Zabar Mace2
Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Zab'ar Mace Ko Namijin Aure Ayoyin masu yawa ne suka zo a cikin littafi mai girma na kur'ani suna nuni zuwa ga dokokin zamantakewar aure da zamu kawo su a dunk'ule kamar haka:
1- Namiji shi ne shugaba a cikin iyali: Nisa'I:34.
2- Mace nutsuwar mijinta ce: Rum: 21.
3- Miji da mata tufafin juna ne: Bak'ara: 187.
4- Kyautata zaman tare da mata: Nisa'I: 19.
5- Kiyaye adalci tsakanin mata: Nisa'I: 3.
6- Namiji da mace daidai suke a kamalarsu ta 'yan adamtaka: Nahal: 97.
7- Kiyaye hak'k'ok'in mata: Nisa'I: 7.
8- Abin da namiji zai yi wa mace mai k'in shimfid'arsa; Na farko: Wa'azi. Sannan sai: k'auracewa shimfid'arta. Sannan sai: sanya k'arfi da duka da takurawa daidai yadda shari'a ta gindaya. Nisa'I: 34.
9- Kyautata wa mace yayin da ake ci gaba da zaman tare ko yayin da za a rabu: Bak'ara: 231.
10- Bayar da kyauta mai dacewa ga mace yayin da za a rabu: Ahzab: 49.
11- Bayar da kyauta ga mace daidai ikonsa idan za a rabu kuma ba a san juna ba a shimfid'a, kuma ba a ayyana sadak'i ba: Bak'ara: 236.
12- Bayar da rabin sadak'i ga mace yayin rabuwa kuma an ayyana sadak'i amma har suka rabu d'in ba su san juna ba a shimfid'a: Bak'ara: 237.
13- Kada a takura wa mace domin ta halatta masa sadak'inta: Nisa'I: 19.
14- Dokokin hak'k'ok'in mace bayan rabuwa, kamar wajan zamanta, da rashin k'untata mata, da ciyar da ita: D'alak': 6.
15- Rashin halaccin cin sadak'in mace ga miji yayin rabuwa: Bak'ara: 229.
16- Sulhu tsakanin miji da mata: Nisa'I: 35 .
Samun nutsuwar ruhi da abokiyar zama ba ya yiwuwa sai ta hanyar auratayya, domin idan ta fuskar fasik'anci ne ake zaune da juna wannan nutsuwar ruhi har abada ba ta samuwa, wannan kuwa abu ne sananne da d'abi'ar halittar mutum, da ilimi, suka gaskata da shi.
Saboda haka duk wanda zai yi aure ya tuna ko ta tuna cewa za ta yi aure ne da wanda zasu zauna domin gina rayuwa maras iyaka da gina gida salihi. Amma tambaya a nan ita ce: Wane mutum ne zamu zab'a domin wannan rayuwa da kuma samun nutsuwa, da soyayya, da tausasawa, da tausayawa juna?.
Ba a son a samu shak'uwa sosai sai da wanda za mu yi aure da shi, saboda haka irin soyayyar da ake yi ta al'adun da suka shigo cikin al'ummar Hausa musamman daga yammacin duniya ba ta da kyau matuk'ar ba aure za a yi ba, domin saudayawa takan kai ga aikata haram wanda zai yi tasiri a kan saurayi da budurwa har k'arshen rayuwarsu, kuma saudayawa rayuwar 'yan mata ta lalace ta hakan sakamakon irin wad'annan miyagun al'adu.
Saudayawa mace mai sauk'in hali da samari sukan iya shawo kanta ta hanyoyi daban-daban wani lokaci ma har wani shak'iyyi yakan ce da ita: Idan kika yarda da ni muka kwanta to lallai zan aure ki. Irin wannan da yake son sha'awa ne ba na Allah da Annabi ba, da zaran ya san ta a 'ya mace sai ya yi wurgi da ita, ya watsar, ba ma zata san cewa mugu ba ne mai tsananin wulak'anci sai idan ta samu cikin d'an shege ta wannan mummunar hanya, a lokacin ne zata san cewa ba ya k'aunarta koda k'wayar zarra. Saudayawa a k'asashen duniya da k'asashenmu 'yan mata suka kashe kan su saboda wannan mummunan hali da mayaudaran samari suka jefa su a ciki, rayuwa ta gurb'ace musu suka koma abin tausayi bayan da suna abin haushi, ko kuma suka gudu daga garuruwansu, ko ma suka haife d'an amma suka yarda shi a kwararo suka gudu.
Da yawa mata suna da sauk'in hali shi ya sa suka yaudaru da wuri, wasu kuma kwad'ayi ne yakan kai su ga fad'awa irin wannan mummunan hali, don haka yana kan iyaye su rik'a sanin menene 'yarsu take yi a waje, kuma da wad'anne irin k'waye ne take mu'amala, sannan kuma su waye suke zuwa zance wajenta da sunan suna son aurenta.
Nasihohinmu Gareku
Wannna wasu tattararrun nasihohi ne da zan ba masu son aure ko miji da mata domin zamansu da rayuwarsu su kyautata, da kuma gida wanda zai zama d'aya daga asasin gina al'umma ta gari.
*Kada iyaye su yi wa 'ya'yansu auren dole.
*Nisantar auran mai miyagun halaye kamar mashayin giya.
* Shiryar da mumini ga wata mumina don ya aureta.
*Ka yi aure don nutsuwa da kame kai, ko taimakon juna, ko gina al'umma ta gari.
*Kada a tsananta aure ya yi wahala domin wani lokaci ana samun wannan wahalhalu ta hanyar al'adu ne ko rashin sanin ya kamata daga masu ikon zartarwa.
*In za a had'u a had'u kamar yadda Allah ya ce, haka ma rabuwa, saboda haka wajan rabuwa sai da shedu da cikar sauran sharud'd'a kamar yadda suke a Addini.
*Kada a fara neman aure sai in da gaske ana so a yi auren ne.
*Babu laifi mace ta nemi namiji ya aure ta, wannan ba aibi ba ne ga mace, saboda haka mace in ta ga tana son wani tana iya shaida masa domin tarihin salihan bayi ya nuna mana haka.
*Wajan yin zance tsakanin saurayi da budurwa dole ne su kiyaye dokokin Allah kamar haramcin ganin abin da yake ganinsa haramun ne.
*Kada mai neman aure ya sanya sharud'd'a masu wahalar cika ga wacce yake son aura wad'annan saudayawa ba su sami burinsu ya cika ba.
*Kada a yi yaudara yayin neman aure haka ma a kula da kyawawan d'abi'u.
*Kyautatawa mace haka nan ita ma ta kyautata masa, kuma a rik'a godiya kan abin da ake yi wa juna na alheri, wannan kan sanya kowane b'angare ya dad'a himma kan abin da yake yi na alheri.
*Kar ka ce ai ba wajibi ba ne in yi mata kaza, domin kai ma akwai abubuwa da yawa da ba wajibi ba ne a kanta, kuma tana yinsu.
*Ku raba ayyukan kwanaki da suke hawan kanku a matsayinku na masu auratayya.
*Kada mace ta yi wa miji gorin satifiket ko wata shaida ta ilimi ko wani abin da ka iya nuna gori a kansa haka nan shi ma haka.
*Kada ki sa ran sai an yi miki abu irin na k'awarki, ya kamata ki kula da iyakar mijinki da godewa, domin rashin hakan kan iya karya masa k'arfin yi miki hidima.
*Tsafta, magana mai sanyaya zuciya, da nisantar jayayya ko bak'ar magana, suna daga cikin sirrin zama mai albarka na soyayya da gina gida na gari da salihar al'umma.
*Kada a yi wa juna nasiha a gaban yara ko mutane, a bari sai hanakali ya kwanta an huta sannan sai a yi wa juna nasiha cikin wasa da dariya hakan yakan fi tasiri ga ma'aurata.
*A jawo k'aunar juna da aiki ba da magani ba ko barazana.
*Kowa ya yi mu'amala da abokin zama da tausasawa ba da tsanantawa ba, domin ba ta magani sai dagula al'amuran zamantakewa.
*Kada mace ta sake ta bayar da fuska sai ga mijinta, haka ma kada ta sake ta tsananta wa mijinta, kuma ta sani kullum dole ta bujuro da kanta ga mijinta.
*Ba wa 'ya'ya isasshen lokaci da zama da su, da hira da su, da saita tunaninsu kan rayuwa.
*Girmama na gaba kamar uwar miji ko uwar mata yana daga kyawun zamantakewa da k'argonta, wato girmama iyayen juna.
*Ba wa juna isasshen lokaci na tattaunawa da hira da warware matsalarsu.
*Tanadar kyauta ta musamman ga juna ta bazata ko kuma ga iyayen juna.
*Wani lokaci matar mutum ta kan cutar da shi wajan ta taimaka masa ko makamancin haka, wannan wani abin yafewa ne da kauda kai saboda yana faruwa ne daga k'auna da son taimakawa daga mata.
Nasihohin Wata Mata Ga 'Yarta
Wata mata yayin tarewar 'yarta gidan miji ta yi mata nasiha ne kamar haka tana mai cewa da ita:
**Ki zama baiwarsa zai zama bawanki [wannan magana tana da hikima sosai domin duk wanda kake jin dad'insa to shi kake kyautatawa]
**Ki k'ask'antar da kai gareshi.
**Ki ji ki bi.
**Ki bi idanunsa [wato ki duba duk abin da yake k'ayatar da shi ki yi abin da ba ya so ko yake k'insa to ki bari]
**Ki kuma bi hancinsa [wato abin da yake so na k'anshi ki yi wanda ba ya so ya ji na daga wari ki nisance shi]
**Ki bi lokacin baccinsa [wato ki kula a lokacin bacci kada ki nisanci wajan baccinsa, wato shimfidarku d'aya, zaninku d'aya, kuma ki yi masa tabarruji]
**Ki bi abincinsa da abin shansa [wato kada lokacin cin abinci ya yi ya nema ya rasa ko ba ki dafa masa ba]
**Ki kiyaye masa dukiyarsa da kula da 'ya'yansa da tarbiyyarsu, da iyalansa, da uwayansa.
**Kada ki sab'a masa umarni ko ki yad'a sirrinsa, domin idan kika sab'a masa ya yi bak'in ciki da ke, idan kuma kina yad'a sirrinsa ya yi miki kaidi ta inda ba kya tsammani.
**Kada ki yi farin ciki a gabansa lokacin da yake bak'in ciki ko abin bak'in ciki ya same shi, haka nan kada ki rik'a bak'in ciki lokacin da farin ciki ya same shi.
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai
Rabi'ul Awwl 1424