Sanin Imam Mahdi
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI
Jagoran Shi’a na karshe kuma halifan Manzon Allah (s.a.w) na goma sha biyu, ya zo Duniya ne a ranar juma’a a watan sha’aban shekarar hijira kamariyya 255, wato miladiyya 868 a garin Samra’u (ko samarra) daya daga garuruwan Iraki. Babansa shi ne imamin Shi’a na goma sha daya Imam Hasan Askari (a.s) kuma babarsa ita ce: "Narjis” wacce a wata ruwaya ya zo cewa tana daga zuriyar Yasha’u ne dan shugaban Rum, kuma babarsa daga zuriyar Sham’un take wasiyyin Annabi Isa (a.s). A wata ruwaya ya zo cewa: Narjis ta tafi yaki ne da shiryarwa da kuma umarnin Imam Hasan Askari (a.s) sannan kuma a yaki ta fada cikin ribatattun yakin musulmi, sannan sai Imam Hasan da kansa ya aika wani domin ya je ya sayo masa ita ya kuma kawo masa ita garin Samra’u . Amma abin da yafi muhimmanci shi ne Narjis ta kasance a karkashin kulawar Hakima ‘yar’uwar Imam Hadi (a.s) kuma ta samu ilimi da tarbiyya a hannunta kuma ta samu girmamawar Hakima sosai. Narjis ta samu yabo daga zantuttukan Manzo (s.a.w) da Imam Ali (a.s) da Imam Ja'afar Sadik (a.s) kuma sun yaba ta sosai, sun kuma ambace da mafificiyar baiwa. Kuma akwai wasu sunaye da suka zo game da sunan mahaifiyar Imam Mahadi (a.s) kamar; Susan, Raihana, Malika, Saikal.
Suna Da Alkunya Da Lakabi
Sunan Imam Mahadi da alkunyarsa kamar suna da alkunyar Annabi (s.a.w) ne, a wasu ruwayoyi kuwa an hana ambaton sunansa har sai ya bayyana. Lakabin da ya shahara su ne Mahadi, ka’im, bakiyyatul-Lahi, muntazar, hujjat, khalaf salih, mansur, sahibul amr, sahibuz zaman, waliyyul asr wanda mafi shahararsu shi ne Mahadi. Kowanne daga wadannan lakabobi yana bayar da wani sako game da wannan Imami mai girma ne.
An ce ana ce masa Mahadi ne saboda shi ne zai shiryar da mutane zuwa ga gaskiya, kuma ana ce masa ka’im domin shi ne zai tashi da yaki, kuma ana cewa da shi muntazar domin ana sauraron zuwansa, kuma ana ce masa bakiyyatul-Lahi domn shi ne ya rage daga cikin hujjojin Allah a bayan kasa. Kuma hujja yana da ma’anar mai sheda ga bayi, kuma khalafussalih da ma’anar cewa shi ne halifan waliyyan Allah da suka gabata, kuma ana ce masa mansur domin Allah zai taimake shi, kuma sahibul amr domin shi ne wanda zai samar da hukuma mai tsayar da umarnin Allah da adalcin Allah, kuma shi ne sahibuzzaman da kuma waliyyul asr da ma’anar wanda yake shi ne mai hukunci da umarni shi kadai a wannan zamani.
Yanayin Haihuwarsa
Ruwayoyi masu yawa sun zo daga Manzon Allah game da cewa wani zai zo mai suna Mahadi daga zuriyarsa kuma zai tsayu da gina adalci, kuma shugabannin Abbasawa saboda wannan ruwaya ne suke son su kashe Imam Mahadi (a.s) tun farkon haihuwarsa. Saboda haka ne ma tun lokancin Imam Jawad (a.s) rayuwar imamai ta fara samun takurawa mai tsanani, kuma a lokacin Imam Hasan Askari (a.s) ta kai matuka ta yadda mafi karancin motsinsa da kai-kawon gidansa suka zama karkashin kulawar hukuma da ba abin da ya buya garesu. A fili yake cewa a irin wannan yanayi haihuwar hujjar karshe kuma alkawarin Allah dole ne ta zama a boye kuma nesa daga idanuwan wasu mutane. Don haka ne ma hatta makusanta Imam Hasan Askari ba su da masaniya game da haihuwar Imam Mahadi, kai har zuwa wasu awowi kafin haihuwarsa ba a ga alamar ciki ga mahaifiyarsa ba.
Hakima ‘yar Imam Jawad (a.s) tana fada game da abin da ya faru a haihuwarsa (a.s) da cewa: Imam Hasan (a.s) ya aika a kirawo ni, ya ce: Ya ammata! Yau da dare ki kasance tare da mu! Domin yau daren rabin sha’aban ne, kuma Allah (s.w.t) a wannan daren ne zai bayyanar da hujjarsa na karshe a bayan kasa.
Sai na tambaya wace ce babarsa, sai ya ce da ni Narjis! Sai na ce: Amma ai ba ta da alamar ciki! Sai ya ce: wannan shi ne abin da nake gaya maka! Sai na shiga wajan Narjis, na yi sallama na zauna. Ina shiga sai ta gaggauto wajena ta kwabe mini takalmana ta ce da ni: Yaya kike ne tawa? Sai na ce: Ai ke ce tawa kuma ta cikin dangina! Amma ba ta yarda da abin da na fada ba, amma sai ta ce da ni, ya ammata mene ne? Sai na ce: ya ‘yata, yau da dare Ubangiji madaukaki zai ba ki da wanda zai zama jagoran Duniya da lahira gaba daya, sai ta ji kunya.
Hakima tana cewa: Bayan sallar isha sai na ci, na sha ruwa, na kishingida kan shimfidata, a tsakiyar dare na tashi domin yin sallar dare, na idar da sallar, a wannan lokaci Narjis tana bacci ba tare da wani abu ya same ta ba, bayan na gama wuridin bayan salla sai na yi bacci. Sannan sai firgigi na tashi, amma har wannan lokaci tana bacci, sannan sai ta tashi ta yi sallar dare ta koma bacci.
Hakima ta kara da cewa: Sai na fito waje ina kallon sama ko zan ga alfijir ya keto. Sai na ga alfijir din farko amma Narjis har wannan lokaci tana cikin bacci, sai na fada kokwanto! Bagatatan sai na ji kira daga wajan da Imam Hasan Askari yake yana cewa: Ke amma kada ki gaggauta, al’amarin haihuwa ya kusata. Sai na zauna ina karanta surar sajadati da kuma yasin, sai Narjis ta tashi da rawar jiki. Sai na gaggauta zuwa wajanta na ce: Ismul-Lahi alaiki. [Sunan Allah ya tabbata a gareki] shin kina jin wani abu ne?. Ta ce haka ne ya ammata. Sai na ce ki samu nutsuwa waje daya ki kuma daidaita zuciyarki, domin wannan shi ne abin nan da na gaya miki. A wannan lokaci sai wani rauni ya same ni da ni da Narjis. Sai na ji kira daga shugabana [jaririn da aka haifa] ya zo da kansa, na dauke lullubin da yake jikinsa, sai na same shi a cikin sujada! Na kuma dauke shi, na kuma same shi da cikakken tsarki! A wannan lokaci ne Imam Askari (a.s) ya kira ni: Ya amma kawo mini dana! Sai na kai masa shi, ya dora shi a kafadarsa ya ce: Ya dana ka yi magana, sai ya bude bakinsa ya ce: Ash’hadu an la’ilaha illal-Lah wahdahu la sharika lah, wa ash’hadu anna Muhammadar rasulullah. Sai kuma ya nemi tsira da amincin Allah ga Imam Ali (a.s) da imamai biyu -Hasan da Husain- (a.s) har ya kai zuwa ga sunan babansa (a.s). Sai Imam Askari ya ce: Ya amma mayar da shi wajan babarsa domin ya nema mata tsira da amincin Allah.
Hakima ta ce: Wani mutum a wannan rana ya zo wajan Imam Askari ya yi masa sallama, na kawar da labule domin in ga shugabana (Imam Mahadi (a.s) amma sai ban gan shi ba, sai na tambayi babansa (a.s), ina fansarka da raina yaya ban ga shugabana ba? Sai ya ba ni amsa da cewa: Na bayar da ajiyarsa wajan wanda babar Musa ta bayar da ajiyar Musa (a.s) wajansa.
Hakima ta ce: Ranar da rana ta bakwai ta zagayo, sai na yi sallama na zauna. Amma Imam ya ce. Kawo mini dana, sai na kawo shugabana. Imam (a.s) ya ce: Ya dana yi magana! Sai jaririn ya bude bakinsa bayan ya yi kalmar shahada da kadaita Allah da mika gaisuwa da aminci zuwa ga Manzon Allah (s.a.w) da kakannisnsa ma’asumai (a.s) sai ya karanta wadannan ayoyi na Kur'ani mai girma: "Da sunan Allah mai rahama mai jin kai. Muna son mu yi baiwa ga wadanda aka raunatar {zalunta da kuntatawa} a bayan kasa mu sanya su shugabanni mu kuma sanya su masu mayewa {gajewa}, kuma mu ba su iko a bayan kasa, mu nuna wa Fir’auna da Hamana da rundunarsu abin da suka kasance suna gudunsa” .
Siffofin Imam Mahadi
Siffofin Imam Mahadi (a.s) da dama sun zo a ruwayoyi daga Manzon Allah da Ahlul Baiti (a.s) wadanda zamu yi nuni da wadansunsu a nan:
Fuskarsa ta samari ce, goshinsa yana da tsayi kuma mai haske ne, girarsa kamar jinjirin wata, idanuwansa bakake ne kuma masu girma, hancinsa madaukaki ne kuma mai kyau, hakoransa masu haske ne, a tsakanin habarsa akwai wata alama kamar alamar Annabi, jikinsa madaidaici ne.
A wata ruwaya ta zo da siffofinsa kamar haka; Shi mai ibada ne, mai raya dare, mai hakuri da adalci da kyayawan ayyuka, …shi ne ma’abocin tashi da gwagwarmaya da jihadi, shugaban Duniya, mai tseratarwa, mai gyara mai girma, shi samuwa ne mai haske daga zuriyar Manzon Allah (s.a.w) daga kuma ‘ya’yan fadima (A.S, kuma na tara daga zuriyar Imam Husaini (a.s) wanda a lokacin bayyanarsa zai dogara a jikin ka’aba ne, ya kuma rike tutar Manzon Allah (s.a.w), kuma da gwagwarmayarsa ne zai raya addinin Allah (s.w.t) ya kuma aiwatar da hukuncin Allah a duk fadin Duniya, ya kuma cika Duniya da tausayi da adalci bayan an cikata da zalunci .
Marhaloli Uku A Rayuwar Imam Mahadi (a.s)
1- Zamanin boyewa; rayuwa a boye da ta fara daga lokacin haihuwarsa zuwa lokacin shahadar babansa Imam Hasan Askari (a.s).
2- Zamanin boyuwa; da ya fara daga lokacin shahadar babansa Imami na sha daya (a.s) zuwa lokacin da zai bayyana da nufin Allah da umarninsa.
3- Zamanin bayyanarsa: bayan tsawon lokaci yana mai boyuwa zai bayyana da nufin Allah (s.w.t) zai cika dukkan Duniya da kyawawan abubuwa da kuma ado da kawa. Babu wani wanda ya san lokacin bayyanarsa kuma an rawaito daga gareshi cewa wadannan da suke ayyana lokacin bayyana makaryata ne .