khalifanci da mulki.
--------------------------------------------------------------------------------
[1] Za a iya samun wannan riwaya a cikin littafin Kashful-Gummah, na Arbili, juz’i na 1, shafi na 15; kamar yadda Allama Ja’afar Murtadha al-أmili ya fitar a shafi na 63, juz’i na 2 na littafinsa al-Sahih min Siratin-Nabiyyil-A’azam; bugun Darus-Sirah
[2] A kokarin da suka nace a kai na hadin kan Musulmi, masamman tsakanin Shi’a da Ahlussuna, malaman Shi’a, bisa tsarin Imam Khumaini (RA), sun fitar da shirin shagaltuwar Musulmi da tattuna matsalolinsu da hanyoyin magance su a kwanakin dake tsakanin 12 zuwa 17 ga watan Rabi’ul Awwal na kowace shekara. Suka yiwa makon da ranakun suka fada cikinsa suna da makon hadin kai. Ya zama hakki a kan malaman Musulmi da shugabanninsu da su himmatu da raya wannan ingantaccen shiri da duk iyawarsu, wajen kusantar juna da kulla zumunci tsakanin juna, tare da yiwa juna uzuri da afuwa kan abubuwan da aka saba. Kamar yadda ya zama wajibi ga al’ummar Musulmi da su godewa Imam Khumaini bisa wannan dogon hange na shi.
[3]An fitar da wannan a littafin Kamusur-Rijal na Balaziri, wajen tarihin Suwaiba, juz’i na 10, shafi na 427.
[4]A cikin Kasaful-Gummah, juz’i na 1, shafi na 16.
[5] A cikin littafinsa na tarihin Annabi mai tarin kima, wato al-Sahih Min Siratir-Rasulil-Akram, juz’i na 2, shafi na 68, bugun Darus-Sirah dake Lebanon.
* Wannan shi ne abin da nazarin tarhi da bin diddigi ya tabbatar. Abin da ya shahara na cewa ya aure ta a lokacin tana da shekaru arba’in ya sabawa abin da shi, da kansa, ya karantar da Musulmi na mustahabbancin saurayi ya auri budurwa. Manzo kuwa bai kasance yana aikata abin da zai zo ya karhanta shi daga baya ba. Kara da cewa tarihi ya tabbatar da cewa ita ce ta haifi dukkan ’ya’yan Annabi banda Ibrahim; a ilmance kuwa zai yi wuya tsohuwa mai irin wadancan shekarun ta haifi irin wadannan ’ya’yan cikin shekaru goma sha uku kacal. Ga kuma wata riwaya ta Ibin Abbas dake karyata wancan zance, take kuma tabbatar da abin da muke fada (Duba littafin al-Fatima wal-Fadimiyyun, na Abbas al-Akkad don karin bayani).
* Biyun da tarihi ya kasa tabbatar da ingancin samuwarsu su ne Rukayya da Zainab, wadanda aka ce ’ya’yan Abu Lahabi biyu (Abdullahi da Ubaidullahi) sun aure su a lokacin Jahiliyya, bayan zuwan Musulunci (wai) sai aka raba su Usman ya aure su daya bayan daya ta rasu a hannun shi. Wa ya sani, ko wannan na cikin abin da aka kirkira don samun wata daraja ga Usman, ko don wani abin daban. Uhum! dama haka tarihin na mu ya ke gunin takaici!!
* Idan mutumin yau na so ya fahimci mummunan yanayin da duniya ta kasance kafin aiko Annabi (SAWA), sai ya dubi yadda duniya ta ke a yau, da halin da take ciki na rashin gaskiya kiri-kiri da zalunci da barna da rashin tsari. Don haka a yanzu ma muna raye ne a zamanin Jahiliyya.
* Abin takaici da ban kunya ga Musulmi shi ne, suna cikin halin gafala da sabawa addininsu Yahudawa, bisa goyon bayan wasu kasashen Turai, suka zo suka mamaye wannan wuri mai tsarki. Sabani, da kace-na-ce, batanci ga juna da kafirta juna sun hana su yin katabus a kan wannan. Wasa-wasa al’amari ya cabe musu, suna kallo ana kashe ’yan’uwansu alhali ba sa komai sai surutan da ba sa da wani amfani. Wallahi kuwa ba su da wata mafita a kan wannan sai sun koma bisa karantarwar addininsu, sun kiyayi rarraba da kafirce-kafircen juna. Allah Ya nuna mana wannan lokaci.
[6] Sakayyar tarihin Musulunci ga Abu Dalib kan wannan babbar gudunmawa shi ne kafirta shi da cewa ya mutu Mushriki. Ban sani ba wane irin shirka ne wannan mai kariya ga Musulunci. Kuma me yasa Annabi ya yi bakin-ciki da mutuwarsa har ya sawa shekarar suna Shekarar bakin-ciki?
* Wani abu mai jan hakali shi ne cewa Sarki Najjashi, a wannan lokacin, Kirista ne shi da mutanensa. Kuma da haka ya karbi Musulmi ya ba su mafaka a kasarsa. Don haka mu ke cewa: a cikin wadanda suka ba addinin Musulunci gudunmwa akwai Kirista. Wannan wani babban kalubale ne ga Musumi da Kirista, a bangaren zamantakewa. Wane Muslmi ne zai fito ya ce Annabi bai yi daidai ba da ya tura Musulmi kasar Kirista hutu? Ko wane Kirista ne zai ce Najjashi ya yi kuskuren karabar Musulmi? Sai dai mai son zuciya. A cikin wannan akwai darasi na zamantakewa tsakanin mabiya addinan biyu.
[7] Wannan shi ya fi kyau a kan yadda yawa-yawan malamai da marubuta tarihi ke fada, na cewa “tsakuwa na tasbihi a hannun Annabi”. Domin tsakuwa na tasbihi a hannun kowa ma, kamar yadda AlKur’ani ke cewa: Babu wani abu face yana tasbihi da gode maSa (Allah), sai dai ku ba ku jin tasibihinsu. Amma ana ji a hannun Manzo.
[8] Wani abin lura da ya wajaba a fadaka da shi, shi ne cewa Musulmi ba sa shakka a kan dukkan Mu’ujizozin Annabi (SAWA). illa dai daga baya an sami wasu Wahabiyawa (da duk bangarorinsu) suna musanta Mu’jizozin; kai! Wasu na yi musu izgili ne ma, suna cewa: ya ya za a yi mutum ya ga bayansa? Ko ya ya za a yi mutum ya ji magana a lokacin da yake barci? Wani ma ya taba ce min wai surkulle ne a ce ana ganin alamun kafar Annabi in ya yi tafiya a kan dutse, alhali ba a gani in yana tafiya a bisa yashi. Wannan ba abin mamaki ba ne, domin su ne suka haramta raya ranar haihuwarsa, da ranar aiko shi da ranar rasuwarsa. Kai sun ma hana Musulmi ziyarar kabarinsa, bisa dogaro da wasu riwayoyin karya da makiya Musulunci suka dasa a littafan Musulmi don raba su da Annabinsu (SAWA).
[9] Sayyid Murtdha al-Amili, al-Sahihu min Siratil-Rasulil-Akram
wanda ya cirato ya shigar Dan'uwa Sa'idu Funtua