Muassasar alhasanain (a.s)

Akidar Wahabiyanci

3 Ra'ayoyi 03.0 / 5

WALLAFAR: JA'AFAR SUBHANI
Akidar Wahabiyanci

FASSARA: YUNUS MUHMMAD SANI
DUBAWA: HAFIZ MUHAMMAD SA'ID
Wahabiyanci Akidu Da Aiki A bahsin da ya gabata mun yi bayani a kan cewa, wannan akida ta Ibn Taimiyya ta bayyana ne a lokacin da al'ummar musulmi suke fuskantar tsananin hare-hare daga gabas da yamma a hannun kiristoci da Magul, wato lokacin da suke tsananin bukatuwa zuwa ga hadin kai a kan akidar da ta hada su wato akidun addinin na asali kamar imani da Allah da Manzonsa, ranar lahira da sauransu.
To ana cikin wannan hali ne wanda ko abin da Ibn Taimiyya yake fada yana da inganci to muna iya cewa ya zo da wannan kira nasa wanda ya raba kan al'umma a lokacin da yake mawuyacin hali ga musulmi. Duk da cewa kamar yadda muka gani a baya daga manyan malamai da suka yi magana a kan wadannan akidu nasa, kuma kamar yadda zamu gani a nan gaba dangane da wannan akida akwai maganganu masu yawa a kan rashin ingancinta.
Kuma kamar yadda muka gani, tun bayyanar wannan akida ta Iban Taimiyya muka ga yadda ya fuskanci kalu bale daga manyan malaman zamaninsa, wannan ne ya sanya aka kyamaci wannan akida tasa, wato bata samu karbuwa ba daga al'ummar musulmi. Amma abin bakin ciki bayan wucewar karni biyar da bayyanar Ibn Taimiyya sai wannan akida ta sake bayyana ta hanun wani malami mai suna Muhammda Bn Abdul Wahab, wato ya sake farfado da wannan akida wacce take raba kan al'ummar musulmi ta yadda abin zai kai ga kashe-kashe a tsakaninsu.

Jefa Rarraba A Tsakanin Musulmi A Mafi Mawuyacin Hali
Abin bakin ciki kamar yadda ya kasance Ibn Taimiyya ya zo da wannan akida tasa a lokacin da musulmi suke tsananin bukatuwa zuwa ga hadin kai, haka nan Bn Abdul wahab shi ma ya sake jaddada wannan akida yayin da musulmi suke tsananin bukatar hadin kai, muna ma iya cewa wannan lokacin ya fi zama mawuyacin hali a kan zamani Ibn Taimiyya.
Yada wannan akida ta Ibn Taimiyya ta hanyar Muhammad Bn Adulwahab wacce ta haka ne ake yi wa wannan akida lakabi da wahabiyanci. Sun ci gaba ta yada wannan akida a cikin garuruwan Najad da sauran garuruwan Hijaz kamar su Iraki, Yaman, Sham da dai sauransu, tare da taimakon wasu manyan kabilun Najad. A farkon karni na sha uku wato karni na sha tara na miladiyya wannan al'amari ya auku a wadannan garuruwa. A wannan zamanin ne musulmi suke fuskantar tsananin hare-hare na 'yan mulkin mallakan kiristoci.
Turawan Birtaniya da karfin tuwo suka kwaci wani bangare mai yawa na India wanda yake a karkashin ikon musulmi wanda ya hada garuruwan Kabul da sauran sassan kasashen tekun farisa ta yadda ya hada har da kasar Iran.
Haka nan Turawan Faransa karkashin jagorancin Naflion suka kama Garuwan Sham da Misra da Palasdin.
Haka nan Turawan Rusia wadanda suke da'war rikon Kanbun shugaban kiristoci a wannan zamani suma suna cikin yunkuri domin kama garuruwan Iran da sauran inda daular Usamaniyya take iko, wato daga Kustantaniyya zuwa abin da ya kai palasdin har zuwa garuruwan Tekun Farisa. Ta haka ne suka yi nufin kama garuruwan Iran da duk wasu garuruwan daular Usmaniyya da suke cikin kasashen turai da wani bangare na Rusia (Kafakaz).
Ta bangare guda kuma Amerikawa suma suna da kwadayin kama wasu daga cikin garururwan musulmi kamar wasu kasahsen arewancin Afrika sakamakon haka ne suka kai hare-hare zuwa Libiya inda suka yi ruwan bama-bamai a kan garuruwan Kasar Libiya da Algeriya domin su samu iko a kan kasashen musulmi. Haka nan ta bangare guda yakoki na faruwa tsakanin Kasar Otrish da daular Usmaniyya a kan kasar Saberiya tare da taimakon jirgin yakin ruwan Kasar Holand da Birtaniya yayin da suka kewaye kasar Algeriya, duk wannan abu ya faru ne a wannan zamani.
A wannan lokaci ne da musulmi suke tsananin bukatar hadin kai domin su fuskanci wannann barazana ta makiyansu, kwatsam sai Muhammad Bn Abdulwahab ya tashi domin yada wannan akida da take raba kan al'ummar musulmi. Yayin da ya zargi musulmi da laifin neman ceto daga waliyyan Allah da ziyarar kaburburan waliyyai, yayin da yake ganin wannan aiki shirka ne kuma yana wajabta a kashe wanda yake yin wannan aiki. A wannan lokaci ne ya kira wasu daga cikin larabawan kauye domin su tashi su yaki garuruwan da musulmin Sunna da Shi'a suke zaune ta yadda zasu kashe su sannan su kwashe dukiyoyinsu a matsayin ganimar yaki da kafirai domin kawai suna ziyarar waliyyai kuma suna neman ceto daga garesu.
Abin da yake da wuyar fahimta a cikin wannan al'amari kuwa shi ne, yaduwar wannan fatawa ta Muhammad Bn Abdulwahab a matsayin fatawar malami fakihi ta yadda yake kafirta musulmi duniya da kwadaitar da mabiyansa a kan yakar musulmi da kwashe dukiyoyinsu a mastayin ganimar yaki domin tuhumarsu da yake a matsayin mushirikai, kuma masu bautar gumaka. Wanda wannan aiki na Bn Adulwahab ya kwashe tsawon wadannan karnoni guda biyu na karshe da muke cikinsu, wanda wannan fatawa tasa wani abu ne wanda yake sabo a cikin al'ummar musulmi.
A cikin littafinsa mai suna (Kashfu shubhat) yana cewa: "Wadanda suke daukar Mala'iku da annabawa a matsayin masu ceto ko wadanda zasu kusantar da su zuwa ga Ubangiji, to lallai wadannan jininsu ya halatta kuma ya halatta a kashe su".
Mugun abun da yake cikin wannan akida ko mazhabar wahabiyanci yana iya bayyana a ta'addanci da yake faruwa a Pakistan da Afganistan a yau, wanda yake wani abu mai ban al'ajabi kuma mai wuyar fahimta.
A nan zamu yi bincike ne a kan rayuwar Muhammad Bn Abdulwahab wanda yake shi ne mujaddadin wannan akida ta wahabiyanci wacce ta samo asalinta daga Ibn Taimiyya, sannan mu yi bayanin akidojin wannan mazhaba ta wahabiyanci.
Muhammad Bn Abdulwahab an haife shi a shekara ta 1115BH a garin Uyaina wanda yake gari ne a yankin Najad da ke kasar Saudiyya. Mahifinsa kuwa shi ne Abdulwahab wanda mutumimn kirki ne mai tsoron Allah, sannan kuma ya kasance daya daga cikin alkalan wannan yanki. Muhammad Bn Abdulwahab ya koyi fikihun Hambaliyya a garinsu wato Uyaina. Sannan ya tafi Madina domin karo ilimi, a can ne fa ya ci gaba da koyon hadisi da fikihu.
A lokacin da yake karatunsa a garin Madina ya kasanshe a na jin wasu kalamai wadanda suke hikayar wata sabuwar akida, sakamakon haka ne malamansa suka damu a kan abin da zai faru daga gareshi a nan gaba, suna cewa: Idan har wannan mutum ya ci gaba da kira zuwa ga addini to tabbas zai batar da mutane".
Bayan wani lokaci Muhammad Bn Abdul wahab ya bar Madina zuwa wasu garuruwan musulmi a inda ya yi shekara hudu a Basra sannan ya yi shekara biyar a Bagdad sannan ya yi shekara daya a garuruwan kurdawa, sannan ya yi sheka biyu a Hamadan. Bayan wani lokaci kuma ya bar nan ya koma Isfahan ya zauna can sannan ya wuce Kom ya zauna a can zuwa wani lokaci. Sannan ya bar nan zuwa Basra wanda a kan hanyarsa ta zuwa Basra ne ya tsaya a garin Ihsa, daga nan ne kuma ya tafi Huraima inda yake nan ne garin da babansa yake zaune.
Duk tsawon lokacin da mahaifinsa yake raye bai cika yin magana ba, sai dai wani lokaci jayayya takan kama tsakaninsa da mahaifinsa. Amma bayan mutuwar mahaifinsa a shekara ta 1153BH sai ya yaye hijabin da ya rufe akidunsa.
Kiran da Muhammad Bn Abdulwahab ya fara yi duk ya rikita al'ummar garin Huraima, abin da ya tilasta masa barin wannan gari zuwa garin Uyaina wanda yake a can ne aka haife shi sai ya koma can domin ya zauna a wannan gari. Ya kasance ya samu alaka da hakimin wannan gari na wannan lokaci wato Usman Bn Ma'amar ta yadda ya gabatar masa da wannan sabuwar akida tasa ya kuma neme shi da ya taimake shi wajen yada wannan akida tasa. Amma ba da dadewa ba sai Hakimin Ihsa wanda yake sama da hakimin Uyaina yake ya nuna rashin jin dadinsa a kan wannan aiki nasa. Sannan ya ba shi umarni da ya fitar da Muhammad Bn Abdulwahab daga wannan gari.
Sakamakon ya zamar wa Muhammad Bn Abdulwahab tilas a kan ya zabi gari na uku domin ya zauna can, sai ya kama hanyar garin Dir'iyya wato garin da Muhammad Bn Sa'ud yake mulki wanda yake kaka ne ga Ali Sa'ud.
Bn Abdulwahab ya gabatar da da'awarsa ga hakimin wannan gari, kuma suka kulla alkawari a kan cewa Bn Abdulwahab zai dauki bangare malanta yayin da shi kuwa sarkin gari zai dauki abin da ya shafi mulkin gari. Domin su kara karfin wannan dangantaka sai suka samar da alakar aure a tsakaninsu.

Taimakonsa Ga Ali Sa'ud
Muhammad Bn Abdulwahab ya fara da'awarsa domin karfafa hukumar Bn Sa'ud kamar yadda suka yi alkawari. Sakamakon haka ne ba da jimawa ba a ka fara kai hare-hare zuwa garuwan kabilolin da suke kusa ana kashe su ana kuma kwashe musu dukiya. Wadannan dukiyoyi kuwa ba wasu ba ne sai dukiyoyin garuruwan Musulmin Najad wanda an kai musu wannan hari ne sakamakon tuhumarsu da ake yi a kan yin shirka da bautar gumaka, sakamakon haka ne dukiyarsu da rayukansu suka zama halas ga Muhammad Bn Sa'ud wanda yake shi ne hakimin Dir'iyya kamar yadda muka fada a baya, kamar yadda aka sani Alusi yana karkata ne zuwa ga akidar wahabiyanci amma a cikin littafinsa yana hikaitowa daga wani malamin tarihi mai suna Ibn bushr cewa:
A farkon al'amari na san garin Dir'iyya gari ne mai tsananin talauci amma bayan wani lokaci sai ya koma daya daga cikin garuruwa masu arziki, ta yadda ya kasance har makamansu ana yi musu kawa ta musamman. Sannan sun kasance suna hawan dawakai na asali, sannan duk wani abin jin dadi sun kasance suna da shi a wannan lokaci ta yadda harshe ba zai iya siffanta wannan jin dadi ba.
Ya ci gaba da cewa wata rana ina cikin kasuwar Dir'iyya ina kallo yayin da mata da maza kowane yana bangarensa. Sannan a cikin wannan kasuwa akwai zinari da azurfa da sauran kayan ado, sannan ga kayan abinci kamar alkama nama da dai sauran kayan abinci ta yadda mutum ba zai iya fadarsu ba. Na kasance ina jin hayaniyar masu saye da sayarwa a wannan kasuwa kamar yadda kudan zuma ke wucewa, ta yadda wancan yana cewa na sayar wancan yana cewa na siya.
Abubuwa guda biyu ne suka taimaka wajen yaduwar da'awar Bn Abdulwahab musamman a kauyuka.
1-Karfin ikon hukumar Ali Sa'ud.
2-Nisantar mutanen Najad daga cigaban Musulunci da hakikanin musulunci.

Hare-Haren Wahabiyawa A Kan Garuruwan Musulmi
Yakokin da wahabiyawa suka yi a a garuruwan Najad da wajensu sun kasance masu janyo hankali kamar yadda idan aka kai hari a wani gari to duk dukiyar da aka samu a wannan gari ta mayakan ce, wato idan har suna iyawa zasu iya mayar da har gidaje da gonaki wadanda suna iya mayar da su mallakinsu, idan kuwa haka ba ta yiwu ba, to sai su hakura da abin da suka samu na ganima daga dukiyoyi.
Kowace sabuwar akida idan ta bayyana musaman idan tana kira ne zuwa ga tauhidi to farko tabbas zata ja mutane, musamman a inda mutanen wurin ba su da cikkiyar masaniya a kan addini. Lokacin da Muhammad Bn Abdulwahab ya fara kiransa a kan tauhidi da yaki da shirka, wasu daga cikin manyan Najad da Yaman sun karbi wannan kira nasa. A matsayin misali a lokacin da guguwar kiransa ta isa Yaman sai Sarki Muhammad Bn Isma'il mawallafin littafin nan mai Subulu Salam fi sharhi bulugul muram ya yi wata kasida a kan yabon Muhammad Bn Abdulwahab in da yake cewa:
Aminci ya tabbata ga Najad da wanda ya sauka a Najad
Duk da cewa sallamata daga nesa ba zata amfanar ba.
Amma lokacin da shi wannan mutum ya samu labarin hare-hare da kisa da kwace dukiyar da wahabiyawa suke yi a garuruwan musulmi sai ya fahimci cewa Bn Abdulwahab yana kafirta muslmi ne, sannan ba ya ganin darajar jini da dukiyoyinsu, sai ya yi nadama a kan wakar da ya yi ma shi a baya, sai ya yi wata sabuwar kasida wacce take cewa:
Na warware maganar da na yi kan Najad
Domin kuwa ya iganta a gare ni sabanin abin da nake tunani a kansa.
Kisan da wahabiywa suka yi wa al'ummar musulmi a wajen ziyarar Imamai (a.s) wani bakin shafi ne a tarihin musulunci. Wani daga cikin marubutan wahabiyawa mai suna Salahuddin Mukhtar yana rubutawa kamar haka:
A shekara ta 1216 sarki Sa'ud ya tanadi wata runduna wacce ta kunshi mutanen Najad da sauran kabilolin kudanci da na Hijaz da dai sauran al'ummu daban ya nufi Iraki da niyyar kai hari. Ya isa Karbala a watan zulkida yayin da ya kewaye garin Karbala. A lokacin ne sojojinsa suka rusa garun Karbala da karfi suka shiga cikin garin suka kashe mafi yawan mutanen da suke waje da cikin gida da kasuwa. Sannan gab da azahar suka fita daga garin Karbala tare da ganimar da suka kwasa, sannan suka sauka a wani wuri mai ruwa inda ake kira Abyadh. Sai shi Sa'ud da kansa ya dauki kashi daya daga cikin biyar din dukiyar da suka kwaso saura kuwa mayaka suka kassafa a tsakaninsu. Wato duk sojan kasa zai dauki kashi daya sojan saman doki kuwa zai dauki kashi biyu, da haka ne kowa ya dauki rabonsa.
Ibn Bushr wanda yake masanin tarihi ne kuma mutumin Najad dangane da harin da wahabiyawa suka kaiwa Najaf yana rubuta cewa:
A shekara ta 1220BH Sa'ud ya jagoranci runduna mai yawa ya nufi garin nan mai tsarki shaharare na Iraki (wato Najaf) yayin da ya isa wannan gari sai ya zuba sojojinsa a wajen garin. Sannan ya bayar da umurnin kai hari da ruguza wannan gari, amma lokacin da suka isa bakin garin sai suka tarar da katon rami a gefen garin ta yadda ba zasu iya shiga ba. Sakamakon haka ne suka ci gaba da yaki ta hanyar musayar kibau, da haka ne a ka kashe da yawa daga cikin sojojin Sa'ud a wannan lokaci, sannan saura kuwa suka koma da baya, sai suka ci gaba da wawashe dukiyoyin kauyukan da suke gefen garin.
Mai yiwuwa a yi tunanin cewa Wahabiyawa sun kasance suna kai hari zuwa garuruwan da 'yan Shi'a suke zaune ne, amma abin ba haka yake ba, domin kuwa sun kasance suna kai hari ga dukkan garuruwan da musulmi suke zaune abin da ya hada da garuruwan Iraki Sham Hijaz kamar yadda tarihi ya ruwaito da yawa a kan wannan mugun aiki na wahabiyawa, ta yadda a nan ba zamu iya fadar duk abin da ya faru ba, sai dai kawai zamu yi nuni da wasu daga ciki a matsayin misali:
Jamil sadiki Zahawi yana rubutawa musamman dangane da harin da wahabiyawa suka kai wa garin Da'if yana cewa: Daya daga cikin mafi munin ayyukan wahabiyawa shi ne kisan gillar da suka yi wa al'ummar musulmin Da'if ta yadda ba su tausaya wa kowa ba, babba da yaro, mace da namiji, ta yadda har da yaro mai shan nono sukan kwace shi daga mamansa su yanka shi. Wasu mutanen da yawa sun kasance suna cikin koyon karatun Kur'ani duk suka kashe su. A lokacin da ya kasance babu kowa a cikin gida sai suka nufi shaguna da masallatai duk wanda suka samu har suka tarar da wasu suna cikin ruku'u da sujjada duk suka kashe su. Littattafan da suka kasance a hannun mutane wadanda suka hada da Kur'ani mai tsarki da sauran Littattafan hadisi kamar su Sahih bukhari da Muslim da sauran Littattafan hadisi da na Fikh duk suka yi daidai da su. Wannan kuwa ya faru ne a shekara ta 1217Bh.
Bayan kisan gillar da wahabiyawsa suka yi wa mutanen Da'if, sai suka rubuta takarda zuwa ga malaman Makka suna kiran su zuwa ga wannan Mazhaba tasu. Sannan suka yi hakuri har lokacin ayyukan hajji su wuce, ta yadda mahajjata zasu fita daga garin Makka ta yadda zasu kai wa garin Makka hari.
Kamar yadda Sha Fadhl Rasul Kadiri Hindi yake rubuta cewa: Ya ga malaman Makka sun kasance duk sun taru a gefen Ka'aba ta yadda zasu amsa takardar da Wahabiyawa suka aiko musu, suna cikin tattaunawa sai wasu daga cikin mutanen Da'if wadanda aka zalunta suka shigo cikin Harami, sannan suka yi musu bayanin abin da ya auku a garesu. Kuma ya yadu a cikin mutane cewa ai wahabiyawa sun riga sun shigo cikin garin Makka kuma zasu yi wa mutane kisan gilla. Mutanen Makka suka shiga cikin tsoro da tararrabi, kai ka ce kiyama ce ta tsaya, malaman da suke gefen mimbari a cikin masallacin ka'aba duk suka taru waje guda. Sai Abu Ahmid Khadib ya ta shi ya hau mimbari ya karanta takardar da Wahabiyawa suka aiko da amsar da malaman Makka suka rubuta musu a kan raddin akidojinsu. Sannan ya juya ga malamai da alkalai da duk masu bayar da fatawa ya ce: Kun ji abin da mutanen Najad suka ce kuma kun ji dangane da akidunsu. Saboda haka me zaku ce dangane da akidunsu? A wannan lokacin dukkan malaman Makka da ko'ina daga mazhabobin Sunna guda hudu da suka halarci garin Makka domin gabatar da ayyukan hajji suka bayar da fatawa a kan kafirtar Wahabiyawa, Sannan suka yi kira ga Sarkin Makka a kan wajibci a kan ya yi gaggawa ya tashi domin fito na fito da Wahabiyawa. Sannan suka kara da cewa ya wajabta a kan musulmi su taimaka masa a kan wannan al'amari su halarci wannan jihadi na yaki da Wahabiyawa. Sannan duk wanda bai bi wannan umurnin ba kuma ba tare da wata matsala ba to ya yi babban zunubi, sannan duk wanda ya halarci wannan kira yana matsayin mujahidi a tafarkin Allah, sannan idan aka kashe shi yana matsayin shahidi. Dukkansu suka amince da wannan takarda sannan suka sanya hannu a kan wannan fatawa da aka ambata.
Daga nan ne zamu fahimci cewa dukkan bangare guda biyu na musulmi wato sunni da Shi'a ba su amince da wannan akida ta wahabiyawa ba, duk sun tafi a kan rashin ingancinta.
Raddi na farko da aka yi wa wannan mazhaba ta wahabiyanci kuwa ya kasance daga dan'uwan shi kansa Muhammad Bn Abdulwahab wato Sulaiman Bn Abdulwahab, yayin da ya rubuta littafi a kan haka mai suna Assawa'ikul Ilahiyya (wato tsawar Ubangiji) a cikin wannan littafi ga abin da yake rubutawa:
Abubuwan da Wahabiyawa suke cewa shirka ne wanda sakamakonsa ne suke halatta rayuka da dukiyoyin musulmi dukkansu sun kasance ana yin su a zamanin Imamai na musulunci (Shugabannin mazahabobi) amma ba a taba jin wata magana ba daga su wadannan shugabanni, suna cewa masu yin wadannan ayyuka kafirai ne ko kuma sun yi ridda daga addini, ko ba da fatawa a kan a yaki wadanda suke aikata wadannan ayyuka, ko su ambaci garuruwan musulmi da sunan garururwan kafirci kamar yadda wahabiyawa suke yi.

Malaman Da Suka Fara Yin Raddi A Kan Akidun Wahabiyanci
Bayan shi Sulaiman Bn Abdulwahab malamai da dama sun ta shi a kan kalu balantar wannan akidu na wahabiyanci. Wasu kuwa daga cikin wadannan malamai na Ahlussuna su ne kamar haka:
1-Abdullahi Bn latif shafi'i marubucin (Assawa'ik warrudud)
2-Muhammad Bn Abdurrahaman Bn Afalik Hanbali (Tahakkumul mukalidin)
3-Afifuddin Abdullahi Bn Da'ud Hanbali (Assawai'ku war rudud)
4-Ahmad Bn Ali kabani Basri ya yi (risala a kan raddin iyalan Abdulwahab).
5-Shaikh Ada'illahi Makki marubucin (Al'arimul Hindi fi unkil Najdi)
Wadannan wasu daga cikin malamn Ahlus-suna kenan wadanda suka rubuta kalubale a kan akidar wahabiyawa, wanda yake so ya ga sunan wasu daga cikin wadannan malamai sai ya koma littafinmu na Milal wannanhl (juzu'i na 4 shafuka na 355-3 59 domi Karin bayani.
Amma daga cikin malaman Shi'a da suka yi raddi a kan wahabiyawa na farko babban malamin nan ne wato Shaikh Ja'afar Kashiful Gida wanda ya rubuta littafi mai suna (Manhajir rashad liman aradas sadad) wanda a cikinsa ne ya bayyanar da hakikanin al'amurra sannan ya aika wa sarkin Makka Bn Abdul Aziz wanda yake mai tsattsauran ra'ayi ne a kan wahabiyanci.
Sannan daga cikin iyalansa masu girma marigayi sheikh ayatulla Muhammad Husain Asli Kashiful Gida ya rubuta littafi mai suna (Ayatul bayyinat) a lokacin da wahabiyanci suka rushe makabartar Ahlul Baiti (a.s) a Madina ta yadda ya yi raddin akidojinsu tare da amfani da Kur'ani da Sunna.
Littafi mafi girma da aka rubuta dangane da raddin akidun wahabiyawa shi ne (kashiful irtiyab an atba'i Muhammad Bn Abdulwahab) wanda Ayatullahi Muhsin Amuli ya rubuta, yana da muhimanci ga wanda yake so ya samu masaniya sosai a kan wahabiyanci ya duba wannan littafi.

Neman Canza Ra'ayi A Cikin Akidun Wahabiyanci
Wahabiyanci ya ginu ne a kan salafiyya wanda yake fito-na-fito da dukkan wani canji da dan Adam zai samu a rayuwa. A shekara ta 1344 ranar da Abdul aziz Bn Abdurrahaman ya hau karagar mulkin Sa'udiyya sai ya zama tilas a gare shi a kan canja salon mulkinsa ta yadda zai yi daidai da zamanin da yake ciki, ta yadda zai canza rayuwar wahabiyawa wacce take tafiya a kan rayuwar mutanen kauye. Sakamakon shigowar abubuwan zamani ne fa kamar su telfon mota da keke da makamantansu, sai ya yarda da a yi amfani da su, a nan ne fa ya gamu da fushin masu tsattsauran ra'ayin wahabiyanci inda aka zubar da jini ta hanyar (Ikhwan) kamar yadda aka sani a tarihi.
Ahmad Amin marubucin nan na Misra kuwa a cikin bahsinsa a kan wahabiyanci yana da wani nazari wanda yake bayyanar da hakikanin wahabiyanci, wanda yake bayyanar mana da bambancin da yake akwai tsakanin wahabiyanci na zamanin da, da wanda yake akwai yanzu, ga abin da Ahmad Amin yake cewa:
Wahabiyawa ba su yi tunani da kyau ba dangane da cigaban zamani, mafi yawa daga ciki, ban da garuruwan da suke rayuwa a cikinsu ba su dauki sauran garuruwan da sauran musulmin suke rayuwa ba a matsayin garuruwan musulmi ba, domin su a wajensu suna cikin Bidi'a, sannan suna ganin dole ne a yake su.
Amma lokacin da Bn Mas'ud ya hau karagar Mulki, ya fuskanci barazana daga sassa guda biyu ta yadda ya sanya shi dole ya sasanta da su. Na farko su ne shugabannin addini a Najad wadanda suke tsananin biyayya ga Muhammad Bn Abdulwahab, sannan suna tsananin gaba da dukkan sabon abu. Na biyu kuwa suna fuskantar guguwar sabon ci gaba na tsarin hukuma ta yadda yana bukatuwa zuwa ga wadan su na'urori na zamani.
A wannan lokaci sai hukuma ta tsaya a tsakiya wato tsakanin wannan tsanani na mutanen Najad da kuma Guguwar cigaban zamani, ta yadda suka dauki sauran musulmin da suke rayuwa a wasu garuruwa a matsayin musulmi sannan suka dauki ilimin addini da na zamani a matsayin cewa dukkansu abin koyo ne, sannan suka gina tsarin hukumarsu dai-dai- da na zamani.
Amma abin farin ciki shugabanni sa'udiyya sun canza salo a kan wancan tunaninsu na kin yarda da sauran musulmi da fito na fito da dukkan wani sabon abu da sunan gujewa bidi'a, wannan kuwa ya faru ne sakamakon wasu dalilai masu yawa, daga cikinsu kuwa su ne kamar yadda ya kasance Amerika ta yi kaka gida a cikin saudiyya da yadda jamhuriyar musulunci ta Iran take jagorantar fito na fito da sahayuna, wannan ya janyo Sa'udiyya ta canza ra'ayoyinta dangane da Jamhuriyar musulunci ta Iran, sannan suka dawo daga tunaninsu na kafitrta sauran musulmin da ba sahu daya suke ba, Musamman kasancewar hukumar saudiyya ta yanzu wacce ta sanya wa kanta suna da mai hidimar harami guda biyu, ka ga kenan babu wani mai abu mai kyau wanda ya fi sai su dawo su canza ra'ayinsu na da, ta yadda zasu karbi bakuncin dimbin sauran al'ummar musulmi da suke bakuntar Makka da Madina domin aikin Hajji a kowace shekara.
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)