Muassasar alhasanain (a.s)

Hakkin Mai Bawa

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5


Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Amma hakkin mai mulki da kai yana kama da mai mulki a kai a jagoranci, sai dai wannan -jagora- ba ya mallakar abin da wancan -mai bawa- yake mallaka. Don haka haka biyayyarsa ta zama wajibi a kanka a cikin komai karami da babba, sai dai idan wani abu ne da zai fitar da kai daga biyayyar hakkin Allah, wanda zai hana ka biyan hakkinsa (ubangiji), da hakkokin sauran halittu, idan ka gama da hakkinsa (ubangiji) sannan sai ka shagaltu da hakkinsa (ubangida). Kuma babu karfi sai da Allah".
Mulkin mai bawa a kan bawa, ya fi na mai mulki a kan bawa, saboda yana da wasu hakkoki a kan bawa da shi mai mulki ba shi da su, sai dai kuma idan mai bawa ya yi wa bawa mugunta kamar lahanta shi ko nakasa shi, to hakki ne a kan mai mulki ya dauki mataki mai tsanani kansa, ta yadda a wasu matakan yana iya kaiwa ga 'yanta shi wannan bawan.
Musulunci bai son bautar da mutum, amma idan ya tarar da mutane bayi a hannun wasu, to ba ya kwace wa mutane dukiyoyinsu, sai dai yana sanya wasu sharudda da dokoki wadanda zasu kare mutunci da 'yancin shi wanda ake mallaka, sannan ya shimfida wasu dokokin da zasu samar wa wanda ake mulka 'yanci.
Ya shimfida dokokin kyautata wa bayi da 'yanta su da kwadaitar da hakan. Ya karfafai ba su damar fansar kawukansu ta hanyar fansar kansu da kudi, ko kuma su yi wani aiki kamar yadda manzon rahama ya sanya fansar wadanda suka iya koyarwa su koyar da yara goma rubutu da karatu, sai a sake su.
Daga cikin wasiyyar imam Ali (a.s) ga dansa Hasan (a.s) yana cewa da shi: Kada ka mayar da kanka bawan wani, alhalin Allah (s.w.t) ya halicce ka mai 'yanci .
Musulunci ya hana bautar da mutane in banda ribatattun yaki, ya sanya bautar da mutane daga cikin manyan laifuffuka, su kuwa bayin bautar da su ni'ima ce garesu, domin wanda ya zo kashe musulmi hukuncinsa shi ne a kashe shi, sai musulunci ya yi musu ni'ima da a bautar da su, su samu rayuwa, domin su ga adalcin musulmi da musulunci idan suka rayu a cikin su, sai su musulunta.
Don haka ne zamu ga musulunci bai taba yarda da wulakatan bawa ba, balle kuma a nakasa shi da sauran abin takaici da ya zo a tarihin musulmi wanda aka samu wasu kurakurai a kasashenmu game da irin wadannan lamurran.
Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: Mutum uku ni ne abokin gabarsu ranar lahira, kuma duk wanda nake abokin gabarsa to zan yi galaba kansa: Da mutumin da aka yi amana da shi, sai ya yi yaudara, da mutumin da ya sayar da 'yantaccen mutum sai ya cinye kudin, da mutumin da ya dauki mai aiki, sai da ya gama aikin amma sai ya hana shi kudinsa .
Sannan a fili yake cewa; bayar da dama ga bawa ya 'yanta kansa da abin da aka fi sani da "mukataba" ya kore tunanin da wasu suke yi na cewa bawa ba ya iya mallakar dukiyarsa.
Musulunci bai tsaya nan ba sai da ya sanya wasu dokoki masu muhimmanci kamar sanya dukiyar zakka domin 'yantar da bayi, sannan ya sanya cewar duk wanda ya gudo daga daular kafirci ya shiga daular musulunci to ya zama 'yantacce.
Abin mamaki sai ga shi a yau saboda musulmi sun bar koyarwar musulunci sai ya ga shi wanda ba shi da 'yanci sakamakon zalunci da danniya ga hakkokin dan Adam da suka yi katutu a kasashe marasa ci gaba da suka hada da kasashen musulmi, sai ga shi idan wani daga 'yan wadannan kasashe ya gudu ya shiga kasashen yammacin duniya da ba su da wata alaka da musulunci, to a can ne yake samun 'yancin da ya rasa, wani lokaci har da na yin addininsa yadda ya so.
Haka nan duk wanda ya azabtar da bawansa azaba mai tsanani to bawan ya 'yantu, kamar wanda ya yanke wata gaba ta bawansa; wani mutum ya taba zuwa wurin manzon rahama (s.a.w) yana ihu, sai ya tambaye shi me ya same ka? Sai ya ce: Ubangijinsa ne ya yanke masa azzakari saboda na sumbanci wata baiwarsa. Sai manzon Allah (s.a.w) ya ce a kamo masa mutumin, sai aka neme shi aka rasa. Sai manzon Allah (s.a.w) ya ce: Tafi kai 'yantacce ne.
Irin wadannan halayen na mafificin halitta ne 'yan mishan suka ara a tarihin zuwansu kasashen Afrika da Latin Amrika, har ya kai ga karbar addininsu a wadannan nahiyoyi. Da musulmi sun yi aiki da rabin abin da manzon rahama (s.a.w) ya koya musu da duk duniya ta zama musulma!.
Sannan ya sake sanya wasu dokokin 'yanta bayi, kamar cewa; idan ubangida ya ce da bawansa kai bawa ne zuwa bayan mutuwata, to da ya mutu bawansa ya zama da, ko kuma mutum ya mallaki daya daga jininsa kamar iyaye, to kai tsaye sun zama 'yantattu, ko kuma baiwa ta haifi da na cikin ubangijinta, to da ya mutu ta zama 'yantacciya, don haka ba a sanya ta cikin gado, ko kuma 'yatar da bayi ta hanyar kaffara, kamar kaffarar shan azumi, ko ta yin zihari, ko ta kisan kuskure, da makamantansu.
Bawa wani mutum ne da aka yi wasiyya da kyautata masa matukar gaske, har ya zo a cikin ruwaya manzon rahama (s.a.w) yana cewa: Masoyina Jibril ya yi mini wasiyya da kyautata wa bayi, har sai da na yi tsammanin cewa; ba a bautar da mutane, kuma ba a sanya su aikin hidima!. Don haka ne zamu ga imam Ridha (a.s) yana cin abinci tare da bayinsa. Musulunci ya yi umarnin ciyar da bayi da tufatar da su, da irin abincin da uwayen gijinsu suke ci, da kuma irin tufafin da suke sanyawa, kuma ya hana sanya su aikin da yake da wahala garesu, idan kuwa aka ba su shi, to sai ya ce a taimaka musu wurin aiwatar da su. Musulunci ya kara da cewa; Idan bayi sun yi laifi sai a yafe musu, kuma kada a sake a azabtar da su.
Tirkashi! Yaushe ne aka samu wani ubangidan yana ba wa bawansa abin da yake ci, ko ya sanya masa irin tufafinsa, balle kuma maganar ya taya shi aikin da ya sanya shi idan ba zai iya ba. Lallai musulunci yana wata duniyar, musulmi suna wata duniyar daban ne!, ba ma bayi ba, hatta da yaran da muke sanya su yi mana aiki a gida da shguna ba mu ga ana yi musu mu'amala ta kirki ba.
Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: Ni bawa ne kawai, ina ci kamar yadda bawa yake ci, ina zama kamar yadda bawa yake zama. Wannan yana daga cikin kaskan da kan manzon rahama (s.a.w).
Daulolin da suka gabaci musulunci, da addinai sun gurbata da wariya da kabilanci, wasun su ma har da wariyar launin fata, da ta yare, don haka ne musulunci ya zo da rahama, da daga taken daidaito tsakanin 'yan adam, ya sanya bambanci tsakaninsu yana kasancewa ne da takawa, shi ma wannan fifikon ba a dokoki ake aiwatar da shi ba, wani abu ne da yake wurin Allah wanda shi ya bar wa kansa sani.
Don haka ne ma ya ce: Mafi girmanku a wurin Allah, shi ne wanda ya fi jin tsoronsa.
Sau da yawa manzon rahama (s.a.w) ya yi umarni da a goya bawa a bayan dabba, ko kuma a ciyar da shi abincin da ya kawo wa uban gidansa, domin shi ne ya sha wahalar dafawa. Addinai masu yawa sun zo da nuna fifikon su a kan sauran al'ummu, misalin yahudawa, da fararen indiyawa a cikin ganin fifikon su kan sauran al'umma a fili yake. Sai dai musulunci ya zo da taken cewa babu wani bambanci tsakanin bawa da mai 'yanci sai da tsoron Allah madaukaki. Haka nan ya rushe nuna bambanci tsakanin baki da fari, wannan kuwa lamari ne da har yanzu duniya take fama da shi.
Musulunci bai hana bawa auren 'ya ba, kamar yadda ba a hana mace 'ya auren bawa ba, ya dauke shi mutum cikakke kamar sauran mutane, ya nuna fifiko yana iya kasancewa da imani ne kawai. Bawa ne yake da hakkin ya auri matarsa, ya sake ta, ya yi kasuwanci, ya yi sheda a kotu, ya yi riko da mukami, ya zauna da sauran 'ya'ya, yana da hakki kamar sauran mutane. Amma idan da zamu bincika tarihin bayi a cikin al'ummu da mun ga abubuwan ban tausayi marasa iyaka. Ana yi musu mu'amala kamar ta lodin itace da aka kwaso a bayan babbar mota, bincika ka ga tarihin sayar da bayi a Afrika da latin Amurka da sauransu.
Amma sai ga shi musulunci ya hana bautar da dan Adam, sai dai wasu zasu iya cewa ai an bautar da mutane a lokcin kafuwar musulunci! Sai mu ce: haka ne, amma irin wannan bautarwar rahama ce ga su bayin, domin su mutane ne da suka zo domin su kace musulmi sai aka kama su, don haka maimakon a kasha su, sai a yi musu ludufi da bautarwa ko tayiwu su ga adalcin musulunci a cikin kasarsa kuma su san addini, su yi ilmi, idan suka ga hakan suka kuma musulunta, to a nan ne sai su sami 'yanci.
Don haka kama su da bautar da su, domin su samu shiriya ne, kuma ba a yi musu wata mu'amala mummuna da saba wa musulunci. Don haka ne duk wanda aka samu da irin wannan halaye na muzgunawa bawa, to sai jagoran musulmi ya 'yanta masa shi!. A bias hakika abin da aka gain wanda ya faru a tarihin musulunci gata ne ga bayin.
Sai abin ya yi kama da sauran abubuwan da suke faruwa wanda musulunci bai yarda da su ba, amma idan suka faru to yana da mataki mai kyau da yake dauka kansu. Kamar mutumin da ba ya son wani bako ya zo masa ne, amma idan ya zo masa to ya zama dole ya girmama shi.
Sannan babu dama musulunci ya 'yanta bayin da ya samu hannun mutane domin dukiyarsu ce, don haka ne ya kyale wannan hannun mutane, amma sai ya yi kokarin kwadaitar da 'yanta su. Bauta abu ne na tattalin arziki da musulunci ba zai iya zaluntar mutane da kwace musu bayinsu ba, sai dai ya taimaka domin 'yantar da mutane ta hanyoyi daban-daban kamar kaffara da suaransu. Sai dai yau duniya tana fuskantar wata bautar mai wuyar gaske, yadda ake cinikin yara da mata ana kai su wasu kasashe domin su kula da gonaki har rayuwarsu ta kare, wannan wani abu ne da duniya ta kasa shawo kansa har yanzu musamman a kasashenmu na Afrika.
Manzon Allah (s.a.w) rahama ne ga dukkan talikai da ya hada musulmi da kafiri, da bawa da da, da mai kudi da talaka, da mai mulki da wanda ake mulka, babu wani wanda ya fita daga wannan da'irar ta rahamar ubangiji madaukaki.
Haka nan musulunci ya dauki dan Adam da kima matuka ko da kuwa bai musulunta ba, sai dai duk wanda ya taba musulmi ya kashe su to shi kadai ne musulunci ya yarda musulmi su taba, don haka ne zamu ga a rayuwar Manzon Allah (s.a.w) bai taba kai hari kan mutanen da ba su suka fara kai masa hari ba. Kuma idan mutanen wani gari suka kai masa hari to bai taba yakar wasunsu na wani garin daban ba ko da kuwa addininsu daya ne, sai dai ya rama kan wadannan dai da suka kai masa hari kawai.
Duk da a rayuwar musulunci an samu yakoki masu yawa a Madina kuma dukkanninsu sun zama domin kare kai ne daga makiya mushrikai da yahudawa da kiristoci da suke kai hari kan musulmi, kuma Annabi a kowne lokaci yana zabar bangaren sulhu da zaman lafiya ne da rangwame. Don haka ne ma adadin wadanda ake kashe wa bangarorin biyu ba su da yawa a dukkan yakokinsa tamanin da wani abu. Wadanda aka kashe na musulmi da kafirai duka ba su kai sama da dubu daya da dari hudu ba. (Littafin Tafarkin Rabauta: Fasalin; Aiko Annabi Mai Daraja (s.a.w).
Musulunci bai taba yarda da zaluntar wani mutum ko wani mai rai ba, kai hatta da barnar abinci da lalata wuri da lalata kasa ya hana balle azabtar da dan Adam ko kashe shi, ya kuma sanya kalma mai dadi da zaka gaya wa dan'uwanka mutum ya yi farin ciki a matsayin sadaka. Don haka ne ya soki mai lalata kayan gona da dabbobi, ya kira shi mai yada fasadi da barna, balle kuma mai isar da cutarwa ga mutum. Saboda haka ne ma muka samu dukkan matsalolin da muke ciki a yau musamman a kasashenmu sun taso daga rashin fahimtar musulunci ne, sai dan Adam ya kasance ba shi da wata kima.
Musulunci ya sanya lamunin rayuwa ta hanyoyi masu yawan gaske, sai ya shimfida dokokin da zasu wadatar da dan Adam kamar zakka, humusi, sadaka, Baitul mali, kyauta, da ayyukan jin kai, sannan ya yi matukar gaba da jahilci da ba a taba samu ba a rayuwar dan Adam, sai ya tilasta neman Ilimi ko da kuwa a kasar Sin ne. Musulunci ya yi gaba da rashin ganin kimar dan Adam matuka, har ma ya 'yanta bawa saboda ubangidansa ya yanke masa al'aura. Kai hatta da iradar yara da 'yan mata yayin zabin wanda zasu aura ya ba ta kariya. Sannan a fili yake hatta da addini bai tilasta kowa riko da shi sai wanda ya ga dama.
Kulaini ya karbo daga Hasan ya ce: Yayin da Sayyidi Ali (a.s) ya rusa rundunar dalha da Zubair (r) sai mutanen suka gudu suna ababan rusawa, sai suka wuce wata mata a kan hanya ta firgita daga garesu ta yi bari saboda tsoro, kuma dan nata ya fito rayayye sannan sai ya mutu, sannan sai uwar ta mutu. Sai Imam Ali (a.s) da sahabbansa suka same ta an jefar da ita da danta a kan hanya, sai ya tambaye su me ya same ta?. Sai suka ce: Tana da ciki ne sai ta ji tsoro da ta ga yaki da rushewar mutane da gudunsu. Sai ya tambaya: Waye ya riga mutuwa a cikinsu?. Sai suka ce: danta ya riga ta mutuwa.
Sai ya kira mijinta baban yaro mamaci ya ba shi gadon sulusin diyyar dansa, sannan sai kuma ya gadar da uwar sulusi, sannan kuma sai ya gadar da mijin rabin diyyar matar wacce ta gada daga dansa sannan sai ya ba wa makusantan matar ragowar gadonta, sannan kuma sai ya gadar da mijin rabin diyyar matar wato dirhami dubu biyu da dari biyar, sannan sai ya ba wa makusantanta rabin diyyarta wato dubu biyu da dari biyar na dirhami, wannan kuwa saboda ba ta da wani da banda wannan da ta jefar da shi -barinsa- ya mutu. Ya ce: Wannan kuwa duka ya bayar da shi ne daga Baitulmalin Basara. (Biharul anwar, mujalladi 32, shafi: 214. Da Mustadrikul wasa'il, mujalladi 17, shafi: 446).
Haka nan ne musulunci ya sanya Baitulmali domin amfanin al'ummar musulmi da biyan bukatunsu, da bayar da hakkokinsu. Kamar yadda ya zo a hadisi cewa: Hakkin mutum musulmi ba ya faduwa banza. (Manla yahaduruhul fakih, mujalladi 4, shafi: 100). Wani hadisin ya zo cewa: Jinin mutum musulmi ba ya tafiya banza. Da wannan ne musulunci ya yalwata wa al'umma da yalwa da arziki, da lamunce rayuwa, da adalci.
Cibiyar Al'adun Musulunci
www.hikima.org
hfazah@yahoo.com
Hafiz Muhammad Sa'id
Wednesday, March 09, 2011

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)