Muassasar alhasanain (a.s)

Hakkin Kafa

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

MARUBUCI: Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com
Hakkin Kafa
Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Amma kuma hakkin kafafuwanka, shi ne kada ka yi tafiya da su inda ba ya halatta gareka, a kansu ne zaka tsaya kan siradi, ka duba domin kada su zamar da kai sai ka halaka cikin wuta".
Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Duk wanda ya yi tafiya domin biyan bukatar dan'uwansa, Allah zai rubuta masa lada saba'in da kowane taku ya yi, ya shafe masa zunubi saba'in har sai ya koma inda ya rabu da shi, idan kuwa bukatarsa ta biya a wurinsa, to zai fita daga zunubansa kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi, idan kuwa ya mutum a tsakanin hakan, to zai shiga aljanna babu wani hisabi". (Sharhin Sakon Hakkoki: 212)
Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Da mutum ya yi I'itikafi na wata biyu a masallacina, gwara ya yi tafiya da dan'uwansa mumini domin biyan wata bukata". (Sharhin Sakon Hakkoki: 212)
Kafa tana da matukar muhimmanci a cikin gabobin jikin mutum, don haka yana da kyau mu kiyaye hakkinta, kamar yadda zamu iya ganin cewa Kur'ani mai daraja ya yabi kafafun gaskiya na wadanda suka yi imani.
Sannan an yi nuni da wani abu mai muhimmanci kuma mai ban tsoro na cewar wadannan kafafu zasu kasance sheda a kan mutane ranar kiyama, don haka yana da kyau mu kiyaye inda zamu tafi. Mu yi kawukanmu hisabin ina ne zamu tafi duk sa'adda muka tashi zuwa wani wuri, idan ya kasance akwai alheri a cikin sai mu gabatar da shi, idan kuwa babu alheri sai mu dakatar.
Mu tuna da cewa wannan kafa ni'imace da Allah ya yi mana, don haka ba zamu saba masa da ita ba, kamar yadda ba zamu take hakkin wasu da ita ba, kamar dukansu da kafa, ko tafiya domin shiga inda ba su amince mana ba, ko kuma sanya takalmansu da wandunansu, da zannuwansu da sauransu.
Imam Ali Sajjad (a.s) muna ganin yadda ya yi mana nuni da cewa, saba wa Allah ta hanyar zuwa wuraren da aka haramta, kamar zuwa gidan giya, ko gidan matan banza, ko sinimar da ake nuna batsa, ko tafiya domin sabo kamar yanke zumunci, sa saura ire-irensu, su ne ummul haba'isin zamewar kafafu daga kan siradi a ranar gobe kiyama.
Sannan kamar yadda yake wajibi ne a kanmu mu kare kafafunmu haka nan wajibi ne mu kiyaye lafiyarsu da lafiyar kafafun wasu, don haka masu hayar babura kamar acaba, da makamantansu, yana da muhimmanci matuka su yi tafiya kan titina da taka tsantsan, domin kare lafiyar kafafu da hannaye da ma rayukan mutane.
Hannaye da kafafu suna alamta mutum ne, don haka ne suke zama ma'aunin gane aikin mutum da matsayinsa gurin wasu mutane. Sau da yawa wasu sukan fara duba hannun mutum domin su san me yake yi, ko wane aiki ne yake yi, idan sun ga hannunsa ya yi alama da na makeri ko mahauci, ko manomi, ko mai faskare, ko marubuci sai su yi hasashen aikinsa da wannan. Haka nan sukan duba takalmin kafarsa domin sanin matsayinsa, kuma sau da yawa sukan auna shi da takalmin fiye da yadda suke auna shi da wandonsa, ko ma rigarsa, kai suna iya auna hankalinsa da takalminsa.
Kur'ani mai daraja yana jingina barna ga hannayen mutane yana nuni da lalacewar al'ummu da bayyanar fasadi mai yawa a duniya sakamakon abin da hannayen mutane suke yi na barna, ko da yake hannaye a nan suna nuna samuwar mutane ne gaba daya. Ga wadannan hannayen da kafafun ne ake jingina dukkan wata barna da lalaci, wannan lamarin kuwa domin yawancin ayyuka su ne suke yin sa.
Nijeriya kasa ce mai al'ummu daban-daban, kuma wadannan al'ummun suna da nau'o'in al'adu da wayewa, da addinai, da garuruwa, da yanayi, da shiga, da abinci, da yare, iri-iri, mafi girman yarurrukan wadannan al'ummu sun hada da Hausa, da Yoruba, da Igbo, da sauran kabilu. Idan da za a amfana daga wadannan al'ummun yadda ya kamata da an samu ci gaba maras misali, sai dai kaico! Sau da yawa an yi amafni da damar da aka samu ta bambace-bambance wurin rikita al'umma.
Babbar matsalar da take ci wa wannan al'umma tuwo a kwarya ita ce; samun wanda zai kama hannunta zuwa ga tudun mun tsira a tattalin arziki, da tsaro, da wayewa, da ilmantarwa, da lafiya, da rayuwar zaman tare, da walwalar jama'a, da gyaran tituna, da hanyoyi, da magudanan ruwa, da samar da ruwa, da wutar lantarki, da kayan masrufi, da farashin kasuwa mai dacewa, da makamantansu.
Wani babban abin takaici a yau an mayar da al'umma musamman yaransu cikin mafi munin kauyanci da gidajenci, idan aka kawo wuta sai ka ji yara sun dauka gaba daya da ihu Nepa! Nepa! Kai ka ce lantarki wani abu ne wanda ba a taba jinsa ba! Hasali ma abin kunyar da ake zuba mana a wannan kasa hatta da mai kamfen din zama shugaba har yau yana kamfen da ruwan sha da lantarki ne! Muna kira ga gwamnatocin da suke jagorancin wannan al'umma da su yi kokarin ganin sun fitar da ita daga kangi iri-iri da take ciki, wadannan kangogin suna bukatar aiki mai wahala domin ganin an shawo kansu, sai dai gwamnati ba zata iya yinsu ita kadai ba, amma mafi girma yana hawa kanta ne, domin matukar ba ta sanya hannu a komai ba, to ba inda za shi. Muna iya daukar misalin tsaftar gari; Idan muka ce: Gwamnatocin Nigeria ne suke da hakkin daukar nauyin tsaftace gari da su da al'ummarsu, zamu ga nauyin da ya hau kan gwamnati ya fi yawa:
Uwa-uban tafiyar tsafta shi ne samar da ruwa isasshe wanda zai wadatar domin kawar da dukkan wani datti, da dauda, da najasa. Idan mun duba abin takaici da yake kasashenmu muna iya ganin a misalin birananmu akwai yankunan da sama da shekaru ishirin zuwa sama har yau ba su san wani ruwa na famfo ba, mutum ba zai iya buda famfu a bandakinsa, ko tsakar gidansa, ko kofar gidansa ba, kai hatta ma a layin da yake babu famfo, hasali ma sai dai ya sayi ruwan da zai yi wadannan tsaftace-tsaftace da ya hada da; wanke kayansa, da yin wanka, da wanke gidansa, d.s.s.
Idan ya ci sa'a yana da rijiya to ya samu sauki, amma idan ta kafe kuwa sai halin kakanikayi da ni- 'yasu, sai ya fada cikin halin damuwa matuka, sai wannan rashin ruwan ya haifar da matsalolin da ba sa kirguwa, matsalolin rashin lafiya, rashin tsafta, rashin kwanciyar hankali, rashin ilimi, rashin tattalin arziki mai kyau, rashin tsaro, lalacewar tarbiyya, wannna kadan ke nan daga cikin matsalolin. Mafi muni shi ne rashin isar ruwan da za a yi tsarkin ibada, ga kuma yaduwar fasikanci; sau da yawa 'yan mata suka lalace garin neman ruwan sha ko na wanka a wasu gidaje ko wurare, ko kuma zuwa rafi yin wanka da wanki da wanke-wanke.
Idan muka waiwayi matsalar karancin wayewa da ilimi, sai mu ga ta kawo mana halaye munana masu ban takaici. Ba na mantawa a shekarar 2004, na taso daga B.U.K zuwa Kabuga da ke Kano, akwai wata Jar mota a gabanmu kiran Marcedes, direbanta yana shan rake, sai ya zama duk raken da ya shanye to bawon zai wurga shi kan titi ne, abin da na lura da shi yana nuna cewa babu mai ganin wannan matsala ce a cikin wadanda muke tare a motar daya! A daidai lokacin da nake yawo da ledan pure water a hannuna domin na rasa kwandon sharar da zan wurga ta, sai ga wani yana ganin zubar a bawon rake a tsakiyar titi haka kawai, a matsayin wani abu da ba matsala ba, wai ni da nake ganin hakan matsala ashe wai ni ke da matsala. A wannan lokacin ne wani tunani da ya sanya ni bakin ciki ya zo mini, sai na fara tunanin cewa; ashe ke nan domin in zama cikakken banajeriye dole ne in siffantu da irin wadannan siffofin ko kuwa?!
Irin wannan kidahumanci ya janyo mana samun yin Tsuguno a bakin titina, da bola, da rariyoyin ruwa, da magudanan ruwa, da bayan gidajen mutane, da gefen kwatami, da kofar gida hatta ga manya a wani zubin, da daudar jiki, da wari, d.s.s. Tayiwu irin wannan mummunar dabi'ar ta samo asali daga zamanin da babu ci gaba da wayewa ne, ko kuma abin da yake faruwa a yanzu a kauyuka na cewa; bayan gida dazuzzuka ne, don haka mutum yana iya fita ya gewaya domin yin tsuguno, wala'alla ma daga nan aka samu wannan kalma ta "Bayan gida" ko "Bayan gari". To amma wannan al'ada yanzu a cikin gari ake yin ta ba a "Bayan gari ba". Shin wannan lamarin waye zai gyara shi? Ashe ke nan wata mata da take yi mana gorin cewa; ba ta taba ganin wani yana bayan gida ko fitsari ba a rayuwarta duk da kuwa ta kusa shekaru arba'in a duniya sai da ta kawo mana ziyara kasarmu a garin Kano, bai kamata ba in ji haushin wannan gorin da take yi mana.
Sai dai kada mu manta cewa; gwamnatoci ba su himmantu da yin gidajen wanka da ba haya ba; Ya kamata ne a ce a duk tafiyar kilo mita daya ko kasa da hakan akwai gidajen wanka da ba-haya a kwanar kusurwowi hudu na wannan nisan domin su taimaka wurin tsafta. Idan ma bai kasance a kyauta ba, sai a sanya kudi kadan, ke nan a lokaci guda kuma zasu samar da kudin shiga ga gwamnatin kanta, sannan kuma zasu iya samar da aiki ga wasu mutanen! Sannan sai a sanya dokar duk wanda aka kama ya yi a gefen kwata ko titi za a kama shi a ci shi tara.
Abin takaici ba wa tsarin birane hakkinsa ba a san da shi ba a kasashenmu, kana iya ganin yanki mai girma babu wuraren shakatawa, babu su balle a samu gidajen gewayawa a cikinsu, babu wuraren wasanni! Babu ma asibitoci, da kasuwannci, da makarantu tsararru daidai yawa da bukatun al'umma. Idan kuwa kana maganar kwatami da magudanar ruwa, kusan duk wurin shakatarwar mutane da wuraren hirarrakinsu suna gefen kwatami da ruwan rariya mai wari da doyi ne, wannan kuwa a sakamakon rashin samar musu da wuraren shakatawa da hutawa a cikin unguwanni. Ga kududdufai gidajen sauraye, kuma matattarar bayan gida da ba-haya a cikin inda al'umma suke rayuwa, ba tare da an kawar da ruwansu an cike su ba. A yanzu yaushe ne muke tunanin lokacin da zamu fara tunanin mu ma mutane ne a duniya? yaushe ne zamu fara tunanin cin moriyar ni'imar da Allah ya yi mana? yaushe ne zamu fita da kangin bauta mu kasance 'ya'ya 'yantattu? yaushe ne zamu ji dadin wannan duniyar da aka yi ta kuma aka hore mana duk abin da yake cikinta domin mu more su, mu bauta wa Allah cikin ni'ima? yaushe ne wannan duniyar da aka yi ta domin mu yalwata zata canja daga kasancewarta gidan kunci ga al'ummarmu? Wai yaushe ne! yaushe ne!
Muna iya gani a fili cewa; Titunanmu cike suke da kwari da rami, kuma a cike da ledodi da kazanta, gefen rafuka da tituna hatta da gefen masallaci cike yake da wurin kazanta da warin fitsarin mutane ba fa na dabbobi ba! A farkon da na je hutu a farkon 2004 "March", na raka abokina asibitin cikin birnin Kano na Murtala, ga shi ban dade da dawo gida ba, har na manta da inji warin fisarin mutum, a inda na zauna sai wani zarnin fitsari ya rika bugowa, na kalli mutanen da suke kusa na ga ba su damu ba, ina zaune wani ya sake kewayawa ya yi fitsari, ban yi kwata a wurin ba sai juwa (hajijiya) ta fara daukata, a kan wannan warin da ya buge ni sai da yi rashin lafiya!. Irin wannan warin hatta da inda ake yin salloli akwai shi; wani babban abin takaici sai ka ga wani ya gina masallaci amma ba ya ma tunanin yin magewayi koda kuwa na fitsari ne, wai shi ya dauka ya isa mutane su gewaya jikin bango da garun mutane su rika yin fitsari. Wato an kai ga lalacewar tarbiyya da al'adun da hatta masallaci ba a yi masa magewayi.
Koda yake kada mu manta masu mulki su ma sun taso daga cikin al'ummar ne, don haka ne ma ba mu ga suna sanya dokar rashin yarda da yin masallaci sai da yi masa wurin kama ruwa ba! Kuma ba mamaki ka samu gwamna guda shi bai ma dauka wannan matsala ba ce balle ya gyara, ba na mantawa a 2008 a unguwar Kurna Tudun Bojuwa ta Kano na je wani gida sai na ga yara sun yi kashi a kofar gida, ga kudaje ta ko'ina suna mamaye mu, ga kwatamin kofar gidan yana wari, ga yaran da suka yi kashi sun zauna suna wasa kusa da kashin da kwatamin. Sai na ce a raina: "A yanzu da daya daga wadannan yaran zai zama kansila, ko ciyaman, ko gwamna, an ya zai ga wannan lamarin a matsayin matsalar da ya kamata a magance?! Wai shin zai ma ga wannan wani abu ne da ya kamata a lura da shi domin a magance shi?! Duba kowane lungu ka gani yaushe ne ka ga kwandunan tara shara, yaushe ne mutocin kwasar shara suke bin lunguna domin su kawar da ita a kowace rana? Yaushe ne wata gwamnati ko wani hamshakin mai kudi yake tunanin yin Kampanin ledodi da za a rika sanya su cikin bokitai domin idan shara ta taru sai a daure a kawo babban kwangirin tara shara na layi, hasali ma ina kwangirin ko motar da zata juye abin da yake cikinsa kowace rana? Sannan kuma idan an yi Kampanin wadannan ledodin shin gwamnati ta tanadi doka, ko hanyar wayar da kan mutane domin su saya su kiyaye tsaftar lungunansu, da gidajensu.
Idan ka duba titunanmu zaka ga babu masu kula da shara ko motocin da suke wanke tituna cikin gari da lungunanmu, hasali ma ba a yi titunan ba a cikin lungunan biranen, domin hatta da manyan titunan da ake da su sun farfashe balle a ce an samu motocin da zasu rika wanke su! Sai ya kasance babu wani mai wayar da kai kan hakan, kuma babu wani mai yin hakan, babu wani lungu da yake da abin tara shara da mota zata zo ta dauka, babu motar ma, kai lungunan ma an yi su tsukuku ta yadda wasu lungunan ma motocin ba zasu shiga ba, amma duk da hakan don me ba a yi ba a manyan titunan da gefen lungunan?!. Wa ye ke da alhakin ganin Ledar zuba shara ta yawaita? Wa ye yake da alhalkin gyara tituna da lunguna da yi musu kwalta da wanke su da share su?! Wa ye zai wayar da kan mutane su rika sayan ledar suna kula da lafiyarsu?! Mu sani mutane sun fi kula da cikinsu da abin da zasu ci kawai, kana iya ganin mutum ya sayi abincin Naira 300, amma ba zai ware wa tsaftar gidansa, ko layinsa, Naira 20 ba!. Wa ye yake da alhakin yin Pampers da arha saboda amfani da shi domin tsaftace kashin yara kanana 'yan kasa da shekaru uku?! Wadannan misalai ne a bangare daya kawai na yin tsafta, haka nan duk wani bangare yake tattare da irin wadannan abubuwan takaici!
Cibiyar Al'adun Musulunci
www.hikima.org
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
Saturday, June 19, 2010
 

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)