Gadir da Shugabancin Ali
MARUBUCI: Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
GADIR MANUNIYA CE GA JAGORANCIN ALI A.S Jagorancin tafarkin Ahlul Baiti (a.s) da aka kafa da umarnin Allah madaukaki a Gadir Khum a inda Annabi (s.a.w) yake cewa "Duk wanda nake jagoransa to Ali jagoransa ne", yana mai karawa da cewa: "Ya Ubangiji ka jibanci lamarin wanda ya yi biyayya gareshi, ka ki wanda ya ki shi", lamari ne mai muhimmanci da yake nuna jagorancin al'umma bayan manzon Allah (s.a.w) ga Imam Ali (a.s).
Wasu sun yi musun ma'anar kalmar "Wali, Maula" da suka zo a cikin wannan hadisin suna masu nuni da cewa don me Annabi (s.a.w) ya yi amfani da wannan kalma?. Su sani hannun Annabi a bude yake a kan ya yi amfani da wannan kalma ta "Wali, Maula", don haka babu mai iya iyakance masa irin kalmar da zai yi amfani da ita, kuma shi ne shugaban masu hikima. Kuma a sarari tana nuna wajabcin biyayya gareshi hada da wajabcin soyayya kamar yadda masu nuna cewa ma'anar wannan kalma tana nuna soyayya ne ko taimakawa kawai. Kuma wannan yana nuna halifancin Ali (a.s) kai tsaye ko tantama babu, saboda abubuwa kamar haka:
Na daya: Shin mai musun tafarkin Ahlul Baiti (a.s) yana ganin Annabi (s.a.w) zai tara mutane dubu hamsin zuwa dubu dari (bisa sabanin tarihi kan adadin) a wuri har ya sanya a dawo da wadanda suka yi gaba, a kuma tsaya har na baya su iso a wannan hanya mai zafi da suke cire rawunansu suna sanyawa kasan takalmansu, ga wahalar tafiya…! Domin kawai ya ce musu "Duk wanda nake abin sonsa ne to Ali (a.s) ma abin son sa ne. Ko kuma duk wanda nake abokinsa ko mai taimakonsa Ali ma abokinsa ne ko mai taimakonsa ne".
Sai ya zama ke nan wato; Duk wani sahabi ko aboki ko abin taimako, ko mai son Annabi (s.a.w) ya zama ke nan sahabi ga Ali (a.s) ko abokinsa ko abin taimakonsa, ko mai sonsa, alhalin tarihi ya nuna mana wadanda suka yi zamani da Manzo (s.a.w) suka nuna masa so, amma bayan wafatinsa suka ki Ali (a.s), sai ya zama ke nan wannan bayanin na Manzo (s.a.w) ya zama labari ba insha'i ba, alhalin Manzo (s.a.w) ya barranta daga wasa.
A tunanin mai jayayya da jagorancin Ali (a.s) shin wani mai hankali zai yi hakan balle Annabi (s.a.w) da ya fi kowa kamala; Ashe yana bukatar haka bayan ya riga ya gaya wa musulmi gaba daya da cewa su abokai ne masoya juna mataimaka juna. Kai har ma ya ce idan daya ya koka yana gabas ko yamma daya kuma yana gabas ko yamma bai taimaka masa to shi ba musulmi ba ne. Ashe duk bayan wannan sai Annabi ya tara mutane domin kawai ya gaya musu hakan game da Ali (a.s)!
Na biyu: Sannan kuma har Annabi ya yi addu'a da Allah ya taimaki wanda ya taimaka masa, ya tabar da wanda ya ki taimaka masa, kuma ya kebance shi da wannan banda sauran musulmi. A yanzu kana ganin wannan idan yana nufin so kawai zai kebanta da shi a cikin dukkan sahabbai! Don haka sai ya kasance sauran sahabbai bai wajabta son su ba ke nan, don haka ba laifi idan mutum ya ki su, kai yanzu ka yarda da hakan!.
Na uku: Bai'ar da aka yi masa, kuma hatta da halifofi sun yi masa bai'a a wannan wuri ba ta nuna so kawai, ta hada har da mika wuya ga jagorancinsa. Ga Umar dan Khaddabi bayan ya yi masa bai'a a nan take ya ce: Farin ciki ya tabbata gareka ya dan Abi Dalib, hakika ka wayi gari jagorana kuma jagoran dukkan mumini da mumina.
Na hudu: Murnar da Abubakar da Umar suka yi masa suka ce: Farin ciki ya tabbata gareka ya dan Abi Dalib, ka zama shugabana kuma shugaban kowane musulmi. Ban sani ba ko kai mai musun jagorancin Imam Ali (a.s) kana nufin Umar bn khattab ko Abubakar ba su fahimta ba ne, da su da sauran sahabbai da suka yi wa Imam Ali (a.s) murnar zama jagoransu. Ko kuma kana nufin ka ce suna taya shi murnar cewa dole ne su so shi, alhalin soyayya abu ne wanda yake na tarayya tsakanin musulmi. Kuma da yadda kake nufi ne da ba su taya shi wata murna ba. Ko kuwa bai'ar da suka yi masa a wannan sahara mai zafi tana nufin soyayya da kauna kawai!, kuma idan haka ne wannan bai kebanta da shi ba, sai a yi wa kowane musulmi bai'a domin nuna soyayya da kauna gareshi. Sannan kuwa idan an yi masa bai'a domin nuna soyayya da kauna ne to yaushe ne aka nuna masa kauna da soyayya bayan wafatin Annabi (s.a.w) yayin da aka kewaye gidansa da wuta aka cutar da matarsa har ta yi bari.
Duba littattafai kamar: Shawahidittanzil na kanduzi bahanife: 1/ 175. Yana bi'il mawadda: juzi 1, shafi: 30 -31. Tarikhi bagdad: 8/ 290. Kuma Ahmad da ibn majah sun kawo haka daga Barra'. Kamar yadda Tirmizi da nisa'i daga Zaid. Ka duba littafin Gadir, zaka ga daruruwan masdarori da suka kawo wannan al'amarin. Haka nan Dabari ya kawo wannan magana ta taya murna gareshi.
Na biyar: Gabatarwar da manzon Allah (s.a.w) ya yi a farkon hadisin yayin da yake cewa da su: "Shin ba ni ne shugaban kowane mumini da mumina ba?! A fili yake cewa ba komai ne karshe yake nufi sai abin da farko yake nufi.
Na shida: Maganar da ya rufe da ita na cewa Allah ka shaida bayan ya gama da kuma shaidawarsu. Ka ga ke nan sun shaida kan wannan al'amari mai girma ne da ya kebance shi a cikin sauran musulmi na wannan lokaci.
Na bakwai: Idan muka yi kokwanto kan cewa wannan kalma tana nufin masoyi ko shugaba, to sai mu yi hukunci da duka ne da ya hada da wajabcin sonsa da kuma mika jagoranci gareshi; domin ka'idan nan ta ilimin Usul ta komawa ga ma'ana gamammiyya "amm" idan an rasa komawa ga kebantacciyar ma'ana "khas". Don haka wannan ya tabbatar da ma'anar shugabancinsa da jagorancinsa kan duk wani mutum bayan Manzo (s.a.w), domin umarnin Allah bai kebanta da musulmi ba.
Na takwas: Akwai ayoyin Kur'ani da hadisai masu yawa da suke karfafar ma'anar jagora. Kamar ayar "kawai shugabanku … da muka kawo a bayanin da ya gabata wanda a karara take nufin jagora saboda karinar ayar da ta gabace ta, da wacce ta biyo baya da kuma tafsiran masu tafsirai.
Na tara: Daga hannunsa da Manzo (s.a.w) ya yi a wannan wuri da kuma nuna shi ga al'ummarsa, ba ya nuna komai sai ma'anar jagoranci da shugabanci ga wannan al'umma tasa bayan wafatinsa. Hada da cewa bayan wannan waki'a ta Gadir manzon Allah (s.a.w) bai yi wata biyu a duniya ba ya rasu.
Ya kai mai jayayya da cewa wannan yana nuna jagorancin Imam Ali (a.s) ne, akwai abubuwa masu yawa game da hakan, sai dai Sheikh dan fodio yana cewa: Masu hikima sun ce: Nuni ya isar wa yin magana ga mai hankali. "ÇáÅÔÇÑÉ ÊÛäì Úä ÇáãŞÇáÉ ááÚÇŞá"
Na goma: Saukar azaba kan Nu'uman yayin da ya ki yarda da shugabancin Ali (a.s) nan take, da musun da ya yi wa Annabi (s.a.w) da cewa yaya zai ce su bi dan amminsa bayansa (s.a.w), da saukar azaba kansa wanda yake nuna dalilin saukar da ayoyin farko na surar Ma'arij. Ka duba tafsirin Durrul Mansur, da asbabun nuzul na Suyudi, da littattafai kamar Nurul absar na shiblanji basha'fi'e. Duk sun kawo ingancin wannan magana game da halakar Nu'uman yayin da ya yi musun jagorancin Ali (a.s) a wannan mas'ala ta Gadir.
Na sha daya: Ya tabbata a ilimi mantik da palsapa cewa; Ma'ana gamammiya "kulli" fuska ce ta "juz'i", don haka wilaya a nan tana nufin ma'anar jagoranci, musamman da yake juz'i ana kawo shakku kansa, domin a sani har abada ba yadda za a yi juz'i ya kasance fuskar kulli.
Mu sani wannan kalma ta wilaya kalma ce da tana daga cikin kalmomin da aka yi wa tawili kamar yadda aka yi tawili ga wasu kalmomin da wasu daga umarnin Annabi don son rai ko kuma saboda rashin yarda da wannan abin. Wasu sukan yi kokarin tawilin wasu abubuwa ne domin gyara barnar da aka yi wa addini wanda wannan cin amanar Allah da manzonsa ne. Kuma wannan ba sabon abu ba ne, domin ba kawai tawili domin rashin yarda ba, hatta da zamanin Annabi (s.a.w) da yawa ya bayar da umarni amma ba a bi umarninsa ba.
Amma batun cewa Annabi (s.a.w) ya rayu akan tafarki da shi da mabiyansa ba bisa mazhaba ba; ai ba komai muka tabbatar maka ba da wannan maganganun bayan da muka kawo game da kasuwar jama'a 73 sai wannan, wato: cewa wannan jama'ar da take kan abin da Annabi (s.a.w) ya bari su ne mabiya Ahlul Baiti (a.s). Ai wasiyyar da Annabi (s.a.w) ya yi ta bin Littafin Allah (s.w.t) da Ahlul Baiti (a.s) yana nuni da hakan. Kuma bin su shi ne dawwama kan tafarkin Annabi yardajje gun Allah (s.w.t).
Ka sani Annabi (s.a.w) shi ne shugaban masu hikima da hankali, sannan kuma ya san babu wani Annabi bayansa, kuma babu wani wahayi bayan nasa, don haka ya dauki matakai da zasu hana bacewar al'umma da karkacewarta. Idan kuwa ka ga al'umma ta ki to wannan ita tajiyo wa kanta. Don haka wahalhalun da kake gani da rarraba duk ya faru ne tun farko saboda barin wasiyyoyinsa. Kuma abin da ya faru ga yahudawa da Kirista shi ne ainihin abin da ya faru ga musulmi kwabo da kwabo, sai dai mu musulmi muna da ludufin Allah (s.w.t) na cewar muna iya bugun kirji mu ce: Duk wanda yake son ya ga sakon manzon Allah (s.a.w) ba tare da wani jurwaye ba to ga shi nan a tare da Ahlin gidansa; alayensa Ahlul Baiti (a.s).
Darajar Ahlul Baiti (a.s) ta fi ta annabawan Banu Isra'ila (a.s), ruwayoyi sun zo cewa; malaman al'ummata sun fi (ko kuma kamar) annabawan Banu Isra'il suke. Matsayin malaman al'umma matsayi ne na wasiyyan Annabi (s.a.w) da Allah ya ba su ilimi, a cikin kofar birnin ilimin Annabi Imam Ali (a.s) yake. Ruwayoyi sun zo da karfafar ilimin imamai (a.s) a kan komai kamar yadda aka yi nuni da shi a littafin Kafi na Kulaini sh; 260.
Su ne suke da ilimin da babu mai shi kamar yadda duniya ta yi musu sheda da shi; suna da ilimin zahiri da badinin Kur'ani, su ne masu ilimin kowace aya da sababin saukarta, da sha'anin nuzul, da muhkam da mutashabih, da nasih da mansukh, da mujmal da mubayyan, da amm da khas, da mutlak da mukayyad, da tazil da tawil.
Amma batun tsayuwar daular imamai a hannun Imam Mahadi (a.s), da batun cewa zasu yi mulki irin na alayen Dawud: Wannan ya inganta cewa Annabi (s.a.w) ya bayar da labarin yadda hukumar Imam Mahadi (a.s) zata kasance, domin kada ta zo mutane su sha mamaki. Mu sani babu abin da Annabi (s.a.w) ya boye wa wannan al'ummar domin kada ta sami rudewa. Sai dai ya rage wa al'umma ta karba ko ta ki karba. Annabi Dawud da Sulaiman (a.s) sun yi hukunci da iliminsu ne, kuma Allah ya ba wa Imam Mahadi (a.s) wannan ikon kamar yadda Annabi (s.a.w) ya isar mana.
Sannan kuma mai son zuwa ga ilimi dole ne ya zo ta kofarsa, idan kuwa ya ki ba a la'akari da shi, kamar jami'a ce da wani yake da iliminta amma bai yi karatu a can ba, babu yadda za a ba shi shedar yin karatu a jami'a. Wannan ilimin ne ya sanya Ubangiji ya mika musu ikon wannan duniyar da tafiyar da al'amuran bayinsa. Kafi: sh.407.
Don haka ne aka ruwaito cewa: manzon rahama (s.a.w) ya riki hannun Hasan da Husain (a.s) sannan sai ya ce: Wanda ya so ni, kuma ya so wadannan, da babansu, da babarsu, to ya kasance tare da ni a darajata a ranar kiyama. Masnad Ahmad bn Hambal, j 1, shafi: 77. Tirmizi ya ruwaito shi a j5, shafi:305, ya ambace shi hadisi kyakkyawa.
Domin kawata wannan bahasi na jagorancin Imam Ali (a.s) wanda ya yi kama da na wasiyyan annabawa da muka kawo baya, ta yadda zamu gane abin da ya faru cikin al'ummun annabawan da suka gabata cewa kwafinsa ne ya faru cikin wannan al'ummar ta Annabi (s.a.w), zan so in kawo amsar da na ba wa wani mai musun jagorancin alayen manzon Allah (s.a.w) ina mai cewa da shi:
Ka sani cewa yayin da al'umma ta bar Ahlul Baiti (a.s) ba kowa ne ya watse ya bar su ba, domin sun samu wasu jama'a masu karba daga garesu. Ka duba ka gani mana wancan bangaren ya ruwaito hadisai 5 374 daga Abuhuraira da ya zauna da Manzo (s.a.w) wata goma sha shida ne kawai a rayuwarsa kafin a aika shi Baharain mai hidima ga gwamnan Manzo na can. Amma Imam Ali (a.s) ya zauna da manzon rahama (s.a.w) shekaru 33, kuma shi ne ya fi kowa ilimi da ittifakin sahabbai da wannan al'ummar gaba daya. Amma sai gashi ba shi da hadisan da suka wuce guda dari biyar 500, 'ya'yansa (a.s) kuwa sai abin da hali ya yi. A yanzu kana tsammanin sun yi shiru ne sun kame bakunansu tsarkaka alhalin suna wasiyyansa ba su ce komai ba!
Amma da kake cewa kalmar "Wali, Maula" ba a fili take ba, sai in ce maka: Yana da kyau ka yi wa kanka adalci domin dukkan hadisan Gadir da wasiyya da jagorancin Imam Ali (a.s) bayan Annabi (s.a.w) suna da karinoni a kan ma'anar jagora. Hada da cewa farkon hudubar Manzo (s.a.w) da karshenta duk yana nuna wannan karinar karara. Wadannan karinonin kuwa a cikinsu akwai: "zikra liman kana lahu kalbun au alkas'sam'a wahuwa shaheed".
Amma batun da kake cewa ba a ruwaito hadisin Gadir ba sai in ce maka: Sahabban da suka rawaito Gadir suna da yawa kwarai matuka, ka koma wa littafin Gadir na Allama Sheikh Amini ka sha mamaki, kuma akwai ruwayoyi sama da 360 da ya yi nuni da su, wadanda sun zo game da Gadir daga sama da sahabi 125.
Sannan kada ka dauka in ka kaddara masu ruwaya koda daya ne idan ta inganta ba ta zama hujja, domin ku kun doru a abubuwa da yawa kan ruwaya mai maruwaici daya tal hatta a al'amarin akida. Wannan hadisin an kasa boye shi, don haka ya zo hannun mutane da ikon Allah (s.w.t), amma akwai wasu hadisai da siyasa ta kan sanya a ki yada su, ko kuma boye wasu kalmominsu ko canza su kamar karshen hadisin halifofin Annabi (s.a.w).
Amma da'awar cewa Annabi (s.a.w) ya yi mummunar addu'a ga wanda ya ki biyayya ga Ali (a.s) da cewa wannan ya saba wa usulubin da'awa ta gari da da'awarka ta cewa Annabi (s.a.w) ba ya yi wa al'umma addu'a mummuna da fakewa da cewa rashin taimakawar yana iya kasancewa cikin rashin sani. Sai na ce maka: Duk wannan babu kokwanto cikin shari'a idan ta inganta, domin Annabi Nuhu (a.s) ya yi wa al'ummarsa mummunar addu'a, haka nan Manzo (s.a.w) ya yi wa wasu a farkon da'awarsa har Allah (s.w.t) ya halakar da su a rana daya, kuma ya saukar masa da ayar da take cewa: "Ka ci gaba da abin da aka umarce ka, mu mun isar maka da masu isgili".
Sannan abin da ka fada na cewa ya saba wa da'awar Annabi (s.a.w) da Kur'ani mai girma ta la'antar duk wani wanda ya saba wa tafarki bayan gaskiya ta zo masa: surar "Tabbata yada Abi lahabin" babban misali ne gareka. Hada da abin da yazo yana la'antar magabata kamar su Fir'auna da wadanda suka gabace shi da wadanda suka zo bayansa, da la'antar munafikai da Kur'ani ya yi, da masu cutar da Annabi (s.a.w) aka kuma muzanta su muzantawa mai muni kamar kiransu marasa hankali da sauransu.
Sannan a cikin maganganunka akwai alamar tsananin kushewa game da abin da ya zo yana yabon Ahlul Baiti (a.s) ko yana ba su wata falala, wannan ba ya cikin dabi'ar mumini.
Amma da'awar ayar tablig a Arfa da ka yi hakika masdarori sun zo suna masu tabbatar da saukar wannan aya a Gadir, akwai dalilai masu yawa kan hakan, sannan kuma wasu sun kawo ta game da cewa a ranar hajjin wada' ne. wasu kuma sun hada duka biyun ne, kuma wannan abu ne mai sauki, ana iya hada su, da cewar ta sauka kuma Manzo (s.a.w) ya karanta ta a dukkan wadannan wuraren.
Sannan musun hadisi ko ingancinsa saboda ya yabi Ahlul Baiti (a.s) wani abu ne da na fahimta yayin da kake maganar musun ruwayar Suyudi, ka sani wannan ya inganta daga littattafai masu yawa tun kafin Suyudi, amma wani abin da nake fahimta daga wajenka duk wata magana da ta yabi Imam Ali ko Ahlul Baiti (a.s) ko ta karfafi wilayarsu, to kana kokwanton ingancinta ba tare da ilimi ba, ko kuma saboda inadi ne! Shiblanji ya karbo shi daga sa'alabi, sannan kuma Halbi ya kawo shi mursali a matsayin wani hadisi da aka sallama wa ingancinsa, a siratul halbiyya, j 3, shafi 214.
Amma batun me Annabi (s.a.w) ya bari ga al'ummarsa, ya riga ya tabbata cewa; shi ne tafarkin da Ahlul Baiti (a.s) suke kai, su ne ma'auni da za a koma gareshi yayin sabani. Hadisin wasiyyar manzon Allah (s.a.w) wanda yake nuni zuwa ga cewa ya bar mana abubuwa biyu da idan muka yi riko da su ba zamu taba bata ba har abada; Littafin Allah da Ahlul Baiti (a.s) ya isa hujja. Wannan hadisi ne da babu wani wanda ya taba musun sa, koda kuwa ya yi da'awar cewa ba ya bin tafarkinsu.
Addini ya cika, kuma daga cikin cikarsa akwai biyayya ga Ahlul Baiti (a.s) kamar yadda Manzo (s.a.w) ya yi wasiyya da bin su, wannan duk yana daga cikar addini. Allah (s.w.t) da manzonsa (s.a.w) sun barranta daga wautar da ake jingina musu, Manzo (s.a.w) ya san wannan addini shi ne karshe, kuma yana da hadafin shiryar da mutane gaba daya, ba zai yiwu ba ya tafi ya bar su kara zube, ba su san inda zasu dafa ba.
Kuma wannan rashin hikima abin takaici ba wanda ake jingina wa shi sai mafi hikimar bayin Ubangiji, kowane jagora zai tafi yana nuna wa al'umma makomar da ya kamata ta bi, amma sai Annabi (s.a.w) ne ake jingina wa rashin hadafi!
Amma batun da'awar da ka yi na cewa Allah (s.w.t) ya yi alkawarin kare sunnar ma'aiki sai na ce maka: Allah bai yi alkawarin kare Sunna ba, ya yi alkawarin kare Kur'ani ne! don haka ne ma Sunna take cike da mai inganci da waninsa: Wannan ne ma ya kawo ilimin hadisi da masu ruwayarsa da sauransu. Abin mamaki rashin ma'auni da kuma wata ka'ida ko madogara mai kyau da kake da ita, ya sanya ka kana magana kana warwara. Kana musun wata sunnar ta Annabi (s.a.w) da ya bari saboda ta yabi Ahlul Baiti (a.s) ko ta shugabantar da su, a lokaci guda kuma kana cewa Allah ya yi alkawarin kare ta. Idan ka san Allah ya yi alkawarin kare ta to don me kake wahalar da mutane wajen musun ta da neman ba ka hujjoji kan ingancinta!?
Sannan da Allah ya yi alkawarin kare sunnar Annabi (s.a.w) ai hadisai suna kunshe da sunnar Annabi (s.a.w) wanda ya hada bayanin zancensa sai ga shi a tarihin musulunci manzon Allah (s.a.w) bai dade da bari duniya ba, aka tattara dukkan hadisansa da sahabbai suka rubuta aka konsa su gaba daya. Wannan lamarin ne ma ya sanya bayan shekaru tamanin da dan Abdul'aziz ya nemi hada hadisan Annabi (s.a.w) an riga an yi lati, an shigar da kage da karya da yawa an jingana Annabi (s.a.w) al'amarin da ya sanya wajbcin nemo ingantacce domin a tsame shi da wanda bai inganta ba domin a yi wurgi da shi.
Amma game da abin da aka yi wa alayen Annabi (s.a.w) ina mamakin jahiltar ka ga addini: Idan ka yi musun tarihin la'antar Imam Ali (a.s) to lallai ka nuna wa duniya rashin saninka da tarihin addininka sannan kuma ka jahilci musallamat na tarihi da al'umma ta hadu a kai. Amma Imam Hasan (a.s) bai bayar da iko hannun Banu Umayya ba, sai dai abu ne wanda ya zama masa tilas kamar yadda dukkan imamai (a.s) suka yi hakuri kan abin da ya fi karfinsu. A yanzu zaka iya cewa manzon rahama (s.a.w) ya bar mulki ga mutanen Makka ne bisa sonsa, ba don saboda ba shi da karfin yardar al'umma da zai iya kwata daga hannunsu ba?!
Ka sani musulunci bai zo da shirmen kwatar mulki daga hannun wani ba, ko dankarawa al'umma abin da ba ta so koda kuwa daga wani annabi ne, don haka ne ma da mutanen Madina ba su zabi Annabi (s.a.w) a matsayin jagoransu ba, da har ya bar wannan duniya bai kafa daula ba. Domin yana iya shugabantar mutane ne duk da kuwa Allah shi ya zaba amma sai da kuma zabin mutane.
Sannan da kake cewa ya kamata a yi shiru kan abin da ya faru: Inda abin da ya faru ya kamata a yi shiru kansa da Kur'ani ya koyar da mu hakan: sabanin hakan Kur'ani ya karfafi mu binciki abin da ya faru baya domin kada mu fada irinsa, sannan kuma manzon rahama (s.a.w) da wasiyyansa (a.s) duk sun koya mana hakan; Wannan doka da Basari da Nu'uman Alhanafi suka sanya ta saba da Kur'ani da hadisai ingantattu kuma ba yadda za a yi ta fitar da mu matsalolinmu na duniya da lahira.
Ka sani binciken tarihin da ya gaba ta, ba don a gano laifin wani ba ne, sai dai domin ka san waye yake hujja kanka ka bi shi da wanda yake ba hujja ba, domin yanzu muna iya tambaya cewa; waye yake hujja ne bayan Annabi (s.a.w) a kanmu mu karbi addini daga gareshi waye kuma ba hujja ba?! Kai ka dauka domin a ce wane ya yi laifi ne, wane kuma bai yi ba shi ke nan. Idan kuwa haka ne da ba shi da amfani, da Kur'ani bai yi binciken halayen wadanda suka gabata ba?.
Ka rika sanin abin da kake cewa: Ka sani hujja tana cikin biyayya ga Littafin Allah da wasiyyan Annabi (s.a.w) wannan kuma su ne hujja a kan kowa, idan wani ya ki bin su wannan shi ya jiwo wa kansa, wannan kuwa ko musulmin tun lokacin Manzo (s.a.w) ko a yau ko a nan gaba, kamar yadda sauran kafiran duniya duk wannan hujja ne kansu.
A natijar wannan bahasin mun cin ma abubuwa kamar haka: Na daya: Ahlul bait (a.s) su ne kadai makoma da Allah (s.w.t) da manzonsa (s.a.w) suka bari tare da Kur'ani mai daraja. Na biyu: Maganar manzon Allah (s.a.w) ita ce hujja, kuma ya yi wasiyya da Ahlul Baiti (a.s). Na uku: Ahlul Baiti (a.s) su goma sha biyu ne, kuma Shi'a imamiyya suna biyayya garesu gaba daya a matsayinsu na halifofin Annabi (s.a.w) da Allah ya ayyana masa. Na hudu: Tun farkon zuwan Manzo (s.a.w) ya ambaci kalmar halifa da waziri ga Imam Ali (a.s). Na biyar: Har yanzu ka kasa nuna waye jagoranka da kake biyayya gareshi, ko kuma ma ba ka san shi ba!
Amma musulmin duniya kowa yana da nasa ra'ayi a kan hakan, domin akwai wanda ya hana a ma koma baya a kalli wannan kuskure da ya faru da ya hada da barin wasiyyar Annabi (s.a.w) kan wanda zai gaje shi a tafiyar da lamurran al'umma bayansa, don haka ne ma wasu suka yi kokarin toshe wannan kuren da cewa; ba a ma yi wasiyya ba duk da lamarin wasiyya da Littafin Allah da Alayen Annabi (s.a.w) wani abu ne mutawatiri.
Sa'an nan ga lamarin kwacewa 'yar manzon Allah gonarta da manzon Allah ya ba ta wacce aka fi sani da Fadak wadda hatta da asbabun nuzul na Suyudi da littattafai da yawa sun yi magana kan cewa yayin da aka saukar da ayar: "Ka ba wa ma'abocin kusanci hakkinsa…". Sai manzon Allah ya ba wa Fadima Fadak.
Mafi muni shi ne sabbaba mata yin barin dan cikinta Muhsin da kuma fasa kyauren gidanta da dukansa ya sanya yi mata rauni da huda kirjinta kusoshi biyu a bayan kyaure da ta kasance, wanda ya yi sanadin rayuwarta har ta yi fushi da al'ummar musulmi gaba daya ta nemi a boye kabarinta kada kowa ya sani domin kawai ta nuna fushinta da wannan al'umma. Har ma Buhari ya kawo maganganunta masu zafi kan halifofin farko da suka gabaci mijinta Imam Ali (a.s) na rashin yi musu magana da rashin amsa sallamarsu, da alkawarin yi musu mummunar addu'a a salla, da alkawarin kai karar su wurin Annabi (s.a.w), wannan duk a sahihul Buhari, kan sha'anin da ya faru na jagorancin al'umma bayan Annabi (s.a.w). Wannan ne ma ya sanya aka samu kowa yana kallon abin ta mahangarsa da da ra'ayoyi iri-iri daban-daban daidai gwargwadon fahimtarsa.
Sai aka kasu gidaje mabanbanta, kowa yana da nasa ra'ayi, sai masu bin koyarwar Banu Umayya da malamansu suka tafi a kan farin ciki da wannan lamari, wani abin mamaki shi ne yin biki da ranar da aka kashe danta wato; Imam Husain (a.s) a ranar Ashura. Kwanan nan ne wasu littattafai suke dada karfafa jin dadin abin da ya faru na kashe shi suna masu nuni da gwara haka! kai suna cewa ma laifinsa ne!! Wal'iyazu bil-Lah!.
Lamarin sanin matsayin wadanda suka yi watsi da wasiyyar Annabi (s.a.w) lallai lamari ne mai wuyar sha'ani da ya sanya gaba mai tsanani tsakanin musulmi, har ma na kai ga natijar cewa duk wanda ya yi bincike ya samu abin da yake ganin shi ne zai zame masa uzuri har ga Allah to sai ya yi aiki da wannan ya kyale sauran masu ra'ayoyi kowa ya je da nasa in ya so ranar lahira sai Allah ya yi wa kowa hisabi da abin da yake gani maslaha ga kowane bawa daidai yadda ya yi ikhlasi ya cimma gaskiya ba son zuciyarsa a ciki.
Mafi yawancin masu bayani sun kawo wannan canjin a matsayin abin da ya haifar da musibu sakamakon kauce wa Ahlul Baiti (a.s) da ya sanya komai ya jirkice kuma sun fassara wannan lamarin yana cikin irin matsayoyi da Annabi ya yi nuni da shi mai tsanani kan wasu daga cikin sahabbansa a hadisan nan da Buhari da Muslim da Ahmad da sauran manyan malaman hadisi suka ruwaito: Muslim: 4/1793. Buhari: 28/26. Masnad Ahmad: 1/ 253, 258.
A ciki akwai hadisan da suka yi nuni da za a yi wuta da wasu daga sahabbai sai ka duba, har ma manzon Allah ya ki yarda sai a ce masa ba ka san abin da suka yi bayanka ba, a wasu ruwayoyin sun yi ridda bayanka. Babban abin mamaki duk daga littattafai ingantattu da Sunna, da Wahabiyawa, da wasunsu suka yarda da su. Sannan Abuddarda' da Anas dan Malik sun yi furuci tun a zamaninsu da babu wani abu da ake yi lokacin manzon Allah (s.a.w) sai da aka canja shi, hatta da salla!
Hada da abin da manzon Allah (s.a.w) ya gaya wa halifa na farko kamar yadda ya zo a cikin littafin nan na Muwadda'r Malik cewa; Ba zai nema masa gafara ba domin bai san abin da zasu yi ba a bayansa. Kuma wannan lamari na matakin da Annabi ya fada a hadisai madaukaka su ne abin da wasu manyan sahabbai masu daraja kamar su Salman Farisi, da Ammar, da Bilal, suke a kai; sai dai ni bayan bincike da ya dade tare da malamaina na tafi a kan cewa; Wannan lamari ne mai wuyar sha'ani kuma ina ganin wadanda suka yi hakan na saba wa wasiyyar Annabi (s.a.w) da hayewa karagar jagoranci su ne suka san dalilanasu, amma Imam Ali (a.s) shi yana da nasa mahanga game da abin da suka yi.
Amma matsayin wadanda ba su yi biyayya da koyi ga tafarkin Ahlul Baiti ba?: Wannan ma matsayinsu yana koma wa ga Allah madaukaki ne, kuma shi ne zai saka wa kowa da abin da ya yi daidai gwargwadon ikhlasinsa da tsarkin niyya. Domin haka ne kowa sai ya yi sa'ayi "Hakika sa'ayinku mabambanci ne… da ayoyin da suka biyo bayanta.
Sai kowa ya koma ya yi binciken wasiyyar Annabi (s.a.w) da cewa me ya yi wa al'umma wasici da shi, kuma shin al'umma ta kiyaye ko kuwa? Waye ya ce a yi biyayya gareshi bayansa domin ya binciki me ya ce domin ya samu uzurin yin addini daidai a wurin Allah madaukaki? da sauran tambayoyi masu yawa da suke cikin kwakwalenmu.
Idan ka duba da mai gani zaka samu wadannan hujjoji a fili kuma mun gabatar maka da su tun tuni, sannan kana iya karawa da wannan: Kifayatul asar: shafi: 134: inda aka yi nuni da matsayin Ali kamar Haruna da Musa (a.s) ne, da wasiyya da imamai goma sha biyu. Sharhu Ihkakul Hakk: j 13, Mar'ashi Najafi: 78: a cikin akwai magnar Fakhrur Razi da take nuna ismar Ulul amr da dogaro da wannan ayar da cewa su ma'asumai ne ba sa sabo. Sanna ka duba Zamakhshari: Manakib; 213. da Hamwini: fara'idus Simdain. Da Kanduzi a Yanabi'u: shafi: 82, Istambul. Da: sauran masdarori masu yawa matuka. Kamar Sawa'ikul Muhrika: 234. Nahajul balaga: j 2, shafi: 27. Ibn Abil Hadi: j 9, shafi: 313.
Wallahi su ne Khairu ummatin (a.s) da aka fitar da su garemu mu mutane! yaya sauran mutane zasu kasance Khairu ummatin alhalin wannan al'ummar ta Annabi (s.a.w) ta kashe daukakkin jikokinsa da alayensa wasiyyansa goma sha biyu gaba daya, sai na karshe da Allah (s.w.t) ya boye domin ya bayyana a karshen duniya don ya cika ta da adalci. An kashe alayen Annabi (a.s) fiye da kisan da yahudawa suka yi wa wasiyyan Annabi Musa (a.s) da wanda suka yi wa wasiyyan Isa (a.s)!
Suyudi ya ruwaito cewa: Ahlul baiti (a.s) ake nufi da su a tafsirin wannan ayar. Da sauran littattafan Sunna da Shi'a masu yawa da suka nuna ma'anar da manzon Allah (s.a.w) ya bayar ta cewa alayensa su ne Khairu Ummatin (fiyayyar al'umma).
Lallai ne wanda yake yi wa Annabi (s.a.w) kallon wani mutum mai siffofi marasa daraja da reni ga matsayinsa zai ga bai yi wasiyya ba domin reni, ta yadda ya nuna muminai su yi wasiyya da cewa; Kada mumini ya sake ya yi kwana uku bai rubuta wasiyya ba, amma shi ka sanya shi ba ya yi. Koda yake kun samu maganarku ta yi karo da juna a lokacin da kuka ce ya zo ya rubuta wasiyyarsa sai Umar dan Khaddabi ya hana shi ya ce: Ba ya cikin hankalinsa!!! Kamar yadda kuka kawo hakan a cikin Littafin Buhari, Inna lil-Lahi wa'inna ilaihi raji'un!!!
Hafiz Muhammad Sa'id
www.hikima.org
hfazah@yahoo.com
Tuesday, Nobember 17, 2009