Muassasar alhasanain (a.s)

Umarar Tamattu'i

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5


Na Shida: Binciken Hukunce-Hukunce Da Mas'alolin Da Suka Shafi Ayyukan Umarar Tamattu'i

Ayyukan Umarar Tamattu'i
Ayyukan umara daga harami zuwa mikati ne suke farawa, kuma ayyukan da suka zama wajibi a yi su sun hada da: Dawafi, sallar dawafi, sa'ayi tsakanin Safa da Marwa, rage gashi, duk da cewa tsakanin harami da yin dawafi akwai ayyukan da suka haramta kan mai yin harami, wato duk abubuwan da suke an haramta su yayin yin harami to suna hawa kan wanda ya yi harami. Kuma kamar yadda suke haramta a aikin hajji haka suke haramta a umara tun lokacin da muka yi harami daga mikati har zuwa lokacin da muka aske gashi. Don haka dukkan abubuwan da aka haramta lokacin haramin hajji haka nan ma suke haramta lokacin yin Umara Mufrada, don haka ba zamu maimaita bayanin su ba a nan, don haka zamu ci gaba da yin bahasi; sai mu sanya kayan a harami a mikati, mu yi niyya, mu fadi labbaika, sannan sai mu tafi Makka don yin sauran ayyukan Umarar Tamattu'i wanda na farko shi ne yin dawafi.
Dawafi
1. Dawafi yana daga cikin rukunai muhimmai a ayyukan umara da hajji, yana da muhimmanci matuka, kuma akwai mas'aloli da suke dole da zamu kula da su sosai. Mas'alolin dawafi sun kasu gida biyu: bangaren da yake na sharuddan dawafi, da bangaren wajiban dawafi. Na farko sun shafi mai yin dawafi ne yawanci, na biyu kuwa sun shafi dawafin ne kansa wadanda zamu kawo muku su a nan; wato mas'alolin dawafi kala biyu ne: sharudda da wajibai.
Sharuddan sun hada da: 1- Yin niyya, 2- Tsarki, (wato yin alwala, -wanka ba dole ba ne-, sai tsarkin jiki, da tsarkin tufafi). 3- Halaccin tufafi. 4- Jerantawa.
Sanya tufafin halal shi ma sharadi ne na lokacin yin dawafi kawai.
Wajiban dawafi kuwa sun hada da: Farawa da Hajarul Aswad da karewa da Hajarul Aswad (watan kwanar Ka'aba da bangaren Hajarul Aswad yake ta nan ne za a fara dawafi haka ma daga karshe da nan ne za a kare shi). Sai a sanya Ka'aba a hannun hagun mai dawafi, sannan ya kasance daga wajen Hajaru Isma'il ga mai yin dawafi, wato Hajaru Isma'il shi ma ya kasance yana cikin abin da za a rika gewayewa domin shi ma yana cikin daki a asalinsa, haka nan ma kada ya kasance mun yi tafiya saman bangon Ka'aba yayin yin dawafi wanda aka sani da Shazrawan, Ka'aba tana da wata Katanga da take gewayayya to ita ake nufi da kada a yi tafiya a kanta yayin dawafi, wannan ma yana daga cikin wajiban dawafi da muka kawo a jerin wajibai; Yanzu za mu fara bayanin kowanne daga cikin wadannan.

Niyya
2. Niyya ita ce sharadi na farko da ya shafi mai yin dawafi, niyyar yin dawafi wani bangare ne na Umarar Tamattu'i, kuma yanki ce ta ibada, kuma dole ne niyya ta kasance da nufin kusanci da Allah; wato dole mai yin dawafi yayi niyyar yin dawafi da nufin ibada ga Allah, kuma idan babu wannan nufin to babu dawafi, don haka babu matsala ta wannan bangaren domin tun lokacin da muka yi harami muka kudurci cewa dukkan ayyukanmu zasu kasance don ibada ce da Allah ya wajbata a kanmu, wato mun riga mun yi nufin hakan tun farkon kulla harami da niyyar yin umara. Wani abu mai muhimmanci a nan shi ne a niyya dole ne a sanya cewa dawafin Umarar Tamattu'i ne ko na Hajji Tamattu'i, kuma shi ma dawafin umara sai a kudurci cewa na Umarar Tamattu'i ce ko Mufrada; wato dole ne niyyar mu ta kasance sananniya bisa abin da muka kudurce. Sai dai ba dole ba ne mu fadi niyya da harshe, ya isa mu kudurce ta, wato da mun yi harami da Umarar Tamattu'i, mun tafi masallaci mai alfarma da nufin neman kusanci da Allah madaukaki da nufin yin aikin da ya shafi umrar tamattu'i, sai mu gewaye Ka'aba sau bakwai da wannan niyar dai, wannan duka ya isa babu wata matsala.

Tsarki
3. Sharadi na biyu daga sharuddan da suka shafi mai yin dawafi shi ne yin tsarki; wato dole ne ya kasance yana da alwala, sai dai wanka ba wajibi ba ne, lokacin da muke son zuwa harami mu yi dawafin umara, ya zama dole ne mu yi alwala musamman tun da yake yin dawafin umara ba tare da alwalba ba bai inganta ba. Kuma idan akwai wani uzuri da zai hana yin alwala to dole ne a yi taimama, mata ma idan suna da uzuri bisa shari'a ta yadda ba za su iya alwala ba to dole su yi taimama su shiga msallaci su yi dawafi, sannan sai su zo da sauran ayyukansu. Idan a mikati wata mace ta samu uzuri na shair'a kamar yin haila kuma tana so ta yi harami, to ba zata iya shiga masallaci ba, amma sai dai idan zata iya wucewa masallaci ba tare da ta tsaya ba, tana cikin tafiya tana yin harama to sai ta yi hakan. wannan game da masallacin Shajara ke nan, amma a Juhufa babu wannan matsalar, don haka sai ta yi haramarta a wajan masallaci a wannan yanki na Juhufa ko kuma ta tafi wani mikatin ta yi harami duka babu wata matsala. Amma idan mace ta san cewa kafin ta tafi Arfa kafin yin harami da aikin hajji zata samu tsarkaka, to sai ta yi harami da haramar Umarar Tamattu'i, ta tafi Makka, sai ta tsaya a nan zuwa lokacin da zata samu yin tsarki, sannan sai ta yi dawafi da sallar dawafi ta zo da sauran ayyukan.
4. Amma idan mace ta san cewa tun farko ba zata samu yin tsarki ba (wato jinin haila a misali ba zai dakata ba) to sai ta yi niyyar hajjin ifradi kawai, wato sai ta tafi mikati da niyyar yin aikin hajji, bayan ta yi harama sai ta tafi Arfa ta yi ayyukan hajji, bayan nan kuma sai ta zo da ayyukan Umara Mufrada. Amma idan mace ba ta da wata matsala a tare da ita, tana da tsarki, sai ta yi harami ta tafi Makka, amma kafin ta yi dawafi sai wani uzuri ya same ta, kuma ta kasa zuwa masallaci ta yi dawafi. Wannan ma sai ta yi hakuri tukun har sai ta samu tsarki, sannan sai ta yi ayyukan hajji.
Amma idan ta yi hakuri har ta kai ga yin tsarki, sai ta bar yin dawafi da yin sallar dawafi, sai ta yi sa'ayi ta dan yanke gashi kawai, bayan nan sai ta yi harami da haramar yin hajji, sai ta tafi Arfa ta yi aikin hajji, wato sai ta yi ayyukan Mina da waninsa, bayan nan sai ta koma Makka don yin ayyukan hajji kafin dawafin hajji ko bayan dawafin hajji da sallarsa, sai ta yi wannan dawafin ta yi sallar dawafin da Umarar Tamattu'i. Ko da yake wannan mas'aloli sun shafi mata ne, suna da kuma rassa masu yawa, kuma yanzu ba mu da wata damar yin bayanin su, kuma sau da yawa idan muka yi bayanin su ma sai mata su manta da su.
Wata maganar da take da muhimmanci shi ne tun farko kada ku samu rawar jiki da garaje, domin musulunci ya bayyana dukkan wadannan mas'alolin, kuma ko da wata mas'ala ta taso to sai a yi aiki bisa hukuncin da aka bayar a hukuncin shari'a, in Allah ya so za a samu yin umara da hajji ingantacce, kuma idan uzuri ya samu to sai a koma wa littafin aikin hajji za a samu hukuncin a nan, sai a yi aiki da shi, ko a gaya wa wani malami wanda shi ya san aikinsa, kuma sai a yi aki da abin da ya yi bayani.
5. Daya daga cikin tambayoyin da suke zuwa ga mata shi ne shin za su iya shan magani saboda kada su samu wata matsalar yin jinin haila, kuma suna iya yin ayyukan umara? Shin haka daidai ne ko kuwa?
Amsa a nan ita ce; idan shan magani ba shi da wata matasla gare ta, babu wata matsala, kuma idan ya hana ta yin haila haka nan babu wata mataslar, wato sai ta yi ayyukan ta na shari'a.
6. To mun kawo cewa mas'alolin da suka shafi mata suna da yawa matuka, in Allah ya so sai ku duba, idan wata mas'ala ta same su sai su nemi sanin hukuncinta, sai su tambaya su san me zasu yi.
7. Wanda duk yake son zuwa yin dawafi sai ya yi kokwanton ya yi alwala ko kuwa? To sai ya yi alwala bisa wajibi; wato kafin dawafi sai ya yi alwala domin dawafinsa ya inganta. Amma idan wani ya yi alwala kuma ya san yana da ita don yin dawafi, sai ya yi kokwanto ko alwalarsa ta bace ko kuwa, to wannan ba ta bace ba, kuma ba dole ba ne ya sake yin wata alwalar.
Kuma idan wani ya yi dawafi, bayan nan sai ya yi shakkun ko yana da alwala ko kuwa, ko alwalarsa ta bace ko kuwa? Da tsarki ya yi dawafi ko kuwa? Wannan dawafinsa ya yi, kuma idan har lokacin bai yi salla ba, to dole ne ya yi alwala don yin salla a nan. Amma idan ya riga ya yi sallar dawafi ma sannan sai ya yi shakku, to dawafinsa da sallarsa duk sun yi.
Wata mas'alar ma da ta shafi tsarki ita ce, a dawafi a tsakiyar ayyukan umara da hajji, dawafi ne kawai da sallarsa suke bukatar tsarki da alwala, amma sauran ayyukan kamar sa'ayi da jifa, da tsayuwar Arfa, da kwanan Mina, duk ba sa bukatar tsarki; wato ba sharadi ba ne mutumin da yake da tsarki ko alwala; idan ba shi da alwala ma ya yi to duk babu wata matsala a kan hakan.
Ko da yake yin su da alwala duka mustahabbi ne, a wasu ayyukan ma kamar sa'ayi an yi wasiyya da mustahabbancin yin alwala. Don haka dawafi ne kawai da sallarsa (dawafin Umarar Tamattu'i da sallarsa, da dawafin hajji da sallarsa, dawafin mata da sallarsa) su ne kawai suke bukatar tsarki. Don haka wadannan sauran ayyukan ba sa bukatar wajabcin tsarki.
Don haka duk wanda yake son ya yi sa'ayi ba dole ba ne ya yi alwala sai dai mustahabbi ne.

Sanya Tufafi Don Yin Dawafi
8. Wani sharadin da ya hau kan mai aikin hajji da umara kuwa shi ne sanya tufafi; dole ne mai dawafi ya kasance yana da cikakken tufafi, kuma mata sai su kiyaye sosai, amma idan wani lokaci wani bangare na gashin kai ya fito ba tare da sun kula da hakan ba, to ba su yi laifi ba, kuma dawafin su ya yi. Haka nan idan suka san cewa kansu ba bude yake ba don haka ba su rufe shi ba, to dawafin su ya yi, amma tun da akwai maza ajnabiyyai da suke ganin gashin kansu to rashin rufe kan zunubi ne suka yi.

Tsarkin Tufafi da Jiki
9. Wani sharadin da ya shafi jiki da tufafi shi ne tsarkin jiki da tufafi a salla. Duk kun san wadannan mas'aloli, lokacin dawafi dole ne mutum ya kasance yana da tufafi mai tsarki. Kuma game da sauran najasosi ma dole ne a yi ihtiyadi wajibi, sai dai mun riga mun fadi sharuddan mai yin dawafi, cewa dole ne ya kasance yana da tufafi mai tsarki, amma akwai wasu wurare da aka toge kamar haka:
Tufafi ya kasance karami wanda ta yiwu ma ba za a iya kiran sa tufafi ba, misalin safa, da hankici, kamar a ce suna cikin aljihu, ko ma zobe, idan duka wadannan sun kasance ba su da tsarki to babu matsala.
Haka nan ma jini kamar digo da yake kan tufafi ko kan hankici ko mayafin harami ko bisa tufafin mai yin dawafi, kuma girman sa bai kai fadin dirhami ba, wato kusan fadin saman dan yatsa, to babu matsala don an yi dawafi da shi.
Haka nan wanda yake da ciwo a jikinsa kuma yana son yin dawafi, sannan ba zai iya tsarkake shi ba, ko kuma zai samu wahala idan ya tsarkake shi, to wannan jinin da yake kan ciwon yana daga cikin abubuwan da aka yi afuwar su. Ba ma fatan a samu wannan mataslolin ma ina Allah ya so.

Jerantawa Tsakanin Gewayon Dawafi
10. Daga sharuddan dawafi (ba sharuddan mai yin dawafin ba) akwai jeranta dawafi ta yadda ba za a samu tsawon lokaci tsakanin gewayen da ya gabata da mai biye masa ba. Don haka dole ne a samu jerantawa tsakanin wadannan gewayon baki daya, idan kuwa aka samu tsawon lokaci ta yadda ba za a iya kiran sa dawafin da aka jeranta gewayen Ka'aba ba, to wannan dawafin ya baci.
Idan da wata matasla ta taso a cikin tsakiyar yin dawafi kamar matsalar wanke masallaci, ko kuma aka tayar da sallar jam'i da makamantansu to sai a lura sosai idan lokacin bai tsawaita da yawa ba ya bata dawafi, amma idan kadan ne to babu wata matsala a kai sai a ci gaba da yin dawafi bayan an gama. Haka nan yake game da sauran uzurori.

Wajiban Dawafi
11. Wajiban dawafi; wato abubuwan da suke wajibi ne a kiyaye su a dawafi su ne: dole ne dawafi ya fara da Hajarul Aswad kuma ya kare da shi. Dawafi yana da wurin farawa da wurin karewa. Akwai tsari da dawafi; don haka ba kawai sai mutum ya fara daga inda ya ga dama ba, kuma ya kare da inda ya ga dama, ko kuma ya yi gewaye adadin da ya ga dama. Don haka dawafi yana da wurin farawa da na karewa, da adadin gewaye guda bakwai, da yanayin yadda za a yi tafiya a gefen kaba'a, da yadda za a yi tafiya din, duk suna nan a littattafai da aka yi bayanin su.
12. Rukunin Hajarul Aswad shi ne wurin fara dawafi, shi ne wurin da aka sanya wani dutse mai daraja da daukaka a daidai wurin da aka fi sani da sunan rukunin Hajarul Aswad, to daga nan ake fara dawafi da kuma nan ne ake kaiwa karshen sa. Idan zamu fara dawafi zamu fara da daura da shi wannan rukunin na Hajarul Aswad, amma idan zamu kare sai mu kare dawafi da shi kansa Hajarul Aswad ne. Daya daga cikin muhimman bayani da zamu kara a nan shi ne cewa; Hajarul Aswad yana kusan tsawon sentimita 20 ne.
Sannan kuma muna iya tambaya cewa; shin dole ne mu fara da inda ake farawa wato rukunin Hajarul Aswad da dikka sosai? Amsa ita ce; yadda yake bisa al'ada ya isa idan muka fara daga wurin da ake farawa, sai dai bisa ihtiyadi da zamu dan yi baya kadan kafin wurin sannan sai mu fara da ya yi kyau, ta yadda sai mu yi niyya mu fara da mun karaso wannan rukunin na Hajarul Aswad sai ya kasance mun fara dawafi ke nan. Idan muka shiga cikin masu dawafi sai mu fara tafiya tare da su kafin wurin da yake na Hajarul Aswad ne, ta yadda da mun zo saitin rukunin Hajarul Aswad sai ya kasance mun fara dawafin namu ke nan bisa niyya, don haka tafiya da zamu yi tare da mutane kafin mu zo wurin ba ta nufin mun fara dawafi, sai dai mun dan yi baya ne tukun bisa ihtiyadi. Kamar yadda idan an gama dawafi zai kasance an kawo daidai Hajarul Aswad sannan za a kammala shi.
13. Muna sake karfafawa cewa ana fara dawafi da daura da Hajarul Aswad ne, kuma duk sa'adda aka yi gewayo aka zo saitin sa, to an so mutum ya sumbance shi idan zai iya, idan kuwa ba zai iya ba, sai ya yi nuni zuwa gare shi da hannunsa sannan sai ya sumbanci hannun nasa, amma tsayawa a wurin ba dole ba ce, musamman idan zai damu masu yin dawafi a wurin. Don haka kada ya dami masu yin dawafi, sai ya yi nuni yana cikin tafiyarsa da hannunsa, sannan sai ya sumbanci hannun ya wadatar, sannan sai ya ci gaba har sai ya kammala kewayensa guda bakwai.
14. Abu na uku daga wajiban dawafi shi ne wajabcin gwaye Hajaru Isma'il, ta yadda dole ne ya kasance cikin abubuwan da ake gewayewa yayin dawafi. Shi wani rabin gwaye ne da kuke iya ganin sa a jikin dakin Ka'aba; shi wuri ne da aka binne Hajara babar annabi Isma'il (Tsira da amincin Allah su tabbata gare shi, da zuriyarsa da kakanninsa masu daraja) sai ya gewaye shi don kada masu dawafi su bi ta kan kabarin babarsa, sannan daga baya kuma suka ja wata Katanga a wurin kamar yadda kuke iya gani, kuma Imamai masu daraja (tsira da amincin Allah ya tabbata gare su baki daya) sun karfafi hakan cewa dole ne a kewaye Hajaru Isma'il yayin dawafi.
15. Ko da yake ma kofar dakin a kulle take ta yadda mutane ba sa iya shiga. Don haka suna yin dawafi gefen ka'aba ne da Hajaru Isma'il don haka babu wata damuwa.
Wajibi ne a yi gewayen a gefen ka'aba cikakken gewayo, don haka ba zai iya yiwuwa daga cikin ka'aba ba, kamar yadda akwai wani dan tudu da ya karkace a jikin garun ka'aba da ake kiran sa "Shazrawan" wani lokaci saboda yawan mutane da cunkoso wasu muatne suna bi ta kansa, to mu sani duk wanda ya bi ta kansa ko da wani bangare nasa ne ya bi ta kai ya yi dawafi to dawafinsa bai yi ba, don haka sai a kiyaye.

Adadin Gewayon Dawafi
16. Gewaye ka'aba sai bakwai a dawafi yana daga cikin wajibai, kuma ba ragi ba dadi, ko da kuwa kadan ba za a bari ba, haka ma ba za a dada ko da rabin gewayo ba ne da sunan dawafi. Amma idan muka bi yawan tafiyar mutane don mu fito waje ba da niyyar dawafi ba to babu komai, muhimmi dai kada ya zama daga dawafi ne.
Domin kiyaye yawan adadin dawafi yawanci wasu mahajjata suna tafiya tare da saurna mahajjata ne, sai dai wasu kuma suna yin wata addu'a ne a duk kiwayo sai su kiyaye da dan yatsansu ko gewaye nawa suka yi.
Amma dai akwai wata ka'ida da za a kiyaye kamar haka: Duk sa'adda muka manta yawan dawafi mu shiga wani tunani daban, to dawafi ya lalace dole mu sake tun farko; da mutum zai yi kokwanto dawafi uku ya yi ko hudu, kuma ya kasa tunawa, to dawafinsa ya bace, sai ya bar shi ya sake tun farko daga kan Hajarul Aswad. Hanya daya ce kawai dawafi yake inganta da shi ko da kuwa an yi kokwanto, wannan kuwa shi ne idan mai dawafi ya yi kokwanto bayan ya zo kan Hajarul aswa cewa gewayo bakwai ya yi ko takwas, to a nan dawafinsa ya inganta.

Iyakokin Dawafi
17. Dawafi a gewayen ka'aba ba shi da iyaka a cikin masallaci, duk nisan da mai dawafi ya yi ko kusanci da ka'aba da ya yi, sannan ya yi dawafinsa ta yadda a bisa al'ada za a kira shi gewayen ka'aba, to ya inganta. Don haka ba dole ba ne ya kasance tsakanin dakin ka'aba da makamu Ibrahim, sai dai idan babu cunkoso hakan ya fi.
Misalin haka a cikin dawafi; da mutanen da suke dawafi kamar mutane dari ne ko dari biyu, sai wani ya yi nesa da ka'aba yana dawafi ta yadda duk wanda ya gan shi ba zai ce yana dawafi ba. Amma idan da akwai mutane masu yawan gaske ko da kuwa ba su hadu sosai ba saboda karancin cunkoso, idan ya yi dawafi a tare da su a karshen sahunsu wannan duk wanda ya gan shi zai ga yana dawafi ne, to shi wannan kada ya takura kansa da cewa dole ne sai ya yi dawafi tsakanin ka'aba da makamu Ibrahim.

Wasu Mas'aloli Kan Dawafi
18. Daga karshen wannan bahasin zamu so kawo wasu bayanai da zamu kammala bahasin dawafi da su kamar haka: Duk ta inda muka fito wa ka'aba babu matsala, sai dai ba zamu iya fara dawafi ba sai mun zo daura da Hajarul Aswad, don haka idan muka zo sai mu kewaya gefen ka'aba tare da mutane saboda tsoron cunkoso mai yawa amma ba da niyyar dawafi ba, idan mun zo daidai Hajarul Aswad sai mu yi niyyar dawafi mu ci gaba da gewayen ka'aba. Sau da yawa muna ganin wasu lokuta saboda cunkoso mai tsanani babu dama mu kutsa mutane ta yadda idan muka yi haka zamu takura su, don haka sai ya zama ba yadda zamu yi sai mu gewayo tare da mutane har sai mun zo saitin Hajarul Aswad sai mu yi niyyar fara dawafi daga daurarsa, mu fara dawafi mu ci gaba har gewayon ka'aba guda bakwai. Kamar yadda bayan gama dawafi ba dole ne sai an zo daura da makamu Ibrahim a daidai inda muka gama ba saboda cunkoson mutane, don haka duk inda muka fi samun sauki sai mu fita daga cikin cunkoson mutane, sannan sai mu yi sallar dawafin.
19. Abu muhimmi na biyu shi ne duk sa'adda muka yi gewayen ka'aba muka kawo daidai gurin Hajarul Aswad, haka nan ma bayan gama dawafi baki daya, to zamu tsaya a daura da Hajarul Aswad, kamar yadda muka kawo a baya.
20. Bayani na uku shi ne wani lokaci kana samun matsatsi da mutane wannan babu matsala a kai, amma da sun matse ka ta yadda suka tura ka tafiyar da babu nufinka ne ta yadda suka daga sama kafarka ba kasa take ba ka tafi, to dawafi bai yi ba. Ko kuma ya kai ga yin 'yan dage ta yadda ba da son sa ne yake tafiya ba shi ma haka.
Amma idan sun sanya ka ka dada sauri ne sosai ta yadda suna turowa amma kana tafiya da sauri ne kawai, ko kuma sun matse ka matukar gaske ta yadda ba ka gane ba cewa da kanka ne kake tafiya ko kuwa su suke tafiya da kai ne, to wannan duka babu matsala cikinsa, dawafinsa ya inganta.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Thursday, April 12, 2012

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)