Muassasar alhasanain (a.s)

Ziyarar Madina

2 Ra'ayoyi 02.0 / 5


Ziyarar Garin Madina
1. Da sunan Allah mai Rahama mai Jin Kai
Darasi Na Biyu: Ziyarar Garin Madina Da Mas'aloli Da Hukunce-Hukuncen Da Suka Shafi Haka
Wurare Masu Tsarki
Mun zo madina mai haske, kuma da nufin Allah in alah ya so bayan wasu 'yan kawanaki zamu tafi mikata don fara yin ayukan umarar tamattu'i.
Kusan dukkan wadanda suka zo yin aikin Allah a makka suna zuwa madina na wasu 'yan kwanaki da zasu yi a can, ko dai kafin yin ayyukan hajji, ko bayan yin ayyukan hajji, wadanda suke farawa da madina kafin yin ayyukan hajji ana ce musu masu "'yan Madina kafin hajji", wadanda kuma suke zuwa madina bayan ayyukan hajji su ana ce musu "'yan madina bayan hajji". A 'yan kwanakin da muke zama a madina ba mu da wani abu na aikin wajibi da ya shafi umara ko aikin hajji. Wadannan ayyukan suna farawa ne bayan mun kama hanyar zuwa mikati, mun yi haram ada aikin umara ko hajji, amma a muddara zama madiha mai haske muna da dama mai yawa na ziyara da karatun kur'ani, da addu'a, da salla a masallacin madina, haka nan ma idan kafin mu yi ayyukan hajji muka zo madkia to muna da dama sosai na yin ayyukan umara da hajji, wato muna da damar sanin wadannan ayyukan sosai da za a rika yi ana koyar da yadda ake yin ayyukan a zama daban-daban, kuma da haka ne mutane zasu san ayyukan sosai in Allah ya so, har su sami tafiya mikati su fara ayyukan.
2. amma wuraren ziyara a madina suan da yawa, kuma zai iya yiwuwa mai matukar gaske, zamu iya cewa duk garin madina gaba daya wurin ziyara ne, sai dai babban wuri duka shi ne haramin manzon Allah (s.a.w), sannan sai bakiyya, sai kabarin shahidan uhudu na makabatar shahidan uhudu.
3. Mai ziyara a wannan lokaci muna da damar yin ziyara annabi (s.a.w) da imamai masu dara tsarkaka (a.s) da suka hada da Imam Hasan, da Imam Sajjad, da Imam Bakir, da Imam Sadik (a.s) wadanda aka binne su a bakiyya. Bayan haka akwai kabarin sayyida zahara (a.s) wanda yake ba a san inda yake ba, a madina yake ko bakiyya, sannan bayan kaburburan ma'asumai guda hudu, akwai kuma kaburburan 'ya'yan imamai da sahabbai da tabi'ai da aka binne su a nan, kuma masu ziyara dukkansu suna shagaltuwa da wadannan ziyarori a wasu lokutan.
Wani lokaci a ziyarar wurare masu yawa a cikin madina masu ziyara suna kebantar rana guda domin ziyarar Uhudu, wato shahidan uhudu da kabarin sayyidina Hamza jagoran shahidai ammin manzon Allah (s.a.w) wanda aka binne shi a wannan wurin uhudu da yakin uhudu ya wakana.

Masallatan Madina
4. amma masallatan madina suna da yawa matuka kuma da yawa suna da tarihi da ya safhi lokacin annabi (s.a.w) ko wani abu da ya faru a wurin ko manzon Allah ya yi wata tsayuwa a wurin ko kuma ya yi salla a wurin sai musulmi don su tuna da wadannan abubuwan da suka faru da tunawa da manozn Allah (s.a.w) da koyi da shi sai suak yi masallataria wurin don su rika yin salla. Wanda daya daga cikin mafi girman su shi ne masallacin annabi (s.a.w) wanda yake shi ne mafi darajar masallatan madina ta fuskatsin tsarkaka da daraj wanda ruwayoyi suka zo kan hakan game da shi: Salla a sallacin annabi yana daidia da salla dubu goma, wato ladan wannan sallar a masallacin annabi (s.a.w) da darajarta ya kai ladan salla dubu goma.
5. Akwai albishir ga masu yin ziyara da suek cikin wannan garin na annabi suan yin sallolin wajibinsu da sallolin ramuwarsu da na mustahabbi a masallacin annabi (s.a.w). masu ziyara su sani wasu ayyukan nasu da wasu lokauta nasu suan yin su a msallacin annabi ne, suna masu shagaltuwa da ibadar Allah da addu'a da karatun kur'ani mai daraja.
6. Wani masallacin na madina shi ne masallacin Kuba, wannan ma akwai falalr yin salla a cikiknsa, zamu iya cewa ya fi sauran masallatai daraja da fallaa bayan maslalacin annabi (s.a.w). Ya zo a wasu ruwayoyi cewa; idan mutum ya tsarki ya tafi masallacin kubba ya yi salla, to yana da ladan umara mufrada.
Akwai wasu masallatan ma da mai ziyara zai tafi ya yi salla kamar masallacin kiblatain ko ma'abocin alkibloli biyu; wannan masallacin shi ne wurin da manzon Allah (s.a.w) ya yi salla zuwa ga alkibloli biyu a wurinsa, wato bangaren masallacin aksa, da kuma masallacin ka'aba.
7. msallacin Khandak, da masallacin fatahu, wannan shi ne wurin da rundunar musulmi suka tsaya a yakin khanda suak gina wannan rami, wanda yake a wurin akwai masallcin da aka sani da masallacin budi, wanda shi ne mafi shahararsu mafi muhimmancinsu. Sannan daga masallatan madin aakwai masallacin gamama wurin sallar annabi (s.a.w), wanda ya yi sallar idi a wurin, masalaci an gian shi ne da sunan gamama wanda wake yamma da masallacin annabi (s.a.w) , kuam ba shi da wani nisa da masallacin annabi (s.a.w) a yau. Sannan akwai masallacin Imam Ali (a.s) wanda yake kusa da masallacin gamama. Sannan akwai masallacin amsa addu'a ko kuma an sani shi da masallacin mubahala. Da kuma masallacin Abuzar da sauran masallatai da suke garin madina.

Hukunce-Hukuncne Da Suka Shafin Madina
8. amma akwai wasu ayyuka da suak shafi garin madina musamman wasu 'yan kwanaki da mai ziyara zai yi a wannan garin, wadanda suak shafi mas'aloli game da salla, da kuma wadanda suka shafi mas'aloli game da azumi da zamu kawo muku su a nan.

Salla
Mas'alar farko ita ce salla da zamu kawo a nan, da farko masu ziyara suan tambaya cewa shin zasu yi salla raka'a hudu ne wato su cika salla ko kuma zasu yi kasaru ne? amsar wannan zamu iya cewa idan mai ziyara yana nufin zma kwana goma ko sama da haka a madin ane ta yadda zai zauna kwanaki goma ko kuma sama da haka, to dole ne ya cika salla, wato ya yi sallarsa raka'a hudu. Amma idan ya san cewa bai kai kwana goma ba, kamar zai yi sati daya, ko kwanaki shida ko takwas, a nan ya zama matafiyi, sallarsa kasaru ce. Sai dai a bisa fatawar jagoran juyin musulunci na iran sayyid khamna'I (d.z), a dukkan fadin garin madina da kuma garin makka ko da kuwa matafiyi ba zai yi kanaki goma ba, to yana iya yin sallarsa raka'a hudu ya cika, ko kuma ya yi raka'a biyu ya yi kasaru duk babu wata matsala.
Wato idan matafiya yana makka ko madina a bisa wannan yanayin yana da zabi ko ya cika ko ya yi kasaru; wato ya yi sallarsa raka'a hudu ko biyu, duk zai iya yin hakan; hatta a bangarorin da suke sababbi ne, wato wuraren da ake ginawa wadanda ake kirga su a matsayin wani bangare na garin madina. Misali idan wurin da kuke zama yana da nisa da masallacin annabi (s.a.w) amma kuma ana ganin sa a matsayin wani bangare na garin to a nan ma kuna iya yin salla raka'a hudu ku cika, ko kuma ku yi kasaru raka'a biyu.
9. Wata mas'alar kuwa ta shafi tarayya a sallar jam'I ce wacce a ganin sayyid khamna'I yin tarayya a sallar jam'I yana da lada mai yawan gaske, kuma ana yi wa masu ziyara nasihar su rika halartar sallar jam'I suna musharaka. Kuma a lokutan salla hatta da kuwan lokacin sallar lokacin da mutan suke tafiya zuwa ga masallacin annabi da sauran masallatai don yin salla to kada su fito daga masallaci, kada su rika tafiya akasin motsin da musulmi suke yi zuwa ga yin sallar jami, sannan kada su kasance ana yin salla suna kallon sallar jam'I ba tare da sun kasance sun yi tarayya a ciki ba su ma.
Wani bahasin kuam shi ne na yadda ake yin salla a nan; wato lokacin da zasu yi tarayya da salla da sauran 'yan sunna, ana kawo tambayoyi game da yadda ake yin sallar wanda shi ma zamu kawo bayani kan hakan. Yanzu mas'alar farko ita ce wacce ta shafi lokacin salla.
10. Kiran sallar da ake yi a lokutan salla; misali kiran sallar asuba da kiran sallar azhar duk da cewa da asuba akwai kiran salla da ake yi kafin kiran sallar asuba, wato kafin bullowar alfijir domin yin sallar dare, wannan kafin lokaci ne, wato kafin lokacin sallar asuba ne.
Amma kiran da ake yi wanda bayan yin sa da mintina goma ko kwata ko ma sama da hanak sai a yi ikama a yi salla, wanna lokacin kiran sallar asuba ne kuma ya yi daidai, kuma ba shi da bambanci da lokacin kiran salla a mahangar malamanmu. Haka nan ma lokacin sallar azahar wanda yake a farkon lokacin sallar azahar ne. Amma game da kiran sallar magariba, tun da lokacin faduwar rana suke yin kiran salla, kuma har yanzu lokacin magariba na shari'a bai yi ba, sai dai sau da yawa zuwa lokacin da zasu yi ikama su yi sallar jam'ai maganri ba takan yi. Ko da yake wani lokaci zai iya yiwuwa da gaggawa suka yi lokacin salla bai yi ba, to a nan idan mutum yana son ya yi salla dole ne ya samu tabbacin cewa lokacin yin magari ba ya yi, wato kusan mintina goma ko kwata bayan faduwar rana bayan kiran sallar da aka yi, wannan lokacin magariba na sharia' ke nan. Wannan su ne bayanai game da lokaci.
11. Amma wata mas'alar kuma ita ce mutane da suek zuwa sallar jam'I suna yin sujada ne akna darduma, tambaya anan ita ce shin mu ma zamu iya yin sujada akan dardumakuwa? A mahangar sayyid khamni idan ba zai yiwu ba mu yi a kan yatsu, kuma ba zai jawo hankalin mutane ba, ta yadda zai zama babu wata matasla ko kuma zamu iya zuwa wurin da yake da dutsen darduma, wanda yin sujada a kan sa ya inganta, kamar dutse, to sai mu tsaya a nan, ko kuma idan muna da dardumar kaba wacce babu wata matsala ba zata jawo hankula ba, kuma ba zata dami muten ba, sai mu yi sujada a kan wadanna, idan kuwa ba haka ba kamar ya zama akwai matsala, koi kuma yin sallar jam'I akwai wani wuri da muka tsaya wadan yake darduma ce, idan kuma muna son zuwa wani wurin ba zai yiwu mu canja wuri ba, ko kuma zamu jawo hankalin jama'a, to sai mu yi salla a nan, kuma mu yi sujada kan darduma.
12. mas'alar hada safu kwua wani lokacin ana tamaya cewa, kamar dai yadda suek yin salla jarma'I suna ganin ta inganta, kuma ya zama an samu haduwar sahun gaba da na baya, idan mutane suak yi tarayya a cikin to babu wata matsala a kai.
Game da kunubi kuwa tun da yin sa mustahabbi ne, idan ba sa yin kunuti to kuma kada ku yi kunuti kuma babu matsala. Wani lokaci kuwa a sallar asuba wasu lokuta bayan ruku'in raka'a ta biyu en suke yin kunuti, to wannan ma babu wata matsala, idan suak yi kunuti a nan ku ma sai ku yi, kuma salla ba ta da wata matsala.
Wani lokaci bayan ruku'u kafin yin sujda suan dan daukar lokaci, to kuma kada ku tafi yin sudaja, ku rika sauraron kabbarar lasifika.
13. Wani lokaci limamin jam'I a salla yana karanta surar sujada wanda zamu ga ni a wadanan shekarun nan na karshe wani lokaci suan karanta shi a lokacin sallar asuba, duk da kadan ne yake faruwa, kuma duk da cewa a fatawar malamanmu da fatawar sayyid khamna'I jagoran juyin musulunci ba zai yiwu a karanta surar sujada a sallal ba, amma wani lokaci suan karantawa, kuma a wanna lokacin suek yin sujada, to idan suak yi sujada ku ma ku bi su ku yi sujada, sannan sai ku ci gaba da yin salla, sai dai bayan sallama daga salla sai ku sake yin salla.
Wata mas'alar ita ce bayan yin sajada ta biyu ba tare da wani jinkiri ba ne suek tashi zuwa ga raka'a mai biye mata, to ku sai ku dan jinkirta ku dan zauna kadan bayan sujada ta biyu sannan sai ku tashi, wannan ma ba shi da wata matsala.
14. Inda kuma suke fadin kalmar amin bayan karanta fatiha to ku kada ku fadi amin, amma kuna iya cewa: "alhamdu lil-Lahi rabbil alamin". Kuma da yake kuna yin sallar jam'I ne to kuna sakin hannu ne, ko da yake wasu daga mazhabobin ma wadanda ba shi'a ba su ma suna sakin hannu ne.
Wata tambayar a nan ita ce cewa; Idan muna yin sallar jam'i, kuma muna yin sallolin mu na wuni a jam'I, shin dole ne bayan nan ko kafin nan mu sake yin salla ko kuwa? A fatawar sayyid khamna'I babu bukatar sake wata sallar; wato idan kuka yi tarayya a cikin yin sallar jam'I, wanna sallar ta wadatar, kuma ta may gurbin sallar azhara da sallar la'asar, kuma ba dole ba ne mu sake yin wata sallar.

Azumi
15. Wata mas'alar kuma game da yin azumi ne. mu muna da azumi kala biyu ne, na wajibi da na mustahabbi. Shin lokacin da muke madina zamu iya yin azumin wajibi kuwa; misali wanda yake da ramuwar azumi kuma yana son ya yi a wannan ranakun saboda ibadarsa ta fi zama kammalalliya tare da yin sallolinsa, salar jami'I, ziyara, ziyarar kabarin annabi (s.a.w), ziyara imaman bakiyya, sai ya kasance tare da azuminsa kuma?
Game da azumin wajibi akwai sharadi ga mutum ya yi nufin zaman kwanaki goma a madina; wato mafi karanci kwanaki goma da zai kasance a madina, kada wani tunani ya zo muku ku yi kiyasi da cewa ai tun da a nan muna iya cika salla, to azumi ma muna iya yin sa; ba haka ba ne, azumi yana da na hukunci daban da na salla. Wannan mas'alar ta kebanta da salla ce. Hukuncin salla da azumin yana da bambanci a wannan mas'alar.
Kada ku yi kiyasi ku ce: to ai tun da zamu iya yin salla cikakkiya, kuma an ce duk inda zamu iya cika salla to zamu iya yin azumi, to ai zamu iya yin azumi ke nan. To ba haka ba ne, wannan hukuncin zabin ya kebanta da salla ne, don haka ba zaku iya yin azumi ba, sai dai idan zaku zauna ne mafi karanci kwana goma.
Don haka da farko idan mun iso madina sai mu tambayi jagoran tafiya ko idan mun sani cewa mafi karanci kwanaki goma zamu yi, to dukkan wani azumin wajibi zamu iya yin sa; kamar azumin ramuwa, da na kaffara, ko na watan ramadhan, idan muka je umara duk zamu iya yin su, amma idan kasa da kwanaki goma ne, to ba zamu iya yin azumin wajibi ba.
16. Amma azumin mustahabbi wani azmin mustahabbi na musamman wannan garin ne wanda matafiya zai iya yi, shin zai yi kwana goma ne a nan ko kasa da haka ne, wannan kuwa shi ne na kwana uku na mustahabbi, wanan babu wata matsala. Zai iya yin azumin kwana uku na mustahabbi a madna mai haske don neman biyan bukatunsa wurin Allah. Ku kuna neman biyan bukatunku wurin Allah, in Allah ya so za a amsa muku, duk da yana da kyau wadannan ranakun su kasance ranar laraba, da alhamis, da juma'a ne. sai dai akwai tambaya a nan cewa; da mun ji cewa wanda yake da azumin ramwau ba zai iya yin na mustahabbi ba, to yaya ke nan ga shi ya zo madina kuma 'yan kwanki zai yi a nan madina, shin zai iya yin azumin kwanaki uku na mustahabbi kuwa?
Haka ne, wannan yana daga cikin abin da aka toge ne, don haka yana iya yin azumin mustahabbi na kwanaki uku, babu wata matsala a nan; wato idan yana da ramwua ma to zai iya yin wadanann azumomin na mustahabbi na kwanaki uku.
Haka nan idan wani ya yi nuzuri amma da sharadin ba shi da azumin ramuwa a kansa, babu wani azumin wajibi a kansa, misail da ma can ya yi nuzuri cewa idan ya je madina ko da kuwa ba zai yi kwanaki goma ba to zai yi azumi, to a nan ma wannan mutum zai iya yin azumin mustahabbi wanda ya zmaa wajibi da yin nuzuri.
Wannan ma wasu hukunce-hukunce na a takaice da suka shafi garin madina mai haske har zuwa wurin da zai tafi zuwa mikati in Allah ya so, ya yi harami, mu fara yin ayyukan umrar tama'ttu'I.
Wasslamu alaikum wa rahamtul Lah wa barakatuhu
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Saturday, December 24, 2011

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)