Muassasar alhasanain (a.s)

Safarar Hajji

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5


Wasu Nasihohi Kafin Safarar Hajji
Na farko: mas'alar gyara salla da zai sanya kowa ya tafi wurin malami ya yi salla domin ta yiwu wani yana da shekaru yana yin salla amma sallarsa tana da matasla, kuma ba fata ake yi ba idan sallarsa ta kasance ba daidai ba. Domin a ayyukan hajji da uamara muna da salloli uku ne, daya ita ce ta umarar tamattu'I, ta biyu ita ce ta dawafin ahhjin tamattu'I, ta uku ita ce ta sallar dawafin mata. Duk da ko da yaushe dole ne salla ta kasace ta yi daidai sai dai tana da muhimmacni matuka a wadannan ayyyukan, kuma wani lokci tana da matsala, don haka ne ole ne kowa musamman wanda yak eniyyar tafiya hajji ya je wurin malami ya yi salla domin ya gani idan akwai matasla sai ya gyara masa, ya yi kokri ya gyara ta daidai domin ayyukansa wadanna su ma su yi daidai.
1. Na biyu: Dole ne kudin da ake kashewa domn zuwa hajji dole ne su kasance na halla; tufafin harami, kudin yanka, da sauran kudaden da yake kashewa kada suka kasacne akwai hakkin wasu a ciki.
Dukiyoyin da ba a bayar da zakkarsu ba, da dukiyoyin da ba a bayar da humusinsu ba, da sauran hakkokin mutane da ba a bayar ba. Haka nan wadanda ba su lissafa dukoyar mutane ba sun bayar to lallai ne kafin tafiya hajji su yi wannan aiki, su koma su duba lissafin dukiyarsu, idan akwai wani bashi a kansu sai su biya domin idan ba ma zasu iya biya ba a wannan lokcin, to sai su sake karbar a daga musu lokaicn biya, domn su iya zuwa haji su yi aikinsu da samun nutsuwar zuciyar, sannan daga bayan idan sun dawo sai su biya bashinsu.
2. Na uku: Neman yafiya; muna son mun je wurin da muke son Allah ya kasance ya yarda da mu, kuma ya yafe mana dukkan zunubanmu, don haka mu ma a nan sai mu nemi wasu su yafe mana laifuffukanmu da muka yi musu, kuma bayan haka mu ma mu yafe wa mutune duk wani lafini da suka yi mana, mu yi musu afuwa, don mu ma Allah ya yi mana afuwa, kuma kafin tafiya yana da kyau mu buga waya ko 'ina mu je wurin mutane mu nemi afuwarsu, sannan sai mu yi tafiya.
3. Yin wasiyya. Yin wasiyya yana daga mustahaban yin tafiya, sai dai a safarar haji mustahabbi ne mai karfi, kuma a ko da yaushe a safara ana son yin wasiyya sai da a wannna sarfarar ta hajji an fi karffawa da kwadaitarwa ga samun lada mai yawa. Ya zo a wata ruwaya cewa: "Ba kamata bag a mutum musulmi ya kwana, sai dai wasiyyarsa tana karkashin matashinsa".
Rubutun wasiyya ba wani wahala ne da shi ba, ya wadatar mutum ya rubuta kamar haka cewa: Da sunan Allah mai rahama mai jin kai. Ni wane dan wane na yi wasiyya da abu kaza, kan abu kaza: Ba ni da sallar ramuwa, ko kuma idan ina da adadi kaza na sallar ramuwa. Ba ni da azumin ramuwa, ko kuma ina da adadi kaza na azumin ramuwa. Ina da bashi a kaina na kudi kaza da humusi kaza a kaina.
Haka zai rubuta duk wani abu da yake kansa, da abin da yake nasa ne, har zuwa karshen wasiyya, sannan sai yayin tafiya kuma a fara da yin sadaka da yin addu'a. Da akawai addu'in safara da surorin da ake karantawa da suka zo kan haka, kamar surar Nas, Tauhid, Kadari, Ayautl Kursiyyu, da sauran addu'o'I.
4. Sannan kafin tafiya idan akwai dama wannan ma wata nasiha ce, idan zamu iya sai mu yi mutala'ar littafin ayyukan hajji da hukunce-hukuncensa, sai kuma wurare da kayan tarihin makka da madina, sannan sai kuma sirrorin wadannan ayyukan hajji. Kuma kowanne daga wadannan abubuwa uku an rubuta littafi a kansa, sannan kuma akwai kayan sauti na sididdika da kasitoci kan hakan. Iyakacin lokacin da aka samu sai a yi amfani da wannan damar don dubawa in Allah ya so, sai a samu yin tafiya da masaniya sosai. Sai a fara yin shiri a hankali har sai an samun yin tafiya, amma ina? Madina ma tana da nata hukunce-hukunce da mas'aloli da zamu kawo su a nan gaba in Allah ya so.
Aminci ya tabbata gareku da rahamar Allah da albarkarsa
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Saturday, December 24, 2011

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)