Shin Imamai (a.s) Sun San Gaibu?
Da Sunan Allah Ta'ala Mai Raham Mai Jin Kai
Shi Imaman Ahlulbaiti (A.S) Sun San Gaibu?
Tabbas ya tabbata a cikin bahasi na ilimi cewa nau’in mutum an halicce shi ne ta hanyar da ba zai wadatu da rabuwa da gaibu ba, saboda saninsa da hadafin yin alaka da shi, hakan kuwa saboda tabbatar da hadafofin Allah ya dogara ne a kan sanin wannan duniyar mai yalwa a fage na biyu.
Ba cin karo tsakanin abin da mutum yake da shi na ‘yanci da irada da tsakanin matafiyar samuwar da ta dogara a bisa tushen Jabriyya (cewa Allah ne yake amfani da mutum a cikin ayyukansa, yadda Allah Ta'ala ya so haka mutum yake yi kuma ba shi da zabi a karan kansa), saboda mutum an ba shi guzurin ilimin da sanadiyyar wasidarsa ya tsinkayi sirrikan samuwa da motsawar Illiyya (mai samarwa Allah ke nan) (cause) da makomarsa da tukewarsa, wannan ilimin ba zai gushe ba yana tare da ismar da zata hana shi yin wasa da wadannan sirrikan, saboda isma tana nufin cewa tabbas ma’asumi yana riskar hakiknain abubuwa kamar yadda suke sanadiyyar wannan ilimin da gani mabayyani da yanayin da ba zai karbi kokwanto ba, wanda zai jawo ya yi amfani da shi saboda manufofin Manzanci da hadafin Manzancin, ba wai ana nufin ilimin da yake samuwa ta hanyar nema da ba da himma ba, domin wannan tauyayye ne iyakantacce, Manzanci kuma yana bukatar cikakkiyar masaniya, saboda haka abin da ake nufi shi ne ilimi Hudurin da Allah yake bayarwa.
Ilimin Imami ya sha bam-ban da ilimin Allah (S.W.T) domin ilimin Allah (S.W.T) daddada ne (wato kadimi) ya gabaci ilimummuka shi ne ainihin zatin Allah, amma ilimi huduri na Imami baya yin tarayya da ilimin Allah a cikin wani abu na wadannan al’amuran, domin ilimin Imami fararre ne kuma abubuwan ilimi sun gaba ce shi kuma shi ba zati ba ne, don haka ilimin Imami zuwa yake yi (Accidental) na baiwa ne, Allah ne yake bayar da shi don haka ilimin nan biyu ne ba daya ba ne.
Ayoyi da yawa sun bada labarin gaibu a rayuwar Annabawa da salihai kamar Annabi Yusuf da Annabi Sulaiman da Annabi Isa da Annabi Dawuda (a.s).
Sannan ba cin karo a tsakanin ayoyin da suke kebantar da sanin gaibu ga Allah (T.A) kuma suke korewa wanin Allah sanin gaibu da ayoyin da suke tabbatar da shi ga wanin Allah.
Ta farkon tana tabbatar da shi a matsayin asali, ta biyun tana tabbatar da shi ne a bisa yanayin bi. Bugu da kari a kan haka tabbas ilimi Huduri (intuitibe knowledgde) a wajen ma’asumi yana siffantuwa da ci gaba da wanzuwa, abin da ake nufi da shi shi ne iko, ba wancan ilimin da ba shi da iko ba.
Kamar yadda ilimin Ma’arifa yake karfafa mana cewa tabbas ilimi hakikaninsa dai shi ne yaye ko bayyana hakikanin abu yadda yake lallai ilimi ko bayyana hakikanin abu alama ce wacce take sama da madda (jiki ko abin da yake kamar jiki) (material) saboda kebance-kebance ta ba za su hau kansa ba, ilimi ko bayyana hakikanin lamari ba zai tabbata ba sai da saduwar samuwa da tabbatar abu yadda yake a tsakanin zukata da abin da ake son saninsa. Sanannen abu ne tabbas saduwar ilimi da hakikanin lamari ko dai ta hanyar ji ko gani ko ta hanyar hankali ko da saduwa ta hanyar da take ba tare da wasidar ji ko hankali ba wanda ake fassara shi da ma’arifa shuhudiyya ko ma’arifa ta zuciya, wadannan hanyoyin samun ilimin duk kowa-da-kowa an ba shi damar hakan ba tare da togaciya ba.
Ta wani bangaren cewa nafsun mutum kamar yadda ilimin nafsul falsafi (psychology) tana da makamomi da martabobi, tana siffantuwa da ikonta a kan riskar kulliyyat (masu gamewa kamar mutum a karkashinsa akwai Husain, Zainab, Nasiru, Ali d.s.s) (unibersals) mafi girman darajar ta a ciki shi ake cewa riska ta zuciya ko shuhudi ko ilimi Huduri na hakikanin yadda abu yake, sai dai wadannan martabobin suna da masaukai da martabobi mafi rauninsu shi ne mafarkai masu tabbata, matsakaicinsu shi ne ilhama da zancen Mala’iku, mafi karfinsu a cikin wannan tsanin da tsahonsa shi ne rabauta da wahayin Allah da karbarsa.
A bisa wannan maganar, tabbas nafsun Imani ta saba da sauran nufus ta bangaren yalwar riska da kewayewa da hakikanin yadda abu yake da rashin samun yanayin madda (non materialism) da tsarin illa da ma’alul (cause and caused) wanda ya ke hukunta Talikai duk a gaban Imami suke, ya san su, tabbas abu ne a fili cewa sanin illa yana nufinn sanin ma’aulu (misali idan aka san Allah mai samarwa ka ga ai an san wadanda Allah ya samar da su tun da shi ne asalin wadannan abubuwan) don haka sai Imami ya tsinkayi iradar da ita ce dayan wadancan illolin, haka ma sauran illolin sai ya tsinkaye su cikakken tsinkaye.
Tabbas a mafi daukakar marhalolin samuwar abubuwa daga ciki akwai wadanda suka kasance a karkashin gudanar zabin mutum tana dawowa a samuwarta zuwa ga cikakken saninsa da ita, ta karkashin hanyarsa da bayar da labarinsa mai girma da buwaya kan waninsu.
Amma a mahangar wadanda ba ‘yan Imamiyya ba a kan wannan mas’alar, suna karfafa ta da abin da baya karbar kokwanton cewa ilimin gaibu tabbas ba ma Annabawa kawai aka bawa ba, har wasu ma da ba ma’asumai ba ma an ba su, amman dai sani da yayewar abin da suka fada ba ya tabbatar da wilaya, ai wilaya tana tabbatuwa ne da nassi, ta wannan bangaren ke nan, ta wani bangaren kuma sun yi magana a kansa da sunan karama da yayewar abu a san shi ba ilimi Huduri ba (intuitibe knowlegde) wanda yake abotar isma a wajenmu.
A karshe ‘yan Imamiyya sun yi riko da wannan layin cewa wannan ilimin dole ne Annabi ko Imami ya siffantu da shi, shi ne sanin abubuwan da suke waje da sauran abubuwan da suke faruwa a cikin duniya na talikai bugu da kari ga sanin hukunce-hukunce.
An yi munakasha a kan wasu bijire-bijiren da suka zo a cikin wannan mas’alar tun a zamanin Imamai (a.s) inda amsoshinsu gaba daya suka karfafa cewa suna da ilimi Huduri, wanda ba ya cin karo da maganar jefa kai cikin halaka ko rashin samun amfani a cikin ayyukansu, kamar yadda ba sabani tsakanin abin da Sheikh Mufid ya tafi a kai ko Sheikh Dusi ko Allama Hilli, haka ma sauran malamai ‘yan baya, ai sabani ya zo ne a kan tafsirin mas’alar kawai.