Hakikar Mutuwa1
Hakikar Mutuwa1
WALLAFAR: JA'AFAR SUBHANI
Rayuwa Bayan Mutuwa
Mawallafi: Ayatullahi Ja'afar Subhani
Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani
Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id
Sanin makomar mutum bayan mutuwa yana daya daga cikin abubuwan da mafi yawan mutane suke so su sani, sannan mafi yawa suna so su san hakikanin al'amarin mutuwa menene ita?
Shin mutuwa shi ne karshen rayuwa, ta yadda fitilar rayuwar mutum zata dushe da zarar ya mutu, wato bayan mutuwa babu komai sai rashi? Ko kuwa mutuwa wata kofar shiga wata duniya ce wacce take tafi wannan duniyar daraja da haske, kuma hakikanin al'amari ma shi ne, mutum ya tsallake wata gada ce ta yadda ya fadacikin wata sabuwar rayuwa?
A hakikanin gaskiya muna iya kasa batutuwan falsafa zuwa gida biyu kamar haka:
1-Batutuwan da suke masu zurfi wadanda kawai sai wadanda suka yi zurfi a cikin wannan fannin na falsafa, Su ne kawai zasu iya yin tunani har su bayar da ra'ayi dangane da hakan.
2-Batutuwan da suka shafi kowane mutum, ta yadda kowane mutum yana so ko yana tunani a kansu, wadannan kuwa sun hada da abin da ya shafi batun rayuwa bayan mutuwa.
Haka nan batun abin da ya shafi kaddara duk da cewa Bahasi ne na falsafa amma kuma ya shafi kowane mutum wato kowa yana so ya san menene hakikanin wannan al'amari. Duk da cewa ba tunanin kowa bane yake iya gane hakikanin al'amura, amma masana falsafa wadanda suke zurfafa tunaninsu suna iya gano hakikanin al'amura ta hanyar tunaninsu.
Sanin abin da zai faru bayan mutuwa ya kunshi wasu batutuwa guda uku da suka shafi mutum kamar haka:
1-Shin menene hakikanin dan Adam, wannan jikin nasa shi kawai ne babu wani abu bayan wannan, ko kuwa hakikanin mutum wani abu ne daban ba jikinsa ba sai dai yana da alaka da jikinsa.
2-Menene hakikanin mutuwa, shin mutuwa shi ne karshen rayuwa ko kuwa wata kofa ce ta shiga wata sabuwar rayuwa a wata duniya?
3-Idan mutum ya mutu ba shi ne karshen rayuwarsa ba, mecece alakar da take akwai tsakanin wannan rayuwar da waccan rayuwar?
A nan zamu yi magana ne dangane da wadannan muhimman batutuwa guda uku:
Asali Na Farko
Menene hakikanin dan Adam?
Shin hakikanin dan Adam ya takaita ne kawai ga jikinsa, ko kuwa wannan jikin ya rufe wani abu ne wanda shi ne hakikanin mutum? Da wani kalamin shin wai hakikanin mutum wannan jikin ne kawai babu wani abu wanda ake kira "ruhi"? Ko kuwa bayan wannan jikin akwai wani abu wanda shi ne hakikanin dan Adam, wannan jikin kawai yana matsayin na'ura da yake amfani da ita ne?
Amma wadanda ba su yi imani da wani abu sai wanda kawai muke iya gani ko muke iya tabawa da makancinsu ba, Suna goyon bayan ra'ayi na farko ne wato hakikanin mutum bai wuce wannan jikin nasa ba. Ruhi a wurinsu bai wuce daidaitar gabobi ba, wato ruhi kawai sakamakon aiki da karbar aiki ne tsakanin gabobi, bayan wannan babu wani abu daban mai suna ruhi. Ruhi ya samu ne ta hanyar haduwar gabobi ta yadda mutum yake ji yake gani, saboda haka dukkan wannan babu wani abu daban wanda ba jiki ba. Haka nan sakamakon haduwar gabobi mutum yake ji yake gani, fushi da farin ciki, so da kiyayya da dai sauransu!
Saboda haka ruhi a wajen wadannan ba wani abu ne ba sai kawai abin da yake faruwa sakamakon haduwar jiki, ba wai wani abu ba ne wanda yake daban da jiki ba. Duk da cewa ma'abuta addini sun yi imani da cewa akwai wani abu mai suna ruhi wanda kuma yana da alaka da wannan jiki.
Bahasi a kan dalilan masu inkarin ruhi da dalilan suke kawowa da raddi a kan wannan tunani ba zamu iya kawo su ba a cikin wannan 'yar karamar kasida ba , saboda haka a nan kawai zamu takaita ne da dalilan da malaman akida suke kawowa a kan hakan.
Malaman akida na muslunci suna bayyanar da hakikanin mutum ta cewa mutum bai takaita ba ga wannan jikin kawai, domin kuwa akwai wani abu bayan wannan kuma shi ne hakikanin dan Adam, kuma yana da wata alaka da wannan jikin, suna da bahasi mai fadi a kan haka sannan sun kawo dalilai guda goma da suke tabbatar da wannan da'awa ta su. Amma a nan zamu wadatu ne kawai da wasu daga cikinsu wadanda suka fi zama bayyanannu kuma kusan kowa zai iya gane su ya kuma yarda da su, sannan ana iya gwada su domin tabbatarwa.
1-Kalmar "Ni" wato "I" a cikin harshen turanci
Wannan kalma wacce kowa yake nuni da kansa da ita yayin da ya aikata wani abu, kamar ya ce; na ce, na tafi, na gani, na ci, na sha. Ba ma kawai ya takaita a nan ba, mutum yakan jingina dukkan gabobinsa zuwa ga wannan kalma yana cewa; kaina, zuciyata hannuna da dai sauransu…
Wani lokaci ma mutum yakan jingina dukkan jikinsa zuwa ga wannan kalma, yana cewa jikina, wannan al'amari na jingina ayyuka da gabobi da ma dukkan jiki ga wannan kalma ta "ni"to lallai zai zama ba jiki ba ne domin kuwa mutum ya jingina dukkan jikinsa zuwa gare shi wanda yake nuna wani abu ne daban.
Saboda haka a cikin kowane mutum akwai wannan hakika ta "ni" wacce kuma ita ba jiki ba ce. Wannan kuma shi ne hakikanin Mutum, Idan kuwa muka yi inkarin wannan abu wanda yake a fili, to dole ne ya zamana abubuwan da muka ambata a sama babu inda aka jingina su, tunda babu wannan hakika ta "ni". Saboda haka tunda wannan hakika tana sama da jiki, don haka ita ba jiki ba ce wani abu ne daban wanda ba jiki ba. Duk da cewa yana da alaka da wannan jiki.
2-Kasantuwar mutum ba ya canzawa
Wata sheda ta biyu wacce take tabbatar da samuwar ruhi wanda yake daban da wannan jiki ita ce, Mutum tun daga farko rayuwarsa kowane lokaci cikin canzawa yake, amma akwai wata hakika wacce take ita ba ta canzawa a duk tsawon zamani.
Da wata ma'ana matakan rayuwar mutum suna farawa ne daga yarinta, bayan wani lokaci zai wuce zuwa samartaka har zuwa tsufa, ta yadda duk zai tamuke, amma akwai wata hakika wacce duk tsawon wannan zamani da matakai tananan a tabbace kuma dukkan wadannan abubuwa suna bi takansa ne. Ta yadda mutum zai ce "wata rana na kasance yaro, wani lokaci kuma matshi, yanzu kuma na manyanta na tsufa". Duk da cewa mutum ya samu cikakken canji a jikinsa, amma akwai wata fuska inda bai canza ba, ta yadda yana jin cewa duk wadannan matakai sun bi takan wannan hakika ne. Idan da hakikanin mutum ya kasance wannan jikin nasa ne, ba zai taba samun wannan tabbatuwa ba da ya samu ta wata hanya, (Inda yake jin cewa shi ne lokacin da yake yaro yanzu ma shi ne bayan ya tsufa) domin kuwa dukkan jikinsa ya canza saudayawa, ta yadda a bisa wannan hanya ta rayuwa ya kasance da jiki daban-daban. Saboda haka hakinin mutum ba zai yiwu ya takaita ba a jikinsa wanda yake duk bayan lokaci yana canzawa, tabbas a bayan wannan jikin mai canzawa akwai wani abu wanda shi ba jiki ba ne, ta yadda kodayaushe yana nan ba tare da canji ba kamar yadda jiki yake samun canji, sannan ya zamana yana karbar canjin da jiki yake samu a kodayaushe. Sannan ya ci gaba da tafiyarsa har ya kai inda yake so ya kai.
Idan muna so mu yi bayanin wannan al'amari wanda ake iya gwada shi domin tabbatarwa yana iya kasancewa kamar haka:
1-Mutum yana jin wani abu tare da shi wanda kowane lokaci ba ya canzawa wannan kuwa shi ne "ni"
2-Dukkan kwayoyin halittar jikin mutum bayan shekara takwas suna canzawa baki dayansu.
Saboda haka wannan kalma ta "ni" ba jiki ba ce, wani abu ne daban ba jiki ba, domin kuwa idan da hakikanin mutum jiki ne, babu yadda mutum zai rika jin wannan hakika tsayyya wacce yake jingina al'amuransa gareta. Sannan ba zai yiwu ba kotu ta hukunta mutumi dan shekara 40 ba, wanda ya aikata laifi tun yana dan shekara 20, domin kuwa wannan jikin ba shi ne yanzu ba, saboda ya canza dukkan shi, yanzu wani mutumne na daban!
3-Rashin mantawar mutum da kansa yayin da yake mantawa daga dukkan jikinsa. Mu dauka cewa mutum yana cikin wani lambu wanda yake da yanayi mai dadi ta yadda babu sanyi ko zafi mai matsawa, ko kuma iska wanda zai janyo karar ganyen itatuwa, ko tsuntsaye masu kuka ta yadda zasu ja masa hankali, Sannan babu karar komai wanda zai iya zuwa ga kunnuwansa. Wato akwai cikakkiyar natsuwa a wannan wuri ta yadda babu wata matsala ko wani abin damuwa, a wannan lokaci mutum ya yi kokari ta yadda zai yanke tunaninsa ga komai sai kansa, a hankali har ya manta da dukkan gabobinsa, a wannan lokaci zai kasance cikin wata irin mantuwa ta gaba daya, amma akwai wani abu guda wanda bai manta da shi ba, wannan kuwa ba wani abu ba ne hakikanin kansa, sam ba zai manta da kansa ba, duk da cewa ya manta da dukkan gabobinsa, wannan hakika ita ce wacce mutum duk cikin halin da ya shiga ba zai manta da ita ba, saboda haka wannan abu wani abu ne daban wanda ba jiki ba, domin kuwa duk abin da yake daga jikinsa yana cikin kogin mantuwa.
A cikin bayanin wannan hujja babu bukatar doguwar gabatarwa, wato ana iya yin bayaninta a takaice, wannan kuwa shi ne kamar haka cewa, wani lokaci mutum yakan shiga cikin zurfin tunani ta yadda zai manta da komai koda kuwa wani muhimmin abu zai faru a kusa da shi ba zai kula da abin da yake faruwa ba, amma a wannan lokaci ba zai manta da wani abu guda ba, wannan kuwa shi ne kansa. Wato shi mutum ne da yake cikin halin tunani, wannan kuwa shi ne yake bayyanar da hakikanin dan Adam, abin da yake bayan jikinsa da gabobi, wadanda suka kasance ya gafala da su a cikin halin da ya shiga na tunani kamar yadda muka yi bayani a baya.
4-Hakikanin ruhi a ilimin kimiyya
Zuwa yanzu mun fahimci wata hakika wacce ita ba jiki ba ce mai suna ruhi. Abubuwan da muka ambata a baya kuwa duk sun kasance cikin abubuwa wadanda za a iya gwadawa domin tabbatar da cewa lallai ruhi wani abu ne wanda ba jiki ba (mujarrad) Sannan mafi yawan mutane suna iya fahimtar wannan sannan ya haifar musu da yakini a kan wannan magana.
Amma yanzu domin mu kammala wannan bahasi bari mu koma ga wata kungiya wacce aka kafa ta ilimi a karni na sha tara wacce ta fara da sanin hakikanin dan Adam, ta yadda idan ra'ayin falsafa da ilimin gwaje-gwaje (Science) sun bayyanar da wannan al'amari sannan sai mu koma zuwa ga al'Kur'ani da Sunna domin mu ga hukuncin da zasu yi a kan al'amarin.
A shekara ta 1882 an kafa wata kungiya mai suna "kungiyar bincike a kan ruhi'wacce Babban masanin nan kuma malamin jami'ar Kambirij (Cambridge) mai suna Jomik yake jagoranta wannan malami ya kasance daya daga cikin masanan kasar Birtaniya.
"Yan wannan kungiya kuwa sun hada da mutumin nan da ake yi wa lakabi da suna Darwin, Wiliam wanda yake babban malamin kimiyya ne na kasar Engila, Fedrik, Hursen wadanda suke malaman Jami'a ne a Kasar Amurika Da sauran manyan masanan kimiyya shararru na duniya…
Wannan gungu na masana suka ci gaba da bincike a kan al'amarin ruhi, suka kuma rubuta littafai a kan hakan, ta yadda a cikin shekaru 45 zuwa 50 suka rubuta littafai kusan hamsin a kan wannan magana da muka ambata a sama. Ta yadda sakamakon taimakonsu ne aka warware matsaloli da yawa a kan abin da ya shafi haka.
A hakikanin gaskiya Allah madaukaki ya bude wasu hanyoyi na ilimi a wannan zamani ta yadda dan Adam zai iya fahimtar cewa mutum yana da wani bangare wanda ba jiki ba ne kuma wajen ci gaba da rayuwarsa yana iya amfani da wannan shi kadai don ya ci gaba da rayuwa.
Ilimin da ya shafi alaka da ruhi wanda a wannan zamani wato karni na sha tara aka kirkire shi, ya yaye hijabi zuwa wata duniya wacce ba wannan ba, ta yadda ya bai wa mutum dama ta yadda zai iya alaka da waccan duniya.
Ta bangaren abubuwan da aka tabbatar daga duniyar ruhi ta hanyar kirawo ruhi, yana iya ba da sakamako a kan cewa, lallai bayan wannan duniya ta jiki akwai wata duniyar wacce ba ta jiki ba. Sannan kuma tabbas ba zai gushe ba sakamakon mutuwa, don haka alakar da take akwai tsakanin ruhunan mutanen da suka mutu da mutanen da suke rayuwa a wannan duniya yana tabbatar da cewa lallai ruhuna sunanan bayan mutuwa.
Wannan bahasi kuwa har zuwa yanzu yana ci gaba a yammacin duniya, saboda haka wanda yake ganin kimar abin da ya zo daga kasashen turai yana iya amfani da wannan domin ya kara samun tabbas a kan samuwar wata duniya wacce ba wannan ba.
Da wannan ne bayan mun yi bayani a kan ra'ayoyin masana kimiyya dangane da wannan magana a yanzu zamu koma zuwa ga Kur'ani domin muga hukuncinsa a kan hakan, sannan muga yadda Kur'ani yake bayyana hakikanin dan Adam.
Kur'ani Yana Tabbatar Da Ruhi Ba Jiki Ba Ne
Ayoyi da dama a cikin Kur'ani suna bayar da shedar cewa ruhi ba jiki ba ne kuma ba shi da duk wasu alamomi na jiki, ta yadda yake nuna cewa hakikanin mutum bai takaita ba ga wannan jiki. Ba ma kawai haka ba, domin kuwa wannan jiki bai wuce wata na'ura ba wacce mutum yake amfani da ita, saboda haka hakikanin mutum shi ne ruhinsa. Ayoyin da suke magana kuwa a kan hakan suna da yawa, amma a nan zamu kawo wasu ne daga ciki a matsayin misali:
1-Daukar rayuka yayin mutuwa:
A nan Allah madaukaki yana tunatar da mutum cewa yana daukar rayukan dan Adam yayin mutuwa da barci, saboda haka wanda yake lokacin mutuwarsa bai riga ya zo ba, sai a mai do masa ransacikin jiki. Kamar yadda yake cewa:
"Allah yana daukar rayuka yayin mutuwa da lokacin barci, wadanda mutuwarsu ta zama tabbas sai a rike ruhinsu, amma wasu rayukan a kan rike su ne zuwa wani lokaci (masu barci), a cikin yin hakan akwai aya ga masu tunani"
Kalmar "Tawaffa" wacce ta zo a cikin wannan aya tana nufin kama abu ne baki dayansa ba tana nufin kashewa ba. Saboda haka zuwan wannan kalama yana nuna cewa a lokacin mutuwa da barci akwai wani abu wanda ba jiki ba wanda Allah madaukaki yakan dauke shi. A wannan lokaci rayukan wadanda mutuwa ta zama tabbas a kansu sai ya rike ruhinsu, Sannan kuma yakan saki rayukan wadanda mutuwa ba ta kai ga zama tabbas ba a kansu, wato lokacin mutuwarsu bai riga ya iso ba, sai ya mai da musu rayukansu, ta yadda zasu ci gaba da shugabancin jikunnansu da shi. Saboda haka idan har da jikin mutum shi ne hakikarsa to amfani da kalmar "Akz, irsal da Imsak" wadanda suke da ma'anonin dauka, aukawa da rikewa, zasu zama ba su da ma'ana a nan. Domin kuwa suna iya zama sun dace da ruhi amma ba su dace ba da jiki a nan, domin kuwa yayin da mutum yake barci ko ya mutu muna iya ganin ransa bai tafi ko'ina ba.
2-Hakikanimmu yana wurin Allah
Kur'ani mai girma ya dauka daga abin da mushirikai suke cewa yayin da suke inkarin tashin kiyama yana cewa:
"Yanzu bayan jikin ya lalace a cikin kasa sannan a ce za a sake tayar da mu"? Wato a cikin wannan aya suna cewa yayin da mutum ya mutu kuma jikinsa ya lalace ya koma kasa, to sam ba zai yiwu ba a sake harhada shi sannan a tayar da shi.
Jawabin da Kur'ani yake baiwa mushrikai kuwa a kan wannan magana tasu yana karfafa abin da muka fada, inda yake cewa, hakikaninsu ai a wajenmu take, wato wannan abin yake lalacewa ya kuma koma kasar ba shi ne hakikaninsu ba. Ga abin da Kur'ani yake cewa: "Ka gaya musu ana horon mala'ikan mutuwa da kama rayukanku, wanda kuma aka wakilta shi akanku, a wannan lokaci zaku koma zuwa ga ubangijinku".
Kamar yadda muka ambata a ayar da ta gabata cewa kalmar "Tawaffa" ba tana nufin kashewa ba ne, wannan kalma tana nufin dauka kokamawa ne, saboda haka wannan yana nuna cewa mutum bayan mutuwa yan kasuwa ne zuwa gida biyu:
A-Jikin mutum wanda yake a fili, wanda sakamakon dadewa a cikin kasa zai lalace ya yi dai-dai a cikin kasa.
B-Hakikanin dan Adam wanda ake nuni da shi a cikin wannan aya kuma wanda mala'ika zai dauka, yana wurin Ubangiji kuma ba zai taba lalacewa a cikin kasa ba.
A hakikanin gaskiya wannan aya tana ba da amasa ne dangane da wata hujja ta ilimin kimiyya, wannan kuwa ita ce: Wannan abin wanda yake lalacewa a cikin kasa, ba wani ba ne illa abi ya rufe hakikanin mutum, amma abin da yake shi ne hakikanin dan Adam yana hannun mala'ikan mutuwa, sannan kuma za kasance a wurin Allah ba tare da ya lalace ba. Wannan kuwa yana tabbatar mana da cewa hakikanin dan Adam ba wannan jikin ba ne wanda yake lalacewa a cikin kasa, hakikaninsa wani abu ne daban wanda yasha bamban da jiki, sannan duk wasu siffofin jikin ya nisanta daga gare su, (Saboda haka kamar abin da ya shafi rubewa ko lalacewa da bata a cikin kasa duk ya koru a gare shi).
Saboda haka ayoyin da muka ambata a baya da abubuwan da suka zo a cikin ilimin kimiyya duk suna tabbatar da cewa hakikanin dan Adam ba wannan jikin ba ne wanda zai iya lalacewa a cikin kasa. Hakikanin dan Adam wani abu daban ne wanda yake saman wannan jiki, wanda kuma ba ya canzawa, kowane lokaci yananan a tabbace ba tare da wani canji ba.
Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com - www.hikima.org - www.haidarcip.org
Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)
Facebook: Haidar Center - December, 2012