Muassasar alhasanain (a.s)

BABBAR FITINA 1

4 Ra'ayoyi 02.3 / 5

BABAR FITINA

 

Babu wani marubuci, komai kwarewarsa wajen fahimtar abubuwan da suka faru a tarihi, da zai iya fahimtar hakikanin abin da ya sami al’ummar musulmi bayan wafatin Annabi (s.a.w) sama da yadda da yadda Alkur’ani mai girma ya bayyana hakan. Allah Madaukakin Sarki na cewa:

﴿وَمَا مُحَمَّدٌ إِلاَّ رَسُولٌ قَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِهِ الرُّسُلُ أَفَإِن مَّاتَ أَوْ قُتِلَ انقَلَبْتُمْ عَلَى أَعْقَابِكُمْ وَمَن يَنقَلِبْ عَلَىَ عَقِبَيْهِ فَلَن يَضُرَّ اللّهَ شَيْئًا وَسَيَجْزِي اللّهُ الشَّاكِرِينَ

“Kuma Muhammad bai zama ba face manzo, lalle ne manzanni sun shude a gabanninsa. Ashe idan ya mutu ko kuma aka kashe shi, za ku juya a kan dugaduganku? To wanda ya juya a kan dugadugansa, ba zai cuci Allah da komai ba. Kuma Allah Zai saka wa masu godiya”[1].

Hakika dubi sosai cikin bala’in da bakar fitinar da ta fada wa al’umma bayan wafatin mai cetonta (Annabi Muhammad) za a iya fahimtar cewa lalle juyawa ne a kan dugadugai, ruguza tushen al’umma, juya baya ga akida da kuma karen tsaye wa shari’ar Ubangiji. Shin akwai wata girgizar kasa da ta wuce wannan girgizar?

Tun ma kafin Manzon Allah (s.a.w) ya koma ga Mahaliccinsa alhali yana gidansa a kwance (cikin rashin lafiya) rarrabuwa mai hatsarin gaske da fitina mai girma tsakanin al’ummarsa ta kunno kai, wacce ita ce masdarin babbar fitinar da ta sami al’ummar musulmi kuma ta zamanto musu babbar jarabawa tsawon tarihi. Yanzu bari mu kawo – a takaice – kadan daga cikin abubuwan da suka faru jin kadan bayan rasuwar Manzon Allah (s.a.w), su ne:

TARON SAKIFA

A hakikani gaskiya ban taba ganin wani lamarin da yafi zama hatsari ga Musulunci kuma wanda yafi cutarwa ga musulmi kamar taron Sakifa da Ansarawa suka shirya don rike madafan mulki ba. Hakan shi ne ummul aba’isin din rarrabuwan kan al’umma da irin bala’oin da suka fada musu. Bolis Salama yana cewa:

Abubuwa sun jeru karkashin taron Sakifa

Wadanda suka motsar da mu suka jawo hankula.

Jayayya wadda ta kawo rarraba tamkar rassan

Itacen ausajah…..

Jim kadan da rasuwar Ma’aiki (s.a.w) sai Ansarawa cikin gaggawa suka shirya wannan taro saboda sun ga wasu shirye-shirye na siyasa da wasu daga cikin manyan Muhajirai da ke adawa da Imam Amirul Muminin (a.s), saboda irin kashin da ya ba wa Kuraishawa da girbe kawukan manyansu da yayi, suke yi. Yayin da yake nuni da irin adawar da Kuraishawa suke yi da Imam Ali (a.s) da kokarin da suke yi na daukan fansa a kansa, Al-Kinani yana cewa:

A dukkan taron jama’a, akwai wata gaya da ta kunyata ku,

Gajiyawa wajen halaka…..

Wannan da ga Fatima[2] wanda ya karar da ku,

Yanka da kisa, wasu ba tare da yanka ba.

Wadannan baituka suna nuni da irin gaba da adawar da Kuraishawa suke nuna wa Imam Amirul Muminin Ali (a.s) wanda ya kunyata da tarwasu saboda daukakar tafarkin Musulunci lokacin da suka tsaya da dukkan karfinsu wajen ganin sun dushe hasken Musulunci da mayar da al’umma bisa tafarkin Jahiliyya.

Ala kulli hal, su dai Ansarawa wadanda su wani sashi ne na karfin da Musulunci yake da shi a bangaren makamai sun fahimci cewa matukar Kuraishawa suka rike madafun mulki (halifanci) za su mayar da su saniyar ware da kuma kokarin daukan fansa a kansu kamar yadda Habbab bn al-Munzir ya bayyana musu a fili lokacin da yake gabatar da jawabinsa a Sakifa yana cewa:

“Mu dai muna tsoron madafan mulkin su fada hannu wasu a bayanku wadanda muka kashe musu ‘ya’yansu da iyayensu da ‘yan’uwansu…” abin da Al-Munzir din yake tsoro shi ne kuwa ya faru, saboda lokacin da Kuraishawa suke rike madafan mulki sai suka yi kokarin zaluntar Ansarawa da yada talauci da rashi a tsakanisu. Mu’awiyya bn Hind yayi iyakacin kokarinsa wajen daukan fansa a kansu kamar yadda dansa Yazid bn Mu’awiyya ya aikata da su yayin da ya halalta dukiyarsu da jininsu da mutumcinsu ga sojojinsa karkashin jagoranci dan’ta’addan nan Muslim bn Ukbah wanda malaman tarihi suke kiransa da ‘Mai wuce haddi’ hakan kuwa saboda abin da ya aikata ne a waki’ar al-Harra da tarihi bai taba ganin irinta ba wajen muni da tada hankali.

ªMamaye Sakifa Da Kuraishawa Suka Yi

A daidai lokacin da Ansarawa suke ci gaba da taronsu a Sakifa da musanyan ra’ayi kan lamarin halifanci, har sun kusan cimma matsayar zabar shugabansu Sa’ad bn Ubadah a matsayin halifa, kwatsam sai wasu daga cikinsu dake da alaka da Abubakar suka fita daga dakin taron, daga cikinsu akwai: Uwaim bn Sa’ida al-Awsi, Mu’in bn Adi Halif al-Ansari da sauransu, cikin sauri suka nufi wajen Abubakar da Umar suka sanar da su abin da ake ciki, su kuwa tare da Abu Ubaida bn al-Jarrah da Salim Maula Abi Huzaifa da wasu jama’a ba tare da bata lokaci ba suka nufi dakin taron Sakifan, inda nan take suka mai da hannun agogo baya ga Ansarawan da kwace komai daga hannunsu. Ta haka suka rusa dukkanin shirye-shiryen Ansarawa na rike madafun mulki.

ªHudubar Abubakar

Bayan wasan kurar da Muhajirai suka yi da taron Ansarawa a Sakifa, halifa Umar ya so ya fara magana amma sai halifa Abubakar ya hana shi saboda masaniyar da yake da shi na irin tsanani da kaushin halinsa da ba ta yi daidai da irin halin da ake ciki a wancan lokacin ba da ake bukatar sausauci don janyo hankula da tabbatar da doka da oda. Sai Abubakar ya kalli Ansarawa da murmushi yana cewa:

“Mu Muhajirai mu ne musulmin farko cikin musulmi, kuma wadanda suka fi su kyautatawa da matsayi sannan suka fi su cancanta ga Manzon Allah (s.a.w), ku kuwa ‘yan’uwanmu ne a Musulunci, abokanmu a addini, kun taimaka, Allah Ya saka muku da alheri. Don haka mu ne shugabanni ku kuma mataimaka. Larabawa ba za su amince da wanda ba Bakuraishe ba. Kada ku yi gasa da ‘yan’uwanku Muhajirai kan abin da Allah Ya daukaka su da shi. Ni na yarda muku da ku zabi daya daga cikin wadannan mutane biyu – wato Umar bn al-Khaddab da Aba Ubaidah bn al-Jarrah –a matsayin halifa”[3].

Duk wannan jawabi na Abubakar yayi shi ne alhali ya mance da batun wafatin Ma’aiki (s.a.w) wanda shi ne babbar musibar da ta fada wa musulmi. Abin da yafi dacewa shi ne Abubakar ya isar da ta’aziyyarsa ga musulmi kan rashin da suka yi na mutumin da ya ceto su daga duhu, da gaggauta yi masa jana’iza da rufe shi a makomarsa ta karshe, daga baya kuma sai a dawo a shirya wannan taro da zai kumshi dukkanin kungiyoyin musulmi don su zabi wanda zai zamanto musu halifa cikin ‘yanci da son zuciyarsu hakan ma idan har a ce Manzon Allah (s.a.w) bai ayyana wani mutum guda da zai rike wannan matsayi a bayansa kenan ba.

Har ila yau wannan huduba ta mance da tsarkakakkiyar zuriyar Ma’aiki wacce ita ce ‘yar’uwar Alkur’ani mai girma, amma haka aka mance da ita. Abin da yafi dacewa ga Abubakar shi ne ya saurari ra’ayin Zuriyar Ma'aiki don halifancin ya samu halalci na shari’a. Imam Sharafuddeen, Allah Ya yi masa rahama, yana cewa:

“Idan ma abin mu dauka cewa babu wani nassi kan halifancin wani daga cikin Zuriyar Muhammad (s.a.w), kuma mu dauka cewa ba su ne kan gaba ba wajen halifanci saboda nasaba ko kyawawan dabi’u ko jihadi ko ilimi ko aiki, ko don imani da ikhlasi, kai ba su ma da wata daukaka ta azo a gain, matsayinsu tamkar na sauran sahabbai ne, to shin akwai wani dalili na shari’a ko na hankali ko kuma na dabi’ar al’umma da zai hana a jinkirta yin bai’a har sai an gama da jana’izar Manzon Allah (s.a.w) ko da kuwa za a mika al’amarin kula da tsaro da doka da oda ne ga kwamandojin soji na wani lokaci kafin a tabbatar da halifa.

Ashe wannan dan jinkiri ba zai zamanto tausayawa ba ga wadannan mutane wadanda amanar Annabi (s.a.w) ke wajensu. Allah Ta’ala yana cewa: “Lalle ne, hakika Manzo daga cikinku ya je muku. Abin da kuka wahala da shi mai nauyi ne a kansa. Mai kwadayi ne saboda ku. Ga muminai Mai tausayi ne, Mai jin kai”[4], ashe ba hakkin wannan Manzo – wanda abin wahalar al’ummarsa ya zamanto masa mai nauyi ba, wanda yake nuna damuwa ga sa’adarta kuma mai tausayi gare ta da jin kanta – ba ne ya nuna damuwa ga zuriyarsa, kada ta fuskanci abin da ta fuskanta ba….”[5].

Haka nan wannan huduba ba ta tabo abin da al’umma take bukata ba a bangaren tattalin arziki, siyasa da zamantakewa, face dai cike take da batun neman mulki, da bukatar Ansarawa da su bar musu mulkisu kuma suzama mataimaka, duk da cewa hakan ma ba ta samu ba lokacin da suka amince suka bar masa mulkin.

ªDarewa Karagar Mulkin Abubakar

Haka Abubakar ya samu nasarar zama halifa ta hanyar hikima da diplomasiyyarsa sakamakon yabon Ansarawa da yayi da jinjina musu kan irin kokarin da suka yi. Da haka ne ya kashe wutar boren dake zukatansu. Rikici dai ya barke tsakanin halifa Umar da wasu Ansarawa sai dai Abubakar ya iya samun nasarar kashe wutar rikicin, inda nan take mabiyansa suka gaggauta yi masa bai’a saboda tsoron da suke da shi kan yiyuwar tabarbarewar lamurra. Daga cikin mabiyansa wanda ya fi kowa zakalewa wajen gaggauta yi masa bai’a shi ne halifa Umar bn Khaddabi wanda ya ta kai gwauro ya kai mari wajen sanya mutane yin bai’ar. Hatta lokacin da yaji Ansarawa suna cewa:

- “Kun kashe Sa’ad…”

Sai ya juyo cikin fushi yana cewa:

- “Ku kashe shi, Allah wadaransa, saboda shi fitinanne ne…”[6].

Lokacin da aka gama bai’a ga Abubakar sai jama’arsa suka kewaye shi, suka gaggauta kai shi masallacin Manzon Allah (s.a.w) kamar yadda ake kai amarya[7].

 

ZAMU CI GABA A MAKALA MAI ZUWA:-

 

 

[1]- Suratu Ali Imrana 3:144.

[2]- Fatima: Ita ce Sayyida (Fatima) bint Asad mahaifiyar Imam Amirul Muminin (a.s).

[3]- Tarikh al-Dabari, 3/62.

[4]- Suratut Tauba, 9:128.

[5]- An-Nass wa al-Ijtihad, shafi na 7.

[6]- Al-Akd al-Farid, 3/62.

[7]- Sharh al-Nahj 2/8.

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)