Muassasar alhasanain (a.s)

Hakkin Dan'uwa

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5


Hakkin Dan'uwa
Imam Aliyyu Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Kuma hakkin dan'uwanka shi ne ka sani cewa shi ne hannunka da kake shimfidawa, kuma bayanka da ake jingina da shi, kuma daukakarka da kake dogaro da ita, kuma karfinka da kake ijewa da shi, don haka kada ka rike shi makami a kan sabon Allah, ko ka sanya shi tanadi domin zaluntar halittar Allah, kuma kada ka bar taimakonsa, da agaza masa kan makiyinsa, da shiga tsakaninsa da shaidancins, da ba shi nasiha, da fuskantuwa zuwa gareshi a tafarkin Allah, to idan ya karkatu zuwa ga ubangijinsa, ya kyautata amsa masa, in kuwa ba haka ba, to Allah ya kasance shi ne ya fi zabuwa gunka, kuma mafi girma gareka fiye da shi".
Da farko muna iya cewa musulmi duka 'yan'uwa ne saboda haka hakkin da yake hawa kan dan'uwa yana hawa tsakaninsu amma dan'uwa na jini yana da kari kan dan'uwa na musulunci da wajabcin sadar da zumuncinsa.
Wani lokaci ana kiran abota da 'yan'uwantaka domin samun kusanci mai karfi da la'akari da cewa dukkan musulmi ma'abota juna ne, don haka abokan juna ne, kuma 'yan'uwan juna ne.
Daga cikin hakkokin dan'uwa a kan dan'uwa: Yi masa nasiha da kare shi daga wahalhalun da zaka iya taimaka masa wajan maganinsu kamar taimakonsa wajan sana'a, da samun magani, da kudin makaranta, da biyan bukatunsa, da kokarin kawar masa da talauci, da taimakonsa a kan makiyinsa.
Malam Muzaffar a Littafinsa yana cewa: Daga cikin mafi girma da kyawun abin da Musulunci ya yi kira zuwa gareshi shi ne 'yan'uwantaka tsakanin musulmi a kan duk sassabawarsu da martabobinsu da mukamansu. Kamar yadda mafi munin abin da musulmi suka yi a yau da kuma kafin yau shi ne, sakacinsu wajan riko da wannan 'yan'uwantaka ta musulunci.
Domin mafi karancin koyarwar wannan 'yanuwatakar ita ce "Ya so wa dan'uwansa musulmi abin da yake so wa kansa, kuma ya ki masa abin da yake ki wa kansa, kamar yadda zai zo a hadisin Imam Sadik (a.s).
Ka duba ka yi tunani a kan wannan dabi'a mai sauki a mahangar Ahlul Baiti (a.s), za ka samu cewa yana daga mafi wahalar abin da zaka iya samu wajan musulmi. Da musulmi zasu yi wa kansu adalci su san addininsu sani na hakika, su yi riko da wannan dabi'a ta so wa dayansu dan'uwansa abin da yake so wa kansa, da ba a ga zalunci daga wani ba ko ketare iyaka, ko sata, ko karya, ko yi da wani, ko annamimanci, ko zargi da mummuna, ko suka da karya, ko wulakanci, ko girman kai.
Da musulmi sun tsaya sun fahimci mafi karancin ma'anar hakkin 'yan'uwantaka a tsakaninsu kuma suka yi aiki da ita, da zalunci da ketare iyaka sun kau daga bayan kasa, kuma da ka ga 'yan Adam sun zama 'yan'uwa suna masu haduwa da juna cikin farin ciki, kuma da mafi daukakar sa'adar zamantakewa ta cika garesu, kuma da mafarkin malaman falsafa na samar da mafificiyar hukuma ya tabbata, da sun kasance masu musayar soyayya a tsakaninsu, da ba su bukaci wasu hukumomi da kotuna ba, ko 'yan sanda, ko kurkuku, ko dokokin laifuffuka, da dokokin haddi da kisasi, kuma da ba su rusuna wa 'yan mulkin mallaka ba, kuma da dawagitai ba su bautar da su ba, kuma da kasa ta canja ta zama aljannar ni'ima gidan rabauta.
Kuma da dokokin soyayya sun jagoranci rayuwar 'yan Adam kamar yadda Addini yake so na koyarwar 'yan'uwantaka, to da kalmar neman adalci ta bace daga harsunanmu, wato ba zamu zamanto muna bukatar adalci da dokokinsa ba ballantana har mu bukaci amfani da kalmarsa. Saboda dokokin soyayya sun isar mana wajen yada alheri, da aminci, da sa'ada, da murna, domin mutum ba zai bukaci amfani da adalci ko dokoki ba, sai idan ya rasa soyayya daga wanda ya wajaba ya yi masa adalci, amma a wajan wanda yake nuna masa kauna da soyayya, kamar da, da dan'uwa, sai dai ya kyautata musu ya hakura da abubuwan da yake so, duk wannan sakamakon so da kauna ne daga yardar zuciya, ba don adalci ko masalahar kansa ba.
Sirrin haka kuwa shi ne cewa mutum ba ya so sai kansa ko abin da ya dace da kansa, kuma mustahili ne ya so wani abu ko wani mutum da yake wajen ransa, sai dai idan yana da alaka da shi, kuma ya shiga ransa. Kamar kuma yadda yake mustahili ne ya sadaukar da zabin kansa gareshi a cikin abin da yake so yake kuma kauna saboda wani mutum da ba ya sonsa, ba ya kuma kaunarsa, sai dai idan yana da wani imani mai karfi da ya fi karfin son ransa, kamar imani da kyawun adalci da kyautatawa, a yayin nan yana iya sadaukar da dayan abubuwan da yake so, ya yi fansa da shi saboda son wani.
Farkon madaukakan darajoji da suka wajaba musulmi ya siffantu da su, su ne; ya kasance yana jin hakkin 'yan'uwantaka ga sauran mutane, idan kuwa ya kasa wannan, to zai gaza aikata mafi yawa da haka saboda galabar son ransa, saboda haka yana wajaba a kansa ya cusa wa kansa akidar son adalci, da kyautata biyayya ga shiryarwar musulunci, idan kuwa ya gaza hakan to bai cancanci ya zama musulmi ba sai dai a suna, kuma ya fita daga soyayyar Allah (s.w.t), kuma Allah ba ya da wani buri a kansa kamar yadda zai zo a hadisi mai zuwa.
Sau da yawa sha'awar mutum takan yi galaba a kansa, sai ya zamanto mafi wahalar abin da yake fama da shi, shi ne ransa ta yarda da adalci, balle kuma ya samu imani cikakke da ya fi karfin sha'awarsa.
Saboda haka ne ma kiyaye hakkin 'yan'uwantaka ya zama daga mafi wahalar koyarwar addini idan babu imani na gaskiya game da 'yan'uwantaka. Don haka ne imam Abu Abdullah (a.s) ya ji tsoron yi wa sahabinsa "Almu'ula Bn Khunais" bayanin tambayarsa game da hakkin 'yan'uwantaka sama da abin da ya kamata ya bayyana masa, domin tsoron kada ya koyi a bin da ba zai iya aiki da shi ba.
Sai Mu'ula ya ce : Mene ne hakkin musulmi a kan musulmi?
Sai Abu Abdullahi ya ce: Yana da hakkoki bakwai wajibai, babu wani hakki daga cikinsu sai ya wajaba a kansa, idan ya tozarta daya daga ciki to ya fita daga soyayyar Allah da biyayyarsa, kuma Allah ba shi da wani buri a gareshi.
Sai na ce masa: A sanya ni fansa gareka! Mece ce?
Sai ya ce: Ya Mu'ula ni ina mai tausasa wa gareka, ina tsoron ka tozarta ba zaka kiyaye ba, ko kuma ka sani ba za ka aikata ba.
Na ce: Babu karfi sai da Allah.
Yayin nan sai Imam (a.s) ya ambaci hakkoki bakwai, bayan ya fada game da na farkonsu cewa: "Mafi saukin hakki daga cikinsu shi ne ka so wa dan'uwanka kamar yadda kake so wa kanka, ka kuma ki masa abin da kake ki wa kanka".
SubhanalLahi! Wannan shi ne hakki mai kankanta, to yaya wannan hakkin mafi kankanta yake a garemu yau mu musulmi? Kaicon fuskokin da suke da'awar musulunci amma ba sa aiki da mafi kankantar abin da ya wajaba na daga hakkokinsa. Abu mafi ban mamaki kuma shi ne, a dangata wannan rashin ci gaban da ya samu musulmi ga musulunci, alhalin laifi ba na kowa ba ne sai na wadanda suke kiran kansu musulmi amma ba sa yin aiki da mafi karancin abin da ya wajabta musu da su yi aiki da shi na koyarwar addininsu.
Domin tarihi kawai, kuma don mu san kawukanmu da takaitawarta zamu ambaci wadannan hakkoki bakwai wadanda Imam (a.s) ya bayyana su:
l- Ka so wa dan'uwanka musulmi abin da kake so wa kanka, kuma ka ki masa abin da kake ki wa kanka.
2- Ka nisanci fushinsa, ka bi yardarsa, kuma ka bi umarninsa.
3- Ka taimake shi da kanka, da dukiyarka, da harshenka, da hannunka, da kafarka.
4- Ka zamanto idonsa, dan jagoransa, kuma madubinsa.
5- Kada ka koshi, shi kuma yana cikin yunwace, kada ka kashe kishirwarka shi kuma yana jin kishirwa, kada ka zama a suturce shi yana tsirara.
6- In kana da mai hidima shi kuma dan'uwanka ba shi da mai hidima, to wajibi ne ka tura mai hidimarka, sai ya wanke masa kaya, ya dafa masa abinci, ya gyara masa shimfida.
7- Ka kubutar da rantsuwarsa, ka amsa kiransa, ka gaishe da maras lafiyarsa, kuma ka halarci jana'izarsa. Idan kuwa ka san yana da wata bukata sai ka yi gaggawar biya masa ita, kada ka bari har sai ya tambaye ka, sai dai ka gaggauta masa.
Sannan ya rufe maganarsa da cewa: "Idan ka aikata haka to ka hada soyayyarka da soyayyarsa, kuma soyayyarsa da soyayyarka".
Akwai hadisai da yawa da suka kunshi ma'anar da ta zo a wannan hadisi daga imamanmu (a.s), wasunsu daga littafin Wasa'il a babobi daban-daban.
Tayiwu wasu su yi tsammanin cewa abin nufi da 'yanuwantaka a hadisin Ahlul Baiti (a.s) ya kebanci tsakanin musulmi ne wadanda suke daga mabiyansu a kebance, amma komawa ga ruwayoyinsu yana kawar da wannan zato, koda yake sun kasance ta wani bangare suna tsananta musantawa ga wanda ya saba wa tafarkinsu kuma ba ya riko da shiriyarsu. Ya wadatar ka karanta hadisin Mu'awiya Dan Wahab da ya ce :
Na ce masa : Yaya ya kamata gare mu mu yi tsakaninmu da mutanenmu, da kuma wadanda muke cudanya da su na daga mutane wadanda ba sa kan al'amarinmu".
Sai Ya ce: "Ku duba Imamanku wadanda kuke koyi da su, ku yi yadda suke yi, na rantse da Allah! su suna gaishe da maras lafiyarsu, suna halartar jana'izarsu, suna ba da shaida garesu da kuma a kansu, kuma suna bayar da amana garesu".
Amma 'yan'uwantakar da Imamai suke son ta daga mabiyansu, tana saman wannan 'yan'uwantaka ta musulunci, Kuma ya isar ka karanta wannan muhawara tsakanin Abana Bn Taglib da Imam Sadik (a.s) daga hadisin da Abana ya rawaito da kansa yana mai cewa: Na kasance ina dawafi tare da Abi Abdullah (a.s) sai wani mutumi daga cikin mutanenmu ya bujuro mini wanda ya riga ya tambaye ni in raka shi wata biyan bukatarsa, sai ya yi mini ishara, sai Abu Abdullahi (a.s) ya gan mu.
Sai ya ce: Ya Abana kai wannan yake nema?
Na ce: Na'am.
Ya ce: Shin yana kan abin da kake kai?
Na ce: Na'am.
Ya ce: Maza ka tafi zuwa gare shi ka yanke dawafin.
Na ce: Koda ya kasance dawafin wajibi?
Ya ce: Na'am.
Abana ya ce: Sai na tafi, bayan nan -wani lokaci- sai na shiga wajansa (a.s) na tambaye shi game da hakkin mumini. Sai ya ce: Bari kada ka kawo wannan! Ban gushe ba ina sake tambaya har sai da ya ce: Ya Abana ka raba masa rabin dukiyarka, sannan sai ya kalle ni ya ga abin da ya shige ni, sai ya ce: Ya Abana ashe ba ka san Allah ya riga ya ambaci masu fifita wasu a kan kansu ba?
Na ce: Haka ne!
Ya ce: "Idan ka ba shi rabin dukiyarka ba ka fifita shi ba, kana fifita shi ne kawai idan ka ba shi daya rabin!
Na ce : Hakika a yanayinmu mai ban kunya bai dace ba mu kira kanmu muminai na hakika. Mu muna wani waje ne, koyarwar Imamanmu (a.s) tana wani wajen. Kuma abin da ya shigi zuciyar Abana zai shigi zuciyar duk mai karanta wannan hadisin, sai dai ya juya fuskarsa kawai yana mai mantar da kansa shi kamar wani ake wa magana ba shi ba, kuma ba ya yi wa kansa hisabi irin na mutumin da yake abin tambaya.
Dan'uwan mutum na jinni ba shi ne kawai dan'uwansa ba a shari'ar musulunci, addinin rahama na musulunci ya sanya duk wani mutum musulmi a matsayin dan'uwa ne ga musulmi.
Don haka kowane mutum yana da hakkoki masu yawa a kan dan'uwansa mutum musamman abokin zamantakewa na kasa ko gari, ko makaranta, da duk wani waje da alaka ta kan hada juna kamar wajan aiki. Babban ma'auni na hakkin junanmu a kanmu shi ne wanda ya zo a cikin Hadisai na cewa: "Mu duba duk abin da muke so a yi mana sai mu yi wa mutane shi, mu kuma duba duk abin da muke ki a yi mana shi sai mu guji yi wa mutane shi" . Misali kana kin a wulakanta ka, kuma kana son a girmamaka, to a nan sai ka ki wulakanta mutane kuma ka girmama su.
Wannan hadisi da za a yi aiki da shi, da Duniya gaba daya ta zauna cikin aminci, da ta juya ta zama kamar aljanna, da so ya game tsakanin mai kudi da talaka, da mai ilimi da maras ilimi, da miji da mata, da 'ya'ya da iyaye, da malami da dalibi, da mai mulki da wanda ake mulka, da dukkanin nau'i na mutane gaba daya.
Wannan hakkoki kuwa sun hada nisantar cutar da waninmu ta kowace hanya kamar duka ko da kuwa dalibinmu ne, amma a kasashenmu duka wani abu ne mai sauki. Kai a makarantun Furamare da na Allo har yakan yi muni kwarai; mai dukan ba ya neman izinin Shugaban musulmi, ko uban da, sai a yi ta jibga ko mai kankantar abu.
Duka ba ya halatta koda kuwa uwa ce ga danta sai da izinin uba , ko dukan uba ga dansa ko wanda Shugaban musulmi ya ba wa izini. Shi ma uban a matsayin tarbiyyantarwa da ya zama sai ta hakan, kuma ba mai cutarwa ba. Ko kuma miji ga mace mai nushuzi , shi ma a mataki na uku na karshe kuma ba mai cutarwa ba, sai kuma Shugaban musulmi ga mai laifi kamar a haddi ko ladabtarwa.
Daga cikin hakkin mutum a kan waninsa shi ne ya shiryar da shi abin da zai amfanar da shi, kamar hakkin mutane a kan likita na ya nuna musu hanyar tsafta da kare lafiya, da yadda zasu tsara abinci da abin sha mai sanya lafiya, da magunguna, musamman ta hanyar Gidan Radio da Talabijin; Da maras lafiya zai tafi wajan likita sai ya cutar da shi to dole ne ya biya shi diyya, amma idan da gangan ne sai a yi masa kisasi.
Kamar yadda yake wajibi ne a kan malami ya shiryar da al'umma kuma ya ilmantar da ita, mai kudi kuwa ya yi odar abin da yake tattalin rayuwa na al'umma kuma ya sanya farashi da talaka zai iya saya cikin sauki, haka ma injiniya ya kyautata mota ta yadda ba zata zama hadari ga mai hawanta ba, mai gini kuwa ya kyautata shi.
Haka nan yana kan mai sayan kaya ya girmama mai sayarwa shi ma mai sayarwa ya mutunta mai saya, likita da marasa lafiya, mai kudi da talaka, malami da marasa sani, mai haya da dan haya, mai aiki da shugaba. Bai kamata ba shugaba a ma'aikata ya rika kallon masinja kallon wulakanci, hakki ne a kansa ya girmama masinja, ya tuna shi ma dan kasa ne kamarsa kuma ma'aikaci da bai fi shi da komai ba a wajan Allah sai dai idan ya fi shi takawa domin ita ce ma'aunin fifiko.
Haka ma dan hayar mota kamar Taksi da Bos (hayis) kada ya zama idan ya ga fasinja yana ganin naira goma ne ko ishirin, hakki ne a kansa ya ga mutum yake kallo kafin ya ga Naira ishirin, kuma ya yi mu'amala da shi ta mutunci da girmamawa tsakanin juna.
Haka nan alakar na kan mota da na kan jaki, da na jirgin sama da na kasa , duka daya ne a wajan Allah kuma ba mai fifiko sai da takawa, rashin kiyaye wannan da mantawa da Allah ya sanya rashin kiyaye hakkin juna.
Wata rana wani mai kudi shahararre ya taba kade wani almajiri da mota a kan titi, maimakon mutane su nemi ya bayar da kudin magani a kai almajirin kyamist tun da shi ba shi da mutuntaka domin ba ya ganin almajirin mutum ne kamarsa don ko taba shi bai yi ba, sai suka zo suna ba shi hakuri.
Har wani mai matacciyar zuciya yana cewa: Ai da ma haka almajirai suke ba sa jin magana. Haka mutakabbirin ya hau mota ya wuce! Shi kuwa bawan Allah yana ta nishi har ya samu da kyar ya taka. Su kuwa mutanen ba mai ji a jikinsa cewa an ji wa wani mutum daga cikin mutane masu hakki kamar kowa ciwo! Wallahi da dabba ce aka kade da sun fi ba ta muhimmanci!.
Daga cikin hakkin dan'uwa a taya shi bakin ciki idan wani abu ya same shi musamman dan'uwa na jini ko na Addini da makoci, idan an yi masa mutuwa to ya kamata ne bisa koyarwa ta Manzo (s.a.w) a yi abinci kwana uku daga makota ana kai musu kamar yadda ya koya mana kyawawan dabi'u da fadinsa: "Ku yi wa iyalan Ja'afar abinci hakika wani al'amari da ya shagaltar da su ya same su" . Amma abin sai ya zama bisa akasi, maimakon a kai gidan mutuwa, sai ya zama su ne kuma za a shagaltar da su da ciyar da masu taruwa.
Idan muka waiwayi alakar mai kudi da yaronsa al'amarin ya kai ga ana iya samun yaron Alhaji da rashin lafiyarsa bai fi a kashe kudi kankani a kansa ba ya warke amma yana iya mutuwa alhali Alhajin da ya yi wa hidima a gida, da shago, da kanti, shekaru masu yawa yana gani sai dai ya mutu. Wani kuma yana aiki karkashin uban gidansa amma canja riga mai tsada yana iya tayar da mugunyar tsatsar nan ta hassada a zuciyar ubangidan, sai ya ce da shi: Ka tattara naka ka yi gaba kuma ka bar min shagona.
Akwai wata kabila da galibinsu ba ma musulmi ba ne amma har bikin yaye yaron shagonsu suke da shi. Idan kuwa ka duba bangaren kere-kere to a nan sun yi nisa, sannan wasu abubuwan idan kana nemansu ranar lahadi to lallai ka wahala domin sun kulle shaguna.
Don haka idan ana son mafita da ci gaba ya zama dole ne a siffantu da siffa ta gari a bar hassada da kyashi, a cire duk wata dauda daga zuciya. Idan wani ya ci gaba ta hanyarmu sai mu gode wa Allah, amma rashin kishin kai da son ci gaban juna, da rashin kyawawa dabi'un musulunci ya sanya ana danne hakkin juna, kuma mu sani cewa dukkan ayyukanmu suna da hisabi a Lahira.
Bari mu leka hadisai mu ga yadda suka kawo bayanai kan 'yan'uwantaka ba tare da wani karin bayani ba:
Kur'ani mai daraja yana cewa: "Hakika muminai 'yan'uwa ne ku yi sulhu tsakanin 'yan'uwanku, kuma ku ji tsoron Allah ko a yi muku rahama" .
Daga Manzon Allah (s.a.w) ya ce: muminai 'yan'uwan juna ne, jininsu yana daidaito, ku su masu taimakon juna ne a kan wasunsu, kuma na kasansu suna tafiyar da yarjejeniyarsu .
Daga Imam Ali (a.s) ya ce: Da yawa (zaka samu) wani dan'uwa da ba mahaifiyarka ce ta haife shi ba .
Abu Ja'afar (a.s) ya ce: Mumini dan'uwan mumini ne ta uba daya da uwa daya .
Imam Sadik (a.s) ya ce: "Mumini dan'uwan mumini ne, idonsa kuma dan jagoransa, kada ya ha'ince shi, kiada ya zalunce shi, kada ya yi masa algus, kada ya yi masa alkawari ya saba masa" .
Imam Sadik (a.s) ya ce: "Mumini dan'uwan mumini ne kamar jiki daya, idan wani bangare ya ji zogi sai ya samu zogin sa sauran jikinsa, ruyukansu daga ruhi daya ne " .
'Yan'uwan Gaskiya
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Ku yawaita 'yan'uwa, hakika kowane mumini yana da ceto ranar kiyama" .
Imam Ali (a.s) ya ce: "Ka yi riko da 'yan'uwa na gaskiya, ka yawaita adadinsu, su a gobe tanadi ne gun yalwa, kuma kariya ne gun bala'i" .
Son 'Yan'uwa
Imam Ali (a.s) ya ce: "Kada dan'uwanka ya fi ka karfi kan kaunarsa" .
Imam Ali (a.s) ya ce: "Ka so 'yan'uwa daidai gwargwadon takawarsu" .
Imam Sadik (a.s) ya ce: "Yana daga son mutum ga addininsa son sa ga dan'uwansa" .
Abu Mai Wajabta Wanzuwar Kauna
Imam Sadik (a.s) ya ce: "Ya kai Nu'uman! Idan kana son tsantsar son dan'uwanka gareka, to kada ka yi masa raha, kada ka yi jayayya da shi, kada ka yi masa alfahari, kada ka nuna shi da dan yatsa" .
Imam Sadik (a.s) ya ce: "'Yan'uwa suna bukatar abubuwa uku a tsakaninsu idan suka yi amfani da ita, idan kuwa ba haka ba to lallai zasu nisanci juna su yi kiyayya, su ne: yi wa juna adalci, da tausasa wa juna, da kore hassada" .
'Yan'uwantaka Don Allah
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Duba zuwa ga dan'uwan da kake sonsa ibada ce saboda Allah" .
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Mutum bai taba amfanuwa ba bayan amfanuwar musuluci da wani abu da ya kai dan'uwa da yake amfana daga gareshi saboda Allah" .
Imam Ali (a.s) ya ce: "Da 'yan'uwantaka saboda Allah ne kauna take tsarkaka" .
Imam Ali (a.s) ya ce: "Masu 'yan'uwantaka saboda Allah kaunarsu tana dawwama saboda dawwamar musababinta" .
59. Imam Ali (a.s) ya ce: "Da 'yan'uwantaka saboda Allah ne kauna take fitar da alheri" .
'Yan'uwantaka Don Duniya
Imam Ali (a.s) ya ce: "Duk wanda kaunarsa ba saboda Allah ba ce ka guje shi, kaunarsa mummuna ce, kuma abotaka da shi mai shu'umi ce" .
Imam Ali (a.s) ya ce: "Duk wanda ya yi 'yan'uwantaka saboda Allah ya rabauta, wanda ya yi abota don duniya ya yi hasara" .
Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya yi abotaka da kai don wani abu, zai bar ka yayin da ya kare" .
Shelantawa Dan'uwa Kauna
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Idan dayanku ya so abokinsa ko dan'uwansa to ya sanar da shi" .
Wani mutum ya wuce a masallaci Imam Abu Ja'afar Bakir (a.s) da Imam Sadik (a.s) suna zaune, sai wani a majalisin ya ce: wallahi ina kaunar wannan mutumin. Sai Abu Ja'afar ya ce masa: " Lallai ka sanar da shi, wannan zai fi wanzar da kauna, kuma ya fi ga hada zukata" .
Kaunar Dan'uwa Nuni ne Ga Kaunar Dan'uwansa Gareshi
Imam Ali (a.s) ya ce: "Ku tambayi zukata game da labarin kauna; Su sheda ne da ba sa karbar rashawa" .
Imam Bakir (a.s) ya ce: "Ka san kaunar da kake da ita a zuciyar dan'uwanka ta hanyar abin da kake da shi a zuciyarka (game da shi)" .
Imam Hadi (a.s) ya ce: "Kada ka nemi kyakkyawar kauna daga wanda ka gurbata wa (rayuwa), ko nasiha daga wanda ka juya mummunan zatonka zuwa gareshi, ka sani zuciyar waninka gareka kamar zuciyarka ce gareshi" .
Yankewar 'Yan'uwa
Imam Ali (a.s) ya ce: " Idan kana son yankewar dan'uwa, to ka rage masa wani abu daga gareka da zai iya dawo wa zuwa gareka wata rana idan ya ga yana son hakan " .
Imam Ali (a.s) ya ce: " Yankewa bayan sadarwa, da jafa'i bayan 'yan'uwantaka, da gaba bayan kauna, sun munana kwarai da gaske " .
Imam Sadik (a.s) ya ce: "Wanda duk ya sanya kaunarsa ba a mahallinta ba, to hakika ya jefa kansa gun yankewa" .
Sadar Da 'Yan'uwa
Imam Ali (a.s) ya ce: "Kada dan'uwanka ya fi karfin yankewa fiye da karfin sadarwarka, kuma kada karfin munanawa fiye da kyautatawa" .
Imam Husain (a.s) ya ce: "Hakika mafi sadarwar mutane shi ne wanda ya sadar da wanda ya yanke shi" .
Rabe-raben 'Yan'uwa
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Mafi karancin abu a karshen zamani shi ne dan'uwa da za a aminta da shi ko kuma dirhami (kudin) na halal" .
Imam Sadik (a.s) ya ce: "'Yan'uwa kala uku ne; wanda ake kamar abinci ne da ake bukatarsa a kowane lokaci, to wannan ne mai hankali, na biyu shi yana kama da cutga ce wannan shi ne wawa, na uku kuwa shi ne mai kama da magani, wannan shi ne mai lura" .
Imam Sadik (a.s) ya ce: "'Yan'uwa uku ne, da mai ba ka taimakon kansa, da wanda yake ba ka taimakon dukiyarsa, wadannan su ne 'yan'uwa na gaskiya. Sai kuma wanda yake karbar wani dan guzuri a hannunka, kuma yake bukatarka don wani jin dadi nasa, to wannan kada ka sanya shi cikin amintattu" .
Hanin 'Yan'uwantaka da Wasu
Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanada kake bukatuwa zuwa ga cudanyarsa ba dan'uwanka ba ne" .
Imam Ali (a.s) ya ce: "Kada ka yi abota da wanda yake boye darajojinka yake yada munananka" .
Imam Bakir (a.s) ya ce: "Tir da dan'uwan da yake kiyayewa da kai kana mai wadata, kuma yake yanke maka kana mai talauci" .
Imam Bakir (a.s) ya ce: "Kada ka yi abota ko 'yan'uwantaka da mutane hudu: wawa, da marowaci, da matsoraci, da makaryaci" .
Imam Sadik (a.s) ya ce: "Ka yi hattara da 'yan'uwantakar wanda yake son ka saboda kwadayi ko tsoro, ko karkata, ko ci da sha, ka nemi abota da masu tsoron Allah, koda kuwa a cikin duhun kasa ne, kuma koda kuwa zaka karar da rayuwarka wurin neman su" .
Kiyaye Dadaddiyar 'Yan'uwantaka
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Allah yana son dawwama a kan 'yan'uwantaka tsohuwa, sai ku dawwama a kanta" .
Imam Ali (a.s) ya ce: "Ka zabi sabo daga kowane abu, daga 'yan'uwantaka kuwa ka zabi dadaddiya" .
Gaskiyar 'Yan'uwantaka
Imam Ali (a.s) ya ce: "Hakika dan'uwanka na gaskiya shi ne wanda ya yafe maka kuskurenka, ya toshe aibinka, ya karbi uzurinka, ya rufa asirinka, ya kawar da tsoronka, ya kuma tabbatar maka da gurinka" .
Imam Ali (a.s) ya ce: "Dan'uwanka shi ne wanda ba ya barin ka yayin tsanani, kuma ba ya gafala ya bar ka yayin alkawari, kuma ba ya yaudararka yayin da ka tambaye shi" .
Zabar Dan'uwa
Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya nisanci dukkan 'yan'uwa a kan duk wani kuskure to abokansa zasu yi karanci" .
Imam Sadik (a.s) ya ce: "Wanda ba ya abota sai da maras aibi to abokansa zasu yi karanci kuwa" .
Jure Kaskancin Dan'uwa
Imam Ali (a.s) ya ce: "Jure wa kuskuren masoyinka na wani dan lokaci, kayar da makiyinka ne" .
Imam Ali (a.s) ya ce: "Juriya adon abota ce" .
Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda duk bai jure wa kuskuren aboki ba, to zai mutu shi kadai" .
Fiyayyen 'Yan'uwa
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Mafificin 'yan'uwan shi ne wanda ya taimaka maka a kan biyayya ga Allah, kuma ya hana ka sabonsa, ya umarce ka da yardarsa" .
Imam Ali (a.s) ya ce: "Mafificin 'yan'uwa shi ne mafi karancinsu kirkirar nasiha" .
Imam Ali (a.s) ya ce: "Mafificin 'yan'uwanka shi ne wanda ya taimaka maka, wanda ya fi shi kuwa shi ne wanda ya wadatar da kai, kuma idan ya bukace ka sai ya yafe maka" .
Imam Ali (a.s) ya ce: "Mafificin 'yan'uwa shi ne wanda soyayyarsa ta kasance saboda Allah ne" .
Imam Ali (a.s) ya ce: "Mafificin 'yan'uwanka shi ne wanda ya gaggauta zuwa ga alheri, kuma ya jawo ka zuwa gareshi, kuma ya umarce ka da aikata kyakkyawa, ya taimaka maka a kansa" .
Imam Ali (a.s) ya ce: "Mafificin 'yan'uwanka shi ne wanda ya yawaita fusata ka saboda gaskiya" .
Imam Ali (a.s) ya ce: "Mafificin 'yan'uwa shi ne wanda ba ya bukatar da 'yan'uwansa zuwa ga waninsa" .
Imam Sadik (a.s) ya ce: "Mafi soyuwar 'yan'uwana zuwa gareni shi ne wanda ya nuna mini aibobina" .
Mafi Sharrin 'Yan'uwa
Imam Ali (a.s) ya ce: "Mafi sharrin 'yan'uwa shi ne wanda aka dora wa kai nauyi saboda shi" .
An tambayi Imam Ali (a.s) game da cewa; wane aboki ne ya fi zama sharri? Sai ya ce: "Shi ne mai kawata maka sabon Allah" .
Zabar 'Yan'uwa
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Idan ka ga halaye uku daga dan'uwanka to ka kaunace shi, Kunya, da Rikon amana, da Gaskiya, amma idan ba ka gan su ba, to kada ka so shi" .
Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda duk ya riki dan'uwa bayan kyakkyawar jarrabawa to abotarsa zata dawwama, kuma sonsa zai karfafa, wanda kuwa ya riki dan'uwa ba tare da jarrabawa ba, to tilasa zata sanya shi abota da ashararai" .
Imam Sadik (a.s) ya ce: "Ku jarraba 'yan'uwanku da halaye biyu; idan suna da su, to sai ku yi abota da su, idan ba haka ba, to ku bar su, ku bar su, ku bar su: Kiyaye salloi a lokacinsu, da kyautata wa 'yan'uwa a cikin tsanani da sauki" .
Shiryar da 'Yan'uwa
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Mumini madubi ne ga dan'uwansa mumini, yana yi masa nasiha (adalci) idan ba ya nan, yana kuma kawar masa da abin da yake ki idan yana nan" .
Imam Ali (a.s) ya ce: "Wanda ya yi wa dan'uwansa wa'azi a boye hakika ya kawata shi, wanda kuwa ya yi masa a fili hakika ya aibata shi" .
Imam Sadik (a.s) ya ce: "Wanda ya ga dan'uwansa kan wani lamari da yake ki bai hana shi ba kuma yana da ikon hakan, to hakika ya ha'ince shi" .
Girmama 'Yan'uwa
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Babu wani bawa daga al'ummata da zai tausaya wa dan'uwansa a kan wani abu, sai Allah ya hore masa masu hidimar aljanna" .
Imam Sadik (a.s) ya ce: "Wanda duk dan'uwansa musulmi ya zo masa sai ya girmama shi, to hakika ya girmama Allah madaukaki ne" .
Biyan Bukatun 'Yan'uwa
Imam Ali (a.s) ya ce: "Kada waninku ya kallafa wa dan'uwansa nema a wurinsa idan ya san yana da bukata" .
Imam Sadik (a.s) ya ce: "Allah yana cikin taimakon mumini matukar muminin yana cikin taimakon dan'uwansa" .
Imam Sadik (a.s) ya ce: "Wanda ya biya wa dan'uwansa mumini wata bukata, to Allah zai biya masa bukatu dubu dari a ranar lahira" .
Imam Sadik (a.s) ya ce: "Lallai dogaron mutum da dan'uwansa ya isa, ya kawo masa bukatarsa" .
Ladabin 'Yan'uwantaka
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Idan dayanku ya yi abota da wani mutum ya tambaye shi sunansa, da sunan babansa, da kabilarsa, da gidansa, wannan duk yana daga cikin wajabcin gaskiya, da tsarkakar 'yan'uwantaka, idan kuwa ba haka ba, to abota ce ta wauta" .
Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Ka hadu da dan'uwanka da sakin fuska" .
Daga Biharul Anwar, Manzon Allah (s.a.w) ya kasance idan ya rasa wani mutum daga 'yan'uwansa har kwana uku ya kan tambaya game da shi, idan ba ya nan ne, sai ya yi masa addu'a, idan kuwa yana nan sai ya kai masa ziyara, idan kuwa marasa lafiya ne sai ya je ya gaishe shi .
Imam Ali (a.s) ya ce: Idan gyara ya mamaye zamani da mutanensa, sannan sai wani mutum ya munana zato ga wani mutum da babu wani kuskure da ya bayyana gareshi, to ya zalune shi! Amma idan barna ta mamaye zamani da mutanensa, sai wani mutum ya kyautata wa wani mutum zato, to ya yaudari kansa.
Imam Ali (a.s) ya ce: "Aboki ba ya zama aboki sai ya kiyaye abokinsa cikin abubuwa uku: Cikin bala'insa, da boyuwarsa, da mutuwarsa".
Imam Ali (a.s) ya ce: "Ka so masoyinka da sauki, tayiwu ya kasance makiyinka kwarai a wata rana, kuma ka ki makiyinka da sauki, ta yiwu ya kasance masoyinka kwarai wata rana".
Imam Ali (a.s) ya ce: "Da ina da wani dan'uwa aboki don Allah, kuma ya kasance karancin duniya a gunsa yana girmama shi a idanuwana, ya kasance ya fita daga ribacewar nan ta cikinsa, ba ya sha'awar abin da bai samu ba, kuma ba ya yawaita abin da ya samu, ya kasance mafi yawancin lokutansa mai shiru ne, idan kuwa ya yi magana, sai ya yi fice ga masu magana, ya kashe kishirwar masu tambaya, kuma ya kasance mafi yawan lokutansa shi mai rauni ne abin raunatawa! Idan kuwa yaki ya zo to shi ne zakin jeji, kuma macijin kwararo, ba ya kawo hujjarsa sai ya yanke dukkan wata hujja, kuma ya kasance ba ya zargin kowa kan abin da yake samun uzuri a irinsa har sai ya ji hanzarinsa, ya kasance ba ya kukan wani ciwo sai gun inda za a warkar das hi, ya kasance yana fadar abin da yake yi, ba ya fadar abin da ba ya yi, kuma ya kasance idan an yi galaba kansa kan yin magana, to ba a galaba kansa kan yin shiru, kuma ya kasance ya fi kwadayin ya ji fiye da ya yi magana, kuma idan wasu abubuwa biyu suka zo masa bagatatan, sai ya duba wanne ne ya fi kusa da son rai sai ya saba masa.
Na umarce ku da wadannan halaye ku lizimce su, ku yi rige a cikinsu, idan kuwa ba zaku iya ba, to ku sani yin kadan ya fi barin mai yawa".
281. Imam Ali (a.s) ya ce: "Ba don Allah ya yi alkawarin azaba ga saba masa ba, da bai kamata a saba masa ba, don godiya ga ni'imarsa".
Imam Ali (a.s) ya ce: "Kada ka yi abota da wawa, domin shi yana kawata maka aikinsa, kuma yana son ka kasance misalinsa".
Imam Ali (a.s) ya ce: "Masoyanka uku ne, makiyanka uku ne: Masoyanka: Masoyinka, da masoyin masoyinka, da makiyin makiyinka. Amma makiyanka su ne: Makiyinka, da makiyin masoyinka, da masoyin makiyinka".
Imam Ali (a.s) ya ce: -da wani mutum da ya gan shi yana kokarin taimakon wani makiyinsa da abin da zai cutar da shi: - "Kai dai kamar mai sukan kansa ne (da makami), domin ya kashe wanda ya goya".
Imam Ali (a.s) ya ce: "Jarraba ka ki". (Wato ka jarraba mutum kafin ka zama abokinsa ta yiwu ka ki shi saboda wani abu sai ka ki kulla abota da shi).
Akwai kuma mutanen da suke ruwaito wannan daga manzon Allah (s.a.w), sai dai abin da yake karfafa cewa daga maganar Imam Ali (a.s) ce, shi ne abin da Sa'alab ya ruwaito cewa: Ibnul A'arabi ya gaya mana ya ce: Ma'amun ya ce: Ba don Imam Ali (a.s) ya ce: "Jarraba ka ki" ba, da sai in ce: Ki ka jarraba.
Cibiyar Al'adun Musulunci
www.hikima.org
hfazah@yahoo.com
Hafiz Muhammad Sa'id
Thursday, June 22, 2011

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)