Muassasar alhasanain (a.s)

Hakkin Uwa

3 Ra'ayoyi 01.7 / 5


HAKKIN UWA
Hakkin Uwa
Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Ka sani hakkin babarka cewa; Ta dauki cikinka a inda babu wani mutum mai iya daukar wani, ta ciyar da kai daga cikin zuciyarta da abin da babu wani mutum mai ciyar da irinsa ga wani, ta zama lokacinka da jinta da ganinta, hannunta da kafarta, gashinta da fuskarta, da dukkan gabobinta, tana mai murna da farin ciki. Tana mai jure duk wani abin kinta, da zoginta, da nauyinta, da bakin cikinta, har dai hannun kudura ya cire ka daga gareta, kuma ta fitar da kai zuwa duniya, sai ta yarda da koshinka ita ta ji yunwa, ta tufatar da kai ita kuwa ta tsaraita, ta kosar da kai ita kuwa ta yi kishi, ta sanya ka inuwa ita kuwa ta sha rana, ta ni'imantar da kai da wahalarta, da jiyar da kai dadin bacci da rashin baccinta, cikinta ya kasance wurin zama gareka, dakinta ya zamanto matattara gareka, kuma nononta ya zama salkar sha gunka, ranta kuma kariya ne gareka, tana shan zafin duniya da sanyinta don kare ka, to sai ka gode mata a kan wannan sai dai ba zaka iya ba sai da taimakon Allah da dacewarsa" .
Ubangiji madaukaki yana fada cewa: Ubangijinka ya hukunta cewa kada ku yi bauta sai gareshi, kuma ku kyautata wa iyaye…
Imam Sajjad haka ya kasance mai kiyaye hakkin uwa, an taba tambayarsa me ya sa ba ka cin abinci tare da babarka? sai ya ce: Ina jin tsoron kada in riga babata daukar wata loma da ita take so, sai ya kasance na saba wa abin da take so da wannan!
Imam Sadik (a.s) yana cewa; "Wani mutum ya zo wajen manzon Allah (s.a.w) sai ya tambaye shi ya ma'aikin Allah! Wane makusancina ne zan yi wa alheri? Sai ya ce: Babarka. Ya sake tambaya: bayan nan? Sai ma'aikin Allah ya ce: Babarka. Sai ya sake tambayaka a karo na uku. Sai ma'aikin Allah ya ce: Babarka. A karo na hudu Sai ma'aikin Allah ya ce masa: Babanka .
Amma kada mu manta irin wannan girmamawa ba mai cancantar ta sai uwa da ta dauki nauyin shiryar da 'ya'yanta ta sha wahala wajen nuna musu hanyar daidai ba wacce ta wulakanta su ba ta watsar da su babu wani tausayi ko damuwa da abin da zasu iya kasancewa nan gaba.
Yaron da bai samu soyayya da kauna daga uwa ba, zai taso tabbas cikin matsalolin rayuwa iri-iri na tunani, kuma a nan gaba zai iya kasancewa daga cikin wadanda ba zasu iya fahimtar ma'anar tausayi ga iyaye ko al'ummarsu ba, don haka iyayen da suka yi masa irin wannan tarbiyya suna kawo wa al'ummarsu wani bala'i ne.
Game da girmama uba kuwa Imam Sajjad yana cewa: "Amma hakkin babanka ka sani shi ne asalinka kuma ba don shi ba, da babu kai, kuma duk wani abu da kake gani gareka da yake kayatar da kai, to ka sani babanka ne mafarin wannan ni'imar gareka, sai ka gode wa Allah, ka gode masa gwargwadon wannan. Babu karfi sai da Allah" .
Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Addu'ar mutane uku tabbas abin amsawa ce;
1- Addu'ar wanda aka zalunta;
2- Addu'ar matafiyi;
3- Addu'ar Uba ga dansa ;
Sannan akwai fadin Ubangiji game da iyaye da cewa: Ya hukunta kada a bauta kowa sai shi kuma a kyautata wa iyaye, suna manya ne ko kuma dayansu, Ubangiji ya hana a ce musu tir ko kaico, sannan ya yi umarni da a gaya musu magana mai girma da girmamawa. Kuma akwai bayanai da suke nuni ga cewa; wadanda suke cutar da iyayensu suna nesa da rahamar Allah kuma suna cikin azaba a lahira.
A wata ruwayar Imam Sadik (a.s) yana cewa: "Me zai hana wani mutum musulmi ya kyautata wa iyayensa suna raye ne ko suna mace! Ya yi musu salla, ya bayar da sadaka don su, ya yi musu hajji da azumi, kuma ladan nan kamar yadda za a ba wa iyayensa shi ma fa haka nan za a ba shi, haka nan saboda wannan al'amari da yake ji na alheri ga iyaye Allah zai ba shi lada mai yawa.

A takaice muna iya fahimtar cewa; musulunci ya karfafa yin alaka da juna tsakanin 'yan'Adam kuma ta wannan hanyar ne zai kiyaye kasantuwar al'ummu a matsayin tsintsiya madauri daya, kuma ya samar da wata nau'in hadin kai tsakanin al'umma gaba daya da kara mata dogaro da juna.
Sabanin al'ummar da babu koyarwar addini a cikinta da dan'Adam ba shi da wata kima, a nan ana daukar dan'Adam kamar wani kaya ne da za a yi amfani da shi domin cimma burace-buracen duniya kawai, sannan kuma babu batun maganar kimar dan'Adam balle maganar dogaro da juna.
A irin wadannan wuraren babu maganar kimar kyawawan halaye kamar kyautata wa iyaye da sadaukar da kai, da zabar wani a kanmu, da kunya, da kame kai, da sadar da zumunci, da mutuntaka, da daukakar rai.
Abu Walad Hannad ya tambayi Imam Sadik (a.s) game da ma'anar fadin Allah (s.w.t): "Ku kyautata wa iyaye"? sai Imam Sadik (a.s) ya amsa masa da cewa: "Kyautatawa a nan tana nufin ku yi musu kyakkyawar mu'amala, kada ku tilasta su su biya muku bukatunku koda kuwa masu kudi ne. Kuma ku kula da halayensu da matsalolinsu, shin Ubangiji madaukaki ba ya cewa ba zaku iya samun kyakkyawa ba har sai kun ciyar daga abin da kuke so?
Sannan sai Imam Sadik (a.s) ya ce: "Koda kuwa sun tsufa kada ka sake ka yi musu mafi kankantar wulakantawa, sannan kada ka daga murya a kansu, wato koda sun bata maka rai kada ka wulakanta su, idan suka dake ka to kada ka yi kara a kansu, kada ka fadi magana mai zafi, ka gaya musu magana ta girmamawa; wato ka yi musu magana mai taushi da nuna kauna kamar ka ce musu Allah ya ba ku hakuri, wannan shi ne fadin alheri.
Amma da Allah madaukaki yake cewa: Ka shimfida musu fukafukin rusunawa don tausayi da kauna, wato ka tausasa zukatansu da kallon tausasawa da tausayawa, kuma kada ka taba daga murya a kan tasu, kada ka sanya hannunka a kan nasu, kada ka shiga gabansu yayin tafiya" .
Sannan wannan hidimar da suka yi ne dai ta sanya Ubangiji mahallici ya yi umarni da kiyaye hakkinsu ko da kuwa ba masu imani ba ne: Mu'ammar dan Khallad ya tambayi Imam Ridha (a.s) cewa: Shin zai iya yi wa iyayen da ba bisa tafarkin gaskiya suke ba addu'a? Sai Imam ya ce: Ka yi musu addu'a kuma ka yi musu sadaka, kuma idan suna raye ba su san hanyar gaskiya ba to ka kyautata musu! Domin manzon Allah (s.a.w) ya ce: Ubangiji ya aiko ni da rahama ne da tausayawa, ba da tsanantawa da cutarwa da rashin kyautatawa ba .
Kyautata wa iyaye yana daga alamomin sanin Allah madaukaki da girmansa, domin babu wata ibada da take gaggauta kusantarwa zuwa ga Allah fiye da kyautatawa iyaye, domin hakkin iyaye reshe ne na hakkin Allah madaukaki. Amma da sharadin kada iyaye su kautar da 'ya'yansu daga tafarkin gaskiya da shiriya, su ba su tarbiyya sahihiya mai amfani da inganci, kuma ba su canja yakinin 'ya'yansu da kokwanto ba, ba su damfara su da duniya ba maimakon Allah (s.w.t) da gudun duniya.
Amma idan iyaye suka kauce wa tafarkin Allah madaukaki to saba musu zata kasance ibada ce, domin ba a saba wa Allah domin biyayya ga abin halitta, kamar dai yadda Allah madaukaki ya ce: "Idan suka tilasta maka ka yi shirka da ni da wani abu wanda ba ka san shi ba to kada ka yi biyayya garesu" .
Daga nan zamu iya fahimtar cewa girmama uwa da uba dole ne ya kasance ba a cikin abin da ya saba wa Allah ba, domin babu biyayya a kan bata da sabon mahalicci madaukaki, amma kuma duk da haka ba a yarda da yi musu wulakanci da mummunan halaye ba, dole ne kuma a girmama su ko suna da imani ko ba su da shi. Kuma Imam Bakir (a.s) a game da haka ya kawo mana magana mai gaskiya abin gaskatawa da cewa; Ubangiji madaukaki bai toge kowa ba game da abubuwa uku:
1- Kiyaye amana ga kowa koda kuwa kafiri ne;
2- Cika alkawari ga kowa koda kuwa ga mutumin banza;
3- Kyautata wa iyaye koda kuwa na gari ne ko batattu ;
Allah madaukaki ya ce: "Idan suka tilasta maka ka yi shirka da ni da wani abu wanda ba ka san shi ba to kada ka yi biyayya garesu" .
A wani hadisin mai girma da daukaka yana cewa: Babu wani mutum da zai kalli iyayensa da soyayya da kauna da tausayawa sai Ubangiji ya ba shi ladan hajji karbabbe a kowane kallo da ya yi, sai aka tambayi manzon Allah (s.a.w)! Idan da mutum zai kalli fuskar iyaye sau dari yana da wannan ladan kuwa? Sai ya ce: Haka ne, idan ya yi hakan sau dari a rana yana da ladan hajji dari da zai samu .
Ibrahim dan Mahzam yana cewa: Wata rana na fito daga wajen Imam Sadik (a.s) a Madina na tafi gidana, babata tana rayuwa tare da ni, sai ta yi jayayya da ni kan wani al'amari kuma na gaya mata magana maras dadi da ba ta dace ba. Wayewar garin wannan ranar bayan sallar asuba sai na sake zuwa wajensa (a.s). Yayin da nake shigowa ba tare da na ce komai ba sai Imam (a.s) ya ce da ni: Ya kai dan Mahzam! Daren jiya ka yi magana mai zafi mai kaushi ga babarka, shin ba ka sani ba cewa cikinta ne ya zama gidanka tsawon lokaci, da goyonka da ta yi, kirjinta ya zama abincinka, saboda me kake yi mata magana mai zafi, kada ka sake yin hakan !
Wani saurayi daga sahabban manzon Allah (s.a.w) da ya yi rashin lafiya aka kwantar da shi. Sai manzon Allah (s.a.w) ya tafi domin ya gai da shi. Ga halinsa ya yi tsanani kuma ga shi karshen rayuwarsa ne. sai manzon rahama ya umarce shi da ya fadi kalmar shahada, amma sai harshensa ya kasa kawo wannan kalma.
Sai manzon Allah (s.a.w) ya tambayi wata mata da take wurin cewa: Shin wannan saurayi yana da uwa kuwa? Sai ya ta ce: E, ni ce babarsa. Sai ya ce: Shin kina fushi da shi ne? Sai ya ta ce: E, ya ma'aikin Allah. Sai manzon rahama (s.a.w) ya nemi ta yafe masa kurakuransa, sai ta ce: Ya ma'aikin Allah na yafe masa saboda kai.
A wannan lokacin sai manzon Allah ya sanar da wannan saurayi wannan addu'a: Ya man yakabalul yasira wa ya'afu anil kasir, ikbil minni alyasir wa'afu annil kasir, innaka antal afuwwul gafur. Sannan sai ya lakkana masa kalmar shahada, a wannan lokacin ne saurayi ya bude bakinsa cikin sauki ya fadi wannan kalma ta shahada" .
Imam Sadik (a.s) yana cewa; "Wani mutum ya zo wajen manzon Allah (s.a.w) sai ya tambaye shi ya ma'aikin Allah! Wane makusancina ne zan yi wa alheri? Sai ya ce: Babarka. Ya sake tambaya: Bayan nan? Sai ma'aikin Allah ya ce: Babarka. Sai ya sake tambayaka a karo na uku. Sai ma'aikin Allah ya ce: Babarka. A karo na hudu Sai ma'aikin Allah ya ce masa: Babanka .
Tun ranar farko da Allah madaukaki ya halicci mutum ya sanya jagorancin 'ya'ya a hannun iyaye wanda yake shi ne uba na farko Annabi Adam (a.s). Wadannan hakkokin an yi bayaninsu a wasu ayoyin na Kur'ani mai girma, aka kuma hada tauhidi da biyayya ga iyaye domin nuni zuwa ga girman wadannan hakkoki a fadinsa madaukaki; "Kuma yayin da muka riki alkawarin Banu Isra'ila da cewa; kada ku bauta wa kowa sai Allah kuma ku kyautata wa iyaye" .
Sannan har ilayau aka sake nuna matsayi babba da Annabi Yahaya ya kai saobda biyayya ga iyaye ana yabonsa da cewa:
"Ya kasance mai biyayya ga iyayensa bai kasance jabberi shakiyyi ba ". Kamar yadda Annabi Isa (a.s) yake fada da dukkan alfahari cewa: "Kuma mai biyayya ga mahaifiyata kuma bai sanya ni jabberi shakiyyi ba" .
Musulunci ya himmantu da nuni zuwa ga wannan matsayi na hakkin iyaye yayin da manzon rahama (s.a.w) yake shelanta cewa: "Aljanna tana karkashin tafin iyaye mata ne" . a wata ruwayar ya zo cewa; "Karkashin tafin iyaye mata, dausayi ne daga dausayin aljanna" .
Akwai bayanai masu mihimmanci da zamu so mai karatu ya koma wa littafinmu na alakar iyaye da 'ya'yansu domin sanin karin bayani kan su kamar haka:
Sanin Hakkin Iyaye
Sanyaya Halaye Ga Iyaye
Nisantar Tsananta wa Iyaye
Godiya Ga Iyaye
Kiyaye Mutuncin Iyaye
Ba Wa Iyaye Dukiya
Biyayya A Kan Tafarkin Gaskiya
Taimakonsu Lokacin Tsufa

Hakkokin Iyaye Bayan Mutuwa
A mahangar musulunci hakkin iyaye kan 'ya'ya baya karewa da mutuwa, kamar yadda iyaye suke da hakki a lokacin da suke raye haka nan ma suna da hakki kan 'ya'ya bayan mutuwarsu. Wasu daga cikin irin wadannan hakkokin sun hada da:
1- Ziyarar kabarinsu;
2-Karanta musu Kur'ani;
3-Ba su ladan ayyukan alheri;
4-Biya musu basussukansu;
5-Yi musu hajji a ba su ladan;
6-Yi musu sadaka a ba su ladan;
7-Yi musu azumi a ba su ladan;
8-Ba su ladan 'yanta bayi;
9-Yi musu salla a ba su ladan;
10- Yi musu addu'a .

Sakamakon Kyautata Wa Iyaye
Idan mun koma zuwa ga hadisan imamai (a.s) zamu samu cewa sun yi nuni zuwa ga wani sakamako da za a samu sakamakon kyautata wa iyaye, kuma zamu yi nuni zuwa ga wasu daga cikinsu:
Samun Aljanna

Ladan Shahada:
Akwai wadanda ruwayoyi suka zo suna nuni da cewa suna da ladan shahidai da suka hada da:
1-Wanda ya kone a wuta;
2-Wanda ya mutu a cikin matsatsin mutane;
3-Matar da mutum yayin haihuwa;
4-Wanda gini ya fado masa ya mutu;
5-Wanda ya nutse a ruwa ya mutu;
6-Musulmin da ata dabba ta cinye shi;
7-Da wanda yake kokarin ganin ya yalwata wa iyalinsa dai iyayensa;
Wadannan dukkaninsu suna cikin shahidai ;
Kyautata wa Iyaye ya fi Jihadi Lada
Shi ne Mafi Kyawun Aiki
Tsawon Rayuwa Da Samun Da Nagari
Saukin Mutuwa
Ladan Hajji
Shafe Zunubai
Samun Baban Matsayi

Dacewa a Rayuwa
1- Samun ilimi sakamakon girmama malami;
2- Tabbatar imani sakamakon girmama Allah madaukaki;
3- Jin dadin rayuwa sakamakon girmama iyaye;
4- Samun tsira daga jahannama sakamakon barin cutar da mutane.
Biyayya Ga Manzon Allah (s.a.w) ne

Mummunan Sakamakon Saba Wa Iyaye
Kamar yadda biyayya ga iyaye take da kyakkyawan sakamakon duniya da lahira saboda biyayya ce ga Allah haka nan ma munana halaye ga iyaye yake da nasa munanan sakamako masu cutarwa, kuma zamu yi nuni da wasu daga cikinsu a nan kamar haka:
1- Korewa daga wurin Annabi (s.a.w) ;
2- Nisanta daga adalci ;
3- Rasa ni'imomin Ubangiji kamar aljanna ;
4- Matsaloli a duniya ;
5- Azabar rai mummuna ;
6- Fushin Allah ;
7- Gajarcin rayuwa ;
8- Hana shi hakkokin zamantakewa ;
9- Sabo ne babba .
Cibiyar Al'adun Musulunci
www.hikima.org
hfazah@yahoo.com
Hafiz Muhammad Sa'id
Tuesday, May 31, 2011

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)