Muassasar alhasanain (a.s)

Ranar Idi a Mina

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5


Darasi Na Goma: Bayanin Mas'aloli Da Hukunce-Hukunce Da Suka Shafi Ranar Idi

Shirye - shiryen Tafiya Mina a Ranar Idi
Bayan mun baro Muzdalifa a goma ga watan zulhijja sai mu kama hanya zuwa Mina, tsakanin Muzdalifa da Mina wasu 'yan mitoci ne kamar mita dari, da mun fito daga mash'ar zamu ga wurin da aka rubuta shi karshen Mash'ar, don haka ne ma a zama a Mash'ar bai halatta mu wuce wannan sanarwar ba, muna wucewa zamu ga an sa karshen Mina, to mun shigo Mina ke nan, Mina wurin ne da yake tsakanin wasu duwatsu manya kuma yana da fadi sosai, tsakanin wannan sanarwar da aka sanya karshen Mina wato bayan mun shigo cikinta daga iyakar Mash'ar zuwa wurin Akaba (Dutsen da shi kadai ne za a jefa ranar goma ga wata) ya kai kilo mita biyar. A ranar Idi muna da ayyuka uku ne da zamu yi kamar haka: Jifan Akaba, yankan layya, da kuma aski ko rage gashin kai (suma).
1. Zamu kawo bayanin kowanne a jere.

Jifan Akaba
Idan muka shiga Mina to karshen Mina bayan an wuce masallacin Haif akwai amudai masu tsayi da ake jifa, a yau sun yi benaye hawa - hawa sun kara tsayinsu don a yi jifa ta saman su, a da suna da fadin kamar mita daya ne, amam a yau sun mayar da su kamar Katanga ce mai fadin mita 25, da in Allah ya so zamu yi maganar wadannan amudai da ake jifa.
2. A ranar idi ya zama dole ne mu jefi amudi na uku da aka fi sani da amudi mafi girma, ko amudin Akaba, zamu wuce na daya da na biyu har sai mun kai gare shi sai mu jefe shi da duwatsu guda bakwai.

Mas'alolin Jifan Akaba
Akwai mas'aloli game da jifan wanan amudin da zamu kawo su kamar haka:
3. Jifan amudai kamar sauran ayyukan hajji ne shi m ibada ce ga Allah da za a yi niyya yayin yin sa, don haka jefa duwatsu ma suna da tasu niyyar, kuma ba a so duwatsun su zama kanana sosai ko manya sosai, don haka dole ne su zama matsakaita, girman sa kamar daidai kan dan yatsa ne.
4. Lokacin jefan Akaba a ranar goma wato ranar Idi, da lokacin jifan amudai uku wato Akaba da sauran amudai biyu a ranar 11, da 12, ga wata yana kasancewa daga bullowar rana zuwa faduwarta ne, wato wajibi ne ya kasance a cikin wuni ba tare da jinkirtawa zuwa dare ba.
5. Dole ne dutse ya samu wannan bangon da ake jifa, a yau an samu sauki yana da fadi tun da an mayar da shi kamar bango, amma a da yana kamar amudi ne a tsaye sai samun sa ya yi wahala hada da cunkoso mai yawan gaske da turereniya.
Idan da wani zai jefa wani dutse sai wani dutsen daban da yake hannunsa wanda ba shi ya yi niyyar jefawa ba, ko dutsen ya fadi kasa ko kuma hannunsa ya karkace sai bai same shi ba, to wannan jifar ba ta yi ba, sai ya sake jefa wani, amma ba daga farko ne zai faro ba. Misali idan ya jefa na daya da na biyu da na uku suka samu, amma na hudu sai ya fadi bai samu ba, ko wani daban ya fita daga hannunsa ba wanda ya yi niyyar jefawa ba, to sai ya sake jefa wani a matsayin ci gaba da jifa wato na hudu ke nan, ba wai ya sake tun daga farko ba.
Kuma adadin duwatsun da za a jefa guda bakwai ne, idan kuwa ya gama jifa sai ya yi kokwanton shida ya jefa ko bakwai, to sai ya sake jefa wani a matsayin cikon na bakwai don ya samu nutsuwar cewa ya kammala duwatsunsa guda bakwai.
6. Wata mas'alar ita ce; ya zama wajibi a jefa dutse, don haka da wani zai zo kusa da amudin da ake jifa, sai dutsen hannunsa ya fadi ya gangara ya samu amudin to wannan jifan bai yi ba, sai ya sake shi. Haka nan da zai dora shi a jikin amudin shi ma dai bai inganta ba.
Sannan akwai mas'ala muhimmiya da zamu kawo cewa; a da can wannan bangon babu shi da fadi haka kamar yadda muka fada, wani amudi ne maras fadi sai suka kara masa fadi, kuma daidai wurin amudin yana tsakiya ne, don haka idan mun je jifa mu yi iyakar kokari mu ga cewa mun jefi tsakiya ne, idan kuwa cunkoso ya hana mu saboda tsakaninsa, sai mu yi kokari mu jefi wurin da ya fi ko'ina kusa da tsakiyarsa, domin asalin amudin yana tsakiyar garun ne.
7. An yi wa wurin jifa hawa hawa ne, don haka duk mai dama yana jiya jifa ta sama ma, sai dai bisa ihtiyadi idan zai yiwu ya yi jifa a kasa shi ne ya fi kyau.
8. Muna da bayanai masu muhimmanci guda uku game da duwatsun da ake jifa da su: Na farko; duwatsun da ake jifa da su dole su kasance daga cikin haramin Makka ne aka tsince su, don haka ne ana iya dibar su daga garin Makka, birnin Makka yana kamawa tun daga Tan'im ne zuwa cikin gari ya wuce har zuwa daya bangaren Makka da ya hada da Mina da Mash'ar duk suna cikin haramin Makka, amma Arfa ba ta cikin haramin Makka tana wajensa ne, don haka jifa ba ya inganta da duwatsun da aka dauko su daga Arfa.
9. Wani sharadin shi ne ka da ya kasance an yi jifa da dutsen, don haka idan wani ya yi jifa da shi kuma ya samu garun da ake jifa to jifa da wannan dutsen ba ya inganta.
Sharadi na karshe shi ne dole wannan dutsen ya kasance na halal ne. Don haka wajibi ne ya kasance mu ne muka debo shi ko kuma wani ya debo ya ba mu shi da yardarsa ya kawo mana. Don haka mu kiyaye daukar duwatsun wasu sai mun tabbatar da yardar su ne.
10. Don haka idan ba mu da isassun duwatsu to sai mu ara daga hannun wasu. Sannan bisa ihtiyadi mu kiyayi daukar duwatsun da muka ga sun zuba a kasa a wurin tsayawar masu jifa.

Wasu Bayanai da Suka Shafi Jifan Akaba
Muna son mu dan kara bayani game da abin da ya shafi duwatsu, kamar yadda muka kawo ne cewa ka da su kasance kanana sosai, ko manya sosai, su kasance matsakaita kamar dai girman kan dan yatsa.
11. Sannan ya zama mu muka debo su ko kuma wasu suka ba mu bisa yardar su.
Sannan mustahabbi ne mu tara duwatsun daya bayan daya mu rika dibar su, sai dai babu matsala ko da mun samu wani babban dutse ne sai muka farfasa shi muka mayar da shi 'yan kananan duwatsu.
12. Sannan tsarki ba sharadi ba ne yayin jifa, don haka ba dole ne sai an yi alwala ba, duk da ya fi kyau da muna da alwalar. Sannan duk sa'adda za a jefa dutse sai a yi kabbara "Allahu Akbar".
Haka nan yayin jifan wadannan bangaye guda uku muna iya tsayawa ta ko'ina ne mu jefe su duk babu wata matasla ko ta wane bangaren su ne.

Jifan Dare
13. Da farko mun kawo cewa lokacin jifa tun bullowar rana ce zuwa faduwar rana, sai dai mata su suna iya jifan garun Akaba baki dayansu a ranar Idi ko da kuwa ba su da matsala, babu bambanci da mai rashin lafiya, da tsohuwa da mai jin karfi mai lafiya, sai dai wannan hukuncin ga mata ya kebanci jifan ranar idi ne kawai. Amma jifarn bangaye da dare a sauran kwanakin ranar goma sha daya da goma sha biyu ya kebanta da masu uzuri ne maza ne ko mata kamar mara lafiya, da marasa karfi saboda tsufa ko wata tawaya da sauran su.
Idan mace zata iya jifa da kanta da rana a kwanakin 11 da 12, to bai halatta ta yi jifa da dare ba.
Don haka a ranar goma ga wata mata baki daya zasu iya zuwa su yi jifa, haka nan marasa lafiya da tsofaffi da masu tawaya, amma mazajen da suke raka wadannan mata ko marasa lafiya da gajiyayyu zuwa jifa tun da su ba masu uzuri ba ne, su ba zasu iya jifa da dare ba, don haka sai su raka su don su yi jifa da dare, sannan su kuma su koma da rana su yi jifan su.
Idan da wata mata mai uzuri kamar tsufa ko rashin lafiya aka kai ta wurin jida da dare sai ta kasa bayan ta isa wurin jifan Shedan, to sai kuma ta wakilta wani wanda shi ba shi da wani uzuri don ya yi mata jifan, to shi wannan mutumin (mai rakiya ne ko wani daban) ba zai iya yi mata jifa a wannan daren ba, don haka sai dai ya bari sai gari ya waye sannan sai ya yi mata jifan, kuma wannan wakilin ko da kuwa mace ce ita ma.

Yanka Dabba
14. Yanka dabba shi ma dole ne ya kasance da nufin bauta da ibada ga Allah kamar dai yadda muka kawo game da dukkan sauran ayyukan hajji. Wadannan dabbobi su ne dabbobi uku kawai, ba a yarda da wanka wani ba ko da kuwa ya fi su daraja a gun mutane, wadanan dabbobin su ne dai wadanda ake yin zakka da su, da suka hada da; rakuma, shanu, tumaki da awaki. Kuma yanka rakuma ko shanu ya fi yanka kananan dabobi kamar tumaki da awaki.
15. Akwai wani wuri da ake kira "Wadil Mu'aisam" to wannan wurin ne ake yanka dabbobin layyar, shi wuri ne wanda wani dan dutse ya raba tsakaninsa da Mina. Wannan wurin akwai inda ake kira da "Mahotar Wadil Mu'aisam" da a nan ne ake yanka wadannan abubuwan yanka wanda yake daga ayyuka muhimmai na hajji domin neman kusanci da Allah.
16. To yanzu dai mun san dabbobin da ake yankawa.

Lokacin Yanka
Ana yin yanka ne ranar idi kamar yadda aka sani, kuma ya gabata cewa lallai ne bisa ihtiyadai a kiyaye jeranta wadannan ayyukan a ranar Idi kamar haka: da farko jifan Akaba, sannan sai yanka, sai kuma aski ko rage sumar kai. Amma wadanda ba su da abin da zasu yanka, sai ya samu da dare, to idan zasu bar shi yana iya zuwa ya yanka ko ya wakilta mai yanka masa idan akwai, ko kuma ya bari sai ranar sha daya da safe sai ya yanka.
Amma wanda bai samu abin yanka ba ranar goma baki daya, to sai ya yi sauran ayyukan da suka hada da aski ko rage suma, don ya samu ya iya cire kayan haraminsa ya sanya na gida, ka da ya jira sai wasu ranakun.
17. Yanka dabbobi shi ne kawai aikin da kowa yana iya bayar da wakilci a yi masa shi, ko yana da ikon yi da kansa ko kuma ba shi da ikon yanka da kansa, ko yana da uzuri ko babu wani uzuri.
18. A wadannan shekarun ba sa bayar da dama ga mahajjata su tafi wurin yanka da kansu, sannan babu ma wurin yanzu, mata da man can ba sa ba su damar zuwa. Don haka kowa dole ne ya bayar da wakilcin yanka masa layyarsa. Saboda haka mutanen da suke jagorantar mahajjata sai su dauki wannan nauyin na ganin kowane mahajjaci ya samu an yanka masa abin yankansa, domin ya sauke wannan wajibi da Allah madaukaki ya dora masa.

Wurin Yanka
Wurin yanka wuri ne da aka yi wa alama da kaloli, kuma akwai takardu da suke dauke da sunayen mahajjata daidai gwargwadon adadinsu, duk wanda aka kawo sai a duba takardar a yanka da sunansa, don haka ne ma yanka wa mutane dabbarsu yake tafiya da sauri. Idan masu yanka sun san ba zasu samu damar yanka dabbar mahajjaci a ranar idi ba, to sai su sanar da shi don ya yi wajibi na uku a wannan ranar wato aski ko rage suma, sannan ya cire kayan haraminsa ya sanya na gida kamar yadda yake a jere.
19. Mu lura sosai cewa matukar ba a ba ku labarin cewa an yi muku yanka ba, to ka da ku sake ku yi wajibi na gaba wato aski ko rage sumarku. Mu sani wurin yanka shi ma kamar sauran wajiban Mina ne dole ne ya kasance a cikin Mina, sai dai abin takaici sun yi wata mayanka a wajan Misa sai dai kusa da ita ne. A bisa fatawar da Sayyid Khamna'i ya bayar ba laifi a yi yanka haka nan a wurin da suka yi mayanka tare da sauran musulmi baki daya.
20. Game da dabbar yankawa ba dole ba ne ta kasance namiji, mace ma kamar tunkiya ko shanuwa ko rakuma duk babu komai, kuma ta fuskacin shekaru da sauran sharudda su ma duk za a kiyaye. Masu yanka bisa kwarewa ta shekaru da suke da ita duk sun san wannan sharudan.
21. Wani lokaci ana samun aibobi ga dabbobi kamar huda a kunne, ko kuma an yanke kunnen tun tana karama, sai ta girma sai wannan yanka ya yi girma saboda girmanta, to wannan duka babu wani aibi a ciki, amma da an yanke ta ne ta yadda aka ragi namanta to a nan akwai matsala ba zata wadatar ba. Don haka masu zuwa wurin yanka sai su kula da sharudan da aka ginda game da abin yanka.

Aski ko Rage Suma
22. Karshen aikin da za a yi a ranar idi shi ne yin aski ko rage suma wato saisaye, ko kuma rage gashi ko yanke farce da mun riga mun yi nuni da su a bayanin ayyukan umara.
23. Sai dai duk wanda yake hajjinsa na farko ne to dole ne ya yi aski baki daya, amma wanda ya taba zuwa aikin hajji to shi yana da zabi ko ya yi aske ko ya rage suma, duk da dai aski ya fi lada.
A lura sosai cewa ko da mutum ya taba zuwa umara sau da yawa ma matukar bai taba yin hajji ba, to wannan hajjin da ya yi shi ne hajjinsa na farko don haka dole ne ya yi aski ba rage suma ba. Kuma yin aski ba shi da bambanci a hajjin farko cewa hajjin nasa ne ko na wakilci ne, ya zama wajibi a kansa ya yi aski ne.
Sannan kuma dole ne ya kasance da reza ce za a yi askin, don haka injin aski na wuta da sauran su ba sa iya isarwa ga wannan, domin mahajjaci ba zai iya rage gashi da inji ba da farko sannan kuma sai daga baya ya sanya reza, dole ne dai ya sanya reza tun farko ya aske gashin kansa baki daya. Haka nan ba zai iya rage wani bangare ba sannan sai aske shi a haka har ya gama, dole ne tun farko ya sanya reza ya aske gashinsa baki daya.
24. Duk da aski ya shafi maza ne, amma mata ma suna yanke wani abu daga gashinsu ko faratansu da nufin ibada ga Allah a matsayin daya daga ayyukan Hajji Tamattu'i.
25. Dole ne aski ko rage suma ko yanke farci su kasance a cikin Mina ne, don haka sai a lura sosai, mutumin da ya fita daga Mina kamar ya je garin Makka bayan jifa, ko kuma ya tafi mayanka da take yanzu kamar yadda muka ce tana wajen Mina ne, to ya kula sosai ka da ya yi aski daga can, dole ne sai ya dawo cikin Mina sannan zai iya yin wadannan abubuwan.
26. Wadannan ayyuka guda uku dukkan su dole ne su kasance a Mina wato jifan Akaba, yanka, da aski, sai dai wanda bai samu damar yanka ba to sai ya yi aski, don haka wanda ba a yanka masa layyarsa ba sai ya yi kokarin yin aski a wannan ranar ka da ya bari rana ta fadi bai yi aski ko saisaye ba. Haka nan da sai da yamma aka ba shi labarin an yi masa yanka sai ya yi askinsa lokacin, domin idan ma ya yi askin bayan faduwar rana da dare to babu komai dai, ba dole ba ne don dare ya yi ya jinkirta kuma sai gobe da safe.

Fitar Jini daga Kai Lokacin Aski
27. Yayin aski idan mutum ya yanke kansa to babu komai a kansa, ta yiwu wasu su yi tunanin saboda haramcin fitar da jini wani abu ya hau kansa sai dai ba haka ba ne game da aski domin bisa dabi'ar yin aski ta yiwu a yanke.

Marhalolin Fita daga cikin harami a Hajjin Tamattu'i
28. Yana da kyau idan zamu tafi Arafa mu dauki wasu kayan gida tare da mu don sanyawa a ranar idi, domin bayan mun yi jifan Akaba da yanka da aski, to sai mu cire tufafin harami mu sanya na gida. Saboda bayan an yi aski to mafi yawan abubuwan da suka haramta ga mai harami zasu koma halal gare shi, daga ciki akwai kaya, don haka sai ya cire kayansa na harami zani da mayafi ya sanya na gida.
Sakamakon abubuwan da aka haramta ga mai umara su ne aka haramta ga mai yin hajji don haka ba zamu maimaita su a nan ba. Sai dai bambancin shi ne; a umara idan muka rage sumarmu to duk abin da yake haram gare mu sakamakon umara yana halatta gare mu, amma a hajji bayan rage gashi ko aski wasu daga ciki ne suke zama halal gare mu ba duka ba.
29. Bayan aski komai yana halatta ga mai hajji ban da shakar abu mai kanshi, da kuma mata (ga namiji, ko namiji ga mace), sai bayan mun je Makka ne mun yi dawafin hajji da sallarsa, da kuma sa'ayi tsakanin Safa da Marwa ne, sannan shaka ko sansana abu mai kamshi yake halatta gare mu. Amam miji da mata ba sa halatta ga junansu sai bayan sun yi dawafin mata da sallarsa. Don haka da wannan bayanin mun san yadda zamu fita daga aikin hajji baki daya ke nan.

Wurare Masu Tsarki a Mina
30. A Mina akwai wurare masu tsarki na ziyara da wasu masallatai, sai dai abin takaici sun rusa wasu daga masallatan: daga ciki akwai masallacin Akaba wanda yake daga dama bayan an wuce wurin jifa kadan, shi ne mahallin bai'ar mutanen Madina ga annabi (Tsira da amincin Allah su tabbata gare shi da alayensa masu tsarki) a bai'ar akabar Mina wanda har yanzu akwai alamunsa da suka dan rage ana kiran sa da masallacin Kabsh.
31. Daga bangaren Mash'ar kuwa da muke shiga Mina har zuwa karshen Mina akwai masallacin Khaif, wanda yake kan hanya kafin a karasa wurin jifa, wasu bisa kuskure suna cewa da shi masallacin Khif, masallaci ne mai falala da lada mai yawa, sai dai abin haushi ko da yaushe a dukkan tsawon shekara a kulle yake, suna bude shi ne a kwanakin Mina kawai, wato 10, 11, 12, ga wata kawai. Sai dai wani abin haushi da yawa mahajjata suna mayar da shi wurin kwanan su ne, ta yadda suke cika shi babu wata dama ga wani na yin salla a ciki, sai a lokutan sallar farilla.
32. Ranar idi ta wuce, sai mu kwana a daren ranar sha daya a wurin da nufin kwana a Mina wanda yana daga cikin wajiban ayyukan hajji, wato kwana a Mina, amma sauran hukunce - hukuncen kwana a Mina zamu yi bayanin su a darasi na gaba.
Wassalamu alaikum wa rahamtullah wa barakatuhu.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Thursday, April 12, 2012

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)