Muassasar alhasanain (a.s)

Dawafi da Sa'ayi

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5


Na Bakwai: Bayanin Mas'alolin Da Suka Shafi Dawafi Da Sa'ayi Da Kuma Yanke Suma A Umarar Tamattu'i

Sharuddan Sallar Dawafi
Bayan mun yi dawafi to abubuwa uku ke nan suka rage mana: sallar dawafi, sa'ayin tsakanin safa da marwa, da yanke gashi. Idan muka kammala dawafi sai mu yi salla raka'a biyu, sai dai akwai mas'aloli guda uku game da sallar dawafi: zamanin yin ta, wurin yin ta, yadda ake yin ta.
Amma zamanin yin ta shi ne bayan an gama dawafi babu wani jinkiri sai a yi sallar, idan masallaci yana da matsatsi da cunkoso sai mu koma can baya inda babu masu dawafi sai mu yi sallarmu a nan. Sai dai bai halatta ba mu shiga wasu ayyukan daban kafin yin sallar dawafi, don haka bayan dawafi abu na gaba da zamu yi ita ce sallar dawafin.
1. Amma wurin yin sallar dawafi; Ba za a iya yin ta a ko'ina ba, dole ne ta kasance a cikin masallaci mai alfarma na ka'aba, kuma ta kasance a bayan makamu Ibrahim (Tsira da amincin Allah su tabbata gare shi, da zuriyarsa da kakanninsa masu daraja), makamu Ibrahim shi ne wannan dutsen mai daraja da annabi Ibrahim (Tsira da amincin Allah su tabbata gare shi, da zuriyarsa da kakanninsa masu daraja) yake tsayawa kansa yayin gina ka'aba, kuma bisa mu'ujiza har yanzu akwai sawun kafafunsa a kai, a yanzu zamu ga an sanya masa wani ado na zinare a samansa, kuma tsakaninsa da ka'aba ya kai mita 13.
2. Bayan mun gama dawafi sai mu tafi wurin makamu Ibrahim cikin nutsuwa ba tare da mun damu mutane ba ko mun jawo ture - ture, don mun riga mun kammala dawafinmu. Sai mu tafi bayan makamu Ibrahim ta yadda zai kasance muna kallonsa kuma muna kallon ka'aba a lokaci guda kuma kusa da shi, don haka yin salla a gefensa da nisa bai inganta ba. Haka nan idan babu mutane da yawa amma muka tsaya nesa da makam shi ma bai inganta ba. Amma idan taro ya yawaita ta yadda jama'a ta yi yawan gaske da cunkoso mai tsanani, ko kuma mutane sun cika wurin babu wurin da zamu yi salla mu, to sai mu koma can baya muna kallon makam da ka'aba mu yi salla a hakan ta inganta.
3. Domin karin bayani zamu kawo misali cewa: Idan da wani mutum yana tafiya, amma a can bayansa da 'yar tazara akwai wasu mutane biyu suna bin sa, duk wanda ya gani zai ga cewa ba shi suke bi ba, amma da a ce mutane dari ne a bayansa daya bayan daya suna bin sa, to duk wanda ya ga na karshe ma zai ce shi yake bi. To haka ma makam Ibrahim yake, idan akwai fili ba jama'a to dole a kusance shi a yi salla a kusa da shi a bayansa, amma idan jama'a tana yin dawafi babu damar yin salla bayansa, to sai mu yi bayan wasu dawafi har sai mun kai ga inda yake akwai sararin da zamu iya yin sallar komai nisantar sa kuwa.
Sau da yawa sai mu ga wasu jama'a sun rike hannaye suna damun masu dawafi har ma sau tari sai an ture su sallar ta bace sannan sai su sake, to wannan bai yi daidai ba. Don haka koma sun koma can bayan masu dawafi ta yadda tsakaninsu da makam masu dawafi ne komai nisa babu komai.

Yadda Ake yin Sallar Dawafi
4. Ita sallar dawafi raka'a biyu ce kamar yadda ake yin sallar asuba sai dai bambancin niyya, na biyu sallar dawafi ba ta da ikama da kiran salla domin ba a yi wa salla kiran salla da ikama sai ta wajiban yau da kullum
5. Ana iya karanta duk wata sura a cikin wannan sallar ban da surar da take da sujada, sai dai an so a karanta surar Ikhlas bayan fatiha a raka'ar farko, a raka'a ta biyu kuma surar Kafirun bayan fatiha.
Kuma mata suna karanta karantunta a cikin yin kasa - kasa da muryar su, maza suna iya karantawa da daga murya ko yin kasa - kasa da murya. Bayan an gama sai a yi addu'o'i.
6. Wasu muhimman bayanai biyu a nan su ne: ba a yin jam'I a sallar dawafi. Don haka mai sallar dawafi ba zai iya bin jam'I da ita ba, ko da kuwa karatun sa ba daidai ba ne. Don haka yana da kyau kafin ya tafi hajji ya yi kokarin ganin ya koyi karatun salla sosai.
7. Wani lokaci saboda cunkoso akan samu mace ta tsaya don yin salla kuma ga maza a kusa da ita, to idan zai yiwu ya zama akwai kamar taku guda tsakanin mace da mazan, kuma babu komai salla ta yi. Sai dai yana da kyau namiji ya tsaya wurin da babu mace a damansa ko hagunsa ko a gabansa idan zai yiwu.

Sa'ayi Tsakanin Safa da Marwa
8. Bayan mun kammala sallar dawafi to ya zama wajibi mu yi sa'ayi tsakanin Safa da Marwa, wato sai mu fara daga kan Marwa mu kare da kan Safa. Don haka kada mu samu tsawon lokaci tsakanin sallar dawafi da yin sa'ayi tsakanin Safa da Marwa sai dai ga wanda ya gaji yana son ya huta kamar awa daya ko awa biyu, wannan babu matsala. Sai dai idan da rana ne to kada ya bari sai dare ya yi, idan kuma da dare ne to kada ya bari sai da rana ya yi, to wannan tsawon lokaci bai halatta ya kasance tsakanin yin sallar dawafi da yin sa'ayin Safa da Marwa ba.
Shan ruwan zamzam yana daga mustahabbobi da ake son yi, don haka sai ku sha ruwan zamzam sannan sai ku kama hanya zuwa ga yin sa'ayi tsakanin Safa da Marwa. Rijiyar zamzam a rufe take, sai dai an yi mata famfuna an aje wasu kofuna a wurin don ku sha ruwan zamzam.
9. Safa da Marwa wasu kananan duwatsu ne guda biyu da yau an rufe wani bangare nasu saboda gine - gine. Idan muka yi sallar dawafi bayan makamu Ibrahim da zamu yi hagu zamu tarar da kofar da zata komar da mu zuwa ga Safa da Marwa kusa da nan farfajiyar ka'aba. Kuma idan muka duba zuwa ga bangaren da Safa da Marwa suke daga nan farfajiyar harami idan babu wani cunkoso mai yawa zamu iya hango kaikawon masu sa'ayi tsakanin Safa da Marwa.

Mas'alolin Da Suka Shafi Sa'ayi Tsakanin Safa da Marwa
10. Akwai wasu mas'aloli game da sa'ayi tsakanin Safa da Marwa da zamu kawo kamar haka: na farko shi ne cewa sa'ayi tsakanin Safa da Marwa wani bangare ne na ayyukan ibada, don haka dole ne a yi su da niyyar yin ibada ga Allah, sai dai ba dole ba ne ta kasance da harshe tun da tun farko ya yi niyyar yin umara ko hajji saboda neman kusanci ga Allah ne, don haka ya isa ya kudurce cewa yana yin bauta ne ga Allah da wannan sa'ayin da yake yi. Don haka ne a dawafi da sallar dawafi ma bai zama dole sai ya yi niyya da harshe ba.
11. Yin sa'ayi tsakanin Safa da Marwa sau bakwai ne, zuwa safa ya zama daya ke nan, dawowa marwa ya zama biyu ke nan. Ba wai zuwa marwa da dawowa safa shi ne daya ba, don haka sai a kiyaye, duk sa'adda aka tafi daga safa zuwa marwa to an yi daya, idan aka dawo zuwa safa to an yi biyu ke nan, idan aka koma warwa ya zama uku ke nan, don haka za a fara daga safa a kare na bakwai da zuwa marwa daga karshe.
12. A lura cewa duk sa'adda muka je marwa zamu samu adadin tilo wato daya ko uku ko biyar ko bakwai, amma duk sa'adda muka je safa zamu samu adadi mai aure wato biyu ko hudu ko shida, don haka ne ma zamu fara daga safa amma mu kare da marwa.
13. Idan aka fara sa'ayin tsakanin Safa da Marwa to dole ne a kai har karshe wannan sharadi ne, dole ne mu kai har kai safa ko marwa yayin sa'ayi, idan muka rage ko kadan ne bai inganta ba. Sai dai ba dole ba ne har sai mun kai ga hawa can saman safa ko marwa, don haka ya isa da mun isa kan tudun marwa ko safa mu juya mu koma safa ko marwa.
14. A lura cewa duk sa'adda zamu tafi marwa ko zamu dawo safa dole ne mu fuskanci marwa ko safa, bai halatta mu tafi da baya baya ba, ko kuma mu tafi da gefe gefen mu, sai dai idan wani ya isa wuri mai tsananin cinkoso sai ya dan kaikaita kadan don ya kutsa su ya wuce, to wannan babu komai idan ya kasance ba mai yawa ba ne; don haka dole ne mu fuskancin safa ko marwa yayin zuwa gare su.

Hutawa a Sa'ayi
15. Idan mutum yana sa'ayi tsakanin Safa da Marwa sai ya gaji, to zai iya tsayawa ya huta, sai dai idan zai ci gaba, sai ya fara daga daidai inda ya dakata, sa'ayi tsakanin Safa da Marwa ba kamar dawafi ba ne da sai an bibiye shi a jere, don haka shi sa'ayin tsakanin Safa da Marwa wanda ya gaji yana iya dakatawa ya huta sannan sai ya ci gaba. Haka nan idan ya ji kishirwa ko ya ji yunwa zai iya zuwa ya sha ruwan ko ya ci abincin ya dawo ya ci gaba daga inda ya dakata.

Tsarki a Sa'ayi da Abubuwan da Suka Shafi Sa'ayi
16. Tsarki ba sharadi ba ne ga sa'ayi tsakanin Safa da Marwa, don haka wanda ya yi sa'ayi babu alwala to sa'ayinsa ya yi, sai dai mustahabbi ne ya yi alwalar kamar yadda muka kawo a baya.
Sannan yin sa'ayi a saman bene da aka yi bai inganta ba, domin yana sama da Safa da Marwa ne, kuma ko da wani yana da matsala kamar rashin lafiya, sai ya yi a sama shi ma bai yi ba, don haka idan ba shi da lafiya sai dai ya sanya wani ya yi masa, ko kuma ya hakura har sai ya samu sauki ko kuma mutane sun yi karanci babu cunkoso sannan sai ya yi.
Sannan kuma haka nan yin sa'ayi a wurin da aka kara bayan an fadada wurin shi ma a fatawar Ayatul-Lahi Sayyid Khamna'i ba shi da wata matsala don haka ya inganta.

Mustahabban Sa'ayi
17. Mustahabban sa'ayi suna da yawa, sai dai zamu kawo wasu daga ciki kamar haka: shagaltuwa da ambaton Allah, da addu'a, da karanta Kur'ani duk mustahabbi ne, akwai addu'o'in da suka zo kamar yin allahu akbar sau dari, alhamdu lillahi sau dari, la'ilaha illallah sau dari, kuma yana da kyau ya zama akwai hadawa da yin tasbihi tare da su. Idan muka shagaltu da addu'a da ambaton Allah da karanta Kur'ani zamu dadin wannan ibada kuma wannan zai hana mu shagaltuwa da gafala daga wannan ibada.
18. Sassarfa da tafiya da sauri suna daga cikin ayyukan sa'ayi tsakanin Safa da Marwa, sai dai wannan ya kebanci maza ne kawai kuma mustahabbi ne gare su. Muna iya ganin daidai wurin da zasu yi sassarfa (wato tafiya da sauri sosai) an sanya masa wani koren fitila a sama don su gane iyakacinsa.
Idan mace ta yi sassarfar ko namiji ya ki yin sassarfar duk da haka sa'ayinsu ya yi, haka nan idan namiji ya manta bai yi sassarfa ba, to kada ya dawo bayan don ya yi sassarfar domin gudun ka da ya haifar wa sa'ayinsa matsala.
19. Wadannan wasu bayanai ne da suka shafi sa'ayin tsakanin Safa da Marwa.

Cire Kazanta (Kamar Yanke Sumar Kai)
Yanke Suma shi ne karshen aikin umara, kuma zamu sake kawo muku ayyukan umara a jere kamar haka: Yin harama da sanya harami a Mikati, dawafin ka'aba, sallar dawafin ka'aba a bayan makamu Ibrahim, sa'ayi tsakanin Safa da Marwa, yanke kazanta.
20. A game da yanke kazanta akwai mas'aloli kamar guda uku da aka kawo: na farko, lokacin yanke kazantar, na biyu wurin yakewa, na uku yadda ake yankewa.
Amma bayanin yanke kazanta a umara: shi ne yanke wani abu daga gashin kai, ko kuma farce (akaifa) da niyyar cewa shi wani bangare ne na ayyukan Umarar Tamattu'i. Amma lokacin yin sa shi ne bayan yin sa'ayi tsakanin Safa da Marwa, kuma babu matsala don ya dauki tsawon lokaci bai yi ba, sai dai ya sani cewa matukar bai yi ba, to har yanzu bai fita daga harami ba, don haka duk abin da yake haramta ga mai harami ya haramta gare shi.
21. Amma game da wurin da za a yanke (gashin ko farce), babu wani wuri takamaimai da aka ayyana don yin hakan. Don haka idan ya kammala sa'ayinsa tsakanin Safa da Marwa to yana iya yankewa a marwa ko a waje, ko kuma ya je gida ya yanke. Sai dai ya yi hattara kada ya mata idan lokaci ya yi tsawo ya yi wani abu da ya haramta ga mai yin harami da umarar.
22. Kamar yadda muka ce dan kadan daga gashi ko akaifa ya isa idan muka yanke shi, da almakashi ne ko abin yanke a kaifa, kuma dole ne mu yi niyyar yankewa da sunan mun yi wani bangare na ayyukan umara a matsayin ibada ga Allah madaukaki.
Sannan mu sani cewa idan ba mu yanke namu ba, to ba mu da damar yanke wa wani nasa, domin idan ba ku manta ba yana daga cikin abubuwan da suka haramta ga mai yin umara shi ne ya yanke gashi ko da na waninsa ne. Sannan muna iya yankewa da kanmu ko kuma mu ba wa wani ya yanke mana in ya so sai mu yi niyya.
23. Idan mace tana son ta yanki wani dan kadan daga gashin ta bayan ta gama sa'ayi a nan kusa ne da marwa ko kuma daga waje farfajiyar masallaci, to ka da ta fito da gashinta waje, sai wasu mata su kewaye ta su yi mata kariya, in ya so sai ta yanki wani dan kadan daga gashinta, don gudun kada maza su ga gashinta.
24. Bayan mun kammala dukkan wadannan ayyukan yanzu ke nan mun fita daga harami mun kammala ayyukan Umarar Tamattu'i, don haka mu yanzu ke nan ba masu harami ba ne, muna iya sanya tufafinmu, kuma dukkan abubuwan da aka haramta mana saboda muna da harami sun halatta gare mu ke nan. Ko da yake akwai ayyuka biyu zuwa uku da suke wanzuwa da haramcinsu tsakanin Umarar Tamattu'i da Hajji Tamattu'i da za mu kawo muku su nan gaba.
Wassalamu alaikum wa rahamtullahi wa barakatuhu
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Thursday, April 12, 2012

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)