Muassasar alhasanain (a.s)

Abubuwan Haram a Harami

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

Abubuwan Haram a Harami


Daga lokacin da mai hamra ya fadi labaika ya yi haram, to wasu ayyukan sun zma haram gae shi da ake kiran su abubuwan haram ga mai harama, haka suke a umarar tamattu'I da kuma hajjin tamattu'I da kuma umarar mufrada. Don haka lokacn da muka yi haram dole ne mu guji wasu ayyuka. Wadannanan ayyukan su ishirin da biyu ne, wadanda hudu daga ciki sun kebanci maza ne kawai, daya kuma ya kebanci mata ne ba haram ba ne ga maza, amma sauran duk an yi tarayya a ciki tsakanin maza da mata duka haram ne.
Daga farko zan kawo sunayensu gaba daya, sannan sai kuma mu bi wadanda muka ga tayiwu su same ku a lokacin haramar ayyukan umara ko hajji, sai mu yi bayanin su dalla-dalla, saboda wasu suan faruwa, wasu kuwa zai iya yiwuwa su faru, wasu kuwa suna faruwa da yawa ne, wasu suan da kaffara, wsu kuam ba su da kaffara, wasu a lokacin ihrami ne kawai suke haram amma lokacin da babu ihrami halal ne, kamar kallon madubi don ado da gyara jiki, wasu kuwa a lokacin da ba na ihrami ba ma haramun ne, sai dai a lokacin ihrami ne zunubinsu yake karuwa.
1. Jerin abubuwan da suke haram ga namiji kamar haka:
Na Daya: Sanya tufafi dinkakke
Na Biyu: Sanya abin da zai rufe saman kafa kamar takalmi kafa ciki ko safa
Na Uku: Lullube kai da kowane abu ne
Na Hudu: Tafiya karkashin inuwa, ko kuwa sanya wani abu da zai ba shi inuwa
2. Amma aikin da ya ke haram ga mace kawai shi ne abin da ya shafi fuskar mace a lokacin ihrami. Bai halatta mace ta rufe fuskarta ba
Amma abubuwan da aka haramta, wandanda suke haram ga maza kuma haram ga mata su ne:
- Amfani da abu mai kanshi kamar turare
- Kallon madubi don ado
- Amfani da lalle ko kala (rina gashin kai, sanya lalle)
- Shafa mai a jiki, kamar man shafawa
- Cire gashin jiki, gashin kai ko fuska
- Sanya kwalli a ido
- Sanya zobe
- Fitar da jini daga jiki, misali ji wa jiki ciwo
- Fasikanci
- Jidali
- Kashe kwari a jiki
- Cire ko yanke shuke-shuken harami
- Daukar makami
- Farautar dabbobin daji (na jeji da sahara)
- Jima'in mace ko namiji haram ne
- Kulla aure
- Fitar da Mani
Wadannan su ne ayyukan da suke haramun yayin harama da ayyukan umara ko hajji
3. Wannan shi ne jerin abubuwan da suka haramta yayin harami.

Bayanin Wasu Daga Abubuwan Haram A Harami
Amma wasu daga wadannan aubbuwan da aka haramta zai iya yiwuwa ya faru ga mai aikin umara ko hajji:
Mu kula sosai cewa da farko: Ba duka ba ne ake samun wakanarsu ga mai aikin umara ko hajji, wato ba sa faruwa, wasu suna dan faruwa jefi-jefi, wasu kuma ba kasafai suke faruwa ba, don haka ba dole ne a nemi sanin mas'alolin duka ba. Don haka ne mu a nan zamu yi bayanin wadanda suka faruwa ne a jefi-jefi, mu yi bayanin hukunce-hukuncen su.
Ku kula sosai cewa ku koyi wadannan mas'alolin kuma ku kiyaye kada ku yi su lokacin ihrami, sai dai idan kuka manta ko kuma kuka sha'afa; misali kuka kalli mudubi, ko kuka gyara gashinku, sai kawai kuka farga cewa kun kalli madubi, sai kuka yi maza kuka juyar da fuskarku wannan ba haram ba ne, kuma ba shi da kaffara, saboda ba da gtangan ba ne.
Wato duk da kun koyi sanin abubuwan da suke haram, amma sai ya kasance kun yi su ba da gangan ba, sai kuka tuna. To wannan da ya kasance ba da son ku ba ne ya faru, ba laifi ba ne, kuma babu kaffar, kuma shi kallon madubi ba shi da wata kaffara, kuma hatta da wadanda suke da kaffa idan mutum ya yi su bisa rafkanwa, to su ma babu matsala.
4. Wata mas'alar kuma ita ce; idan mutum ya zama cikin halin larura ta yadda ba makawa ya yi wani daga ayyukan haram, to bai aikta haram ba, sai dai zai iya yin kaffara; misalin wannan shi ne wanda yahau mota mai rufi bayan ya yi harar umara ko hajji, to wannan bai yi zunubi ba, kuma ayyukansa ba su da matsala, sai dai yana da kaffara da zai yi bisa wajibi.
A nan zai iya yiwuwa a yi tambaya cewa mece ce kaffarar? Mu zamu kawo su daya bayan daya a nan. Abubuwan haram dan ihrami da sukan iya faruwa zamu kawo bayaninsu su ma, wani lokaci kuwa zai iya yiwuwa mu hada da bayanin kaffara ko kuma mu kowa cewa ba shi da kaffara misali. Fatana ku kasance tare da mu a nan.
5. Amma abubuwan haram da suka kebanta da maza wadanda ba haram ne kan mata ba su ne.

Tufafin Haramin Maza
Da farko, sanya tufafi dinkakke: mu a bahasin ihrami mun ce: Ya wajaba kan maza su fitar da duk wani tufafinsu dinkakke yayin yin ihrami, babu wani tufafi da ya kamata ya rage a jikinsu wanda yake dunkakke. Sannan zasu sanya fallayen zannuwa biyu ne kawai, sai ya kasance kamar sanya tawul ne, ko wani zane, kuma bayan niyya sai a fadi labbaik. Fitar da dinkakken tufafi da sanya tufafin ihrami wajibi ne kan maza, sai dai ga mata ba wajibi ba ne; kamar yadda muka fada a baya.

Tufafin Haramin Mata
6. Amma mata zasu iya sanya tufafinsu da suka saba su yi ihrami da shi babu wata matsala, sai dai an saba sanya tufafi fari ga mata yayin yin ihram. Game da tufai dai bau wani sharadi ga tufafin mata sai na lokacin da zasu yi salla; kamar tsarkin tufafi, halaccinsa, da sauran sharudda da aka kawo a nan. Haka nan bisa ihtiyadi kada ya kasance na tsantsar alhariri, wannan lamarin na sanya tufafin alhariri ba shi da matsala ga mata, sai dai a ihrami bai halatta gare su ba. Don haka mata zasu iya sanya tufafi dinkakke lokacin ihrami kamar tufafin da yake wuyansu, kuma idan akwai wani tufafin ma da zasu kara duk babu wata matasla, maza ne kawai suke da haramcin tufafi dinkakke.

Abubuwan da Ba a Ganinsu a Matsayin Tufafi
7. Amma sanya abubuwan da ba a ganin su a matsayin tufafi -kamar belt, layar wuya, marikin agogo- ba su da matsala a lokacin harami, kuma hatta ma idan gefen tufafin harami a dinke yake, da sahradin cewa daya bangaren da zaran dinki ya bi, ba yana kan dayan ba ne, kawai dai an dinke shi a mike ne kan fallen yadi daya to babu komai, amma idan aka ninka wani fallen kan wani to wannan bai ingnta ba.
Game da tufafin da aka dinke ba dole ba ne ya kasance da zare, da za a sanya maballai ko allura a harhade tufafi ta yadda zasu kasance kamar dinkakken tufafi da ya yi shakalin riga ko wando ko wani tufafi, to sanya irin wannan tufafin bai inganta ba. Haka nan idan wani ya sanya yadi ya hade shi da gam ko wani abu ta yadda suka hadu suka yi shakalin riga, shi ma dai bai halatta ba a sanya wannan. Amma zama kan tufafin da aka dinka ko wata shimfida ko wani bargo babu komai, haka ma yn bacci a kai, sai dai kada a sanya shi saman kai wannan haram ne, amma sanya shi kan jiki da lullube shi wannan babu komai.
8. Haka nan a kwanakin zama a masha'arul haram a wasu lokutan shekara tayiwu a samu sanya mai tsanani, to shi ma a nan sanya bargo a lullube jiki babu komai ko da kuwa dinkakke ne, amma dai kada ya sanya tufafi a kansa, ko saman kafadarsa, kada ya janyo shi daga jikinsa.
9. Saboda haka idan shimfida ko wani abu da mutum yake kwana a kansa yana dinke ne, to babu komai, sai dai kada ya sanya shi kan kafadarsa ko ya lika shi da jikinsa, kamar dai tawul ko da kuwa akwai iska da yanayi mai sanyi, kuma sanya shi a kan kafada idan dai gefe ne yake a dinke kuma wani bangare bai hau kan wani bangaer ba, to wannan babu komai, zuwa wannan haddin ba shi da wata matsala.

Kaffarar Sanya Dinkakken Tufafi
Sanya dinkakken tufafi yana da kaffara, wato idan wani da gangan ya sanya tufafi dinkakke to dole ne ya bayr da kaffara,, ita kuwa wannan kaffarar ita ce tunkiya; wato zai yanka tunkuya ya bayar da naman gaba daya ga talakawa. Daga baya zamu yi magana mai fadi kan kaffara.
10. Idan wani ya yi haram da umara ko hajji kuma bai fita da tufafinsa dinkakke daga jininsa, to yaya zai yi? Amsa shi ne dole ne ya yi gaggawar cire wannan tufafi, kuma idan ya yi jinkirin cire shi to ya yi laifi, kuma yana da kaffara. Amma idan da gaggawa ya fita da shi daga jikinsa bai yi laifi ba kuma ba shi da wata kaffa a kansa. Wannan dai daya ne daga cikin abubuwan da suka haramta kan mazaje.

Sanya Abin da Yake Rufe Kafa Baki Daya
Amma abu na biyu shi ne sanya abin da yake rufe kafafu baki daya; kamar takalmi, safa, da sauran su, amma silifa masu marikin kafa, ko da kuwa sun daure samara kafa amma bas a rufe ta baki daya, kamar dai yadda muke ganin masu harami suna sanyawa to babu komai, kuma maza zasu iya amfani da shi babu wata matsala.
Abin da yake da muhimmanci a nan shi ne haramcin sanay abin da yake rufe kafa, ba abin da yake lullube kafa ba, domin akwai bambanci tsakanin wadannan abubuwa biyu, misali da namiji zai sanya mayafi da ya fado kan kafarsa ya lullube ta, wannan babu matsala, ko kuma yayin dayke son ya yi bacci sai ya lullube karafarsa da bargo wannan ma babu wata matsala, ko kuma a a wurin da yake mai kura kamar filin arafa sai ya ksacne kafarsa ta shiga cikin kasa yayin dayake tafiya wannan ma babu komai a kansa. Sai dai abin dayake da matsala shi ne a sanya wani abu dayake rufe kafa kamar takalmi, da safa, da sauran su, wannan idan namiji ya sanya su to yana da kaffara a kansa; wato idan namiji ya sanya su da gangan, to ba wajibi ba ne ya bayar da kaffara, sai dai bisa ihtiyadi mustahabbi, kuma yana da kyau idan zai iya yin kaffara da tunkiya/rago.

Rufe Kai
11. Abu na uku da ya haramta ga mza lokacin haram da aikin umara ko hajji shi ne rfe kai, wannan kuwa a kula sosai da cewa a kafa mun ce sanya wani abu da rufe kafa da shi ne matasla kamar takalmi ko safa ba tare da idan wani abu ne ya lullube ta ba, kamar zane da mai ihrami yake sanyawa. Sai dai a game da kai da bambanci, domin duk wani abu da zai rufe kai ko yaya yake matsala ne kuma bai halatta a sanya shi ba, wannan kuwa ya hada da mayafi, ko hula, ko hankici, ko magogin gumi, da duk wani abu; kai hatta da kunnuwa malamai suan sanya su wannbi bangaer ne na kia da bai halata a rufe ba, wato tayiwu wani ya rufe kunnunwasa alhalin yana da ihrami, wto wannan ma haramun ne ga mai ihrami. Hatta ma daukar wani kaya a kai malamai sun tafi a kan cewa bisa ihtiyadi kada a sanya kaya a kai. Missal da safe idanmai haram da hajji zai tafi daga mas'ahar zuwa mna kuma ga shi yana da harami, yana da wani buhu, buhun nan nasa yana da nauyi da ba zai iya rike shi a hannu ba, to bisa ihtiyadi ne kada ya sanya shi akansa.
Tambaya a nan ita ce; idan mai harami ya yi harama da umara tun daga mikati, sai ya kasance kuma ya tafi makka amma ya fara zuwa masauki ya yi wanka domin ya samu tafiya masallacin mai alfarma don yin saurna ayyukan umara, shin a nan zai iay sanya tawul a kansa ya busar da kasan bayan wanka? Sai malamai suak bayar da amsa cewa ba zai iya sanya tawul gaba daya a kansa ba, tun da sanya shi rufe kai ne,kuma wannan haram ne gare shik, amma idan da sannu-sannu ne yake sanya shi yana busarwa, sai ya tsane da wani bangare, sannan sai ya sake tsane wani bangaren har ya busar da kansa baki daya, to a nan babu wata matsala, kuma ba hara ba ne.
12. Haka nan gane da shiga inuwa akwai bayani masu muhimmanci da ya kamata mu lura da su: na farko yayin tafiya ne shiga inuwa yake zama haram ba lokacin tsayuwa ba. Don haka idan misali mai harami yana tafiya a hanya zuwa wani gidan abinci, sai ya shiga cikin gidan abinci to babu komai ydon ya zauna karkashin wani wuri rufaff, haka nan ma da mota zata tsaya karkaashin rufin wurin shan mai, don bbu matsala, ba dole ba ne sai sun sauko kasa. Haka nan ma tsakanin gidaje biyu idan yana tafiya, ko kuma a gidan abinci daga wata kujera zuwa wata kujera ko wani tebur zuwa wani tebur, wannan duka duk babu matsala a lokacin tafiya.
Shiga inuwar da take da matsala ita ce wacce take yayin tafiya daga wani gida zuwa wani gida, ko daga mikati zuwa makka, ko daga juhufa ko masallacin shajara zuwa makka, ko kuma bayan ya yi ihrami hajji daga makka zuwa arafa, ko ranar idan salla baba zuwa mash'arul haram zuwa mina, wannan tsakanin duka da yake tafiya bai halatta ba ya kasance a karkashin inuwa.
13. Wata mas'alar ita ce cewa inuwar da take gefen inda mai harama yake wucewa kamar inuwar garo ba ta da wata matsala, haka nan ma inuwar mota da take wcewa ko kuma mai harama yana cikin mota da samanta a bude yake, sai dai ita kuma motar tana wucewa inda yake da shuke-shuke da suke yi masa inuwa yayin wucewa, ko tana bin ta karkashin gada ko tunnel da makamantansu a lokacin da yake mai haram da umara ko hajji, to wannan duk babu wata matsala.
14. Amma idan dare ne mai sanyi ko kuma mai rowan sama, sai ya zauna karkashin rufin wano ta yadda idan da za a yi ruwa, to rufin zai hana rowan zuba kansa, to a nan akiwa matsala; wato bai kamata ba hatta da dare mai harami ya shiga rufaffiyar mota. A nan ne zamu ga akwai wani muhimmain bayanin cewa idan da za a yi ruwan sama kadan, sai mota ta tsaya, bayan ruwan ya tsaya kuma sai motar ta ci gaba da tafiya, wanan ma ba shi da wta matsala. Tayiwu wasu su ce mu muna son mu tafi daban mu samu wata motar a wannan loakcin da kuke cewa akwai sanyi da ruwa, duk da cewa idan suka dauki wata motar da samanta yake bude a lokcin sanyi ko ruwa to zasu samu kamuwa da mura, babu wata mafita, ko kuwa ba zasu iya raba kansu daga 'yan shiyyar da suke tafiya tare da ita a mota daya ba, ko kuma ba ma zasu iya hawa motar da samanta yake bude ba, ko kuma ba zasu iya samun motar da samanta yake bude ba, to a nan me zasu yi?
A nan duk babu wata matsala gare su, babu wani laifi don sun yi hakan, suna iya hawa mota mai rufi, sai dai suan da kaffa a kansu da zasu yi.
Kaffararsu ita ce tunkiya / rago da zasu bayan bayan sun dawo, idan zasu iya bayarwa a mina sai su yanak a nan. Amma idan a makka suan da haramin umara ne, to idan ya samu dama bayan ya yi haramin hajji ya je mina sai ya yanka a can. Haka nan dai kaffarar dai da take kansa tana nan ita ce tunkiya / rago; In Allah ya so zamu yi bayanin kaffara dalla-dalla daga baya. Hakan nan misali idan da wani mai harami zai yi tafiya da dare da motar da take samanta a rufe, babu sanyi babu kuma ruwa, sai mota ta lalace a kan hanya, kuma rana ta bullo, haka nan dai yana tafiya cikin motar da take rufaffiya, idan zai iya yin tafiya a kasa da mota wace ba rufe samanta yake ba, idan ba zai iya ba, to ba shi da wata dama sai ya tafi cikin rufaffiyar mota, sai dai duka akwai wajabcin yin kaffarar tunkiya / rago a kansa.
15. Wata tambayar da ake kawowa ita ce; idan ya tafi daga mikat zuwa makka, kuam daga makka zuwa hotel din su, kuma yana son daga nan sai ya tafi masallacin harami ay yi sauran ayyukan hajji, ko kuma misali yayan da haramin aikin hajji ne sai ya ya tafi afara, yana son ya canja wurinsa a arafa ko kuma ranar salla ce a mina, kuma muna son mu tafi jifan shedan daga himomin alhazai.
Shin a duk wannan lamurran zamu iya amfani da lema ne, ko kuma idan muna makka ne zamu iya amfani da mota mai rufi kuwa?
A bisa fatawar sayyid Khamna'I bisa ihtiyadi wajibi ne cewa maza ba zasu iya amfani da lema ko mota mai rufi ba yayin da suke kaiwako a makka yayin harami, ko a arafa da mina, da sauran wurare da suke kaikawo. Wannan ma duk yana daga abubuwan da aka haramta wa mai aikin hajji ko umara.

Rufe Fuska (ga Mata)
16. Rufe fuksa ga mata kawai yake haram, ga maza ba haram ba ne. Don haka ga maza rufe kai haram ne, amma ga mata rufe fuska haram. Mata ma a yayin da suke harami da ihrami dole ne su bude fuskarsu, kuma bai kamata ba su rufe fuskarsu gwargwadon wurin da ake wankewa yayin yin alwala. Don haka sanya nikabi da sauran abubuwan da suek rufe fuska da suek sanyawa a lokacin sallar dawafi ko sauran salloli duka da mata suak saba yi don kada fuskarsu ta bayyana duk bai halatta ba yayin ihrami da haramin hajji ko umara kuma haram ne, sai dai rufe gefen fuska yayin sanya hijabi don kare iyakacin inda ba a yarda a bayyanar da shi ba ga ajnabi, to babu matsala gare shi.
Haka nan zai iya yiwuwa wata mata don kada rana ta cutar da ita ta sanya hijabinta ko mayafinta don rufe fuskarta, ta rataye shi a gaban fusrkarta. A nan fatawar ita ce idan ya zama dole ne ta sanya wani abu ne da zai iya kare mata hasken zafin rana, sai ta sanya su a daurar fuskarta don kada hasken ya samu fuskarta, to babu matsala.
17. Wani lokaci kuma domin kiyaye lafiya suan umarni da sanya mask a fuska don kariya wanda yaek rufe hanci da baki, wannan ma idan ba babba ba ne ta yadda zai rufe hanci da baki ne kawai yayin harami ga mata, to babu matsala. Maza kuma fa? Su maza idan ma suak rufe fuskarsu to ba su da wata matsala; ko da kuwa dinkakke ne daidai fuska, to babu komai, domin ba a lissafa shi a cikin tufafi, kuma karami ne, dinkakkensa ba shi da wata matsala ga maza.
18. Wata matsalar ce: Idan mata suak yi wanka suak yi tsafta, shin zasu iya shafe fuskarsu da tawul kuwa, domin wannan yana nufin sun rure fuska ne?
To wannan mas'alar haka nan take ta yi kama da mas'alar rufe kai ga maza da muka ce idan ba su sanya tawul a kai ba ta yadda zai rufe kai gaba daya ba, to babu komai. To haka ma ga mata idan ba a sanya tawul kan fuska ta yadda zai rufe ta ba, to babu komai, don haak sai su rika busarwa a hankali a hankali har sai sun busar da shi gaba daya, ta yadda ba zai rufe fuska baki daya ba a lokaci guda, a haka ba zai zama abin haramtawa ba.
Wadannan su ne wasu daga hukunce-hukunce da suka kebanci maza da mata, kuma tun farko mun riga mun fadi cewa zamu kawo hukunce-hukuncen da suka kebanci maza da wadanda suak kebanci mata. Sannan yanzu zamu kawo abubuwan da suka haramta ga maza da mata bisa tarayya a bayanai masu zuwa da ya zama wajibi a kan maza da mata gaba daya su nesanci yin su.
Wassalamu alaikum warahmatul-Lah wa barakatuhu
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Sunday, January 15, 2012

 

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)