Muassasar alhasanain (a.s)

ZIYARAR ARBA'IN DIN IMAM HUSAIN

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Qai

 

FALALAR ZIYARAR ARBA’IN DIN IMAM HUSAIN DAGA HADISAI

                    

Ziyarar Imam Husain tana daga cikin ziyarorin da aka rawaito hadisai da suke nuni a kan girman sha’aninta wanda a cikin wannan littafi da yake hannun dan’uwa mai karatu muka kawo guda arba’in daga cikin ruwayoyi mafiya inganci da suka yi magana a kan falalar ziyaran Imam Husain dan Ali (a.s).

Kuma hadafin rubuta wannan makala shi ne don mu kara riskar irin nau’o’in ni’ima da allah ya yi mana da kuma irin girman sha’anin da yake akwai ga iyalan Manzon rahama musamman shahidin karbala Husain dan Ali (a.s), da fata Allah ya katarcemu (ya yi mana katari) da samun ceton iyalan gidan manzon Allah (s.a.w) a duniyarmu da lahira.

 

 

 

 

 

  

 

 

ALAMOMIN MUMINI

 

An ruwaito daga Hassan dan Ali (a.s) ya ce: alamomin mumini guda biyar ne:

1. Na farko sallah raka'a hamsin da daya a kowace rana.  

2. Na biyu ziyarar arba'in.

3. Sanya zobe a hannnun dama.

4. Na hudu ta'afir (wato dora kumatu biyu a.kan turba bayan sajdatus-shukr).

5. Na biyar kuma bayyanar da basmala a raka'o'i biyu na farkon kowace salla.

 

 

 

 

ADDU’AR IMAM SADIQ GA MAZIYARTAN HUSAIN BN ALI (a.s).

 

Daga shekh kulaini da sanadinsa zuwa ga mu'awiyatu dan wahab ya ce: na nemi izinin shiga wajen  baban Abdullahi sai aka ce min na shigo, amma sai na same shi a wajen sallarsa yana sallah  sai na zauna domin in jiran shi ya gama sallarsa,  bayan na zauna sai na ji shi yana addu'a yana cewa:

"ya wanda ya kebancemu da karama kuma ya kebancemu da wasiyyah, ya kuma ba mu sanin duk abin da ya wuce da kuma wanda zai zo, kuma ya sanya zukatan mutane suke karkatowa zuwa gare mu a ko yaushe, ina rokonka da ka gafartamin ka kuma gafartama y'an'uwa na, ka kuma yi gafara ga maziyartan babban Abdullahi Husain (a.s) wadanda suka sadaukar da dukiyoyinsu kuma suka sallama jikkunansu domin kwadituwarsu ga yin biyaiya zuwa gare mu da kuma fatan samun sakamakon da ke wajenka wanda ka tanadar ma maziyartanmu, sannan kuma suke da burin sanya farinciki a cikin zuciyar Annabinka (s.a.w) kuma suke saurin biyan dukkan buqatunsu kuma suke sanya bakinciki a cikin zukatan  makiyanmu, kuma suka nemi yardanka da hakan, to ka saka musu da yardanka domin mu, ka wadatasu da arzikin dare da rana, ka kula mana su da iyalansu da suka baro a gidajensu da mafi kyawon kulawa, ka isar musu daga kowane mai karfi da kowanne mai rauni da kuma kowane mai tsanani daga cikin halittunka, ka kuma kare su daga sharrikan dukkan mutane da aljanu ka kuma ba su mafificin abin da suke nema daga gare ka albarkacin nisantarsu da garuruwansu, ka kuma ba su saboda abin da suka fifitamu  da shi a kan iyalansu da ‘ya’yansu da makusantansu, ya Allah! lallai makiyanmu sun azabtar da su a kan fitowa zuwa gare mu kuma hakan bai hana su yin ganganmi zuwa gare mu ba saboda sabawa duk wanda ya saba mana, ya Allah! Ka tausayawa wadannan fuskokin da rana ta canzasu, ya Allah! Ka tausayawa wadannan kumatu da aka shashshafasu a kan kasar kabarin Abu ABDILLAH, ya Allah ka tausayawa wadancan idanuwan da suka shekar da hawaye saboda tausayin mu, ya Allah! Ka tausayawa wadancan zukatan da suka yi raki saboda mu ya Allah ka tausayawa duk wata kara da aka yi ta sabodamu, Ya Allah! lallai lallai muna baka amanar wadancan rayukan da jikkunansu har zuwa lokacin da zamu riskesu a tafki ranar kishirwa".

 

Bai gushe ba yana halin sujada a lokacin da yake karanta wannan addu'ar har sai da ya kammala, bayan ya gama sai na ce: raina fansa gare ka da ace wannan abin (addu'ar) da na ji gare ka zai kasance ga wanda bai san Allah ba ne to wallahi na tabbata wuta ba zata ci komai daga gare shi ba, wallahi na yi burin a ce na kasance cikin jerin maziyartansa kai koda bazan sami damar zuwa hajji ba.  Sai ya ce da ni" ai banga wani nisa tsakaninka da shi ba don haka babu wani abu da zai hana ka ziyartan shi"  sai na ce raina fansa zuwa gare ka ai bansan yanda al'amarin yake ba, sai imam ya ce da ni ya kai mu'awiya ka sani cewa  masu yin addu'a ga maziyartansa a sama sun fi masu yi musu du'a'i a kasa yawa.

 

 

 

 

 

 

BABI NA UKU

NIYYAR ZIYARAR IMAM HUSAIN (a.s)

Ni ina mai nufin ziyartar shugabana kuma majibincin al'amura na, baban Abdullahi Husain (a.s) ziyara daga gare ni da mahaifana da y'anuwan maza da mata, da kakannina maza da mata, da y'anuwan mahaifina maza da mata da y'anuwan mahaifiyata maza da mata da danginsu da zuriyoyinsu da abokaina da makwabtana da wadanda sukayimin wasicci da inyi musu addu'a da ziyara, da dukkan muminai maza da mata musamman ma wadanda sukeda hakki akaina na in nema masu kusanci zuwa ga Allah madaukaki.

 

 

 

ZABABBUN HADISAI ARBA’IN A KAN FALALAR ZIYARAR IMAM HUSAIN (a.s)

 

 

HADISI NA FARKO

 Daga baban Samit ya ce: na ji baban Abdullahi (a.s) yana cewa: "duk wanda ya je kabarin imam Husain (a.s) yana mai tafiya a kasa Allah (s.w.t) zai rubuta masa ga kowane  taku ladan kyawawan aiyuka dubu, kuma zai shafe masa munanan aiyuka guda dubu kuma ya daga darajarsa har sau dubu kuma idan ka je furat sai ka yi wanka ka cire takalmanka ka yi tafiya ba tare da shi ba  ka yi tafiya irinta kaskantaccen bawa, idan ka je kofar ha'ir sai ka yi kabbara sau hudu sannan sai ka matsa gaba kadan sannan ka kara yin kabbara hudu sannan sai ka je wajen kan Imam Husain ka tsaya ka yi kabbara hudu bayan nan sai ka yi sallah raka'a biyu ka roki dukan bukatarka.

 

HADISI NA BIYU

Daga Husaini dan Suwair dan Abeefakhah ya ce; baban Abdullahi (a.s) ya ce duk wanda ya fita daga gidansa yana mai niyyar fuskantar kabarin Husain dan Ali (a) idan a kasa yake Allah zai rubuta masa hasana ( wato ladan aiki nagari) ya kuma shafe masa dukkan wani mummunan aiki ga kowane taku har zuwa lokacin da zai isa ha'ir , kuma Allah zai rubuta shi cikin masu nasara kuma tseratattun bayi, zuwa lokacin da ya gama ziyara ko Allah zai rubutashi cikin bayi masu babban rabo zuwa lokacin da ya yi nufin tafiya gida kuwa mala'ika zai sauko ya ce da shi; lallai ma'aikin Allah yana yi maka sallama kuma yana cewa da kai ka sabunta aiyuka a gaba amma zunubanka na baya kuwa Allah ya gafarta maka su.

 

 

HADISI NA UKU

Daga Bashir Al-dahhan, daga baban Abdullahi (a.s) ya ce; mutum yakan sami gafarar zunubansa sakamakon takunsa guda da ya yi bayan barin iyalinsa da niyyar tafiya zuwa kabarin Imam Husain (a.s), sannan kuma ba zai gushe ba ana tsarkake shi har sai ya isa, a sannan sai Allah (s.w.t) ya yi magana da shi ya ce mai; yakai bawana ka tambayeni domin na baka duk abin da ka nema daga gurina! Sai Imam sadiq ya ce: kuma hakki ne a kan Allah da ya ba shi duk abin da ya nema din.

 

 

HADISI NA HUDU

Daga Ali dan Maimun as-sa'igh, daga baban Abdullahi ya ce; "ya Ali ka ziyarci Husain kada ka yanke zumuntarka da shi, sai na ce meye ladan wanda ya ziyarce shi? Sai Imam ya ce duk wanda ya je ziyartansa  a kasa Allah zai rubuta ladan aiki na gari ga kowane taku sannan kuma zai shafe masa mummunan aiki ga kowane taku, kuma ya daukaka darajansa, idan kuma ya isa Allah zai wakilta masa mala'iku dubu da zasu rika rubuta duk abin da ya fito daga bakinsa na alkhairi kuma ba zasu rika rubuta abin da ya fita daga bakinsa na sharri ba, idan ya tashi tafiya zasu yi masa bankwana su ce da shi; ya masoyin ubangiji, lallai kana cikin rundunar Allah kuma rundunar ma'aikinsa da rundunar iyalan gidansa (wato Ahlulbait tsarkaka), muna rantsuwa da Allah a kan cewa ba zaka ga wuta da idon ka ba kuma ba zata ci daga jikinka ba har abada. [1]

 

 

 

HADISI NA BIYAR

Daga baban sa'ed ya ce; wata rana na shiga wajen baban Abdullahi na same shi a wani dan karamin daki, na ji shi yana cewa: "wanda ya je kabarin Imam Husain (a.s) a kafa yana da lada kwatankwacin ladan wanda ya y'anta wuyaye daga cikin 'ya'yan Annabi Isma'il (a.s) idan kuma a jirgin ruwa ya je Allah zai kare su kuma mai kira zai yi kiransu daga sama yana mai cewo lallai kun samu babban rabo kuma aljannan tana farincikin saduwa da ku [2] .                                  

 

HADISI NA SHIDDA

Daga basheer Ad-duhan ya ce: nafada ma Abu Abdillahi cewa a duk lokacin da ban samu damar zuwa hajji ba nakan tafi ziyarar kabarin baban Abdullahi Husain (a.s) sai Imam (a.s) ya ce da shi ka kyauta ya bashir domin duk muminin da ya je kabarin Imam Husain alhali yana mai sanin hakkinsa da matsayinsa (wato waliyyancinsa) idan a ranar da ba ta idi ba ce Allah zai rubuta mashi ladan hajji guda ashirin ladan umara  ashirin (20) cikakku kuma karbabbu da kuma ladan hajji da umara guda ashirin tare da Annabi  Manzo da kuma  Imami adili, sannan kuma duk wanda ya je ziyarar tasa a ranar idi Allah zai rubuta  masa ladan Hajji dari 100  tare da umara dari 100 da kuma musharaka a cikin yaki a karkashin Annabi ko Imami adali.

Sai nace masa (duhan) yanzu ya matsayina kenan?, sai Imam ya yimin wani irin kallo sannan ya cemin; ya bashir lallai mumini idan ya je ma imam Husain (a.s) a ranar arafah, kuma ya yi wanka da ruwan furat sannan ya fuskanci haramin imam Husain (s) Allah zai rubuta masa ga kowane taku hajji da ........, kai abin da ban yi tsammaninsa ba ma shi ne daya ce har da ladan gazwa (yaqi) {wato ladan wanda ya je ya ki a tare da Manzon Allah (s.a.w)} [3] .

 

 

HADISI NA BAKWAI

Daga Yazidu dan Abdulmalik ya ce; na kasance tare da baban Abdullahi (a.s) sai wasu mutane suka wuce a kan jaki, sai imam ya ce ina wadannan mutane suke son tafiya ne?  sai na ce da shi zasu je ziyaran shahidai, sai Imam ya ce: me zai hana su ziyartan gareeb (wanda ya yi shahada a wajen bakunci, garinda ba nasa ba)  sai wani mutum daga cikin al’umar Iraq ya ce shin ziyarar tasa wajibi ce? Sai imam ya ce ziyararsa tafi hajji da umrah, a lokacin sai da Imam ya lissafa hajji da umara guda ashirin sannan ya ce kuma cikakku karbabbu, Yazid ya ci gaba da cewa wallahi ban mike ba a gurin sai ga wani mutum ya zo inda muke zaune ya ce ma Imam; hakika ni na samu damar yin hajji sha tara 19, yanzu ina so ka rokamin Allah ya azurtani na sami damar cika ashirin 20  sai Imam ya ce ka ziyarci kabarin Husaini kuwa?   Ya ce: a’a, sai Imam ya ce wallahi, da ka ziyarce shi sau daya da yafiye maka hajji guda ashirin 20. [4]

 

 

 

HADISI NA TAKWAS

Daga salih Annayli, ya ce: Abu Abdillahi (a) ya ce: “ duk wanda ya je ma Imamu Husain (a.s)  alhali yana mai sane da matsayinshi na Imamama da wilaya , Allah zai rubuta masa ladan wanda ya y’anta wuyaye dubu 1000 ya kuma dora kaya a kan dawaki dubu masu sirdi ya sallamasu saboda Allah”. [5]

 

 

 

HADISI NA TARA

Daga Abban dan Taglib ya ce : daga baban Abdullahi, ya fadi cewa: “lallai a makwancin shugaban shahidai (Husain  (a.s) akwai mala’iku guda dubu arba’in 40,000  shugabansu wani mala’ika ne mai suna mansur, su wadannan mala’iku babu abin da suke a kabarin sayyidush-shuhada’ sai kuka har zuwa ranar tashin kiyama,  babu wani maziyarci da zai ziyarci Imam face sai sun marabce shi, babu wani maziyarci da zai yi mai bankwana face sai sun raka shi, babu wani maziyarcinshi da zai yi rashin lafiya face sai sun ziyarce shi a gadonsa na rashin lafiya, babu wani maziyarcinshi da zai rasu face sai sun yi ma gawarshi sallah kuma sun roka masa gafarar Allah (s.w.t). [6]

 

 

 

HADISI NA GOMA

Daga Haris dan mugira, daga Abu abdillahi  ya ce; hakika Allah ya wakilta wasu mala’iku a bigiren kabarin imam Husain (a.s) wandasu aikinsu shi ne idan mutum ya yi azamar fita zuwa kabarin Husain (a.s) domin ziyararsa Allah zai ba su zunubansa idan ya yi taku daya sai su share masa su, idan ya kara wani takon sai su ninka masa ayyukansa da ya yi na alkhairi, ba zasu gushe suna ninka masa aiyukansa na alkhairi ba a lokacin da yake tafiya har sai lokacin da ayyukan nasa suka sa ya cancanci aljanna, sai su zagaye shi a lokacin su tsarkake ruhinsa da jikinsa,  sai mala’ikun sama su yi kira suna masu cewa ku gaggauta tsarkake maziyartan habibullahi (masoyin ubangiji Husain (a.s))  idan suka gama wanke shi sai annabin rahama ya kiraye su yana mai cewa; ya ku ma’abota wannan ayari, ina mai yimuku bushara da kasancewa tare da ni a aljannah, sannan sai shugaban muminai Ali dan Abi-Dalib ya kira su yana mai cewa na lamunce muku biyan dukkan bukatunku da kuma kariya daga dukkan bala’in da zai fuskance ku a duniya da lahira, sai manzon Allah ya kasance a tare da su yana mai kewaye bangaren hagu da bangaren damansu har sai sun koma zuwa ga ahalinsu. 7

 

 

 

 

 

HADISI NA GOMA SHA DAYA

Daga mufaddal dan umru ya ce:  baban Abdullahi ya fadi cewa; “wallahi gani ina gani da idona wasu mala’iku sun yi cincirindo a kan muminan da suke tsaye kan kabarin sayyidush-shuhada’, sai nace (inji mufaddal) shin suna gadin Imam Husain dinne? Sai Imam ya ce sam sam, wallahi suna bibiyan muminai ne kai har ma suna  shafar fuskokinsu da hannayensu”  sai ya ce; “ kuma Allah yana saukar da abincin aljanna dare da rana ga maziyartan Husaini (a.s) kuma mala’iku ne suke hidimta musu, kai babu wani bawa da zai tambayi Allah Ta’ala wata buqata face ya biya masa ita” sai Mufaddal ya ce kai amma wannan babbar karama ce! Sai imam ya ce:” ya Mufaddal shin in kara maka ne?” sai na ce e ya shugaba na!  sai ya ci gaba da cewa:  “wallahi ga ni ina ganin wani gado na haske an ajiye shi an buga masa kubba ta jan yakutu wanda aka yi mashi ado da jauwhari, sannan wallahi kamar ina ganin cewa  ga Imamu Husaini nan zaune a kan wannan gadon kuma a gefensa akwai wasu korayen kubbobi dubu casa’in 90,0000  sannan kuma ga muminai suna ziyartansa suna masa sallama, sai Allah ya rika cewa da su: “ masoyana  ku tambaye ni dukkan bukatunku domin an dade ana cutar da ku, ana kaskantar da ku  sannan kuma ana yi muku danniya, to yau rana ce da babu wata buqata ta duniya da lahira  da zaku rokeni face sai na biya muku ita a wannan rana cin su da shan su zai kasance daga aljanna ne,, wannan ita ce ake cema karama wadda ba ta da karshe. 8

HADISI NA GOMA SHA BIYU

Daga Haisam dan Abdullahi daga baban Hassan, Aliyur Ridha (a.s) daga babansa, shi ma ya rawaito daga baban Abdullahi Ja’afar dan muhammad as- sadiq (a.s) ya ce; “ lallai kwanakin da maziyartan Husain suke yi a lokacin ziyararsu gare shi ba’a lissafasu a cikin  kwanakinsu na duniya kuma ba’a rage su a cikin lissafin ajalinsu” 9.

 

 

 

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)