Muassasar alhasanain (a.s)

Tattaunawa Ta Goma

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

MARUBUCI: Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
TATTAUNAWA TA GOMA Amma da kake cewa: ((3) Matsayin Annabi Muhd SAW a Addinin Shi'a, Wannan Annabi da suke karyar so da yadda suke yaudarar wawaye da son yayan gidansa, zaka ga abinda suke fada a kansa. Majlisi Zinkidi yana fada a littafinsa Biharur Anwar shafi na 43 cewa "Annabi `SAW' baya iya bacci har sai ya sunbaci Fatima a tsakanin nonuwanta" to kaga wannan babbar alama ce da ta nuna kuna kaunar Annabi yan Shi'a, sai yasa Jaza'iri ya fada a Anwarunnu'umaniyyah Mujalladi na daya shafi na 17 "Aliyu yafi Annabi Muhd Jarumta koda yace shi Annabi Muhd dama can ba jarumi bane tun asali" to don haka karku ga na kafe akan ra'ayi na na cewa Shi'a ba Musulunci bace addini ce mai zaman kansa ku zarje ni ina da hujja)).
Sai in ce maka: Allah wadaran irin wannan tunani naka, kaiconka sakamakon karancin dirayarka da jahilcinka! Shi'a sun ruwaito maganar sumbuntar kai da fuska da kumatun sayyida Zahara (a.s) masu tsarki, da kuma sanya fuskarsa mai fuskantar tsakanin kirjinta, ka sani ire-irenka masu tunanin duniyanci da shedanci su ne suke kawo wani abu a irin wannan misali, ka sani sanya fuska alkibla ba ya nufin dora fuska, mu sanya ma haka ne to wannan yana komawa zuwa ga kallonka na shedanci ne da ba zai taba fahimtar motsi da ayyuka na ma'asumi ba.
Kai tir da tunanin da ya zo maka a kwakwalwarka, kaicon shedaninka da ya sawwala maka wani abu daban da abin da yake shi ne manufar hadisin!
Ina ganin idan akwai abin suka to yana koma wa zuwa ga kallonku ga Annabi (s.a.w) da yake dora matarsa a kafadu ko kumatu a kan kumatu a gaban mutane suna kallon rawar matan Afrika a masallacinsa. Wal'iyazu bil-Lah!
Sannan idan ka koma hukuncin shari'a Annabi (s.a.w) ma'asumi ne, kuma sumbuntar 'ya saboda kauna ga kowane mahaluki bai haramta ba, wannan jawabi a matakinka ke nan na marasa fahimtar matsayin imamanci da wilayar annabawa da wasiyyansu (a.s).
Da kake cewa: ((4) Matsayin Alkur'ani a Addinin Shi'a. To shi Alkur'ani sakon da Allah ya aiko Annabi Muhd (SAW) ne dashi izuwa dukkan alamina, mu Musulmi munyi imani dashi a matsayin tsiranmu na duniya da lahira, suma a addinin Shi'a nasu Allan ya aiko nasu Annabin da nasu Kur'anin, saurara kaji daga bakin mai ita. Kulaini Zindiki ya fada a littafinsa Usul Kafi mujalladi na daya shafi na 239 cewa "Akwai wani kwafi na Kur'ani da muke kiransa Mus'hafi Fadima misalinsa yakai ninki uku na Kur'anin "Musulmai" "maganar Kur'anin Shi'a daya sha ban_ban dana musulmi ta kai haddin tawa tiri cikin addinin Shi'a duba littafin Fuslul Kitab Fi Taharifi kitabu rabbil Arbabba na Nurul Dabarisi)).
Sai in ce maka: Ka ci amanar nakaltowa: Ruwaya ba ta ce Kur'ani ba, tana maganar "Mus'hafin Fadima" ne, wanda ba Kur'ani ba ne, kamar yadda tana maganar "ilmu makana wamayakun". Kur'ani wani abu ne wanda yake guda daya duk duniya gun Sunna da Shi'a gaba daya, kokarin da kake yi na cewa wasu suna da shi kuma ya saba da wanda yake hannun mutane kana musu ayar Allah ne da take nuna cewa ba za a iya yin waninsa ba!.
Sannan abin mamaki nisantar Ahlul Baiti (a.s) ya sanya ku ganin kowa ya cancanci ya kasance yana da littafi amma ban da su da ilimi yake gangarowa daga gidajensu. Wannan yana nuna mummunar niyya game da wannan gida mai daraja mai tsarki da kake da shi.
A yanzu kai kana da bakin magana! Amsa mana wadannan tambayoyin?
Ina ayoyin nan na "Asshaihu wasshaihatu…", idan surar Ahzaba ta fi bakara yawa ina sauran ta wanda ya fi kashi biyu cikin uku nata yawa? kamar yadda kuka ce daga Umar kuka karbo. Ina kuma sauran Kur'ani kamar yadda kuka karbo da Umar cewa miliyoyin haruffa ne wanda yanzu bai wuce dubu dari uku ba kamar yadda ya zo a Ausat na Dabarani. Ina kuma surar Hifdi wal Khul'i" da kuka ce Umar yana yin salla da su?!! A yanzu kai har kana da bakin magana ka soki wasu!
Amma da ka ce: ((5) Matsayin Fatima da Aliyu a Addinin Shi'a
Wannan ma'aurata biyu masu girma da matsayin irin nasu wanda ya kamace su cikin Addinin Musulunci, to a addinin Shi'a sunfi karfin tinaninka domin matsayinsu ya zarce na du mahaluki har shi kansa Annabi (SAW) da mabiya Addinin Shi'a suke faman yi masa Jafa'i ga ra'ayoyin malamansu tsaya kaji,Hassan Dan isuhu ya fada a littafinsa Kashaful Yakeen fi Fada'ilu Amirur Muminina shafi na 229 cewa "Allah ya yiwa Manzon Allah "SAW" Magana a daren Mi'iraji da sautin Aliyu dan Abi Dalib")).
Sai in ce maka: Matsayin Ahlul Baiti (a.s) ya wuce na mahluki gaskiya ne, amma kuma bai kai na mahallici ba domin dukkan wannan matsayin Allah mahalicci ya ba su shi. Ban sani ba ko kana cikin "am yah sudunan nasa…" da kake yi musu hassada kamar sauran masu yi musu da suka gabata.
Amma maganar Allah ga manzo (s.a.w) da muryar Ali (a.s) ya inganta, idan kun karkata ruwayar kuka ce da muryar Abubakar ne kuma wannan bai sanya kun yi wa Annabi (s.a.w) jafa'i ba, to don me idan mabiya Ahlul Baiti (a.s) sun karbo daga garesu cewa da muryar Ali (a.s) sai Banu Umayya suka jirkita shi suka ce da muryar Abubakar ne wanda kai kwakwalwarka take cike da koyarwarsu zai kasance su ba su yi jafa'i ga Annabi (s.a.w) ba!
Da wannan ne nake ganin karancin tunaninka ya yawaita, jahilcinka ya tabbata! Yaya "ba" dinka zata yi jarra amma ta Shi'a ba ta yi! Da wane jirkitaccen hankali ne ka samu wannan kiyasin batacce!!?
Da wannan ne na san cewa matsayinsu dole ya wuce tunaninka!
Sannan da kai da Shi'a waye ya yi wa Annabi (s.a.w) jafa'i a matsayinka na mai tunani game da shi kamar haka:
Jingina masa shafar shedan sadda aka haife shi: Buhari 4, 94.
Jingina wa Annabi kurakurai da Umar dan Khaddabi ke yi masa gyara sai kuwa Allah ya goyi bayansa a kan abin da ya yi wa Annabi (s.a.w).
Daukar tawassuli da ziyarar Annabi (s.a.w) shirka.
Daukar Annabi da rashin kimar da ibn Abdulwahab ya shelanta cewa; shi "Darish" ne, wato dan sakon da kawai ba shi da kima sai kimar sakon kawai.
Kun sanya Annabi yana kokwanton annabtarsa har sai da wani kirista ya gaya masa ai kai Annabi ne sannan ya samu nutsuwa, amma wahayi ya sake jinkiri ya sake kokwanto har ya kusa kashe kansa.
Kun sanya Annabi (s.a.w) yana koyon tauhidi wurin kirista.
Kun sanya Annabi yana samun galaba daga shedan da hatta da a sakonsa sai ya gafala ya yabi gumaka maimakon kushe su.
Kun sanya Annabi (s.a.w) kasan darajar sauran annabawa.
Kun sanya Annabi (s.a.w) yana fushi da kausasawa har ya la'ani wasu mutane ba bisa hakkinsu ba.
Kun sanya Annabi (s.a.w) bai san yadda ake auren dabino ba har shukar mutane ta lalace.
Kun sanya Annabi (s.a.w) yana zaluntar 'yan Badar ya kama ribatattun babu hakki kuma ya karbi fidiya babu hakki.
Kun sanya Annabi (s.a.w) yana fitsari a tsaye a Bolar mutane.
Kun sanya yana kuskure da yawa har sai Umar ya gyara masa.
Kun sanya shi shedan yana iya hana shi sallarsa ta dare.
Kun sanya shi yana tsere da matarsa a cikin rundunar yaki a sahara.
Kun sanya shi yana hana abu shi kuma ya yi.
Kun sanya shi yana zuwa kallon rawar 'yan matan Afurka a masallacinsa.
Kun sanya shi yana yin alwala da giyar dabino.
Kun sanya shi yana samun shagaltuwa da rafkanwa a zuciya har sai ya manta ko ya yi salla ko kuwa, ya zo matansa ko kuwa!!
Kun sanya shi ana iya yi masa tsafi ya kama shi har ya yi wata shida bai san me yake yi ba!!
Ina tambayarka don Allah da wannan munanan tubarau da ta cikinsa kake ganin Annabi (s.a.w) da kai da Shi'a waye ya yi masa jafa'in?!!.
(Mahallin kuka) Kun sanya shi yana zo wa matansa tara a rana daya, yana zo masu suna haila, yana yin abin da bai dace ba sai ya yi bawali a tsaye, ya karbi baki yana rigingine, ya saurari waka, ya kalli rawa, ya sha Nabiz (giyar dabino)! Ya shagaltu da matarsa A'isha, ya fifita ta a kan sauran matansa, ya saurari kida da waka tare da ita, ya dora ta kan kafadarsa domin su yi kallo ta taga kumatunsa a kan nata domin kallon rawar matan Afrika, ya bar rundunarsa ta yaki ya yi tsere da ita. Kai tsarki ya tabbata ga Allah da annabinsa daga abin da suke siffantawa.

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
May, 1, 2009

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)