Muassasar alhasanain (a.s)

Amsar Wasikar Najashi

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

Da Sunan Allah Madaukaki
Wannan shi ne jawabin Amsar Wasikar Abdullah Najashi (gwamnan yankin Ahwaz) da Imam Ja'afar asSadik (a.s) ya ba shi, amsar tana kunshe da nasihohi da shiryarwa ga abin da ya kamata masu tafiyar da mulki da jagorancin al'umma su kasance a kansa.

Tambayar Najashi:
Allah ya tsawaita rayuwar shugabana (Imam Ja'afar Sadik)! Ya sanya ni fansa gareshi daga dukkan abin ki, kuma kada ya nuna mana wani mummunan abu (ya same shi) domin shi (Ubangiji Madaukaki) mai iya yin haka ne, mai iko a kan haka.
Ka sani ya shugabana cewa ni na samu kaina cikin (jarrabawar) cewa ni ne gwamnan Ahwaz, idan jagorana shugabana yana ganin ya shata mini iyaka, ya ba ni wasu dokoki da zan samu mafita, da hanyar da zata sanya ni zuwa ga kusancin ubangijina madaukaki da manzonsa, ya kuma ba ni abin da ya ke ganin zan yi aiki da shi a takaice, da abin da zan bayar, da inda zan bayar da dukiyata, kuma ga waye zan sarrafata? da waye zan samu nutsuwa, kuma wurin waye zan samu nutsuwa? da wa zan yarda? da wa zan aminta? da wanda zan dogara da shi a sirrina?, ta yiwu Allah ya ba ni mafita da shiryarwarka da kaunarka, domin kai ne hujjar Allah a kan halittarsa, kuma amintaccensa a kasarsa, Ni'imar Allah ta tabbata gareka.
(Sai Imam Ja'afar asSadik ya amsa masa da abin da yake kunshe da abin da yake kamata ga jagorori kamar haka):

Amsar Imam Ja'afar asSadik (a.s):
Da sunan Allah Madaukaki
Allah ya kare ka da ludufinsa, ya tausasa maka da baiwarsa, ya kare ka da kiyayewarsa, domin shi mai yin haka ne. Amma bayan haka: Wani dan sakonka ya zo mini da wasikarka sai na karanta, kuma na fahimci duk abin da ka ambata, kuma na tambaye shi game da shi, kuma ka ambaci cewa an jarrabe ka da jagorancin Ahwaz, sai wannan ya faranta mini rai kuma ya bata mini rai, kuma zan ba ka labarin abin da ya bata mini rai da abin da ya faranta mini rai in Allah madaukaki ya so.
"Amma farin cikina" da samun jagorancinka sai na ce; ta yiwu Allah ya taimaki wani mai neman taimako mai jin tsoro daga masoya alayen manzon Allah (s.a.w) ta hanyar ka, kuma ya daukaka kaskantaccensu da kai, ya tufatar da matsaraicinsu da kai, ya karfafi mai rauninsu da kai, ya kashe hurar wutar masu saba musu da kai.
"Amma abin da ya bata mini rai" da wannan; mafi karancin abin da nake jiye maka tsoro shi ne kada ka cutar da wani masoyinmu sai wannan ya hana ka jin kanshin aljanna.
Don haka ni zan takaita maka dukkan abin da ka nema, idan kai ka yi aiki da shi ba ka ketare shi ba, to ina kaunar ka samu kubuta in Allah ya so.
Ya kai Abdullah anNajashi! Babana ya ba ni labari daga iyayensa daga Ali (a.s) daga manzon Allah (s.a.w) cewa: Duk wanda dan'uwansa musulmi ya nemi ya ba shi shawara bai kyautata masa nasiha ba, to Allah zai cire masa hankalinsa. Ka sani kubutarka da tsiranka suna cikin kiyaye zubar da jini ne da kamewa ga barin cutarwa ga masoya Allah, da tausaya wa al'umma, da tausasawa, da kyautata rayuwa (da mutane), tare da tausasawa ba tare da kuma nuna rauni ba, da tsanantawa ba tare da sanya karfi ba, da sanin makamar rayuwa tare da jagoranka na sama da kai da wanda zai zo maka na daga 'yan sakonsa.
Ka tausaya wa al'ummarka ta hanyar tsayar da su kan abin da ya dace da gaskiya da adalci in Allah ya so. Ina hana ka masu annamimanci, (yi hattara) kada wani daga cikinsu ya zamar da kai (daga hanyar kwarai), kuma idan kana karbar maganganunsu to wuni da dare Allah ba zai karbi farillarka ko nafilarka ba, kuma sai Allah ya yi fushi da kai ya keta sirrinka (kariyarka).
Amma wanda zaka zauna da shi ka huta gunsa, ka mika lamarinka zuwa gareshi, to ya kasance shi ne mutumin da yake da imani, da sanin makamar aiki, da basira, amintacce, mai taimaka maka kan addininka.
Ka jarraba mataimakanka (kamar ministoci, kwamishinoni, ciyamomi, da manyan ma'aikata), ka jarraba jama'a nau'i biyu, idan ka ga akwai wata shiriya to sai ka rike su.
Ka yi hattara da bayar da wani dirhami (kudi) ko sanyar da tufafi (baiwar kyauta) ko dora wa kan wata dabba (bayar da kyautar mota), ga wani mawaki ko mai bayar da dariya da mai barkwanci da raha ba saboda Allah ba, (in kuwa ka bayar to kaffarar wannan shi ne) sai ka bayar da kwatankwacin wannan ga wani taimako saboda Allah.
Kyautarka da baiwarka (ta dukiyar da ka mallaka) ta kasance ne ga runduna, da 'yan sako (kamar masinjoji), da na kewaye da kai, da masu isar da sako (kamar malamai da marubuta) da masu kula da tsaro, da masu aikin kula da dukiyar kasa.
Kuma (kyautarka ta kasance ga) duk abin da kake so ka sarrafa shi a tafarkin ayyukan alheri da tsira (da ya hada) da sadaka da fidda kai, da hajji, da shayarwa (kamar gina rijiyoyi da gayara ruwan shan famfo), da tufafi da ake salla ko abin da ake salla a kansa, da kyautar da ake bayar da ita don Allah da manzonsa daga mafi kyawun kudinka.
Ya kai Abdullahi! Ka yi kokari kada ka taskace zinare da azurfa (kana mai yin rowa) sai ka kasance daga cikin mutanen nan da suke cikin wannan ayar mai cewa: "Wadanda suke taskace zinare da azurfa kuma ba sa ciyar da ita a tafarkin Allah".
Kada ka rena wani abu mai zaki, ko ragowar wani abinci da kake bayar da shi don kosar da wani ciki mai jin yunwa da kake kashe fushin Allah ubangijin talikai da shi (wannan kyautar). Ka sani na ji daga babana yana fadi daga iyayensa daga sarkin muminai Ali (a.s) cewa ya ji manzon Allah (s.a.w) wata rana ya gaya wa sahabbansa cewa:
"Duk wanda ya kwana mai koshi alhalin makocinsa na cikin yunwa to bai yi imani da Allah da ranar lahira ba". Sai muka ce ya ma'aikin Allah mun halaka ke nan. Sai ya ce: Ku bayar da ragowar abincinku, da ragowar dabinonku, da arzikinku, da (kyautata) halayenku (ga mutane), da (bayar da kyautar) tsohon tufafinku, (sai ku kasance) kuna masu kashe fushin Allah madaukaki da wannan.
Da sannu zan ba ka labarin wulakantuwar duniya da wulakantuwar daukakarta ga wadanda suka gabata na magabata da tabi'ai. Hakika babana muhmmad dan Ali dan Husain (a.s) ya ba ni labari cewa: Yayin da Husain (a.s) ya yi shirin zuwa Kufa, sai Ibn Abbas ya zo masa ya hada shi da Allah da zumunci cewa (yana jin tsoron) ya kasance shi ne wanda za a kashe a "Duff" -wato Karbala-. Sai ya ce masa: Ni na san makasata, kuma ba ni da wata manufa da duniya sai rabuwa da ita. Sannan sai imam Husain (a.s) ya yi masa bayanin zuhudun iyayensa na barin duniya, da kaucewarsu ga kyale-kyalinta da adonta.
Ya kai Abdullah! Na hana ka tsorata mumini, hakika babana ya ba ni labari daga iyayensa daga Ali (a.s) cewa: Duk wanda ya yi duba zuwa ga mumini don ya firgita da shi, to Allah zai firgita shi ranar kiyama ranar da babu wata inuwa sai inuwarsa, kuma zai tashe shi a kan surar kwayar zarra da kwantankwacin girman namanta da jininta ('yar kankanuwa). Kuma duk wanda ya biya bukatar dan'uwansa mumini to Allah zai biya masa bukatu masu yawa, daya daga cikinsu ita ce aljanna. Wanda kuwa ya tufatar da dan'uwansa mumini da riga (ya kare shi) daga tsaraicinsa, to Allah zai tufatar da shi sundusin aljanna da istabrak da alharirinta, kuma ba zai gushe ba yana kutsawa cikin yardar Allah matukar kuwa wannan tufafin akwai zare da ya rage ga wanda aka tufatar.
Wanda kuwa ya ciyar da dan'uwansa daga yunwa, to Allah zai ciyar da shi daga abincin dadin aljanna, wanda kuwa ya shayar da shi daga kishirwa, to Allah zai shayar da shi daga rahikul makhtum, wanda kuwa ya yi wa dan'auwan wata hidima, to Allah zai yi masa hidima daga yara masu dawwama, kuma ya zaunar da shi tare da masoyansa masu tsarki.
Wanda kuwa ya dora dan'uwansa a kan wani abin hawa to Allah zai dora shi kan taguwa daga taguwoyin aljanna, kuma ya yi wa mala'iku makusanta alfahari ranar alkiyama da shi. Wanda kuwa ya aurar da dan'uwansa matar da zai samu nutsuwa da ita don ya karfafi rayuwarsa ya samu hutu wurinta, to Allah zai aura masa matan aljanna, kuma ya debe masa kewa da zaman da wanda yake so na daga siddikai daga alayen gidan annabinsa (s.a.w), da 'yan'uwansa, kuma ya sanya musu nutsuwa da shi.
Wanda ya taimaki dan'uwansa musulmi kan wani sarki (jagora) azzalumi, to Allah zai taimake shi kan ketare siradi yayin da kafafuwa suke zamewa. Wanda ya ziyarci dan'uwansa a gidansa ba don wata bukata ba da yake da ita gunsa, to za a rubuta shi cikin masu ziyarar Allah, kuma Allah yana da hakkin ya girmama mai ziyararsa.
Ya kai Abdullah! Babana ya ba ni labari daga iyayensa daga Ali (a.s) cewa ya ji manzon Allah (s.a.w) yana cewa da sahabbansa wata rana cewa: Ya ku jama'ar mutane ku sani duk wanda ya yi imani da harshensa bai yi imani da zuciyarsa ba, to ba mumini ba ne, kada ku nemi bin tona sirrin mumini domin duk wanda ya nemi bin tona sirrin mumini to Allah zai bi tona nasa sirrin ranar kiyama, kuma ya kunyata shi (tun) a cikin gidansa.
Kuma babana ya ba ni labari daga iyayensa daga Ali (a.s) cewa ya ce: Allah madaukaki ya dauki alkawarin mumini (da dora wa mumini jarabawa mai tsanani cewa a wannan duniya) kada a gaskata shi a cikin maganarsa (da zai yi magana mutane ba sa karba saboda son ransu), kuma kada a yi masa adalci gun makiyinsa (da makiyinsa ya yi masa ba mai jin komai, amma da zai rama to babu mai yi masa adalci), kuma kada ya samu huce haushinsa sai da tozarta nasa kan (da zai kuwa rama abin da aka yi masa to sai ya samu tozartuwa da ba shi rashin gaskiya), domin dukkan mumini abin yi wa takunkumi ne (don mutane ba sa son fadin gaskiyarsa), wannan kuwa (ya kasance ne) saboda wani hadafi gajere (rayuwar duniya mai wahala ga mumini), da kuma hutu mai tsawo (rayuwar lahira mai dadi ga mumini), sai Allah ya dauki alkawarin mumini (da ya dora masa a duniya), wanda mafi sauki daga ciki ita ce wahalar da zai sha hannun mumini irinsa (mumini hatta gun dan'uwansa mumini zai samu bala'i da jarrabawa mai tsanani) da zai rika magana irin tasa (don tunaninsu da akidarsu iri daya ce, amma) yana zaluntarsa yana yi masa hassada, shedan yana halakar da shi (mumini macuci mahassadi), kuma (shedan) yana sanya masa kiyayyarsa, ga kuma (a gefe guda) wani shugaba (mai zalunci) yana bin duddugensa (don ya cutar da shi), ga kuma wani kafiri (shi ma) yana ganin halaccin zubar da jininsa a matsayin wani addini, yana halatta huruminsa a matsayin ganima (Kafiri a nan yana iya hada munafuki da maras addini musamman a wannan zamin da munafukan musulmi suke kashe musulmi da dukkan ma'abocin wani addinin, kamar yadda muka ga suna kai hari kan musulmi suna kuma kwace musu kantinan kasuwanci, wannan ya faru a Sakkwato da sauran wurare, da ma wasu kasashe kamar Bahrain) me ya rage wa mumini bayan wannan?! (wato mai wannan munanan ayyukan ba mumini ne ba ne, ba shi da wata alaka da imani)!.
Ya kai Abdullah! Babana daga iyayensa daga Ali (a.s) daga annabi (s.a.w) ya ce: Jibril (a.s) ya sauka sai ya ce: Ya kai Muhammad Allah yana isar da gaisuwa gareka kuma yana cewa na tsaga suna daga sunayena ga mumini, na ambace shi mumini, mumini daga gareni yake kuma ni daga gareshi nake, wanda ya wulakanta mumini to ya fuskanto ni ne da shelanta yaki.
Ya kai Abdullah! Babana ya ba ni labari daga iyayensa daga Ali (a.s) daga annabi (s.a.w) cewa wata rana ya ce: Kada ka yi jayayya da wani mutum har sai ka duba halayensa, idan halayensa na gari ne, to Allah madaukaki ba zai tozarta masoyinsa ba, amma idan halayensa munana ne, to munanan halayensa sun isar maka (duk wani abu da zaka yi masa), kuma da ka yi matukar kokari ka yi masa wani abu (mummuna) fiye da abin da munanan halayensa suka yi masa da ba zaka iya ba.
Ya kai Abdullah! Kuma babana ya ba ni labari daga iyayensa daga Ali (a.s) daga annabi (s.a.w) ya ce: Mafi karancin kafirci shi ne mutum ya ji wata magana daga dan'uwansa sai ya kiyaye ta yana son wata rana (ya yi amfani da ita) don ya tozarta shi, wadannan su ne wadanda ba su da wani rabo (a lahira).
Kuma Ya kai Abdullah! Babana ya ba ni labari daga iyayensa daga Ali (a.s) ya ce: Duk wanda ya fadi wata magana game da mumini da abin da idanuwansa suka gani, kuma kunnuwansa suka ji, (kuma ya zama) abin da yake muzanta shi (mumini ne) yake kuma rushe masa mutuncinsa, to wannan shi yana cikin wadanda Allah ya ce: "Wadannan da suke son alfahasha ta yadu ckin wadanda suka yi imani suna da azaba mai radadi".
Ya kai Abdullah! Kuma babana ya ba ni labari daga iyayensa daga Ali (a.s) cewa ya ce: Duk wanda ya kawo wani labari game da dan'uwansa mumini da nufin ya rusa mutuncinsa da aibata shi, to Allah zai yi masa dauri da kamu da kuskuransa ranar kiyama har sai ya samu mafita daga abin da ya fada, kuma ba zai iya samun wata mafita ba har abada daga wannan sabon (ke nan zai dawwwama a wuta), kuma wanda duk ya sanya wa wani dan'uwansa mumini farin ciki, to ya shigar da farin ciki ga alayen gidan annabinsa. Kuma wanda ya shigar da wani farin ciki ga alayen gidan annabinsa to hakika ya shigar da farin ciki ga manzon Allah (s.a.w) ne, kuma wanda ya faranta ran manzon Allah (s.a.w) to lallai ya faranta ran Allah, wanda kuwa ya faranta ran Allah, to Allah ya dauki alkawari ya shigar da shi aljannarsa.
Sannan ina yi maka wasiyya da tsoron Allah da zabar biyayyarsa da kuma yin riko da igiyarsa, domin duk wanda ya yi riko da igiyar Allah to hakika ya shiriya zuwa tafarki madaidaici mikakke, ka ji tsoron Allah kada ka zabi (fifita yardar) wani mutum a kan yardarsa da sonsa. Ka sani wannan wasiyyar Allah madaukaki ce ga halittarsa, kuma ba ya karbar wanin wannan garesu, kuma ba ya girmama waninta. Ka sani ba a dora wa halitta wani abu da ya fi nauyi ba a kansu fiye da tsoron Allah, kuma wannan ita ce wasiyyarmu Ahlul-baiti (a.s), idan ka samu damar kada ka samu wani abu na duniya da Allah zai titsiye ka a kansa to ka yi. (nan ne karshen wannan amsa ta Imam Ja'afar asSadik (a.s) zuwa ga Najashi gwamnan Ahwaz).
Yayin da amsar wasikar ta je wa Najashi sai ya ce: Wallahi! Na rantse da ubangijin da babu wani ubangiji sai shi, shugabana sayyidina ya yi gaskiya, kuma babu wanda zai yi amfani da wannan rubutun sai ya tsira.

Cibiyar Al'adun Musulunci
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Friday, June 03, 2011

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)