Yakin Khaibar
A rana irin ta 24 ga watan Rajab shekara ta 7 bayan hijirar Manzon Allah[SAWA] ne bayan Imam Ali[AS] ya kasha Marhaba babban kwamandan yaki na Khaibar aka ci nasarar yakin a hannun sa.
Wannan lamari ya faru ne mataki-mataki, a matakin farko Manzon Allah[SAWA] ya bada tuta ne ga Abubakar Khalifah na farko, yaje ya dawo ba tare da nasara ba, sannan washe gari sai ya mika tutar ga Ummar ,Khalifah na biyu shima kazalika.
To a rana ta uku sai Manzon Allah[SAWA] yace: "Zan bada wannan tuta a gobe ga wani mutum wanda yake son Allah da Manzon sa[SAWA] kuma Allah da Manzon sa[SAWA] suke son sa, mai kai hari, ba mai ja da baya ba,Allah Ta'ala zai yi budi a hannun sa". A lokacin sai kowa ya yi buri ya kasance shine wannan mutumin da Manzon Allah[SAWA] zai baiwa wannan tuta, amma yayin da gari ya waye sai Manzon Allah[SAWA] ya nemi Ali[AS], sai aka ce masa yana ciwon ido ba zai iya zuwa ba, sai Manzon Allah[SAWA] yace a zo masa da shi.
Sai Salmah Ibnul Akwa ya tafi ya zo da shi, sai Manzon Allah[SAWA] ya shafa idanun sa da wani abu na yawun sa, sannan yace: "Ya Allah ka tafiyar da zafi da sanyi daga gare shi".
Sai Manzon Allah[SAWA] ya sanya masa sulken sa, yayi masa rawani da hannun sa masu albarka, ya rataya masa takobin sa Zul-Fiqar, ya mika masa tuta sannan ya dora shi a kan dokin sa, sannan yace: "Tafi Ya Ali[AS] Jibril yana daman ka, Mika'il yana hagun ka, Azra'il yana gaban ka, Israfeel yana bayan ka, Nasarar Allah na saman ka, Addu'a na kuma na bayan ka".
Bayan Imam Ali[AS] ya isa ya fara ne da kiran su zuwa ga addinin Allah, da lokaci basu amsa ba, sannan daga karshe aka gwabza, kuma Allah ya bada nasara a hannun sa, bayan ya tsaga Marhaba biyu.
Amiral Mumineen[AS] ya cire kofar wannan ganuwar ta Khaibar da hannun sa, ya mayar da ita kamar wata gada musulmi na bi suna shiga cikin ganuwar ta Khaibar, alhali kuwa ita wannan kofar ana mata kirari da Khandaq ta biyu saboda babu me iya cire ta.
wanda ya cirato ya shigar Dan'uwa Sa'idu Funtua