Muassasar alhasanain (a.s)

Gurbatar Kur'ani

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Kur’ani Mai Daraja: "Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18) .

Gurbatar Kur'ani "Hakika wannan (Littafin na) Kur'ani yana shiryarwa zuwa ga abin da shi ne ya fi zama daidai, kuma yana yi wa muminai wadanda suke yin kyawawan ayyuka albishir cewa lallai suna da lada mai girma". 17: 9.

Littafin Allah Madaukaki Hakika Allah ya saukar da kur'ani mai girma mai ingancin da babu wani kowanto a cikinsa, kuma barna ba tazo masa ta gabansa da ta bayansa, kuma ya jibanci daukar nauyin kare shi da kansa.sannan kuma sai manzon Allah (S.A.W) ya yi sharhinsa yayi bayaninsa da maganganunsa da ayyukansa madaukaka, don haka babu wani abu da ya rage mana bayansa sai neman fahimtarsa da aiki da shi. Kuma kur'ani littafi ne da yake magana da mutane a kowane zamani da wuri, ya sauka yana mai bayanin komai. Sai dai kuma ba ya iya cimma fahimtarsa da gane shi sai da abin da ya zo da su na daga asasai da usulubai da wajibi ne a bi su. Wadannan asasai dausulubai din kuwa ita ce wacce shi kur'anin ya bayyana ta saboda kaiwa zuwa ga fahimtarsa, kuma kowane malami da yake son bin ta zai iya kaiwa gareta. Yayin nan ne zai sami sharhin da annabi (S.A.W) ya yi mata. Kuma zai ga kur'ani da sunna suna kammala juna ne, kuma wannan ne zai bude masa wasu fagage sababbi masu fadi da zai aminta da su a cikin bincikensa.

Kage A Kan 'Yan Shi'a Daga cikin babatu da tuhumar da ake amfani da su domin sukar Mazhabar Ahlul Baiti (A.S) domin rusa ko ruguza wannan mazhabi madaukaki da kima da daraja wanda yake dogaro da abin da ya zo daga wasiyyar annabi (S.A.W) ta biyayya ga Ahlul Baiti (A.S) bayansa, kuma ta dogara da kur'ani mai daraja da sunnar annabi (S.A.W) ingantacciya a kan hakan. Amma sai ga makiya wannan mazhaba madaukakiya ta alayen annabi (S.A.W) ba ta gushe ba tana samun zagon kasa da suka daga makiyanta, da kage-kage da tuhumce-tuhumce, da kuma jafa'i da mugun kulli da batanci domin ganin sun ruguza kima da daraja da inganci na wannan mazhabi mai daukaka domin kokarin ganin sun nisantar da dukkan al'ummar musulmi daga fahimtar sakon da take dauke da shi, wanda yake kunshe cikin abin da muka ambata, da kuma kawar da su daga karanta littattafan wannan mazhabi mai daraja, da kuma neman hana sauran musulmai yin hulda da su da hana tattaunawa da su, domin kada su tasirantu da karfafan hujjojin da suke da su, wadanda suka dace da fidirar dan Adam wacce ba ta gurbata ba.
Kuma sanannen al'amarine cewa wannan mazhabi yana amfani da hujjojin da suka ginu akan kur'ani da sunna da hankali masu gamsarwa da kowane dan adam mai adalci zai mika wuya garesu bayan komawa zuwa garesu. Kuma duk wanda ya koma wa littattafansu to lallai zai iya fahimtar gaskiyar da yake cikin sakonsu mai girma kuma duk wani hijabi da shamaki da aka gindaya masa domin kiyayya ko nisanta daga wannan mazhabin to zasu yaye su kwaranye. Kuma wannan yana iya sanya shi mika wuya ga Ahlul Baiti (A.S) da karkata zuwa ga maganganunsu ko kuma mafi karancin abu da zai yi, shi ne; ya yi adalci ga mabiyansu.
Daga cikin mafi hadarin kage da ake yi wa wannan mazhabin da mabiyinsu Shi'a shi ne; mas'alar cewa sun yi imani da tawayar kur'ani, kuma suna da wani Kur'ani koma bayan wanda yake hannun sauran musulmai! Da tuhumar cewa Shi'a sun jirkita Kur'ani, da cewa; kuma sun caccanza ayoyinsa da cewa; wai sun kara wasu ayoyinsa kuma sun cire wasu daga cikinsa! da sauran makamantan irin wadannan tuhume-tuhume da kage-kage da batanci da karairayi marasa asasi da tushe.

Hujjar Masu Kage A Kan Shi'a Masu kage sun dogara da wasu tsirarun ruwayoyin da aka samo a gun 'yan shi'a ne wadanda ta yiwu wani ya iya fahimtar abin da ya yi kama da kagen da suke yi na cewa an jirkita Kur'ani mai girma, sai dai, manyan malaman shi'a da masu bincikensu, sun yi bayani kan wadannan ruwayoyi inda suka nuna cewa wadannan ruwayoyi sun zo cikin babi ne na nawadir, wanda irin wadannan hadisan ba a iya dogaro da su, don kuwa mafi yawansu ruwayoyi ne wadanda daidaikun mutane suka ruwaito (wanda ake kira aahaad) ko kuma ka samu ba su da cikakken sanadi, mursalai ne, wadanda ba a iya dogaro da su a irin wadannan al'amura muhimmai.
A takaice lallai manya manyan masanan shi'a sun karfafa kan rashin canza Kur'ani madaukaki kuma sun kawo kwararan dalilai wadanda suke nuna cewa Kur'ani mai girma ba jirkitacce ba ne. Wato babu wani kari ko ragi a cikinsa, kuma mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) sun yi imani cewa Kur'anin da Allah ya saukar wa Manzo (S.A.W) shi ne dai wannan Kur'anin da aka sani, wanda kuma musulmai suke amfani da shi a tsakaninsu, a kowane zamani, shi ne kuma dai wannan Kur'anin da ake buga shi a kasashen musulmi daban-daban, a Masar ko Suriya ko Lebanon ko kuma Iraki ko Saudiyya ko Iran, ba tare da an samu wani bambaci tsakanin wadannan Kur'anan ba, domin kuwa Allah madaukaki ya riga ya kare shi. Da kuwa za a ce an ga wani kari ko ragi cikin wani daga cikinsu, to da musulmai sun sani, kuma da sun guje shi, kana sashensu ya hana sashe amfani da shi. Ga abin da Allah Madaukaki Yake cewa dangane da kare Kur'ani: ""Hakika Mu muka saukar da Kur'ani kuma Mu masu kariya ne gareshi". Hijr: 9.

Littattafan Hadisai Gun Shi'a Shi'a Imamiyya ba su yi imani da samuwar wani littafi na ruwaya wanda babu kuskure a cikinsa ba, kuma wannan littafin nasu ne ko na waninsu. Saboda haka littafi matukar ba Kur'ani ba ne, ba sa ganinsa ma'asumin littafin da babu kuskure a cikinsa, domin kuwa dukkanninsu ba su wuce a yi bincike a cikinsu game da sanadinsu ko mataninsu ba domin tsage da fayyace ingantattun ruwayoyi da wadanda ba ingantattu ba. Sabanin abin da Malaman Ahlus Sunna suka yi imani da shi kan cewa dukkan ruwayoyin da suka zo a cikin littafin Bukhari da Muslim ingantattu ne, don haka ne ma suka sanya musu sunan sahihaini, wato ingantattu biyu.
Idan dai har ya inganta mutum ya hukunta cewa 'yan Shi'a sun yi imani da jirkita Kur'ani ba don komai ba sai kawai domin wasu tsirarun ruwayoyi da aka samu a cikin littafansu, wadanda ta yiwu wani ya fahimci irin abin da aka jingina musu cikin zalunci da kage inda aka ce wai sun yi imani da jirkicewar Kur'ani. Ahlussunna ba su da tacewa game da kagen da suke yi kan Shi'a game da al'amarin jirkicewar Kur'ani mai girma domin abin da ya zo a littattafansu ya wuce wanda suka samu yawa a cikin littattafan Shi'a na daga raunanan ruwayoyi. Kuma muna iya komawa ga misalai kamar haka:

Jirkicewar Kur'ani A Littattafan AhlusSunna Ya zo cikin littafm Sahih Bukhari juzu'i na 2 babin Aswak, daga Ibnu Abbas cewa ya ce: Ukkaza da Majna da Zul Majar sun kasance kasuwanni a zamanin jahiliyya, yayin da musulunci ya zo sai suka dakatar da saye da sayarwa, sai Allah Madaukaki ya saukar da cewa: "Laisa alaikum junahun fi mawasimil Haj" Ma'ana: "Babu laifi a kanku cikin lokutan Hajji", Sai aya ta sauko tana cewa za su iya yin kasuwanci a lokacin Hajji, alhali kuwa babu irin wannan aya mai lafazi kamar haka a Kur'ani, duk da kuwa cewa kasuwanci ya halatta da wasu ayoyin da suka tabbata a Kur'ani.
Kuma ya zo a cikin littafin Muwatta na Imam Malik juzu'i na biyu a kitabul Hudud cikin wani dogon hadisi cewa yayin da Halifa Umar bin Khattab ya taho daga Mina, har zuwa inda Halifa Umar yake cewa: Ahir dinku daga halaka kan barin ayar rajamu (jefe mazinata), kada wani ya ce mu ba mu ga wani zance a littafin Allah (kan jefe mazinata ba) to hakika Manzo (S.A.W) ya jefe mazinata kana mu ma mun jefe su, na rantse da wanda raina ke hannunsa, da ba don kada mutane su ce Umar ya kara wani abu cikin littafm Allah ba, to da na rubuta ta: (wato ayar da ta sauko kan batun jifa) "Ash sheikhu wash sheikhatu far jumuhuma albattata" ma'ana' "Tsoho da tsohuwa (da suka yi zina) to ku jefe su ba makawa" sai Umar bin Khaddabi ya kara da cewa: Lallai mun karanta wannan ayar.

To wannan ruwayar da aka ruwaito daga Umar bin Khaddabi dangane da jefe mazinata wanda ya nuna sun karanta ta, amma yanzu babu ita, ta zo cikin littafai da yawan gaske, wanda daga cikinsu akwai:
1. Sahih Muslim juzu'i na 3 babin hudud.
2. Sahih Bukhari juzu'i na 4 shafi na 179.
3. Tafsirin Tabari juzu'i na 1 shafi na 361 a bugun Bulak. Kamar yanda Bukhari ya ruwaito a cikin tarihinsa daga Huzaifa yana cewa: "Na karanta wa Manzo (S.A.W) suratul Ahzab sai na manta aya saba'in (70) daga cikinta, kuma ban same su ba (wato sun bace)." Kamar kuma yanda Abu Ubaida ya fitar a cikin Gana'im haka nan Ibnul Anbari da Ibnu Murdawaihi daga Ummul Muminin A'isha tana cewa: "Suratul Ahzab ta kasance a zamanin Manzo ana karanta ta aya dari biyu (200) ne, to yayin da Usman (R.A.) ya rubuta mus'hafi bai sami sauran ayoyin ba sai abin da yake nan a yanzu (wato aya 73)."
Wannan ruwayar ta zo a cikin Durrul Mansur juzu'i na 5 shafi na 180, kamar yanda ta zo a cikin Itkan fi ulumil Kur'an juzu'i na 2 shafi na 25. Wanda duk yake neman karin bayani dangane da irin wadannan ruwayoyin sai ya duba wadannan littattafai da zamu ambata:
Sahihul Bukhari juzu'i na 3 shafi na 305 Al Itkan juzu'i na 1 shafi na 66
Tafsirin Ruhul Ma'ani juzu'i na 1 shafi na 20 da kuma na 25, bugun Munira a Masar.
Durrul Mansur juzu'i na 1 shafi na 105.
Amma duk da samuwar irin wadannan ruwayoyi wadanda suke bayani karara game da jirkita Kur'ani da tawayarsa wadanda aka samu a littattafan malaman AhlusSunna, sai mu samu cewa AhlusSunna ba su yi imani da cewa Kur'ani yana da tawaya ko an jirkita shi ba, abin da dai suke yi shi ne suna tawilin wadannan ruwayoyin ne ta yanda zasu kare darajar Kur'ani da nesanta shi daga tawaya ko jirkita.
A daya bangaren kuma za mu samu cewa mabiya mazhabar Ahlul Baiti ba su tuhumar 'yan uwansu musulmi Ahlus Sunna da cewa sun yi imani da tawayar Kur'ani, a dalilin wadannan ruwayoyin da aka ruwaito cikin littattafansu, duk da cewa suna iya riko da irin wadannan dalilan masu karfi wadanda suke cike makil a manya manyan littattafan Ahlus Sunna wadanda su malaman suka yarda da su, domin tuhumarsu kan imani da tawayar Kur'ani, sai dai saboda (Su mabiya mazhabar Ahlul Baiti sun) kyautata zato ga 'yan uwansu AhlusSunna, tare da kwadayin hadin kan musulmi wanda shi ne sirrin karfinsu gurin fuskantar makiyan musulunci masu neman ruguza shi, wannan shi ne ya sa suke kau da kai don karfafa dankon zumunci da 'yan'uwantaka na musulmi.
Amma abin takaici shi ne yadda makiya son hadin kan musulmi daga cikin masu da'awar cewa su ma Ahlus Sunna ne, ba su iya aikata kwatankwacin abin da mabiya mazhabar Ahlul Baiti suka yi, gurin yi musu kyakkyawan zato dangane da hukuncin wadannan ruwayoyin kamar yanda su (mabiya ahlul Baiti A.S.) suka kyautata musu zato ba!
Irin wannan hukunci mai fuska biyu yana haifar da wasu tambayoyi masu rikitarwa idan mutum ya yi la'akari da su, irin tambayar da ta yi kama da cewa: Shin irin wadannan makiya hadin kan musulmi sun jahilci tarin wadannan ruwayoyin ne masu bayani a fili karara kan jingina jirkita da tawaya ga Kur'ani a littafan Ahlus Sunna a zahirinsu? Ko kuwa suna da wata manufa ne? ko akwai wani hannu ne a boye wanda yake ingiza gafalallu da hadafin tayar da fitina ta hanyar bijiro da tuhumomi da kage-kage don kekketa al'ummar musulmi, domin amfanin makiyan musuluci da musulmi, domin su zama cikin kwanciyar hankali daga hatsarin da ka iya rusa su matsawar kan musulmi a hade yake?

Ra'ayoyim Malaman Shi'a Manyan malaman Shi'a sun dage kuma sun yi tsayin daka domin kwaranye shamakin da ya lullube wannan mummunan makirci ta hanyar kore samuwar kowane nau'i na tawaya ko jirkita ko kari a cikin littafin Allah Mai girma, kamar haka:

1- Abu Ja'afar As-Saduk Muhammad bin Ali bin Husain bin Babawaihi Al-Kummi wanda ya yi wafati a shekara ta 381 bayan hijira, yana cewa: "Akidarmu dangane da Kur'ani mai girma wanda Allah ya saukar, wa manzonsa (S.A.W) shi ne wannan Kur'ani da ke tsakanin bango biyu. Wato; daga Fatiha zuwa Nasi, babu kari babu ragi, kuma duk wanda ya jingina mana cewa mun ce Kur'ani ya fi wanda ke hannun mutane yawa, to shi makaryaci ne. Littafin Al'I'itikadat.

2-Imam Khumaini (Allah ya ji kansa) yana cewa lallai mu muna hana samuwar tawaya ko jirkita cikin Kur'ani hani mai tsanani kamar yanda wannan shi ne mazhabar masana daga malaman sunna da shi'a kamar yanda wannan shi ne abin da dukkan bangarori biyu na musulmai suka yarda da shi. A wani wajen kuma a halin yana yin raddi ga wanda ya raya cewa akwai jirkita cikin Kur'ani, sai ya kara da cewa: To muna ce masa: Lallai bacin wannan mummunar magana, kana bacin irin wannan yasasshen ra'ayi ya fi karfin ya buya ga duk wani mai hankali.
Littafin Anwarul Hidaya fit ta'alikat alal kifaya shaft na 243.

3-Sheikh Tusi babban malami masanin fikihu a mazhabar Jaafariyya wanda aka fi sani da sheihut ta'ifa wanda ya yi zamani tun shekaru dubu da suka gabata yana fadi a Mukaddimar Tafsirinsa; Tibyan cewa: Kari ko ragi sam bai dace da martaba da matsayin Kur'ani ba.
Mukaddimar Tafsirin Ala'ur Rahman shafi na 25.
 

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)