Muassasar alhasanain (a.s)

Adalcin Allah a Al'umma

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5


ADALCIN ALLAH A MAHANGAR AHLUL-BAITI
"Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi, kuma Mala'iku da ma'abuta ilmi sun shaida, Yana tsaye da adalci, babu abin bautawa sai Shi, Mabuwayi, Mai Hikima". (Surar Aali Imrana, 3: 18)
Adalci siffa ce, cikin siffofin Allah (S.W.T.). Muna iya ganin gurabun adalcinSa a dukkan bangarorin samammu, kamar fagen halitta da samarwa da fagen dabi'a da halittar mutum da dabba da tsiro, haka kuma muna ganin wannan adalcin cikin shari'a da dokokin Ubangiji.
Duk abin da muke ganin yana gudana a cikin wannan duniya da dukkan abin da yake wakana to adalcin Allah yana kewaye da shi, sai dai kafin adalcin Allah ya yi aiki, to rahamarsa ce take rigo, domin da adalcin Allah yana rigon rahamarsa, da mun samu azaba mai tsanani a wannan duniya da lahira.
Sai dai Allah yana yin rahama kafin ya yi adalci a cikin abin da ya shafi saba masa wanda bai shafi hakkin bayinsa ba, don haka sai ya jinkirta wa mutum ko zai tuba, idan ya ki tuba har ya je masa da wadannan laifuffukan sai ya rike shi da su. Amma idan bawa ya yi zalunci ga wani daga halittun Allah, to a nan sai ya nemi yafiya da neman afuwa wurin wanda ya zalunta, in ba haka ba to Allah zai rike shi da adalci kan hakan.
Akwai masu ganin cewa tun da rahamar Allah ta yalwaci komai don me ya sa zai yi riko da adalci ya azabtar da bayinsa, suna ganin cewa ai wannan azabtar da bayin ba zai amfane shi da komai ba. Sai na ce: yana da kyau mu san cewa kowane adalci na Allah madaukaki yana tare da hikima, domin Allah mai hikima ne kamar yadda yake mai adalci ne. Kuma muna iya duba wasu bayanai kamar haka:
1- Mutumin da ya saba umarnin Allah, ya ki furuci da annabawan da ya aiko masa tare da cewa ubangiji ya yi masa ni'imomin da ba zasu kirgu ba, amma shi kuma yana keta hurumin Allah da wannan baiwar da ya yi masa. Haka nan mutumin da ya ba shi dukiya amma sai ya ki fitar da zakka, sai talauci da fasadi da sace-sace suka addabi al'umma, sai aka rasa aminci a cikin al'umma saboda masu kudi ba su bayar da hakkin Allah, masu mulki ba su raba arzikin Allah kamar yadda ya saukar ba.
Da zaka tambayi mutum cewa; Bayan ka yi shekara sittin kana kasuwanci ka tara dukiyarka, kana son ka samu hutu yanzu domin ka amfana da ita bayan karfin ya fara karewa, sai kawai wani ya zo ya karbe ta lokaci guda, ya barka ziro kamar ba ka taba zuwa kasuwa ba! Wane hukunci kake ganin ya dace da shi? Wace amsa zaka bayar kan hakan!.
Idan da al'umma zata kasance babu wanda zai hukunta mai irin wannan aikin, shin wannan ba yana nufin a samu karancin aminci da zaman lafiya a cikin al'umma ba?! To haka nan ne idan Allah bai hukunta wanda suke keta hurumin dokokinsa ba, zai kasance ya bude kofar kowa ya yi abin da ya ga dama!!
2- Hikimar Allah ta hukunta cewa zai saka wa kowa da aikinsa bisa hikima, domin babu hikima ya daidaita mai kyautatawa da mai sabawa a hukunci daya! Kamar soja ne da ya yi yaki ya kare kasa daga sharrin makiyanta, ba yadda za a daidaita sakamakonsa da wanda yake barawo dan fashi da ya addabi al'umma ya hana ta zaman lafiya.
2- Hikimar Adalci: Ba zai yiwu a sanya masu kyautatawa da masu munanawa a matsayin madaidaita ba. A cikin wannan akwai karfafar mai munanawa ya ci gaba, da kashe gwiwar mai kyautatawa ya bar yin alheri. Don haka hikimar adalcin Allah shi ne ya ba wa kowa sakamakon abin da ya yi na alheri ko na sharri!.
3- Hikimar Rahamar Allah tana bayyana a adalcinsa, don haka rahamarsa ce ya azabtar da masu yin sharri, domin a cikin azabatar da su akwai rahama. Kamar 'yan fashi da barayi masu takura al'umma da masu fyade da 'yan zambo ne, sai kawai don kasancewar ana son su samu rahama sai a kyale su suna kashe mutane suna kwace musu dukiya, wannan kuwa shi ne azaba ainihinta!.
Don haka rahama shi ne daukar mataki kan wadancan kashi 1% don kashi 90% su samu rayuwa cikin yalwa da aminci. Wannan ne ma ya sanya fadin nan na Allah mai hikima cewa "Kuna da rayuwa cikin kisasi", Domin wanda ya san idan ya kashe wani mutum to shi ma za a kashe shi, sai ya kame hannunsa, mutane su amintu daga sharrinsa, sai ya kasance sun samu rayuwa!.
Adalcin Allah (s.w.t) bai takaita da tsakaninsa da bayi ba, adalcinsa ya mamaye komai, kuma yana cike da rahamarsa kamar yadda muka kawo. Don haka yana yin adalci tsakanin dabbobi a junansu, da tsakanin mutane, ko tsakanin mutane da dabbobi. Ruwaya ta zo cewa; Allah (s.w.t) ya azabtar da wata mata saboda tsare da mage da ta yi har ta mutu, ita ba ta saki mage ta yi kiwo ba, ita kuma ba ta kawo mata abinci ba .
Malam Najafi yana cewa: Kafin juyin musulunci a Iran an yi wani lokaci a birnin Kum da wasu samari suka daure wata mage da sarka a wani turke, sai suka cinna mata wuta bayan sun balbale ta da fetur. Da zafin wutar ya ratsa ta sai ta rika gudu tana kara tana tsalle, da zarar ta fita da gudu sai wannan sarkar ta dawo da ita, haka nan ta rika har ta mutu! Ya ce: Wani abin mamaki kwana biyu da yin haka sai ga sarki Sha ya zo gewaya wannan birnin, ba tare da wani dalili ba sai ya bayar da umarnin harbe wadannan samari biyu ba tare da ya san sun yi wa mage wannan izayar ba!.
Idan kuwa Allah zai sanya wata mata wutar jahannama saboda ta halaka mage daya, yaya tsammaninmu ga mutumin da yake sakin hayakin mota ko na babur yana halaka dubunnan mutane! Yaya muke tsammanin mutumin da yake zuba shara a hanya tana haifar da kwalara dubunnan mutane suna mutuwa a shekara! Yaya muke tsammanin irin azabar da zata fada wa shugaban da yake cinye dukiyar al'umma alhalin ga asibitoci babu kula da magani! Babu hanyoyi masu kyau sai ramuka da suke haddasa hadarin da yake sanadiyyar salwantar dubunnan rayuka! Babu cikakken ilimi da ake ba wa 'ya'yan talakawa! Babu cikakken tsaro da al'umma take samu! Idan ran mage daya yayi sanadiyyar shiga jahannama, to yaya wadannan rayukan na mutane!
Yaudarar kai ne idan mutane suka tsammanin zasu samu adalci wurin Allah alhalin sun ki yin adalci! Allah madaukaki yana umarni da adalci, da kyautatawa, don haka babu wani wanda zai saba wannan dokar tasa ya ki yin adalci sannan shi kuma ya samu ganin daidai. "Lalle Allah yana yin umurni da adalci da kyautatawa". (Surar Nahli, 16: 90)
Haka ma adalcin Ubangiji ya bayyana cikin abin da Yake hukumtawa da kaddarawa kan halittunSa na hukumci da kaddara, da cikin abin da Ya shar'anta na shari'u da sakonni. Kamar yadda yake bayyana a fagen lahira, ranar hisabi da sakamako. Zai sakantawa mai kyautatawa da kyautatawar, mai mummunan aiki kuwa da irin aikinsa.
"Kuma Ubangijinka ba Ya zaluntar kowa". (Surar Kahf, 18: 49)
"Sa'an nan kuma a cika wa kowane rai abin da ya sana'anta". (Surar Bakara, 2: 281)
"Allah ba Ya kallafawa rai face ikon yinsa, yana da ladan abin da ya aikata, kuma a kansa akwai zunubin abin da ya yi ta aikatawa...". (Surar Bakara, 2: 286)
Bisa wannan tsarin ne musulmin farko suka tafi wajen fahimtar alakarsu da Allah (S.W.T.) da fahimtar halayyar 'yan Adam da ayyukansu. Daga bisani sai falsafa ta shigo ga kuma ra'ayoyin ilmin tauhidi dukkansu masu sassabawa juna. Hakika wadannan sun tsirar da ra'ayoyi uku kan fassarar ayyukan mutane da alakarsu da iradar (nufi) Allah Madaukakin Sarki.
Wadannan ra'ayoyi kuwa su ne:
1. Jabru (Tilastawa).
2. Tafwidhu (Sakarwa).
3. Babu Jabru ballantana Tafwidhu.
Hakika wadansu kungiyoyi da mazhabobi sun yi mummunan fahimta ga zahirin wadansu ayoyin Kur'ani, kamar fadinSa (S.W.T.) cewa:
".
Zahirinsu ya sanya irin wannan kungiya suka yarda da Jabru. Abin da wannan ra'ayi yake nufi shi ne dan'Adam ba ya mallakar nufi kuma ba shi da zabi, shi ba kome ba ne face bigire da gurin saukar kaddararrun abubuwa daga Allah (S.W.T.). A bisa wannan ra'ayi, mutum abin tilastawa ne, ba shi da wani zabi cikin al'amurransa. Masu irin wannan ra'ayi ana kiransu da sunan Mujabbira.
Ra'ayi na biyu kuwa shi ne mai cewa an sakar wa dan'Adam ikon zabi wajen ayyukansa, da kuma nufinsa babu nufin Allah a cikin ayyukansa. Kai suna ganin ma cewa Allah ba Ya iya hana mutum yin abin da ya yi nufin yi ko sabo ne kamar kisan kai, zalunci, shan giya, ko kuwa ayyukan biyayya ne kamar su adalci, kyautatawa, salla da dai sauransu. To da wannan, dan'Adam yana da 'yanci ga barin Allah (S.W.T.), wannan kuwa shi ne ra'ayin Mu'utalizawa.
To Imaman Ahlul-baiti (a.s) sun yi raddi wa wadannan ra'ayoyi guda biyu, sun nuna bacinsu gaba daya. Kowanne daga ra'ayoyin nan biyu sun saba da abin da Kur'ani ya zo da shi, akidar tauhidi kuwa ta kafu kan tushensa ne. su Imamai (a.s.) sun fayyace mana cewa akwai bayyananniyar alaka tsakanin irin yadda ake fahimtar halayyar mutum da imani da adalcin Allah. Suka ce lallai abin da ra'ayin cewa mutum ba ya mallakar wani nufi ko zabi sai dai shi abin tilastawa ne kurum, yana janyo tuhumtar Mahalicci Mai girma da Daukaka da zalunci da kore adalci daga gare Shi, lallai kuwa Ya girmama daga hakan. Saboda ma'anar wannan shi ne Allah Ya tilastawa mutum aikata sharri sannan kuma Ya yi masa ukuba dominsa, haka nan Ya tilasta masa aikata alheri sannan kuma Ya hana shi ladansa. Domin haka ne Imamai (a.s.) suka kakkabe wannan
mumunan fassara wanda da yawan musulmi suka fada ciki a dalilin gurguwar fahimtar da suka yi wa zahirin wadansu ayoyi kamar cewa:
"Yana batar da wanda Ya so, Yana kuma shiryar da wanda Ya so".
Imaman Ahlul-baiti (a.s) sun yi wa matsalolin shiryarwa da batarwa tafsiri bayyananne mai dacewa da adalcin Allah (S.W.T.). Bayanin wannan yana tafe.
Haka nan kuma Imamai (a.s.) sun yi watsi da ra'ayin masu cewa an sakarwa mutum akala sai yadda ya ga dama zai yi, ba tare da Allah Yana iya hana shi ba. Sun bayyana cewa wannan ra'ayi karkatacce da cewa tuhumar Allah ne da rashin cikakken iko kan bayinSa da gajiyawarSa kan hakan. Alhali kuwa Allah (S.W.T.) Mai cikakken iko ne, kuma Mamallakin dukkan halittunSa.
Imamai (a.s.) suna da matsaya matsakaiciya dangane da al'amarin da ya shafi adalcin Ubangiji. Wannan matsaya tana kore Tilastawa da Sakarwa, tana cewa: (Nufin mutum baya iya rabuwa da nufin Allah). Sun bayyana wannan alakar da take tsakanin nufin mutum da nufin Ubangiji bayani cikakke a akidance. Nan gaba za mu kawo ruwayoyinsu masu nuna wannan ra'ayi.
Kafin mu kawo wadannan ruwayoyi, bari mu yi dan sharhi kan batutuwan da mazhabar Ahlul-baiti (a.s) suka bambanta da masu ra'ayoyi kan mas'alar adalcin Allah, bisa abubuwa guda uku na asasi:
Dan'Adam yana da nufi da ikon zabin duk aikin da zai yi, ko na alheri ko na sharri, haka kuma kin aikata shi. Mutum yana iya kisan kai ko sata ko zalunci ko karya, da wannan nufin da ikon da yake da shi. Haka kuma yana da daman tsai da adalci da aikata aikin kwarai da yin salla da barin haramtattun abubuwa, da wannan nufi nasa da iko.
Hakika Allah (S.W.T.) Yana da ikon hana mutum kowane aiki, kamar yadda yake da ikon sanya mutum aikata kowane aiki ba tare da zabin mutum ya sami tasiri ba. Sai dai Allah ba Ya tilastawa kowa aikata alheri ko sharri.
Amma Shi Allah, domin tausayinSa da jin kanSa, Yana shiga tsakanin bawan da ya cancanci taimakonSa wajen aikata mummunan aiki, domin jin kai. Haka ma Yana taimaka masa wajen aikata alheri idan ya cancanci taimakon.
1. Wani abin da yake da dangantaka da adalcin Ubangiji kuma shi ne: Allah Yana sakantawa kowane mutum ranar kiyama da abin da ya aikata, alheri ko sharri. Sai dai kuma wata kungiyar ta musulmi tana ganin cewa mai yiyuwa ne Allah Ya shigar da mai kyautata aiki cikin wuta, mai mummunan aiki kuma aljanna, suna kuma dogara ne, bisa kuskure da mummunan fahimta, kan wannan aya mai girma: "Ba a tambayarSa ga abin da Yake aikatawa, alhali kuwa su ana tambayarsu". (Surar Anbiya, 21: 23)
Wasu jama'a daga cikin musulmi sun dogara da wannan ayar ne bisa tafsiri na kuskure, suka ce ba ya wajaba kan Allah (S.W.T.) Ya cika alkawarin sakayya da Ya yi a ranar kiyama. Imaman Ahlul-baiti (a.s) sun mai da martani kan wannan zance da cewa, wannan ya sabawa gaskiyar Allah Madaukaki da adalcinSa.
Wancan ra'ayin yana daidaita mai kyautatawa da mai mummunan aiki, hakan kuwa yana rusa kimar kallafawa bayi da kuma sanya shari'a. Ingantaccen zance dai shi ne babu wani aikin da ba shi da sakamako, ko kuma mai daukar laifin yinsa, kamar yadda aya ta ce:
"To wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai ganshi. Kuma Wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi". (Surar Zalzala, 99: 7-8)
2. Ra'ayoyin sashin musulmi sun tafi a kan cewar ya dace ga Allah (S.W.T.) Ya kallafawa bayi abin da yafi karfinsu, wannan kuwa sun fade shi ne domin dogara kan fahimta ta kuskure da suka yi wa wannan aya mai girma:
"Ya Ubangijinmu Kada Ka sanya mu daukar abin da babu iko gare mu da shi". (Surar Bakara, 2: 286)
Imaman Ahlul-baiti (a.s) sun kore wannan fahimta suna masu bayanin cewa ta saba da adalcin Allah da kuma bayyanannen fadi na Kur'ani mai girma, cewa:
"Allah ba Ya kallafa wa rai face abin da zai iya dauka". (Surar Bakara, 2: 286)
To yanzu za mu kawo sashen ruwayoyi da tattaunawar Ahlul-baiti (a.s), masu mana sharhin wadannan ginshikai na asali da fassara halayyar mutum da alakar da ke akwai tsakanin nufin mutum da ta Allah (S.W.T.). Wadannan ruwayoyi suna kulla tafsiri da sharhin halay-yar mutum da tushen adalcin Allah domin su karfafa mana dayantaka (ta Ubangiji) fahimta da tunani da kuma i'itikadi cikin sakon Musulunci. A lokaci guda sun bata ra'ayin Jabru da Tafwidhu da ma dukkan sauran tunace-tunace da kirdado wadanda suka fice daga tafarkin Kur'ani.
Imam Sadik (a.s.) ya ce:
"Allah Ya halicci halittu Ya kuma san makomarsu. Ya umarce su (da ayyukan biyayya) Ya hane su (ayyukan sabo). Kuma bai umarce su da abu ba face Ya sanya musu hanyar barin abin. Ba su zamowa masu riko (da umarnin) ko masu bari face da izinin Allah( )".
Yayin da Imam Ali bn Abi Dalib (a.s.) ya tafi kasar Sham (Syria), domin yakar Mu'awiyya a Siffin, wani daga sahabbansa ya tambaye shi cewa:
"Ya Amirul Muminina! Ka ba mu labarin wannan tafiya tamu, shin da hukumcin Allah ne ko da kaddararSa?" sai ya amsa masa da cewa: "Saurara dattijo, na rantse da Allah ba kwa hawan wani tudu ko ku gangara cikin wani kwari face bisa hukumcin Allah da kaddararSa".Sai Dattijon ya ce: 'Ga Allah nake neman ladar wahalata, Ya Amirul Muminina'. Sai Imam Ali (a.s.) ya ce da shi:"Kaiconka! Ta yiyu kana zaton hukumci lizimtacce da kaddara yankakkiya! Da haka al'amarin yake da sakamako da horo sun baci, kuma da alkawari da narko sun warware. Allah (S.W.T.) Ya umarci bayinSa bisa zabinsu, Ya hana su domin gargadi, Ya kallafa musu sassauka bai kallafa musu mai tsanani ba, Yana biyan kadan da mai yawa. Ba a saba masa domin rinjaya, ba a tilastawa don a yi maSa biyayya. Bai aiko Annabawa don wasa ba, kuma bai sauko da Littafi wa bayi haka a banza ba. Bai kuwa halicci sammai da kasa da abin da yake tsakaninsu a banza ba; "Wannan shi ne zaton wadanda suka kafirta. To, bone ya tabbata ga wadanda suka kafirta daga wuta( )".
An ruwaito daga Imam Ali bn Musa al-Ridha (a.s.) cewa an ambaci Jabru da Tafwidhu a gabansa, sai ya ce: "Shin ba zan sanar da ku wata ka'idar da ba za ku sassaba a cikinta, kuma duk wanda ya yi jayayya da ku sai kun rinjaye shi ba?Sai muka ce: 'E, a sanar da mu', sai ya ce:"Allah Mai Girma da Daukaka ba a biyayya gare Shi domin tilastawa, ba a saba masa don rinjaya, ba ya sake da bayinSa cikin mulkinSa. Shi ne Mamallakin abin da Ya mallakar masu, Mai iko kan abin da Ya ba su ikonSa. Idan bayinSa sun yi biyayya gare Shi, ba zai tare ko Ya hana su ba. Idan kuwa suka zabi su saba masa, in Ya ga damar tare su sai Ya yi, idan kuwa bai tare su ba suka aikata sabon, to ba kuwa Shi Ya jefa su ciki ba". Daga nan sai ya ce: "Wanda duk ya kiyaye wannan maganar, to lallai zai rinjayi mai sabawa da shi( )".
A cikin littafin Sharh al-Aka'id na Shaikh Mufid an ce:
"An ruwaito daga Abul Hasan na Uku (a.s.) yayin da aka tambaye shi batun ayyukan bayi; shin halittattu ne daga Allah Madaukaki? Sai ya amsa da cewa: "Da Shi Ya halitta su da bai barranta da su ba, alhali Yana cewa: 'Lalle ne Allah Barrantacce ne daga masu shirka'. Barrantan nan ba ta shafar zatinsu, Ya dai barranta ne daga shirkarsu da munanan ayyukansu( )".
A cikin littafin Kitabul Tauhid na Muhammad bn Ajlan, ya ce: "Na tambayi Abu Abdullah (a.s.) cewa: 'Shin Allah Ya sakar wa bayi al'amarinsu ne?', sai ya ce: "Karimcin Allah ya wuce gaban Ya saki al'amurransu gare su", sai nace: 'To kenan Allah Ya tilasta wa bayi aikata ayyukansu kenan?, sai ya ce: "Adalcin Allah Ya wuce gaban tilastawa bawa yin wani aiki sannan kuma Ya azabta shi a kan wannan aiki( )".
A ruwaito cikin Uyunul Akhbar al-Ridha (a.s.) wajen fadar Allah Madaukaki cewa:
"Kuma Ya (Allah) bar su a cikin duffai, ba su gani". (Surar Bakara, 2: 17)
Abu Abdullah (a.s.) ya ce:
"Ba a siffanta Allah da bari kamar yadda ake siffanta halittunSa, sai dai yayin da Ya san cewa ba su dawowa ga barin kafirci da bata ba, sai Ya hana su taimako da ludufi (tausayi), Ya bar su da zabinsu( )".
Har ila yau ya zo cikin wannan littafin wajen tafsirin Imam Ridha (a.s.) kan fadin Allah (S.W.T.) cewa: "Allah Ya sa rufi a kan zukatansu".
Sai ya ce: "Abin da ake nufi da 'Khatam' shi ne 'al-Dab'u' watau rufi a kan zukatan kafirai domin yi musu ukuba kan kafircinsu, kamar yadda Allah (S.W.T.) ya ce:
"A'a Allah ne Ya rufe a kansu (zukatansu) saboda kafircinsu, saboda haka ba za su yi imani ba face kadan( )". (Surar Nisa', 4: 155)
To haka ne tafarkin Ahlul-baiti (a.s) yake fayyace manufar shiriya da bata da kuma cewa Allah (S.W.T.) bai halicci mutane suna batattu ko shiryayyu ba. Sai dai Ya bar musu zabi, Ya ba su nufi, Ya kuma bayyana musu hanyar alheri tare da gargadi kan hanyar sharri da halaka, Allah Madaukaki Yana cewa:
"Lalle ne Mu, Mun shiryar da shi (mutum) ga hanyar kwarai, ko ya zama mai godiya, ko kuma ya zama mai kafirci". (Surar Insan, 76: 3)
Kuma Yana cewa:
"Kuma Muka shiryar da shi ga hanyoyi biyu". (Surar Balad, 90: 10)
Watau Mun sanar da shi hanyar alheri da ta sharri, zabi kuma na gare shi.
Manzon Allah (s.a.w.a.) ya fassara ayar da cewa:
"Su dai hanyoyi ne guda biyu, hanyar alheri da hanyar sharri. Kada hanyar sharri ta fi soyuwa gare ku bisa hanyar alheri( )".
Tafarkin Ahlul-baiti (a.s) ya zabi ra'ayi tsarkakakke na bayani kan halayyar dan'Adam na alheri ko sharri, da wata ka'ida:
"Babu Jabru ba tafwidhu, sai dai al'amari ne tsakanin al'amurra biyu, watau mataki tsakanin matakai biyu".
Yayin da aka tambayi daya daga cikin Imaman Ahlul-baiti (a.s), shin akwai wani mataki tsakanin tilasta-wa (jabru) da sajarwa (tafwidh)? Sai ya amsa da cewa:
"Abin da yake tsakaninsu ya kai fadin tsakanin sama da kasa".
Wannan shi ne takaitaccen bayanin tafarkin Ahlul-baiti (a.s) kan batun Jabru da Tafwidh, haka ne kuma akidar musulmin da suka yi koyi da tafarkinsu take.

Hafiz Muhammad Sa'id
Cibiyar Haidar don Yada Musulunci
www.hikima.org
hfazah@yahoo.com
Sunday, November 20, 2011

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)