Muassasar alhasanain (a.s)

Makaloli

Manzo Da Alayensa
BABBAR FITINA 1

BABBAR FITINA 1

Babu wani marubuci, komai kwarewarsa wajen fahimtar abubuwan da suka faru a tarihi, da zai iya fahimtar hakikanin abin da ya sami al’ummar musulmi bayan wafatin Annabi (s.a.w) sama da yadda da yadda Alkur’ani mai girma ya bayyana hakan. Allah Madaukakin Sarki na cew

Manzo Da Alayensa
AHLULBAITI (A.S) A KUR'ANI DA HADISI 3

AHLULBAITI (A.S) A KUR'ANI DA HADISI 3

  . “ Ibn Haska ya yi qarya Allah Ya la’ance shi, kaiconka lalle ni ban sanshi cikin mabiyana ba, Allah Ya la’ance shi. Na rantse da Allah ba a aiko Muhammad da sauran Annabawan da suka gabace shi ba sai da….salla da zakka da azumi da hajji.

Manzo Da Alayensa
AHLULBAITI (A.S) A KUR'ANI DA HADISI 2

AHLULBAITI (A.S) A KUR'ANI DA HADISI 2

An ruwaito halifa Abubakar yana cewa: “Na ga Manzon Allah (s.a.w) ya kafa wata haima ya jingina da ita a cikin haimar akwai Ali da Fatima da Hasan da Husain sai ya ce: Ya ku jama’ar musulmi ina zaman lafiya da wanda ya zauna lafiya da waxanda suke cikin wannan haimar, kuma mai yaqi da wanda ya yaqe su, mai qaunar wanda ya miqa musu wuya (wanda ya so su), babu mai sonsu sai mai halaltattun iyaye, sannan ba mai qinsu sai haramtattun iyaye, wanda ba xan halal ba [1] ”.

Manzo Da Alayensa
AHLULBAITI (A.S) A QUR'ANI DA HADISI

AHLULBAITI (A.S) A QUR'ANI DA HADISI

Manzon Allah (s.a.w) ya sanya garkuwa don kare al’ummar daga fitina da bata a bayansa su ne kuwa Ahlubaitinsa, magada iliminsa, masu yada hikimarsa sannan mafiya imanin al’ummarsa da shiriya da kyawawan dabi’u. Ya tarbiyatar da su tsoron Allah, tsantsaini da riko da Musulunci. Alkur’ani mai girma da hadisan Ma’aiki (s.a.w) cike suke da bayanan falalolinsu da matsayinsu mai girma. Ga wasu daga cikinsu da suke da alaka da abin da muke magana a kai:

Imamanci
Halifanci Wajibin Musulunci 2

Halifanci Wajibin Musulunci 2

Na Farko: Imam Ali (a.s) ya mallaki kwarewa mai girman gaske na ilimi, da cikakkiyar masaniyan hukumce-hukumcen Musulunci musamman a bangaren shari’a inda ya zama gagarabadau. Malaman tarihi sun ruwaito shahararriyar maganar nan ta halifa Umar inda yake cewa: “Da ba don Ali ba da Umar ya halaka”, babu wani da yake da irin wannan kyauta da ni'ima da Ali yake da ita. Imam Ali (a.s) ya kasance daga cikin shugabannin da suka yi fice wajen ilimi da sanin ya kamata a bangaren siyasa da zartarwa. Wasiyyarsa ga Malik al-Ashtar

Imamanci
Halifanci Wajibin Musulunci 1

Halifanci Wajibin Musulunci 1

Halifanci a Musulunci yana daga cikin tabbatattun abubuwa na asasi wajen gina al’umma musulma sannan daga cikin wajiban rayuwa ta Musulunci da ba za a iya wadatuwa daga shi ba. Da shi ne ake kafa abin da ake bukata na tsarin duniya da lahira, da shi ne ake tabbatar da adalcin da Allah Yake son ganin an tabbatar da shi a bayan kasa. Don haka dole ne mu tsaya kadan don yin bahasi kansa saboda alakar da yake da shi da Shi’anci.

Tarihin Shianci
Asasin Shi'anci 2

Asasin Shi'anci 2

bn Khaldun ya tafi kan cewa Shi’anci ya bayyana ne lokacin Shura , wato akwai wasu sahabbai da suke tare da Ali, suna ganin shi ne yafi cancantar halifanci sama da waninsa, lokacin da aka hana shi aka ba wa waninsa sai suka nuna rashin amincewarsu, daga cikinsu akwai Zubair, Ammar bn Yasir, Mikdad bn Aswad da sauransu sai dai jama’a sun tsaya kyam suka gargade su kan hakan, ba su ci gaba da boren nasu ba [1] .

Tarihin Shianci
Asasin Shi'anci 1

Asasin Shi'anci 1

  Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “ Ya Ali! Kai da ‘yan Shi’anka za ku same ni a bakin tafki [1] ” . Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “ Ya Ali! Za ka gabato wajen Allah alhali ‘yan shi’anka suna a matsayin yardaddun abin yarda, sannan kuma za a gabatar da makiyanka alhali ana fushi da su [2] ” . Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “ Ali da ‘yan Shi’ansa su ne masu rabautuwa ranar kiyama [3] ” . Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “ ’Yan Shi’an Ali su ne masu samun rabo [4] ” . Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “ Ya Ali! Hakika Allah Ya gafarta maka da zuriyarka da ‘ya’yanka da iyalanka da ‘yan shi’anka da kuma masoyan ‘yan Shi’anka…. [5] ” .

Game da Kur'ani
SURAR KECEWA

SURAR KECEWA

9. Kuma ya juya zuwa ga iyalinsa yana mai raha.   وَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَهُ وَرَاءَ ظَهْرِهِ    10. Kuma amma wanda aka bai wa littafinsa, daga wajen bayansa.   

Manzo Da Alayensa
Sanin Imam Mahdi

Sanin Imam Mahdi

An ce ana ce masa Mahadi ne saboda shi ne zai shiryar da mutane zuwa ga gaskiya, kuma ana ce masa ka’im domin shi ne zai tashi da yaki, kuma ana cewa da shi muntazar domin ana sauraron zuwansa, kuma ana ce masa bakiyyatul-Lahi domn shi ne ya rage daga cikin hujjojin Allah a bayan kasa. Kuma hujja yana da ma’anar mai sheda ga bayi

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)