Muassasar alhasanain (a.s)

Ziyarar Kabari5

0 Ra'ayoyi 00.0 / 5

Ziyarar Kabari5

WALLAFAR: JA'AFAR SUBHANI


Girmama Kaburbura Masu Tsarki 2

Mawallafi: Ayatullahi Ja'afar Subhani
Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani
Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id
Kaburburan Manzanni Da Tarihin Magabata Ma'abota Tauhidi
Tafiye-tafiye domin bude ido zuwa wuraren da aka rufe annabawa da 'ya'yansu wani abu ne wanda yake ba sabo ba a cikin al'umma. Wannan kuwa yana nuna cewa mabiya annabawa suna nuna kulawa ta musamman dangane da wadannan wurare, tare da gina gine-gine a kan kaburburansu suna kare su daga rushewa. A yanzu a kasashen Iraki, Palasdin, Jordan, Misra da Iran, akwai kaburburan annabawa (a.s) wadan aka yi gine-gine masu kawatarwa ta yadda kodayaushe mutane suna zuwa wurin domin ziyara. Sannan dakarun musulunci da su kai hare-hare don bude garuruwan Sham, sam ba ruwansu da wadannan kabuburan annabawa, ba ma haka ba kawai sun bar mutanen da suke hidima a wadannan wurare don su cigaba da aikinsu a wajen kamar yadda suke a da. Sannan ba su nuna rashin amincewarsu a kan hakan ba ko kankani. Idan da yin gine-gine a kan kaburburan annabawa wani aiki ne da ya haramta kuma ya shafi shirka, da wadannan dakaru da suka zo da umurnin khalifa domin bude wadannan garuruwa duka sun rusa wadannan gine-gine, amma koda wani dan karamin canji ba su yi ba ga wadannan kaburbura an cigaba da tafiyar da su kamar yadda suke kafin wannan lokaci. Sannan har zuwa yanzu wadannan gine-gine suna nan kamar yadda suke ta suke jawo hankalin al'ummar musulmi da ma duk mai bin addinan da Allah ya aiko da su.
Sannan a farkon zuwan musulunci ma musulmai sun rufe annabinsu a cikin dakinsa, kuma babu wani daga cikin wadannan musulmai da yake tunani cewa yin gini a kan kabarin Manzo haramun ne.
Sannan binciken littattafan tarihi da labaran tafiye-tafiyen masana addinin muslunci yana bayar da shedar cewa akwai daruruwan kaburbura a kasar da wahayi ya sauka da sauran kasashen musulmi:
1-Mas'udi wanda ya rasu 345Bh. wanda yake shahararren masanin tarihi ne, ga abin da yake cewa dangane da kaburburan imamai (a.s) da suke a "Bakiyya"yana cewa:
"A bisa kaburburansu a akwai dutse wanda aka rubuta: Da sunan Allah mai rahma mai jin kai, godiya ta tabbata ga Allah wanda yake kashe al'umma yake kuma raya matattu. Wannan shi ne kabarin Fadima "yar manzon Allah (s.a.w) wadda take ita ce shugabar matan duniya. Da kabarin Hasan Bn Ali Bn Abi Dalib da kabarin Ali Bn Husain Bn Ali Bn Abi Dalib da kabarin Muhammad Bn Ali Bn Husain Bn Ali Bn Abi Dalib da Kabarin Ja'farus Sadik Bn Muhammad".
Mas'udi ya kasance daga cikin masana tarihi na karni hudu Bayan hjira. 'Yan salafiya wadanda suke da kankamo sun tafi a kan cewa; wannan karni da karnonin da suke kafinsu su ne fiyayyun karnonin tarihin musulunci, sannan ayyukan da suka yadu a tsakanin musulmi a wannan zamani suna nuna kasantuwar abubuwan da shari'a ta yarda da su. Amma abin bakin ciki wannan babban dutse wanda Mas'udi yake fada wanda aka yi wannan rubutu a kansa, sakamakon rushewar da wahabiyawa suka yi wa "Bakiyya" yanzu babu shi a samuwa. Saboda haka yanzu wadannan kaburbura ba a iya bambance su.
Ibn jubair (540-614) shahararren mai yawo bude ido ya ziyarci kaburburan annabawa da bayin Allah a kasashen Misra, Makka, Madina, Iraki da Sham, yayin tafiye-tafiyensa kuma ya yi bayani a kan kowane daya daga cikinsu a cikin littafinsa na tafiye-tafiye, ta yadda dukkammu zamu iya samun wannan a cikin wannan littafin nasa. Ta hanyar karanta wannan littafin musulmi suna samun masaniya a kan tarihin gina hasumiyoyi da gine-ginen kaburburan annabawa da waliyyan Allah. Dangane da abin da ya zo a cikin wannan littafin tafiye-tafiye nasa shi ne: Tarihin gina manya-manyan gine-gine a kan kaburburan Imamai da waliyyai da shahidai a tafarkin Allah, wanda yake komawa zuwa ga zamanin sahabbai da tabi'ai. Wanda yake nuna yadda a wancan zamanin da musulmai suke nuna kauna da kulawarsu dangane da shugabanni da manyan addini. Ta yadda suka tashi domin gina wurare masu kawatarwa domin girmamawa gare su. Sannanbabu wani daga cikin sahabbai wanda ya nuna cewa wannan aiki yana komawa ne zuwa ga shirka ko kuma ya saba wa tauhidi da kadaita Ubangiji.
Kamar yadda Ibn Jubair ya fara tafiyarsa daga gaban duniyar musulunci (Andulus) zuwa yammacinta ta yadda kasar Misra ta kasance wuri mafi kusa gare shi, Sai ya fara da wuraren tarihin da suke a Misra musamman Alkahira. Zamu kawo wasu daga cikin abin da ya rubuta daga cikin wadannan gine-gine na musulunci a wannan kasa:

Gini Mai Girma Na Kan Imam Husain A.S A Alkahira
Wasu sun tafi a kan cewa an rufe kan Imam Husain (a.s) a garin Alkahira, saboda haka suka gina wani wuri da sunan "Ra'asul Husain" inda mutane suke zuwa ziyara daga cikin gida da waje. Masu sabon aure a wannan gari sukan je Masallacin Husain (a.s) wanda yake a wannan wuri sukan yi dawafi .
Ibn Jubair yana cewa: Daya daga cikin wurare masu tsarki a Alkahira shi ne Wurin da aka rufe kan Husain, an kawata wannan wuri da azurfa, wannan gini yana da girma da daukaka ta yadda harshe ba zai iya siffanta shi ba. A kan wannan gini akwai wani dutse na alfarma kai kace madubin Indiya ne, ta yadda yake haske yana dauko hutunan abubuwan da suke a gabansa.
Ya ce: Da idanuna na ga masu ziyarar Husaini (a.s) yadda suke kuka suna sumbatar yadin da aka dora a kan abin da aka rufe kabarinsa da shi suna neman tabarraki suna addu'a, ta yadda kwallarsu kamar ta rufe wannan kabari.
Ibn Jubair ya ambaci wani wuri da ake kira "Karafa" inda yake cewa yana daga cikin wurare masu ban al'ajabi kamar yadda ya bayyana akwai kaburburan annabawa da iyalan Manzo da sahabbansa da tabi'ai da sauran kaburburan manyan malamai da aka rufe a wannan wuri.
Dan Annabi Salih (Raubil) dan Annabi Yakub (Ishak) da matar Fir'auna dukkansu an rufe su ne a wannan wuri. Haka nan daga cikin iyalan Manzo akwai dan Imam Ja'afar mai suna kasim da dansa Abdullah Bn Kasim da dansa Yahya Bn Kasim, sannan da kabarin Ali Bn Kasim Bn Abdullah Bn Kasim da dan'uwansa Isa Bn Abdullah.
Ibn Jubair ya ambaci da yawa daga cikin 'ya'yan Ali (a.s) wadanda aka rufe su a can. Haka nan akwai kaburburan Sahabbai tabi'ai ba shuganni kamar Imam Shafi'i ta yadda yake magana a kan girma da matsayin haraminsa, kamar yadda yake cewa Salahuddin Al'ayubi shi yake biyan kudin da ake bukata domin gabatar da bukuwa a wannan harami na Imam Shafi'i.

Hasumiyoyi Masu Tsawo A Garin Makka
Ibn Jubair yana bayyana yadda garin Makka ya kasance da hasumiyoyi masu daukaka a kan kaburbura a garin Makka, wanda ambatonsu a nan zai janyo mu tsawaitawa. Akwai wurare kamar Maulidin Nabi, Maulidin Zahara da Darul Khaizaran (wurin ibadar Manzo na sirri).
Sannan ya ambaci wurare masu girma na sahabbai da tabi'ai a Madina, A cikin wannan kuma yake ambatar Raudhar Abbas Bn Ali Bn Hasan Bn Ali (a.s) wanda yake da gini mai tsayi a garin Madina. Sannan ya cigaba da bayyana yadda wadannan wurare suke.
Idan muna so mu fadi duk abubuwan da Ibn Jubair ya gani a garuruwan Sham da Iraki na sahabbai da manyan bayin Allah zai janyo mu tsawaita a cikin hakan, don haka muna iya wadatuwa da wannan. Saboda haka wanda yake so ya samu Karin bayani sosai a kan haka sai ya koma zuwa ga wannan littafi na sa.
Ibn Najjar (578-643) Muhammad Bn Mahmud wanda aka fi sani da Ibn Najjar wanda yake shi ma shahararren musulmi mai yawon shakatawa ne a cikin littafinsa "Madinatur Rasul" yana cewa:
"Akwai wata dadaddiyar hasumiya mai tsawo a farkon makabartar "Bakiyya"wadda take da kofofi guda biyu wanda kowace rana ake bude daya daga cikinsu domin masu ziyara.
Wadannan suna daga cikin littattafan tafiye-tafiye da muka dauko daga cikinsu, sannan ana iya komawa zuwa ga wasu littattafai na tafiye-tafiye wadanda suke tabbatar da yin gine-gine a kaburburan annabawa da bayin Allah wani abu ne da yake sannane kuma wata Sunna ce mai tsawon tarihi a tsakanin masu kadaita Ubangiji.
Ibn Hajjaj Bagdadi (262-392) wanda yake mawaki ne shararre a iraki ya yi wata kasida ta yabon Imam Ali (a.s), sannan ya yi wannan kasida ne a haramin Imam Ali (a.s) acikin taron mutane, a farkon wannan kasida ga abin yake cewa: "Ya kai ma'abocin wannan hasumiya fara a garin Najaf duk wanda ya ziyarce ka kuma ya nemi ceton Allah daga gareka to Allah zai karbi cetonsa".
Wannan baiti yana nuna cewa kabarin Imam Ali (a.s) a farkon karni na hudu ya kasance yana da hasumiya.
Abin mamaki a nan shi ne a mahangar ilimin Usul fikh haduwar mutane a kan hukuncin wani abu har zuwa karnoni da dama yana nuna ingancin wannan abin ne. Amma muslmi sun hadu a kan ingancin gine-gine a kan kabarin annabawa da waliyyan Allah tsawon karnoni masu yawa, amma mahangar wasu wannan bai isa ya zama dalili ba, ta yadda kowane lokaci suna kokarin kaucewa a kan yarda da wannan al'amari.

Gine-Ginen Tunawa Da Bayin Allah Da Dalilai Masu Sabani A Kan Haka
Mun yi bincike a kan dalilan da suke nuni da ingancin ziyar da girmama kaburburan bayin Allah daga Kur'ani da Sunna da tarihin magabata, amma yanzu lokaci ya yi da zamu yi bincike a kan dalilan masu inkarin hakan. Wanda sukan yi riko da hadisin Abil Hayyaj Asadi ne a kan hakan, yanzu zamu auna wannan hadisi ta yadda zamu ga kimarsa ta hanyar ma'aunin da ake gane ingancin hadisi.
Muslim a cikin sahih dinsa yana ruwaitowa daga Abil Hayyaj kamar haka: "Ali bin Abi Dalib ya ce da ni: Ba na aike ba akan abin da Manzo ya aika ni a kansa ba, kada kabar wani hoto sai ka lalata shi, ko wani kabari mai tudu sai ka daidaita (baje) shi".
Masu adawa da wannan al'amari suna kafa dalili ne da wannan hadisin a kan haramcin gina haramin wani Imami daga cikin Imamai (a.s) sakamakon haka ne a shekara ta 1344Bh suka rusa makabartar "Bakiyya" a wannan rana ne kuma a cikin jaridar "Ummul kura" aka sanya tambaya da amsa dangane da dalilan da suka sanya aka rusa wannan makabarta, domin mu gane ta yadda a ka kafa hujja da wannan hadisi yana da kyau mu yi bincike a kan ma'ana da kuma dangane wannan hadisi:

A-Sanadin Wannan Hadisi
Maruwaitan wannan hadisi su ne kamar haka: 1-Waki 2-Sufyanus sauri 3-Habib Bn Abi sabit 4-Abu wa'il 5-Abu hayyaj Asadi.
Dangane da maruwaici na farko kuwa abin da Ahmad Bn Hambal wanda malaman hadisi ne yana cewa dangane da shi ya wadatar da mu inda yake cewa: Waki ya yi kuskure a cikin hadisai guda 500 . Sannan ya cigaba da cewa: Ya kasance yana ruwaito hadisi da ma'ana (ba tare da kiyaye lafuzzan da aka yi amfani da su ba) Sannan ba shi da cikakkiyar masaniya a harshen larabci.
Dangane da maruwaici na biyu kuwa (Sufyanu sauri) Ibn hajar Askalani ya ambace shi da cewa yana yin "Tadlis" a cikin hadisi. An ruwaito daga Ibn Mubarak cewa, Sufyanus Sauri ya kasance yana ruwaito hadisi yana yin "Tadlis" a lokacin da na iso sai ya ji kunya akan abin da yake yi . Kuma duk yadda aka fassara ma'anar tadlis ba ya dacewa da adalci.
Dangane da maruwaici na uku kuwa, Habib Bn abi Sabit, Ibn Hibban ya ruwaito daga Ata yana cewa: Ya kasance yana tadlis a cikin hadisi, don haka ba a bin hadisinsa,
Amma mai ruwaya na hudu kuwa, wato Abu wa'il wanda sunan shi Shakik Bn Salma Asadi Kufi, ya kasance abokin adawar Ali Bn Abi Dalib ne, Ibn Abil Hadid yana cewa: Ya kasance daga cikin masu sabani da Imam Ali (a.s) Lokacin da aka tambaye shi Ali kake so ko Usman, Sai ya ce: wani lokaci Na kasance Ali amma yanzu Usman.
Sai dangane da maruwaici na biyar wato Abu Hayyaj Asadi wanda sunansa Hayyan bin Husain, Tirmizi yana kauce wa ruwaito hadisi daga gare shi, haka nan Ingantattun Littattafan hadisai guda biyar ban da wannan ruwayar ba su ruwaito komai daga gare shi.

B- Dangane Da Ma'anar Wannan Hadisi
Dangane da kirkirar wannan hadisi na Abu hayyaj kuwa kamar yadda muka gani a sama a fili yake abin, domin kuwa maruwaita wannan hadisi ta yadda ake tuhumar su yin tadlis da kuskure wajen ruwaya. Saboda haka ba za a iya dogara da shi ba wajen kafa dalili na shari'a. Koda an runtse ido daga raunata maruwaita wannan hadisi, ma'anarsa ba tabbatar da wannan ma'ana. Saboda haka domin bayyanar da wannan al'amari ta hanyar bayyanar da wasu kalmomin don fahimtar ma'anar wannan hadisi. 1-"Kalmar Kabran musharrafan" 2-"Illa sawwaitahu" wadannan kalmomin sune suka zo a cikin wannan hadisi.
Dangane kalma ta farko zamu bayani ne a kan kalamar "musharraf" wadda take da ma'anar daukaka wato abu madaukaki. Don haka ne wadanda suke daga babban gida kamar iyalan Manzo ake kiransu da sharifai, sannan tozon rakumi saboda kasantuwarsa yana da bisa a kan sauran jikinsa ana kiransa da "Sharaf".
Ya zo a cikin Tajul Arus cewa: Sharaf ma'anarsa shi ne wani wuri mai bisa wato madaukaki. Sannan ana kiran tozon rakumi da sharaf, Sannan wurare masu bisa kamar gidajen sarakuna ana kiransu da Sharaf, Haka nan akan kira tudun da yake a kan bangaye da wannan kalma.
Saboda haka wannan kalma tana nufin abu mai daukaka ko kuwa kawai tana nufin tozon rakumi ko bayan kifi?.
Tare da kula da ma'anar kalmar "Sawwaitahu" kamar yadda zamu yi bayanin a kanta zamu fahimci cewa wannan kalma ta Sharaf a cikin wannan hadisi tana nufin ma'ana ne ta musamman.
Dangane da kalma ta biyu kuwa muna iya bayani kamar haka: Kalma ta Sawwaitahu da ta zo da ma'anar aiki wato baje wani abu ko dai-daita shi, ana mafani da ita a cikin harshen larabci da ma'anoni guda biyu.
1-Daidaita wani abu da wani abu daban ta hanyar tsawo ko girma ko makamancin haka, saboda haka idan da wannan ma'ana kalmar sawwa ta zo tana da aikau guda biyu (maf'ul) wanda a cikin harshen larabci wannan maf'ul na biyu yana bukatar harafin jarra wanda zai dai-daita wannan abin da waninsa.
2-Ma'ana ta biyu kuwa shi ne baje wani abu ta yadda zai daidaita babu tudu da kwari, saboda haka a nan wannan fi'ili na sawwa yana bukatar maf'uli guda daya, ba shi bukatar na biyu. Saboda haka duk lokacin kafinta ya daidaita wani katako, kawai zai ce na goge katako, (wato sawwaitul kashab).
Saboda haka bambanci wannan ma'anoni guda biyu a bayyane yake, wato a ma'ana ta farko siffa ce ta abubuwa guda biyu, amma a ma'ana ta biyu kuwa siffa ce ta abu guda (wato daidaita wani abu ba tare da an hada shi da waninsa ba kamar yadda muka gani).
Saboda haka yanzu mun fahimci ma'anonin wadannan kalmomi guda biyu wato "Sawwaitahu da musharrafan". Don haka muna iya fahimtar cewa wannan hadisi yana magana ne dangane da yadda wannan kabari yake domin kuwa yana magana ne a kan abu guda, ba wai kabari ba da kasa (wato ba a dai-daita shi da kasa ba wato a dai-daita shi kansa kabarin) Domin da haka ake nufi sai a ce "sawwaitahu bil ard". Saboda haka abin da Imam yake nufi a cikin wannan hadisi shi ne, duk inda ya ga wani kabari yana da tudu da kwari kamar tozon rakumi ya dai-daita shi ya gyara shi ya zama kamar dakali. Saboda haka wannan hadisi yana nuna mana yadda za a yi kabarin musulmi ta yadda za a baje samansa ba a yi masa tulluwa ba kamar bayan rakumi ko kifi.
Domin kuwa wannan zamani a kan yi kaburra ne da tudu kamar yadda bayan rakumi yake, don haka ne Imam ya ba Abu hayyaj umarni da ya daidaita duk kabarin da ya gani a haka. Saboda haka wannan hadisi wace alaka yake da shi wajen rusa shi kansa kabari ko ginin da aka a samansa?!
Kuma cikin su maruwaitan wannan hadisi da masu sharhinsa sun bayyana ma'anar wannan hadisi kamar yadda muka yi bayani a sama.
1-Muslim ya ruwaito wannan hadisi karkashin babin "Amr bi taswiyatul Kubur" wato ruwayoyin da suke magana a kan daidaita saman kabari, saboda haka muna iya cewa shi ma Muslim abin da ya fahimta da ma'anar wannan hadisi kenan (wato kasantuwar kaburbura kamar yadda dakali yake ba kamar yadda bayan rakumi yake ba).
2-Muslim a farkon wannan babi ya ruwaito cewa: Fudhala tare da wasu mutane sun kasance a Rom, Sai wani daga cikin mutanensa ya rasu sai ya rufe shi ya yi kabarinsa kamar yadda ake dakali (Rectangle) sai ya ce haka na ji daga Manzo (s.a.w) ya ce: Ku yi kaburbura kamar haka wato samansu a baje ba tare da tudu ba.
Saboda haka dukkan wadannan hadisai suna bayyanar mana da ma'anar Kalmar Musharrafan da ta zo a cikin hadisi, ba tana nufin kasancewar kabari ya yi bisa ba daga kasa ko kada ya yi, tana nufin shi kansa kabarin kada ya kasance yana da tudu kamar bayan rakumi.
3-Nabawi kan sharhin wannan hadisi yana cewa: Bai kamata ba kabari ya yi bisa da kasa ba ko kuma ya zamana ya yi tudu kamar bayan rakumi. Ya cigaba da cewa dole ne bisansa ya kasance kamar kamun hannu guda sannan samansa ya zamana a baje ba mai tudu ba.
4-Kurdabi acikin tafsirinsa ya ruwaito wannan hadisi da a ka ambata yana cewa: Wannan hadisi abin yake nunawa shi ne baje kabari shi ne Sunna, sannan yi masa tulluwa bidi'a ne.
5-Ibn Hajar askalani bayan ya yi bayani a kan mustahabbancin baje saman kabari yan rubuta cewa: Hadisin Abi Hayyaj ba yana nufin cewa ba a baje ya zama daidai da kasa, abin da yake nufi shi ne a baje saman kabari ta yadda za a daidaita shi babu wani tudu a samansa, duk da yake cewa ya dan yi sama da kasa.
Kamar yadda wasu ba su ba wannan bayani muhimmanci ba, (mu dauka ma wannan hadisi yana nufin cewa a baje kabari ta yadda zai zama daya da kasa babu wani tudu) kafa hujja da shi a kan rusa gine-ginen da aka yi a kaburburan bayan Allah, zai fuskanci matsaloli guda biyu:
1-Baje kabari ta yadda zai zama daya da kasa babu wani tudu ya sabawa dukkan ra'ayin fukaha domin kuwa dukkansu sun tafi a kan haka din cewa mafi karanci tashinsa ya kai kamun hannu guda.
2-Idan muka dauka cewa wannan hadisi yana nufin cewa a baje kabari ta yadda zai zama daidai da kasa, to dole ne mu rusa kabari ta yadda zai zama daya da kasa, ba wani gini da aka yi ba a saman kabarin. Saboda haka sam wannan hadisi ba yana magana ba ne a kan ginin da yake kan kabari yana magana ne a kan shi kansa kabarin!
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012

Ku yi bayanin Ra'ayinku

Ra'ayoyi Masu Dubawa

Babu wani Raayi
*
*

Muassasar alhasanain (a.s)