Mugun Hali
MUGUN HALI
*Kimar Abota
* Mummunan Hali Yana Korar Mutane
* Manzo (S.A.W.A.) abin koyi
Kimar Abota
Kauna tana daya daga cikin dabi’un mutum, saboda haka ne muke ganin zuciyar mutum tana ingiza shi zuwa ga shakuwa da wasu daga cikin mutane. Ba ai yiwu a dankwafe wannan dabi’a ba. Dan haka yake zama wajibi a biyawa zuciya wannan bukatar. Kowa yana kulla abota ne da wasu makamantansa a cikin jama’a domin ya zauna tare da su ya debe haso.
Abota tushen aminci da nutsuwa ce, kuma tana daya daga cikin abubuwa masu ba da kwanciyar hankali. A duk fadin duniyar nan babu wani abu da ya kama kafarta a kima.
Kuncin kadaitaka da rashin aboki yana daga cikin masifu masu tsanani. Idan ba domin soyayya ta hada mu da juna har zukatanmu suka shaku da ta juna ba, to da bakin ciki da damuwa sun yi wasan kura da mu, duniya kuma da ta zame mana baka kirin. Wani masani yana cewa:
“Sirrin alheri shine alakarmu ta kasance ta ‘yan uwantaka ba ta kiyayya ba, domin duk wanda ba zai iya son mutane ‘yan uwansa ba, to a bisa dabi’a ba zai rabu da kunci da damuwa a rayuwa ba.”
Hanyoyin da suke karfafa dankon zumunci a al’umma, sune wadanda aka gina su a kan asasin tausasawa da soyayya ta gaskiya. Shakuwar zukata itace take kawo hadin kai da kaunar juna mai zurfin gaske. Saboda haka babu makawa mutum ya yi watsi da sabanin da ke tsakaninsa da wasu domin kulla abota ta gaskiya, sa’annan kuma ya yarda da gaskiyar da ‘yan uwa suke kiran sa zuwa gare ta. Abota ta gaskiya itace wadda ba a kulla ta don abin hannun juna ba, kuma ta kasance cudanye da ruhin ‘yan uwantaka wanda zai gamsar da zuciyar dan adam mai bukatar soyayya. Duk wani aboki na gaske to wajibi ne ya guji raunana jigon abota a zuciyarsa ko ta halin kaka. Sannan ya yi kokarin yaye wa abokin nasa kuncin rayuwa da ya mamaye zuciyarsa, kuma ya shuka masa fata na gari da nutsuwa a zuciya. Bai kamata mutum ya yi abota da kowa ba ko ya ishisshire a inuwarsa, sai ya tabbata zuciyarsa a cike take da sonsa da kaunarsa. Wani masani yana cewa:
“Rayuwar mu kamar kogon dutse ce, duk yayin da mutun ya kwalla kira sai yaji amon muryarsa. Saboda haka duk wanda zuciyarsa take cike da soyayya ga sauran jama’a ba zai ga komai daga gare su ba illa soyayya.harkokin mu na duniya duk cude-ni-in-cude-ka ne, amma ba wai muna nufin mu ce al’amuran mu na ibada ma bisa wannan asasin aka tsai da su ba. Amma ta yaya zai halatta a gare ka kaso wasu su kyautata maka alhali kai ba ka kyautata musu? Kuma ta yaya za ka nemi soyayya madawwamiya daga gare su alhali kai ba ka dawwama a kan soyayyar ka gare su ba?”
Zaman taren da babu kaunar juna da igiyar soyayyar da ta daure zukata, ba zai haifar da komai ba face dacin rayuwa da azaba.
Idan riya tayi kanta a zukata da rayuwar mutane, kuma bambadanci domin neman abin duniya ya maye gurbin abota da zaman tare, to sai kyautatawa juna da zaman tare suyi rauni kuma a rasa taimakekeniya a al’umma.
Ba shakka a rayuwar ku kun taba yin ido hudu da wasu mutanen da babu kauna da rahama a zukatansu. Amma sunyi shigar burtu sun sanya tufafin abota, kuma sau da yawa ba za ku iya gane gaskiyar al’amarinsu da aibobin dake tattare dasu ba, dan haka kwaskwarimar su take rinjayar ku zuwa gare su.
Daya daga cikin sharudan alheri da tafarkin tarbiyar ruhi, itace kulla abota ta gaskiya da salihan mutane. Saboda zuciyar mutum kan sami tarbiyya a sakamakon zama da su, ruhin sa kuma ya daukaka daga matsayinsa na al’ada zuwa ga matsayin takawa da falala. Saboda haka ya wajaba akan mutun ya yi kyakkyawan tunani wajen zaben abokai. Kuskure ne mutum ya yi abota da wanda bai yarda da shi ba. Domin shi mutun an halicce shi da daukar halin wanda yake tare da shi yau da kullum. Kuma wannan shine abin da ake tsoracewa sa’adar mutum, kada ya fandarar da ita ya tozarta.
Mummunan Hali Yana Korar Mutane
Munanan dabi’u suna daga cikin abubuwan da suke girgide rukunan abota. Wanda yake da kaushin hali yadda ba zai yiwu a shawo kansa ko ya shawo na mutane yadda ba zai yiwu ya ga hasken kauna ba. Mummunan hali ya kan zubar da darajar mutum kuma ya ruguza ginshikan sa’adarsa da nutsuwarsa.
Babu shakka kowa yana gudun mai mummunan hali domin zama guri daya da wanda ba ya debewa mutum haso yana da cutarwa. Wannan shi yake sa mai mummunan hali ya kasa samun damar ci gaba a rayuwa.
Ya wajaba a kan wanda zai zauna da wasu ya san al’amura da sharudan zaman tare. Wajibi ne ya koye da farko sa’annan ya yi kokarin aiki da su a rayuwarsa, kuma ya hanu da bin hanyoyin da suka sabawa sahihan hanyoyin rayuwar al’umma idan kuwa ba haka ba, to bai dace ya zauna da jama’a ba, kuma halayen kwarai ba za su kamkama a tsakanin su ba. Kyawawan dabi’u suna daga cikin sharudan samun alheri a tsakanin mutane, kuma har wa yau sune ke taimakawa wajen daukaka darajar mutum. Kyawawan halaye suna sharewa mutum fagen da zai amfana daga dukkan karfinsa kuma suna da tasiri ainun akan gudanar da al’umma. Babu wata sifa daga sifofin mutum wadda za ta iya kaiwa ga matsayin wannan sifar wajen jawo zukatan wasu da rage musu wahalolin rayuwa.
Lallai duk mutumin da ya mallaki irin wannan kyakkyawan hali, ba zai dubi mutane da murtakakkiyar fuska ba balle har su fahimci kuncinsa. Ya wajaba ya yi kokari da’imna domin samar da nishadi da farin ciki yadda zai mantar da mutane bakin cikin su kuma ya kasance da nutsuwa a cikin zuciyar sa har ya kai alheri da samun tsira komai tsananin wahalhalun rayuwa.
Kyawun hali shine musabbabi mafi karfi mai tasiri kai tsaye a tabbatar da muwafaka a rayuwa, kuma ba sai mun fada ba cewa, ci gaban kamfanoni ma ya ta’allaka ne ainun da kyawun halin ma’aikatansu.
Lallai idan shugaban wata masa’anta yana da kyawun hali, bayan girman mukaminsa, to da snnu zai jawo hankalin abokan ciniki da dama.
Babban mai waken Iran, Hafiz Shirazi yana cewa:
Rinjaye su da kyawun hali ka aboce su.
Mai wayo da su yake kama tsuntsu.
Kyawun hali shine sirrin soyayya a tsakanin mutane domin su ba sa jure munin halin wani, ko menene asalinsa da musabbabinsa kuwa. Idan da za ka yi nazarin halayen abokan zaman ka da kyau, da ka gane babban dalilin haduwar jinin ka da wasunsu da kuma yadda wasunsu suka shiga zuciyar ka, za ka ga duk ya danganta ne da halayyarsu da sifofinsu.
Daya daga cikin masanan Turai yana ba da labarin abin da ya jaraba ya gani da kansa game da halin kwarai, inda yace:
“Na yi niyyar gwada sakamakon nishadi na da sakin fuska ta akan kaina, alhali na kasance a cikin damuwa da kunci tun tuni. Sai na fita daga gida na da wannan nufin, kuma ina tafe ina fadi a zuciya ta cewa na lura sau da yawa farin cikin wasu da sakin fuskar su yana bani karfin gwiwa da jin dadi. Dan haka lalle ni ma ya kamata in sani ko zan iya sa wasu su ji haka? Ina tafe a kan hanya ina maimaita nufi na, na nishadi da sakin fuska a zuciya ta. Kuma ina cewa lalle nayi sa’a kwarai da wannan irin tasiri na farkarwar ruhi, sai na ji dadi a jiki na kamar na tashi sama don murna da farin ciki sai dube-dube nake ta yi ina al’ajabi, ina murmushi. Amma kuma kewaye dani sai ina ganin wasu fuskoki a turbune saboda bakin ciki da juyayi. Wannan yasa tausayin su ya kama ni, kuma ina alla-alla in dan haska musu annuri da hasken da ke zuciya ta.
Sai na shiga ofishi na nayiwa Akanta sallama cikin nishadi. Tun da yake da ma can ni ba mutum ne mai fara’a ba, a bisa al’ada ko da kareni ya yi daga mutuwa, ba an iya masa haka ba. Saboda haka ya amsa sallamar cikin farin ciki da tausasawa ba tare da jinkiri ba.
Daga nan sai na ji a zuciya ta cewa lalle wannan ya harbu da nishadi na. Mai wannan kamfanin da nake aiki a ciki kuwa irin mutanen nan ne masu azabar aiki wadanda idan sun dukufa ba sa ko daga ido su ga na gefen su, kuma yana da kaushin hali. A wannan ranar kuwa sai ya tsawatar mini ainun a kan aiki na, yadda da a wata rana ce ba wannan ba, da an ji mu domin ni mai saurin tunzura ne. Amma tunda yake nayi niyyar cewa a wannan ranar ba zan dimauta ba ko da wani abu ya auku, sai na kanne, ina bashi amsa cikin nutsuwa har jikin sa ya yi sanyi ya sake fuskar sa. A ranar sai na dage don dorewa cikin halin nishadin ruhi na da na abokan aiki na.
Ta wannan hanyar na ci nasarar jarraba haka a tsakanin mutanen da muke gida daya da su. Babu sakamakon da na gani daga wannan jarrabawa tawa, illa fara ganin jin kai da tausasawa daga mutanen da da can ko kula ni ba su yi. A sakamakon cin nasarar gwajin da nayi, sau da yawa, sai na gano cewa zan iya ba wa kaina nishadi ta wannan hanya, kazalika kuma wa wanda yake kusa da ni.
Amma idan da ku kanku za ku zauna da mutane da wannan ra’ayi, da kun ga fuskoki cike da farin ciki, fyes-fyes kamar furanni da kaka, kuma lalle da kun samawa kanku abokai masu yawa, da nutsuwa da aminci kuma sun lullube zukatan ku da’iman.”
Babu wani da ke musa tasirin wannan hali, hatta a zukatan makiya, “maganar da aka yi cikin soyayya ta kan ratsa zukatan wasu tamkar sihiri.” Haka kuma ladabi da mutunci a magana na matukar kwantar da husuma.
Wani marubucin Turai yana cewa:
“Dukkan kofofi a bude suke a gaban mai sakin fuska, ma’abocin halin kwarai. Alhali mai mugun hali kuwa tilas ne ya kwankwasa dan a bude masa kamar fakiri. Abu mafi alheri shine wanda aka kammala shi da ladabi da nasara da kyawun hali.”
Ni kuma na kara da cewa kyawun hali yana wajabta alheri, kuma yana kai ma’abocinsa ga kamala ne kawai, idan ya kasance daga tsarkakakkiyar zuciya wadda ta yi nesa da cututtukan Riya. Ma’ana soyayya ta kasance daga zuciya domin matukar ladabi da kyawun hali ba su zamo dabi’ar ruhi ba, to ba su da wata kima kuma ba za a amince da su ba. Kyawun hali na zahiri kawai ba hujja bane a kan kyawun halin mutum da tsarkin ruhin sa ba. Mai yiwuwa ne kyakkyawan hali na zahiri duk kyawunsa ya bullo daga zuciya wadda take dulmiye a cikin bata. Akwai shedanun mutane da yawa wadanda suka yi shigar salihai, sun rufe munanan fuskokinsu da kyakkyawan lullubi.
Manzo (S.A.W.A) abin koyi
duk mun sani cewa kyawun halin Manzon Allah (S.A.W.A) yana daya daga cikin manyan abubuwan da suka ciyar da musulunci gaba. Haka kuma Allah Ya danganta yaduwar musulunci da kyawun dabi’ar Manzon Allah (S.A.W.A.). allah Ta’ala yace:
“Kuma da ka kasance mai fushi mai kaushin hali to da sun watse daga gurin ka.” (surar Ali Imrana:159).
Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana tafi da jama’a ba tare da nuna bambanci ba. Fuskar sa ta kan yi annuri yadda ba za a iya sifantawa ba, yazo a littafin Raudhatul kafi shafi na 268 cewa:
Manzon Allah (s.a.w) ya kan daidaita kallon sa a tsakanin sahabbansa, ya dubi wadannan sa’annan ya dubi wadancan daidai wa daida.”
Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana kushe mummunan hali. Yazo a littafin Nahjol balagha shafi na 371 cewa Manzon Allah (s.a.w) yace:
“Munin hali musifa ce, mafiya munin halin ku kuma sune ashararan ku.”
A wani gurin kuma yace:
“Ya bani Abdul Mudallibi ba za ku taba wadatar da mutane da dukiyar ku ba, dan haka ku nemi yardar su da sakin fuska da fara’a.”
Littafin wasa’ilul shi’a Juzu’i na 2, shafi na 222
Malik ibnu Anas mai yiwa Manzon Allah (s.a.w) hidima ya kasance yana cewa:
“Nayi shekaru goma ina yiwa Manzon Allah (s.a.w) hidima, amma bai taba ce mini kaito ba, ko kuma dan me baka aikata ba, ko kuma kada ka aikata.”
Littafin Fadha’ilul khamsa, Juz’i na1, shafi na 119.
Kyawun hali da nishadi na daga cikin abubuwan da ke karawa mutum nisan kwana.
Imam Sadik (a.s) yace:
“Da’a da kyawun hali suna habaka Kasashe kuma suna tsawaita rayuwa.”
Littafin wasa’ilul shi’a, Juz’i na 2, shafi na 221.
Wani likita mai suna Dakta Sanderson ya rubuta cewa:
“Nishadi na daga cikin abubuwa muhimmai wajen warkar da cututtuka da rigakafin su. Yawanci magungunan cuta da na rigakafi su kan warkar da cutar na dan gajeren lokaci ne, sa’annan ta dawo, har ila yau kuma hucewar maganin kan ba da sakamako mummuna, alhali kuwa nishadi ya kan ba da sakamako na dindindin a kowane bangaren jiki. Nishadi ya kan kara hasken ido, ya kan tsananta digadigai ya karfafa su. Gudun jinin masu kyawun dabi’u yafi gaggawa, kuma sun fi isasshiyar lafiya sun fi lafiyayyen numfashi, cuta kuma ta fi yin nesa daga gare su.”
Littafin Pirozi Fikr
Abun da zamu lura da shi a maganar nan ta Imam Sadik (a.s), shine inda ya hada kyautatawa da kyawun hali ya kuma kidaya su a cikin abubuwan da ke kara nisan kwana. Dalili kuwa shine mai kyautatawa yana jin farin ciki da nishadi a zuciyar sa saboda kyautatawar sa, dan haka da kyakkyawan aiki da mai kyakkyawan aikin sai sakamakon su ya zama daya.
Imam Sadik (a.s) har wa yau ya kidaya wannan sifa daga cikin abubuwan farin ciki inda yace:
“kyakkyawan hali yana daga farin cikin mutum”
Littafin Mustadrakul masa’il, Juz’i na 2, shafi na 83
Samuel smiles ya ce:
“Akwai wata mashhuriyar magana da ke cewa: kyawun hali da danne harzukar zuciya suna da tasiri a ci gaban mutum da jin dadin sa kamar yadda su kuma karfin ruhi da kintsuwarsa suke tasiri a kan su. Alal hakika jin dadin kowa ya ta’allaka ne ainun da kyawun dabi’ar sa da abotartar sa…”
Littafin Akhlak
Kyawun hali yana wajabta wadata a rayuwa da karuwar arziki da farin jini. Imam Ali (a.s) yace:
“Kyawun hali yana yalwata arziki kuma yana debe hason abokai.”
Littafin Gurarul Hikam shafi na 279
Swart Arden ya kawo a littafin sa cewa:
“Na san shugaban wani hotel da ya shahara kuma ya azurta saboda kyawun halin sa, yadda har matafiya da masu yawon shakatawa da suke yin doguwar tafiya domin kyakkyawar mu’amala tamkar suna gidan su ne. Da zarar matafiya sun iso za a karbe su cikin fara’a da farin ciki irin wadda ba a yi musu a sauran hotel-hotel. Hasali ma ba sa ganin irin sanyin jiki da jinkirin nan masu gundurar baki kamar yadda ake yi a sauran hotel. A koyaushe ma’aikatan wannan hotel din suna kokarin kulla abota da kauna a tsakanin su da bakin su, ba sa tsayawa mu’amalar abokan cinikayya kawai. Sun kasance suna sake musu fuska suna himmatuwa kwarai da ayyukan su dan kauna da son baki da son yin mu’amala da su. Wannan shi yasa dukkan bakin suna jin sun shaku ainun da wannan hotel din yadda ba za su iya rabuwa da shi ba, hasali ma har su kan gayyato ‘yan uwa da abokan arzikin su domin su zo su sauka a wannan hotel din. A bayyane yake cewa irin wannan halayya tana jawo jama’a.”
Sa’annan ya kara da cewa:
“A duk tsawon tarihi kyawawan dabi’u da ladubba ba su sami irin kimar da suke da ita a wannan zamanin ba. A yau, kyawawan dabi’u da jawo jama’a a jika da ciyar da su gaba suna daga cikin halayen da suka wajaba duk wani mai son alheri a rayuwa ya zama yana dasu.”
Littafin Khishtan Sazi
Imam Sadik (a.s) kuma ya nuna cewa, sakin fuska alama ce ta kamalar hankalin mutum, inda yace:
“Wanda yafi mutane kamalar hankali shine wanda ya fi su kyakkyawan hali.”
Littafin Wasa’ilul shi’a, Juz’i na 2, shafi na 201
Samuel smiles ya ce:
“Tarihi ya nuna mana cewa mashhuran manyan magabata, mutane ne masu farin ciki da fara’a. Tun da su sun riga sun fahimci manufar rayuwa kuma ba su rabu da hankalin su ba. Duk lokacin da mutum ya yi nazarin tarihin su zai fahimci kaifin hankalin su da kyawun zuciyar su a nisahdin su da abotar su. Madaukaka masu lafiyayyen ruhi, masu cikakken hankali masu hikima duk suna da fara’a da sakin fuska. Halayen su abin koyi ga wanda yake tare da su kuma yake ganin haske da nishadin su da kyakkyawar dabi’ar su.”
Littafin Akhlak
Manzon Allah (s.a.w) ayce:
“Mafi yawancin abubuwan da al’umma ta za ta shiga aljanna saboda su, sune, tsoron Allah da kyawawan dabi’u.”
Littafin Wasa’ilul shi’a, Juz’i na 2, shafi na 221
Dan haka ya kamata duk wanda hankali yake masa jagora kuma yana son ya yi rayuwa ta mutunci ya tanada wa kansa wadannan kyawawan halaye masu kima. Mutum yana bukatar himma mai karfin gaske da tsayuwar daka domin rabuwa da munanan dabi’u. La’akari da illolin da munanan dabi’un mutum suke jawo masa, ya isa yasa ya shiga hankalin sa ya yi damarar yaki da su.
KYAUTATA DABI’U
Sidi Mujtaba Musawi Lari
Fassarar: Yakubu Abdu Ningi
Editoci: Yusif Saleh Gwani da Muhammad Awwal Usman Kunya
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)