BABBAR FITINA 5
FITINA
Shi kuwa Khuzaimah bn Thabit[1] yana daga cikin fitattun mujahidan Musulunci kuma daga cikin fitattun sahabban Annabi (s.a.w). Shi ma ya nuna rashin amincewarsa da kwace halifanci da aka yi daga wajen Zuriyar Ma’aiki (s.a.w). Ga abin da yake cewa:
“Ya ku mutane! Ashe ba ku san cewa Manzon Allah (s.a.w) ya amince da shahadata ni kadai (ba tare da wani mutum dai karfafata) ba? Sai suka ce na’am, sai ya ce: To ku shaida cewa naji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: Ahlubaiti su ne masu bambance gaskiya da karya, su ne shugabannin da ake riko da su, hakika na isar da abin da na sani, kuma babu abin dake kan Manzo face isarwa bayyananniya…”.
Wannan huduba tana kira ne zuwa ga riko da tsarkakakkiyar Zuriya wacce Allah Ya tafiyar da dauda daga gare ta, kuma Ya tsarkaketa tsarkakewa da komar da halifanci zuwa gare ta.
Abu al-Haitham bn al-Taihan ya kasance daga cikin zababbun sahabbai[2] ta bangaren imani, akida da mika wilaya ga Imam Amirul Muminin Ali (a.s). Yana daga cikin wadanda suka nuna rashin amincewarsu ga Abubakar saboda rike halifanci da yayi, yana cewa:
“Lalle na shaida cewa Annabinmu (s.a.w) ya zabi Ali[3](a matsayin halifansa) Sai wasu Ansarawa suka ce: lalle ba zabe shi ba, wasu daga cikinsu suka ce: Bai zabe shi ba face dai ya sanar da mutane su san cewa shi majibincin (maula) wanda Manzon Allah (s.a.w) ya zamanto majibincinsa ne. Da kace-nace yayi yawa kan hakan sai muka aika da wasu mutane daga cikinmu zuwa ga Manzon Allah (s.a.w) suka tambaye shi kan hakan, sai ya ce: Ku ce musu: Aliyu shi ne shugaban muminai a bayana, kuma wanda ya fi dacewan mutane ga al’umma. Na shaida abin da yazo min, wanda ya so yayi imani, wanda kuma yaso ya kafirta, Lalle ne ranar rarrabewa ta kasance abin kayyade wa lokaci….[4]”.
Wannan huduba tana nuni da cewa Manzon Allah (s.a.w) ya zabi Imam Ali (a.s) a matsayin halifa a bayansa, ya ba shi matsayin halifanci da imamanci. Bisa wannan asasi ne Shi'a Imamiyya ta gina akidunta.
Shi kuwa Sahl Ibn Hunaif[5] yana daga cikin sahabban farko-farko da suka yi imani da sakon Ma’aiki (s.a.w) da kuma yin jihadi fi sabillillah. Ya nuna rashin amincewarsa ga Kuraishawa kan kwace halifanci daga wajen Imam Amirul Muminin Ali (a.s) da suka yi. An ruwaito shi yana ce musu:
“Ya ku Kuraishawa! Ku shaida na ga Manzon Allah (s.a.w) a wannan waje – wato a masallacinsa – ya daga hannun Ali bn Abi Talib yana cewa: Ya ku mutane ga Ali nan shi ne shugabanku a bayana, kuma wasiyina a rayuwata sannan a bayan rasuwata, mai biyan bashina, mai aiwatar da alkawurrana, kuma na farko da zai riske ni a (bakin) tafki. Madalla ga wanda ya bi shi, bone kuma ga wanda ya saba masa…[6]”.
Wannan huduba tayi ishara da daya daga cikin nassosin da Manzon Allah (s.a.w) yayi amfani da su wajen tabbatar da halifancin Imam Amirul Muminin Ali (a.s) a bayansa.
Usman bn Hunaif yana daga cikin zababbun sahabban Manzon Allah (s.a.w). Ya nuna rashin amincewarsa ga Abubakar dangane da hawa kujerar halifanci da yi yana ce masa:
“Mun ji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: Ahlubaitina su ne taurarin kasa don haka kada ku wuce gabansu, maimakon haka ku gabatar da su don su ne shugabanni a bayana. Sai wani mutumi ya tashi ya ce: Ya Rasulallah! Wane daga cikin Ahlubaitin naka? Sai ya ce: Aliyu da tsarkaka daga cikin ‘ya’yansa, Manzon Allah (s.a.w) ya yi bayaninsu, don haka kada ka zamanto mutumin farko da zai kafirce masa Ya Aba Bakar, kada ku yaudari Allah da ManzonSa, kuma ku yaudari amanoninku, alhali kuwa kuna sane…”.
Wannan huduba tana kira ne zuwa ga gaskiya da kare al’umma daga rarrabuwa, amma handama ta siyasa ta hana su amsa wannan kira.
Abu Ayyub al-Ansari[8] yayi amanna da cewa Imam Amirul Muminin Ali (a.s) shi ne wanda yafi wasunsa cancantar halifancin musulmi. Don haka ne ma ya yi inkarin halifancin Abubakar yana ce masa da ’yan kungiyarsa:
"Ku ji tsoron Allah bayin Allah cikin Ahlulbaitin Annabinku, ku mayar musu da hakkin da Allah Ya sanya musu. Hakika kun ji abin da 'yan'uwanmu suka ji daga wajen Annabinmu (s.a.w) dangane da wannan matsayi, a lokuta da dama ya sha fadin cewa: Ahlulbaitina su ne shugabanninku a bayana" sannan ya nuna Ali (a.s) yana cewa: Wannan shi ne shugaban masu tsoron Allah, mai kashe kafirai, watsatse ne wanda yayi watsi da shi, sannan kuma wanda ya taimake shi (Allah) Zai taimake shi", ku tuba wa Allah daga ayyukanku don Allah Mai karban tuba ne mai rahama, kada ku juya masa baya juyawa, sannan kada ku kaurace masa….[9]".
Da haka ne za mu kawo karshen magana kan rashin amincewa da inkari mai tsanani da tsarkakan Zuriyar Annabi da Allah Ya tafiyar da kazanta daga gare su da tsarkake su tsarkakakewa tare da fitattun sahabbai suka nuna wajen tabbatar da hakkin Imam Amirul Muminina (a.s) kan halifanci da shugabancin al'ummar musulmi bayan Ma'aiki (s.a.w).
Ala kulli hal, babu shakka waki'ar Sakifa ita ce masdarin babbar fitinar da ta samu musulmi tsawon tarihi. A hakikanin gaskiya fitinar da ta faru tsakanin musulmi ba wai ta faru ne lokacin Usman da Ali ba, kamar yadda malamin adabin larabcin nan Dakta Taha Husain ya bayyana cikin littafinsa al-Fitnatul Kubra.
Shi'a sun yi dubi da idon basira cikin hadisan da suka fito daga Annabi (s.a.w) kan falala da daukakar Zuriyarsa, da kuma abin da ya ce kan dan'uwansa kuma dan baffansa Imam Amirul muminina (a.s) na falala da daukaka, shi ne kofar birnin iliminsa, kuma matsayinsa a wajensa tamkar matsayin Haruna ne ga Musa, kuma shi ne shugaban dukkanin muminai, maza da mata a bayansa – kamar yadda yace-. 'Yan Shi'a sun yi imanin da babu shakka cikinsa cewa shi ne halaltaccen halifan Manzon Allah (s.aw.a) kai tsaye. Hakan kuwa ba wai lamari ne da suka rika saboda son kai da koyi ido rufe ba, face dai sun dogara ne da nassosi na Alkur'ani da Sunna da ba za su iya kau da kai daga gare su ba. A bahasin da ya wuce mun yi ishara da wadannan hadisai.
ªMummunan Hali da Aka Bari
Raba Ahlulbaiti (a.s) da halifanci ya haifar da gagarumin rikici da bala'i da jarabawa mai girma gaske da musulmi suka fuskanta wadanda suka haifar da rarrabuwa tsakanin musulmi. Babban abin da yafi daga hankali da cin rai shi ne yadda halifanci na Musulunci, wanda shi ne inuwar Allah a bayan kasa da ke kula da al'amurran da suka shafi makomar al'umma, ta zamanto abin wasa a hannun Umayyawa da 'yan'uwansu Abbasiyawa. Sun mayar da dukiyar Allah ta zamanto tasu, bayin Allah kuma haja, suna almubazzaranci da dukiyar musulmi ba tare da kula da hakkokin Ubangiji ba. Suka sa ma'abuta gyara a gaba da cutar da su musamman shugabannin Alawiyyawa, suka azabtar da su azabtarwa, suka kashe na kashewa a duk inda suka same su, kamar yadda kuma suka fada wa 'yan Shi'arsu. A nan gaba za mu yi magana kan irin matsalolin da suka fuskanta.
Ala ayyi hal, bari mu bar Sheikh Radhi al-Yasin ya bayyana mana munanan abubuwan da suka faru sakamakon hana Ahlulbaiti (a.s) hakkinsu na halifanci, yana cewa:
"Raba halifanci da Zuriyar Annabi (s.aw.a) shi ne asasin bambance bambance na shekaru tsakanin masoyan halifanci a duk zamunna kuma babban bala'i tsakanin musulmi. A hakikanin gaskiya musulmi za su iya tsira daga wadannan abubuwa da a ce halifanci – tun ranar farko – ya dau tafarkinsa na asali da ijithadi cikinsa ba ya halalta, sannan kuma siyasa ba ta shigo cikinsa ba, kuma babu wani da ya tsoma baki cikinsa in ban da Allah da ManzonSa".
﴿وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ وَلَا مُؤْمِنَةٍ إِذَا قَضَى اللَّهُ وَرَسُولُهُ أَمْرًا أَن يَكُونَ لَهُمُ الْخِيَرَةُ مِنْ أَمْرِهِمْ وَمَن يَعْصِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا مُّبِينًا﴾
“Kuma ba ya halalta ga mumini kuma haka nan ga mumina, a lokacin da Allah da ManzonSa Ya hukumta wani umurni, suna da wani zabi daga al’amarinsu ya kasance a gare su. Kuma wanda ya saba wa Allah da ManzonSa, to, ya bace, bacewa bayyananna” [10].
Rikice-rikice da fadace-fadacen da suka ta faruwa cikin musulmi daga wannan al'umma zuwa wancan sun samo asali ne sakamakon share fagen da aka yi wa masu kishirwan isa ga halifanci ta ko ta wace hanya. Haka nan kisan kiyashin da da kashe-kashen da ya dinga faruwa tsakanin musulmi cikin tarihin Musulunci, tsakanin Bani Hashim da Bani Umayya, tsakanin Banu Zubair da Banu Umayyah tsakanin Bani Abbas da Bani Umayyad a tsakanin Bani Ali da Bani Abbas….basu faru ba face sai saboda sakamakon karya tsarin da Manzon Allah (s.aw.a) ya tsara don ya zamanto garkuwa da kariya daga faruwar irin wannan mummunan yanayi mai ban haushi a Musulunci.
Haka nan musibar da ta fada wa Zuriyar Manzo da ba a taba ganin irinta ba – irinsu kisa, kwace da kora – ta faru ne sakamakon kuskuren farko da aka yi wajen saba wa siyasar Annabi (s.aw.a) kan abin da ya so wa al'ummarsa da kuma Zuriyarsa, da a ce sun yi masa biyayya da hakan ba su faru ba.
Sai dai sun jahilci hakikanin wannan siyasa, suna masu adawa da haduwar annabci da halifanci a gida guda[11], suka riki da wata siyasa ta daban.
Hakan wani uzuri ne na zahiri da masu shi suka rika wajen wasa da hankalin mutane. Amma dangane da boyayyiyar manufarsu kuwa (na kwace halifanci daga masu shi) babu wanda ya san ta in ba Masanin abubuwan da suka buya ba, sai dai mafi girman zato hakan ba zai rasa nasaba da yakukuwan da Musulunci yayi don kare tafarkinsa ko kuma hassada wacce 'take cinye addini kamar yadda wuta ke cinye itace', kamar yadda yazo cikin hadisi.
Son shugabanci da sha'awan mulki babban sharri da annoba ce da take lalata mutum, da ruguza manya da mafiya karfin shugabanni.
Annabci ko imamanci – a matsayinsu na mukami daga Ubangiji – ba waje ne na siyasa da ma'anar da aka fi saninta ba ne, saboda duk wata siyasa ta annabci ko wani abin da yake karkashinsa na gudanarwa wani sashi ne na addini, sannan kuma wanda ke da magana ta karshe cikin dukkan wadannan lamurra shi ne ma'abucin wannan addini, sannan maganarsa ita ce mai raba rigima[12]".
Ra'ayin mai girma Hujjatul Islam Al-Yasin ra'ayi ne tabbatacce, saboda bala'oin da suka fada wa al'umma sun samo asali ne kai tsaye daga kwace halifanci daga wajen Ahlulbaiti (a.s) da aka yi. Da a ce al'umma ta riki tafarkin da Manzon Allah (s.aw.a) ya tsara mata da ya dace da makomarta na sanya jagorancin al'umma a hannun wasu zababbun mutane ma'abuta baiwa, wato shugabannin Ahlulbaiti wadanda ke fifita manufar al'umma a kan dukkanin komai, da a ce al'umma sun yarda da tsarin da Manzon Allah (s.aw.a) ya tsara musu da ba a jarrabe su da shuganni irinsu Mu'awiyya da Yazid ba da sauran sarakunan Umayyawa da Banil Abbas wadanda suka dauki dukiyar Ubangiji daula bayin Allah kuwa bayinsu suka mayar da tattalin arzikin al'umma abin biyan bukatun kansu.
[1]- Khuzaimah bn Thabit: Dan kabilar Aws, ana kiransa da Zul Shahadatain (ma’abuci shahada biyu) Manzon Allah (s.a.w.a) ya sanya shaidarsa ta kasance tamkar ta mutum biyu. Ana masa alkunya da Aba Ibad. Ya halarci yakin Badar da sauran yakukuwan da suka zo bayanta, ya kasance tare da Imam Ali (a.s) a yakin Siffin, lokacin da aka kashe Ammar sai ya zare takobinsa ya ta yaki har aka kashe shi. Ya kasance yana cewa: Na ji Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa: “Batacciyar kungiya ce za ta kashe Ammar”. Ana iya duba littafin al-Isti’ab.
[2]- Abul Haitham: Shi ne Malik dan kabilar Aws ne, yana daga cikin mutane shidan da suka hadu da Manzon Allah (s.a.w.a) kuma suka yi masa mubaya’ar akaba ta farko da ta biyu, shi ne mutumin farko da ya fara yin mubaya’a ga Manzon Allah (s.a.w.a) a daren akaba. Shi ne shugaban Bani Abdul’ashhal. Ya halarci yakin Badar da sauran yakukuwan da Ma’aiki (s.a.w.a) ya yi, hakan ya zo cikin Asadul Gabah 4/274. Ya kasance daga cikin sahabban Imam Ali (a.s) na kurkusa, ya yi shahada ne a yakin Siffin a shekara ta 37 hijiriyya. Imam Ali (a.s) a cikin wasu hudubobinsa ya ambaci abin da ya same shi (Abu al-Haitham) cikin bakin ciki da juyayi yana cewa: Ina ‘yan’uwana wadanda suka hau hanya, suka tafi a kan (tafarkin) gaskiya, ina Ammar da Ibn al-Tayhan, ina Zul Shahadatain, ina makamantansu. Daga nan sai ya sanya hannunsa kan gemunsa yana ta kuka kan wadannan zababbun mutane wadanda suka kasance tare da gaskiya sannan kuma suka fahimci matsayinsa.
[3]- Yayi ishara ne da hadisin Ghadir wanda a cikinsa Manzon Allah (s.a.w.a) ya tabbatar da Ali (a.s) a matsayin halifa a bayansa.
[4]- Al-Ihtijaj 1/103.
[5]- Sahl bn Hunaif: Ba’ansare ne dan kabilar Aws, ana kirasa da Abu Thabit, ya halarci yakin Badar da sauran yakukuwa dukkansu. Ya kasance daga cikin wadanda suka tabbata tare da Ma’aiki (s.a.w.a) a ranar Uhudu ya yi masa mubaya’ar kare shi har mutuwa. Ya kasance tare da Imam Amirul Muminin Ali (a.s) kuma gwamnansa a garin Basra, ya kasance tare da shi a yakin Siffin ya kuma nada shi gwamnansa a Farisa. Ya rasu a shekara ta 38 hijiriyya inda Imam Ali (a.s) ya yi masa salla. Ana iya duba Tahzib al-Tahzib 4/428.
[6]- Al-Ihtijaj 1/102.
[7]- Usman bn Hunaif: Ba’ansare ne dan kabilar Aws, yayi yakin Uhudu da sauran yakukuwan da suka biyo baya tare da Manzon Allah (s.a.w.a). Umar ya nada shi a matsayin jami'i mai kula da yankin Sawad na kasar Iraki, inda ya tsara wajajen nomanta da wadanda ba a noma a wajen da kuma sanya musu haraji, Sannan Imam Ali (a.s) ma ya nada shi jami’insa a Basra da Kufa har lokacin Mu’awiyya inda ya rasu. Ana iya duba Asadul Gabah 3/376.
[8]- Sunansa shi ne Zaid bn Khalid al-Khazraji, ya halarci bai’ar akaba da yakin Badar da sauran yakukuwan da Ma’aiki (s.a.w.a) yayi. A wajensa ne Manzon Allah (s.a.w.a) ya sauka lokacin da ya zo Madina, sannan kuma ya kasance tare da Imam Ali (a.s) a dukkanin yakukuwan da yayi. A lokacin yakin Nahrawan shi ne ya rike tutar kariya ga wadanda suka bar sansanin Khawarijawa suka dawo sansanin Imam Ali (a.s). Yana da maganganu da hudubobi na tada tsumi jama’a wajen taimakon Imam Ali (a.s).
Wata rana mahaifinsa Khalid ya zo wajen Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce masa: Ka yi min wasiyya Ya Rasulallah, sai ya ce masa: Ina maka wasicci da abubuwa biyar: fitar da rai daga abin da ke hannun mutane saboda haka wadata ce, ina maka hani da kwadayi saboda shi talauci ne na dan gida, ka yi sallar tamkar mai ban kwana, ka kiyaye aikata abin da daga baya za ka zo kana neman gafara, sannan ka so wa dan’uwanka abin da kake so wa kanka….Ya rasu a Kasdandiniya a lokacin Yazid bn Mu’awiyya kamar yadda ya zo cikin al-Alkab 1/13.
[9]- Al-Ihtijaj 1/103.
[10]- Suratul Ahzab 33:36.
[11]- Rashin ingancin haduwar annabci da halifanci a gida guda shi ne taken da manyan Kuraishawa suka rika don cimma burinsu na kwace halifanci daga Ahlulbaitin Manzon Allah (s.a.w.a).
[12]- Sulh al-Hasan shafi na 28-29.