Muassasar alhasanain (a.s)

Saukar Wahayi Ga Manzo

3 Ra'ayoyi 02.3 / 5

 Ko da yake mutanen garin Makka suna girmama Manzon Allah (s) saboda kyawawan dabi'unsa, amma shi ya gwammacewa kadaita da nisanta kansa daga wannan mushirikar al'umma; ya kan tafi wani kogo a wajen Makka wanda ake kira Kogon Hira, don bautar Allah, tunanin girmanSa da kuma nisanta daga munanan ayyuka da suka zama ruwan dare a Makka.

Da farko ya kan zauna a kogon na tsawon yini guda zuwa kwanaki biyu, wani lokaci ma har kwanaki goma; amma kusan saukan wahayi ya kan zauna har na tsawon wata guda don bautar Allah da kuma tunanin yadda za a shiryar da wannan lalatacciyar al'umma.

A lokacin da ya cika shekaru arba'in da haihuwa, kamar yadda ya saba, yana cikin wannan kogo na Hira inda yake shagaltuwa da ibada, kwatsam sai ya ga Mala'ika Jibrilu (a.s) ya bayyana gare shi da ayoyin farko na Alkur'ani:

Ka yi karatu da sunan Ubangijinka wanda Ya yi halitta. Ya halicci mutum daga gudan jini. Ka yi karatu da (Sunan) Ubangijinka mafi girma. Wanda Ya sanar da mutum (ta hanyar) alkalami. Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.

(Surar Alak:1-5)

Da wadannan ayoyi, Mala'ika Jibrilu (a.s) ya sanar da Annabi (s) cewa Allah Ya zabe shi a matsayin ManzonSa na karshe ga talikai.

A dalilin haka, Muhammadu (s) ya kasance cikin matukar farin ciki da godiya ga Allah saboda wannan baiwa da Ya yi masa, saboda haka ya gaggauta komawa gida don sanar da matarsa Khadija wannan baiwa ta zabarsa a matsayin Annabi. Sai ya kwanta a gadonsa don ya dan sami hutu. A wannan lokacin ne kiran daga Allah a karo na biyu ya zo gare shi:

Ya kai mai lulluba. Tashi ka yi gargadi. Ubangijinka kuma ka girmama Shi. Tufafinka kuma ka tsarkake su. Gumaka kuma ka kaurace musu

(Mudassir:1-5)

Wannan kira ne na tafiya da sako da yin albishir da sabon addini da daukar da'awar Allah zuwa ga mutane. Don haka ba abin da ya ragewa Manzon Allah sai amsa kira da gaggauta sanar da Ali bin Abi Talib(1). (a.s), wannan da jahiliyya bata gurbata shi da dattinta ba, kuma bai taba sujjada ga gunki ba. Domin ya tashi ne a hannun Manzo (s.a.w.a) kuma a gidansa. Sai ya amsa kiran Allah, ruhinsa ya rungumi ruhin sakon Allah Madaukaki.

Kamar yadda kuma Manzo ya bijirar da da'awarsa ga matarsa Khadija, ita ma sai ta amsa kiransa ta yi imani da sakonsa. Da wannan aka hada wani gungu na al'umma mumina a doron kasa, wanda ya kumshi Muhammad, Ali da Khadija. Da wannan dalili, Khadija da Imam Ali (a.s) suka kasance wadanda suka fara musulunta (Khadija ta bangaren mata Ali kuma a bangaren maza).

Ta haka ne aka saukar da wannan sako na Musulunci wanda ba wai kawai zai tsarkake Larabawa daga daudar shirka ba ne, a'a har ma haskensa zai haskaka duk duniya baki daya.

Sai Manzo (s.a.w.a) ya ci gaba da kira a boye yana samun amsawa, har adadin wadanda suka yi imani da wannan sako ya karu. Don cika tanajin na kololuwa, sai Manzo ya shiga koyar da su Alkur'ani da hukunce hukuncen sakon, kamar yadda kuma suka dinga yin salla wararen da suka nisanta daga idanuwan mutane.

Yayin da adadin muminai ya yawaita har suka fara jin tsoron tonuwar al'amarinsu, sai suka mayar da gidan Arqam al-Makhzumi ya zama wajen karatu da shiri da ibada.
(1)- Ahmad bin Hambali cikin Masnad, juzu'i na 2, shafi na 368; da Hakim cikin al-Mustadrik, juzu'i na 4, shafi na 336; da Ibin Athir cikin al-Kamil, juzu'i na 2, shafi na 22; da littafin al-Isti'ab, juzu'i na 2, shafi na 459; da wasun wadannan.
 Muhd Awwal Bauchi

wanda ya cirato ya shigar Dan'uwa Sa'idu Funtua

 

 

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)