SURAR KECEWA
سورة الإنشقاق
بِِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin Kai
إِذَا السَّمَاءُ انشَقَّتْ
1. Idan sama ta kece.
وَأَذِنَتْ لِرَبِّهَا وَحُقَّتْ
2. Ta saurari Ubangijinta, kuma aka wajabta mata yin sauraron.
وَإِذَا الْأَرْضُ مُدَّتْ
3. Kuma idan kasa aka mike ta.
وَأَلْقَتْ مَا فِيهَا وَتَخَلَّتْ
4. Kuma ta jefar da abin da yake a cikinta, ta wofinta daga kome.
وَأَذِنَتْ لِرَبِّهَا وَحُقَّتْ
5. Kuma ta saurari Ubangijinta, aka wajabta mata yin sauraren.
يَا أَيُّهَا الْإِنسَانُ إِنَّكَ كَادِحٌ إِلَى رَبِّكَ كَدْحًا فَمُلَاقِيهِ
6. Ya kai mutum! Lalle ne kai mai aikin wahalar da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, kuma kai mai haduwa da Shi ne.
فَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَهُ بِيَمِينِهِ
7. To, amma wanda aka bai wa littafinsa a damansa.
فَسَوْفَ يُحَاسَبُ حِسَابًا يَسِيرًا
8. To, za a yi masa hisabi, hisabi mai sauki.
وَيَنقَلِبُ إِلَى أَهْلِهِ مَسْرُورًا
9. Kuma ya juya zuwa ga iyalinsa yana mai raha.
وَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَهُ وَرَاءَ ظَهْرِهِ
10. Kuma amma wanda aka bai wa littafinsa, daga wajen bayansa.
فَسَوْفَ يَدْعُو ثُبُورًا
11. To, zai dinga kiran halaka!
وَيَصْلَى سَعِيرًا
12. Kuma ya shiga sa'ir.
إِنَّهُ كَانَ فِي أَهْلِهِ مَسْرُورًا
13. Lal1e ne shi, ya kasance a cikin iyalinsa yana mai raha.
إِنَّهُ ظَنَّ أَن لَّن يَحُورَ
14. Lalle ne ya yi zaton ba zai komo ba.
بَلَى إِنَّ رَبَّهُ كَانَ بِهِ بَصِيرًا
15. Na'am! Hakika Ubangijinsa Ya kasance Mai gani gare shi.
فَلَا أُقْسِمُ بِالشَّفَقِ
16. To, ba sai Na rantse da shafaki ba.
وَاللَّيْلِ وَمَا وَسَقَ
17. Da dare, da abin da ya kunsa.
وَالْقَمَرِ إِذَا اتَّسَقَ
18. Da wata idan ya cika.
لَتَرْكَبُنَّ طَبَقًا عَن طَبَقٍ
19. Lalle ne kuna hawan wani hali daga wani halin.
فَمَا لَهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ
20. To, me ya same su, ba sa yin imani?
وَإِذَا قُرِئَ عَلَيْهِمُ الْقُرْآنُ لَا يَسْجُدُونَ
21. Kuma idan an karanta Kur'ani garesu ba sa kaskan da kai?
بَلِ الَّذِينَ كَفَرُواْ يُكَذِّبُونَ
22. Ba haka ba! wadanda suka kafirta, sai karyatawa suke yi.
وَاللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا يُوعُونَ
23. Alhali Allah Shi ne Mafi sani ga abin a suke tarawa.
فَبَشِّرْهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٍ
24. Saboda haka, ka yi musu bushara da azaba mai radadi.
إِلَّا الَّذِينَ آمَنُواْ وَعَمِلُواْ الصَّالِحَاتِ لَهُمْ أَجْرٌ غَيْرُ مَمْنُونٍ
25. Sai dai wadanda suka yi imani, suka aikata ayyukan kwarai, suna da wani sakamako wanda ba ya yankewa.