Muassasar alhasanain (a.s)

Iyali Da Yalwa

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

MARUBUCI: Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Da sunan Allah madaukaki
Sau da yawa mutanen kasashenmu sukan yi amfani da tunaninsu da fahimtarsu wurin bayani ko fassara ma'anar wata aya ko wasu ruwayoyi da suka zo musu a tunani, sai su ba su fahimtar da suka ga dama. Dalilin da ya sanya na kawo wannan maganar kuwa ina son yin magana kan wani hadisi da yawancin mutane suke dogaro da shi wurin ganin a yi ta auratayya ana hayayyafa, ta yadda kowane mutum yana iya kawo maka wannan magana cikin sauki kuma ya nuna abin da take nufi kai tsaye. Wannan hadisin shi ne: "Ku yi auratayya kwa hayayyafa, hakika ni ina yi wa al'umma alfahari da ku ranar kiyama (Maslakul Afham: Shahidus Sani / j 7/ s 12). A wata ruwayar da ta zo da karin "hatta da bari" -ina yi wa al'ummu alfahari da shi, kamar yadda wasu ruwayoyin sun kawo cewa; bari ma yana da amfani domin yana tsayawa a kofar aljanna ya ki shiga sai iyayensa sun shiga-.
Da farko dai yawancin wannan hadisin ana kawo shi ne yayin da ake maganar matsalar rayuwa da karancin abin da za a dauki nauyin iyali na tufatarwa da ilmantarwa da ciyarwa. Sai kawai ka ji an jawo wannan hadisin ba tare da sanya fahimta ba, musamman da yake akidar kaddara da ma'anar komai daga Allah ne kuma dan Adam ba shi da wani hannu a kan rayuwarsa ta yi kanta da kamari a cikin al'ummarmu, wanda yake akida ce batacciya.
Da yake bayanin kan kaddara mun riga mun yi rubutu a kansa don haka ba zamu dauki wani sabon lokaci ba a nan domin yin magana a kansa, sai dai muna iya nuni da cewa: Ubangiji madaukaki yana cewa: "Hakika Allah ba ya canja wa mutane abin da yake garesu, har sai dai sun canja abin da yake garesu..." (Anfal: ). Wannan ayar kawai ta isa ta nuna mana cewa waccan maganar ta cewa Allah na nan shi zai yi komai ba tare da shi bawa ya dauki wani mataki ba, babu wani asasi da take da shi!.
Da farko dai muna son a fahimci cewa sau da yawa hukuncin shari'a yana da nasa lokacin da yake la'akari da shi da wuri, da yanayi, don haka wannan hadisin yana kuma daya daga cikinsu musamman idan muka yi la'akari da cewa maslahar bayi ita ce gaba wurin sanya hukuncin shari'a kamar yadda masu ilimin Usulul Fikhi suka tabbatar.
Don haka ne idan muka koma wa wannan hadisin zamu ga yana magana a wani lokaci da yawan musulmi ya yi karanci matuka, kuma da bukatar su hayayyafa. Sai dai wani zai ce ba zai kasance haka ba saboda karshen hadisin yana nuni da cewa; manzon rahama yana son ya yi wa sauran al'ummu alfaharin yawan al'ummarsa ne.
Sai dai wannan maganar tana iya zama karbabbiya ne idan da babu wasu ruwayoyin da suke nuni da cewa babu wani alheri ga 'ya'ya ashararai. Hada da ayoyi masu yawa da suke sukan bin sha'awar duniya ta tara 'ya'ya da mata, da dukiyoyi, da so irin na sha'awa da kwanciya, ba tare da la'akari da tarbiyyarsu bisa tafarki nagari ba (Masalikul Afkari ya yi nuni a j 7, s 12).
Wannan lamarin a fili yake cewa yana nuni da irin nau'in al'ummar da manzon rahama (s.a.w) yake son al'ummarsa ta tara masa, ba yuyar da ba ta da wani amfani ba!.
Da haka ne zamu gane cewa wannan hadisin koda kuwa ba ya nuni karara da abin da muka kawo, ta yadda wani zai musun abin da muka yi bayani, sai dai ga wasu ayoyi da ruwayoyi da suka yi magana kan abin da muka ambata. Manzon Allah (s.a.w) bai nemi a kawo masa ashararai da jahilai, da 'yan sara suka ba, yana son al'umma mai hankali, da tunani, da ilimi, da wayewa, da ci gaba ne.
Sannan akwai wata fa'ida mai girma a wurin kwadaitar da yin aure wacce ita ce kare kai daga fadawa cikin fasadin zina, don haka ne ma zamu ga hadidai da ruwayoyi masu yawa sun zo suna sukan zaman gwagwarci ba tare da wani dalili ba.
Wasu ruwayoyin sun kwadaitar ta hanya kawo falalar yin aure wanda wannan hadisi yana daga ciki, wasu kuwa suna kawo fifikon ibadar mai aure kan maras aure, wasu kuwa suna sukan zaman gwagwarcin kamar ruwayar nan mai cewa:
"Kaskantattun matattunku su ne marasa aure" (Shara'I'ul lslam: Muhakkikul Hilli / j 2/ 491).
Da ruwayar: "Babu wani amfani da mutum zai samu bayan musulunci da ya fi mata musulma da take faranta masa rai idan ya kalle ta, take biyayya gareshi idan ya umarce ta, take kare mutuncinsa idan ba ya nan, ga kanta, da dukiyarsa" (Shara'I'ul lslam: Muhakkikul Hilli / j 2/ 491).
A nan ne zai bayyana a fili cewa wannan ruwayar mai cewa; "ku yi auratayya ku hayayyafa", ba ta nufin komai sai kwadaitarwa kan yin aure da nisantar zaman banza, da kwadaitar da hayayyafa ta hanyar auratayya, ba ta hanyar fasadin zina ba!.
Mai shari'a yana iya sanya hanyoyi daban-daban kamar na gasa da ake iya sanyawa a rayuwar yau da gobe, domin ya kwadaitar da mutane yin wani abu, don haka ne ya sanya kwadaitarwa da cewa a ciki akwai farin cikinsa, kuma zai ma yi alfahari ga wata al'umma da wannan. Don haka wannan kuwa ba yana nufin ya yi umarni da a kawo 'ya'ya barkatai a watsar a titi ba, sai dai yana nufin ya kwadaitar da al'ummarsa su yi wani abu ne wanda zai sanya shi farin cikin, don haka sai ya nuna ma har zai yi wa wasu alfahari da abin.
Wannan lamari a fili yake idan muka duba rayuwar mutane yau da gobe, zamu ga kowane mutum yana da hanyoyin da zai sanya 'ya'yansa su kasance nagari, sai ya sanya musu kyauta da kwadaitarwa, domin su yi wani abu da zai yi alfahari da shi. Don haka ku nuna mini wanda ya fi manzon rahama son ganin ci gaban al'ummarsa da shiryar da ita? Sai dai abin takaici kowa yana fassara maganarsa yadda ya so ne.
Mai karatu ka yi mana afuwar cewa don me ba mu fara bayanin shi kansa gundarin hadisin ba tukun, domin a cikinsa akwai maganganu masu muhimmanci matukar gaske. Jerin bayanin namu ta yiwu ya kasance aje-adawo, sai dai na yi hakan ne saboda muhimmancin wannan matashiya mai tsayi wacce take bangare ce ta wannan bayanin.
Idan muka duba wannan hadisin zamu ga yana da bangarori masu dadin gaske kamar dai kowane hadisi madaukaki daga manzon rahama (s.a.w), wannan ruwaya tana cewa: "Ku yi auratayya kwa hayayyafa, hakika ni ina yi wa al'umma alfahari da ku ranar kiyama (Maslakul Afham: Shahidus Sani / j 7/ s 12). A wata ruwayar da kari hatta da bari -ina yi wa al'ummu alfahari da shi, kamar yadda wasu ruwayoyin sun kawo cewa; bari ma yana da amfani domin yana tsayawa a kofar aljanna ya ki shiga sai iyayensa sun shiga-.
Da farko dai kalmar "Ku yi auratayya kwa hayayyafa" tana nuna mana aure ana yin sa ne tsakanin mutum biyu, ba ya kasancewa sai da yarda bangaren namiji da mace, don haka sai ya zo da kalmar tarayya da aikin da yake daga bangarori biyu a larbci ??????? ku yi auratayya, koda yake ana iya cewa yana nufin ku yi aure wato ku biyu kenan miji da mata.
Don haka sharadi ne sai idan mace ta yarda aure ya yi, wannan ne ya sanya zamu ga musulunci ya sanya auren tilas ba aure ba ne.
Sannan a wannan ruwayar babu wani abu da yake nuna ana nufin a auri mata da yawa, amma kakan ji wasu a gefen titi, hatta da wasu masu da'awar ilimi ya yi mata da yawa yana mai kafa hujja da wannan ruwaya.
Kamar dai yana son ya ce; ba wani abu ake nufi da wannan ruwaya ba, sai a yi ta yin auren mata da yawa ana kawo 'ya'ya barkatai koda kuwa babu wani abu da zai iya na daukar nauyin rayuwarsu!. Sannan mun riga mun yi nuni can baya da cewa ba yadda zamu yi zaune mu yi tsammanin Allah ya kawo mana canji haka kawai ba tare da mun tabuka komai ba, da hujjar cewa Allah yana nan!.
Sannan fadinsa ma'aiki "Ku yi auratayya" yin aure a nan umarni ne na mustahabbi kamar yadda malamai suka yi nuni da shi, kuma aikatau ne shudadde a ka'idar nahawun larabci wanda a Hausa yake bayar da umarni, don haka ne a hausa muke fassara shi da umarni domin ma'anarsa kenan. Amma bangaren wannan jumala mai cewa; "kwa hayayyafa", yana nuna mana dalilin yin auren kenan. Kamar yadda zaka ce da wani mutum ne, ka yi kasuwanci ka samu riba, ko ka yi karatu ka samu ilimi.
Wanda yake nuna sai an yi wadannan ayyukan sannan ake iya samun natija wato bangaren karshe. Don haka hadisin yana nuna mana idan muna son haihuwa da hayayyafa to sai mu yi aure, amma idan ba ma son mu hayayyafa to ba zamu yi auren ba. Sai dai ma'aiki mai daraja ya kwadaitar da yin auren domin da shi ne zai yi alfahari ga sauran al'ummu.
Domin idan hayayyafa ta kasance ta tsaya cik, ko kuma idan hayayyafa ta hanyar fasadi ne kamar zina, to babu wani abu da zai yi wa sauran al'umma alfahari da shi.
Amma fakarar da take cewa: "hakika ni ina yi wa al'umma alfahari da ku ranar kiyama", wannan fakarar tana nuna mana dalili na biyu na yin aure wanda yake nuna cewa; idan kuka yi aure kuka hayayyafa to zan yi alfahari da ku kenan. Wannan yana nuni da cewa; idan kuwa ba ku yi aure kuka hayayyafa ba to babu wani abu da zai yi wa wasu al'umma alfahari da shi na salihan bayin al'ummata, domin samuwarku ta katse kenan.
Sannan alfahari yana yiwuwa ne idan akwai abin da za a nuna na azo-agani kamar salihan bayi da babu kamarsu a cikin wata al'umma, don haka wannan yana nuna cewa idan taci-barkatai ne wannan al'ummar take kyankyasowa take hayayyafarwa babu wani abin alheri da za a iya yin alfahari da shi!.
Sannan duk da muna da dalilai daga aya da wasu hadisai da suke nuna 'ya'ya nagari ne ma'aikin tsira yake nufi, sai dai a wasu ruwayoyin zamu ga akwai karin da yake nuna hakan, domin fadinsa cewa: "hatta da bari -ina yi wa al'ummu alfahari da shi- domin ya zo cewa; yana tsayawa a kofar aljanna ya ki shiga sai iyayensa sun shiga. Tana nuna mana cewa zuriya ta gari ake nufi da wadanda za a yi alfahari da su, don haka sai kowa ya shirya wa kawo wadanda ya san zai iya daukar tarbiyyarsu, idan ya yi nasa sai kuma ya nemi Allah ya kama masa.
Karin bayani kan hakan muna iya ganin wannan ruwayar tana nuna mana abin da muka kawo a fili a fadinsa ma'aiki (s.a.w): manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Babu wani abu da ya fi soyuwa wurin Allah madaukaki a musulunci fiye da gidan da ake raya shi da aure, kuma babu wani abu da ya fi kiyuwa gun Allah madaukaki a musulunci fiye da gidan da yake rushewa saboda saki" (Kafi: j 5/ babin Hassi alan nikah/ 328/ h 1).
Sannan wanda yake ganin cewa; bari in yi ta sako 'ya'ya in watsar da su, ba tare da ya yi kokarin ganin kawo adadin da yake jin zasu dace da yanayinsa ba, ya yi kuskure mai girma. Domin musulunci bai bar wani abu ba sai da ya yi bayaninsa, sannan Imam Ali (a.s) wanda da takobinsa ne musulunci ya tsayu, kuma shi ne kofar birnin ilimin Annabi (s.a.w) ya yi nuni da sabanin hakan yayin da yake cewa: "Karancin Iyali dayan Yalwa ne guda biyu, Soyayyar (mutane) rabin hankali ne, Bakin ciki rabin tsufa ne". Nahajul Balaga: Hikima: 135.
A nan a fili yake cewa Imam (a.s) yana nuni da cewa wanda ya fi karancin iyali nauyin da yake kansa zai fi raguwa, kuma wannan yana nufin zai fi samun yalwar iya tattalinsu da kula da su fiye da wanda ya tara su birjik. Sai dai mu gane cewa wannan lamari yana da alaka da yanayin mutane da bambancinsu ta fuskacin iko da yalawa, ta yadda wani yana iya kula da 2, wani kuwa 5, wani kuwa 12, da makamantansu. Don haka zamu iya fahimtar cewa Allah madaukaki ya dora lamurran wannan duniyar bisa sabubba ne, ba ya yin wani abu bisa wasa, ba ya wani aiki babu hikima, Allah Ka girmama mai hikima!.

Cibiyar Al'adun Musulunci
www.hikima.org
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Wednesday, April 07, 2010

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)