Muassasar alhasanain (a.s)

Kwanakin Makka

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5


Darasi Na Takwas: Bayanin Mas'alolin da Suka Shafi Kwanakin Haramomi Biyu

Mukaddimar Kwanakin Haramomi Biyu
Bayan gama ayyukan umara da sanya kayan gida muna makka har sai lokacin fara ayyukan hajji sun zo, sau da yawa muna sake sanya kayan harami ne ranar 8 ga watan zulhajji bisa mustahabbanci, sai mu yi harama da Hajji Tamattu'i mu nufi Arfa domin yin ayyukan hajji. Wannan dan tsakanin umara da hajji ana kiran sa da "tsakanin yin harami biyu". A nan zamu kawo bayanai game da mas'alar "tsakanin yin harami biyu" kamar haka:
1. A wadannan kwanakin da suke tsakanin umara da hajji akwia abubuwan da suke haram gare mu kamar haka: 1: Yin Umara Mufrada. 2: Aske gashin kai. 3: Fita daga garin Makka. 4: Cire shuke-shuken da suke a harami. 5: Yin farauta a harami.
2. Na barko game da Umara Mufrada: Bai halatta ba mu yi ta matukar muna cikin lokacin nan da yake tsakanin Umarar Tamattu'i da Hajji Tamattu'i, sai dai dawafi shi wannan ya halatta, a nan gaba zamu kawo bayanin cewa dawafi mustahabbi ne shi.
Na biyu game da Aske kai: da ma mata ba sa aske kai, amma maza ma su ma bai halatta su aske kan su ba a wannan lokacin, ko da yake ya halatta su rage shi da injin aski, amma su bari sai ranar idi ya fi shi ma, don haka rage shi da inji ko gyara shi duk ya halatta a wannan lokacin amma ban da askewa shi haramun ne.
3. Fita daga Makka a wannan kwanakin ba ya halatta, dole ne mu ci gaba da zama cikin garin Makka. Sai dai akwai yanayin da ya zama an togace kamar halin larura ko kuma yana son ya je wajen garin makka kamar Arfa ko Jidda, malamai suna cewa idan yana da yakini cewa zai je ya dawo ya samu yin ayyukan hajji to babu matsala gare shi. Amma idan ya san idan ya je ba zai iya dawowa ya samu ayyukan hajji ba, ko kuma za a iya tsare shi a hana shi dawowa ya samu yin aikin hajji to wannan bai halatta ya fita daga garin Makka ba. Amma akwai karin bayani nan gaba da zamu kawo:
4. Bai halatta ba mu fita daga garin Makka bayan Umarar Tamattu'i ya zama dole mu zauna a Makka, sai mu yi harami mu tafi Arfa, sai dai idan muna da larura ko kuma mun san cewa tabbas zamu iya dawowa kafin yin aikin hajji ta yadda lokaci ba zai kure mana ba. Sannan wadanda suke da larurar fita don wani aiki nasu, ko kuma suna ganin zasu iya dawowa, to su ma yana da kyau idan babu wahala gare su, sai su yi harama da hajjinsu sannan sai su fita daga Makka da haraminsu, su yi ayyukansu su dawo da haramin su zuwa Makka, don su fara ayyukan hajjinsu.
5. Wadanda suke da larura suna masu kaikawo da yawa tsakanin Makka da Madina to a cikin kaikawon su zuwa da dawowa sai su rika yin Umara Mufrada, amma a dawowar karshe da zasu yi wacce ba zasu fita ba har sai sun yi aikin hajji, sai su yi umararsu ta tamattu'i, kuma matukar babu wata matsala ga ayyukansu to sai su zauna a Makka. Amma idan suna yawan zuwa su dawo ne kamar a ce duk wata suna fita sau wani adadi sama da daya suna dawowa to ba dole ba ne su yi Umara Mufrada fiye da daya, amma idan wani sabon wata ya kama kamar zul'ka'ada suka zo Makka suka koma, kuma suna son su dawo a watan zulhijja, to tun da sabon wata ya kama to ya hau kansu dole ne su sake yin harami don yin wata umarar.
6. Amma game da sauran mas'a'loli biyu: Wato yin farauta a yankin Harami a Makka, da kuma cire shukoki da ciyayi to haram ne yin su, da man su haramcinsu bai kebanta da lokacin yin harama da umara ko hajji ba. Don haka duk lokacin da mutum ya samu kansa a cikin haramin Makka to bai halatta ya yi farauta ko cire ciyayi da shuke - shuke ba. Haka ma kula da kwarin da suke wurin kamar fari, sai dai idan mutum ya zo wucewa da mota ya take su ba tare da nufi ba, ko ya taka ciyawa ta cire ba tare da nufi ba, to wannan babu komai a kansa.

Wasu Mas'aloli da Suka Shafi Salla a Wadannan Kwanakin
7. A wadannan kwanankin da muke Makka tsakanin Umarar Tamattu'i da Hajji Tamattu'i, shin sallarmu za mu cika ne ko kuma za mu yi kasaru ne?. A nan mu lura cewa duk mutanen da suka riga suka fara ayyukan Madina da wadanda suka gama ayyukan Madina duk suke a Makka sun riga sun kammala ayyukan umara suna jiran fara ayyukan hajji, idan zasu zauna kwana goma a Makka ko sama da hakan kafin zuwa ranar Arfa to zasu yi sallarsu cikakkiya ce domin ba sa cikin matafiya ke nan.
8. Haka nan a Arfa da Mash'ar, da Mina zasu cika sallarsu ne; domin bayan sun yi kwana goma a Makka zuwan su wadannan wurare ba ya cutar da wannan zaman nasu, don haka zasu cika sallarsu ne, kuma haka nan bayan mun dawo Makka zasu ci gaba da cika sallarsu ne.
Amma idan ya kasance ba zamu yi kwana goma a Makka ba kafin tafiya Arfa kamar a ce mun yi kwanaki shida a Makka sannan sai muka tafi Arfa da Mash'ar da Mina to duk a Makka da wadannan wuraren muna da ikon mu cika salla ko mu yi kasaru domin a wadannan wurare a bisa fatawar Sayyid khamna'I muna da zabin ko mu cika ko mu yi kasaru, kuma babu bambanci tsakanin tsohuwar Makka da sabuwar Makka a wannan hukuncin, duk inda muke zamu iya yin kasaru ko mu cika bisa zabinmu.
9. Amma a Arfa da Mina da Mash'ar babu hukuncin zabi domin su ba Makka ba ne, don haka tun da mu matafiya ne domin ba mu yi kwana goma a Makka ba, to su a wadanann wuraren zamu yi kasaru ne, domin hukuncin zabin cikawa ko yin kasaru ya kebanci Makka ne kawai.
Sannan bayan mun dawo Makka idan muka yi niyyar zama kwanaki goma mafi karanci a Makka sai mu cika salla domin ke nan mu ba matafiya ba ne, amma idan ba zamu kai kwanaki goma a Makka ba bayan dawowa, to tun da Makka wuri ne da muna da zabi ko mu cika ko mu yi kasaru zabi ya rage gare mu mu cika ko mu yi kasaru kamar yadda yake a hukuncin matafiyi a Makka.

Salla a Masallaci Mai Alfarma
10. A bisa yadda ya zo a ruwaya cewa salla a masallaci mai alfarma na Makka tana da ladan salla dubu dari ne. Sai dai ka da mu dauka cewa idan muna da sallolin ramuwa sai mu yi salla daya a madadin ramuwa sai ta dauke wannan ramuwar saboda yawan ladan salla a harami, wannan ba haka ba ne, kowane hukunci yana da nasa abin da ya kebance shi daban, don haka salla daya a nan ba ta dauke sallolin ramuwa masu yawa da suke kanmu.

Dawafin Mustahabbi
11. Bayan mun kammala umara mun sanya kayan mu na gida, to muna iya yawaita yin dawafin mustahabbi, shi kewaye bakwai ne kamar yadda yake a dawafin umara da hajji. Kuma yana da sharudan yin alwala da tsarki da tufafi da sauran su kamar na salla. Idan babu wani cunkoso kuma ba zamu damu mutane ba, sannan muna da damar yin dawafi sai mu rika yin dawafi gewaye bakwai, bayan kowane gewayen ka'aba bakwai sai mu yi raka'a biyu kamar dai yadda ya gabata a jawabin dawafin wajibi.
12. Dawafin mustahabbi muna iya mutane masu yawa shi komai yawansu mu ba su ladan sa, sai mu yi dawafi wanda yana nufin gewaye ka'aba sau bakwai da salla raka'a biyu bayansa, wannan shi ne ake kira dawafi. Idan muka yi haka sau daya to dawafi daya ke nan, a rana muna iya yin dawafi masu yawa ga kanmu da mutane daban - daban, kamar yadda muna iya yin dawafi daya idan ba zamu iya yin da yawa ba da niyyar kawukanmu da duk wanda muke niyyar yi masa dawafi baki daya komai yawansu.
13. Muna yi wa masu dawafin mustahabbi nasihar cewa ka da su damu masu yin dawafin wajibi, don haka su hakura sai an samu karancin mutane. Akwai kwanaki masu cunkoso musamman hudu, da biyar ga zulhajji, da kwanakin 11, 12, 13, 14 ga wannan watan. Masu dawafin wajibi suke da hakki fiye da mai yin na mustahabbi don haka ka da ya dame su.
14. Wannan shi ne dawafin mustahabbi.

Dawafin Bankwana
Akwai wani irin dawafi shi ma da ake kiran sa da dawafin ban kwana wanda yake mustahabbi ne yin sa, shi ne dawafin karshe da muke yi kafin mu bar Makka yayin da zamu koma kasashenmu baki daya bayan gama dukkan ayyukanmu. Shi ma ana yin sa kamar yadda ake yin sauran dawafofi da sallarsa bayan makamu Ibrahim kamar dai na wajibi da mustahabbi da aka yi bayanin yadda ake yin su a baya. Kuma duk da an kira shi da dawafin ban kwana, amma ana son mai yin sa ya yi niyyar cewa; yana son Allah ya dawo da shi zuwa ga wannan dakin.

Tilawar Kur'ani
15. Makka ita ce mahallin saukar Kur'ani, don haka an so yawaita karanta Kur'ani a Makka a wadannan kwanakin da muke cikin Makka, akwai lada mai yawan gaske a cikin karanta Kur'ani a Makka. An so mafi karanci mu sauke Kur'ani a Makka, kuma idan mun karanta a masallaci to ragowarsa sai mu karanta shi a gida mu ci gaba da karantawa, ka da mu yi amfani da lokutan da muke da su a hira marasa amfani.
Idan da mutum bai kammala saukar Kur'ani ba har ya fita zuwa Arfa da Mina da Mash'ar, to tun da can ba Makka ba ne, sai ya karanta wani wuri daban ba inda ya tsaya ba a Makka, in ya so idan ya dawo Makka sai ya ci gaba daga inda ya tsaya har sai ya kammala saukar kur'aninsa baki daya a garin Makka.

Masallatai da Wuraren Makka
16. Akwai wurare masu yawan gaske na ziyara a Makka, duk da cewa abin takaici an rusa da yawa daga cikinsu; daga cikin wuraren ziyara akwai kabarorin Hujun ko makabarta Abu Dalib wacce aka binne kakannin manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata gare shi da alayensa masu tsarki) da waliyyan Allah masu yawa a wurin, da Sayyida Hadiza (Tsira da amincin Allah su tabbata gare ta, da zuriyarta masu daraja). Akwai masallatai kamar masjidul jinni (masallacin aljanu), da masjidus shajara, da masjidul raya, da sauran masallatai da za a kai musu ziyara, sai dai wadannan masallatan a rufe suke ko da yaushe, suna zama a bude ne a lokutan sallar azahar da la'asar da magariba da issah, da kuma tsakanin sallar azahar da la'asar, da tsakanin sallar magariba da issha kawai. Don haka sai ku samu damar yin ziyarar su a wadannan lokutan.
Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Thursday, April 12, 2012

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)